x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - BIRNIN GAYU

  • 21001 words
  • 24000 words
  • Out of 99560 words

Category: Love Stories

Views 157

09 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
ta rabu da Inna tun tana
karama har ta taso su yi fada su yi wasa su yi
dariya. '
Fadawa jikin Inna ta yi tana kuka.
Inna ma .sai da ta yi kuka tana lallashi, ganin
hakan ya sa Hajiya ta ce kar ta damu za
a dinga kaita ta ga Kakarta, kuma Innan ma za
ta iya zuwa ta ganta a duk lokacin da ta ke so.
Haka dai suka yi ta kwantar ma ta da hankali har
suka tafi sun yi akan za a dinga tarawa Deeda
kudinta na aiki sabo da Inna tace sana'ar da ta
keyi ya isheta na buka'tun yau da kullum ‘ita
kuma kudinta sai a tara ayi aurenta da su.idan
har lokaci yayi
()()()()()()()()()()()
kwana-a-tashi, a hankali Deeda ta Asoma
sabawa da rayuwar BIRN IN GAYU, haka Hajiya
ta dinga nuna ma ta komai da komai yadda ake
aiki da shi. Deeda ta lura Momi mace ce mai
fara'a da jan mutane a jiki ta hanyar Siyasa. a
Haka nan ba ta da matsala da mutane ko sa ido
da takura, kullum tana cikin fara'a. Sai dai abu
guda Hajiyar muguwar 'yar kasuwa ce me son
kudin tsiya, duk da tana da kudin amma ba ta son
ta ga ta yi asaran k0na Sisi, haka nan bata bari
kudadenta su makale, duk rintsi sai ta sai'n
ayadda za su fito. , Tun da ta fahimci Deeda
yarince mai'wayo, dabara da saurin fahimta saita
jata a jiki yadda Deeda ke hada ma 'kudi na
kayan da suka shiga suka flta bata' kuskure shi
ya fi birgeta, yadda Deeda ke aiki da Computer
lokaci guda tana ma ta Transfer na kudedenta da
ke Bankunan qasashen waje zuwa na Gida naija
yana burgeta, ta lura yarinyar
Bayan wannan Deeda ke gyara ma ta Dakinta don
ba ta yarda wasu masu aiki suna mata gyaran
daki sabo da tsoro da rashin yarda sai '- -
a yanxu, duk wani me harka da Hajiya ya san
Deeda,‘ ta kan bata wasu: shawarwarin wani
lokaci ta yarda
kasuwanci kala daban-daban; take Wani lokaci
Deeda takanyi‘ tunani da mamakin yadda Gidan
yake ' ba ruwan wani da wani, kowa harkar
sa yakeyi ba sabo ba shaquwa tsakaninsu wani
lokaci sai ta yi kwana biyu .bataga wani
mahaluki ba daga Hajiyar sai 'yan Aiki,‘ _ duk
zaman da ta yi a Gidan bata ga
'yan Gidan ba, ta dai ga »
Hoto, Wanda aka ce ma ta sun yi anre amma
bata taba ganin sun 20 ba. '
Bayan maganar kasuwanci da wani aiki ko
shawara ba abin da ke hadata da Momi, haka ma
su aikin Gidan ba mai mata magana balle ta yi
sabo da su, kowa harkar gabansa ya kd ‘ Wannan
ya sa Deeda ~ta tsinci kanta cikin kewa daga ita
sai TV sai Camputer wanda sune Abokanta masu
debe mata kewa anba ta komai;
Ci da Sha da Sutura komai ta sameshi a wadace,
zama cikin ni'ima da cima mai kyau yasa ta
murje ta yi Haske ta yi Kyau, sai dai ba wani
farinciki ko nishadi a tare da ita, jikinta da
yanayin rayuwarta ya canja: sai dai cikin zucin ba
wani canji, zuciyarta tana nan kamar~yadda ta
ke da, Karatunta ya tsaya sai dai ta godewa
Allah‘da ta samu wannan dama. ‘ ‘
‘ Abu . guda ke sa ta farinciki in tana gaban
Computer ko in Hajiya ta ba ta wani aikin don da
alama Deeda tana da sha'awar (Business)
kasuwanci wanda a zahiri shi ne burinta ta
karanci Business ta Zama babbar Yar kasuwa
wata rana.
Lokacin da maganin Deeda ya kare ta cewa Momi
za ta gai da Inna, ba ta musa ma ta ba kuwa ta
bata Driver ya kaita akan da yamma zai dawo ya
dauketa.
///////////////
iNNA ta ji dadin ganin Deeds sosai, musamman
yadda ta ga ta goge ta murje tayi kyau, ga Kaya
kamar wata 'yar Mai kudi ' ta fito fes! Fes!! da
ita, Inna Baki a washe. -- Tare suka je Asibiti.
Yadda Ibrahim ya ga Deeda tabbas akwai canji
sosai a tare da ita, tun daa yanayin shigarta,
yanayin maganarta da wayewarta ya bam-banta
da yadda ya taBa ganinta. Anya zai iya ma ta
wani magana game da "' Sabeer‘.’ . Ga Sabeer
abin nasa sai gaba ya ke, ga Daddy ya kusa
dawowa har yanzu ya kasa Control din Sabeer. '
Deeda ta katse masa tunani. "Likita lafiya kuwe?
K0 akwai matsala ne?" " "Ba komai ina dan wani
tunani ne amma ba a
game da keba
' A halin yanzu ke dai ba ki da matsala don haka
ina ga ba sai kin Kara shan wani magani ba, da
:alama inda ki ke zaune ya karbeki don, na lura
ya taimaka gurin gyara fatar jikinki.
Yanzu za ki iya tafiya, sai dai in akwai wani
matsala nan gaba ki dawo". ;
"Na gode Likita, zan wuce
"To ki gaida inna".
“Za ta ji, tare da ita ai muka zo tana waje
Ya mike yana murmushi ya ce, "Bari in 20 in
gaida 'yan mata kar ta fasa auren
Dariya sukai duka suka fita a tare. Inna na
ganinsu kuwa ta mike tana dariya, suka gaisa ya
ce "Na 20 gai da Kaka 'yan mata kar wani ya min
shigar sauri”.
"Oh to da ba ka 20 ba sai in yi sabon saurayi don
samari har sun min yawa".
wayar da ta yi Kara ya ja hankalinsu.
Bayan daga wayar ta yi sallama ta dan ja
gefe sannan ta'dawo wajensu tana cewa Inna mu
tafi
Nan suka yiwa Ibrahim sallama, har sun fara
tafiya Ibrahim ya tsai da ita, ya iso garesu ya ce
"Miss Dddda in ba za ki damu ba zan iya samun
lambar Wayarki in Saurayinki ba zai damu ba ya
fada cikin zolaya. ‘ “ Ta yi dariya ta ce "Su Likita
manya, Saurayina ba zai damu ba, ga lambata Ta
rubuto masa, ya yi godiya gami da cewa zata lya
Jin kiransa kowanne lokaci. Ta so tambayar'
nasa lambar sai . ta kasa da ya koma ya zurawa
Wayar tasa ido yana kallon lambar
Karfe biyar ta‘yi sallama' ‘da. Inna da Tabawa
don dama dazun Hajiya ne ta yi mata Waya ta
tambayeta karfe nawa za a 20 daukarta. _
'''''''''''''''''''''
Wani dare Deeda na zaune‘ gaban
Computer bayan idar da’ Sallar lsha'i ta‘
mai da hankalinta sosai kan Computer
din sabo da wani Bussiness School da, ta shiga
online(P. C Training and Business Collage) tana
jin
dadin Karatun sosai da koyarwan, haka nan tana
ganewa da yake tana son abin. ‘
Wayartane yayi kara, ta yi mamaki kwarai don
kuwa da_ wuya Momi ta kirata a wanna lokaci.
Haka nan tsira‘run wanda takeda Lambarsu masu
siyen Kaya yana wuya su ma ta Waya a irin
wannan lokaci.
Ganin an matsa da kira yasa ta mike ta nufi inda
Wayar ke Chaji ta dauka, ta ga sabuwar Lamba
ce. ‘ .
Nan ta daure ta danna 0k. tare da yin Sallama.
Muryar Namiji ce.ta ji an amsa ma ta sallamar
nata. __
Yayi dariya ya ce, "Na yi sa'a kenan da har
inatunanin ba za a dauki Wayata ba
Da fatan dai ban matsawa ranki shi dado ba?"
" wace ni?" Ta amsa masa.
""Na so in fahimci' muryar".
"Dr. Ibrahim ne. Ya ba ta amsa.
"Likita Bokan Turai, barka da dare”. Ta fada tana
yin dariya, da alamar kuma ta ji dadin kiran nasa.
"Lafiya, Alhamdulillahi".
"Dama bugowa na yi mu gaisa in ji ya jikin
naki?;Da fatan dai ba wata matsala
"Ba komai, jiki da sauki na warware, ina godiya",
Sun jima suna hira sannan suka yi sallama.
Tun daga wannan rana Ibrahim ya kan yi ma ta
Waya a duk lokacin da ya samu saukin aikinsa.
Haka nan itama tana kiransa sabo da shakuwa ta
shiga tsakaninsu., duk da ba ganin juna suke ba a
, Waya ne’
Sau da dama Ibrahim ya kan nemi shawara
wurinta, haka itama ta kan bude masa
damuwarta da matsalolin da ta ke fuskanta na
rayuwar yau da kullum, domin Deeda jin Ibrahim
take ‘Kamar Aboki, Dan uwa,
Bayan Kakarta ba wanda ta taba kusanci da
shakuwa da shi sai Ibrahim.
A hankali Ibrahim ya fahimci Deeda da ’yadda
take, yanayin rayuwarta da tunaninta duk mai
sauqi ne.
Haka idan ta samu dama za tai abu da yawa a
duk lokacin da ya tsinci kansa cikin damuwa k0
wani Bacin rai to Wayar Deeda da kalamanta ke
kawo masa sauki, yana samun nutsuwa sosai ,da
: kullum sai ya tambayeta Inna mai Fura.
,Yawancin wayarsu yakan mata magana akan
halayen Sabeer, don har yanzu ya kasa shawo
kansa kokarinsa Sabeer ya'fahimta.‘ ta kance ita
laifinsu take gani DA fun farko suka kasa controll
dinsa said yanxu
' ' Ibrahim ya kan yi murmushi ya ce, "Deeda ba
za'ki fuhimta ba a hankali,'wataran zan warware
miki zan fahimtar da ke dangantakar da ke
tsakaninmu da Sabeer da Gidan su halin yanzu,
mu barshi a yaddaki kace . Ta yi ajiyar . zuciya
tace, To.shi ke nan 'Ibrahim, ni dai ‘na san kai
mutumin kirki ne (Very good human being) wanda
wannan halin na ka na daya daga cikin abin da
yake hurgeni ina ganin girmanka da dajarka, ya
yin da Kaninka.,.." ‘ .~
"Ya isa Deeda, ba zan jure yabon dakike min da
kushe Sabecr be, mu bar maganar". Ajiye Wayar
ta yi ba tare da Sunyi 'sallama ba, saboda ta
fahimci maganar da ke had'asu fada . ‘kenan Ta
kan yi mamakin irin yadda Ibrahim ke qauar
Sabeer baya Kaunar abin da zai taBashi, baya iya
jure jin. lafin Sabeer daga bakin wani. A hankali
Deeda ta fahimci cewa ta yi wani irin shakuwa da
Ibrahim cikin kanqanin lokaci. '
&&&&&&&&&&&&&&&&&
Karfe biyun dare amma Ibrahim ya ‘kasa ' .
rintsawa yanata kaiwa da kamowa, komai ya
masa Zafi. Ya tuno yadda suka kwashe da '
Sabeer sannan damuwarsa shi ne wasu sababbin
ABokai da ya ga Sabeer din ya sake, ba su da
aiki sai kashe kudi yawa zuwa Party da neman;
Matan tsiya Maimakon .Sabeer ya gyaru sai kara
dauko hanyar-lalacewa' yake
Ya kasa rikon Sabeer, ya kasa kula da shi, ya
kasa riqe amanar da aka bashi, ga aiki yayi masa
yawa ga nauyin Asibiti a kansa ga na marasa
lafiya ga kuma Kamfanin Alhaji, Kudade da yawa
sun bata wanda bincike ya nuna da Hannun
Hajiya ciki, komai ya masa zafi, ya ma rasa abin
yi, ga nashi Personal Problem din.
Ya dauko Wayarsa ya kira Farida idonsa jawur
"Kanina". Ta kirashi muryarta qasa qasa
Hakan ya fadar masa da gaba. '
"Yayata lafiya na ji muryarki haka?” "Kanina na yi
aiki ne kawai na .gaji, kaina ke dan min Ciwo”.
"Yayata Please ki dinga hutawa kinsha Magani
ko‘ in20 ne?
Ni fa yadda na ji ki ya jefani cikin tashin
hankali‘da damuwa". .
"Kanina kar ka damu na fadi ma gajiyace kar ka
damu zan kula da kaina”.
Sabecr da da Daddy suna bukatarka , ke ba kya
bukatata Yayata". ' "Ba haka bane Kanina".
"Haka ne Yayata?" .-
"To in kc ba kya buqatata ni ina buqatarki
Yayata"
Ya fada cikin murya mai rauni.
"Kanina ka yi hakuri na sun ban maka adalci ba.
ka yafe min kanina, ka yi qokari ka fahimci
matsalata".
Tuni har hawaye ya wanke ma ta fuska Kanina
akwai matsala k0? Me ke faruwa?
"Ba komai Yayata". Ya yi dariyar dole don
kwantar ma ta da hankali.
"Kar ki damu, kawai dai na tsinci kaina cikin
kcwarki ne ina missing dinki, kar ki damu, sha
Magani ki kwanta". .
"To .Kanina na gode. Ina nan zuwa very soon”. ‘
"'Allah Ya kawoki lafiya . Na san in kin zo da
yardar Allah komai zai dai-daita".
'Ka kula da kanka kanina da Sabeer da Daddy
gaba gaba daya. Sai da safe".
Ta yi saurin ajiye Wayar. Ya jima yana kallon‘
Wayar sannan ya soma danna lambar .Deeda sai
kuma ya fasa, qarfe ukun dare me zan ce ma ta?"
Ya nufi dakin Sabeer don ganin me yake ya yi
Bacci in bai yi ba zai masa magana da gargadi
ya qara tuna masa abin da Mahaifinsa ya ce, ya
kuma sanar dashi Daddyn ya kusa dawowa.
Hango qofar dakin ya yi a bude Wuta a kunne
abin ya ba shi mamaki sosai, ya isa dakin da
sauri, gabansa ya yi mummunar faduwa, Sabeer
ne ya gani kwance da Kwalaben Giya, kwance a
gefensa baya cikin hankalinsa yana sake da
kayansa da Takalmansa da wasu Kwayoyi a
gefensa.
innalillahi wa inna ilaihirr'jiu ’un.’.’” Ibrahim ya
fada cikin tashin hankali.
Wani irin baqinciki da tashin hankali ya bayyana a
fuskarsa. " ' " "
Ya isa‘ gareshi da wuri.
"Sabeér" Ya kira sunansa da karfi. ‘ *
"Wato abin na ka har ya kai haka?"
' ‘ ldanunsa suka kada suka yi jawur, kukan ma
ya kasa, ya lura Sabeer k0 hannunsa bai iya
dagawa balle bude ido sai surutan banza
Cikin takaici da bakinciki ya cire, masa Takalma
tare da gyara masa kwanciya, ya tattara
kwalaben ya bude wani Raramin Fridge da ke
manne a bangon Dakinsa.‘ Kwalaben giya ne
masu tsadar qaske a cike a ciki. ‘
Nan ya hau bincikc k0 ta ina a dakin, haka ya
dinga yin karo da kayan maye kala-kala. Bai taBa
shiga tashin hankali da bakinciki irin na wannan
Dare ba.
"Ya aka yi na yi sakaci haka. na ci amanar
Maman Sabeer na ci amanar Farida ban rike
Sabccr ba ban kula da shi ba".
Nan yakama kai awurin yanakukan bakinciki da
takaici tare da tausayawa rayuwar Sabeer in ya
mutu a wannan hali ya yi asara babba ' .
- Sam‘ ba shi da nutsuwa _a duniya balle ya
samu nutsuwar neman lahira. ' ~
A wannan dare Ibrahim bai rintsa ba ya kwana
yana sallah yana kai kukansa gun Allah tare“ da
Addu'o'i sosai.
Hakan ya dan ba Shi nutsuwa. Da Asuba ya kira
Farida amma ba ta dauka ba, ya sake kira, wani
Likita ya dauka ya masa bayanin tana Asibiti
gaskiya bata da lafiya, amma ta ce ba ta son ya
sani, amma Likitan ya tabbatar masa da cewa
jikin na ta da sauki.
Tashin hankalin da lbrahim ya tsinci kansa ya.
munana. ‘
"Yayata ba lafiya ga halin da Sabeer ya shiga, ga
Asibiti ga Kamfani, ga Daddy baya nan Duniyar tai
masa zafi ya rasa abin yi. ,
"Shin da wanne zaiji? Ba zai' yiwu ya tafi wurin
Farida ya bar Sabeer, a wannan haliba , ga Asibiti
da kamfani duk suna buqatarsa, yana kaucewa
kadan komai zai tsaya.
Yana cikin wannan halin nan ya hango Sabeer ya
tashi cikin fishi ya nufi inda yake ya hau fada ta
inda ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba.
Nan Sabecr ya zuciya shima ya amsa masa
cewa, "Uncle IB zan yi abin da na ga dama ba
wanda ya isa ya takura min ko ya‘ hanani. To me
ye in na sha Giya? Me ye a ciki za ka zo kana
min fada? - '
Ni fa ba zan Yi aiki irin ka ba kullum Asibiti
kullum kamfani, zan rayu yadda na keso, Kudine
Uwata da Ubana sun tara min domin jin dadin
‘rayuwa, to me ye damuwarka
dadin rayuwa , ba za ka
Ka matsa min ka sa min ido. Ina kyale ka ne
albarkacin Sister.
Ka rabu da ni, zan yi rayuwata yadda na ke so,
kuma Giya ba wanda zai hanani in sha. Mene ne
in na sha Giya?"
"Tas" Ibrahim ya wankeshi da Mari.
"Meye in ka sha Giya? Ba ka san me ye ba in ka
sha Giya kana dan MusUlmi kana irin wannan
maganar?
Kai da ka san illar shan Giya da muninta da ko'
sunanta aka ambata sai ka ji tsoro da kyamar
kiran sunan na ta. .
Duniya kawai ka _sa a gaba, ba ka san zaka
mutu ba, k0 ba ka san RAYUWA BAYAN MUTUWA
BA? K0 ba ka san kwanciyar Kabari ba ne?
. Ji bi kanka, ba ka jin‘ kunyar zama cikin duhu
ba'ka san addininka ba? '
Ada ina ganin abin na ka kamar yarinta amma
yanzu na lura ya zama ganganci;
To bari ka ji, daga yau na rufe duk wani Account
dinka na kudi, duk wani hanyar Kudi na toshe
maka ita, Makullan Mota babu su, kuma tun da
ka ce ba za ka yi aiki ba, to ba kai ba fita. kana
nan
cikin Gidan nan, ba Waya ba Abokai duk na
rabaka da komai sai ka zaBa k0 zaman Gida a
kulle ko ka bini Office qafata-Kafarka duk inda na
shiga, zabi ya rage na ka".
Nan ya ja kofar dakin ya rufe ya tafi ya kyaleshi
yana ihu yana kwalla masa kire.
"Uncle ib please ka budeni ba zan iya zama a nan
ba.
Please Unclc IB ba zan kara ba, zan yi duk yadda
ka ce‘
Wayyo Uncle iB to ka mai da ni wurin Sister".
Haka ya yi ta ihu amma bai saurareshi ba ya
wuce ya figi Mota.
A wannan lokacin mutum daya ya keson gani ita
ce Deeda, sai dai ya yi rashin sa'a yana zuwa
Gidan ya samu Inna ta ce masa ai Dccda ba ta
nan, ba a nantake zama ba. . ‘
Bai Kara ce ma ta komai ba ya fita ya kira
Wayarta. Sai da yaiyi qara' sau‘ uku kafin ya kai
ga ta dauka, kafin tace Wani abu ya tambayeta.
"Kina ina?"
"Lafiya?" Ta tambaya.
"Ina son ganinki ne yanzu-yanzu! inda hali ki
fada min inda ki ke yanzu zan 20 in sameki, kar
ki min wata tambaya sai na 20".
Ta lura yana cikin zafi da Bacin rai, don haka- ba
ta sake masa wata tambaya ba.
Ya sake tambayarta, "A wacce unguwa ki
ke?"
"Ka san BIRNIN GAYU?" "Birnin Gayu‘?" Ya
maimaita cikin mamaki. Ta ce "Eh inkazo Gidan
ka yi min waya". "Kina nufin a Unguwar ki ke?"
Ta amsa da, "Eh". "To shi ke nan gani nan
zuwa". Ya 'ajiye Wayar ya tafi yana tunani. Shin
wane Gida Deeda ta ke a unguwarsu? To koma
ina nevdai yanzu burinsa ya ganta k0 za ta
taimaka masa ya samu saukin matsalarsa. Haka
Deeda ta dinga kaiwa da kawowa yanda taji
tashin hankali a muryarsa yasa ta cikin damuwa,
sai ta ji itama na ta hankalin ya tashi. Momi ta.
fIto ta ce "Ta kula da Gidan 2a ta shiga wani
miting a Office ana jiranta". Nan ta ma ta sallama
ta fita, ya yin da Deed: ta kasa zaune da tsaye,
Wayar‘ Ibrahim ya shigo, ta yi saurin dauka yace
ma ta, "Ga n’i a BIRNIN GAYU, ta ina ki ke da
Gidan?"
"Jirani a wunrin gani nan fitowa“;
Nesa' da Gate din kadan ya yi parking yana
jiranta, ya yin da ya zurawa wurin ido yana jiran
ya ga ta ina za ta bullo. '
Bude Baki ya yi mamaki ya bayyana a fuskarsa
lOkacin da ya hangota tana fitowa -daga BIRNIN
GAYU, wato cikin Gidansu. :
Tsaye take a qofar Gidan tana kalle kalle.
Ya lura da hakan hakan ya sa ya fito daga cikin
Motar ya nufo gareta, itama ta ganshi ta isa.
gareshi fuskarsa cike da damuwa ta kula ta ce
,"Laflya Likita, me ya-faru haka .ka ke son
ganina?" "
Ya kalleta cike da mamaki ya ce, "Deeda dama a
BIRNlN GAYU ki ke?"
"Eh, labarin mai tsayi ne a Gidan na.‘ ke amma fa
ba Gidanmu bane, aiki na ke a Gidan".
‘ "Aiki? Wane irin Aiki?" ' ' Ta ja dogOn numfashi.
, a i "Zan, fahimtar da kai a hankali. Yanzu dai ka
fada min mene ne?"
Mu je can mu Yi magana".
Ya wucc, ba ta bishi ba sai dai kallon mamaki.
Nan ya dawo ya jawo hannunta har suka isa
bakin wani karamin Garden yaja kujera ya ce,
"Zaunai ‘ Ba ta musa ba ta zauna, ita dai ya
zame ma ta- abin kallo da mamaki.
Ganin haka ya sa ya kalleta ya ce, "Yanzu zan ba
ki dukkan wani amsar tambayarki.
Deeda ina cikin damuwa da tashin hankali '
wanda na ji ina son ganinki don duk duniya a
yanzu bani da wanda zan zauna in fada masa
matsalata.
Deeda k0 ba ki min maganin matsalata ba zan
samu saukin zuciyata tun da na bayyana miki
damuwa—ta.
Deeda ki taimaka min koda kalaman karfafa
guiwa ne da kwantar da hankali don ina
bukatarsu".
Hawaye ya gangaro masa wanda hakan ya daga
hankalinta, Ibrahim da kullum murmushi ke
shimfide a fuskarsa wanda murmushinsa ya isa
‘ya
End Ads