x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - SHALELAN BABA

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 64847 words

Category: Love Stories

Views 82

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
yaushe nafara wasa daku?
Momy dake zaune tana ganin ikon Allah tace haba Alhaji shazali 😃me yayi zafi ne haka ido zaici wuta? Me sukayi ma Daga dawowar ka kahau minsu da fada?
Yanda kasan yayi kuka, cikin takaici da shagwabar dashi kansa Baisan ma yayi ba yace shekaran jiya da zanyi tafiya nacewa Samah su tabbatar sun gyaramin part Dina Amma yanzu Ina shiga ko'ina qura, ni Dan qazamin inane dazan kwanta ahaka?

Samah tayi sauri tace ni?😳
Wallahi Yaya bani bace saide in Safah ce, itama Safah dasauri tace Kai Samah ittaqillah

Nunasu yafara yi da hannu yace kingani Ko? Kinga irin renin hankalin nasu Ko momy? Kasa yarinya aiki saboda tagama renama hankali tace ba ita kasaba

Momy tayi Murmushi ganin yanda yadage yana shagwaba agaban qannansa kokuma Baisan yanayi bane?

Tace to Kai Haneef mashirmacin inane da za'a Haifi Yaran agabanka Amma ace Har yanzu kakasa banbance su?

Yaga alama momy Bata dauki maganarsa serious ba, danhaka ya kallesu yace Dan Allah ku Bari natashi Daga bacci nakoma part din na ganshi da datti, yasa kafa yayi ball da wayar wata acikinsu dake qasan kafet, itama Baisan ta wace ba acikinsu , saboda wayar ma iri daya suke riqewa,🤣 yayi dakin momy yana masifa cikin ransa, da wannan masifar harkokin nasa zaiji kokuma da tsayawa yana banbance wasu yara
********
Acan police station kuwa, d.p.o ya kalli Dr Bilal yace meke tafe daku ranka yadade? Dr Bilal yadauko ID card dinsa ya nuna musu sannan yabasu labarin duk irin azabar da inna tabawa Shalele, ya Dora da Cewa, yallabai Hakan datayi be ishe taba, Saida ta yaudaremu tace yau muzo zata kaimu wajan yayar mahaifiyar yarinyar Nan, ashe batasan inda takeba, Sim card din babanta dazamu samu kowanne information aciki ta cire ta taune, Kai Daga qarshe ma ta tura yarinyar Abuja Wai aiki
Dpo ya kalli Marka yace hakane baiwar Allah?

Tace eh hakane

To meyasa kikai Hakan? Ko kina da dalili?

Saboda mijina yana fifitata akaina, ba yayimin komai sai abinda yarinyar takeso, Daga karshe ma yabata saqon saki tafadamin, ta nuna Bilal da hannu tace Sannan shi wannan Dan tsaurin idon harda marina, shiyasa nadauki mataki dakaina

Dpo yace naji, yanzu Ina yarinyar take?

Nakaita wajan ladidi tijara, nace takai ta koma inane tayi aiki, nide fatana kada Taji dadin rayuwa

Dasauri Bilal yace Aikuwa Nima yau zan nuna Miki Sunana Bilal Dan tijara 🤣😂
Dpo yace kayi hakuri ranka yadade
Sannan ya kalli Marka yace yanzu Ina zamu samu ladidi a karbo yarinyar awajan ta?

Tace sun tafi Abuja jiya, Bansan gidan datake ba, Bansan unguwar datake ba

Shi kansa Dpo din mamakin karfin halin ta yake, yace Amma Yaya akai kika Santa Har kika dauki yarinya kika Bata?

Anan Garin take, Amma Bata zama tana zuwa ne lokaci Zuwa lokaci Takoma Abuja

Kin kuwa San girman laifin da kika aikata?
Ya kalli wani dan Sanda yace aje a sakata a cell

Dr Bilal yace dakata yallabai, yasa hannu ya fizge Aududu Daga hannun Marka yace
Yanda kika dauki 'yata kika turata duniya, to Nima zan dauki danki yanzu, mushiga duniya dashi tare, bazaki sake ganin saba Har sai lokacin danaga 'yata, yakalli Dpo yace yallabai bakuda matsala Dani wajan kudi, Ko nawa kuke buqata zan aiko muku, Abu daya nakeso awajan ku shine, kuci gaba da riqe wannan maha'inciyar ahannunku kuci gaba da gana mata azaba, kada kusaketa har sai nabaku umarni

Aikuwa nan take aka tisa qeyar Marka aka kulle, sai ihu take tana Kiran sunan Aududu

Dr Bilal da Malam yahai da sabuwa suka kamo hanya sukayo gida, Malam yace yanzu likita Yaya zakai da wannan Yaron? Murmushi yayi yace ai baba babu abinda zaka yiwa uwa Taji ciwo irin karabata da danta, tarabani da 'yata Nima narabata da danta🤣🤣

Sabuwa tasa hannu ta karbeshi suka shiga mota, da tambaya suka isa gidan ladidi tijara, gidan a kulle yake, Saida suka tambayi duka maqotanta Ko sun San gidan datake a Abuja kokuma unguwar datake, Amma kowa yace baisani ba, asalima Ko number ta basu dashi, saboda batada mutunci yanzu zata nunama tijara
Haka suka dinga yawo Ana tambayar ladidi, kokuma wanda yasan wani nata, Amma babu wani bayani, Har yamma lis sannan Dr Bilal yace yabawa Malam yahai katinsa yace duk lokacin dayaji wani bayani, Toya kirashi yasanar dashi

Yasa hannu yakarbi Aududu ahannun sabuwa, sabuwa tace yanzu yazakai da yaro likita? Ka barshi zan riqeshi ahannu nah
Yace karki damu inna, insha Allah zai samu kulawa sosai, Kamar Yanda zan Bawa yar'uwar sa

Haka sukai sallama dashi rai duk babu dadi, shi kansa yana driving wani qullutun baqin ciki yakeji aransa, yana ganin Kamar yakasa cika burin Malam surajo ne akan Shalele, Aududu kuwa yana zaune akujera sai wasansa yake

Kai tsaye gida yaje yabawa Mai aikinsu Yaron yace ta kula masa dashi idan Baya nan, idan yadawo Daga aiki Kuma zaici gaba da kula dashi, Hajiya ma ta amince da Hakan, yayin da Sady ma tayi murna da Yaron kasancewar basuda qaramin yaro a gidan

Tabbas Addu'ar wanda aka zalunta batada hijabi tsakanin ta da Allah, Allah ya amsa adduar ki Shalele, haqiqa Aududu yafada hannun wanda bazai taba Yada Shiba

********
Washe gari da safe Suna yin break fast da momy da daddy, Haneef Safah Samah, huzaifa
Safah tanaci tana chtting, yayin da Samah take leqawa tana ganin abinda yar'uwar ta take

Spoon biyu yayiwa abincin, yatashi yabar wajan rai abace
Momy tabi bayansa da kallo Cikeda damuwa sannan ta kalli daddy tace Alhaji Yaron nan bayajin dadi idan ba baba Hanne ce tayi girki ba, Wai yau nasa su Safah ne suyi, shine yanajin dandanon girkin banata bane yatashi, yanzu kaga haka jiya Yazo yayi tayi musu fada saboda gyaran part dinsa
Alhaji Dan Allah asamo wa baba Hanne wata me aikin mana,kaga saita dinga temaka mata

Saida yadau minti biyu sannan yayi magana, (nikwa nace aaaa to inaga Dan awajan uban ya koyi rashin magana😃😂)
Hajiya wannan shine Karo na biyar da ake kawo wa Yaron nan Mai gyara masa part dinsa yana korarsu

Dan haka Nina cire hannu na acikin Al'amarinsa

A a Alhaji ba za'a yi hakaba, kayi hakuri kasa akawo masa, insha Allah wannan Karon ba za'a samu matsala ba
Baice mata komai ba, yadauki waya yakira abokinsa, hello Alhaji Ghali, idan babu abinda kake Dan Allah Mai dakina tanaso kasa a turo mata me Aiki guda daya
Shiru yayi daga yana sauraron abinda ake fada, yace a a idan ansamu din koma yaushe ne, kawai a turo ta, ok, ok to ngd

Yakashe wayar yaci gaba dacin abincinsa, Hajiya tayi Murmushi tace godia Muke Alhaji, Shikuwa baice mata uffan ba

********
Suna zaune Atsakar gida, ladidi ta kalleta tace ow nikuwa zan Dade banga mutum Mai baqin jini irin naki ba😃😒ace kowa Yazo neman Mai aiki basa daukar ki? Koda yake ai na lura da niyya kike musu rashin mutunci, Kuma wallahi dakinqi dakinso sai kinyi aikin nan, yarinya idan bakyason aiki danqamin hamsin Dina na danqa Miki hanya

Shalele najinta tayi banza ta kyaleta, suna wannan zaman doya da manjan wayar ladidi tayi qara, kawai Cewa tayi ah akwai, yanzu ma akwai wata yar ahannu, Dan Allah wannan familyn ne suke buqata? 😳a a yanzu zanje nakaita, ngd Hajiya sai anjima, takashe wayar ta dubi Shalele tace saiki tashi mutafi
Ansamu wani gidan dazan kaiki, Nima cikin satin nan zanbar gari, dama ke kika tsayar Dani, saboda baqin jini

Shalele batace mata komai ba ta tashi tashirya, tadauki kayanta da photon baba, suka fita Daga gidan, taxi suka tare suka shiga, tanaji ladidi nayi musu kwatance Har sukazo kofar wani gida da wani mekeken gate

Suna shiga harabar gidan Shalele tazama yar qauye tuburan domin kuwa Kai bazakace a Nigeria kake ba, shukokin fulawoyi Tako Ina

Batasan dalili ba kawai de tanaji gabanta yana faduwa

Har suka je falon, gaskiya falon yahadu, ita da za'a Barta a Iya falon ma kadai ya isheta rayuwa Allah sarki Shalele 🤣🤣

Wasu yara tagani guda biyu, bazasu girme taba, tsananin Kamar dasuke ne yasa takasa banbancesu , Hakan ne ya tabbatar mata da Cewa Yan biyu ne
Ladidi ce cikin fara'ah tace yanmata sannunku, Safah tace yawwa, Amma Samah Ko Kallan inda suke batayi ba

Ladidi tace Dan Allah Ko zaku yi mana magana da Hajiya?
Batace komai ba ta Daga murya tace momy!!!
Hajiya ta futo tace gani, menene

Ladidi tace Hajiya Ina kwana? Dama anyimin waya ne akan nakawo Miki me aiki, shine nasakota agaba nakawo ta

Momy ta kalli Shalele taganta yarinya, tabe baki tayi tace ok, eh gaskiya muna neman me aiki,akwai aikin da za'a Bata, Amma yanzu de nawa za'a dinga baki kudin aikinta duk wata?

Ladidi tace Hajiya ai mukam bamuda zabi, Ko nawa kika yanke yayi
Tace ok, Jakarta dake kan kujera ta dauka tace to za'a dinga Bata dubu tamanin duk wata
Ladidi ta Washe baki cikin farin ciki

Momy ta kalli Shalele tace Yarinya kudin yayi Miki haka?
Shalele tace a a kawai kibarsh....
Dasauri ladidi ta mintsineta jin zatayi mata katobara, wanne irin a barshi?

Ta kalli momy tace Hajiya yayi, momy ta zaro kudi tabawa ladidi tace to ga kudin ta na wannan Watan, inyaso duk wata saiki dinga Zuwa kina karba mata

Ladidi tace a a Hajiya, adinga Bata abinta, wannan ma abinda yasa na karba nayiwa mamanta alwaqari ne zan Kai mata kudin aikin yarta na farko
(Shalele ta kalleta, jin wannan qarya, aranta tace a a zaki riqe kudin ki de)

Momy tace to shknn za'a dinga Bata insha Allah, Ladidi tayi sallama tatafi

Momy ta kwalawa baba Hanne kira, dasauri tazo, tace Hajiya gani

Momy tace ga yarinya nan aje atufatar da ita, itace sabuwar me aikin dazata dinga gyarawa Haneef part dinsa











Adaure ayi Sharhi Dan Allah 🙏🏻 dafatan wannan shafi ya muku dadi

Ina masoyan shazali? Shikkenan magana ta qare?

Welcome to shazali's house Shalelen baba










Mrs Usman ce 🙏🏻

💕SHALELAN BABA💕
(Romance)

Writing by Amnah El Yaqoub

19&20

Baba Hanne ta kalli Shalele sannan ta rissina tace to hajiya
Momy tace da nayi niyyar ta dinga temaka Miki da girki, but Naga tayi qarama dayawa, kawai zata dinga gyaran bangaren nasa, ki gwada mata komai, gobe zata fara aikinta insha Allah, sannan wannan kayan nata nafada Miki asake mata wasu
Baba Hanne ta rissina tace to hajiya, sannan takama hannun Shalele suka shige daki
Suna zama Shalele tafara Kalle Kalle, baba Hanne tace yarinya Yaya sunanki?

Haka kawai Taji matar ta kwanta mata Arai, Daga gani batada matsala, Murmushi tayi mata tace Sunana SHALELAN BABA

Ah gaskiya ne da alama de wannan yarinyar baban nata yanaji da ita

Shiru tayi, lokaci daya jikinta yayi sanyi, baba Hanne tace menene sunanki na gaskiya?

Kallanta tayi tace HANEEFA

masha Allah, kice ma sunanku daya da uban gidan naki
Kallan rashin fahimta tayi mata, baba Hanne tagane Hakan shiyasa tasake Murmushi tace Ina nufin wanda zaki dinga gyarawa bangaren sa, ai Shima HANEEF sunansa

Shalele tace Allah sarki, menene aikin da zan dinga yi?

Zamanta tagyara tace yawwa kawai zaki share masa ko'ina ne, saiki goge, aikin Iya mopping Ko?

Daga Kai Shalele tayi tace eh na Iya

Yawwa toshi dakike ganinsa bayasan qazanta, yanaso kullum yaga waje tsaf, zaki share ko'ina ki goge, ki wanke masa toilet, ki gyara duk wasu abubuwa da kikaga basu yiba, kiyi Ahankali dashi, Bai cika magana ba, Amma masifaffe ne, qannansa ma Bai barsuba, ni kadai yake ragawa a gidan nan Bayan iyayen sa, Shima Dan yaga na manyanta ne, Haneef bayason qazanta, karkiyi mamaki idan nace Miki sau biyar Ana kawo masa masu aiki yana korarsu

😳😳zaro ido Shalele tayi tace meyasa?

Baba Hanne takama hannun Shalele tace ta farko saboda tayi shara batayi mopping ba, tayi tunanin bazai ganeba, shikuma yagane, hakanne yasa yace tanada ha'inci yakoreta

Ta biyu kawai yace Bata wanke masa toilet da kyau

Na uku sai aka kawo namiji, shikuma satinsa daya yace bazai Iyaba, yagaji da wannan aikin inde baso ake ya mutu ba🤣🤣

Ta hudu Kuma shishshige masa take, yana shareta, Koda yaushe yana nuna mata Baisan ta nayi ba, ita Kuma taqara shige masa, Daga qarshe sai tsintar kayanta tayi abakin gate

Ta biyar Kuma, sata take masa, idan yayi ajiya sai yaga babu, Daga karshe yakama ta, Saida ya nada mata shegen duka sannan ya koreta
Tun daga lokacin yace qannansa su dinga yimasa aikin, sukuma karatu yasa sun sangarce basu Iya komai ba

To yanzu de kece ta shida, shiyasa nace Miki kiyi Ahankali, Amma ni ganin farko Dana Miki naji kin kwanta min, nayaba da hankalinki
Ina Miki fatan alkhairi

Ajiyar zuciya Shalele tayi tace, to amma baba da wannan canje canjen meyasa ba zaiyi Aure ba yahuta?

Yace babu wadda yake so, Amma duk wannan halin nasa na masifa da miskilanci yanada temako, zaiyi wahala yaga kana cikin halin buqata yarabu dakai

To Allah yasawaqe

Baba Hanne tace amin, Bari nakawo Miki abinci kici kihuta Zuwa goben

Tace to baba nagode

********
Gidan Alhaji bukar shazali Kenan, babban gidane Mai dauke da part biyu dakuma Dan qarami guda daya, babban shine na Alhaji da yaransa, madedecin shine na Haneef, sai Kuma Dan qaramin na ma'aikata maza

Daga can Baya wajan part din Haneef akwai Swimming pool me shegen kyau, Saikuma gidan gaba daya dayasha adon fulawa ja da green

Acan gefe kuma motocine birjik Kamar wanda ake saidawa
Babban gida ne sosai

Bangaren Alhaji da Hajiya, anan yaransu mata suke, sai dakin baba Hanne inda akace ta dauki Shalele su tafi tare

Alhaji bukar yanada yara bakwai, babbar yarsa itace anty jiddah, sai Haneef, sai Fadila, sai iklas, sannan twins mata, Safah da Samah, sai Dan qaramin su huzaifa

Anty jiddah tana zaune a Abuja, da yaranta biyu mace da namiji, duk sunkai sa'annin Shalele, sai anty Fadila danta daya namiji, sai iklas tana goyan yarta mace, Dukansu Suna nan Abuja a zaune da mazajen su, yanzu gidan yarage Daga Haneef sai Yan biyu da huzaifa

Rayuwar su Suna gudanar da ita cikin jin dadi, matsalar su daya masifar Haneef, yacika fada dayawa

Shekarunsa 33 miskili ne na gaske, idan ya harde awaje yana bada order kaika rantse Dan wani Sarkin ne, bayasan raini kokadan, dogo ne ba gajere ba, idanunsa a lumshe suke always, saikayi tunanin bacci yake idan yana zaune Yarufe idon, nan kuwa Sarai yana Kallan ka, ahankali yake magana, yamafi wata macen magana cikin sanyi, idan ku biyu ne awajan saika nutsu sannan zakaji maganar sa, idan kanaso kaji yana magana sosai da Daria , to da momy ne sai daddy, Saikuma abokinsa Ajmal,anan Kam zakaga Daria harda dimple sai sun futo, rashin son raini yasa bayama kula qannan nasa

Wannan Kenan

*******

Washe gari da asuba Suna idar da sallah Shalele tafara karatun alqur'ani dawani data gani a dakin
Baba Hanne tanajin ta, Saida gari yayi haske suka gaisa, baba Hanne tace ashe kema kin Iya karatun yarinya

Na'iya mana baba, meya faru?

A a kede Tunda kin Iya zaki dinga Ko yamin, da jikata ce take koyamin Kuma tayi Aure, Amma yanzu Tunda gaki Kinga aina huta

Zan dinga yi miki baba, duk lokacin dakike so

To Aikuwa zansa me gadi ya siyomin wasu littafin ma kidinga yimin

To baba, yanzu yaushe zaki rakani wajan aikin nawa? Ba yanzu zamu jeba?

Ke kuwa inake Ina tafiya part din Haneef yanzu? Ai Yanzu be tashi ba yana kwance, aike yata aikin ki me lasisi ne, Kisha baccinki da safe, saiya shirya yatafi office zakije kiyi masa gyaran, Kinga baya nan kema zakifi jin dadin aikinki, ga kayan sakawa nan, su zaki dinga amfani dasu, wannan na jikin naki sun tsufa

Ni de zan tafi kitchen yanzu, saboda nahada musu break

A a to baba muje narakaki

Kiyi zamanki yata, aikin gidannan yawa gareshi, kada na gajiyar dake

Shalele tayi Murmushi, kada kidamu baba, muje wallahi Nima nadinga koya

Haka suka tafi kitchen din tare abinsu gwanin sha'awa

********
Daddy ne yadawo Daga masallacin gidan, da carbi ahannunsa, dama haka yake qa'ida idan yatafi sallar asuba sai gari yayi haske yake dawowa gida, direct part din Haneef yanufa
Yatura kofar falon yashiga,

Falon nasa yanada girma sosai, Daga gefe daya kayan motsa jiki ne masu yawa, wajan ya nufa Aikuwa yaganshi akwance da gashi sai wando three quarter, da baqar singlet, yana 'Daga wani uban qarfe muscle 💪🏻 dinsa sai motsawa suke, gaba daya jiki a murde qirar kakkarfan namiji, sai gumi yake hadawa
Daddy yace wato Kai bakada aiki sai Daga qarfe, da yamma gudu da safe Daga karfe
Ajiye karfen yayi agefe, yadauki handkerchief ya goge face nashi, yace morning daddy

Idan kagama abinda kake inasan ganinka kafin ka wuce office

Kasa yayi da kansa yace ok daddy

Yadauki goran ruwa faro me sanyi agefensa yakafa Kai Saida ya shanye sannan ya wullar ta awajan yayi cikin dakinsa

Acan part din su Hajiya kuwa, su baba Hanne Suna kitchen Saida suka hada komai itada Shalele, duk abinda Bata ganeba tambayar baba Hanne take, tana Bata amsa

Baba Hanne tazuba musu nasu tabawa Shalele tace gashi yata, kikai mana daki kizauna kici, Nima zan Kai musu nasu dining

Shalele ta karba tayi dakinsu dashi
Baba Hanne taje tasanar da Hajiya angama komai, sannan takoma dakinsu

********

Dukansu Suna zaune Suna break babu me magana acikinsu, yau Kam qananun kaya yasaka, wandon jeans da riga dark green saiya Dora wata rigar fara asama me hade da hula, kayansa Kenan dama, Daga suit sai kananun kaya, sai yar saman dayake dorawa me hade da hula, Kala Kala, duk kayan daya saka to yar saman dazai Dora itama kalar ta daban
Da wahala ka ganshi da manyan kaya
Daddy ne yamiqe yayi daki ya kalleshi yace kai inka gama Ina jiranku a daki kaida Hajiya, yayi dakinsa

Shima Haneef Bai zauna ba yatashi yabishi, momy ma haka, aka bar yaran awajan su kadai, adan qaramin falon daddy suka zauna Haneef yazauna aqasa, kansa aqasa yanaso yaji dalilin Kiran

Daddy yace my son

Dago lumsassun idonsa yayi ya kalli daddy na'am daddy

My son why bakasan yin Aure ne?
Gabansa ne
End Ads