gate din Gidan ta tari
Taxi a nan yayi gaba da ita. - Sabccr. ya girgiza
kai 'cikin. .takaici, ya juya da sauri'ya nufi‘
Bangarensu ya, karasa. wuein Inna mai Fura tace
masa Deeda Asibiti taje. Nan da nan ya-rude. ' .
"Ba ta da: lafiya ne?" ‘ Kafin Inna ta yi-masa
wani baya'ni ya fita‘’ da sauri ya zari mota ya
nufi Asibitin. Inna ta biShi da kallon ' mamaki
*.* .*v* *9*
dccda ta, samu‘ Ibrahim game a. office ta Yi
mamaki kwarai donta zaci'_za ta samu yana
ganin marasa lafiya ne
Sallama ta yi masa ya amsa tare da juya ma ta
baya ya ce, kema dai kin iya fitna ,sa' da ki ka
biyonj Asibitin, ba za ki iya hakura na dawo ba?"
‘
"Ba ni' da wannan. hakurin Ibfahim wai me ke
farawa ne, na kasa fahimta? wane dalili ne zaisa
a bani matsayin da bankai ba? deeda hakane
tunda kikaga qara miki girma murna ya kamata
kiyi A'a Ibrahim, ina murna da- inda aka sani' da
na ' jin dadi a‘inda' na ke,.da nafi son inkai
matsayin da aka kaini a yanzu da gumina
kokarina". , Dceda kiyi godiya ga abin ‘da ki ka a
samu, da. godewa Allah,.kin samu abin da kike so
cikin sauKi"Na ji Ibrahim na gode Allah; amma ina
‘son naji dalili? Dole akwai dalilin yes akwai dalili
daya ne', shi ne ‘kawai kin -cancanta 'da hakan,
domin kina‘ da basira a aiki, you ur good in
business.Sannan Sabccr yana son-haka
"Sabeer yana son haka? Me yasa Sabeer zai so
haka?" .
Ibrahim ya ,juyo a fusace ya ce, "Ya isa haka! A
halin yanzu ina cikin damuwa, kar ki Kara min da
tambayoyinki. _
Sabeer na'son haka,‘ that means yana son haka,
karki‘ Sake mini‘ wani , tambaya, baya nan"
Ta tsorata kwarai da ganin yanayinsa, ba ta taBa
ganinsa cikin zafi da tsanani' haka‘ba Sai yau
’ Tuni jikinta ya hau 'raWa, idanunta Saka yi ja,
ta ji kanta na sarawa; Ba ta iya cemasa komai
ba ta mike zata-fita. «
' A lokacin' ne'kuma Sabeer ya turo Rofa ya
shigo'cikin Office din a rude. .
"Deeda! Deeda!! - Dceda!!!‘ Ba ki‘ "da‘ lafiya k0?
Ba da na jawo'miki zazzaBi ba?"
‘ Zai taBa goshinta ta yi saurin ’kaucewa,»ta
dubeshi'-a fusace cikin daga‘ murya da Bacin rai
tace "Ya isheka haka‘Sabeer! Bana son abinda ka
kemin!!
Tana gama fadin hakan ta yi tsaki ta fice daga
office din tare da‘rufo'kofar office din da karfi,
garam. '' 'Tuni Sabeer ya ji hankalinsa‘ ya ’yi
mummunan‘ tashi a ransa ya ji ba‘bu dadi. Ya
sunkuyar kai Kasa kamar zai yi kuka.
_ Ibrahim ya matso gareshi tare ‘da dafa
kafadarsa' ya ce, "Kaeka damu-Sabcer ba abin da
ya sameta kawai gajiya‘ ne da ciwon kai, na
dubatakuma na ba ta magani, ba ta 'da ‘wani
matsala, kar ka damu da abin da tace, Stress ne
ya mata yawa
"da laifinama . Ya fad'a cikin rashin jin
dadi.
"Nina matsa'ma ta yau harna jawo ruwa
ya bugeta, ga shi yanzu na jawo ma. ta
zazzaBi".~
. ‘ ’Hey! ba 'kOmai ba wani abin daga hankali
bane,‘kar ka damu Sabeer, just ka ragé shige.ma
ta, ka» daina yawan _céwa' za ka taBata k0 ka‘
kai” ma ' ta :hannuu, bata saba da wannan'
rayuwar. ba she will not like it, zAta iya yin
tunanin ’Wani abu daban ka ji"
"Na ji Uncle IB, ba zan sake'ba in dai Deeda
bataso, bana son abin‘ da zai dameta, zan je in-
bata haquri
"Ka. bari ba yau ba, yanzu- tana- bukatar hutu,
ka bari sai gobe,‘kar ka matsa. ma ta".
"To Uncle IB k0 Waya ma kar in yi ma
ta?" , . .‘ ,,’ 'Eh ka baei sai. goben .
Ya bata fuska ya ce,‘"1na son na ganni tare da'
ita- Uncle I will (Mike it) idan ina'tare da ita".
. Ibrahim ya 'yi‘ masa murmushi ya‘ ce, "Karka
damu, you Will be with her, .ba kuna tare a office
ba Tare ?
Ya- yi dariya ya‘ ce, "Haka ne, amma 'ni dai
Uncle IB sai na je'ko sau daya yanzu in gani ’ya
jikin nata yake?" ' . -
Katin. ma ya ce wani abu tuni Sabeer ya juya ya
fice daga’ Office din da sauri. __
Ibrahim ya jima yana kallon koofar d yana‘tunani.
.
Haka kawai ya ji' ba zai iya komawa Gidan ba,
gara ya zauna Busy a Asibitin ko zai ji saukin
matsalarsa
ta?"
‘ halin da 'lnna mai Fura ta ga Deeda
ta shigane' ya dameta matuka; .
Ta matsokusa da ita. -
"Deeda me ye yake damunki?"
Decda ta matsa ta‘kwanta a cinyar Kakar ta ce,
"Inna nima ban sani ba, kawai dai na ji zuciyata
‘ba'dadi ne.
Inna kin san me yake faruwa yau kuwa?"
"A'a sai kin fada'"; lnna ta ba ta‘amsaa
Nan, Deeda ta kwashe labarin abin da ya faru kaf
ta' fadaWa Inn’mai Fura. ’-
Inna ta girg‘iza‘ kai ta 'ce, ."Gaskiya ne Decda,
abin’akwai' alamar tambaya. Sai dai karki damu,
ina‘ .ga ai gaskiyarki da amanarki .ne ya’ jawo
hae aka baki wannan matsayin
Jajircewarki; Ce tasa ‘kika kai .wannan’ matsayi
Ki cire damuwa daga ranki, ki ki karbi
Aikinki hannu bibbiyu". "Na 'ji Inna, 'amma Inna
kulawar da Sabccr ke min yana ban tsoro, yana
sa' ni ,tunanin
ki me
a wani Bangaren'kuma ina ganin' ba Wani abu
bane, kawai haka halinsa yake, kar in je“ in yi
masa zatOn da ba haka' bane".
‘ "Kar ki damu Deeda, saki ranki ba komai bane
kar ma'ki sa wani tunani a ranki".
, ' "To Inna. Wallahi kalamanki ba Karamin
kwantar min da hankali sukeyi ba. sannan Inna
ina so a ciki'n Kudinda na tara na ‘Aiki na kaiwa
Baba‘ ko na siya masa wani abu";
Nan Inna ta Bata fuska. .
"Wane Baban? Baban naki da ya manta da ke, ya
Yar dake?" ' - -_ ‘
"haba Inna, ai koma‘ me ya yi shi Ubana ne
Mahaifi, don .ya yar da ni‘ ni dai ba zan yar da-
shi ba, in dai ina neman albarka' da gamawa
duniya duniya lafiya- dole» in je in da yake in
nemi albarkarsa"'
Inna_itéce, "Shi kenan tun da haka 'ki‘ke so, zan
baiwa' Tabawa'Kudi ta aika masa da su. Sannan
karshen watan nan zamu je Kauyen ki gai da’ shi
da sauran ’yan uwa"., '
Ta yi murmushi; "
"Yauwa Innata.Allah Ya barni da'ke"..
"Améen 'Deeda Inna". Ta- fada tana dariya. ‘ '
Haka Sukayi, ta hira, motsin shigowar
Sabeer ya sa Deeda ta'yi likimo ta rufe idon ta A
Cinyar lnna kamar ta yi bacci. Tana jinsa ‘da .
Inna suna ta hira. , ‘ Motsi kadan sai ya cewa
Inna, "Jikinta - _ ba zafi dai k0? Ba zazzaBin k0?"
’
Inna ta tayu dariya. "Ba komai Sabecr, gajiya ce
kaWai, Bacci ta ke tana hutawa."
"To '
' Ya' fada'yana‘ murmushi yana kallon
fuskarta,“ya kasa_tafiya. ‘ ‘
Déeda tun tana jinsa sama-sama har‘
BaCCin gaska ya dauketa ba ta san tafiyarsa'ba._
’ .
'haka ta 'kasancé tsakanin Sabéer" da Deeda,
ya',.dinga shige.mata da nuna mata' kulawa
qarara, ya yin da ita kuma' ta dinga. kauce'masa
Ibrahim ya dinga gujewa Deeda da tambayoyinta.
.
Sabeer kuwa yini yake ‘yana kallonta a office
wanda. a wannan lokaci ya fi masa kowanne
lokaci .dadi, ya yin da kusan aiki tare §uke yi, ta
yi .nata aikin ta yi kuma nasa, su yini tare, su yi
hira tare, bacci ne kawai' ke rabasu. Tun Deeda
tana kauce masa har' dai daga ‘baya ta sake
délenta, sabo data saba da hakan.
* V * *‘V * if y 3k V ’
SAFIYAR ranar Litinin ' ne itace safiyae ranar da
Ma’aikatan Kainfani suka tashi da ; ' yajin Aiki
akan suna son qarin ‘Albashi k0 kuma a basu
gidajen zama a kusa da Kamfani
Dr. Sulaiman k0 ya ce ba zai Kara musu
ba, sabo da bai jima da yi musu kari ba, kuma
yana ganin gidajen da ya basu ba shi da nisan
da‘ sai an musu canji. ‘ Haka kamfanin ya wanna
kusan sati ba Ma'aikata, Wanda. Dr; ‘ sulaiman
ya yanke hukuncin zai‘kore‘su‘ ya dauki wadansu
sababbin Ma'aikatan. ' idan sunqi dawowa
Haka sauran Directors din Kamfanin suka bi
bayan shawararsa, wanda shi Sabeer bai . ' So
haka ba, yanaganin’in har an koresu ba a yi
musu.' adalci h
va; sabo da da su aka kafa ' Kamfanin. '
Office din Dceda.ya,shiga.wanda:ba ta yi
mamakin ganinsa ba, don kuwa ya Saba shiga
kowanne lokaci. ‘
To amma Kuma abin da ya'ba ta . mamaki shi ne
yadda ya shigo office din ba
' tare ya yi ma‘ta magana ba ya samu waje ya
‘ .‘zauna ya yi' shiru yana tunani, SaBanin da, da
idan ya zo zai yi ta mata sumtu k0 kuma ya saka
mata ido ya yi ‘t'a kallo
~Shirunsasa da ~natsawarsa'ya daméta‘, ta
tashi daga inda fake ta ‘bar'aikin da take tar
matsa kujerar da yake zaune ya yi Tagumi, ta
durkusa a gabansa ta kalleshi cikin sanyin‘ murya
'ta‘ ce "Sabecr‘ mene ne ke damunka? ' ’
Shirunka ya dameni, ba ‘haka naSan Abokina
Sabecr ba a baya. .
.Ya kalleta ’Cikin damuwa ya ce, "Dccda
matsalana na na. Kamfanin nan ne
day Daddy ‘yace zai koresu _idan sunqi su koma
kan‘ aikinsu kuma sun kafe a kan ra'ayinsu in
matukar ana son su koma aiki sai an, yi musu
abin da suka nema. ' ‘
To 'gaskiya ni kuma ina ganin idan aka koresu ba
a yi musu'adalci‘ba. Ki duba'ki ga,.da su aka
kafa‘Kamfaninnan, da shi ne sukeci, suke sha su-
da’iyalansu da suturta su. - '
" Dazu da na shiga indasuke na yi. musu korafi,
amma da na~ji nasu sai naji ‘ai 'suma da
gaskiyarsu.- '
Haka kuma da na yi magana da‘Dadday ,shima
sai na ji -yana da gaskiyarsa. Yanzu ya dora min
‘nauyin ‘kare Aikinsu, yana so komai ya koma
dai-dai ne nan da zuwa ranar Litinin' din nan mai
zuwa, sabo "da . .lnveStors" na Kamfaninmu suna
ta janyewa, haka masu shirin Investing suma sun
fara tafiya ‘ wasu Kamfanunuwan. _ ‘Decda'ni
ban Saba da irin wannan ‘ ba, sannan ' Uncle " ib
yaqi tallafawa “ya zare hannunsa; yace wannan
aikina neba nasaba.
- Daddy kuwa ya bar komai a hannuna, na rasa
yadda zan Bullowa al‘amarin nan, wannan shi ne
ya sakani cikin damuWa da'tunani".
. Deed; tayi murmushi ta ce, "Abokina ya fara
fahimtar responsibility dinsa da sanin damuWa‘r
Wasu da matsalarsu.‘
Ka kwantar da hankalinka, ka dauki . abin
dasauqi. -'Kar ka damu komai zai tafi dai—dai
yardar Allah. Kuma Allah Ya ga zuciyarka da‘
niyyarka,’ Shi zai taimake ka, kar ka karaya, ina
tare da kai! Deeda na tare‘da kai Karfe naWa. ne'
'Meting din?" "Karfe goma sha daya ne' ‘ Ta kalli
agogon'da ke bangon office din,'"Yanzu Saura
minti talatin ke nan"; ' Ya girgiza‘ ma ta'kai
alamar eh Ya. ce, "Yanzu haka Daddy da sauran
Darector's‘ suna a (Meeting Hall) Leburorin ‘duk
sun taru"‘ .
"Karka damu Sabecr, duk da ba lokaci amma
zamu san abin yi".
, "Ban da ni a Meting din, amma zan taimaka,
_dakda ba ’lokaci mu‘ tsara, amma yanzu ba
lokaci; ina ga magana kada ya isa, magana ta
_nutsuwa da farantaWa da ’farantaawa juna
sanin darajar juna da muhimmancinsu",
,Wayar SAbeer ne yayi Kara. Ya kalleta ya ce,‘
"'Dccda Daddy ne 'Ya fada kamar zao yi kuka. ' '
‘ "Kar ka damu ta_ shirya kaje yanZu, ina ga
abin' da za a yi, ka‘yi_.Connecting dina da
Mating Room din na ga me ake, cewa mu dinga
magana a'Waya, kasata-a Kunnenka, insha Alahu
komai zai 'tafi daidai". ' _
' Karfe' sha daya’. suka' hadu aka fara Meting,din
suka' kasa shawo kansu
Deeda dake hangensu kuma tana jinsu, ya yin
data lura Sabeer‘yana cikin rudani, yana kuMa a
tsorace
tace"Kwantar da hankalinka Sabeer ka nutsu ka
maimaita duk abin da na ce.‘ Sabeer ka yarda da
ni?" Ina kallonka in but ka yarda‘ dani ka girgiza
kanka zan fahimta. ‘
Jin haka yasa ya‘girgi‘za ma ta kai.
"Alhamdu lillahi, yanzu" kamaimaita abin da
zan'fada‘maka..‘_ -
Guri ya, yi tsit, Sabéer ya mike ya fara magana. "
- ' "Na ji duk abin ,da ku ka ce, daga kowanne
Bangare
Ni dai' a ganina 'da hangena, kamfanin nan ya
kai wannan matsayin da nasara
ne sabo da Ma'aikatansa, ’ba, don-mu masu
Kamfanin ba, sabo qo‘karinku da jajircewarku,
Zuciya' daya tsakani da Allah, don haka dole mu
durajaku kuma mu girmamaku, kuma mu yi muku
godiya;
A ganina. dukkanmu. matSayin (Family)daya
muke, 'yan uwan‘juna, DANGIN jUNA,‘ .aduk
lokacin da Kamfani' ke cikin matsala taeuwa ya
kamata muyi mu‘cetoshi, Yadda zamu' gyara
A halin yanzu muna so ku bamu hadin kai mu
samu invistors su daina, janyewa, . ku‘ma mu
samu masu Investing'idan kamfani ya habaka aka
samu riba, insha Allahu za mu yi muku yadda
kuke so kamar yadda muke so. ‘ ‘
A yanzu ina fatan kun fahimci maganata?” ‘
_ Tsit! wurin ya yi. Shugabansu ne ya mike ya ce,
"Mun ji .bayaninka, kuma mun’ ‘amince. Bamu
san cewa Kamfani ya daukemu da daraja hakaba;
bamu yi zaton Kama ya san muhimmancin. mu
ba sai yanzu.. “
' Mun yi matukar farinciki dawannan ,bayani
kuma muna- tare da Kamfani dari bisa dari
: 'A'shiryc make do mu bawa Kamfani lokacin da
‘ya nema, muna godiya da sauraron kukanmu’ da
kukayi'. Mu kUma “muna tabbatur muku da .cewa
za mu koma bakin aiki ba tare da bata lukaci ba.
A karshe muna dada ba da hakurin rashin jituwar
da muka samu . Sabeer ya yi murmushin jin dadi,
"yami qe
tsuye yana dubansu yace"Mu ma muna godiya da
wannun guyon baya da hadinkan da ku ka bamu.
Allah Ya taimakemu Ya taimaki Kamfani, ya
barmu tare". Kowa da ke Wajen Ya amsa da,'
"Amin". " Bayan Sabeer ya 'koma ya zauna, .sai
jagoran churoma Mallam Sule ya mike ya yi,
Sallama, suma ragowar‘ Leburorin suka'mike
bayan sun gama fita Wajen‘ya yi tsit Wannan ya
kalli wannan, wancan ya kalli Wancan. ': Duk
abin da ke famwa Dceda tana can daga office
dinta tana kallonsu, marna ya cika mata" zuciya
sabo da samun nasarar Sabeer Nan sukai mai da
kallonsu gareshi, 'Mataimakinsa, yace, "K0 za ka
iya ‘yi mana bayanin_ abin da ka yi yanZu, me ye
:ma'anar hakan?" ‘
mu koresu, in wasu sabbi su'ka zo kafin su ganc
aiki sai kamfani ya yi asara wanda ba za mu so
hakan ba.
Mu bisu cikindabara da hikima yadda za su yi
mana abin da mu ke so". "Wow! '.' Daya daga
cikin 'Directors' din ya fada. ,
"(What a smart move)
Daya daga'cikinsu ya ce,- "Sati‘guda kenan muna
fama dasu amma gashi yau ka yi maganin
matsalar lokaci gUda". '
Nan fa suka yi ‘ta yabon'sa suka watse suna
murna, mahaifinsa ya taso ya matso kusa da shi
ya kalleshi, hawayen dadine- suka cika masa
idanu yace "Sabcer yau“ ka birgeni ina alfahari da
kai. Oya, give me a'huge
Fadawa jikin mahaifinsa yayi yana maena, shima
bai hakura ba hawaye 'yaji na zubo mai yace "I
love you Dad. [promise to Work hard); Ba za ka
sake samun matsala da ni ba
'Wel done Sabeer. Allah Ya taimake ka, Allah Ya
yi maka albarka, gobe Yayarka tanan kan hanya
murnar ganin Sabeer, sosai zata ga canji, Sabeer-
ya kara girma,- Sabeer ya’ zama babban
mutum, interligent
Sun rabu cikin‘ farinciki da kaunarjuna irin ba da
da uba, inda Mahaifinsa ya yi masa alk‘awarin
baashi duk abin da yake so, ‘a rayuwa muddin
dan adam na‘ iya' ba‘wa mutum da gudu,. da
murna Sabeer ya fita' ya nufi office din deeda da
gudu yana kiranta". ' "ddeda! DdddaH Docda!!!" '
~ Dama' .tayi tsammanin hakan, ta yi dariya tace
"Wow! Abokina ya dawo; cikin nasara‘ Nan suka'
kWashe da dariya gaba dayansu sannan saka
nemi' Wurin' zama suka fuskanci juna, ya soma
yi mata‘wannan kallonda bata Son. . Yana cikin
tsananin faeinciki ya ce, "Dccda na ‘gode,
ya ce, "Dccda ban San ya zan yi in fasalta miki
murnar‘ da nake cikibA
Ya kalleta; "in fada miki wani abu zaki yarda da
ni‘.’.toki yarda gaskiya na'ke fadi‘?" Ta yi
murmushi tace;_"Kwarai Sabccr".
Ta, yi murmuShi gami‘ da kwantar da kai
:Na yarda da'kai Sabeer. 'I trust u
"Deeda ki yarda a Wurina you are the best, a
wurina yanzu’,’ rayuwata ita ce deeda, kuma
Dccda ita ce rayuwa, Dccda itace farincikina,
Dccda ita'ce rayuwar Sabeer deeda ita.cc
farinncikin‘ Sabccr, Dccda ita ,ce zaka gani ka
gane Sabeer deeda ita‘ ce (Identity) na ,Sabeer
don Allah Dccda karki'rabu dani
hawaye ya gangaro masa
"deeda plesease don't leave me sabeer
Ya tsinci kansa a cikin tsananin son Deeda wanda
ya so yafi qarfin zuciyarsa, ya dinga jin tamkar
yajawota ya hadiyeta akoda yaushe
ji yake tamkar ya jaWota ya‘rungUmeta ya
'kwana'a jikinta ya kwada mata irin tsananin‘
'son da yake mata, ya kwantar da kai“akan‘
kujera' yana‘ fidda numfashi sama-sama yana
kallonta .yana shakar iskar dake hudo sassanyar
qoramar dake cikin zuciyarta
"deeda kiyi alkawari ba zaki kyaleni’ba kiyi_ min
alkawarin za’ki kasance da ni har’ abadan
Ya fada muryarsa kasa-kasa cike da rauni da
kuma shaukin so ' ' ' ‘ .
~ Ras! Ras! kirjinta ke bugawa Kalamansa sun
firgitata, sun rudata, hankalinta ya tashi. . , ‘ ' ' "
' '
Shike nan abin da take gudu ya' faru, Sabeer
sonta ya keyi..
zufa taji ya Fara keto mata ta mike, "Ba zan bari
haka ta faruba da sauri ta miqe ta fice shima ya
mike ya bita.‘ . " _ "Dccda please tsaya, kar ki ‘
kyaleni
Ba ta saUrareshi ba, kafin ya ankare ta Bace
'masa. hankalinsa' ya. yi mummunan‘ tashi, duk
abinda sukeyi lbrahim najinsu kuma
yana'kallonsu, dama_ yayi.zaton Sabeer ya fara
son Dccda .tun ba yau bA
" Hankalinsa ya tashi da abin da, yaga ya faru.
Yanzu me ita yarinyar' deeda take nufi Shin ta
yaya, Zai
soma controling din Sabeer 'da wannan; sabon"
matsalar data kunno kai"?
"Ya ‘_ Allah!" . Ya 'fada“: cikin damuwa.
ah shared a profile .
birnin gayu
chapter12
hankalin Deeeda ya kara‘tashi ganin‘ ibrahim bai
dauki . Wayarta ~ba_ .har' ta‘ " tsinke.‘ "Ibrahim
ka'dauki wayata, please inason magana da kai".
Ta fada cikin. damuwa.. '
Data sake bugawa sai ta‘ji an kashe gaba daya,
ta ‘wuce kai tsaye ta cewa lnna zata. wuce
gidan’Tabawa kar ta. fadawa Sabccr inda take
"lfy yadai Deeda‘?" lnna_ta DA irin yanayin da
take ciki na damuWa. _
"Inna zan fada—miki. komai idan‘ na dawo yanxu
bana son Sabeer ya sameni". AI ‘ Bata jira tasake
jin’ wani abuba ta fice'daga dakin ta bar Inna a
tsaye cikin damuwa da- tunani
'deeda na fita ta tari taxi tace ya kaita ‘Asibiti
haka nan bata fasa kiran Wayar Ibrahim ba
Amman a kashe har ta iSa ‘ ASibitin,akace mata
'baya nan,ta jira'shi na tsawon lokaci
wata Nurse take fada‘mata cewa'w
yau fa Ibrahim ba zai dawo ba sai dai gobe. zai
dawo
hawaye ya zobo mata
"Ina zan Sameka Ibrahim?
Ya zama dole ka’san’me ke faruwa,.ka Sani bana
son Sabeer Ban 'taba son Sabccr ba, kai; -nake
so
Ibrahim ‘tun farkon haduwata da kai ban san
lokacin da ‘zuciyata ta. kamu da sonka ba, duk
abin' da na yiwa Sabccr na yi ne sabo da- kai, na
jure dukkan wahala da Wulakanci sbd kai. . :
Bana Son Sabccr, kai' nake: "so." ,
Ta fada hawAye na zubo mata a idanunta.
"Ina ka ke Ibrahim?" '
Nan ta mike cikin Bacin rai ta bar Asibilin ta
sake; hawa Taxi ta nufi gidan Tabawa.
Ibrahim kuwa, sai daya tabbalar da deeda"ta bar
Asibitin "Sannan ya fito daga 'office dinsa ya‘
yiwa-wannan nurse din godia sannan
ya juya ya koma office din ya kulle kansa, ya
:‘bara tunani ya mike a-‘doguwae kujera gamida
dafa kai ya rasa ‘mekeyi-masa dadii
Ya tsinci kansa cikin wani irin yanayi mara dadi
kwakwalwarsa ta ‘tsaya,.»ya rasa ta ina zai .fara
tunkarar matsalar, .komai yi masa zafi.
-A Mota deeda ta sake kiran layin' Ibrahim ba
‘iyaka amma' har yanzu a kashe Wayar'taga
Wayar Sabeer sai shigowa take ta kasa dagawa,
baya
da~ abin da zata iya fada masa; karshema'
kashe Wayar tayi ta fashe da kuka~ -a haka ta
isa gidan Ta-bawa. , ganin yanayin DA take ciki
Tabawa ta matsa mata da tambaya. . . ‘ -
+++++++++++++++
a'BIRNIN gAYU kuwa tuni Sabccr ya
haukace musu da_neman_ Deeda, yaje wajen
lnna' yana 'mata kuka akan ta .fada masa ina
Deeda Take
'lnna dai abin kallo ya ‘zame mata, tawani
Bangaren ’kuma tana mamaki, tana kuma godewa
allah
Ashe; akwai namijin da ‘zai nunawa Deeda irin
wannan soyayyah Lallai Wani