x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - SHALELAN BABA

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 64847 words

Category: Love Stories

Views 99

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
akwai turawa dasuka turo mana appointment latter daga Singapore 🇸🇬

Karbar takardun yayi yace OK munir zan duba, sannan meeting asanar za'a zauna gobe insha Allah

Yace ok sir sannan yafice daga office din

Saida yaga yaci karfin aiyuka dayawa sannan yatafi gida yamma lis

********

To Bilal kaji abinda ita hajiya ta yanke, nikuma da hankalina da girmana, da matsayina bazan je nayi wannan aika aikarba, dubafa kagani, Yara ma sun sa aransu anzama daya, tunda gashi suna zuwaa Har gida ganin ita haneefa

Mami tace Alhaji bazaka fahinceni bane, bakasan inda magana ta ta dosa bane

Cikin zafi yace aikuwa inde ban Fahimci inda maganar ki ta dosa ba, to bazan fahimta ba kuwa hafsat, nide nafada Miki babu inda zan maida Kaya, saboda me? A wanne dalili? Sunyi laifi anbaku hakuri, yaran nan daga haneef Har haneefa yaranki ne

Bilal yayi murmushi yace Mami kiyi hakuri, tsakanin da kunya ace Ana maida abun Saka Rana, sannan sunasan junansu, kawai ayi musu adduah abarwa Allah komai

Kallansa tayi, Bilal haneefa batasan haneef, jinake a gabanka tace ita batasan shi, to saboda me za'a takurawa yarinya, a Barta tayi karatunta

Alhaji Tahir yace, hafsat anriga angama magana Akan karatun yaran nan, zasuci gaba da zuwa school dinsu, sannan Alhaji bukar yace zai hadata da yaransa su shiga University tare, hafsat me kuma kike buqata Bayan haka?

Tace Shikkenan Alhaji, Amma Bari na Kirata naji ta bakin ta, hankalina zaifi kwanciya

Tatashi taje Har Dakin nasu ta Kirata

Aqasa ta zauna Kanta kasa
Tace Abba gani

Alhaji Tahir yace haneefa, ki fadaamin gaskiya kinason haneef?

Lokaci daya gabanta yafadi

Tace a.. Abba.. Nifa.. Am Nifa Abba Dama abinda yasa nake Sansa saboda yabani kudi ne nakai baba asbiti

Hajiya hafsat da Bilal dabasusan da wannan magar ba sukace kudi kuma? Yaushe ?

Tace akuje

Nan tabasu labarin komai, sannan tace shiyasa nake Sansa amma saisu momy suka Koreni, shine nace nafasa

Ajiyar zuciya Mami tayi, tace tashi kije
Tatashi tatafi, tana tafiya Alhaji Tahir yace to ai kinji, to yanzu hafsat Kodan wannan abun ai Yaron nan yasamu sassauci daga wajanki, ke hafsat karma kiyi masa danki ne ai, Yana fadar haka yayiwa Bilal sallama yakoma ciki 🤣

Saida Bilal yasake Bata hakuri, tanuna masa komai yawuce, sannan su Afrah suka futo suka rakosu wajan Mota zasu tafi

Da Aududu yakoma, Saida yakai su Samah haar gida sannan ya karbi number ta a wajan Safah, data Daddynsu, yaja motarsa yayi gida baiko kalli Samah ba🤣🤣

********

To Alhaji kunje gidan Alhaji Tahir Amma kazo kayi shiru bakace mana komai ba

Daddy yace a a hajiya Kenan
To ansaka ranar yaranki, nanda wata daya biki

Momy tace alhmdlh, Allah nagode maka, yanzu kuma saide in Kira hajiya laraba nabata hakuri Akan hajara

Daddy yace eh yakamata Kam, Shikuma Allah yasawaqe masa
Momy tace amin Alhaji, ai banga tazama ba Bari inje daki indauko wayata inkira jidda da sauran yan'uwa afada musu, tatafi tana Kiran baba Hanne domin tasanar da ita itama

(anty jidda Kam tarigaki ji🤣🤣)

Su Safah ne suka Shigo, daddy yace a a daga Ina kuke?
Samah tace daga gidan anty jiddah

Yace kafin ku shiga kuje kuyimin Kiran yayanku a part dinsa

Suna zuwa suka dawo dashi, daddy yace to Dama magana ce Akan aurenka, dazu munje mun nemama auren haneefa a wajan Alhaji Tahir, kuma anbamu harma ansa Rana nan da wata daya biki, dakuma na Safah da Ameer

Safah najin haka tashige dakinsu da gudu
Wayyo tasan da haka meyasa zataje gidan dazu? 🙆🏻

Haneef yayi murmushi yace to daddy godia nake, Amma daddy ya maganar hairat?

Hairat tunda kace bakaso ai shikkenan, Alhaji shazali ai munfi San lafiyarka Akan jinya, yaqarasa maganar cikin barkwanci 🤣🤣

Sumar kansa yashafa yatashi yatafi cike da farin ciki
Yana fita yakira Ajmal yace kana inane abokina?

Lafiya najika kamar kana cikin farin ciki haneef?

Ai farin cikima daaya Kenan Ajmal, daga yau kawai ka kirani da angon next month

Aaaa haba Dan Allah abokina?

Yace wallahi, Nima yanzu daddy yake fadaamin, Amma fa yarinyar nan sainayi da gaske, wallahi taqi Bude wayarta, gaba daya ta toshe kafar da zan sameta

Ajmal yace, to muje gidan mana mu sameta

OK to kazo kadaukeni mutafi

Sai Bayan sallar magrib sannan Ajmal yazo suka wuce gidan Mami

Suna zuwa, suka zauna afalo, Mami tana ganinsu tace a a su haneef ne a gidan Namu, sannu ku da zuwa, Alhaji Tahir yadawo daga masallaci Shima suka gaisa sannan yayi ciki yanayiwa hafsat kallan maganin ki kenan🤣🤣tunda gashi anfara Mata sintiri agida, baga Mata ba, baga maza ba🤣🤣

Mami ta kallesu tayi hamdala da yaran Nata basa falo, tace haneef saide fa kuyi hakuri, mutuniyar Taku yanzun nan suka fita, sunje zasusha ice cream sudawo, yanzunnan suka fita, da kunzo kafin minti biyar ma Dakun samesu 🤣😲🤭🤣

Kansa yadafe🤦🏻‍♂, to Mami idan nakirata wayarta a kashe, kuma taqi nemana, Mami metake so namata ne?

Kayya shirman haneefa ne kawai🤣🤣, idan ta dawo saina fadamata kunzo

No Mami zan jirata

Dasauri tace a a haneef, kada kuzauna Kuma su Bata muku lokaci, zansata takiraka idan sun dawo, yace toshikknn Mami, mu zamu wuce

Tace to ku gaida Hajiyan🤣

********

Washe Gari momy takira Mami Akan kayan lefen Yara, tace hajiya hafsat Yaya kike ganin za'a tsara kayan nasu?

Mami tace hajiya ai kece babba, duk yanda kikace, Yara ai duk na kine

Momy Taji dadin furucin hajiya hafsat tace to nida cewa nayi haneefa sutafi da jidda da haneef saisu siyo abinda takeso da Kanta

Ita Kuma Safah saisu wuce da ameer da Afrah

Mami tace eh hakanma yayi, babu damuwa, abinda basu siyoba sai ayi ordering nasa, momy tace to shikkenan wannan de duk maganar mu ce, bamusan Yaya su alhajin zasuceba, duk de yanda Kuka yanke keda Alhaji Tahir din naji, Nima nan idan Alhaji yadawo saina fada masa naji yanda zaice

Dahaka sukayi sallama

********

Da yamma Yana dawowa daga wajan aiki yayi wanka, yashirya cikin Qananun Kaya, meeting suka Gama Yagaji Sosai, key din motarsa yadauka ko abinci baici ba yayiwa momy sallama yatafi gidan hajiya hafsat🤣

Yaarasa gane maganar wa zai yarda da ita acikinsu? Ita Afrah ranar dasuka zo, tace zata yi Mata magana ta Bude wayar, ita Mami jiya tace dasun dawo zata sata ta kirashi, Yana tunanin akwai abinda Mami take boye masa, to Gara yaje wajanta Kai tsaye yaji dalilin wannan shariyar, yafi sauqi, yau Kam inta kama ko kwanane saiyayi a gidan Mami, Amma bazai taho ba saiya ganta, 🤣🤣

Yana zuwa kuwa yayi parking yashiga falon, Mami na zaune cikin ranta tace yau Naga idi🤣🤣

Tace sannu da zuwa haneef, Bari nakawoma ruwa, tashige kitchen tana tunanin irin dabarar dazata masa yau 🤣

Yana ganin shigarta kitchen yatashi yayi wuf yashige dakinsu Afrah

Suna zaune suna karatu itada Afrah sai ganinsa sukai yashigo Dakin da sallama
Afrah tace Yaya Ina yini

Ya kalleta yace lafiya qanwata

Mami na futowa daga kitchen hannun ta daukeda ruwa da just taga falon Wayam babu kowa🤣

Ta tsaya, to Ina Yaron nan yatafi daga shigarta kitchen?

Adede lokacin Afrah tafuto daga Dakin nasu danta basu waje

Mami tace ke kokinga haneef anan yanzu?

Afrah tace Yaya haneef ai yanzu yashiga dakinmu🤣

Dakin ku?

Afrah tace eh Mami, meyafaru?

Ruwan hannun ta ta ajiye tanufi hanyar dakin🤣🤣

Afrah ta riqe ta Mami Ina Zaki?

Kallanta tayi Afrah Zaki sakeni kokuwa?

Afrah tace, Haba Mami Dan Allah karki shiga🙆🏻

Sharhi
Comment
Share

Dan Allah🙏🏻

Mrs Usman Ce✍🏻💕SHALELAN BABA💕
(Romance)

Writing by Amnah El Yaqoub



45&46


Bazade ki sakeniba ko Afrah

To yanzu Mami in kinshiga me zakiyi? Haba Mami Yaya haneef nefa? Dan Allah ki zauna

Zama tayi Akan kujera tace to Afrah bari nazauna Naga da idon dazai futo ya kalleni
Uwa tana zaune kashiga Dakin yarta

Mami ai Shima danki ne, duk daya suke a wajanki

Mami de batace Mata komai ba

********

Saida ya qare Mata kallo, Yana tsaye, uniform ne ajikinta da alama daga school tadawo
Kanta babu dankwali Amma akwai kitso manya, sai littattafai dasuke gabanta
Ita Kanta taji kunyar ganinsa, saboda tasan tayi masa laifi, but mazan ne Sai ka Dan gwarasu wani lokacin za'a daidai ta duk da kana sonsu, Hakan bazaisa ka zaqe ba

Dasauri taja dankwalin ta tarufe Kan, tace uncle sannu da zuwa

Ajiyar zuciya yasauke, yatako yazo gar gaban gadon ya zauna daga gefe
Yazuba Mata ido

Kallansa ta sakeyi, tace uncle Ina yini

"meyasa kikeson kasheni? Why?

Uncle kisa.. 🤭

Yes, gashi kin hanani ganinki, kin kashe waya, bakya nemana, ke ko ajikinki, jiya munzo kunfita kuma dakuka dawo baki nemeniba, kuma Saida nace zan jiraki Mami tace Baku Dade da fitaba

Shiru tayi tana tunani, unguwa kuma? Itade tasan suna gida, to may be Mami ce tafada masa haka🤣

Kanta ta sunkunyar qasa tace kayi hakuri

Baice Mata komai ba yatashi daga inda yake yadawo gabanta ya tsugunna daga kasan gadon, hannayensa duka biyu suna zube Akan gadon

Yayi qasa da murya yace ba hakuri Zaki banida, ni bakimin laifi ba, kuma nasan bazakimin insha Allah, kawai nide ki Bude wayarki, rashin Jin muryar ki zai haddasa min damuwa fa, yanzu ma kinsa duk na kasa aiki a office, duk kinbi kin susutani
Kinshiga cikin zuciya ta kin zauna haneefa, bazan Iya rayuwa batare dake ba

Wata irin kunya ce ta kamata, Wai yau haneef ne a tsugunne a gabanta Yana fada Mata wannan kalaman, tasa hannun ta tarufe idonta 🙈sannan tace Kai uncle please nide katashi

Dogayen yatsun hannunta ya kalla, a hankali yasaka hannu yajanyesu daga Fuskarta

Yariqe hannun cikin nasa, sannan yatashi ya zauna dab da ita, ya kalli takardun gabanta yace meyasa kikamin wannan abubuwan?

Uncle karatu ne yasa, kayi hakuri

Saida yadan murza hannunta sannan cikin sigar rada yace to zakiga Bude wayar?

Wani iri takeji ajikinta, dazai gane daya sakar Mata hannu,ahankali tace eh

Kinyi alqawari?

Nayi uncle

Littafi daya yaja Gabansa , still hannunsu na sarqe Dana juna

Ya kalleta kina gane karatun?

Ta gyada masa Kai, Ina ganewa abinda ban ganeba Afrah tanamin bayani
Yanzu ma itace take sakemin

Ok inci gaba dayi Miki?

Tace eh, sannan tafara zare hannunta daga nashi

Yanajin abinda take yasake riqe hannun, hannun Nata very soft, Shiyasa yakejin dadin riqewa
Karatun yafara yimata, yanayi Yana murza hannunta, hannunsa na yawo acikin tafin hannunta

Kanta a sunkuye takasa Kallansa, shikuwa duk bayanin da zai Mata idonsa akanta yake, basuyi da yawa ba ta dauke littafin tace uncle ya Isa, tayi hakane hakane danta qwace hannun ta, taga alama bazai gane irin yanayin datakeji ba, wani iri haka duk ba dadi

Kallanta yayi yasaki murmushi, yace Toni bai isheniba, yakai hannunta bakinsa ya lumshe idonsa, sannan yasakarwa hannun Nata wani irin zazzafan kiss

Sannan yasaki hannun, ya gyara zama Sosai, Yana fuskantarta, yasaka littafin atsakaninsu, sannan yayi gyaran murya yabude muryar sa Sosai yafara yimata karatun dalla dalla 🤣

Cikin ranta tace Dama da niyya Kenan

Mami afalo taji shiru, tace um Afrah bakida hankali ke yarinya ce, Bari kiga na dubo yaran nan🤣

Afrah na chting a wayarta, ta girgiza Kanta kawai batare datace komai ba

Mami na zuwa tagansu a zaune a gadon, ga littafi atsakaninsu Yana yi Mata karatu 🤣

Tace a a haneef ashe karatu kuke?

Saida yadan Sosa kansa sannan yace wallahi Mami Ina tayata ne

Har cikin ranta taji dadi, haka kuma lokaci daya tasaki sisiyar ajiyar zuciya 🤣tace to idan kungama haneefa kizo ki hada masa abinci

Tace to Mami

Sannan tajuya tafita, Bata zauna afalon Bama tawuce dakinta
Afrah ta bita da kallo tana daria

Sai wajan biyar da wani Abu suka Gama karatun, tagane Sosai yanda batayi zato ba, tashi tayi ta ajiye book din yabi bayanta da kallo, wannan yarinyar ai dole ma tayi nauyi irin wannan uban hips din Nata 🤣

Ita kuwa Batasanma yanayiba, ajiyewa tayi tace muje uncle, nazubama abinci

Da lumsassan idonsa ya kalleta, saide kiyimin kunun gyada idan kin Iya

Laaa uncle na Iya mana

Um um fa kada kije ki qone, Mami takamani

Murmushi tayi masa tace Bari inje inyi maka, tayi gaba, Dasauri yasa hannu yariqo Nata, sannan yace muje

Ta Kalle shi, uncle agidan Mami muke fa

Saida yadafe kansa 🤦🏻‍♂sannan yasaki hannun, yace sorry muje

Falo suka futo, shiya zauna Yana canja Channel din kallo zuwa labarai
Ita Kuma taja Afrah suka shiga kitchen

Suna aikinsu suna fira, Afrah tace nikam Yaya haneef soyaiyarsa taana birgeni, babu ruwansa dawani boye boye, kinsan Mami fa Nina hanata shiga dazu🤣wallahi cewa tayi saita shiga

Shalele tace Mami na Kenan, aigara tazo tasani ko yankewa yarta Kai zaiyi?

Dukansu sukayi daria, Har suka kammala sannan suka kawo masa, Har qasa ta tsugunna tazuba masa, ta kalleshi to uncle gashi

"bazaki Bani ba?"

Murmushi tayi tatashi tabar wajan, Afrah na kallan su daga gefe, kome yace Mata? Shide komai nasa a hankali cikin sigar rada, inba kana kusa dashiba, ba lalle bane kaji meyace

Cikin nutsuwa yakeshan a binsa, saiyaaji kamar baba Hanne ce taayi

(renon baba hannen cede🤣🤣🤣)

Shi Yana gefe Yana shan kununsa Yana kallo itada Afrah suna gefe a zaune, Har aka Kira sallar magrib, yaje yayi sallah yadawo, ya kalli Afrah qanwata ku shirya mana muje ku rakani unguwa

Afrah Dama Zaman ya isheta, kullum mutum Yana gida ba yawo tace to Yaya, sukayi daki suka shirya cikin sauri, Dakin Mami sukaje sukayi Mata sallama sukai fice, afraah na baya, su kuma suna gaba

Har yakaisu wajan shan ice-cream, su kasha, ya lodo musu wani, Yana ganinsu sau murna suke, Shide kawai kallan su yake, yarintama da dadi take 🤣🤣daga zuwa wannan wajan shine abin murna, sude Yara kullum basa gajiya da Abu, inba hakaba jiya jiyan nanfa sukazo🤣🤭

Daga nan sukaje yasiya musu shawarma dasu boga sannan suka tafi gida, a harabar gidan ya ya tsaya, Afrah ta kwashe musu kayan tayi cikin gida, Shikuma ya dubeta yace kada ki manta fa, kibude wayarki

Saida ta sunkuyar da Kanta qasa sannan tace to uncle insha Allah
Saida safe

No bawani Saida safe, first kifadamin maganar dazanji dadinta sannan kitafi

Cikin shagwaba tace to uncle ni mezance

Wani irin yanayi yashiga sakamakon wannan shagwabar data masa, Har baisan lokacin daya kwanta da kansa a jikin seat dinba

Yace ko Maima kice

Shiru tayi, can de tace masa I luv you uncle, thnks you for everything Tabude motar tafice da gudu, murmushi yayi, sannan yaja yarufe yayi gida, Yana hanya saiyaaji kamar ansauke masa wani nauyi a kansa


********

Washe Gari takama weekend, Mami takira Dr Bilal yazo Har gida, suka dunguma gaba dayansu suka tafi kuje, suna tafiya ahanya sunata fira abin gwanin birgewa Mami da shalele da Afrah Abaya sai Aududu dake cinyar Mami, Shikuma Dr Bilal suna gaba shida ameer

Basu tsaya ko'inaba saide kofar gidansu shalele

Ta kalli gidan, aduk lokacin data zo kuje babu mutumin dayake fado Mata irin baba
Rayuwarfa Kenan, Har anzo anyi antafi

Suna futowa sukaga gidan akulle
Basu tsayaba suka shiga gidan baba malam, Inna sabuwa tana Daka sai ganin baqi tayi

Da gudu taje ta rarumi shalele tace, shalelan baba? Wai kuwa kenake gani?

Shalele taayi murmushi tace nice Inna

Inna sabuwa tabisu Mami da kallo tace wannan ai hajiya ce dasukazo kwanaki, sannunku da zuwa

Tashinfida musu tabarma, suka zazzauna, aka sake gaisawa, sannan tace gashi kunzo malam baya nan yatafi kewaya, Amma bar atura yaro yakirashi

Nan da nan tatura danta yatafi Kiran baba malam, shalele tace Inna sabuwa baki gane wannan bane? Tanuna Mata Aududu

Inna sabuwa ta kalleshi tayi shiru, shalele tayi daria Inna Aududu nefa

Laaa Wai Aududu ne ya girma haka? Kekiga yaro yayi bulbul jajir dashi Dan Allah 🤣🤣

Duk saita Bawa su Mami daria

Tace hajiya ai ba abin daria bane, yaro duk ya sauya kamanni, tatashi tafice saigata yadawo da ruwa pure water 💦me sanyi

Dukansu kuwa suka Sha, akaci gaba da fira, malam yahai na zuwa yace a a a a kice yau shalelan baba ce dakanta, Dukansu Saida yabasu daria

Mami tace Dama haka kuke fada Mata ne?

Baba malam yace ai hajiya Kowama anan Garin shalelan baba yake cemata, saide Yan makarantar su ne suke kiranta da haneefa

Amma kinga malam surajo, tunda nake dashi zaiyi wahala kiji yace haneefa, saide yace Shalele nah, komai de Shalele nah

Lokaci daya qwalla tacika idonta, tace hakane kam baba malam, ni tunda nake da baba ma bantaba ji yakira sunana ba, saina ranar dazai rasu
Tana fadar haka tafashe da Kuka
Gaba dayansu jikinsu yayi sanyi, barinma Bilal da agabansa akai komai, shi kansa yaji mutuwar mutumin, suna wannan halin shiyasa a lokacin yayi mamakin Ina shalele tasamu wannan kudin aikin da akayiwa babanta, yaga alokcin Yana fada babu ko dar tace zataje tabiya, ashe Shikuma wannan ta dalilin haneef tasamu, Dama can Allah yariga daya tsara komai, Shiyasa ya aiko Mata shi a lokacin daya dace kuma akayi sa'ah ya temakesu Akan kudin

Allah yajikaan malam surajo

Baba malam yashare qwallarsa yace naje wajan liman nayi masa magana Akan gidanku da kuma gonakin malam surajo, akwai gonakinsa na shinkafa guda biyu saiwata gonar dayake shuka ayaba, dakuma wasu guda biyu dayake shuka kayan gwari aciki saikuma fili guda daya, sai kuma Yan kudadensa dasuke wajena gaba dayansu, ansanar aagari idan akwai Wanda yake binsa bashi to yazo yasameni yayimin bayanin komai, to Alhmdlh babu kowa, ko mutum daya babu


Saikuma amfanin gonarsa yafuto ancire, nakaishi kasuwa ansiyar, Shima duka kudin Yana nan a ajiye
Liman yace nabar takardun a hannu na idan kika zo sai ahada da kudin Araba muku keda dan'uwanki Aududu

Jin wannan bayanin na baba malam saiya Sakata Kuka riris, shi kansa baba malam din hawaye yake, sai sharewa yake da babbar rigar jikinsa

Afrah Kam tuni takasa tsaida hawayen ta, Kai Allah yaqarawa iyayenmu lafiya da nisan kwana, ta tausayawa shalele, haqiqa taga rayuwa, itadin abar atausayawa ce

Mami ce tayi karfin hali tace malam yahai ai baza'ai hakaba, Har gobe Kai ubane a wajan haneefa, kunyi zama na Amana atsakaninku, babu maganar Rabe Rabe anan, haneefa de macece, kuma duk Daren dadewa gidan wani zata, kuma abune dayake a baiyane duka dukiyar za'a Raba gida uku, shi Abdallah yadauki kaso biyu ita Kuma tadauki daya, kamar yanda ubangiji yafada acikin aqur'ani, cikin suratul nisa'i ayata goma, saboda haka Kaci gaba da amfani da gonakin nasu, Har Allah yaraya Abdallah saiya riqe musu gaba daya shida yar'uwarsa, duk da tafishi shekaru shi namiji ne, zuwa gaba shine zai jagoranci rayuwarta, batada kamarsa, Shima haka

Maganar kudi kuma kasa ayi bohol dashi a makaranta, kokuma acikin masallaci al'umar annabi sudinga diban ruwa, Duk Wanda yayi amfani da ruwan Allah yakai ladan kabarin malam surajo

Gaba dayansu suka amsa da ameen, baba malam yace hajiya ai duk da haka kudin sunada yawa

Tace karka damu malam yahai, kasa ayi bohol
End Ads