wandon, Bata taba daukar Aududu inde ba wahalar sace ta tashi ba, tarasa meyasa inna Bata barinta ta dauke shi, kawo mata shi tayi Takoma taqarasa wankin tsarin ta bazashi akan wani babban tabarman zana
Sannan ta wanke wandon da Aududu yayi fitsarin ta shanya, tun kafin ta zauna, Yaron yayi Kashi
Baba yayi tunanin inna zata tashi Dakanta tagyara Yaron, Amma saiyaji tace Haneefa zoki daukemin Yaron nan ki wanke masa Kashi
Tace to inna, ta tashi tadauki Yaron sukayi Bayan gida
Hannu bibiyu baba ya zabga tagumi (🙉) Yama kasa Cewa komai
Futowa sukai Daga bayin itada Aududu tana da gashi sama ta nayi masa wasa, sai babbaka Daria Yaron yakeyi, dasauri inna tace "Ke karki lahanta min yaro mana, ke mahaukaciyar inace!? Eye nace ke mahaukaciyar inace zaki dinga cillamin yaro sama kina cafewa saikace wanda kika dauki Leda
Da karfi baba yace Marka!!!
Mrs Usman ce ✍🏻
💕SHALELAN BABA💕
(Romance)
Writing by Amnah El
9&10
Itama cikin fishi tace zaka dakenine? Malam nace zaka dakenine akan nayi mata magana saboda Dana? Idan ta kashemin shi Kaine zaka bani wani Ko ita? Da wannan din dayaya na sameshi? To bismillah, aiga fili ga me doki, kana yin kuskuren sake fadamin baqar magana Akan yarinyar Nan zakaga mummunan matakin dazan dauka akanta
Dukda yana cikin halin masifa, lokaci daya jikinsa yayi sanyi dajin furucin Marka, Gabansa ya tsanananta faduwa, cikin mamaki yace subhanallah, subhanallah Marka mekike nufi da kalamanki? Wai nikam in tambyeki, su waye suke hure Miki kunne abayan idona?Shalele datayi tsaye tana Kallan abinda Bata taba ganiba, idanunta babu abinda yake zuba banda hawaye, ita ya nuna da hannunsa Sannan yace Marka me kika dauki Shalele ne? Kishiyarki ce Ko yarki?
Inna na girgiza jikinta irin tanaji da masifar nan tace masa oho shafa kaji
Gaskiya ne Marka, zan shafa, zansha fa naji yanzu kuwa, Kallan Shalele yayi idanunta sunyi jajir sabida kuka, Bata taba ganin iyayenta Suna fadi infada da junaba sai yau, ita kuwa wacce irin yace da zatayi silar samun sabani tsakanin iyayenta da ba'a jin kansu Ko kadan?girgiza kansa yayi alamun ta dena kukan datake, Saida ya sassauta muryarsa alamar rarrashi sannan yace share hawayen ki Shalele nah, ajiye Yaron nan
Bata ajiye Shiba, ta qanqame Yaron ajikinta, ahankali baba yasake Cewa ajiye mata shi nace, inna na kallansu tana karkada jiki tana auna musu harara
Still Bata ajiye Yaron ba, cikin tsawa, wadda tsawon rayuwar ta Bata taba ji mahaifin ta yayi Mata ba, yace "nace Ki ajiye Yaron nan!!!"
Lokaci daya jikinta yahau kyarma ta ajiye Aududu tashige dakinta da gudu tana kuka
Baba ya kalli inna Marka yace kin kyauta, sannan yasa Kai yafice Daga gidan
Bai zarce ko'inaba sai gidan maqocinsa Malam yahai, kafin ya qarasa gidan yar qaramar wayarsa tahau qara
Yana dagawa yace eh insha Allahu Ina nan tafe, zaku ganni Hajiya, Yauwa nagode, sanan ya kashe wayar
Sallama ya qwala a kofar gidan, amininsa Malam yahai yanaji yasaka hularsa yafuto kofar gidan, ayanayin da yaganshi yasan Cewa ba kalau ba, akwai damuwa, danhaka yace a a Malam surajo, qaraso mana, mu qarasa ga dakali nan mu zauna, bece komai ba sai zama dayayi, yakama kansa da hannunsa bibbiyu
Dafashi Malam yahai yayi yace meyake faruwa haka Malam surajo? Yanayin ka ya nunamin ba lafiya kake ba
Cikin damuwa baba yace Marka
Malam yace me markan tayi?
Marka ta sauya Malam yahai, nan take yabashi labarin duk abinda yake faruwa, Daga qarshe yace kaji abinda yake faruwa
Innalillahi wa inna ilaihirraji'un gaskiya Malam surajo wanan ba qaramar matsala bace, yanzu ya za'a yi a shawo Kan wannan matsalar?
Baba yace yanzu Kam kaina yariga daya kulle Malam yahai, Amma dole zan dauki babban mataki akan Hakan, ba wanan ne damuwa ta bama, Hajiya takirani Daga Abuja, tana son ganina, Amma idan bazan samu damar zuwaba to tanaso tazo da kanta, tanason zamu yi wata magana Mai muhinmanci dangane da Shalele nah, Amma nafada mata Cewa bama sai tazo da kanta ba, zansa lokaci naje cikin satin nan
Malam yahai yace to ai ta kwana gidan sauqi Malam surajo, ni Ina ganin mezai Hana kawai katafi da ita Shalelen can wajan hajiya, ai zaifi
Malam yahai tana zuwa makaranta yanzu, banaso Ko kadan na katse mata karatunta, idan natafi da ita bazasu Bari nadawo da ita ba,, zan Bata hakuri kawai,idan Naga gidana yagama dedeta yadawo Kamar da, sainaje, Amma yanzu bazan Iya barin Shalele Daga ita sai Marka awannan halin ba
Malam yahai yace eto wannan dinma tunani ne Mai kyau gaskiya, babu damuwa, kada kadamu abokina,kakira Marka ku zauna kaji menene damuwar ta, insha Allah komai zai warware, saika kira hajiyan kabata hakuri kayi mata bayanin komai
Baba yace zan kirata insha Allah, nagode sosai da shawararka a gareni
Malam yahai yace haba abokina babu godia a tsakaninmu
Da wannan shawarar ta Malam yahai baba yaji ransa yadanyi masa dadi
Tashi yayi yace zanje gewaya gona, saina dawo Malam yahai
Malam yahai yace to shikkenan Nima Bari in koma gida
Daga nan baba Bai zarce ko'inaba sai gonarsa, Saida yagama dubata da kyau sannan yadan ciccire mata ciyayin dasuka Dan futo, yahau kekensa ya wuce wata gonarsa ta shinkafa, nanma dubawa yayi yaga ruwa ya wadace ta, sannan yazauna yana hutawa a wata bishiya Mai sanyi, Daga nan Baisan lokacin da bacci ya daukeshi ba
Zafin dayaji aqafarsa ne yasa yafarka da Addu'ah abakin sa, hamma yayi sannan yakai dubansa kan kafarsa, baiga komai ba, wajan dayakejin Zafin yataba da hannunsa nanma de baiga alamun komai ba, danhaka baikawo komai aransa ba yatashi yayi miqa ya wuce gida
Gab da magrib ya isa gida, danhaka ya wuce masallaci Saida yayi sallah sannan yatafi gida, yana shiga ita Kuma tafito zata fita, cikin siririyar muryarta tace sannu da Zuwa baba, yawwa Shalele nah, za'a tafi wajan tulawar ne? Eh baba zan tafi, to shknn Allah yabada sa'ah saikin dawo
Ahankali ta amsa da ameen sannan tafice Daga gidan
Dama haka take safe tatafi makarantar boko, da yamma islamiyya, da dare muma tilawa sai takwas da Rabi zata dawo gida
Atabarmar da inna take zaune anan yazube yana fadin wash, wallahi nagaji sosai
Kamar batason magana tace sannu da Zuwa
Yawwa Marka sannu, tashi ki dubomin rob a daki na shafa akafata ciwo takemin
Batare datace masa komai ba tatashi tadauko masa rob din, ya karba yashafa sannan Yarufe idonsa, shiru sukayi da gashi Har ita, shi yana tunanin rayuwar yarsa gudan jininsa, ita kuwa bacin rai ne danqare acikin ranta
Idonsa arufe yace Marka, inaso zamuyi wata magana dake
Aududu ta kwantar agefe Tace inajin ka
Me Shalele tayi Miki Marka?
Babu abinda tamin, kawai de Ina Bata tarbiya ne akan abubuwan dakake yimata, sannan Malam zamanta a gida haka ai ya isa haka, ayi auranta mana
Murmushi yayi, aransa yace Wai tarbiya, jin dalilin nata bawani Mai tushe bane
Afali saiyace Aure fa kikace Marka, dududu nawa yarinyar take dahar za'a yi mata zancen wani Aure! Idan kin manta lissafin ne saina tuna Miki shakerar Shalele goma sha biyar, ni aganina tayi qanqanta da Aure yanzu, kina gani fa yaran gasunan dayawa anayi musu auren dazaran sunzo haihuwa saisu fara yoyon fitsari, saboda yarinya bazata Iya haihuwa da kanta ba
Yanzu de maigida Tunda ba zakayi mataba ai shikkenan saika sata agaba kana kallo kanajin dadi
Bece mata komai ba sai Murmushi dayayi kawai, yasa hannu yadauki Aududu yafita dashi waje, yanajinta tana sakin wani uban tsaki
**********
Washe gari kafar baba ta kumbura tayi suntum, daqyar yake Iya takawa, Shalele Bata saniba, tun da sassafe data gama share gidan tayi wanke wanke, ta tsaya abakin kofar Dakin ta gaida su ta wuce makaranta Bata dawoba
Shikuwa baba yana kwance a daki yahada uban gumi, Marka tana kallansa ta share shi, ahankali yace Marka!
Tanajin sa ta qyaleshi, Saida yakirata yakai sau hudu sannan ta amsa, yace saka mayafinki kije kikirawo min Malam yahai
Saida tagama abinda yake gabanta sannan tatashi ta leqa ta katangar su tace sabuwa, kice wa Malam yahaya Yazo Malam yanasan ganinsa, kafin sabuwa tace to, Har Marka tabar jikin katangar, habarta ta riqe tace tooo
Tana fadawa mijinta yafuto dasauri yashigo gidan, yace Marka Ina Malam surajon yake? Lafiya deko?
Bata yi masa magana ba Kawai nuna masa dakin tayi da hannunta, yayi bismillah yashiga, yana ganin baba akwance yace subhanallah Malam surajo lafiya kuwa? Yana runtse ido yace kafata ce take ciwo tun jiya wallahi,
Yace subhanallah sannu Malam surajo, muje waje sai Naga kafar, da temakon Malam yahai, yakama baba yafuto dashi Daga cikin dakin, acikin rumfar suka tsaya, ya kalli Marka datake zaune agefe yace Marka temaka ki shinfida mana tabarman nan
Tabarmar ta fizgo agefe ta shinfida musu, Malam yahai yana Kallan ikon Allah, haka ya kwantar da Baba yasaka Fillo Daga bayansa, dage kafar wandonsa yayi, ga kafar nan ta kumbura sosai, yace Malam surajo yaushe kafara jin ciwon ne?
Tiryan tiryan baba yabashi labarin komai tun zuwansa gona Har abinda yafaru, sake ganin kafar yayi sannan yace to gaskiya Ina tunanin miciji ne ya cijeka, kokuma wani qwaron me mugun dafi, Bari inje gidan Dan makandi na karbo ma magani, dasauri yafita Bai jira amsar baba ba
Maganin yakarbo Yazo yajiqa yabawa baba yasha, sannan yabashi goro yace wannan namijin goro ne kaci, inde hasashen mu ya zama gaskiya macijin ne to insha Allah zakaji sauqi, Allah yabaka lafiya, baba Bai Iya amsawa ba illa kansa daya Daga, ahankali Yarufe idonsa Har bacci ya daukeshi
Sannan Malam yahai yatafi gida da nufin idan anjima kafin nan baba yatashi saiya dawo
Har biyu saura baba Bai tashi ba, yana bacci saboda jiya baiyi baccin kirki ba
Tana shigowa gidan da sallama abakinta, dashi tafara tozali da gudu ta qarasa wajan inna Marka tace inna lafiya baba yake kwance anan? Meyasa mi babana inna?
Inna tace kaji me uba, to sannu yar Baba, gashinan akwance ai saiki tambayeshi
Jiki asanyaye Takoma gefen sa ya tsugunna, maganin data gani ajiqe akofi duk da batasan kona menene ba hakanne ya tabbatar mata da babanta baida lafiya, lokaci daya hawaye yacika idonta, ganin tana kuka Amma innarta ta share ta ko rarrashi babu yasa taqara volume din kukanta, wannan wacce irin masifa ce take cikinta? Ace uwarka tana fishi dakai tsawon lokaci Mai tsawo haka
Shashshekar datake ne yafarkar dashi Daga baccin dayake, ahankali yace Shalele nah kin dawo? Daga masa Kai tayi, tana share hawaye idanunta sunyi jajir, karan hancinta yayi jajir abinka da farar Fata
Cikin kuka tace sannu baba, kanta ya dafa da hannunsa yace kiyi hakuri Shalele nah, insha Allah zan warke kinji? Sake Daga masa Kai tayi
Yace tashi kije kici abinci kihuta, kiwuce islamiyya, cikin muryar kuka tace baba yau Alhamis babu islamiyya, yace to tashi kije kici abinci karki zauna da yunwa
Inna tace bandafa dakuba, Iya cikina nayi, saide ki dafa muku, bazan Iya ciyar dakuba
Cikin sanyin jiki ta ajiye kwanon tadauki tukunya tadora musu jallof din taliya yar hausa, kasancewar batada wahalar dahuwa nan da nan tagama, tazuba akwano takaiwa baba nasa, agefensa ta zauna ta rafka uban tagumi
Duk abinda yaje faruwa baba yanajinsu Yarufe idonsa ne kawai Amma ba bacci yakomaba
Bude idonsa yayi yace kici abincin mana Shalele nah
Baba ai kaima bakaci ba, bazan Iya ciba
Murmushi yayi yace to Bari inci, daqyar yatashi zaune, yadauki cokali yafara ci, itama tasaka hannu anasa suke ci tare, inna tajuyo ta kallesu ta zuba tsaki
Baba kuwa Ko Kallan inda take baiyi ba, yaga alama Marka tana jiran Jan kati ne(🤣😃)
Suna gamawa tabashi buta yayi alwala, yayi sallarsa a zaune, duk yanayin hakanne domin Shalele tasaki ranta, Amma shi kadai yasan azabar da yakeji aqafarsa
Har dare Suna nan wajan, itade inna ta dauke danta suka shige daki, baba yace Shalele kiramin Malam yahai yakaini daki na kwanta, kema kije ki kwanta kihuta Allah yayi Miki albarka
Girgiza Kai tayi tace baba zan kamaka, basai na kirashi ba, haka ta kamashi, ya lanqaya hannunsa daya akafadarta takaishi daki sannan tayi masa Saida safe ta futo
Koda ta shiga dakin ta kuka taita yi, tana adduar Allah yabawa babanta lafiya, da taga kukan bazai yimata ba tatashi ta futo ta daura alwala takai kukansu wajan Allah, Saida dare yaraba sannan ta kwanta baccin itama anan kan abin sallar
Innalillah... Ya haiyu ya qayyum, la'ilaha il-lallah, Marka! Marka!! Marka kina Jina kika qyaleni, Marka!!!
Tana daura alwalar sallar asuba take jiyo nishin baba Daga daki, yana Kiran Marka, batasan lokacin datayi wulli da butar datake hannunta ba tabanka kanta cikin dakin
Baba ne kwance acikin mawuyacin Hali yajiqe jarkaf da gumi yayinda ya Dora hannunsa daya Kan kafarsa dayakejin ciwon ta
Inna na kwance agefensa ta rungume Aududu
Jikinta banda karkar wa babu abinda yake yi, tace sannu baba, mekakeso nakawo ma? Baba kafar ce take maka ciwo? Sannu
Duk tagama rikice wa, cikin karfin Hali yace mata Shalele nah inaso ne zanyi sallah
To, to baba, sannu, haka ta cacimeshi daqyar suka futo Daga dakin, yayi alwala, ta shinfida masa tabarma da sallaya akan Tabarmar yazauna yafara sallar a zaune, Saida taga alamun yafara ne sannan itama tayi alwalar taje tayi sallah, tana idar wa tafito tsakar gidan nasu wajansa,, akan sallayar dayayi sallah ya kwanta yanata uban gumi, dakin ta shiga tace inna Ina mafici zanyima baba firfita Kinga sai gumi yakeyi
Saida taja tsaki sannan tace Dan Allah Haneefa kada kidameni, haba duk kunbi kun cikan kunne da surutu idan maficin kike ne..... Bata gama maganar da takeba Shalele ta juya cikin fishi tabar mata dakin
Inna tadaga murya tace iyeeee ni zakiyi wa rashin kunya? Yau kuwa zakici uban ki surajo acikin gidan nan Dani kike zancen
Zama tayi agefensa ta nayi masa firfita, ahankali tace sannu baba,Daga mata kansa kawai yayi alamun amsawa
sannu sannu ta nayi masa firfitar Har gumin dayake fitarwa yafara raguwa
Suna zaune acikin rumfar Har Gari yafara haske, hijabin ta dake gefe a ajiye tasura tafice Daga gidan, Bata tsaya Ko Inaba sai gidan su sha'aban me kaita makaranta
Yayi mamakin ganinta da sassafe haka, yace Haneefa yau da wuri kikeso nakaiki makarantar ne?
Sha'aban yau ba maganar makaranta, Dan Allah taho muje baba baida lafiya, muje kakaimu asbiti adubashi Dan Allah sha'aban
Dasauri yace subhanallah, muje, gaba tayi, shikuma ya buga machine din yabiyota Abaya
Tana shiga gidan tace baba tashi muje asbiti, sha'aban nan awaje zai kaimu
Daqyar yatashi zaune, tadage labulen dakin inna tace inna bamu bargo da kayan baba Ko guda dayane zamu asbiti nasan ba lalle mu dawo yauba
Inna Marka tayi mirsisi ta qyaleta, haka Shalele tasaki labulen tazo takama baba ya miqe suka fara takawa Zuwa kofar gida, kawai saijin saukar kaya sukayi abayansu, atare suka juya itada baba, inna ma Bata fasa abinda takeba haka ta ci gaba da Watso musu kayansu, jikinsu, tace gashinan kufice maza, kufi ruwa gudu, yar kare da shegen iyayi, yar mitsitsiya dake Har kin Iya kwainane waike me uba, sauran kayan dake gefenta na baba tadauka ta qarasa watsa musu kayan ajikinsu saikace wanda aka basu notice a gidan haya(😢😢)
Ahankali baba yace muje Shalele, fita sukai sukabar kayan awajan ayashe aqasa, suna fita sha'aban yatemaka wa baba yahau, itama tahau Daga baya daqyar machine din ya ishesu su uku, basu tsaya Ko Inaba sai a Dan qaramin a sibitin Garin, sha'aban yace Bari najiraku Haneefa, dasauri tace a a sha'aban kaje kawai, idan kaje kafadawa baba Malam yahai abinda yake faruwa kace masa muna asbitin, yace to Haneefa Bari naje
Yana tafiya, taje wajan baba dake zaune abenci, hannu tasa acikin aljihun Rigarsa tadauki dubu daya, taje ta yanki kati, ganin halin dayake ciki Kuma babu mutane sosai yasa Aka dubashi da wuri
Likitan yace yarinya meyasa baki kawo shi da wuri ba? Ai dafi ne akafar tasa, maganar gaskiya abin yafi karfin qaramin asbiti irin wannan, zan rubuta Miki wasiqa inturaku asbitin birni cikin Abuja, zaifi samun kulawa fiye da nan
Yace yarinya, Ina fada Miki ciwon mahaifin ki yayi worst dayawa kina maganar gida? Idan zai Iyu ma kawai ka wuce Daga nan, ga wannan takardar kitafi da ita, Allah yabashi lafiya
Hawayen ta share tace to likita Mungo de, haka takamo baba suka futo Daga cikin asbitin, a wata bishiya tace zauna baba, Bari natare mana taxi, yace to Shalele nah
Bakin titi taqarasa tafara tare taxi saide duk wadda tazo Bata tsayawa, ganin haka yasa tafara tare duk wata mota datake wucewa
Cikin qwarewa da driving wata mota baqa qirar Range Rover ta kunno kanta titin Glas din motar tinted ne baka ganin naciki
Awannan situations din datake ciki batada zabin daya wuce tatare motar, danhaka Kai tsaye tashigo titin tana tare motar, jikake qiiiiii motar tasaki qara daqyar direban ya tsaida motar
Yana harde abayan motar, video call yakeyi da computer datake kan cinyarsa, ahankali yadago Zara zaran gashin idonsa ya kalli direban dake jansa yace "saminu kanka daya kuwa"?
Yallabai tuba nake wata yarinya ce takeso ayi mata lift, yasake yin kasa da kansa yace ayi hakuri Yallabai
Computer dake cinyar sa Yarufe, ya kalli saminu da lumsassun idanunsa yace" lift"? Acikin motata? Motata tayi kama data masu yin lift ne?
Cikin girmamawa saminu yace a a Yallabai, ayi hakuri, dama Naga tana buqatar temako ne
Tsaki yasaki yace "no bazai wuce masu yin bara akan hanya ba, yabude brief case dinsa dake gefe yadauko kudi dami uku Yan dubu daidai, ahankali ya zuge Glas din motar idonsa yasauka akan baba dake zaune abishiya idonsa arufe
Tun lokacin daya sauke Glass din motar tazuba masa ido, lokaci daya Taji gabanta yafadi
Shikuwa zafin daya bigi fuskar sa ne kasance war akwai sanyin esi