x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - SHIMA DA NE free pages

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 65957 words

Category: Love Stories

Views 227

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Abba shiru yayi yana kallon yaron, ji yake yaron yana shiga zuciyanshi, yaji kamar ɗanshi ne na cikinshi, bai taɓa samun wanda ya taimaka mishi gadan gadan ya sadaukar da ranshi ba sai wannan yaron, a hankali yace "ya sunanka?"
yace "nawal"
jinjina kai yayi sannan yace "nawal dan Allah ka faɗamin gaskiya kaga an cutar dani na yadda da mutum ya cutar dani wanene kai? kuma meyasa ka taimakeni?"
shiru yayi yana tsoron bashi amsa, ya riko hanun nawal yace "na rantse da mamana kuma na rantse da babana na rantse da kaina koda ka faɗamin kai wanene ba zan cutar da kai ba zan zauna da kai koda kai ɗin wanene koda ko kai ɗin makiyina ne"
ya kalleshi da mamakin irin rantsuwan da yayi, yace "haramun ne mutum yayi rantsuwa da wani wanda ba Allah ba, haramun ne kayi rantsuwa da mamanka ko babanka babu abinda zaka rantse dashi sai Allah sai kuma alkur'ani, rantsuwa da wani shirka ne"
shiru Abba yayi yana kallonshi, babu wanda ya taɓa mishi gyara koda ya aikata kuskure kowa yana tsoron gyarashi sabida yanada kuɗi yanada matsayi, yace "na gode"
nawal yayi murmushi sannan yace "sunana nawal rahama"
Abba yace "okay daga ina kake?"
yace "daga kauyen gombe"

"meya kawoka Abuja?"
yace "aikin gadi nakeyi a gidan Alhaji Alhasan medara"
shiru Abba yayi, kana yace "naji yana waya ne bai san ina jinshi ba naji duk plan ɗin da sukayi shiyasa naje wajen domin na taimakawa wanda suka shiryawa mugunta"
Abba yace "nawal na yadda da Ahlam harna faɗa mishi wasu sirrikana da suka shafi rayuwa ta, na bashi amanan yarana ya zama shine me kula dasu idan bana gida ashe shi ɗin yaron makiyina ne, nawal babu wanda ya tsaneni nima na tsaneshi kamar Alhaji Alhasan ko ganin juna bama son yi, ashe Ahlam dana yadda dashi Ahlam da yake shiga duk inda yaga dama a gidana ɗanshi ne"
sukayi shiru babu wanda ya kara magana, dr ne ya shigo ya duba Abba ya kara mishi allura, saida ya fita Abba yace "nawal"
a nitse yace "na'am"
"zaka iya aiki dani? ina nufin zaka iya zama personal bodyguard ɗina? zaka rinƙa bawa ƴaƴana mata guda biyu da ɗana namiji ɗaya kariya ka rinƙa kaisu makaranta da kuma duk inda ya kama zasu je? Idan ka yadda zan baka matsayin p.b a gidana wato personal bodyguard"
shiru yayi yana nazari Amminshi kaɗai yake tunawa amma ai yanada bukatan aiki sabida baya taɓa kuɗin daba nashi ba yaci, duk wani kuɗin da yasan ba haƙƙinshi bane baya ci saide ya tara idan bukatanshi ya tashi wa marasa karfi ya biya musu"
abba ya kara cewa "ba zan takura maka ba amma zanso hakan sabida naji ina sanka kamar ɗan dana haifa, ba kowane yaro bane zaiyi abinda kayi koda ko ɗan cikinka ne shiyasa ka kara samun matsayi a wajena"
a hankali yace "na yadda zanyi duk abinda kace"
murmushi yayi yace "na gode nawal daga yau kaine driver ɗina kuma kaine bodyguard na yarana da matata, zan rinƙa biyanka albashin dubu ɗari uku a kowane wata"
sunkuyar da kai yayi yana murmushi a ranshi yace "na godewa Allah na samu aiki hakan zai kara nesantani da cin kuɗin haram, zan fara yiwa Ammi siyayya na rinƙa kula da ita da aikin da nayi da karfina halal ɗina zan fara ci kamar yadda Ammi take cewa"
Abba sai kallonshi yake yadda yake maganan zuci yana murmushi ya nuna mishi yaji daɗin aikin, Abba yace "zaka iya dawowa gidana da zama domin aikinmu na iya kaiwa har dare"
a hankali yace "to zan dawo amma mahaifiyata tana gidan Alhaji Alhasan kuma da wuya ta yadda ta bar gidan sabida itama aiki take yi"
yace "babu damuwa zaka iya zuwa kullum ka dubata"
yace "na gode"

yaci gaba da kula da Abba, wayar Abba ya faɗi shiyasa basu kira gida suka sanar musu ba, yace kawai saiya samu sauki zasu tafi, yau kwanansu huɗu a asibitin
janna ce zaune akan sofa ta ɗaura kafa ɗaya akan ɗaya, wandon jinx blue ne a jikinta da riga shimi sky blue, kanta yasha gyara tasa mayafi siriri glasses na rashin mutunci data saba sawa baƙi tasa a idonta, gabanta kwalaben wine ne da kofunan glass, takalmin kafarta me tsini ne sosai shima sky blue sauti ke tashi a cikin falon gefe kuma kawayenta ne duk sunsa kaya sky blue sunyi bala'in kyau kowacce da glasses a idonta suna danna tsadaddun wayoyinsu, janna ta zuba wine a cup ɗin ta mikawa kowa sannan suka haɗa sukayi cheers, shanyewa sukayi tana rufe ido sabida gas ɗin ciki tace "lokacin yanka cake yayi"
duk suka tsaya kusa da ita itama ta tashi ta rike iphone16 zata yanka cake dashi, har zata fara yankawa tace "wait banga unty ibtee ba ya zama dole mu jirata"
tsayawa akayi saida ibtisam wacce ta shiga damuwa sabida rashin jin labarin Abba ta fito sanye da black abaya tayi kyau sosai amma fuskanta babu walwala tunani ya taru ya mata yawa ga tunanin Abba ga kuma tunanin wannan ɓarawon daya kasa gushewa a ranta, janna tana ganinta tazo da sauri taja hanunta tace "ke muke jira"
murmushin dole tayi sabida kawayen janna suna wajen, fara yanka cake sukayi kawayen suna tafi suna mata "happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday classy janna happy birthday to you"
tafi sukeyi ta fara sawa ibtee a baki sannan tasa musu suma suka sa mata, celebrating suka fara janna sai rawa take tana jin daɗi a ranta, tunda Abba yayi tafiya a cewarta, ta samu freedom sai yawonta take yadda taga dama, duk wani party da kawayenta da abokanta suka haɗa sai taje, yau birthday ɗinta ma zasuje da dare suyi celebrating a wani hotel hall ɗin data kama da makudan kuɗaɗen Abba data sace dalolin da suka jima da naira ɗin data sace babu jimawa, duk wani kuɗin da janna take wasa dasu na Abba take sata, Ibtee tazo kunnenta tace "janna ki daina wannan rawan karki manta fa yau kwana huɗu ba'asan inda Abba yake ba, p.b Ahlam numbernshi baya tafiya shima Abba wayarshi a kashe kuma kin san basu taɓa yin tafiya irin haka ba"
kallon ibteen tayi sannan taja hanunta zuwa tsakiyan falon ta fara rawa da ita, ibtee zatayi magana ta juyata ta yadda dole saita fara rawa, kawayen janna suka fara musu spray babu yadda ibtee ta iya dole ta biye mata suna rawan.
an sallami su Abba yau kuma Alhmdllh jikinshi yayi sauki ya samu kulawa sosai daga likitoci sannan nawal ma yana bada gudunmawa sosai wajen kula dashi, tare dashi suka shiga motan Abba yana gidan baya shi kuma nawal yana mazaunin driver, fita sukayi a asibitin, Abba yace "baka driving da gudu meyasa?"
cikin sanyin muryanshi yace "ban kware a driving ba abokina ne yake koyamin"
yace "okay zaka kware a hankali kuma zaka rinƙa zuwa wajen koyan mota sosai zaka kware tunda ka iya"
yace "to"
Abba ya lura yaron kamar wanda ya taso a takure baya sakin jiki duk shaƙuwan da zakayi dashi, baya yawan magana saide ya bada amsa, wani ma yanaji zaiyi shiru ba dan raini ba sai dan rashin sabo da cikin mutane da kuma takura daya girma a ciki, yi yayi kamar bai san gidan ba abba ne yake nuna mishi hanya har suka isa, hon yayi ba'a buɗe ba, yayi ta hon babu wanda ya buɗe, Abba zai fita nawal yace "bari na buɗe"
zuwa yayi ya tura gate ɗin sannan ya dawo yaja motan zuwa ciki, Abba yayi mamaki da babu megadi "ina yaje?"
tsaki yaja har nawal yayi parking a compound ya buɗe mishi marfin motan ya fito, bin cikin gidan yayi da kallo, fulawa sunyi tsayi sosai sun wuce misali a cikin kwana huɗu da yayi gidan yayi ƙura kamar ba'a wanke ba, saɓanin idan yana gida kullum sai a wanke, hasalima masu aikin baccinsu suke yi a karkashin bishiya kan grass carpet ɗin da yake bada iska me daɗi, a fusace Abba ya karasa wajen cikin tsawa yace "ubanme kuke yi a kwance?"
duk suka tashi a firgice suna kallonshi, kowa yayi zaton ɓata yayi kamar yadda sukaji a rediyo, cikin rawan jiki kowa ya fara neman hanyan kama aikinshi, yace "ku dakata dukanku"
tsayawa sukayi, cikin rawan murya tsaban ɓacin rai wato mutane idan kana wajensu sunada amana idan baka nan suci amanarta su kasa kula da abinka? yace "duk na koreku babu me kara aiki a gidana na sallameku"
zubewa kasa sukayi suka fara bada hakuri, yace "na baku minti goma ku kwashe komai naku ku bar gidannan idan kuma kun kara koda minti ɗaya akan minti goman dana baku kunfi kowa sanin me zai biyo baya lokacinku ya fara 1..2..3..4.."
da gudu kowa ya fara tattara abinda yasan nashi ne suka bar gidan dan sunfi kowa sanin waye shi, ya kalli nawal dake tsaye a gefe yace "muje"
binshi nawal yayi suka shiga ciki, tun daga nesa yake jin sautin waka yana tashi a falon, da farko ya zaci kunnenshi ke mishi gizo saida ya kusa sosai da falon yaji tabbas sautin waka ne yau yake tashi a cikin gidanshi, wakan ma bana masu hankali ba, jikinshi har yana rawa tsaban ɓacin rai, wato basu damu da ɓatanshi ba waka ma suke ji babu wanda ya damu?
tura kofan yayi, ibtisam wacce idonta akan kofa ko zataga mamee wacce ta fita zuwa police station domin sanar da ɓatan mijinta tareda jaad suka tafi, taga abba ya shigo, zaro ido tayi tana kallonshi, murza idon tayi domin tabbatar da shi ɗinne ko kuɗinta ne, tabbas Abba ne, janna ta juya baya tana karya waist nata cikin rawan take kaiwa kasa tana tashi sama, juya mazaunanta take yadda taga dama tana bin wakan kamar a club take, Abba ya kasa magana ji yayi idonshi na rufewa tsaban tsananin ɓacin rai, ibtee ce tace "ja...ja...ja..janna ga Abba"
bata jita ba sabida sautin yayi yawa, Abba jijiyan kanshi sun tashi telephone na gefenshi yasa hanu yaja sannan ya kira wasu numbobi yayi magana, yana huci yaje ya kashe wakan, janna cikin masifa tace "wani ɗan isk..."
ido huɗu sukayi da Abba wanda idanunshi suka rikiɗe suka koma jajur, kawayenta suna ganin haka kowa ya fara ɗaukan jakanshi zasu gudu, rufe kofan Abba yayi yana kallonsu baice komai ba, janna da jikinta ya fara rawa tace "dan girman Allah ka yafeni"
baiyi magana ba kuma bai matsa a bakin kofan ba, saida yaji karan mota sannan akayi knocking ya buɗe kofan, ibtee idanunta suka kara girma ganin police ne Abba ya kira, yace musu "bismilla ku shigo"
shigowa sukayi, janna ta fara ihu tana rokon Abba, a lokacin nawal ya shigo da kayan Abba daya bari a mota, ganin yaran tsaye cirko cirko da wancan fitsararriyar daya gani a wajen party ranan, da kuma wacce ta taimaka mishi a ranan daya shigo ga kuma police, ibtisam da mugun mamaki take kallon nawal wanda shima ya zuba mata ido suna kallon juna, kawar da kai yayi kamar baya kallonta, Abba yace "duk ku kamasu da laifin mayar min da gida club"
ya nuna harda janna, shirin kamasu aka fara, janna ta fara kuka, Abba yace "kafinnan bari na gabatar musu da wani"
ya riko hanun nawal yace "wannan shine sabon p.b ɗina shine zai rinƙa driving ɗinku sannan shine zai rinka kula da shiga da fitanku wannan da kuke gani a tsaye anan yafi min ke muhimmanci"
ya nuna janna dake tsaye ansa mata handcuffs, yace "yafi min ke sabida ya ceci rayuwata kuma ya hana idonshi bacci na tsawon kwana huɗu yana kula da wanda bai san daga ina yake ba baisan waye shi ba, amma keda kike ƴata baki damu ba janna kinzo kin haɗa birthday party ɗinki a gidana kina rawa baki damu da inda nake ba, kinsan na haramta shagalin birthday amma shine kikayi a bayan idona baku sani ba ko na mutu ko ina raye shagalinku kawai kuke yi, wannan shine ya ceceni a lokacin da nake tsananin neman taimako"
yace "officer ku tafi dasu sannan kada a bada belin kowa saina bada umarni"
officer yace "an gama sir"
kuɗi me yawa ya basu, ƴammatan sai kuka suke suna rokon Abba ya taimakesu yasa a sakesu, ko kallonsu baiyi ba, ibtisam ma ansa mata ankwa zasu wuce da Ita kamar yadda suka wuce da sauran Abba yace "banda ita ku saketa nasan bada sonta take biye musu ba"
sakinta akayi ta sunkuyar da kanta ta rasa farin ciki take na ganin wannan ɓarawon daya sace zuciyarta ko na ganin Abba, ko kuma bakin cikin kama janna da akayi?
janna wani kallon da take aikawa nawal saida gabanshi ya faɗi, saida sukazo fita da ita hanunta a rufe mayafinta yana faɗuwa Abba ya wuce zai tafi daidai kunnen nawal ta yadda shi kaɗai zaiji me tace mishi tace "kana ganin kayi abin kirki ne sabida Abbana yace ka fini a wajenshi? ka taɓa ganin inda bare yafi ɗa? ka taɓa ganin inda tuwon dawa yafi couscous? ka taɓa ganin inda damisa ta zaɓi kura a matsayin aboki? ka taɓa ganin inda wuta ya zauna lafiya da ƙanƙara? to ka sani koma wani asiri ka yiwa Abbana har ya furta kalman ka fini a wajenshi ba zaiyi tasiri ba matukar zaka zauna a gidannan saina nuna maka tsantsar tsana sannan Abba da bakinshi zai buɗe yace ni ƴarshi daya haifa a cikinshi na fika mara galihu talaka kazami a wajenshi, gargaɗi nayi maka dan sabida kada kasa a ranka ma ka fini koda da kwayan zarra a wajen Abba"
jan hanunta sukayi suka fita da ita, tana aika mishi mugun kallon tsana, shiru yayi kawai, ibtisam taji duk abinda janna ta faɗa mishi kuma bataji daɗi ba ko kaɗan abin ya mata zafi ganin yadda ya sunkuyar da kai kawai baice komai ba yana wasa da yatsun hanunshi, murmushi tayi ganin yadda yayi kyau daya sunkuyar da kai kamar karamin yaro, Abba yace "ina maminku ake wannan abin?"
Ibtee da sauri tace "taje police station zata kai report na rashin dawowanka itada jaad"
tafiya kawai yayi be amsa mata ba, yana tafiya nawal ya juya zai fita tace "barka da zuwa gidanmu babban ɓarawo"
bai juyo ba yace "barka"
ganin zai fita tace "am baka tambayeni meyasa ban tona maka asiri ba"
a takaice yace "sabida nasan ba zaki tonamin ba"
ya fita daga ɗakin, tayi mamakin amsan daya bata, taɓe baki tayi alaman ko oho.

_Jiddah Ce....✍️_
08144818849
[17/08, 11:13 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸
*SHIMA ƊA NE*
🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 20*


~A ranan ibtee sam batayi bacci ba da tunani ta tashi, washe gari kamar yadda suka saba fita breakfast haka suka fito harda mami, gaisawa sukayi mami ta amsawa janna sama sama zama sukayi Abba ya fito, zasu fara breakfast Abba yace "ku tsaya"
duk suka zuba mishi ido, waya ya ɗaga ya kira numbern nawal yace "shigo"
nawal ya amsa da "to"
aikin da yakeyi na wankin gidan ya bari, ƙafan wandonshi da riganshi hanun ya naɗe, jikinshi a ɗan jiƙe da ruwa ya shigo cikin respect ya gaida Abba, Abba yace "ya kake nawal? yaka tashi?"
yace "lafiya ƙalau"
yace "ina kwana mami"
tace "lafiya ƙalau ya kake?"
yace "lafiya lau"
Abba ya nuna mishi kusa dashi yace "tashi ka zauna muci abinci"
duk suka kalleshi harda mami, da mamaki yadda zai bar bodyguard ya zauna cikinsu suci abinci abinda basu taɓa gani ba ko Ahlam da sukayi zaman amana basu taɓa cin abinci tare ba, yace "a,ah Abba..."
Abba yace "banaso ina magana ana min musu wannan yana cikin dokana ka tashi ka zauna"
a hankali ya tashi ya zauna a kusa da abban, murmushi ibtee tayi wani dadi taji a ranta ganinshi a cikinsu, jannah da wani kallo take binshi tana huci, meyasa Abba zaice ya zauna dasu suci abinci?
duk suka fara breakfast babu me magana, jannah sai jujjuya cokali take a abinci ta kasa cin koda loma ɗaya ne, kallon nawal take ta kasan ido, tashi tayi ta bar wajen, Ibtisam zata mata magana Abba ya ɗaga mata hanu, shiru tayi, jannah a fusace ta haura stair, nawal kallo ɗaya ya mata ya sunkuyar da kai ya kasa sakin jiki yaci abincin shima kaɗan yaci, har saida Abba ya tashi kafin shima ya tashi, fita yayi bayan ya gode musu, jaad yace "unty ibtee wannan p.b ɗin yanada hankali bayada damuwa da yawan surutu"
murmushi kawai tayi, mami tace "Alhmdllh na koshi"
jaad ma yabi mami yace ya koshi, ibtisam ta tashi taje kitchen indomie ta dafa da tea me kauri sannan tasa a plate biyu da cup biyu, ɗaya ta ɗauka ta fita waje, nawal yana wanke mota ya maida hankali kan aikin, kallon bayanshi take yi gashinshi dake a kwance kamar na mata yafi mata kyau, a bayanshi ta tsaya tace "salam"
juyowa yayi ya motsa leɓenshi a hankali yace "wa salam"
kallonta yayi da abin hanunta tana murmushinta me kyau tace "abinci na kawo maka"
yace "naci abinci ai"
girgiza kai tayi tace "ina kallonka kaɗan kaci"
yace "naci karki damu"
juyawa yayi zai ci gaba da aiki yaji hanunta a nashi, juyo dashi tayi, ya zuba mata idanunshi masu kama dana mage, itama kallonshi take yi, taja hanunshi tace "dole sai kaci sabida ba zanyi girki a banza ba"
akan chair ɗin cikin gidan ta zaunar dashi, abincin ta bashi, karɓa yayi ganin ta tsaya a kanshi, tea ɗin yasha sannan yaci kaɗan yace "na koshi, na gode Allah ya miki albarka"
a hankali tace "ameen"
karɓan sauran tayi yaga ta zauna a gefenshi ta fara ci, kallonta yake yi da mamaki ya kasa cewa komai, saida ta cinye tace "bari na koma ciki"
har saida ta shiga ɗaki ya ɗauke kanshi daga kanta, a hankali ya tashi yaci gaba da aikin, Abba ne ya fito yace "nawal ka shirya zamu fita"
cikin ladabi yace "to Abba"
barin aikin da yakeyi yayi da sauri yaje ya shirya cikin uniform ɗin wato bakin suit, sajenshi ya taje da gashin kanshi, ya fito kamar ba'indiye, mota ya buɗewa Abba daya fito da babban riga a jikinshi, shiga Abba yayi shima ya shiga suka tafi.

Ibtee ɗayan plate ɗin da cup na tea ta ɗauka ta nufi upstair, ɗakinsu da janna ta shiga, tace "janna taso kiyi breakfast"
janna tana kwance akan gado tayi rub da ciki ta rungume teddy, idonta ne a rufe amma ba bacci take
End Ads