Bari nakoya Miki yanda zakiyi amfaani da ita, matsowa yayi kusa da ita, Har jikinsu yahadu sannan yafara koya Mata wayar, tun suna zaune Har suka dawo tsakiyar gadon
Saida yagama yace kingane?
Eh nagane, nan danan tafara yi masa bayanin abinda yakoya Mata, yazubawa Dan qaramin bakinta ido
Tana bayanin Yana kusantota, shiru tayi tazuba masa ido
Ahankali yasaka hannu ya janye Mata gashinta, ya Matso da fuskarsa dab da Tata, burinsa kawai ya sumbaci wannan bakin nata
Dasauri tace uncle...
Firgigit yadawo daidai🤣mekake yine haka shazali 🤦🏻♂
Dasauri yafice daga Dakin yaja Mata kofar🤣🤣
(Haji shazalinmu🤣🤣🤣)
Baidawo dakinba Saida tayi bacci, sannan yasaka musu fillo yauma, ya kwanta Shima, tunani yafaara Akan yarinyar nan, yanzu Kam zuwa wannan lokaci haqiqa ya tabbatarwa da kansu son yarinyar ya Kamashi
Yana wannan tunanin baisamu mafitaba bacci yadaukeshi
Cikin dare fillo yayi gefe, babu Wanda yasani atsakaninsu, ga sanyin Gari Gana esi, kowa najin sanyi, hakanne yasa suka Matso jikin juna
Dumin dayaji ajikinta ne yasa yasake janyota jikinsa ya rungume ta Sosai, itama batasan lokacin data sake rungume Shiba, sukaci gaba da baccinsu cikin Jin dadi 🤣
********
Washe Gari suna farkawa da asuba sukagansu manne da juna, Dasauri suka rabu, kunya yakamata, shikuwa Yama kasa kallan ta, haka yashige toilet, baiyi alwalaba Saida yayi wanka🤣
********
Mami! Mami!!! Dasauri tajuyo tace na'am Afrah
Mami yakamata kidena wannan tunanin haaka, idan kina tunani Ina kikeso Musa kanmu ne?
Afrah kalli wannan yarinyar da aka nuna atv yanzu daga gidan talavijin na Russia
Afrah yarinyar nan kuwa Anya ba haneefan zainab bace?
TV din ta kallah, taga sunyi kama da yarinyar Sosai, haka babu abinda zasu fadawa juna, wanima idan yaganta yaga haneefan zaiyi zatan yanbiyu ne
Afrah tun lokacin Dana Kira Malam surajo yacemin zai kawota Har yanzu idan naakirashi wayar Bata shiga, Amma dazaran kungama bikin candy naku, dole zanje Garin kuje dakaina indauko haneefa
Idan kuwa bansameta ba, to tabbas wannan yarinyar Dana gani tareda haneef din momy to haneefanmu ce, dole inje gidan momy nasamu haneef yanemomin haneefa (tab shazali kaga ta kanka🤭🙆🏻🤣)
Afrah tace to Mami Allah yakaimu, tashi muje daki ki kwanta kihuta
(barka da futowa hajiya hafsat 🙏🏻)
********
Tana zaune a dakinta tana kallo, kamar yanda tasaba bibiyar al'amuransa yauma haka, tazauna tasaka TV agaba tana kallo, tunda taji ance yatafi Russian 🇷🇺, tadinga dube duben tashoshin dazataga an Nuna shi, kamar wasa kuwa tana cikin duben taga wata Tasha tana haska haneef shazali da wata yarinya
Tuni tatashi zaune, dede lokacin daya kama kafar yarinyar Yana kissing
Ana hasko idon yarinyar tace kaiiiii wannan ai haneefa ce, Waye yahadata da haneef shazali? A'ina ta sanshi?
Nashiga uku ni sadiya 🙆🏻😱
Cikin sauri tadau wayarta tafara neman number Bilal domin ta fada masa cewa toga yarsa can awata qasa da wani 🙆🏻🤭
(sorry sady😢)
********
Yau Kam a hotel suka wuni, kamar wasu surukai haka suka zauna a Dakin, ita takasa sakewa dashi, tana tuno yanayin jiya daya Matso zaiyi kissing dinta
Shikuma Yana tunanin dumin jikinta nayau dayaji
Gaskiya dole ma duk Wanda ya auri yarinyar nan yahuta, dan haka yazama dole shiya aureta, yarinyar tanada kayan more rayuwa
Haka suka yi shiru shi sai amsa waya yake, ita Kuma tana game da wayarta, Amma kuma sun kasa kallan juna 🤣
Yauda dare yayi kuwa fita yayi daga Dakin sai can daya dedeci tayi bacci sannan yadawo
Shima ya kwanta
Washe Gari dasafe sukai shirin tafiya, yauma anty zeey ce tazo Har dakinsu ta shiryata, doguwar Riga tasaka yar Dubai
Kwalliyar da zeey tayi Mata ta karbeta Sosai, girar nan Tasha gyara
Zaunawa tayi abakin gado, tana daddanna wayarta, ai suna komawa Nigeria 🇳🇬 zata je Har gidan anty jidda tanunawa sajida
Saide Tarasa dalilin wannan kyauta ta uncle haneef
Shigowa yayi Dakin Shima cikin qananun Kaya, ta daga Kai ta Kalle shi
Sai qamshi yake, yace tashi mutafi, yaje yadauko jakar kayansu, da wadda yasiya Mata dakuma tasa dayazo da ita
Tashi tayi tsaye, tasake Kallansa Dan gaskiya yayi Mata kyau sosai
Shima tana tashi yazuba Mata ido Yana kallan ta, zuciyarsa na tunzurashi Akan yasanar da ita abinda yakeji game da ita
Takowa yakeyi ahankali Yana tunkarota, itade tana binsa da kallan mamaki
Yana binta tana yin baya ahaka Har sukaje jikin bangon Dakin
Cikin faduwar gaba tace un... Uncle... Lafiya?
Bece Mata komaiba yasaka hannunsa yakama kyakykyawar fuskarta da duka hannayensa biyu, yamatso da fuskarta dab da tashi
Cikin sauri ta runtse idonta ganin abinda yake shirin yimata
Ahankali yadora bakinsa Akan nata, yanayi Mata wani irin kiss me zafi, dan qarami lips dinta yakama yanasha,
Sun dauki tsawon minti biyar ahaka sannan yazare bakinsa daga cikin nata
Tana Bude ido taga idonsa akanta dasauri tayi qasa da kanta
Baisaki fuskarta da hannun nasaba, cikin rada yace "Haneefahhhh... Yaja sunan nata
Kasa amsawa tayi
Yasake Kallanta, cikin rada yace Mata" I really luv you so much, Zaki Iya aure nah "???
(yau kaam kasa nakasa magana shazali, wallahi ku soye harku qone, Nigeria tana nan tana jiranku☺)
Yaya kuke ganin amsar haneefa zata kasance?
Anya shazali kuwa Yana saane da maganr iyayensa akansa?
To dafatan de yanzu kowa yasan matsayin momy da hajiya hafsat dakuma maman shalele
Yaya zata kasance tsakanin Bilal da sadiya?
Duk kubiyoni zuwa gobe domin Jin Yaya zata Kaya, Ina yinku Sosai fans
Sharhi comment share Dan Allah kada amanta 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Amnah eh ✍🏻💕SHALELAN BABA💕
(Romance)
Writing by Amnah El
35&36
Fuskarta ta qwace daga cikin hannunsa tafice daga cikin Dakin dasauri
Shima yabita da kallo, murmushin daya gani a Fuskarta kadai ya gamsar dashi wajan samun amsarta
Murmushi yayi Shima yabiyo bayanta da jakar kayansu, haka suka futo harabar hotel din, tana gaba Yana binta Abaya, zeey da abbas suna tsaye awaje suna jiransu, zeey tace Kai Ina jambakin Dana shafawa yarinyar nan?
Daria abbas yayi yace sun shanye abinsu🤣
A a haba de Kai kana ganin Hakan zata faru?
Kinga uwargida wasa nake Miki, Bana tunanin Hakan gaskiya
********
Tana samunsa awaya tace Yaya yanzu Naga haneefanka a TV wallahi
Haneefa kuma? Meya hadata da gidan TV ita Kuma?
Yaya wallahi yanzu naganta da haneef shazali, suna Russia shida ita
Haneef shazali de Dan kasuwar nan?
Eh shi Yaya, wallahi dashi naganta yanzu
To ita mezai hadata da shazali? Tayaya ma ta sanshi? Kinga sady idan nagama aiki zanje gidan datake ingani
Toshikkenan Yaya sai ka dawo, Ga Abdallah Yana gaisheka, OK tokishafamin kansa, bye
********
Jirginsu na sauka sukayi sallama dasu zeey, baima yi waya azo daukarsu ba, kawai taxi yatare musu suka wuce gidan jidda Kai tsaye, alokacin uku saura
Suna zuwa gidan sajida ta rungume ta, sukayi ciki, Shima afalo ya zauna shida anty jidda, tace mutanan Russia, Yaya taro? Alhmdlh anty, mundawo lafiya, kuma nagode Sosai
Ba godia zakamin ba haneef, fadamin zakai dalilin dayasa ka dauki yarinyar nan, haneef meyasa zakai haka? Idan wani ne yadauki yanbiyu zakaji dadi qanina?
Ajiyar zuciya yasauke ya kalleta cikin serious voice yace anty kiyi hakuri nasan nayi laifi, Amma naje wajan hajara da hairat sunqi yarda mutafi, anty alokacin Banda zabin daya wuce hakanne, shiyasa nace tashiga Mota mutafi, Amma itama ba'ason ranta ba, saboda Dana dauketa ma da bacin rai muka tafi,Amma kiyi hakuri, insha Hakan bazai sake faruwa ba, ki yarda da qaninki anty, bazai yi abinda zai cutar da 'yar kowaba
Anty jidda tace Toshikkenan, Allah yashige mana gaba, Allah kuma yasa kada wannan labarin ya Isa kunnan Wanda zaice Yana sonta zuwa gaba, domin kuwa bazaiji dadi macen dayakeso tafita da wani namiji daban qasar wajeba
Anty wacce irin magana kike haka? Dama haneefa akwai Wanda zata aura ne daya wuce ni? Haba anty, duk da babu abinda yashiga tsakaninmu ai bazan yarda ta auri waniba, Bayan na dauketa na nunawa Dunia cewa itace wadda zan aura, idan naki aurenta ma ai sai Allah ya kamani
Dadi yakama anty jidda, tace haneef kana nufin zaka auri haneefa ta?
Zan aureta anty, wannan dalilin nema yasa nabiyo ta wajanki ban wuce gidaba, anty nasanar dake inason haneefa, itama nafada Mata Ina sonta
Amma yanzu haneef Yaya kake ganin zamuyi da momy da daddy?
Cikin sanyin jiki yace shine abinda bansaniba anty
Kaga qanina ka kwantar da hankalinka, zanyima adduah, kawai kaje kasamesu kasanar dasu abinda yake faruwa babu maganar boye boye
Toshikkenan anty, nizan wuce, duk yanda mukai dasu zakiji, to qanina sai anjima
Yana tafiya takira haneefa tazo tazauna agabanta, tabita da kallo
Ahankali tace mama Dan Allah kiyi hakuri, wallahi shine yace nashiga mutafi
Tokuma haneefa danyace Kishiga saiki shiga? Idan yace Kishiga wuta ma Kenan saiki fada?
Hawaye ne suka zubo Mata zirrr, tace mama kiyi hakuri Dan Allah
Haneefa duk da haneef qanina ne, bazanso ya cutar dakeba, dole zanyi kokari Naga na qwato Miki yancinki awajansa, yasanar Dani cewa Yana sonki, sannan zaije yafadawa su momy komai
Dasauri ta kalli anty jidda
Anty jidda tace eh haka yafadamin, kada kidamu kiyi muku adduah insha Allah babu komai kinji?
Daga Mata Kai tayi, anty jidda tace tashi kitafi, da yamma sai nasa driver ya maidake
Tana tafiya, anty jidda tadaga hannu ta godewa Allah, wani farin ciki Yana qara ratsata ratsata, alhmdlh addu'arta ta karbu
Wayarta ce tayi qara tana amsawa tace hello Bilal
Na'am antunmu kuma amaryarmu ya gida?
Gida alhmdlh doctor
Dama nakirane ki hadani da haneefa
Godia tayiwa Allah, yanzu dabasu dawoba me zata fada masa? Tasan da daga yau Zaman yarinyar yaqare agiidan su, shikuwa Bilal da biyu yayi Mata wannan tambayar domin ya tabbatar da mgnr sadiya, shin tana wata qasar dinne kokuma tana gida
Anty jidda ta kwala Mata Kira sannan tabata wayar tayi cikin dakinsu tana magana dashi
Da yamma kuwa anty jidda tasa driver da sajida suka rakata gidan momy
*******
Tunda suka dawo daga Russia yau tsawon kwana biyu Kenan, tadena zuwa gyara masa daki saide intaga bays gidan zatayi sauri tagyara masa tadawo, Shima anasa bangaren Bai nemetaba, yasanar da Ajmal komai Shima kuma yadada karfafa masa gwiwa Akan Hakan, saide Har yanzu tunanin yanda zai fuskanci iyayensa yake da maganar
Kwanansu uku da dawowa tana falo tana goge goge tana Taya baba Hanne, dan gyaran part din momy Dama baya daga cikin aikinta, kawai yau din ne take Taya baba Hanne
Shigowa yayi cikin Shiri zaiyi tafiya shine zai sanar da momy
Kawai ya ganta tana goge goge, Dasauri ya qaraso wajanta yariqe towel din, meyasa kike aiki?
Bata bashi amsaba sai qasa datayi da kanta
Yace kada kisake aiki agidan nan kowanne iri ne, Nima na part Dina nahanaki, banaso naqara ganin kina komai kinji?
Daga masa Kai tayi, ya Matso da bakinsa saitin kunnan ta yace zamu tafi England yanzu nida Ajmal zamuje kallan gasar premier
Insha Allah idan muka dawo zan sanar dasu momy komai, kinji?
Qaran kofin dasukaji abayansu ne yasa suka kalli wajan dasauri, daya daga cikin yanbiyu ne, basu gane ko wacece ba acikinsu
Kallan haneefa yayi yace saina dawo OK?
Yakalli yanbiyu yace mahaukaciya koma wacece acikinku🤣🤣
Yashiga dakin momy yayi Mata sallama yatafi
********
Tun lokacin daya tafi, tafara yiwa baba Hanne karatu Sosai, Amma idan tatuna maganar da uncle yafada Mata sai jikinta yayi sanyi, Tasan cewa rabuwarsu tazo, yanbiyu kuwa idan sun ganta harara ce take rabasu, Tasan kuma Hakan baya rasa nasaba da ganinta dasukai afalo itada haneef duk da batasan wacece tagansu ba acikinsu
Haka take kokarin sharesu
Har suka dawo daga England shida Ajmal, da yamma suka dawo, Bata Samu ganin saba, sai washe Gari dasafe da akai baqi agidan
Anty fadila da anty iklas ne qannansa dasuke binsa sukazo, sai hidima ake dasu agida
Yaron anty fadila namiji kyakykyawa dashi taji tana son Yaron, afalo tazuba musu ido tana kallan su Yaron Yana sakawa haneef ice-cream abaki, sai nishadi suke
Anty iklas kuwa mace ce yarta ko zama batayi
Har yamma suka Kai sannan suka tafi, da daddare tana falo tana kallo duk da ba dabi'arta bane, Shima yashigo falon yazauna
Cikin fishi momy tace to baka isaba, aiba Kaine ka haifemu ba
Lokaci daya idanunsa yacika da qwallah, abinda basu taba ganiba a wajan haneef
Ya kallesu, yace momy daddy, yarinyar nan itace bugun zuciya ta, wallahi idan ban auretaba mutuwa zanyi
Cikin masifa momy tace Wai Kai haneef ba kada Aiki da anyima Abu saikace zaka mutu zaka mutu to wallahi wannan Karon saide Allah yaji qanka🤣🤣
A a hajiya, meyayi zafi haka,? Inji daddy
Ya kalli haneef yace wacece wadda kakeso din?
Ahankali yace haneefa
Wacece haneefa?
Tanan gidan yarinyar datakemin Aiki
Lokaci daya momy tafara tafa hannu tana salati, karasa wazaka so sai me Aiki haneef?
Daddy yace Dan Allah hajiya kiyi shiru yasake kallan shazali yace jeka turomin yarinyar inyi Mata tambayoyi
Ahankali yatashi yafuta daga falon, kansa namasa mugun ciwo, dan kada tagane yanayin dayake ciki saiya Dan nutsu
Ya tura dakinsu, tana zaune itada baba Hanne suna karatu, yace Mata haneefa zo mana, Gabanta ne yafadi, tasan kuma shikkenan magana ta qare
Saida suka futo yaqara kwantar Mata da hankali sannan suka shiga Dakin
Gabanta Banda faduwa babu abinda yake, kallan da momy take binta dashi kadai ya Isa ya tabbatar Mata da cewa babu hairu alamarin🤣
Daddy ya Kalle shi yace haneef jeka Dakin momynka kabaamu waje
Saida yajuyo ya kalli haneefa sannan yatafi, suna ganin fitarsa daddy yace yarinya meyasa kikeson haneef? Dan kudinsa ko? Kokuma wani ne yaturoki aboye Bamu saniba?
Hawaye ne suka zubo Mata masu dumi, ta girgizawa daddy Kai
Momy tace toki tattara yanaki yanaki kibar gidan nan yanzu basai anjimaba, kinji nafada Miki, akwai yaran damukeso danmu ya aura
Daddy ya kalleta yace kinji abinda aka fada Miki?
Cikin kuka tace eh, kuyi hakuri, tatashi tafuto tana share Hawaye, Dama tasan haka zata faru, tasan cewa haneef yafi karfin tunanin ta, kawai tana yaudaran kanta ne
Tana shiga dakinsu tafara hada kayan ta cikin jaka
Baba tana tambayrta Amma batace Mata komai ba, sai sharar Hawaye kawai datake
Truly dinta taja, tacewa baba kiyi hakuri baba zamana a gidan nan yaqare, sai wata Rana, tafuto falo tanajan jaka tana ruskar kuka
Samah na ganinta tace sai aqara gaba kuma, Safah kuwa batace da ita komaiba
Itama Bata Kalle suba, tawuce tafuto harabar gidan, tana tafe tana share hawaye
Dakanta tabude gate din gidan tafuto, kanta yasara Mata, afili tace tabbas kowa yabar gida... Allah yaji qanka baba, na tabbatar babu Wanda zai Soni aduniyar nan Sama dakai, zan koma kuje Koda kuwa Hakan Yana nufin Inna zata kasheni Dan azaba, zan zauna a gidan ubana, inda babu me korata bare ayimin gori
Jakarta tabude tasaka number Bilal takirashi, bugu daya yadauka, tace uncle Dan Allah kazo ka daukeni
Haneefa lafiya?
Lafiya uncle nide Dan Allah kazo, tafashe da kuka, yace subhanallah gani nan, kina Ina yanzun?
Ta kwanta ta masa wajan sannan takashe wayarta baki daya ta jefata acikin jaka, kallan gidan tayi, Bata marmarin qara shigowa gidan nan, su riqe dansu Itama ta riqe mutuncin ta
Tafiya tafarayi akafa, harta hango motar Bilal, Yana zuwa kuwa tashige suka tafi
Meyake faruwa haneefa? Kisanar Dani mana
Kuka tasaka masa, lokaci daya tabashi labarin komai
. Dakatawa yayi da driving, Kenan da gaske sadiya take ita din tagani
Cikin fishi yace, ke kinason haneef din?
Tayi shiru, Kenan tana sonsa 🤣yasake cewa shi haneef din Yana sonki?
Ta daga masa Kai
Yace to kunyi sa'ah kunason juna, wallahi dayau saiya gayamin shegen dayasa ya daukeki yafita dake wata qasa, ni tun farko ma Dakin sanar Dani halin dakike ciki a wannan gidan wallahi dabazakiyi kwana daya acikiba, Amma sai kika nunamin a gidan jidda Zaki zauna
Cikin hawaye tace uncle Dan Allah kayi hakuri
Rufemin baki ni, mezaki fadamin (tofa ran uba yabaci 🤣🤣🤣)
Motar yaja suka fara tafiya, tace uncle kuje zaka kaini
Mezaki yi a kuje?
Dan Allah uncle kada ka tambayeni dalili, natuna baba ne pls kakaini can
Tausayi tabashi Dan haka bece komai ba suka tafi kuje, suna zuwa kofar gidan kuwa sukaga wata danqareriyar Mota,dawata motar Abaya, da kuma yansanda kusan biyar suna tsaye
Bilal na tsayawa shalele ta futo, mekuma inna marka tayiwa Yan Sanda?
Mami kuwa tana hangota tace haneefa tah!!!
Dasauri ta kalli matar taga suna mutuqar kama Sosai, afrah tatafi da gudu ta rungume shalele
Hajiya hafsat ma haka, gaba daya sukasa kuka, Bilal kansa Saida yayi qwallah, Hajiya hafsat tace nice mamanki haneefa