Yace to toshknn hajiya, daga gobe zan Nemo ma'aikata ayi famfouna da bohol amakarantu Dama masallatai gaba daya insha Allah, abinda yayi Saura kuma za'a yi masa sadaka dashi
Shalele tace baba malam kadage kabarshi kawai
A a shalelan baba, ayiwa malam surajo, Shima yayi mana lokacin dayake Raye
Shakeran jiya sha'aban me kaiii makaranta kuwa yazo yakawomin machine dinki, nace masa a a yaje saikin zo saiya dawo
Daria tayi tace kawai kace nabar masa baba malam, yace to za'a fada masa
Haka sukaita zubawa Mami godia, daga nan tace suje wajan Marka, akai Mata danta taganshi
Baba malam ne yayi musu jagora, sukaje Har gidan, ahalin dasuka ganta, sun tausaya Mata, tana Kuka tanemi yafiyar shalele, tace babu komai Inna nayafe miki, aka Bata Aududu saide kuma babu idon gani
Dakanta tasake roqarsu alfarma su riqe Mata shi, kada su duba abinda tamusu, suduba halin ubansa malam surajo kawai
Washe Gari Dr Bilal yashirya cikin manyan Kaya, yayi mugun kyau, yadauki hajiya da sady da Abdallah sukayi gidan mami
Mami tace a a baban haneefa wannan wankan haka sai Ina?
Hajiya tayi murmushi tace Kema de kya fada, Wai gidan surukai zaije 🤣
Mami tace a a kace neman auren yayi Nisa, Gara de anema Kam, kowa sai yayi masa yace zaiyi auren ya, shi baiyi ba
Hajiya tace ato ai Gara kidinga fada masa, qanwarsa ma sadiya jiya Bayan kuntafi kuje manema aurenta sukazo, Wai zasu kawo gaisuwa nace suhado Har kayan Saka Rana kawai babu maganar wata gaisuwa, ita bikin Nata sai nanda wata biyu
Mami tace a a lalle, gaskiya zamusha bukukuwa, Allah yakaimu
Yana zuwa gidansu momy yakira daddy awaya yace Yana da baqo
Daddy ya yi mamaki wanne baqo kuma? Haka de yafuto, Yana ganin Bilal yace a a Dana ashe Kaine, yamiqa masa hannu
Dr Bilal yabashi haannu aamma saiya tsugunna bai tsaya a tsaye ba🤣🤣shide daddy mamaki
Yace Dr Bilal ko kazo wajan mijin yar taka ne haneef? 🤣
Ya Sosa qeyarsa yace a a daddy ba wajan haneef nazo ba, wallahi yau zuwan nakane, wajan ka nazo, 🤣🤭
Daddy yace masha Allah, to ko daaga wajan daurin aure kake Naga Kaci manyan Kaya harda babbar riga🤣.
(Kai daddy Dan Allah 😃😒)
Saida yayi murmushi kin furucin daddy sannan yace a a daddy, Dama Samah ce taturoni wajan ka 😳😲🤭🙆🏻
Munyi magana da ita, to sai tace nazo wajan ka duk yanda mukai de, mun dedeta kanmu nida ita, ni inso saamu nema inaso ahada bikin danasu yar'uwarta da yayanta
Daddy yayiwa murmushin su na manya, ai sai yanzu yagane dalilin Saka manyan kayan🤣ashe wajan surukai za'a zo shine dalili
Amma fa yayi mamaki Jin sun dedeta kansu shida Samah, yaran da agabansa Saida sukai fada a asbiti lokacin dasuka je Bilal yarakasu wajan haneef? Koda yake yaran zamani ne qila sun shirya din
Ya kalli Bilal yace to Bilal babu damuwa zaaka Iya turomin magabatanka
To daddy insha Allah zan turo su, Amma daddy Dan Allah kada afamada Mata, inaso nayi Mata surprise
Daddy baice komai ba yayi murmushi gamida girgiza kai yajuya gida 😃
Dr Bilal na zuwa gidan mami yace su hajiya su futo su tafi, sady ta ware acikin su shalele sunata firarsu, tayi Mata murna Sosai Akan auren Miji kamar haneef shazali
Saida suka rakosu Har wajan Mota, shalele tace hajiya kinqi yimin kwalliya de kisamin kwalli🤣🤣
Daquwa hajiya Tamata, kede kin maidani kakarki wallahi
Washe Gari kuwa iyayen Dr Bilal sukaje akai komai aka Gama, aka tsaida lokacin biki danasu shalele, momy tayi farin ciki Sosai zata aurar da yaranta Dukansu
Dr Sulaiman ma dayaji wannan labari sai yace to tunda duka za'ayi wannan auren na dangi Shima Ajmal idan yashirya kawai yafuto, idan kuma bai shiryaba sai ayi nasun daga baya, to Dama gwanin naku kamar Akan qaya yake 🤣🤣baisha wahala ba wajan yiwa iyayen nasa bayanin komai, sukazo suma aka tsaida bikin lokaci daya
Anty jidda tayi murna Sosai, Gara tayi gajiya daya tahuta 🤣
Alhaji Tahir da daddy sunyi magana Akan zuwa siyaiyar kayan Yara
Mami taji dadin Hakan Sosai, Koba komai tasan idan yarinyar taxo gidan ma bazai Bari karatun Nata ya tabarbare ba
Sajida ma tazauna agida tunda ga jiddah nan zataje, yatura Mata kudin komai, furnitures na yanbiyu, da zata siyo musu, sai kuma na sajida ma dazata siyo duka Har ita, uku Kenan
Daga can wajan su mami kuwa itace da Kanta zata tafi, zata hadowa haneef lefe da Bilal data dauke masa nasa, 🤣tunda Yan biyu suka dauko Mata Gara taje dakanta tahado musu komai iri daya, sai kuma furnitures din haneefa, lefe biyu daa kayan daki daya
Ita Kuma anty jidda kayan daki uku, sai kuma lefe daya na haneefa, haneef yace zai tura Mata kudin tasiyo komai, haka ta dage tace wallahi sai yaje, bawani kudi dazai tura Mata zuwa zasuyi yahadowa yarta Kaya nagani nafada
Tayayama zaice zai Bata wani kudi, ai kawai ita shine kudinta suje kawai tana jidar Kaya ga ATM dinta haneef akusa🤣🤣
Idan taje tasiyo masa ma ai yadan samu sauqi, ita Kuma tafi so yaji a jikinsa yasan cewa mace Mai tsada zai aura
Dole sai sake daga tafiyar sukai zuwa Bayan kwana uku tajirashi🤣🤣 yagama ayyukansa sannan suka tafi Dubai ita dashi kafarta kafarsa
🤣
Saikuma Mami
Bataso suyi kwanaki dayawa a Dubai, tana so suyi sudawo tafara gyara yaranta ciki dabai
Ta kalli Dr Bilal dayayi tagumi Yana kallan kayan😱
Dana kayi shiru Kai banji kace komaiba
Ajiyar zuciya yayi, ai Naga kin kashe kudi dayawa ne Mami, wannan marar kunyar yarinyar zaaki siyawa Kaya dayawa haka 🤣
Haba Bilal, kaida ameer ai duk daya kuke a wajena, kada ka manta kariqe yata Amana a lokacin data rasa Wanda zai tallafa Mata, tana nemanka a lokacin da take cikin tsaka me wuya
Zanyima fiye da haka Bilal, saide kuma in basu birgeka bane
A a Mami sunyi kyau Sosai wallahi
Yafadi haka Yana sake yin wani tagumin😱
Mami tasake Kallansa cike da damuwa
Wai meyake damunkane kazauna kayi jirim haka, ko ameer dayake min Dan kawaici yau kawar dashi gefe yayi Yana kallan kayan matar sa🤣🤣
Ameer yasosa Kai yakawar da fuska gefe
Dr Bilal yajanye tagumin dayayi, ai Mami bakisan rikicin Dana hadawa kainabawa,😣😣😣
Yaarinyar nanfa batasan komai ba, sannan nace daddynsu kada yafada Mata, nide kawai mun Riga mun dedeta kanmu😢😢
Tace wakake magana? Wai Samah?
Be Iya cewa komai ba sai gyada kai🤣🤣
Tace zancen banza, to me zatace kuwa Bilal, anriga ansiyo kaya an tsaida ranar biki kuma zasu ce sun fasa ne? Impossible 🙅
Zai iyu Mami 🤣🤣
Saboda me zakace za'a Iya fasawa?
Mami kemafa lokacin da'aka yanke ranar bikin yarki, da ranki yabaci, haka kika tubure kikace sai an maida musu kayansu 🤣🤣
To Kinga Nima zasu Iya fadar haka idan ran yarsu yabaci
Mami tai jimm🤣🤭takasa magana, Saida tayi tunani sannan tace eto babu dadi de gaskiya, Amma nide Dan Allah kasaki jikinka ayi farin ciki a lokacin da ake cikin sa, banaso Naga jikinka a sanyaye
Kaje kasameta kayi Mata bayani cikin fahimta, zata fahimceka idan kuma taqi sauraronka kahadata da Safah
Daga shi Har Bilal suka hada baki wajan fadin Safah kuma!!? 😳
Yace to me Safah zata Iya Mata Mami?
Tace Bilal Kenan, yar'uwata cefa, sufa Yan biyu ne, Safah tana son dangantakarka da Samah, tun suna Yara nasan halin Yara idan daya tanason Abu daya bataso, to zasuyi cece kuce dinsu lokaci daya, ammafa daga baya duk suna dawowa suso Abu dayane
Ina tabbatar ma kosu momy saisu Mata magana Tari biris sabanin Safah
Kaje ka gwada, ba'a shiga tsaakanin yanbiyu, idan mutum yashiga ma kunya zaiji, Shiyasa Yan gidan basa shiga sabgar su🤣🤣
To Mami zan gwada insha Allah
Kafin tace komai shalele tayi sallama tashigo falon, cikin murna ta qarasa wajan su, Mami kayansu Yaya ameer ne? Ba'a Bata amsa ba tafara dagawa Kai ammafa Mami kin Iya zabe, kayan sunyi kyau, kuma komai iri daya
Toba dole nasai ko Mai Iya iri dayaba haneefa, sun je sun dauko min yanbiyu🤣🤣
Dukansu sukai daria, Bilal yace ya makarantar?
Wlhy alhmdlh uncle munkusa zana exam ai
To ki dage da karatu de, abinda baki ganeba ga Ameer nan
Uncle ai kullam ma munayi da Afrah
OK to Allah yasa adace, tace amin
Ta kalli Mami, Mami Ina Afrah? Ita taga kayanne?
Afrah Tana bacci, idan tatashi zata gani itama
Wayar Mami tayi qara, tana dauka suka gaisa da anty jiddah, banji me jidda tace ba, Mami tace to shikkenan, kawai Saita dinga zuwa daga nan ba, eh, Toba damuwa, akwai wata Mata ma Dana Mata waya, zan turota nan gidan naki kawai sai tayi Miki bayani,
Dahaka sukai sallama
Ta dubi shalele tace haneefa jidda tace kidauki uniform dinki da sauran kayan amfani driver yakaiki can, zakici gaba da tafiya school ta gidanta
Tace to Mami meyafaru?
Mami tace Ina zan Sani haneefa? Abinda tacemin kenan🤣
Shalele tace to Mami, ta daga wani takalmi da jaka tace Kai wannan kuwa kamar kinsan kafar Yan biyu wallahi zai hau kafar nan tasu🤣🤣
Mami ta kalli ameer da Bilal tace kungani ko? Bafa zata Dena wannan sururin kayan ba, 🤣inajin idan taga Nata haukacemin zatayi, dan jidda Ina ganinta tana tisa qeyar Yaron nan komai siya Mata yake saikace Wanda zasu Bude shago
Ai tanajin maganar Mami taayi cikin dakinsu da gudu
Duk suka Saka daria Mami tace idan banmata hakaba bazata tatashi taje ta shiryaba 🤣
Suna nan a zaune hartaci abinci tafuto da yar qaramar Jakarta, Afrah tarakota sai hamma take da alama daga bacci tatasheta
Dr Bilal yace Mami Nima Bari inwuce wajan yarinyar nan duk yanda mukai zan Miki waya, tace to kawai kutafi da haneefa idan kasauketa gida jiddah saika wuce
Yace to, ya karbi jakar Tata a hannun Afrah sannan yayi gaba
Shalele Saida taje ta rungume Mami sannan taace bye bye Mami, tabi bayansa da gudu
Mami ta girgiza Kai, haneefa! Haneefa!! Um haneef zaisha fama
********
Anty mu kinsa andauko mu daga gida, kuma ni wallahi kallo nakema momy tasa saida muka taho
Anty jiddah ta kalli Samah, me yarinyar nan take nufi? Takirasu nefa gaba daya duk tahadasu ayi musu komai lokaci daya Amma kuma taga kamar ma ita batasan komai ba
Tace Samah, gyaran jiki fa za'a muku, sannan munyi waya da maminku yanzu tace akai wata Mata ma dazata turomin ita takanas kawai dantazo tayi muku komai Har gida, Amma Dan iskanci kina min maganar kallo, Waye yahanaki dauko system din Taki
Gyaran jiki kuma anty?
Name? Nida ba amarya ba wanne gyaran jiki za'a min, Anty Samah cefa ni ba Safah ba 🤣🤣Naga duk bakwa ganemu, Safah ce amaryar 🤣
Anty jiddah cikin ranta tace tirqashi!! 🙆🏻
Sannan tasake duban Samah cikin nutsuwa tace Samah, nasan kece Samah nake Miki maganar ba ganeki ne baanyiba, Samah kinaso kicemin bakisan dake za'a hada ayi auren ba?
Aure Kuma anty? Kai anty kinada abin daria wani lokacin wallahi 🤣🤣🤣to dawa za'a min wani aure?
Tamaida hankalin ta Kan wayar dake hannun ta tana dannawa
Anty jiddah tace da Bilal mana
Ai tanajin wannan maganar tayi wulli da wayar dake hannun ta
Anty me kikace? Bilal kuma? Yaushe? Yaushe mukai haka dashi? Yaushe nace masa Ina sonsa?
Anty jidda oho muku, Amma kinsan de aure babu fashi, tunda iyaye sun shiga maganar, bazaki maida mana daddy qaramin mutum ba
Kuka tafashe dashi, kukanta ne yaja hankalin Safah da sajida dasuke daki
Cikin kururuwar Kuka tace wallahi ni Bana Sansa, Allah bazan aure shi yaje ya kashe niba, Yaushe mukai haka dashi daza'ace za'a Bani shi, Bayan kullum cikin yimin mugunta yake, Allah bazan yardaba
Girgiza Kai Safah tayi, taqarasa wajan Samah ta dago ta, tace kiyi hakuri mana Samah, menene aibun Dr Bilal? Yana sonki, Samah bazaki gane hakanba sai nan gaba, fadan dakuke Bana komai bane sai soyaiya Samah
Cikin hawaye ta kalli Safah tace dayake ke anbaki Wanda kikeso ba dole kice hakaba, nafasan halin Bilal din, wallahi mugunta ce dashi, mutumin dayake budar baki yace zai zaneni tayaya da hankali na zan yarda naje gidan sa, nace Miki Bana Sansa ko dole ne?
Sajida tace Safah Wazaki Kira? Dan Allah karki fadawa daddy
Safah tace ba daddy zan kiraba sajida, Ameer zan Kira in fada masa nafasa aurensa, inyaso nisai na auri Bilal din
Samah tanajin haka ta miqe tsaye tafara kokari qwace wayar, Safah ta hanata, tace Samah wallahi bazan baki wayar nanba, bakince saboda zan auri Wanda nakeso ne yasa nafadi hakaba? To daga yau Nima nafasa auren ameer din, taqarasa maganar tana fashewa da Kuka
Itama Samah din cikin Kuka Safah nace ki Bani wayar nan ko?
Itama ta kalleta cikin ido tace Samah Abaya Kam duk na Miki biyaiya amatsayinki na yayata, Amma Banda yanzu, kije kiyi abinda kikaga Dama Nima zanyi abinda nagadama
Zan auri Dr Bilal, Kema kije ki auri ameer, Kinga anyi 50 50 kowa ya auri Wanda baya so, tunda haka kikeso
Cikin Kuka Samah tace Safah nikike fadawa haka ko?
Safah tayi shiru tana share hawaye
Anty jiddah tayi shiru tana kallansu, yau Kam tasan ran yanbiyu yabaci, Bata taba ganinsu suna sa'insa Har hakaba
Suna wannan koke koken Haneefa tashigo itada Dr Bilal, sun danna door bell sunji shiru Dan haka kawai sai suka shigo
Haneefa ta kalli kowa tace mama lafiya? Meyake faruwa? Naganku duk a tsaye?
Anty jiddah tace sannunku da zuwa haneefa
Sajida ta karbi jakar hannun Bilal tace uncle sannunku da zuwa
Ya amsa Mata idonsa nakan Yan biyu dasuke Kuka, yakasa gane wacece Samah dinma acikin su
Yace anty sukuma wannan me aka musu?
Harara Samah ta wullo masa, tayi cikin daki da gudu tana Kuka
Anty jidda tace itada yar'uwata ne, fada sukai saboda Kai
Yace subhanallah
Ya kalli Safah, Garin Yaya Safah?
Kafin Safah ta bashi amsa anty jidda tace saboda munyi Mata magana Akan auren ku shine taketa Kuka Wai bataso, shine itama Safah din tace to itama zata fasa Nata auren tunda haka takeso
Yace kash🤦🏻♂Aida kunyi hakuri anty, karkuga laifinta laifinane daban sanar da itaba, kuma wallahi yanzu haka Dama niyyata idan na ajiye haneefa anan inwuce can gida inyi Mata bayani
Ya dubi Safah, yace kiyi hakuri kinji Safah, nasa kinsamu sabani da yar'uwarki Amma insha Allah komai zai wuce kinji?
Ta daga masa Kai
Yace nemi waje ki zauna, anty Dan Allah kuma ku zauna
Safah tatafi wajan shalele tazauna, shalele tafara Bata hakuri
Yadubi anty jidda yace anty zan Iya ganinta? 🙈
Tace Dr shiga mana
Babu kunya kuwa ya tsallake yarsa yatafi lallashi🤣🤣
Yana zuwa yaganta takifa Kanta a cinyarta tana Kuka
Ya zauna dab da ita, Har jikinsu na gogan juna
Ya sassauta murya yace kiyi hakuri, nasan namiki laifi, but sabanin fahimta ne yakawo Hakan, Amma wallahi Ina sonki
Samah tun lokacin Dana Dora idona akanki naji nakamu da matsanancin sonki, Amma kuma sai fada yahadamu a lokacin, na lura idan nasakar miki rainani zakiyi, nikuma babu abinda na tsana arayuwata irin raini, inada son girma Samah
Shiyasa zakiga Ina Miki wasu abubuwan Wanda basu da dadi, Nima ba'a son Raina nake Miki ba, dole ce tasa Samah
Dan Allah kada kice bazakice aure niba, zan Iya fuskantar damuwa Akan haka
Kalamansa sun ratsata, kuma ta gamsu Sosai, sai yanzu ne tagane dalilin sa naayi Mata wani abun
Yace kiyi hakuri ki Dena Kuka haka kinji? Kanki zaiyi Miki ciwo, karkiga ni doctor ne rikicewa zanyi nakasa baki Koda pracitamol ne🤣🤣
Hawaye suka sake zubo Mata, Yana ganin haka yasa hannu yadago ta, ya rungumeta a jikinsa
Yana bubbuga bayanta a hankali, kiyi hakuri kinji
Mutsu mutsun kwace Kanta tafara, bai hanataba yasake ta, dan Shima dole ce tasa yayi Hakan, taqiyin shiru, Shiyasa zai lallasheta ta wannan sigar, Amma Banda haka babu abinda zaisa yayi abinda zai daga masa hankali
Hannu tasa tana goge sauran hawayen Nata
Yace kokinga Dena wannan hawayen kokuma yanzun nan na shanyesu anan
Hararar wasa tayi masa, tace saikace wani maye
Yes ni mayanki ne Samah
Maganarsa tabata daria, tasake murmushi tadauki fillo agefe ta buga masa
Cikin daria yace yanzu shikkenan kin huce?
Ta gyada masa Kanta, yace toshknn kice kina sona Nima