An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
~Bayan awanni masu yawa, buɗe ido tayi tana kallon silin na ɗakin, tashi zatayi taji jikinta yayi nauyi, idanunta suna zafi, kallon gefe tayi taga gado ne take kwance akai, kasa magana tayi a ranta tace "ban kwanta a gado ba meya kawo ni gado yanzu?"
tace "nan inane?"
a hankali tayi yunkurin kara tashi taji jikinta yana azaban zafi, ihu tayi tace "na shiga uku meya sameni?"
taɓa kanta tayi taga gashinta ya barbazu akan pillow, ciza bakinta tayi ta runtse ido, cikin azaba tace "waye anan? waye a gidannan kuzo ku tainakeni"
ganin babu wanda ya shigo ta fara bubbuga jikin gadon da karfi tana girgiza kanta, tulin gashinta yana rufe mata fuska, farin fatarta ya koma jajur, musamman lips nata sunfi yin red, idanunta masu girma suka kara girma, cikin ihu take neman taimako domin ko hanunta ba zata iya ɗagawa ba, tun tana ihu har ta gaji tayi shiru tana hawaye kawai, rufe ido tayi kamar me bacci tana jiran abinda Allah zeyi da ita domin ta sadaukar da rayuwa, a kananan shekarunta wannan azaban yayi mata yawa domin ba zata wuce shekara 17 ba, karama ce sosai, sallama taji muryan mace babban mace ce ta girma sosai, ta shigo tazo inda take kwance tace "sannu baiwar Allah"
a hankali ta buɗe idanunta, saida matar ta tsorata ganin irin girman idanunta, ga kuma gashinta da farin fatarta, tace "baiwar Allah mutum ko aljan?"
cikin muryan daya dashe tace "mutum ce ki taimakeni ban san meya sameni ba"
a hankali tace "fyaɗe akayi miki kuma wanda ya kawoki gidannan shine yayi miki"
idonta a rufe tace "ina matar gidan? sannan ina mijinta?"
matar tace "gaskiya gidannan babu kowa a cikinta gidan Alhaji hassan ne kuma ya jima da kyautar da gidan ma wani wanda shima be taɓa zuwa ba, ɗana shine megadin gidan da jimawa ya kirashi jiya yace yana so yau yazo gidan domin zezo, bayan yazo dake ya fita shi kaɗai ɗana ya kirani yace akwai abinda ya faru kuma yanada tabbacin Alhaji be aikata abu me kyau ba domin ya fito daga ɗakin duk jikinshi zufa sannan baya cikin hayyacinshi ma, ɗana yace ba ze iya shiga ciki ba sabida ke macece hakan yasa nazo domin na ganki na tabbatar be cutar dake ba"
a hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un mama yanzu kenan rabani yayi da MUTUNCINA?"
mama tace "kwarai kuma zanso kiyi shiru kada ki faɗawa kowa Alhaji alhassan ya cutar dake yayi miki fyaɗe, sabida yanada kuɗin da ze iya shari'a dake ya karar da zuri'arki gaba ɗaya, Alhaji alhassan me kuɗi ne kuma yana iya yin komai sabida ya tsira daga wani abinda ya aikata mara kyau, a wannan gidan a wannan gadon ya taɓa yiwa wata fyaɗe bayan ta kaishi kotu daga karshe aka nemeta da iyayenta aka rasa, kuma har yau babu labarinta kuma hukuma basu sa baki akan abinda ya faru ba, sabida haka zanso kija bakinki ki rufawa kanki da iyayenki asiri, ki tsira da ranki"
shiru tayi tana hawaye kawai, zuciyanta yana zafi sosai, ji take inama a maida hanun agogo baya da wallahi ko inda taga yabi har duniya ta tashi ba zata bi ba.
matar tace "bari na taimaka miki kiyi wanka"
shiga cikin bathroom tayi ta haɗa ruwan zafi sosai sannan tazo ta riketa tace "tashi ƴata"
a hankali ta tashi tana rufe ido, ihu tayi jin zafi a kasanta sosai, tace "ki daure kyakkyawar ƴata"
ciza lips tayi a hankali take takawa kafafunta sunki haɗuwa, da kyar suka isa bathroom ɗin, tana kare kirjinta sabida a yage kayan yake, tace "cire kayan ki shiga cikin ruwan"
kunya take ji ba zata iya cire kaya a gabanta ba, ta kula da hakan tace "nifa mamanki ne kada kiji kunya ta"
a hankali ta cire kayan tana kare jikinta da hanu, ruwan ta sata shiga zata tashi ta danneta tace "daure ƴata ki daure"
tana kuka har aka gama wankan, gashinta a jike ta ɗaura mata karamin towel sannan ta bata babban ta ɗaura a kirji, fitowa sukayi tana kuka, matar ce ta kawo mata kaya tasa sannan tasa hijabinta, abinci ta bata ta girgiza kai alaman bataso, tace "to bara na kawo miki tea"
fita tayi tazo mata da tea me zafi ta sata dole saida tasha, ta ɗan ji sauki ba kamar ɗazu ba, a hankali tace "na gode zan tafi"
matar tace "to ga kuɗi ki hau mashin"
ta karɓa tace "na gode"
a hankali take tafiya tana hawaye, mashin ta samu ta hau har kofa aka kaita, bayan ta sauka ta bashi kuɗin kawai bata jira canji ba ta shiga cikin gida, mama na zaune tayi tagumi tunda take da rahama bata taɓa jimawa haka ba idan ta fita, ganin ta shigo babu sallama tace "subhanallah rahama lafiya yau kika shigo babu sallama?"
wucewa tayi batace komai ba, ɗakinsu ta shiga wanda suke tare da yaseer da kanwarta nana, nana tana karatu ta ganta ta shigo, tace "unty rahama lafiya?"
shiru tayi mata kawai ta kwanta akan katifar, tace "unty rahama dama baba yanata kiranki tun ɗazu mukace baki dawo ba, amma kin dawo kamar mara lafiya"
tayi shiru ta juya baya, aje takaddan tayi tazo ta taɓata tace "unty rahama wallahi ba zan jure ganinki haka ba, ki faɗamin meya sameki? waya taɓaki? ban sanki da fushi ba"
shiru tayi mata, nana ta ruɗe tace "unty rahama?"
wani tsawan data daka mata saida mama dake waje tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un meya samu rahama yau?"
tsit nana tayi tana kallonta, da manyan idanunta data kara warowa tace "tashi ki fita a ɗakinnan"
tashi tayi simi simi ta fita daga ɗakin, kuka mara sauti ta fashe dashi, ta zama shiru shiru ta kasa manta abinda ya faru, wayarta kullum take kallo ko zai kira be sake kira ba, yau ta shirya domin tafiya talla sabida kuɗin makarantar nana da zata biya a wannan watan, gidansu Alhaji alhassan taje amma an tabbatar mata baya nan, ta tambaya ina yaje cikin wulaƙanci suka koreta tareda jaddada mata kada ta kuskura ta kara zuwa gidansu, ta tafi tayi tallanta a ranta tasa ba zata faɗawa kowa abinda ya faru ba, kuma ba zata kara nemanshi ba, tallanta taci gaba da yi na alale tana biyawa kanwarta kudin karatu domin so take nana ta zama me ilimi ko zata wankesu idan ta girma.
yau tana wanke waken alale taji warin ruwan waken yana sata jin amai, daurewa tayi tana cigaba da wankewa, ina warin fa bataso amai ne yazo mata, da gudu ta tashi a wajen taje tana amai a banɗaki, mama dake girka ruwan zafin alalen tazo tana cewa "rahma meya sameki?"
tana nishi tace "mama banajin daɗi"
tace "sannu rahama bari nana tazo ta wanke waken yau ita zataje talla"
da sauri ta tashi tace "a,a mama nana zataje makaranta ni zanje ba wani rashin lafiya bane kawai ki wanke waken idan an gama zan fita da alalen"
mama tace "rahama ya kamata ki bari nana tana tayaki watarana be kamata kina hanata ba komai kece kikeyi rahama ki huta mana koda na rana ɗaya ne, tukunna ma ina Alhaji alhassan ne? banga yazo ba kuma baya kiranki a waya lafiya?"
tace "wallahi ban sani ba mama nima na jishi shiru kuma ban kara jinshi a waya ba may be yana aiki ne dan yace min ze tafi"
tace "to Allah yasa lafiya ki koma ɗaki ki kwanta to ki huta"
tace "to"
ɗaki taje ta kwanta saida mama ta gama haɗa alalen kafin ta shirya tazo ta ɗauka ta fita dashi, nana kuma tasa uniform suka fita tare, sai yamma ta dawo tayi shirin islamiyan dare ta tafi.
yaufa wata biyu babu alhassan babu dalilinshi tun tana damuwa har ta manta dashi ta fara abinda yake gabanta duk da surutan mutane bai dameta ba domin cewa suke ai ba aurenta zeyi ba hasalima kuɗinshi suka gani zasu bashi ita, magana babu irin wanda bataji amma bata damu ba, yauma kamar kullum zata wanke wake amai ta fara, mama cikin mamaki tace "wai rahama menene yake damunki? meyasa idan zaki wanke wake kike amai abinda bakya yi da?"
tayi shiru domin itama batasan dalili ba, mama tace "rahama tashi mana"
tashi tayi, mama ta kare mata kallo taga ta kara kiba ga wani haske da fatarta yake yi, tace "rahama ya kikejin jikinki?"
tace "ba komai fa mama"
shiru mama tayi gabanta yana faɗuwa, sanin halin ƴarta yasa ta kawar da abin a ranta, baba dake kwance a ɗaki ya ƙwalawa rahama kira, amsawa tayi taje ɗakinshi yana kwance yace "rahama bani ruwa"
tace "tom baba"
ruwa ta ɗiba mishi a cup na silver tazo ta bashi, karɓa yayi yace "na gode sosai Allah ya miki albarka"
tace "Amin baba"
cikin rahama ne ya fara fitowa, kwance take akan tabarma tana birgima domin zazzaɓi me zafi yake damunta, mama cikin ruɗewa ta shigo tace "muje rahama me mashin na jiranmu a kofa"
tace "mama ba zan iya tashi ba"
nana ce ta fito da hijabi itama a ruɗe take saboda bataso komai ya samu rahama, ɗagata sukayi da mama suka taimaka ta hau mashin ɗin mama ta hau itama nana ta hau suka nufi asibitin dake gefen kauyen kaɗan, gwajin farko likita yace tanada ciki, mama tace bata yadda ba saide ya kara gwadawa, kara gwaji yayi yace "tabbas tanada ciki"
mama zama tayi sabida jiri ta dafa kanta tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un na shiga uku rahama me kunnuwana suke jiye min?"
shiru tayi, tashi mama tayi tace "rahama maganan da nakeji gaskiya ne?"
shiru tayi tana kallon kasa, marinta mama tayi tace "ki gayamin gaskiya ne?"
shiru tayi, mama ta kalli Dr tace "dan Allah ka zubar da cikin nan yanzu kafin mahaifinta yaji, dan Allah ka zubar ka rufamin asiri"
ya kalli rahama sannan yace "kin yadda a zubar?"
tana hawaye tace "eh"
ya basu takadda yace su sa hanu nana ce tasa hanu, ya bata magani sannan yace "kuje ciki ze zube idan be zube ba ga wannan ku bata tasha, idan shima be zube ba ku bata wannan, idan har wannan be zubar ba to cikin ba zai taɓa zubewa ba"
mama ta karɓa tace "mun gode Allah ya saka da Alkhairi"
kuɗinshi suka bashi, har suka koma gida babu wanda yayi magana, saida suka koma gida mama ta sata a gaba tace "waya miki ciki rahama? meyasa kika zama shiru shiru na munafurci? kika cutar dani rahama? dama ba'a talla kike samun kuɗin ba?"
girgiza kai tayi tace "mama wallahi..."
duka mama ta fara mata, kuka take yi tana cewa "mama kiyi hakuri na tuba"
mama tace "waya miki cikin?"
a hankali take tambayanta sabida kada baba yaji, tace "Alhaji Alhasan ne"
tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un na shiga uku"
ranan wuni sukayi cikin kiɗima, haka dai taci gaba da bata maganin amma fa ciki yaki zubewa, duk maganin da suka bata be zubar ba, haka har suka koma wajen Dr ya kara bata magani ciki yaki zubewa, yauma dawowa sukayi daga neman magani mama a gajiye ta zauna tace "ya Allah na gaji rahama kin cucemu"
rahama banda kuka babu abinda take yi.
cikin ya fara girma mama ta hanata fita koda kofar gida ne tana killace a gida, mama ta ɓoyewa baba batasan ta yadda zata fara faɗa mushi ba, cikin yayi girma sosai mama tasa abin a ranta ta rame ta zama wani iri, ga rashin kuɗi ga damuwa, fitowa tayi daga ɗaki tana rike da bayanta sabida cikinta yayi nauyi, baba wanda ya shigo yanzu daga masallaci ya tashi, cikin dauriya yace "ina rahama?"
mama tace "tana bacci"
cikin tsawan da yasa jikin mama ya fara rawa yace "tashe ta kuzo tare"
zuwa tayi ta kira rahama dake ɓoye a bayan kofa tace "sai kizo tunda burinki ya cika kin sani a masifa"
jikinta yana rawa tasa hijabi ta fito.
*Shima ɗa ne complete is 400 via 8144818849 hauwa shuaibu mapi moniepoint evidence via 08144818849*
~Kauyen Tufan kauye ne karami wanda yake ɗauke da tarihi sabida mutanen dake cikin kauyen sun bar yaransu sunyi karatu, basu bari kansu ya kulle ba yaran sunada ilimi sosai da basira hakan yasa suka samu kuɗi da ɗaukaka, saide duk yawanci basa zama a kauyen sunfi zama a waje kamar su Abuja lagos da manyan state, iyayensu basu yadda suna binsu ba koda sunyi kuɗi sunfi son zamansu a kauye sabida al'adunsu da kuma tushensu basa so ya ɓaci, a wannan kauyen akayi wata budurwa kyakkyawa wacce mutane dayawa suke sa ido a kanta, kyawun da take dashi yasa kowa yake so ya aureta amma tafi son tayi karatu ko Allah zesa itama ta wanke iyayenta daga talaucin da suke ciki, itace babba se kannenta biyu mace ɗaya namiji ɗaya, ta haɗu da wani saurayi wanda shima asalin ɗan kauyen ne amma yayi kuɗi yana Abuja acan yake aiki, watarana yazo ziyara kauyen ya ganta yaji duk duniya babu wacce yake so kamar ita, sunanta RAHMA ta kasance me kamun kai, duk da tana talla sabida iyayenta talakawa ne hakan be hana ta kama kanta ba, kannenta bata yadda suna talla ba itace take taimaka musu da komai, mahaifinta baida lafiya yana da ciwon hawan jini wanda ya kawo mishi ciwon ɓarin jiki, itace take kula da komai, wannan mutumin babu wanda be sanshi ba sunanshi ALHASSAN amma ana ce mishi ALHAJI ALHASSAN MEDALA yau sati kenan da ganin wannan budurwa kuma yana nemanta ido rufe.
kamar kullum yau ma ta fito da talla a kanta tana tafiya cikin nutsuwa alale ne a kanta domin shi take siyarwa, daga kayan jikinta zaka san tabbas tana fama da talauci amma fa masha Allah ubangiji yayi halitta, motar da taji ya tsaya a bayanta yasa ta juyo tana kallonshi, da hanu yayi mata alaman tazo, cikin tsoro ta nuna kanta alaman ni?
ya ɗaga mata kai, make kafaɗa tayi alaman ba zata zo ba, fitowa yayi daga motan, baƙi ne amma ba ƙirin ba, yanada kiɓa ba sosai ba skin nashi yana nuna hutu da kwanciyar hankali, yanada kyau daidai gwargwado, tana tsaye tana kallonshi har ya karaso ya ɗaga babban riganshi ya gyara, shadda ne me masifan tsada, a gabanta ya tsaya, ta ɗan sunkuya alaman girmamawa tace "ina kwana"
murmushi yayi sabida yau sati ɗaya kenan da yake nemanta kuma itace dalilin da yasa be tafi ba, duk da ana nemanshi sabida manya manyan company's da yake contract dasu amma ya kashe wayarshi domin dole sai ya ganta, amsawa yayi sannan yace "ya sunanki?"
a hankali tace "sunana Rahma"
yace "sannu rahma idan ba damuwa muje motata muyi magana"
waro manyan idanunta tayi ta dafa kirji tace "mota? gaskiya ba zan iya shiga mota ba"
murmushi yayi sannan yace "to ki bani numbern wayarki"
tace "banada waya"
cikin tsoro ta tashi kawai zata tafi yace "tsaya mana rahma inane gidanku?"
ganin ba siyan abinta zeyi ba yasa ta fara tafiya sabida bata son irin haka"
ganin ta tafi ya tsaya shiru yana bin bayanta da kallo, murmushi yayi sannan ya shiga mota ya tafi, saida yamma likis ta dawo gida ta gaishe da mamanta da kuma babanta dake ɗaki yana kwance, kawarta me suna NANA ta dawo daga islamiyya kaninta kuma sunanshi yaseer se bayan mangrib yake dawowa daga garejin gyaran keke, zama tayi tana kallon nana dake karatu tana burin yin