Kamar ma basa taba wajan wallahi, shine nakeso asamomin wasu masu aikin please daddy
Murmushi yayi, yau shida kansa yace Alhaji shazali Kenan 🤣
Dasauri Haneef ya Kalle shi
Shima daddy yace yes, Alhaji shazali, bahaka suke fadama ba? Wato Kai bakada aiki sai akawo ma yarinya me aiki, Washe gari ka Koreta, shazali Anya kuwa? Anya zaka Iya riqon Aure kuwa?
Kansa ya sunkuyar qasa bece komai ba
Daddy yaci gaba, toka bace kabani waje, babu wata yarinya da za'a sake kawoma, aiba Haifa ta kayi ba, sannan munyi waya da Alhaji Sadiq yace bakaje kaga yar tasaba tsawon wannan lokacin, ba shawara nake bakaba, umarni nake baka, yanzu basai anjima ba kanemi Ajmal kuje ku ganta, zanyiwa babanta waya nasanar dashi
Gobe Kuma kakoma wajan dayar itama ka ganta
Ajiyar zuciya yasauke, baicewa iyayen masa uffan ba, yatashi yafice Daga falon idanunsa jajir, shifa Yama manta da batun wadannan yaran, ashe su daddy Har yanzu abin yana ransu
Wayar Ajmal ya kira, yace masa gashinan Zuwa
Ajikin motarsa ya tsaya yana jiransa, Yaji massage yashigo wayarsa, yana dubawa yaga daddy ne ya turo masa da address gidan
Tsaki yasaki Bayan yagama karanta wa, Daga gefensa yaji ance Yaya gashi Wai inji momy, kakai mata
Kallanta yayi, yaga wata Leda ahannunta , baisaniba Samah dince Ko Safah, Harara yabi yarinyar dashi, yace ajiye anan
Ta ajiye ledar Agefen sa ta juya ciki
Ajmal nazuwa ya miqa masa wayarsa, yace kakaimu wannan address Ajmal, bazan Iya driving ba, daddy ya matsa akan naje Naga yaran nan, wallahi banasan maganar auren nan
Kafadarsa ya Bubbuga kayi hakuri abokina, insha Allah Allah zai kawo mafita
Aharabar gidan suka tsaya, babban gidane na gaske, da alama itama mahaifinta yana dashi sosai
Wani ne Yazo yayi musu iso, Zuwa dakin baqi
Dakin yayi kyau, ga sanyin esi dayake tashi
Ma'aikata ne suka fara shigowa da girke girke, Kala Kala, Saida suka ajiye girki yakai kusan Kala takwas
Sannan aka ajiye musu lemuka
Ajmal yayi Shiru yana Kallan ikon Allah
Qamshin turaren dasukaji ya taso ne ya tabbatar musu da Cewa tazo
Kallan su tayi tace hi
Suka Daga Kai Suna kallanta, baqa ce ba fara ba, saide mayukan datake shafawa yasa tadan Washe, babbar mace ce sosai, shi kansa da kadan zai girme ta
Mayafin jikinta Dan qarami ne, saita yafashi Iya kafadarta daya
Zama tayi a kujerar datake fuskantar su tace Sannunku fa
Shi dakansa ya amsa yace "yawwa"
Tace am Haneef Shazali Ko?
Yace "yeah I am"
Munyi magana da dad Dina, yacemin za'a turo min Kai in ganka kokamin, well nide awajena banda matsala, Tunda naganka yanzu naji kayimin, zaka Iya Zuwa kasanar a gida, mun dede ta kanmu, kawai ayi maganar Aure
Lumshe idanunsa yayi, shi aka turo mata tagani Ko yamata? Hmm
Ahankali yace ba damu
Ta kalli abincin gabansu, meyasa bakuci komai ba?
Ajmal daya Dade da mamakiin wannan uban girki yace, to ranki yadade wannan abubuwan ai sunyi yawa, ruwa ma kawai ya wadatar, saide fa kiyi hakuri kinsan manyan mutane basu cika cin abinci ba awajajan da aka gayyacesu, musanman ma shi angon naki
Murmushi tayi, to aini aganina wannan ma yayi kadan, a kullum Ana girka min abinci fiye da ashirin arana
Ajmal yace Kuma duk ke kadai kikeci? 😳😳
No zanci wanda zan Iya cine, sauran na zubar dashi
Shazali ya kalleta, baice komai ba
Ajmal ya miqa mata ledar dasuka zo da ita, yace to ga wannan amarya, kyauta ce Daga ango
Ledar ta karba, ta bude ta, turare ne aciki, guda uku, masu tsada, aqalla Ko wanne daya acikinsu zaikai dubu hamsin
Yatsina fuska tayi, tace Haneef wannan wanne irin turare ne? Ai sunyi araha dayawa Kamar fiyawota🤣😃🤣
Masu tsada nake shafawa, na dubu Dari biyu, Suma duk wata saina sake wasu koda kuwa basu qare ba
Amma babu damuwa, ngd, kuyi hakuri ban fada muku Sunana ba, ni Sunana Hairat Alhaji Sadiq dala, Haneef abinda nakesan fadama shine, arana Ana girkamin abinci kusan ashirin
Ina zuwa gyaran gashi duk Bayan kwana biyu, Amma Tunda zan auri Haneef Shazali zaka dinga kaini wajan gyaran gashi kullum 😳🤣
Duk wata babana yana kaini yawon bude ido qasashen qetare, Bana girki, zaka samomin ma'aikata Kamar Yanda kagani a gidan mu
Bafa anan abin yatsaya ba🙆🏻♂duk wata dubu dari tana shiga account Dina Daga bankin babana wannan ta Zuwa shan ice cream ce
Kai meyasa ma zan Bata lokaci na wajan yima bayani, nasan banda matsala dakai inde wajan kudi ne, duk da mom Dina tana Cewa Yan kasuwa su a kullum burinsu shine Yanda zasu samu riba, basu yarda da rashin riba akan kasuwanci ba
Huci Haneef yafara 🤣😃
Ajmal yana Kallan yanayin sa aransa yace wannan tun kafin ya wankawa yar mutane mari, babanta yadauki mataki akanmu Gara najashi mutafi
Cikin sauri yace to hajiya Hairat, ga kati nan me dauke da numbers din angon naki, zaki Iya kiransa idan kinsamu time, mu zamu wuce, sai Kuma next time idan mundawo
Tace ok, Bari na rakaku
A a aike gimbiya ce, ki zauna ki huta Mungo de
Haneef baiko kalli inda takeba suka fice
Suna shiga mota, Yadubi Ajmal, meyasa kace zamu tafi baka Bari nayi mata shegen duka ba 🤣😃
Meyasa zaka hanani?
A a Haneef nifa dama Tunda Naga yanayin ka nasan idan na qyale ka, to bazamu Rabu da yarinyar Nan lafiya ba, shiyasa nace mutafi
Huci yaci gaba da yi, matsiyaciya harni zata kalla tace Wai anturo mata ni taga Ko nayi mata? Talla nake dakaina?
Ajmal yayi Daria, au Kai wannan ne damuwar ka? To maganar data fadawa Yan kasuwa fa? Bata duba dukanmu Yan kasuwar neba, yaci gaba da Daria
Haneef yayi tsaki, Wai gyaran gashi duk Bayan kwana daya Kai kaji wani bala'i
Ajmal ya qara da dubu dari tashan ice cream 🤣😃
Tsaki kawai Haneef yake ja, turaren jikinta Ko nawa baikai tsadaba, shine zatace wanda aka kawo mata yayi araha dayawa, ni batasan ma bada kudi na nasiya mataba
Ajmal yaqara tunzurashi, araha Kamar fiyawota, haka tace
, yanzu Kuma sai goben idan Allah yakaimu idan munje wajan dayar saimuji, ita Kuma menene nata qa'idojin 🤣🤣
Haneef de Haushi ya cika shi, yace no bakwa gobe ba, saide jibi Ko gata, ai babu wajan wadda zan sake Zuwa gobe, saina huce da wannan baqin cikin
Ajmal yace to shknn, babu damuwa Allah yakaimu
********
Washe gari yana zaune a qayataccen office dinsa, takardun dasukai meeting akansu yake dubawa, yaduba yaduba yakasa fahimtar komai
Ya tattara su ya ajiye agefe, yazuba tagumi
Meyasa ne Tunda yaga yarinyar Nan tunanin ta yahanashi sakat?
Shide yasan baya sonta, to meyasa zaiyi tunanin ta?
Yasan Ajmal kawai fada yayi, Amma shi yasan babu wata yarinya dayake so
Kawai de yanaji aransa yanaso yasata agaba yanata kallanta, kawai tana birge shi ne yarinyar gata yar qarama Amma tanada abubuwan hutawa masha Allah, shiyasa yake ganinta Kamar yar tsana
Toshi de yanzu idan yakoma gidan anty jiddah yau, dole zata masa wata fassara, dama rannan Daga Dan Kallan yarinyar tafara Watso masa questions
Ajmal yace, Haneef Anya kuwa ba wani Abu kake qullamin ba? 😃kaine yau zaka ce zaka rakani wajan yarka zance?
No serious fa abokina da gaske nake, Naga Nima jiya kana yin aiyukan ka na katse ma nace kazo ka rakani, shiyasa Nima yau zan rakaka, idan zakaje Nina gama aikin danake, kawai ka futo mutafi
Ajmal Bai kawo komai aransa ba yace to shikkenan, ganinan Zuwa, zanje Naga my sajeey
(besan Shima yau ta manya akayi masa ba 🤣🤣)
Saida Yazo kamfnin su Haneef sannan sukabar motar Haneef awajan saminu, yace saminu zaka Iya wucewa gida, akwai inda zamu
Saminu yace to yallabai asauka lafiya
Suka shiga motar Ajmal suka tafi
Saminu yabi Bayan motar su da kallo
Yarasa Ina su yallabai suke Zuwa su kadai kwana biyu, kokuma yakusa samo musu uwargida ne? 🤣😃
Ajmal na driving Amma Haneef gani yake Kamar bayasan tuqa motar, haka de yadan ne komai aransa Har suka je gidan anty jiddah
Nocking sukayi, Amma Shiru ba'a zo anbude ba
Anty jiddah yau tana kitchen da kanta, sukuma su Shalele Suna daki, Sajida tace Kamar fa Nocking nakeji
Shalele tace Bari naje nabude, may be wata ce tazo
Riga da sket ne ajikinta English wears, takama gashin kanta tayi parking, jelar gashin nata tanata bin bayanta
Tatashi ta nufi kofar falon, Zuciyar ta daya ta bude
Sai ganin sa tayi agabanta, Zuciyar ta ta tsinke, Shima anasa bangaren ido yazuba mata yakasa dauke wa
Ajmal ya kalleta, wacece wannan Kuma?
Cikin in.. Ina tace sannunku da Zuwa, tajuyo cikin falon da sauri
Idanunsa Bai tsaya ko'inaba sai akan dogon gashinta
"masha Allah, me irin wannan gashin itace zata ce akaita wajan gyaran gashi kullum aciki umarni akaita "
Cikin daki tashige da sauri, ta Cewa Sajida ke wallahi su uncle Haneef ne, shida wani
Sajida tace haba? Kode Yaya Ajmal ne? Bari naje nagani
Falon ta futo, tana ganinsu tatafi da gudu tafada jikin Haneef, uncle sannunku da Zuwa
Yace yawwa my daughter, Ina anty takene? Kiramana ita mana, tace to, sannan ta kalli Ajmal tace Yaya sannu da Zuwa
Yawwa my sajeey
Yana ganin tafiyar ta, yace gaskiya Haneef bakamin kara wallahi
Agabana yarinyar Nan sai rungumarka take😃
Ya kalleshi, Ajmal mekake nufi? Yarinyar nanfa muharrama tace
To Dan tana muharramarka saikayi ta rungume ta? Ina zaune agefe
Haneef yace shikkenan Ajmal kaima rungume ta, rungume ta inka isa, wallahi Daga ranar bakai ba ita
Kawar dakai kawai Ajmal yayi, sai can Kuma yace kai abokina wacece wannan yarinyar data bude mana kofa?
Yana sane Sarai yace a'ina?
A kofa mana yanzu, wata yar fara me ido irinna Aishwarya
Tsaki Haneef yaja, yanzu Kai harka zuba mata ido kagane wanne irin ido ne da ita?
To yarinyar datake min aiki ce kwanaki
OK Wai me hijabi?
Cikin gatse yace a a
Ajmal yace kome gajeren wando? 😳
Shazali cikin fishi yace a a me uwar gajeren wando😃
Ajmal yasake Kallan abokin nasa, qarara yaga kishi a idonsa, toko itace wadda yace masa yanajin faduwar gaban? Wato kawai Daga yabon yarinya Har kishi yakamashi, shikuma Kenan yamutu shida ya rungume masa budurwa? 🤣kenan da shine hauka zaiyi
Shiru sukai ganin anty jiddah tazo, aranta tace dama nasan zaka dawo yaro 🤣
Gaisawa sukai Ajmal sai sunkuyar dakai yake, waishi me suruka
Su Shalele suka futo itada Sajida suka ajiye musu ruwa da lemo, Har qasa ta tsugunna ta gaida su
Sajida ta nemi waje ta zauna, ita Kam hanyar daki ta nufa
Anty jiddah Tace Ina zaki Kuma? Waike bakya gajiya da zaman daki ne?
Baisan dalili ba cikin ransa yace Alhmdlh, jin furucin anty jiddah
Dawowa tayi ta zauna tayi Shiru, hankalinta yana kan TV
Qasa qasa yake kallanta, wallahi sai yau yasake tabbatar wa kansa Cewa yarinyar Nan kama take da yar tsana, wallahi Har gashin 🤣😃🤣
Garin satar kallanta anty jiddah ta kamashi, dasauri yace am anty dama na rako Ajmal ne, shine nace Bari Nima nazo naganki
Aikuwa Gara haka, nasan badan Shiba aida bazaka zoba 🤣
Gudun kada tace masa meyake kallo irin rannan, tasa yaji kunya saiyayi fuska yace anty zamu wuce, sai wani lokacin
Tace to Allah yakiyaye qanina, ka gaida momy nah
Sajida de Saida tabi bayansu suka Dan zanta da Ajmal sannan tadawo gida
Suna tafiya amota Ajmal na kallansa sai fara'ah yake shi kadai, lalle akwai ayar tambaya akan abokinsa
Shikuwa Haneef tunani yake Yaya za'ai yadinga zarya a gidan anty jiddah? Wannan ai saita dauka ma son yarinyar yake, Bayan Kuma shi yasan ba haka bane 🤣
Kawai de yanaso yana ganin yarinyar ne, sha'awa take bashi wallahi Kamar yar baby 🤣
Gaskiya dole ya nemi mafita
Ajmal na sauke shi a gida, Bai wuce part dinsa ba, part din momy yaje, yanaso yayi Mata maganar Amma saiya kasa
Zama yayi suka gaisa sannan tace yaushe zakaje wajan yar qawar tawa ne? Yace gobe zamuje insha Allah
Toshikkenan Allah yakaimu
Tashi yayi, be Iya cemata komai ba, yatafi part dinsa
Har dare de magana tana cinsa Arai, Daga qarshe yaje wajan momy yace momy dama inaso zamuyi magana ne
Tace inajin ka, wacce iri?
Momy Tunda daddy yace bazai sake samomin me aiki ba, kifadawa anty jiddah tadawomin Dame aiki na🤣
Yanzu Kai Alhaji shazali Ina kataba ganin anyi haka? Itama fa Acan din aiki yarinyar take mata
Hade hannayen sa yayi waje daya 🙏🏻 please momy nah
Tace to shknn, tadauki wayarta takira anty jiddah
Bugu daya ta Daga, Bayan sun gaisa momy tace jiddah babu me gyarawa Haneef dakinsa fa yanzu, yakamata ki dawo da yarinyar Nan haka, taci gaba da gyara masa, yaro duk yanata mita anbar masa dakinsa da datti
Anty jiddah najin haka cikin ranta tace wannan ba aikin kowa bane saina Haneef
Shegen yaro ni zaiyi wa wayo? Tanan ya bullomin kenan🤣
Sharhi, comment, share, Dan Allah 🙏🏻
Amnah El Yaqoub ✍🏻
💕SHALELAN BABA💕
(Romance)
Writing by Amnah El
27&28
Amma momy yarinyar nanfa school nakesan maidata tareda Sajida
To yanzu jiddah Tunda shi wanda yayi silar zuwanta yace a dawo masa da ita basai abar magana ta wuce ba ita Kuma yarinya tadawo bakin aikinta
Momy meyasa kikesan biyewa wannan Yaron ne Dan Allah?
Ba biye masa nakeba jiddah kawai quruciya ce take damunsa 🤣
Quruciya de momy, yanzu Haneef dinne me quruciya? Yaron da kuke shirin liqa masa mata biyu
Yanzu de jiddah Kinga babu wani tone tone Dan Allah kihado mata kayanta tadawo gida, sai anjima, qit takashe wayar saboda kada ma anty jiddah tasake Cewa komai
Yanajin Yanda wayar ta qare wani farin ciki ya mamaye Zuciyar sa, yace yawwa momy to yanzu ba shikkenan ba, kema Yan biyunki sun huta
Kallansa tayi, to kaima Kuma Haneef saika kiyaye gaba, banasan wannan kore koren dakake wa masu aiki
"nikwa momy inani Ina korarta? "
Kallan rashin fahimta Tayi masa me kake nufi?
A a momy babu komai, Bari inje daki na huta, sum sum yatashi yayi part dinsa yana gudun karyaci gaba da zama Kuma momy ta harbo jirginsa
Yana Zuwa part dinsa yafada kan gado, ya janyo computer sa yafara aiki cikin kwanciyar hankali, haba ai Gara haka, Gara tadawo insata agaba ina kallanta San Raina, yafi ace kullum Ina zarya a gidan anty, Tunda inada ikon dawo da Mai aikina, (tofa kaga masu yar aiki😃🤣)
********
Sister Kinga wannan brezia din na siyo mana su a school dazu da safe, Kinga wannan babbar zata Miki
Sajida wacce irin brezia Kuma? Kofa candy ba muyi ba
To brezia sai anyi candy ake sakawa? Nikam saka abata zanyi wallahi
Shalele tace a a nikam babu ruwana, bazan sakaba, aisai inji kunya ma, kowa Yana ganinka yasan me kasaka
Au kunya Ko? To shikkenan ai sai ki zauna da Abu turu turu babu Rigarsa
Anty jiddah ta turo kofar Dakin nasu ta shigo, gefen gadon ta nema ta zauna, tace Haneefa kinason Zuwa gidan su momy?
Mama gidan su momy Kuma? Aiken mu zakiyi?
Ba aikenku zanyiba Haneefa, inaso ne kikoma can gaba daya, dazu munyi waya da momy tace Haneef dakinsa yana zama da datti, shikuma Kinga Baisan qazanta, shiyasa tace kikoma
Sajida tace Amma mama karatun dazata fara fa?
Wannan babu damuwa akan haka, zanyi magana da Haneef yasama mata lesson teacher din dazai dinga yimata karatun, kokuma shi yazauna yayi Mata, Bayan wata daya sainayi masa maganar karatun inji Yanda zamuyi dashi
Ahankali Shalele tace Amma mama ni Bansan rabuwa dake
Kiyi hakuri Haneefa Nima akwai dalilin dayasa zan barki kikoma can din, insha Allah zakiga ribar Hakan agaba, yakamata ku kwanta yanzu dare yafara yi
Taja musu kofar tayi dakinta, dalilin dayasa zatabar Shalele tatafi guda daya ne, tanaso yarinyar ta kusanta da Haneef, yakasance a kullum tana kusa dashi, ta hakanne zaisa ta cimma burin ta akansu
Doctor Sulaiman ma dayaji dalilin nata sosai ya gamsu
Wajan sha biyu saura Sajida ta dubi Shalele data fara bacci tafara tashin ta
Cikin magagin bacci tace Sajida lafiya?
Tashi sis magana zamuyi
Haneefa ta tashi zaune, tace meyake faruwa ke baki fara bacci ba?
Sister shawara zan baki, duk lokacin dakika koma gidan momy, kada ki yarda ki nunawa uncle kina sonsa
Kinsan halin maza, idan sukaga mace tana sansu tofa babu zaman lafiya Daga ranar zasu dinga tashin Kai (🤭 nikam ba ruwana Sajida ce tafada)
Sannan koda wasa kada kisa aranki Cewa Wai bazai Iya sanki ba, a kullum anaso Bawa yasa aransa Addu'ar dayake yi ta riga da ta karbu
Kawai kisa aranki uncle nakine ke kadai
Maganar kina sonsa kuwa kiyi biris ki share shi, kiyi Kamar bakisan komai ba
Ajiyar zuciya ta sauke, gaskiya Sajida maganr ki Hakan take, Kuma naji dadin shawarar dakika bani insha Allah zanyi amfani da ita, Amma yanzu please ki kwanta, dare yafara
Sajida tace to shknn gud 9yt, Daga nan sukaja bargonsu suka kwanta
********
Washe gari da safe anty jiddah da Sajida suka tayata tahada kayanta, momy tace ta turo iliya direban yara zaizo ya dauke ta
Iliya dayazo Shima waje yasamu yazauna yana jiransu
Anty jiddah ta dubeta, Haneefa kiyi hakuri kinji, insha Allah zansa Haneef yana kawomin ke da kansa, Sajida ma Ko weekend ne zansa ta dinga Zuwa Miki
idanunta suka cika da qwallah, ni mama banasan rabuwa dake, Dan Allah kice musu nide su barni awajan ki
Haneefa nafada Miki inada dalilin dayasa banyi musu ba akan komawarki gidan, nan gaba kadan zaki gane dalili na, tashi muje iliya tun dazu yana jiranki
Haka suka futo Har wajan motor sa, Suka sake sallama, sannan ta shiga suka tafi, Sajida ta zauna tayi Shiru Kamar marainiya, dama haka ne sabo yanada dadi rabuwa babu dadi
Suna shiga gidan ta harari part din Haneef, aranta tace a kanka gashinan ansa narabu da Sajida ta
Momy da yara Suna falo, huzaifa yana cinyar Samah yanayin game awaya, tayi sallama tashigo gidan
Momy tace sannunki da Zuwa
Ahankali tace Yauwa momy nagode