x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - SHALELAN BABA

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 64847 words

Category: Love Stories

Views 79

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
acikin motar yasa dasauri ya watsa kudin waje yazuge glass din motar Yarufe batare daya kalli yarinyar data tare suba

Idanunsa ya lumshe Ahankali yace "saminu les go inajin gabana yana faduwa awajan nan"

Ahankali yayi maganar inde ba zuba kunne kayi ba ba lalle kaji maganar tasaba, Shima saminun danya saba ne yasa yaji shi

Nan da nan yacika umarnin uban gidan sa yaja motar sukabar wajan









Mrs Usman ce ✍🏻
💕SHALELAN BABA💕
(Romance)

Writing by Amnah El Yaqoub

11&12

Bayan motar tabi da kallo,inda idonta yakai kan number motar taga ansa SHAZALI NO.7 Saida suka bacewa ganinta
Sannan tasauke kanta qasa takalli kudin da ya wullo mata, to ai ita ba kudin tafi buqata ba a yanzu, tafi buqatar motar akan kudin dazai Bata
Ahankali tasa hannu tadauki kudin tazuba musu ido, Tunda take Bata taba riqe kudi masu yawa hakaba, riqe kudin tayi acikin hijabin ta, taci gaba da tare motar Har Allah yasa wani ya tsaya, bayani tayi masa, Dan haka ya matso da motar Har bishiyar da Baba yake zaune, idonsa arufe suke, da temakon ta da temakon Mai taxi suka saka baba acikin motar sannan yaja suka tafi
Suna cikin tafiya, Amma gaba daya hankalinta yana kan babanta, idanunta cike suke da qwallah tace sannu baba
Bai Iya amsa mataba kawai kansa yadaga
Sunyi tafiya ba wata Mai Nisa sosaiba suka qarasa cikin Abuja, driver yace yarinya Ina muka nufa?

Tace Dan Allah katemaka kakaimu asbiti koma wanne ne, babana yanajin ciwo sosai, baisake maganaba yaci gaba da driving dinsa, Saida yasake wata tafiyar sannan suka isa wani private hospital fashmard, yana tsayawa da motar a harabar hospital din suka bude dasauri shida Shalele, baba yafara kokarin futowa Kenan ma'aikatan asbitin suka kawo gadon da aka tura marasa lafiya akai, nan da nan aka Dora baba akai sukayi ciki dashi dasauri, hankalinta atashe yake tace masa nawane kudin? Lokaci daya Yaji tausayin ta yakamashi, gata qarama, Kuma mace, Amma tana fuskantar irin wannan rayuwar, Ko ina mahaifiyar ta? Itace ta katse masa tunanin dayake Tace Malam nawane kudin?
Firgigit yayi yadawo Daga tunanin dayake yi, yace Kinga yarinya kibarshi kawai

Kanta ta girgiza tace a a gashi, hannu tasa cikin hijabin ta taciro kudin Daga cikin wanda aka wullo mata tabashi, ita kanta batasan nawa taciro masaba, tana miqa masa tashige cikin asbitin da sauri
Tana shiga wata nurse ta nuna mata dakin da aka kwantar da babanta, dakin ta shiga afirgice taga wani likita yana daura masa ruwa, tace doctor Yaya jikin babana? Yace Alhmdlh andaura masa ruwa yanzu, akwai allurar bacci acikin ruwan, zai yi bacci nadan lokaci kafin babban Likitan dazai dubashi Yazo, kiyi hakuri kinji, insha Allah babanki zai warke, yana gama magana yafice Daga dakin
Sai a lokacin ta zauna a kujerar da ke kusa da jikin gadon, a lokacin Har baba yafara lumshe idonsa alamun allurar da suka masa tafara aiki, hannunta takai kan nasa Ahankali ta riqeshi, cikin ranta tana Addu'ah Allah yabashi lafiya
Tana nan zaune riqe da hannunsa itama bacci yafara fizgarta tana sake bude idon duk Wai Dan karya dauke ta, Amma Saida yayi galabar daukarta, kanta ta Dora Agefen fuskar baba itama tafara baccin

Bata San tsawon lokacin data dauka tana baccin ba, saide tana farkawa ta kalli agogon dakin taga lokaci yaja, dasauri ta kalli inda baba yake kwance taga idonsa biyu yazuba mata ido yana kallanta, tace sannu baba, yajikin Naka? Murmushi yayi yace sauqi Shalele nah, kina bacci harma likita Yazo yaciremin qarin ruwan yanzu inajin karfi ajikina
Murmushi tayi tace Yauwa alhmdlh, Allah yabaka lafiya baba, yace amin Shalele nah, hijabin ta tadaga ta dauko kudin da aka wullo mata tace baba gashi

Yunkurin tashi zaune yake, tace Bari in sama Fillo abayanka baba, baiyi mata musu ba tasaka masa, tace wannan kudin baba dazu ne wani ya wullo minsu Daga cikin mota lokacin danake kokarin tare mana abin Hawa, nikuma Baisan ma nafi buqatar motar akan wannan kudin ba
Kudin ya kalla sannan ya kalleta yace wannan ai kudi ne masu yawa Shalele nah, wannan kuwa waye ne? Tace wallahi bansaniba baba, Amma baba kasan me? Ina ganinsa gabana yafadi (😃😃😃) Murmushi Baba yayi, saboda yasan Cewa yar tasa batasan abinda Hakan yake nufi ba, ahankali yace Allah yayi masa albarka, Naso ace naganshi nagode masa saboda ya temaki Shalele nah sau daya arayuwa, Amma duk da haka Allah yabiya masa dukkannin buqatunsa na alkhairi

Tana Murmushi tace amin baba, gasunan, ta ajiye masa kudin agefensa sannan tace Bari inyi sallah baba, toilet din dake cikin dakin ta shiga tayi alwala tashinfida Dan kwalin kanta tayi sallah, sannan ta temaka masa Shima yayi, likita yashigo yace yakamata yaci abinci Ko Yaya ne, Ana jimawa doctor zaizo, tace to

Dubu uku tadauka acikin kudin hannunsu tafice waje da sauri
Lemuka ta siyo musu da kek sannan tadawo, tasaka musu ita dashi agaba sukaci, yana gama ci bacci yasake daukarsa
Tana nan zaune doctor yashigo dakin, da alama anaji dashi kasance war Yanda taga nurse Har guda uku Suna biye dashi, matashin saurayi ne zai Kai 30yrs, fari ne tas, cikin nutsuwa yaduba jikin baba, waye yakawo shi? Ahankali tace ni.. Nice

Saida yasake kallanta sannan yace ok taso kibiyoni, tashi tayi tabi bayansa suka je Har office dinsa, yace yarinya keda waye kukazo nan asbitin? Tace nida shine kawai

Babu wani babban daya biyoku?

Kanta ta Daga masa tace eh, baba nane, nice nakawo shi, likita Dan Allah zaiji sauqi?

Saida maganar ta tabashi Daria, tayaya zai sani Bayan sauqi yana wajan ubangiji?

Afili sai yace mata babanki zai warke insha Allah kinji? Kiyi masa Addu'ah, za'a yi masa operation Dan gaskiya dafi ne yayi masa mugun kamu akafarsa na maciji, nayi mamaki ma da babanki yakawo yanzu Bai mutu ba
Tanajin zancen mutuwa tadora hannunta aka (🙆🏻🙆🏻) ta fasa masa kuka tace nashiga uku, Dan Allah likita karka Bari babana ya mutu Dan Allah na roqeqa

Lokaci day yaji yarinyar tabashi tausayi, yace ki kwantar da hankalinki, ni bance babanki zai mutu ba, nace ne nayi mamaki da Bai mutu ba Har Zuwa wannan lokacin saboda dafin yariga yayi masa illah yagama lalata masa kafarsa duka yana nema yataba masa hantar sa , to amma zamuyi masa aiki gobe insha Allah abin bazai Kai hakaba, saide kiyi hakuri zamu yanke masa kafarsa daya, already ta lalace bazata amfanu ba

Kanta tadora akan tebur din dake Gabansa kawai tana kuka, tarasa me zatace masa, gaba daya Taji duniyar tana juya mata

Shima Ahankali yace kiyi hakuri kinji

Daga masa Kai tayi, yadauko wani file yabata yace gashi zakisa hannu anan domin amincewarki akan yi masa aikin, but zaku je kubiya kudin aikin naku dubu dari biyu da sittin

Dasauri ta karbi biro din dayake hannunsa tayi sign din, mamaki yagama kashe shi a zaune, Ina wannan yarinyar zata samu wannan kudin daya ambata? Anya Taji abinda yace kuwa?

Saida yakare mata kallo sannan yace Daga wanne gari kukazo? Cikin rawar murya tace ku.. Kuje

Yace ok, zaki Iya tafiya, kibasu kudin, zamu shiga dashi operation gobe da safe insha Allah, yanzu yana karkashin kulawar mu Har Zuwa goben

Dasauri tafice Daga office din ta shiga dakin da Baba yake ciki, yana kwance idonsa biyu yanzu, batayi masa magana ba sai kudin dazu data dauka tafice da gudu, Saida taje tabiya kudin komai sannan tadawo da chanjin dake hannunta, wanda batamasan Ko nawane yayi saura ba

Tana dawowa takifa kanta akan gadon nasa tasaki wani irin kuka, cikin ranta kuwa tana ambaton Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, yanzu baban ta zata yanke wa qafa?
Hannunsa yasa yashafa kanta yace kiyi hakuri Shalele nah, kinji? Insha Allah zan warke

Daga masa Kai tayi, idanunta sunyi jajir, haka wuni awannan halin, batama neman abinci, to awannan halin datake ciki wanne abinci zata nema? Har dare yayi idonta biyu babu alamar bacci, baba nede yakeyi, Amma itakam idonta biyu, takama hannunsa ta riqe, haka ta kwana a zaune, Washe gari Suna idar da sallah nurse's sukazo suka sauya masa kayan jikinsa Zuwa light blue, na operation Kenan, lokaci daya hawaye ya zubo mata, ya tabbata de kafar baba za'a cire
Sun fara turashi Kenan zasu kaishi dakin tiyatar Yadubi nurses din yace Dan Allah 'ya' yana kubani minti biyu zanyi magana da yata, suka ce to babu damuwa suka fita Daga dakin
Suna fita yakamo hannunta yariqe yace HANEEFA
Cikin kuka ta kalleshi tace baba meyasa zaka kirani da wannan sunan? Murmushin karfin Hali yayi yace dole ce tasa, inaso ki saurareni da kyau, ki dauki magana ta da muhinmanci, HANEEFA Marka ba mahaifiyarki bace

Lokaci daya ta zaro idonta waje 😳😳meyasa takejin labarai marasa dadi ne Daga jiya Zuwa yau

Ya lura da yanayin data shiga, danhaka yasake Daga mata Kai yace qwarai kuwa ba mahaifiyarki bace, mamanki tarasu tun kina koyon zama, halaiya da kama gaba daya nata kika dauko, su biyu iyayensu suka Haifa akwai yayarta tana nan cikin Abuja Hajiya Hafsat, nayi mata alqawarin Cewa zan riqeki amana bisa gaskiya hakanne yasa ta yarda tabarki a wajena, Kuma Alhmdlh nasan nayi Miki riqon da Ko mahaifiyarki na Raye abinda zata Miki Kenan, insha Allah dazaran anyimin aiki lafiya zan kaiki wajanta kiga yayar mahaifiyarki,munyi magana da ita akan zanje wajanta muyi magana Mai muhinmanci akan ki, nasan bazai wuce akan maganar karatunki ba, koma de menene idan natashi qafata qafarki zankaiki wajanta

Abu nagaba koda ace Allah baiyi zan koma gidaba ki kula da Aududu, kada kiga rannan nace ki ajiye shi, rainane yabaci, shi din dan'uwanki ne, bakida kamarsa aduniya, duk inda zakije kije dashi kada ki yarda ki Rabu dashi, ki riqe mutuncinki na ya mace aduk inda kike, sai Abu nagaba, Koda ace ban dawoba kifadawa Marka Cewa nasaketa SAKI UKU

Hannu takai tarufe masa baki tana girgiza masa Kai a a baba karkayi haka baba meyasa Hakan baba? Taqarasa maganar tana kuka, hannunta ya janye yace akan Hakan na aureta Haneefa, munyi da ita zata kula dake bazata karya alqawari ba, munyi da ita arubuce Malam yahai ne sheda, idan ta karya alqalamin data dauka zamu Rabu, Kuma gashi ta karya din

Kafin tasake magana nurse suka shigo suka fara turashi zasu tafi dashi, itama Binsu tayi hannunta yana cikin nasa, Murmushi shinfide asaman fuskarsa, Saida suka je shiga dakin ne sannan suka dakatar da ita likitocin, tanaji tana gani tasaki hannun babanta yana mata Murmushi ta nayi masa kuka, suna shiga suka rufo kofar, haka ta zauna jagwab agaban dakin kan wata kujera da aka tanada domin zama, takifa kanta acinyarta tana kuka

To masu kallanmu Ayau ne zamu tattauna da wannan de fitacce Kuma mashahurin Dan kasuwar da ake ji Dashi awannan qasa Tamu dama wasu sauran qasashen qetaren

Dakatawa tayi da kukan datakeyi takai dubanta kan TV din dake manne ajikin bango kasance war asbitoci dayawa Suna saka kayan kallo aciki domin debewa marasa lafiya kewa

Lokaci daya gabanta yafadi, Ahankali ta bude pink lips dinta tace Shine.... Tabbas shine wanda ya cillo min kudi jiya, inda Bai bamu wannan kudin ba Ina zamu samu kudin da za'a yiwa babana aiki?
Plasma TV din tazubawa ido tana kallo

Mutane dayawa sunajin sunan SHAZALI Amma dayawa Daga cikin su basu San menene sunanka na gaskiya ba, menene ainashin sunanka?

Sosai aka nuno shi yayi mutuqar kyau cikin suit baqa, Saida yayi Murmushi Har dimple dinsa suka motsa, sannan yace Sunana HANEEF BUKAR SHAZALI, shazali sunan kaka nane abokai da yan'uwa suke kirana dashi Har sunan yabini

Kanada kamfnin shinkafa Shazali's Rice Mill, wanda babu wani kamfani daya kaishi girma bangaren aikin shinkafa a nahiyar Africa gaba daya, dakuma kamfaninka na takalma wanda muka tsinci labari a jarida Cewa kakashe maqudan kudade Har nera billion 10 wajan kirkirar wannan kamfani, katsam Kuma sai muka samu labari kana sake kafa wanin na sugar a gwagwalada Shazali's sugar processing company, Malam Haneef Yaya abin yake ne, kasance war ka matashi Amma ka mallaki wadannan masana'antu menene sirrin?

Ahankali Kamar me rada yace sirrin shine adduar iyaye kawai, sannan ba komai yasa nayi sha'awar bude kamfanin sugar ba nayi hakane saboda asamu a dauki matasa awannan kamfanin marasa aikin yi

Sannan su kansu masu sana'ar Saida rake Hakan zai musu dadi

Atakaice cikin second uku Haneef shazali yanada Aure?

Banda Aure

Amma akwai yanmata?

Eh akwai, Amma Har yanzu babu wadda tamin

Shakarar Haneef shazali nawa?

Saida yayi Murmushi yace 33

To Haneef shazali Mungo de da wannan lokaci daka bamu wajan tattauna wa dakai
To masu kallanmu anan muka kawo karshen wannan tattauna wa Tamu da shahararran Dan kasuwa Kuma young billonia Haneef bukar shazali, mutara a wani satin domin jin.....

Bata gama jin maganar ba saboda muryar baba Malam dataji abayanta yana Cewa Haneefa Ina baban naki?

Ajiyar zuciya tasauke tasanar dashi komai,ciki kuwa harda sakin da Baba yayiwa inna, yazauna Agefen ta ya rafka tagumi yace Innalillahi..., kiyi hakuri yata insha Allah za'a dace, fatanmu Allah ma yabashi lafiya, naje asbitin mu nacan gida jiya Likitan daya turoku nan yatafi gida sai yau nakoma da safe shine yamin bayanin Kuna nan asbitin

******
Cikin dakin operation kuwa kalau suka gama aikin lafiya, likitocin sai gaisawa suke da junan su sunama juna murna, baba ya kalli babban Likitan yace yaro Yaya sunanka? Cikin Murmushinsa Mai tsada yace baba Sunana doctor Bilal
Murmushi Baba yayi yace Bilal banaji zan qara minti goma aduniya, Tunda naganka naji ka kwanta min araina zaka Iya Bawa yata duk wata kulawar data dace, Dan Allah ka riqe min yata amana Kamar Yanda zaka riqe yayanka na cikin ka, ka dauka Cewa Kai muharraminta ne, kadauki Haneefa katafi da ita gidan ka, nabaka ita duniya da lahira, sunan mahaifiyar ta khadija, akwai yayar amahaifiyarta anan Abuja, zaka samun duk wani bayani dazai taimaka maka wajan sanin Hajiya Hafsat yayar mamanta ta hanyar wayata,ka riqe min ita amana, yatace idan tayi kuka nine nayi, idan ranta yabaci Kamar nawane yabaci, banida tamkarta aduniya, Bilal kada kabar Haneefa awajan Marka, kada kabar Haneefa awajan Marka... Kada... Bai qarasaba yayi salati tare da kalmar shahada yace gagarinku nan.... 😭😭
Doctor Bilal Baisan lokacin daya zube qasa yazauna ba, wannan bawan Allah hakika ya Dora masa babban nauyi akansa, wacece Marka? Meta yi ake Cewa kada abar Haneefa awajan ta? To waima wacece ita Haneefan da akeso yazame mata uba?

Jiri yaji yana dibarshi, sauran likitocin kansu abin yabasu mamaki, haka sukaja farin mayafi suka rufe wa baba fuskarsa

Doctor Bilal dake qasa a zaune suka kama suka miqar dashi, kafadarsa suka Bubbuga suka ce kayi hakuri doctor

Haka yakamo hanya yafuto Daga dakin tiyatar cikin sanyin jiki

Yana futowa Shalele da Malam yahai sukai wajansa, atare suka ce likita ya aikin?
Shalele tace doctor angama lafiya Ko?
Shima Malam yahai dafatan anyi wa abokina aikin lafiya Dana

Bai basu amsaba ya kalli Shalele yace kece Haneefa?
Dasauri tace eh nice

Cikin qwallah yace saide kiyi hakuri Allah yayiwa mahaifin ki rasuwa, kiyi hakuri yabani umarnin Cewa intafi dake

Lokaci daya ta Dora hannunta akanta dayake barazanar rabewa biyu, tace doctor mekace? Numfashin tane yake sama sama sai riyammm Tafadi qasa sumammiya



(haka rayuwar take, zaka tashi cikin tsananin gata da kulawa, Amma bakasan Yaya karshan ka zai kasance ba, zamu tashi da iyayenmu Suna sanmu muna sonsu Amma ubangiji daya fimu sansu ya dauke manasu 😭😭😭😭bawai Dan munfishi sansu ba




Doctor Bilal kana cikin cakwakiya aradu🤣


Dan Allah Sharhi da comments da share




Amnanku ce✍🏻
💕SHALELAN BABA💕
(Romance)

Writing by Amnah El

13&14

Bata tashi farkawa Daga Suman datayiba sai akan gado, baba Malam yana zaune a kujerar gefen gadon, yayin da doctor Bilal yake zaune akan gadon saitin kafafunta
Dishi Dishi tafara gani, ahankali harta bude idonta, baba Malam ta kalla tace baba Malam da gaske ne baba na ya mutu? Baice mata komai ba sai hakuri daya Bata
Tashi tayi zaune tamaida kanta kan cinyarta tafashe da kuka Mai ciwo, sunkuyawar datayi ne yasa Dan kwalin kanta yafadi, Bata damu dashi ba taci gaba da kukanta
Bilal yana Kallan kanta Gabansa yafadi, wanne irin gashi gareta saikace aljana? Anya yarinyar Nan kuwa bahaushiya ce? To Amma ai gashi tana hausa

Cikin nutsuwa da manyan ce yace mata, kiyi hakuri, mutuwa tazama dole, muma dukanmu ita muke jira, nayi Miki alqawarin zan riqeki amana, babanki yabani umarnin intafi dake gidan mu, kada nabarki da Marka

Dago kai tayi ta kalleshi, baba Malam yace hakane Shalele, yayimin bayanin komai, Kuma awajan nasa Ina ganin zakifi samun kulawa fiye da wajan Marka, Bayan hakama yanzu bakida wata alaqa da Marka
Kiyi hakuri ki bishi, idan yayi bincike yagano inda yayar maman ki take shikkenan saiya maidake can

Babanki ba kuka yake buqata ba a yanzu, Addu'ah yake so, nizan wuce gida dashi akai shi makwancinsa kema ki bishi kutafi

Idonta ta share tace baba Malam Yaya sunan mamata?

Sunan ta khadija, Kuma kamarta kikai babu abinda yarabaku da ita, mahaifin ki kuwa kin riga da kinsan baida kowa, iyayensa sun Dade da rasuwa, inda yanada dangi dazai sanar dake, nine danginsa Nima shine dangina

Bilal yace Nima babanta yayimin bayanin komai, Dan Allah idan kunje gidan kayi kokari kadauko min wayarsa, zanzo nakarba dole saita nan ne zamu gane komai

Baba Malam yace to Dana insha Allah zan karba

Sannan Dan Allah baba kayi hakuri ayi masa komai anan, muma na nan Ko zamu samu Ladan jana'iza, inyaso idan kaje gida saika sanar dasu komai, Nima din zanzo
Baba Malam yace to shikkenan babu damuwa dana
********
Acikin asbitin akayi wa baba wanka, Bilal yasanar da mutane nan da nan kuwa suka taru Kamar ansan shi, jama'ah sukai ta tsayawa aka hadu aka sallaceshi Aka kaishi gidan sa na gaskiya

Sannan yasaka Malam yahai a wata motar domin kaishi gida

Wajanta yakoma ya sameta a zaune ta rafka uban tagumi, domin ya kawar mata da tunani yace my daughter kidena tunani haka kinji?
(tofa😃🤣😱 kaji su Dr Bilal manyan iyaye)

Kiyi Addu'ah Ina ganin Hakan shine yafi ,
End Ads