x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - SHIMA DA NE free pages

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 65957 words

Category: Love Stories

Views 220

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
gidansu mami take ihu, buɗe baki tayi zatayi ihu ya ciro bindiga ya nuna mata, tsit tayi tana kallonshi jikinta yana rawa, a hankali yake takowa har inda take, hanu ya mika mata tana kallonshi ta cire hanunta daga bakinta, ɗan karamin pink lips nata ya kara bayyana kyawun da Allah ya bata, ganin yadda jikinta yake rawa ya ɗaga riganshi yasa bindigan a aljihun wandon, yana kallonta idonshi kawai take iya gani, hanu ya mika mata cikin kasa da murya ta yadda bayaso aji yace "ba zan cutar dake ba"
a hankali tasa yatsunta cikin nashi, ɗagota yayi ta tsaya a gabanshi, yace "sata kawai nazo yi ba cutar da kowa ba"
kallon cikin idanunshi take yi wanda yake tabbatar mata da gaskiyan abinda yake faɗa, shiru kawai tayi, har yanzu a tsorace take hakan yasa ta fara ja da baya domin ta samu ta fita daga ɗakin domin tabbas zai iya cutar da ita gara ta fita ta faɗawa su Abba da suke searching nashi lungu da saƙo na gidan, cikin rashin sa'a kafanta ya harɗe tayi baya zata faɗi ya riketa, kallanshi tayi da mugun mamaki yadda ya taimaka mata ya tseratar da ita daga mugun faɗuwan da zatayi, cikin sanyin muryanshi yace "easy"
idanunshi kawai take gani, sakinta yayi ya juya baya jin ana knocking na ɗakin, ahlam ne yace "IBTISAM ku buɗe kofan zamu duba ɓarawo, mun duba ko ina na gidannan bamu ganshi ba ɗakinku ne kaɗai ya rage kuma Abba yace yaga kamar ya shigo ɗakin ku"
shiru tayi tana kallon nawal daya rike jaka, Ahlam ya kara cewa "IBTEE bakwa jina ne? ku buɗe kofa kada ya cutar daku"
hanunshi yaji ta rike, ɗago kai yayi yana kallonta ya gama sawa a ranshi yaune ranan rabuwanshi da ammi domin tabbas asirinshi zata tona, jan hanunshi tayi da mamakinshi yaga taje gaban wardrobe dashi ta tsaya, buɗe wardrobe tayi sannan tayi mishi alama ya shiga, kallonta yake domin tabbatar da abinda yake ganin tana shirin yi, cikin muryanta mara hayaniya tace "shiga mana"
shiga yayi ta rufe wardrobe ɗin sannan tace "na'am ya Ahlam"
buɗe kofan tayi tana ganinshi ta nuna a tsorace take tace "Ahlam ɓarawo a gidanmu? ka duba mami kada ya cutar damu, ina mami bai mata komai ba?"
girgiza kai yayi yace "bai mata komai ba ina ƴar uwarki?"
tace "tana toilet ka shigo ku duba ɗakin amma babu wanda ya shigo"
shigowa sukayi suka fara duba ɗakin har ƙarƙashin gado, basu ga kowa ba, zasu buɗe wardrobe tace "Ahlam naji kamar karan kafar mutum a waje"
tare suka fita, sun duba ko ina babu shi, Abba cikin faɗa yace "ya tsira yau amma watarana zamu kamashi, tunda nake babu ɓarawon daya taɓa ruɗamin gida ya rainani kamar wannan ɓarawon duk ranan dana ganeshi saina sa rayuwarshi ta zama abin tausayi, kowa ya bar nan bana buƙatan ganin kowa"
duk suka watse harda Ahlam wanda ya koma ɗakin mami domin duba lafiyanta, mami hawan jininta ya tashi maganinta ya bata tasha tace "Ahlam a tsorace nake"
yace "sannu mami ki kwantar da hankalinki ya gudu kuma ba zai kara dawowa gidannan ba, ya bar gidannan kenan har abada kinji mami?"
tace "to Ahlam amma ka duba su ibtisam babu abinda ya samesu?"
yace "babu komai daya samesu suna lafiya mami matukar ina gidannan babu abinda ze samu kowa"
tace "na gode Allah da wannan mugun mara imanin bai shiga ɗakinsu ba a ɗakina ya tsaya na tabbata daya shiga ɗakinsu babu abinda ze hanashi cutar dasu, ina JAAD?"
yace "jaad yana bacci babu abinda ya sani ma"
tace "to kaje ka kula dashi"
yace "to"
saida ya tabbatar ta daina surutun ta samu bacci kafin ya tashi yana jin haushin ɓarawon da har yasa matar excellency hawan jininta ya tashi, bayan ta jima be tashi ba, daya kamashi yau babu abinda zai hanashi illata shi, ɗakinshi ya koma wanda suke kwana tareda karamin yaron gidan wato jaad shine personal bodyguard nasu a gidan Abba ya bashi lasisin zama tare dasu domin basu tsaro na musamman, duk inda kaga Abba zaka ga Ahlam sabida shine PB ɗinshi wato personal bodyguard, kwanciya yayi kowa ya koma ɗaki har Abba.
saida ta tabbatar gidan yayi shiru sannan ta rufe toilet na cikin ɗakin da makulli tazo wajen wardrobe ta buɗe, yayi zufa sabida zafi hadarin daya haɗu a waje ya fara walƙiya da alama ruwan sama zai iya sauka a kowane lokaci, fitowa yayi a hankali yace "na gode"
hijabinta me tsayi ta ɗauko gani yayi tasa mishi, sannan ta karɓi jakanshi daya sa sarkokin daya sata a ciki, drower ɗin da suke zuba duk abinda ya shafi gold ɗinsu ta buɗe sannan ta kwashe duka ta zuba mishi a jakan tazo ta mika mishi, kanshi ya sunkuyar ya kasa kara kallonta, ruwan sama ne ya sauko kamar da bakin kwarya, jan glass na window tayi tana nishaɗi idan taga ruwan sama, ruwan sama yana sata jin wani sanyi da samun nutsuwa a zuciyarta, a hankali tasa hanunta a waje ruwan yana taɓa hanun tana murmushi, tasa kanta a waje tana kallon ruwan da yake sauka, saida ruwan ya fara tsayawa kafin ta juyo ta kalleshi, tace "baka tafi bane? me kake jira?"
shiru yayi, ta rufe window sannan tace "dama kana tsoro ka shigo sata a gidan tsohon gomna wanda kasan dole akwai tsaro na musamman?"
shiru yayi, tayi smiling daya karawa kyakkyawan fuskanta kyau sannan tace "masu tsaron gidanmu sunada kafiya da wuya ka iya fita yau a gidannan basu kama ka ba, koda ruwan sama ake suna tsayuwa cikin ruwan saman suna gadin gidanmu, sannan idan Abbanmu ya kamaka a wannan gidan ina me tabbatar maka ba zaka kara numfashi koda na minti ɗaya bane a duniya"
a gabanshi ta tsaya sannan tace "zan taimaka maka amma saika kula"
waya ta ɗaga ta kira wani number, ana ɗauka tace "baba megadi barka da warhaka"
bayan ya amsa tace "baba dama inaso na fitane yanzu kuma Inaso ka rufamin asiri yau zan nemi alfarma a wajenka kada ka faɗawa kowa na fita idan na tashi dawowa ta bayan gida zan shigo"
murmushi tayi tace "na gode baba ka buɗemin gate yanzu zan fita sannan ka janye hankalin security's kada su gane"
ta ɗan russuna kamar yana gabanta tace "na gode baba"
katse wayan tayi ta juya baya tace "zaka iya fita"
kallon bayanta yayi, a hankali yazo gabanta ya tsaya, mask na fuskanshi ya cire ta yadda zata kalleshi da kyau, murmushi yayi mata, kallonshi tayi taga asalin fuskanshi, tun daga idonshi data gani jikinta yayi sanyi yanzu kuma da taga fuskanshi taji jikinta ya gama yin sanyi, wani irin wutan kyau yake dashi kamar balarabe, badan yayi hausa ba daya shigo zata rantse ba daga nigeria yake ba, maida mask ɗin yayi ya rufe fuskanshi baice komai ba kawai ya kara gyara jakan daya goya a baya ya buɗe kofan ya fita sanye da hijabinta.
Allah ya taimakeshi itama ta taimakeshi ya fita ya bar gidan ba tareda an kamashi ba, cikin ruwan saman da bai gama tsayawa ba yake tafiya, duk lokacin daya taɓa jakan ya tuna abinda ya faru sai yayi murmushi, a inda yake ɓoye duk abinda ya sace yaje ya ɓoye sannan ya koma gida, momy wacce batayi bacci ba sabida Dady da take bashi magani akai akai tana tsaye a stair tana kallon cikin gidan dake ɗauke da haske kamar rana, idanunta ya sauka akan nawal daya shigo yanzu, da sauri tace "daga ina yake?"
kasa kwanciya hankalinta yayi saida ta fita taje ɗakinshi, babu sallama ta tura kofan, da sauri yasa bindigan a kasan katifa, ta tsaya a kanshi tace "daga ina kake?"
yace "daga asibiti ina wajen Ammi"
tsaki taja sannan ta fita daga ɗakin, ta manta da kazamar gurguwan Amminshi tana asibiti, kwanciya yayi akan katifan ya rufe ido kamar me bacci, deep down yana tunanin abinda ya faru, bai taɓa zaton akwai masu taimako har yanzu a rayuwa ba sai gashi yau ta taimaka mishi, yana tunanin har bacci ya ɗaukeshi.

_Jiddah Ce...✍️_
08144818849
[17/08, 11:13 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸
*SHIMA ƊA NE*
🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 13*


~Ibtisam yana fita ta sauke ajiyan zuciya ta kwanta akan gadon ta rufe ido, a ranta tace "thank god ya fita ba'a kamashi ba"
tashi tayi da sauri tace "amma meyasa na rufa mishi asiri? ɓarawo nefa meya...."
kiran sunanta da akayi yasa tayi shiru "Unty Ibtee? waya rufe bathroom?"
da sauri ta tashi taje ta buɗe bathroom ɗin, juya baya tayi sabida gani take kamar za'a gane abinda tayi, subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangijin da yayi kowane halitta, tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci Annabi yusuf Annabi me kyawun halitta, hakika Allah shi yake kowane halitta idan yaga dama yayi mummuna idan yaga dama yayi kyakkyawa, suna tsananin kama da ibtisam amma wannan siririya ce bata kai ibtisam cika ba, karan hancinta yafi na ibtisam tsayi da tsini, ga wani gashin daya rufe saman idonta zara-zara baƙi wuluƙ, babu lokacin bayanin kyawun wannan yarinyar wacce a shekaru ba zata wuce 18 ba itako ibtisam 21 take, baƙin sleeping dress ne a jikinta silk yard da less a hanu da wuyan, ya mugun fito da kyawun fatarta, this is the real definition of beauty, tace "unty ibtee nace miki mu ɓuya a toilet ɓarawon ba zai ganmu ba kinki yadda tsaban tsoro kika ɓuya a bayan gado amma be shigo ba ai ko? kinsan ni bacci nayi banma sani ba"
hamdala tayi a ranta da bataji abinda ya faru ba, juyowa tayi tace "JANNAH meyasa idan bacci ya ɗaukeki a ko ina yinshi kike? jan kullum ina cewa ki daina bacci a duk inda kike amma bakya ji"
turo karamin bakinta tayi sannan tace "am sorry na daina"
tsaki taja tace "ke kika sani"
hawa gado ibtisam tayi taja duvet ta rufe har kanta, so take tayi bacci, janna dake shafa night face cream nata tace "unty ibtee amma fa cikin bacci kamar naji kina magana da wani kuma kamar shima naji yana miki reply"
da sauri ta janye duvet ɗin tana kallon janna, ta cikin madubin ta jinjina kai tace "yes ko dai mafarki nayi ne?"
ajiyan zuciya ta sauke tace "yes dear mafarki kikayi banyi magana da kowa ba"
zatayi magana tace "shii please kiyi shiru kada Abba yaji muryanmu"
tace "gaskiya saina faɗi abinda yake raina..."
tace "haba jan meyasa bakya ji ne? kinfi kowa sani ko tari akayi na kirki idan Abba yaji sai ran kowa ya ɓaci, kinfi kowa sanin idan yana gida babu me yin magana me tsayi har sai ya fita, meyasa kike son janyo mana matsala ne?"
shiru tayi tana kallonta har ta gama taja duvet ta kara rufuwa rufe ido tayi.
janna gama shafawa tayi sannan ta hau gadon, kallon bayan ibtisam tayi batason ranta yana ɓaci sabida tana bala'in sonta, a hankali ta rungumeta ta kanƙameta sosai, haka ta saba bacci tun ibtisam tana jin haushin yadda take kankame mutum idan zata kwanta har ta kyaleta sabida hakan ɗabi'anta ne, cikin sanyin murya tace "am sorry unty ibtee ba zan kara tsallake dokan Abba ba"
kullum haka take faɗa amma babu wanda ya kaita tsallake dokan, sam janna batajin magana duk abinda Abba ya hana yana fita zatayi, idan taga dama yana gida zatabi ta baya ta tsallaka katanga ta tafi yawon daya hanasu zuwa ta dawo babu wanda ya sani sai ibtisam, har ta fita har ta dawo ibtisam bata iya zama da taji muryan Abba gabanta zai fara faɗuwa, mutanen gari da mutanen gida babu wanda baya tsoron Abba sai janna wacce take tsallake dokan daya sanya a duk lokacin da taga dama, kawayenta yaran masu faɗa aji ne domin bata ƙawance da ƴaƴan talakawa, bata ɗaukan raini indai class ne babu me nuna mata domin har kawayenta kiranta suke da suna CLASSY JAAN indai dressing ne an barwa janna domin babu wacce take gaya mata dressing a school nasu, matukar tasa kaya kuma biyayya yake a jikinta, ita kuma ibtisam sauƙin kai gareta batada hayaniya batason rigima gata da bala'in tsoro batason faɗa, tanada tarin kawaye sabida sauƙin kanta harda yaran talaka tana mu'amala dasu, kawarta da tafi so sukafi shaƙuwa itace YUSURA ƴar senator ce, shi kanshi Abba yasan ibtisam tafi hakuri a cikinsu.

washe gari weekend ne babu school yau shiyasa duk suke gida, kuku sun gama girki an jera a dinning table, babu wanda Abba yake jira idan lokacin cin abinci yayi duk abinda kakeyi ya zama dole ka bari kazo kaci abinci saɓanin haka zaka fuskanci fushin shi, ibtisam da janna sun fito rike da hanun juna, duk sunyi kyau cikin simple dress ɗinsu, zama sukayi jaad da bai jima a tashi daga bacci ba shima ya fito kyakkyawa ne karamin yaro kamarsu sosai dasu, yace "good morning"
Ibtisam tace "morning jaad ya ka tashi?"
yace "lafiya ƙalau"
ya kalli janna wacce bata amsa ba yace "unty janna?"
harara ta watsa mishi sannan tace "karka sake ka kara kiran sunana idan ba haka ba saina fasa maka baki"
ibtisam tace "A,a me ya miki?"
tace "shi ya sani ai"
kallon jaad tayi tace "me kayi mata?"
cute eye's nashi ya zuba mata, tace "me kayi mata?"
yace "just because dan naga tana haura katanga zata fita shine...."
gyaran murya Abba yayi, tsit wajen ya zama babu wanda ya kara ko tari, fuska ba walwala ya zauna duk suka gaisheshi a tare, a tsanake yace "lafiya"
babu wanda ya kara ko numfashi me karfi, breakfast suka fara bai tambaya ina mami ba, sam baya tambaya ina wane, a cewarshi duk wanda yaci abinci dan cikinshi yayi wanda baici bama dan kanshi baya lallashin mutum.
jaad ne ya kalli ibtisam itama ta kalleshi, alama yayi mata ina mami?
itama tayi mishi alaman bata sani ba, zai kara mata wani alaman Abba ya ɗago kai zai ɗau ruwa ibtisam a tsorace ta maida hankali kan abincin kamar batayi komai ba.
janna ta kalli agogo karfe tara da rabi yayi kuma yau dole saita fita ko me zai faru sai taje birthday party ɗin classmate ɗinta saarah satan kallon Abba tayi taga baya kallonta, karamar wayarta ta ciro daga inda ta ɓoye a aljihun wandon jikinta me faɗi, numbern da yake dialing call ta shiga ta tura text, kara ɓoye wayan tayi ganin time yana tafiya tayi breakfast da sauri sauri, tissue ta zara ta goge bakinta sannan ta tashi zata tafi, cikin rashin sa'a karamar wayar ta faɗi ashe be zauna da kyau a cikin aljihun ba, dafa kirji ibtisam tayi ta waro ido ganin Abba yaga wayan, jaad dafa kai yayi ya rufe ido sabida yasan yau akwai tashin hankali a gidannan, jikinta yana rawa tasa kafa zata taka wayar cikin wani irin tsawa Abba yace "idan kika sake kika taka saina kasheki da duka"
cak ta tsaya da kafarta jikinta yana rawa tana kallon abban da har jijiyan kanshi ya tashi, cikin tsananin ɓacin rai yace "AISHA? AISHA? AISHA?"
mami dake kwance akan gado cikin zazzaɓin tsoron da jiya ta shiga da daddare sanadin ɓarawon daya shigo taji muryan Abba yana mata kiran da idan yayi to fa babu lafiya, ta dafa kirji tace "na shiga ni Aisha me kuma ya faru?"
sauka tayi a gadon bata cire bargo a jikinta ba sabida zazzaɓi ta fita, ganin janna a tsaye gaban Abba shima yana tsaye tace "me kuma janna ta kara yi yau? janna zata kara min hawan jini"
durkusawa tayi tace "gani"
kallon janna yayi yace "kinga uwarki ai ta durkusa ke kuma kina tsaye kina nema ki haɗa kirji dani"
a hankali ta durkusa kusa da mami, ya ɗauki wayan sannan yace "me wannan?"
mami tace "waya ne"
cikin tsawa yace "kenan za'a iya tsallaka dokan dana aje a gidana? sau nawa nake cewa kada wani ya rike waya a cikinsu? kina sane suke rike waya?"
ta girgiza kai, cikin zazzaɓi tace "wallahi ban sani ba ban san janna tana rike waya ba"
ya kalli janna sannan yace "ke tun yaushe kika fara rike waya a gidannan?"
tace "ji..ji.ji"
marin daya sauka a gefen kumatunta yasa taga taurari a idanunta, yace "zaki faɗamin ko saina taka wuyanki?"
tana rike da kunci tace "jiya ne..."
duka ya fara mata cikin zafin rai yace "karya zaki min? karya zakimin janna?"
ihu take yi tana neman taimako, jaad da ibtisam jikinsu ya fara rawa sun kasa zuwa su karɓi janna sabida Abba baida sauki, mami kuma ihun da janna take yi yana kara ɗaga mata hawan jininta saima jiri da take ƙara ji fiyeda na jiya da dare, saida ya tabbatar ta daku kafin ya buga wayan da kasa, ya cire sim ɗin ya kakkarya sannan ya wurgar da wayan bayan yayi raga-raga, tsallakata yayi ya barta kwance a wajen tama kasa kuka sai rike hanunta da take ji kamar ya karye tayi, sai a lokacin ibtisam tazo da gudu itada jaad suna ɗaga ta, bakinta ya fashe yana jini, ibtisam tace "mami bakinta jini yake"
mami tace "ibtee me zan faɗawa janna? ta maida duka ba komai ba a wajenta kullum tana cikin shan duka a wajen Abbanku amma ba zata nutsu ta daina yin abinda ze sa ya dake ta ba? yaushe rabon da Abbanku ya dake ki ibtee? keba mutum bane? bakya son rayuwar ƴanci ne kema? kin hakura amma ita batada hakuri kullum tana cikin aikata laifi bayan tasan koni tsoronshi nake, nida ba ƴarshi bama ji nake kamar na gudu na bar gidan bale ita daya haifa a cikinshi"
gwada ɗaga hanun da janna take rike dashi tayi, ihu tayi da alama hanun ya karye, tace "innalillahi janna meyasa kike nemawa kanki ciwo ne?"
ta kalli jaad tace "jeka kira Ahlam yazo mu kaita asibiti"
da gudu ya tashi yaje ya kira Ahlam, cikin dressing na bodyguard yazo tsaye yayi a kansu yace "meya sameta?"
tace "dukanta Abba yayi kuma ina ganin hanunta ya karye mu tafi asibiti kawai"
yace "okay"
ibtisam tace "mami ki kawo kuɗi mu kaita dole zasu nemi kuɗi"
girgiza kai tayi tace "wallahi banada kuɗi ibtisam a hanuna, kuma nasan Abbanku ba zai bada ba, bari na ɗauko gold ɗina Ahlam ya siyar saiku kaita dashi"
tashi tayi har amai amai take ji dauriya kawai take yi, ɗakinta taje ta buɗe drower ɗin da take aje gwala-gwalanta waro ido tayi ta dafa kirji, batasan lokacin data saki ihu ba, tare suka shigo Ahlam ne
End Ads