x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - SHALELAN BABA

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 64847 words

Category: Love Stories

Views 91

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
maza tashi mutafi gida
Batace dashi komai ba ta tashi tabi bayansa suka futo harabar asbitin, bude mata gaban motarsa yayi ta shiga, sannan Shima yashiga yajasu, babu wanda yake magana acikinsu , sai karatun qur'ani dayake tashi acikin motar, tayi lamo tana saurara, rayuwa Kenan tazo da babanta yanzu Kuma zata koma ita kadai
Tana duniyar tunani batasan adadin tafiyar da sukai ba sai gani tayi sun shigo gidan, megadi yabude masa gate yashiga

Yana tsayawa yafuto dasauri zai bude mata, saita bude da kantama ta futo, yace mata taho mushiga ciki
Abaya take binsa Har suka shiga falon gidan, wata babbar mata zaune akan kujera sai wata yarinya bazata wuce 20 ba, tana kwance akan kujera Agefen ta

Duk ido suka zuba masa ganin yashigo gidan tare da baquwar fuska

********
Babban office ne qayatacce, wanda aka Qawata shi da kujeru lafiyaiyu, biro ne ahannunsa yana zagaye cikin office din yayi masifar kyau cikin suit ruwan toka

Meyasa tun jiya Hankalinsa yakasa kwanciya da ganin wannan bawan Allah? Ko kalau yake yazauna abishiya yana bacci?

Yasan Cewa bashida alaqa da yarinyar da saminu yace tatare su, yasan Cewa wannan kudi kawai take nema, Amma Har yanzu Zuciyar sa takasa nutsuwa da rashin tsayawa awajan, gashi lokaci daya yaji Gabansa yana faduwa, menene dalilin Hakan? Oh ya Allah shazali wannan ba halinka bane meyasa ka aikata Hakan? Sumar kansa ya hargitsa afili yace Allah yasa ba abinda nake tunani bane, Allah yasa batare suke da yarinyar data tare muba

Yana tsaye wata ma'aikaciya ta shigo office din nasa, takardu tabashi tace yallabai ga takardun dakace ayi kokari ahada makasu

Hannu yasa ya karba yace "OK"


Babu irin thank you dinnan ma
Inda Sabo tasaba da rashin maganar mutumin nan, dakuma Halin share mutane irin nasa tamkar jinin sarauta

*******
Kuka take yi haiqan tana ihu, kan gari take danna ihu tana jama'ah kukawo min dauki, nan da nan aka cika gidan nasu
Kowa tambayar ta yake lafiya kuwa? Nuna musu shi tayi da hannu, gashinan Malam yahai ne Yazo yacemin Wai mijina yamutu, wallahi bazan yarda ba nasan hada baki sukai shida Haneefa suka je suka ba dashi awajan masu shan jini wallahi bazan yarda ba kotu ce zata rabani dakai yahai, idan mutuwa yayi Ina gawarsa take? Wayyo Allah jama'ah kukawomin taimako yahai yagama cutata yasiyar min da mijina

Malam yahai yace Marka kiyi hakuri, wannan iface ifacen naki babu inda zai kaiki, nide gaskiya nafada Miki Allah yayiwa Malam surajo rasuwa, yana gama fadar Hakan yakada babbar Rigarsa yabar mata gidan, domin kuwa Har yanzu radadin rabuwa da amininsa Bai barshi ba
Shin tana wannan haukan tayaya zai sanar da ita Cewa Malam surajo yasake ta? Idan ta gama saiya dawo suyi maganar anutse
********
To hajiya kinji abinda yafaru, Ina fatan zaki so yarinyar Nan Kamar Yanda zaki Soni

Babu damuwa Lal, Allah yabamu ikon riqeta, dubansa yakai kan qanwar sa sadiya yace Sady, ga qawa nan nakawo Miki
Kikaita daki tahuta Ko?

Tana Daga kwancen tace Yaya ga dakin can taqarasa ta zauna, Bansan tashi ni wallahi nagaji (๐Ÿ˜”๐Ÿ˜”)

Bilal Yadubi Hajiya,, tagane nufinsa Dan haka tace zaki tashi ki rakata dakin Ko saina saba Miki, nonsense

Tashi Sady tayi tana zumbura baki tayi gaba, Bilal Yadubi Shalele yace tashi kibita Haneefa

Bayanta tabi tana Kallan ikon Allah, itama Sady cikin qunquni take Cewa mutum sai shegen San girma Kamar gyanbo, shi meyasa bazai kaita dakin ba, suna Zuwa dakin ta dubi Shalele tace ga dakin nan, gakuma toilet nan idan zaki shiga

Ahankali tace mata to, ta zauna Agefen gadon tafara tunanin sauyin rayuwar data samu lokaci daya

Acan falo kuwa, Hajiya ta kalli dannata tace Lal Yaya sunan yarinyar ne? Yana Murmushi yace Haneefa sunanta Hajiya, tace to Allah yajikan mahaifin nata, yace amin
Tashi yayi yabi Bayan Shalele, yana Zuwa yaganta a zaune tayi Shiru, yace nace kidena tunani fa haka, kada wani ciwon yakama ki, cire tagumin tayi tace to,

Kitashi kiyi wanka, ga wardrobe nan kisake kaya, kafin muje asiyo Miki wasu, Nima zanje na watsa ruwa

Daga masa Kai tayi, sannan ta tashi tashige cikin toilet din

Shima cikin kwanciyar hankali yayi dakinsa ganin yarinyar tasamu karbuwa awajan hajiyar sa

Bilal mukhtar Kenan Dana farko awajan Hajiya Halima, suna kiranta da Hajiya, mahaifin sa yadade da rasuwa shine yake kula da mahaifiyar sa dakuma qanwarsa sadiya datake University yanzu, Hajiya babu ruwanta tanada abin Daria, batada matsala kokadan, Bata cika boye abuba, Kai tsaye zata futo fili tafada babu ruwanta da boye boye, idan tanaji da gayu Bata Cewa Bilal saide ace masa lal๐Ÿคฃtofa Shima idan yaji Hakan yasan Yan gayun nata Suna kusa, Shima de babu ruwansa, matsalar sa daya San girma, yanada masifar son yaga Ana bashi girma
Wannan Kenan

********
Yana zaune akan lafiyaiyun kujerun falon, yadora kafarsa daya Kan daya akan dining table din dake Gabansa Dan qarami, gorar ruwa ne akan table din da Glas cup, yariqe jarida yana karanta wa

Qannansa dasun doso falon Suna ganinsa zasuyi birki su koma daki, momy ta futo falon ta zauna tazuba masa ido tana kallansa, leshin jikinta kadai zaka kalla kasan Cewa anzubar da dukiya awajan

Sake kallansa tayi yayi Shiru yana karatun jarida hankalin sa kwance, wannan wacce irin rayuwa ce ace mutum idan yana gida qannanka bazasu sake ba, saikace wani dodo yara su dinga gudun masifar ka

Ajiyar zuciya tasauke tace wato Kai Haneef anyi fira dakai Ana tambayar ka Ko kanada Aure shine isa isa kace bakada shi, a a abin Bai tsaya haka bama Saida kaqara da Cewa babu wadda tayima
Saboda kana ganin mun zubama ido muna kallanka, ai Kai da kunya ma kace bakada Aure, dasai kadan sakaye kace inada Aure, rabuwa mukayi ๐Ÿ˜ƒkokuma kace inada Aure mutuwa tayi matar tawa๐Ÿคฃ
Amma inaaa, awajan Yan jaridar ma saika nuna halin ka, to nikam nagaji, nagaji da wannan zaman Naka haka

Kallanta yayi da lumsassun idonsa, yace yanzu momy so kike nayi karya? Momy kowafa yana Kallan wannan tattaunawar, tayaya qanne na zasu ganni babba Dani Ina qarya

Au ashe kana kunyar qannan Naka, ai nayi zatan baka kunyar su shiyasa kayi mirsisi da maganar Aure

Kafin yabata amsa wayarsa tayi qara, ahankali Kamar mace cikin muryar sa me kama da rada yace momy zan amsa waya Ina zuwa, yatashi yafice Daga falon

Ajiyar zuciya tasauke tadauki remote din gabanta, tasan Cewa ba dawowa zaiyiba, ya silale kenan๐Ÿคฃ๐Ÿ˜ƒ

********
Tunda baba ya mutu tasauya, tadawo Shiru Shiru babu magana, zaka sata komai tayi but walwala Kam babu ita, idan tayi Shiru kawai tunanin rayuwar da sukayi da Baba take, Allah Kenan baya barin wani dan wani yaji dadi, shikkenan inna saiki zuba ruwa aqasa Kisha baba yatafi yabarmu dagani Har ke
Tana zaune acikin daki da daya Daga cikin kayan da Dr Bilal yasiyo mata na kanti masu kyau da tsada, yau ake ukun mahaifin ta Shima yatafi Bai dawo ba Har yanzu, tasan Cewa Tunda yamma tayi yakusa dawowa


Wani magazine ne Agefen ta tasa hannu tadauka ta bude tana karanta wa shafin farko photon sane ya baiyyana aciki yana tare da wasu mutane Kamar ma turawa

Zara zaran yatsun hannunta tasa shafa fuskar sa, wannan mutumin yanada kyau, ita kanta tasan Cewa yafita kyau nesa ba kusaba, Abu daya zata fada masa shine hasken Fata

Hannunta yana kan face dinsa tatafi tunanin lokacin data fara ganinsa, sajen dayake fuskarsa tatuna, Har gobe bazata taba mantawa dashi ba, mutumin daya temaketa da kudi Har akayi wa babanta aiki, badan yabata wannan kudin ba tasan Cewa da kafin ayiwa babanta aiki ma zai rasu, Tunda dole saita koma gida an hada kudin, koma ace sai anzo Ana sayar da wata kadarar

Qasan photon ta Kallah inda aka saka sunansa, HANEEF BUKAR SHAZALI, Murmushi tayi afili tace takwarana

Batayi aune ba Taji an fizge magazine din hannun nata, tana dago kai taga Sady ce sai huci take

Ke wacce irin shashasha ce zaki daukamin Abu na kina kalla? Kinsan waye wannan din? To shine rayuwa ta๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ, Har gobe neman inda zan ganshi nake bansamu ba, saide na ganshi a photo Ko video shine saboda wulaqanci photon Dana samu Ina ganinsa zaki dauka Shima ki lalata min?

Ahankali tace kiyi hakuri anty sadiya

Kanta tadafe da hannunta ๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€tace yar qauye Wai sadiya, Sady ake Cewa kingane? Fuuuuu tashige toilet tare da banko kofar toilet din

Shalele cikin ranta tace ikon Allah, wato shi wannan din Har San ganinsa ake anrasa Yaya za'a yi, shine ni na ganshi a araha a titi ๐Ÿคฃ๐Ÿ˜ƒ

Tashi tayi tafice falo wajan Hajiya, tana zaune tana kallo, tace Hajiya akwai aikin da za'a yi? Hajiya ta kalleta da sauri ta kawar da kanta gefe tace a a Haneefa jeki daki kihuta babu komai

Tace to shknn, tareda Juyawa tana mamakin Hajiya meyasa yau Kuma batasan kallanta? Koma menene Allah masani

Da daddare ta idar da sallah tana azkar Dr Bilal yashigo dakin yaganta, gefen gadon yasamu yazauna, zuba mata ido yayi, yana yaba tsantsar kyau irin nata, dazai Iya ajiye San girman sa agefe daya Aure ta, but bazai Iyaba, shifa Tunda akace anbashi ita jiyake tamkar shine babanta, kyautar mutum sukutum batare dakasha wahala ba? Aishi yanzu babu yashi yazama babba๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ

Saida tashafa yace mata nadawo Daga kuje yanzu, munfara magana da Malam Yahya akan issue naki but bamu gamaba nataho saboda ciko war mutane Amma nace masa zan koma, inaso ayiwa Marka bayanin komai tare Dani

Kanta ta Daga masa tace to shknn Dr nagode

Dasauri yace what? Dr kikace kome? Kada kisake fada banasan jin wannan sunan Daga bakin ki, Ko kice daddy kokuma uncle, kin fahimta?

Ahankali tace nagane uncle

Yace Yauwa yatashi yabar dakin

Tunda baba yarasu yaune tayi daria, Kai wannan mutum wallahi dason girma yake, ๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜ƒKo Aure baida shi yana saurayi Amma Wai ince masa daddy

********
Zaune suke a dining su uku Suna break, Dr Bilal ya kalli Sady yace ke tashi kije kikiramin yarinyar can adaki
Kallansa tayi tace yanzu Yaya yarinya da girman ta ita ba qarama ba Amma kana cemata yarinya?

Ina ruwanki? Yarki Ko yata?

Tace yarka ce Yaya, aranta tana Cewa Wai shi Ala dole yasamu "ya
Bata tashiba sai kira data qwala mata da karfi
Futowa tayi daga daki da gudu kanta Ko Dan kwali babu, dama gashin nata babu kitso, tana zuwa wajan Hajiya ta kalli gashin kanta taga Abu dogo Kamar aljana, ta kalli idonta taganshi wani Kala daban qwayar idon ba baqa bace Kamar ta mage

Dasauri tayi qasa d kanta, Haneefa data lura da yanayin ta tace Hajiya Ina kwana? Kan Hajiya aqasa tace lafiya Haneefa, Dr Bilal yace me kikeyi ne a daki bazaki futo muyi break ba? Ahankali tace to uncle Ina zuwa, ta juya tayi cikin daki domin dauko dankwalinta

Washe gari Alhamis kwanan baba shida da rasuwa, Dr Bilal na dawowa Daga aiki Hajiya tace Bilal yace na'am Hajiya
Bilal, na'am Hajiya
Bilal na'am Hajiya

Saunawa nakiraki?

Sau uku Hajiya

To Bilal ba shawartarka nakeba umarni nake baka kadauki yarinyar Nan kamaidata garinsu, banasan ganin qwayar idonta, tsorata nake ๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜ƒBilal ka tattara ta kutafi Dan Allah, ni wallahi tsoron ta nake

Amma Hajiya.... Karka ce komai Bilal Dan Allah nace

Toshi yanzu ya zaiyi? hanyar dakin Sady yayi, yana shiga yaga tana Daria, tace uncle kada kadamu, naji komai, nasan Hajiya nasona, bada niyya tayi hakanba, dama Kuma zamana anan nasan bawani dadewa zanyiba, Tunda dazaran kagano inda dangin mamata suke zaka maidani can, kada kadamu, zan zauna a gidan baba Malam harka Gano inda yayar mamata take nakoma can, kaga sainaci gaba dazuwa makaranta ta Nima, aiba wani dadewa zanyi ba aqauyen ma idan nakoma

Ajiyar zuciya yasauke yace kin amince da Hakan? Hakan yayi Miki?
Tace eh yayi uncle, ita kuwa tayi hakanne kawai domin tasan Yanda zatai tacika burin baba na karbe Aududu Daga hannun inna marka

********
Washe gari sukayi sallama da Hajiya zasu tafi, sadiya ma da batasan baqi saitaji babu dadi, Shalele harda tsokanar Hajiya tace to hajiya saina sake dawowa zan zauna kiyimin kitso da kwalliya ๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜ƒHajiya de ba um bare um um

Basu tsaya ako'inaba sai Garin kuje, suna Zuwa kuwa kofar gidan danqam da mutane Ana sadakar bakwai, lokaci daya mutuwar baba tadawo mata sabuwa, yana yin parking din motarsa suka futo, yagaggaisa dasu Malam yahai, sannan Malam yahai yayi masa jagora Zuwa cikin gidan, Adede soron gidan Dr Bilal yace Malam inaga yau yakamata a fadawa Marka komai, sannan inasan zan karbi wayar baba intafi da ita can Abuja, baba Malam yace to likita babu damuwa, mu qarasa cikin gidan

Suna shiga cikin inna taga Shalele, nunata tafarayi da hannunta tace gatanan tadawo, Gara da Allah yakawo ki Haneefa, yau saikin fadamin gidan uban wa kika kaimin mijina? Kinje kinbawa masu shan jini shi Ko, nan da nan kunsan mata da tsegumi aka fara magana qasa qasa wasu Suna salati, inna tataso tacakwami wuyan Shalele ta shaqeta, lokaci daya tafara Tari

Dr Bilal da ransa yayi mutuqar baci yace kisaketa mana kada kiyi mata illa, inna ta kalleshi da jajayen idonta tace bazan sake taba tsohon magulmaci ai dakai aka hada baki aka salwantar min da mijina
Kasa controlling kansa yayi yadaga hannu ya wanke Marka da kyakkyawan mari







(๐Ÿ’•Dan Allah karka karanta bakace komai ba, inasan Sharhi da comments,pls๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป
Ina whatspp readers masu tambaya yaushe Shalele zata hadu da shazali Dan Allah kudena tambyata, mekukeci nabaka na zuba? Lokacin haduwar ne Baizoba idan Yazo dole zasu hadu, babu wata wadda zata rubuta labari batasan qarshan saba, labarin yanada tsayi , shiyasa nake kokarin yi muku meyawa, nide fatana ku kasance tare Dani

idan mutum yasamu dama zai iya tura shi Zuwa Ko ina๐Ÿ˜Š๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ˜Š๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ˜Š๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ’•



Mrs Usman โœ๐Ÿป

๐Ÿ’•SHALELAN BABA๐Ÿ’•
(Romance)

Writing by Amnah El

15&16

Zafin Marin dataji ne yasa tasaki wuyan Shalele dasauri, gida ya kaure da hayaniya Ana ayi hakuri mana, wasu suka fara tafiya Suna Allah wadai da Hali irinna Marka, banda shirme yaushe yarinya da ubanta zataje ta siyar dashi
Dr Bilal banda huci babu abinda yake
Baba Malam yace meyasa kayi haka Dana? Bai Bawa baba Malam amsa ba ya kalli inna Marka data riqe kumatun ta inda aka mareta,

Nunata yayi da hannu yace idan kinyi wa babanta ya qyaleki, ni bazan dauki wannan ba

Baqin ciki Kamar ya kashe Marka, ita kuwa me zatayiwa wannan yaro da Shalele ta huce? Anty murja ce tazo taja hannun inna Marka suka shige daki, haka ta dinga tausarta harta Dan sakko, tace kiyi hakuri Yaya, nasan abinda zamuyi

Atsakar gida kuwa sabuwa matar baba Malam ce tazo takama Shalele suka zauna agefe, dayake duk Suna gidan
Tace kiyi hakuri Shalele, me hakuri yana tare da Allah

Baba Malam yaja hannun Bilal sukabi Bayan Marka daki, suna shiga baba Malam yace Marka akwai maganar data kawomu wajan ki me muhinmanci, Amma yanzu kafin nan munaso kibamu wayar Malam surajo akwai abinda zamu duba aciki

Saida ta watsa musu Kallan harara sannan tace za'a duba, Shima Dan tana tsoron shan wani Marin ne

Baba Malam yace to shikkenan muje Daga waje Bilal, suna fita murja tace me zasuyi da wayarsa?

Oho musu, inji Marka

To wacce irin magana zakuyi Kuma? To Allah yasa de ta rabon gadonsa ne abaki kasonki Dana danki, kekam ai kece da dukiya keme da namiji
Marka aka turo dankwali gaban goshi tace wallahi kuwa (nikwa nace zakiga gado๐Ÿ˜ƒShima baban ai yasan meyake)

Awaje su Dr Bilal suka zauna Har aka gama sadakar bakwai, Har kusan magrib Saida mutane suka watse sannan, su baba Malam suka shiga gidan, baba Malam yace sabuwa kuje gida keda Shalele tahuta, sabuwa tace to Malam, takama hannun Shalele suka tafi, sukuma suka tsaya a yar rumfar, murja ta futo tsakar gidan ta shinfida musu tabarma, gidan ba kowa duk an tafi, tace musu ga wajan zama, suna zama Marka ta dauko musu wayar baba me coculan,Saida ta tsaya tacire Sim card din ciki tun a daki sanan takawo musu tace ga wayar, wacce magana ce Kuma kuka zomin da ita?

Bilal yayi hamdala ga Allah, yasa hannu ya karbi wayar
Baba Malam yace Marka akwai saqon da Malam surajo yabari abaki kafin Allah yayi masa rasuwa, wannan saqo yasanar da Shalele ne da kansa tafada Miki, sannan ita Kuma yarinyar tasanar Dani, shiyasa nace Gara nafada Miki Tunda wuri,Marka Malam surajo yasauke nauyin dayake kansa naki

Tace ban fahimtaba, mekake nufi Malam yahai?

Yace Ina nufin Malam surajo yayanke igiyar Aure tsakanin ki dashi, yace asanar dake saboda cutarwa dakuma azabar dakika Bawa yarsa yace yasakeki saki uku

Marka tadauki hannu ta Dora aka, tace nashiga uku ni Marka, Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, nacuci kaina Marka, Malam yahai wannan maganar taka da gaske ne? Baba Malam yace hakane Marka saide kiyi hakuri, kuka taci gaba dayi haiqan

Kiran sallar magrib da akayi ne yasa, baba Malam yace likita muje muyi sallah mu dawo muji Yaya za'a yi

Dr Bilal yace to Malam, suka fice masallaci

Suna fita, murja tace Kai amma surajo Bai kyautaba, yanzu duk irin riqon dakikayi wa yarinyar Nan ashe baya gani? Dan gadon damuke jira shine yayi mana buqulunsa? Yanzu duk uban gonaki irin nasa shikkenan kefa kin tashi atutar babu
Marka ta goge hawayen idonta tace Niba wannan nema ya dameniba, Tunda akwai kason Aududu aciki ai shikkenan, abinda yafi damuna ya qonamin rai shine saqon sakin daya Bawa Shalele ta fadamin, yarasa wazai aika sa saqon Cewa yasakeni sai ita? Yanzu murja Malam idan be Iya rubutu ba, aiya Iya ajami
, gashi shi wannan Yaron danme tsaurin ido Yazo yatsaya harda mari nah, waini Marka uwar Aududu ni zai mara? Bazai Iyuba saina dau fansa akansa murja, itama Shalele bawai taci banza bane, saita gane Shayi ruwa ne akan abinda zanyi mata

Murja tayi Ajiyar zuciya tace Gaskiya de abin babu kyautata wa aciki, kome zasuyi da wayarsa Kuma?

Marka tace sai yanzu nagane abinda zasuyi da wayar Malam, murja tace me zasuyi da ita Yaya?

Murmushi tayi tace bazaki ganeba murja, Amma idan suka dawo zaki gane komai, tashi muyi sallah, suna yin sallah basu idar bama su Dr Bilal suka dawo,
End Ads