x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - SHALELAN BABA

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 64847 words

Category: Love Stories

Views 88

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
sakani adakin duhun nan har yanzu idanun babu🤣😱bana gani,bana ganin komai

Malaam yahai yace marka kiyi hakuri,amma wannan yaron likita dakike gani dan boko ne ,bazaima kula kiba ,yafi karfinki marka

Fashewa tayi da kuka ,innalillahi...wai yanzu ni marka nice bana gani nice awannan hali

Malam surajo ka yafemin,hakika na karya alkawari

Yanzu Malam yahai dan Allah kakaini gidanmu wajan murja ,ko zata dinga temaka min,zamana anan gidan nikadai bazai iyuba,babu Malam surajo,babu shalele,babu Aududu

Haka Yakama mata sandarta ,sukayi gidansu markan

Rayuwar kenan😢


********

Jirginsu na sauka ,suka futo a gajiye ,tafishi galabaita saboda akwai nisa,Abbas yana ganinsu yaqaraso suka gaisa ,haneef ya harareshi

Yace eh naji de ,inba haka nayimaba ai bazakazoba

Kallan shalele yayi, masha Allah gaskiya abokinsu ya Iya zabe
Tace ina yini ?

Lafiya qanwata ya rigimar wannan gayen ,nasan kina shan shagwaba ko ?

Murmushi tayi,ta sunkuyar dakanta Qasa ,uncle dayake babba ina zaiyi wata shagwaba

Shazali yace dan Allah Abbas muje ,mungaji wallahi
Kafadarsa Abbas Yakama yace kai shegen gaye,ina kasamo sweet 18 ne ?
Yarinyar tayifa

Shalele de tafiya suke amma batajin me suke fada

Shazali yace nima haka naganta

Karya kake shazali,yaushe kadena ra'ayin manyan yanmata ?

Har yanzu ina ra'ayi

Abbas yace OK dakaga ta mallaki komai ko ?

Abbas kadena wannan maganar kada taji ta rainani

Dukan wasa yayi masa yace shege shazali🤣😃

Motar suka shiga ,suka wuce hotel din da ake saukar baqi
Motarsu na tsayawa matar Abbas ta qaraso dasauri cikin fara'ah ta rungume shalele

Bawata babba bace ,bazata wuce 26ba,tanaji da gayu dakuma yanmatancinta

Sannuku da zuwa ,sannunku,sai da suka gaisa da shazali sannan Abbas yace kuje ciki sweety tahuta gamunan zuwa muma

Ciki suka shiga itada shalele, zama sukai agefen gadon,dakin yayi kyau sosai babu tarkace dayawa kamar de yanda hotel suke

Tace sannunku

Shalele tace yauwa Anty

Dadi taji,lokaci daya taji son yarinyar, daga gani badata raini,tace sunana zainab,mijina kuma Abbas
Abokin haneef dinki ne ,suna kasuwanci tare🤣🤣

Cikin ranta tace haneef dina,to Allah yasa🤣

Zainab tace kekuma menene sunanki ?

Sunana haneefa

Wow nice ,wato shazali saida yajemo kyakykyawa kuma me irin sunansa sannan yafara soyaiya,shiyasa yadade bai samu budurwa ba

Shalele tace amma Anty..ni babu soyaiya atsakaninmu🤣🤣wannan tafiyar dakikaga anyima...

Murmushi Zeey tayi,takama hannunta duka biyun ta riqe
Haneefa ,azamanin nan na yanzu ,bakowanne mutum ne zai bude baki yace wance ina sonki ba

Kawai idan ya nuna mata a aikace ya wadatar

Kamar shazali ,na tabbata kallan dayake binki dashi naso ne,tunda kikaga ya zabeki yadaukoki yataho nan dake to yana sanki ne,bazai iyu ya nunawa abokan kasuwancinsa wata wadda ba ita zai Aura ba

Kiyi kokari kiga kin mallake zuciyarsa,tahakanne zaki tabbatar da abin danake fada miki

Inaji awajan mijina yanmata dayawa suna sonsa ,suna kai masa hari ,harkokinsa ne kawai dasuke dayawa yasa baya samun lokacin saurarensu

Bude kofar akayi ,Abbas ne da shazali ,Abbas yace mata kenan ,memakon kikaita dakinsu tayi wanka tahuta a a ,sai kuka baje kolin fira

Toga abinci ,Ku sauko kuci

Shazali yace no Abbas, sainayi wanka tukunna

Anty Zeey tace a a to itama ai gara tayi wankan kawai dakunci abinci saita kwanta tahuta

Daga kansa yayi yace OK yayi kofar fitadaga dakin
,yace Abbas

Abbas yatashi yabishi wajan kofar ,kallansa yayi yace abbs yaza'ayi ne

Kamarya ?

Ina nufin tazauna su kwana da zainab, saimu tafi dakai dayan dakin

A a shazali gaskiya ina buqatar matata ,kadauki abarka kutafi 🤣🤣


Haba Abbas...

Haba shazali,babu abinda zai faru insha Allah

Yadubi zainab yace ke zainab rakata dakin su, Anty Zeey tayi murmushi takama hannun shalele da takeaway dinsu na abinci suka tafi dakin da aka tanada domin su


********

Cikin tashin hankali tace hajiya wallahi naduba ko ina bangantaba

Momy tace a a to ina yarinyar nan zata shiga ?Tun safe ana nemanta

Safah tace Momy samah tacemin sunyi fada dasafe,saide in zuciya tayi tatafi garinsu

Momy tace kai Samah ,samah kincika matsala wallahi
Zaiyi wahala tatafi garinsu

Ta kalli baba hanne tace baba bari nakira Jidda naji ko can tatafi

Ana kiran Anty Jidda Momy tace Jidda yarinyar nan kuwa tana gidanki?tun safe muke nemanta bamu gantaba

Wacce yarinyar Momy?

Yarinya de datakewa haneef aiki,shalele take kowa?

Tuni Anty Jidda tadau haske😃hakan yana nufin babu sanin yan gidan ya dauketa kenan

Tace eh Momy tana nan ,sunma fita itada sajida

To alhamdlh tunda tana wajan naki,wai fada sukai itada samah shine tayi fishi tataho nan wajan naki

Kuma yanzu Jidda komai na duniya ba dan hakuri bane ?🤣
Idan taqi dawowa shi kuma yana dawowa daga tafiyar nan zai sani agaba ince kidawo da ita

Anty Jidda tasha daria tace to Momy zansa tadawo

A a Jidda yanzun ki barta,idan haneef din yadawo itama saida dawo,tunda shima yanzun baya nan

Anty Jidda tace toshinn Momy sai anjima

Wayar takalla tasake daria kai,Momy kenan,wani bikin sai agidan momu kina zaune agida ana wani budirin baki saaniba🤣😃🤣

Momy ta kalli baba hanne tace to baba kinji tana gidan Jidda

Baba tace to alhamdlh tayi kitchen

********
Suna shiga dakin Zeey tabata abincin nasu ,tamatso kusa da ita tayi mata rada akunne

Ki kwantar da hankalinki qanwata ,nasan halinsa babu abinda zai miki,tana fada mata hakan tace musu saida safe tafice

Yana ganin fitar Zeey ya kalleta ,duk tatakure kanta ,girgiza kansa kawai yayi cikin ransa yace yarinta kenan🤣

Bece mata komai ba yafara cire suit dinsa ,yajefata kan gadon ,niktile dinma ya cireshi ,agogon hannunsa ya kunce ya ajiyeshi daga gefe yakalleta atsaye ita bata zaunaba ita bata fitaba
"Idan kingama tsewar zaki Iya zama,nizanyi alwala nayi sallah"

Yana fada mata haka yashige toilet, tabi bayansa da kallo tasaki murmushi wannan mutumin yana birgeta ,zama tayi agefen gadon tana jira yafuto itama tashiga tayo alwala,tagumi tayi hannu bibbiyu😱 tana tunanin yanda zata kwana dashi daki daya











To mutara zuwa gobe domin jin yanda zata kasance ☺

Sanarwa

(Wannan sanarwar ta fan's dinane na Facebook kadai,har yanzu ban bude group nawa nakaina a facebook ba

Ku fahimta niba admin bace akowanne group na Facebook, nima member ce kamar yanda kuke members aciki
Idan naturo muku littafi bazai iyu Ku ganshi alokacin Dana turoba,dole sai admin sungani saannan sukuma su sakeshi,kowa yagani ,dafatan kun fahimceni ,ina jin dadin comment dinku sosai wallahi hakan yana qaramin qwarin gwiwa akan yin typing kullum nagode🙏🏻🙏🏻









Amina Muhammad el Yaqoub✍🏻💕SHALELAN BABA💕
(Romance)

Writing by Amnah El

33&34

Tana nan zaune harya futo daga toilet din, sannan tasaki ajiyar zuciya
Kallanta yayi, "kitashi kiyi alwaya ayi sallah ko"

Daga masa Kai tayi, tatashi tashige toilet din

Ga mamakinsa saiya tsinci kansa da jiranta, haka yatsaya Saida tafuto sannan yajasu sallar
Saida suka Rama duk sallolin dake kansu sannan yaita karanta musu addu'oi suka shafa saika rantse wasu sabin amare ne🤣

Dubanta yayi yasaki Dan qaramin murmushi,haka kawai yakejin wani irin nishadi na shigarsa, Anya kuwa Ajmal ba gaskiya yafada masa ba?gaba daya ko tunanin gida ma bayayi tunda yaganshi tareda ita
Ajiyar zuciya yasauke
kinajin yunwa ko?

Cikin sigar shagwaba tace eh uncle inaji

Wani yarrr yaji ajikinsa, Allah yaso sallah suka idar, Toda ansamu matsala gaskiya🤣

Abincin yadauko musu yasaka musu agaba, shinkafa ce wadda taji kori, da gasashiyar kaza aciki
Yakalleta cikin maganarsa ta sigar rada yace Mata taso kici Abincin
Aikuwa hajiya shalele babu musu ta matso tasaka hannu tafara cin abincinta
(hoo yunwa ba dadi 🤣🤣
)

Tagumi yayi Yana Kallanta, shi baifara ciba, ta kalleshi uncle Kai bakajin yunwa ne?

Cikin nishadi yace kedin yunwa kikeji?

Emana sosaima

No ban yarda kinajin yunwaba

Ta kalleshi meyasa?

Da idanunsa ya nuna Mata Abincin datakeci

Sannan yace inda kinajin yunwa dasauri Zakici ai

Murmushi tayi, tace haka nakeci ai

Innalillah... Kalli murmushinta, yarinyar nan kada takashewa momy ni🤣

Matsowa yayi dab da ita, Har gabanta yadan fadi, jikinsa Yana gugar nata, atsorace ta kalleshi
Shima yaga Hakan kawai saiya share, yasaka hannunsa acikin Abincin ya karyo kazar babba yakai Mata bakinta

Yanda ya matso tan Kamar zaiyi Mata kiss, ahankali yace "eat"

Jikinta yayi sanyi, kasala ta Kamata, ta kalleshi, Shima ya Kalle ta yace ci mana

Ahankali ta Bude bakinta yasaka Mata naman takaryi kadan taci

Yanda takecin abincinma kadai abin kallo ne, yazubawa pink lips dinta ido, komai nata me kyaune

Haka yayita dura Mata Abincin, hartace uncle na qoshi

Cikin sanyin jiki yace da gaske?

Ta daga masa Kai

OK jekishiga kiyi wanka ki kwanta kiyi bacci

Tace to

Saida yaga shigarta toilet din sannan yasaki ajiyar zuciya, meyake damunkane shazali? Wadannan abubuwan dayakeji na menene?

Karfa maganar Ajmal ta tabbata, Innalillah... How? Wannan qaramar yarinyar? Sannan ma yar aiki, yar aikinsa

Idan yagama tabbatar wa kansa gaskiya, tofa da an dafka abin kunya🤣😃Aida kunya ma yatunkari Ajmal da wannan maganar bare Kuma su momy, Kai Allah yasa Bahaka bane Bama
(to zamu gani de🤣)


Kadan yaci Abincin, yasake tafiya duniyar tunani, daga karshe ma saiya fice daga Dakin domin yabarta tashirya

Ita kuwa Tana Gama wanka taga babu towel, dube dube tafara sai can taga wata rigar fara, Jikinta Mai laushi, tadauka tasaka, rigar dukanta iyakarta gwiwarta, hakade ta Kalli kanta, tasake kallan kanta, Anya kuwa zata Iya fita ahaka?

Kai bazata iyaba
Dan kwalin datai rolling na rigarta tadauka tabazashi akanta sannan tafuto cikin Sanda
Tana futowama taga baya nan, tasaki ajiyar zuciya taje takashe wutar Dakin ta kwanta Akan gadon, tashige cikin bargo tayi adduah tarufe idonta

Saida yadau lokaci sannan yadawo Dakin, Yana shigowa yaga duhu, kunna wutar yayi yahangota ta makure akarshan gadon,Koda wanne kayan ta kwanta? Basu taho da kayantaba ko daya
murmushi yayi yasake kashe Mata wutar sannan Shima yashiga toilet yayi wankansa cikin nutsuwa, jallabiya yasaka yafuto, yadauki fillon dake gefensu yasaka shi atsakaninsu 🤣sannan ya kwanta batare daya rufaba

Cikin dare yaji sanyi, yaja bargon yaci gaba da baccinsa, itama tana bacci taji anjanye bargon, dasauri ta matso tasake shigewa ciki

Da asuba, shine yafara farkawa, ahankali ya Bude idonsa yaganta, sai yanzuma yatuna tare suke, fillon dayasa atsakaninsu Yana nan, tana kwance tana baccinta, gashin kanta duk ya barbaje

Sunkuyawa yayi zaiyi kissing dinta🙆🏻🙈saiya fasa, yasaka hannu yashafa gashin nata ahankali sannan yashige toilet yadauro alwala

Yazo gabanta yasaka hannu yana bubbuga fillon nata "ke"
Yaji shiru

Yasake cewa "qawar sajida🤣" still yaji shiru

Kawai saiya share ta yatada sallah, yasan baccin gajiya take saboda Bata sababa

Saida ya idar sannan yakoma wajanta ya sunkuyo dab da ita yace
" Haneef"

(zakayi bayanine🤣)

Yasake cewa "Haneefa"

Juyi tayi hadeda hamma tabude idonta, sannan ta karanta adduah tatashi daga bacci

Kallansa tayi da idanunta dasuka cika da bacci, batace masa komaiba

Shima ya kalleta yace ki tashi kiyi sallah fa

Cikin shagwaba tace uncle Allah ni baccin be isheniba
Tarufe idonta

Innalillah... Sufa mata matsalarsu kenan🤣😃

Yace am Kinga, asuba tayi, yakamata kitashi, kinji

Taja bargon harkanta tace um um

Toshi yanzu yazai Mata?

Bargon ya janye, yasaka hannu yadago kafadarta, yazaunar da ita
Dab da kunnanta yace tashi kiyi sallah kinji?

Anjima za'a fara taron

Daga masa Kai tayi, shikuma yafuce daga Dakin dasauri

Jikinta ta kallah, tashafa Jikinta, aranta yace um uncle baimin komaiba 😃Dama anty zeey tace bazaimin komaiba


Tatashi tayi alwala tayi sallah sannan tayi wanka tasaka kayan ta na jiya

Saida Gari yayi haske sannan yadawo Dakin da Kaya ahannunsa, yace gashi, kije da wannan wajan zainab tana jiranki

Saida ta gaisheshi sannan takarbi kayan tafita, tana zuwa daki wajan anty zeey suka gaaisa, ta kalleta tace dafatan lafiya ko?
Murmushi tayi tace babu komai anty, wallahi baimin komaiba

Tabawa anty zeeey Daria yanda tayi maganr 😁, Sosai zaka Fahimci da gaske take

Shiryawa sukai anan, anty zeey akwai gayu lokaci daya ta sauyawa shalele kamanni
Tayi kyau Sosai acikin doguwar Riga, light blue, harda jakarsu da takalminsu, takalmin yayi tsini dayawa, tana sakawa tace gaskiya bazan Iya tafiya da wannan takalmin ba

Kiyi hakuri haneefa haka Zaki zaka, shine yasiyo Miki su, yazakiyi

Haka tasa takalmin tana turo baki gaba, suka zauna suna fira kadan kadan

Sai wajan karfe Tara sannan Abbas yashigo Dakin Shima yasaka suit baqa yayi kyau, yace ku tashi mutafi

Shalele ta gaidashi ya amsa Mata cikeda fara'ah, ahankali shalele take tafiya anty zeey ta kamata, Yana harabar hotel din yajuya baya Yana waya sai Daria yake, tana hangoshi tace kodawa yake waya?

Juyowa yayi yaga sun futo, cak ya tsaida idanunsa akanta, tayi masa kyau Sosai, tafiyarta ya kallah yasan Dama daqyar zata Iya tafiya dashi

Ahankali Shima yataho Yana fuskantarsu, Saida sukazo dab dashi sannan yayi sallama awayar yace to anty sai anjima

Anan tagane da anty jidda yake magana

Babu kunya yasa hannu yakamo hannunta, Abbas ya kalleshi yayi murmushi Kai shazali Dan duniyane wallahi

Yakalleshi, shazali ni baka fadamin sunan babyn takaba, yasan da biyu yayi masa wannan maganar saboda kowa yasan cewa shazali bayasan qaramar yarinya

Shiyasa Wai baka fadamin sunan babynka ba🤣😃

Kallansa yayi yace "baby haneefa"

Kafahimta?


Cikin Daria yace ai dole na fahimta🤣

Hannunta Yana cikin nasa suka qarasa cikin Mota, zeey na gaba abbas na driving

Itadashi Kuma Abaya, yaqi sakin hannun nata, ahankali yake murzawa, laushi hannun nata kamar Bata aikin komai shiyasa yaqi saki

Ita kuwa duk wani iri takeji, idan Yana murzawa saitaji wani iri haka ajikinta, ahankali tafara zare hannunta, Amma saiya sake riqewa
Yajuyo ya kalleta cikin rada yace Mata why?

Kasa tayi da idonta,batace masa komaiba, Shima saiya kawar da kansa zuwa kallan titi Amma Bai saki hannun nataba, Har motarsu ta tsaya

Su zeey suka fita, mutane damqam a wajan, Yan Nigeria dakuma sauran qasashe turawa, Kallanta yayi yace Mata "wait"

Dakatawar tayi kuwa yayi sauri yafita ya zagaya yabude Mata motar dakansa, abinda yayi ba qaramin birge mutanan wajan yayi ba, ita kanta zeey Saida tace gaskiya yarinyar nan tayi Dace da samun shazali

Kafarta daya tasakko sannan tafuto gaba daya, masu camera kuwa me zasuyi dauka, Yan jarida da sauran gidan TV kasancewar ansanshi bane mu'amala baane da Mata, duk taron dazaai shi kadai yake zuwa, Amma abin mamaki yau gashi ga budurwa mace sai Hakan ya birgesu

Hannunsa ya miqa Mata, Saida ta kalleshi sannan tadora nata Akan nasa, yariqeta suna tafiya ahankali
Sun kusa shiga wajan takalmin Kafarta yagurde kadan, 🤣🤣Allah yasosu hankalin mutane ba Akan takalminta yake ba😅, a kansu yake

Cikin sauri ya saketa ya tsugunna a gabanta, yakama Kafarta ta Yana dubawa kamar me neman wani Abu, yadago kansa yace Mata sorry, sannan yakai kafar bakinsa yasakar Mata wani zazzafan kiss

Zeey de yau tana ganin ikon Allah, takalli shalele ta kalli shazali, gaba daya sun birgeta🤣

Yan jaridafa ansamu abinda akeso, tun lokacin daya tsugunna suka fara daukarsu photo

Shikuwa ko ajikinsa Bai dauki Hakan dakomaiba

Kamata yayi suka shiga wajan, wajan yatsaru matuka, abinci nan agaban kowa da ruwa da lemuka

Kamar yanda suka fada haka aka tsara kowanne mutum bibiyu

Cikin kwanciyar hankali aka fara Kiran sunayen mutane suna gabatar da kansu, Har akazo kansu suma suka fadi nasu😍

Sannan aka fara taron, Wanda suka dauki tsawon awa uku Ana wayarwa damutane Kai wajan habbaka harkar kasuwancinsu

Kallanta yayi, baya ganin fukarta Sosai, saboda gashin ta daya Dan saqqo yarufe Mata fuska

Yace kinsan me? Kallansa tayi tace a a uncle

Pls kidan janye gashin nan ki, Yana bani tsoro, ya qarasa maganar cikin sigar wasa

Daria yabata, Saida tayi Daria Sosai sannan tasaka hannunta ta janye gashin ta

Text ne yashigo cikin wayarsa yabude "" Shege abokina wato kana zaune Ana gyarama gashi, gaba daya ka rikicewa yarinya qanqanuwa""

Murmushi yayi, Kai Abbas, abbas bashida damuwa wallahi, kana wajan zamanka Amma hankalinka Yana Kan wasu🤣

Suna zaune Har aka Gama taron, inda suka yiyyi photuna, kowa sai tayashi murna yake Akan samun shalele, harda masu cewa sai sunzo biki
Shikuwa Yana amsawa kamar ya manta da maganar iyayensa

Hotel suka koma, tabi zeey dakinsu taqi komawa nasu dakin🤣

Sai can yamma Sosai abbas yashigo sannan tatafi, tabasu waje

Tana shiga Dakin taganshi zaune Yana amsa waya dawata Leda akusa dashi, da Alama daga office dinsune

Zama tayi, tayi shiru tana tunanin taron da akayi dazu
Fatanta daya, Allah yabatashi amatsayin miji

Saida yagama wayar Yajuyo ya kalleta, kina buqatar yawo,?

Ina zamuje?

Idanunsa cikin nata yace ko'ina

Tace eh inaso

OK ga rigar sanyi nan kisa, akwai sanyi yanzu, saimuje

Dasauri tatashi, ta cire mayafin kanta, gashin ta ya kallah tayi fakin sai qyalli yake, tasaka rigar agabansa, sannan tadora mayafin Iya kanta, Shima yasaka tasa suka fice daga hotel din, Hannunsa Yana cikin nata

Meyasa ne uncle yakesan riqe Mata hannu? (laushi yaji🤣🤣)

Tafiya sukai Sosai akafa Yana nuna Mata wajaje daban daban, wani waje ma daya nuna nata ruwa Yana futowa ga fulawa masu kyau a wajan, ta kalleshi tace uncle kaimin photo anan idan munkoma na nunawa sajida da mama

Wace mama?

Tace mama de

Oh Wai kina nufin anty? Ashefa ke mamanki ce🤣
Nikuma anty nace

Tace nasani

Kema idan kinso zata Iya Zama antynki

Antyna Kuma tayaya?

Yace ki tambayeta kiji, zata fada Miki ko ita ko qawarki,🤣🤣 tace masa to

Photon yayi Mata, wani mutum daga gefe Yazo yakarbi wayar yayi musu su biyu, yanda ya rungumeta ajikinsa akayi musu photon Kai saika rantse Samah da Safah ne🤣🤣


Har dare Suna yawo, daga qarshe sukaje waani shago yasai Mata waya qirar sumsung

Sannan suka dawo, dakansa yasaka Mata wayar acharge sannan sukai sallah sukaci abinci

Zama tayi shiiru agefen gadon, yaje yadauko wayar dakansa yazauna dab da ita
Yace ga wayarki

Kallan mamaki tayi masa tace

Uncle waya kasai min?

Yes tayi Miki kokuma asake Miki wata?

Tayi Sosai uncle nagode

Nine yakamata nayi Miki godia, dakika boyoni batare danayi Miki bayaniba

Kallansa tayi, babu komai uncle, yanzu zan Iya Kiran waya?

Wazaaki Kira?

Uncle Bilal

Lokaci daya ransa yabaci, yanzu yanzu yasiya Mata wayar Amma tana cewa zata Kira wani?
Waye Bilal? (um kaji manya wato Waye Bilal Bama Waye uncle Bilal ba 🤣🤣)

Tace masa babanane

Babanki?

Tace eh, shine babana, banda kowa saishi, mamata tarasu babana yarasu, shine gatana banida wani uba saishi saikuma anty jidda

Tana Gama maganr idanunta suka cika da kwalla

Tausayinta ne yakamashi, yace sorry, Ina so kibani labarinki, wacece ke?

Sunana haneefa suraj daga kuje,..... Tsaf tabashi labarinta kaf Bata boye masa komai ba

Sosai ya tausaya Mata no wonder take aiki, yasan cewa ayanda tabashi labarin babanta babu yanda za'ayi yabarta tatafi aikatau wani gida

Ajiyar zuciya yasauke, kiyi hakuri, insha Allah komai zai wuce
Nasan kuje, akwai wata yar'uwarmu acan, Amma tarasu da dadewa
Kwanaki ma nawuce ta Garin, munje gwagwalada Akan aikin company na da akeyi acan

Murmushi tayi tace Aina ganka

Cikin mamaki yace kinganni? A'ina?

Tace acikin Mota zankai babana asbiti na tsaida motarku ku rage mana hanya kuka tsaya Amma Baka futo ba ka Watso min kudi kuka tafi, da wannan kudin nayi amfaani wajan biyan kudin aikin da aka yiwa babana

Kansa ya dafe🤦🏻‍♂innalillah, kina nufin Babanki ne awata bishiya a zaune?

Ahankali tace shine uncle

Kiyi hakuri? Kiyafemin bansaniba, kada ki qullaceni aranki pls bansaniba

Murmushi tayi tace wallahi uncle babu komai, ni gode makama nayi, da Baka bani kudinba Aida bansan Yaya zanyi ba

Kidena maganar kudin nan, nawa yake ma?
End Ads