Alhaji Tahir yace saide kuma wani hanzari ba gudu ba kasan yarinyar tana ma karanta a yanzu
Daddy yace a a wannan ai ba abin damuwa bane, Nima yaran wajena University suke shirin tafiya, kaga kowa sai tayi karatunta a Dakin mijinta
Nan da nan kuwa kowa yayarda da wannan hukunci na daddy, aka sake gaisawa sannan suka tafiya gida domin yasanar wa dasu momy hukuncin dasuka yanke
Shima Alhaji Tahir yashiga gida domin sanarwa da hajiya hafsat abinda yake faruwa, yashiga gidan da goron sa da alawa nasaka Rana
(kuyi hakuri da wannan Banda chrgi ne wallahi ngd🙏🏻)
Sharhi, comment, share to others groups Dan Allah 🙏🏻
Amnah El ✍🏻💕SHALELAN BABA💕
(Romance)
Writing by Amnah El yaqoub
41&42
Yau gidan anty jiddah anyi baqi, yanbiyu sunzo sai fira suke da sajida, kasancewar ba zuwa suke Sosai ba, sai zuwan nasu yayi Mata dadi
Anty jidda na waya da mijinta adaki, Bayan sun Gama takira Bilal
Tace doctor Har yanzu Baka zoba Akan maganar danace zamuyi shekaran jiya
Jiya kuma bakabimu gidan momy ba daga asbiti saika wuce wajan aiki
Yana shiga cikin falon yaganta a harde akujera, cikin fara'ah ya Bata goro da alawar hannunsa yace hafsat riqe wannan
Tasa hannu ta karba tana binsa da kallan mamaki
Na menene wannan Alhaji?
Nasaka ranar yayanki ne, ameer da haneefa, nanda wata daya insha Allah za'a daura musu aure, saiki fara shirye shirye
Wanne irin aure Kuma Alhaji? Yarinyar Dana maidata makaranta?
Ita hajiya Amina Aina fada Mata namaida yata makaranta abinda suka kasa yimata
Kwana da kwanaki tana zaune agidansu, amatsayin me aiki, sun zaunar da ita tana musu bauta, sannan ni da take musu aikinma bantaji haneefa tacemin tana karbar kudinsu ba, saide faman wahala datasha
Tsakani da Allah abban Afrah, gida de kamar gidan Alhaji bukar tayaya zasubar ma'aikatansu batare dasun sakasu a makaranta ba, aiko yar islamiya ce sa sakasu aciki
Kuma haka kawai saboda rashin adalci dason Kai irinnasu suzo dawata magana ta aure?
OK sai yanzu ma nagane, saboda dansu Yana kwanciya jinya saboda ita, shine za'a katsewa yarinya karatunta ace za'a Mata aure, bazai iyuba
Ajiyar zuciya yasaki, to yanzu hafsat me kike so ayi?
Kaje kafada musu cewa ni nan, nace bazan Bawa dansu auren yata ba, ai itama tanada gata ba marar galihu bace, shide ameer din tunda namiji ne kuje kuyi masa, Amma Banda haneefa
Yanzu ni din kike so naje nasamu shi Alhaji bukar da wannan maganar?
Cikin fishi taace toshi kuwa yazo yasameka da ita? Qarewa mafa Yaron nan zuwa yayi yadauki haneefa yafita qasar waje da ita, yarinyar Bata nuna masa korafin komaiba, sannan Bata samu iyayensa tafada musu maganar ba
Saikace wata marar gata, wallahi baban Afrah ko ameer dinane yadauki haneefa suka fita wani waje batare da sanina ba dole zan hukuntashi Akan haka
Idan yarinya bame kamun Kai bace wayasan mezai faru?saboda kawai suna taqamar cewa ita yar aikin su ce? Shin masu aiki basuda iyaye ne? Kokuma idan andaukesu aiki Hakan Yana nufin za'a iyayin komai dasu?
Kuma still yanzu azo ace Wai anbada ita, saboda me? Bazai iyu Bama Alhaji, kamaida musu kayansu, ta watsar da goron aqasa 🙆🏻😭
Hannayenta yakama yace hafsat, kiyi hakuri, nasan Yaron nan da iyayensa sunyi Mata laifi, kuma sunzo Har gida sun Bata hakuri kema kuma sunbaki, sannan sun sake neman yafiyarku
Kisani Allah mafa muna masa laifi kuma yayafe mana
Bare mu Yan Adam, yanzu hafsat idan kikace nakoma namaida musu kayan Saka ranarsu, mekike tunanin zai faru? Kina nufin suma zasu Bawa danmu ameer yarsu ne?
Hafsat bazasu bashi ba, saboda muma mun hanasu tamu yar
Alhaji Dan Allah kadenamin maganar wannan marar mutuncin Yaron 🤣🤣tatashi fuuuu tayi dakinta, Alhaji Tahir ya girgiza kansa sannan ya tsugunna yasaka hannu ya tsince goron da alawar
Cikin ransa Yana cewa nide bazance komaiba kiji babu dadi kice nayiwa Dan yar'uwarki maganar daba daidai ba🤣🤣🤣
********
Yana zuwa yadanna door bell, Sajida tatashi tabude, tana ganinsa tasaki murmushi laaa uncle ashe Kaine, sannu da zuwa
Ashe yau da babban baqo kazo mana, kawoshi, ta meqa hannu takarbi Aududu dake hannunsa
Tajuya tana cewa Bari nakira mama
Yace to Sajida, Yana qarasowa cikin falon
Akujera ya zauna, Safah takalleshi tace uncle sannu da zuwa Ina yini?
Cikin fara'ah yace Lfya Alhmdlh, Yaya school
Laaa uncle ai munyi candy
Yace to masha Allah, kice yanzu sai University
Kafin Safah tasake magana
Samah tace masa Ina yini, batare data kalli inda yake ba
Shima Yace lafiya ataqaice,🤣 wato wannan yarinyar shi zata gaisar asheqale ko,yagama lura bataso ma ta kalleshi, to menene da jikin nasa daza'a qi Kallansa?
Itama anata bangaren takaici ne yakamata, ita bazai tambayata ko Yaya gida ba? Batakai ba Kenan
Safah na kallan su tana Daria cikin ranta
Tasake dubansa tace uncle ashe kaima kana zuwa gidan anty jiddah
Ina zuwa mana, tunda yata tana gidan ai dole nazo
Daria tayi tasake cewa to ai yanzu Bata nan uncle, ko wajan wata kazo🤣🤣
Dasauri yace no, no, nazo wajan antynku ne, daganan kuma zan wuce wajan haneefa
Aikuwa uncle muma saimu bika muje muganta, rabonmu da ita tun shekaran jiya
No kusa driver yakaiku, bancika son damuwa ba wani lokacin 🤣
Haba uncle wacce irin damuwa kuma Ana zaune lafiya?
Kema de da shegiyar jaraba kike wallahi Safah, Ana yageki kina qara liqewa a'inda bakida kwarjini, cewar Samah 🤣🤣
Cikin fishi Shima ya kalli Samah din yace ke wato bakida kunya ko? Ba'a Isa dake ba, ba'a Isa asaki bako?
Dede lokacin anty jidda tazo tatarar da wannan rikicin nasu, Safah kuwa Daria kamar me, in Banda Abu irinna uncle Bilal meya Saka Samah din taqi yi? 🤣🤣
Harda cewa ba'a Isa asata tayi ba🤣🤣
Anty jidda tace sannu da zuwa babban doctor
Yawwa anty
(mamaki yakamata, yau Bilal dinne yace Mata anty🤭to inajin de da biyu🤣)
Ta Kalle su tace kutashi kukoma daki, zanyi magana dashi
Safah tace anty, sannan ta kalli Bilal tace uncle inkun Gama ka tabomu saimu wuce
Suna tafiya anty jidda tace Dr Dama zan Baka hakuri ne Akan komawar haneefa gidanmu, banyi Hakan dawata manufa ba, saide Inada babban dalili na nayin Hakan
Dr haneefa itace tafara son haneef, naji hakaanne lokacin dasuke fira itada sajidata
Nan ta bashi labarin komai
Sannan taci gaba da fadin nabarta Takoma can dinne saboda shaquwa tashiga tsakaninta da haneef Har Shima yasota, saboda a lokacin anriga da anyi masa Matan dazai aura
Kuma sai gashi alhmdlh yafara yimata sonda ita Kanta tasan Bata sonsa Har haka, likita cewa yayi zuciyar sa zata Iya samun matsala idan ba'a bashi abinda yake soba
Bilal tace subhanallah
Anty jidda tace to wannan ne dalili na, Amma ban karya alqawarin Dana dauka maba kayi hakuri
Aikomai yawuce anty, tunda anriga da ansa musu Rana ma
Rana kuma Dr? Yaushe?
Yace a a Wai baki saniba? Dazu fa su Alhaji Tahir suka kirani Wai naje manema auren haneefa sunzo
Ai anma Saka Rana nanda wata daya biki, itada ameer da Safah
Yanzu hakama zuwa zanyi gidan inji menene za'a fara shiryawa
Cikin mamaki tace to aikuwa su momy basu fada ba, kuma da alama ma yanbiyu basu saniba
Yace ansaka wallahi, inajin mu kadai ne iyaye muka sani🤣🤣
Tace a a doctor muma ai iyayene🤣
Yace to anty Bari natafi
Kituromin wadannan yaran
Tace to
Tana zuwa Dakin tace yanbiyu tahowarku kuwa daddy Yana gida?
Samah tace a a gaskiya yafita
Tace to kuje Dr Yana jiranku awaje
Duk suka futo, sajida da Samah Da Safah
Suna zuwa wajan motarsa sukaga Yana waya, aikuwa suka Bude suka shiga baya Dukansu, Aududu Yana hannun Samah
Yana Gama waya, yashiga yatada motar, yajuya ya kallesu, waiku driver Kuka samu kome? Duk kun shige baya 🤣🤣
Yakalli Samah data riqe Aududu, yayi tunanin Safah ce, saboda yasan cewa Samah bazata karbi dansaba, dan haka tunanin sa yabashi Safah ce yace, Shiyasa nace Miki banason damuwa😣
Cikin fishi ta kalli sajida da Safah tace Aidama Saida nace muku karmu shiga karmu shiga Kuka nace, aiga irinta nan
Tabude murfin motar tafice ko rufewa batayi ba
Owk Dama kece? Cewar Bilal
Sajida da Safah suka kama Daria qasa qasa
Sukaja murfin suka rufe
Ita kuwa tana tsaye, yaleqo ta window yace idan bazaki shigo ba kifadama na muwuce
Wannan page din nakune masoyan wannan littafi, nabaku shi kyauta🤗
Masu sharhi wallahi kunfi kowa birgeni, dan Allah adinga sharhi tahanake zanji dadi Har insamu qwarin gwiwar yin wani typing din 😊, sharhi Yana temaka wa Sosai, Amma wasu basayi saide acema tnx, wasu kuma suce godia, Wanda sukafi Bani Daria ma sune masu cewa t, Wai t , nide dakacemin t Har gara kacemin sannu wance😃😃, nasan ka kulani
Posting din yau zakuga baida yawa wallahi zazzabi nake, tun Daren jiya, dan yau banmayi tunanin zanyi posting ba, to Amma nasan za'a jirani, ajini shiru, Shiyasa nace bari naayi ko yayane yafi ace anji shiru din, babu sanarwa
Koda ace kunjini shiru to wallahi zazzabi ne yahanani typing, idan kuma kunjini shikkenan Dama haka akeso, gani nande under probability
Ngd Sosai 🙏🏻
Amnah Muhammad El yaqoub✍🏻💕SHALELAN BABA💕
(Romance)
D prince Abba
Princessiko
Maman maama
Samira Aliyu
Nawara Ahmad
Maman Ja'afar
Maman mee'ad
Fatima salihu
Maman Yasmeen
Samira Yahya(gaisuwarki tana samuna)
Ummu farouq
Kai bazaku lissafu ba, Amma Sarai nasan kowa😃🤣Har masu cewa T, nagode Sosai da yanda kuke bibiyata, dakuma Jin lafiya ta, Alhmdlh nagode da addu'arku agareni dukanku masoyana baki daya, zamu Dora daga inda muka tsaya🤗🤗
43&44
Zuba Mata ido yayi, ta kalleshi da tsananin mamaki a Fuskarta
Malam lafiya zaka rufeni amota?
Yaushe zakiyi aure?
Abazata maganar tasa tazo Mata, aure Kuma? Ta kalleshi, menene hadinka da aure na?
Meyasa ne ke kincika rashin kunya da yawa?
Tambayarki nayi, saiki amsa min
Dan Allah kabudemin kofa na fita, wannan wacce irin tambaya ce ta qwa qwa? Tambayar yaushe zaka mutu na auri maatar ka? Dan kaga budemin infice, inba hakaba...
Katseta yayi inba hakaba me?
Nide kawai abudemin kofa
zaki aureni? Yasake jifanta da wata Tambayar
Kallansa tayi ido cikin ido tace Aure de? Ni in aureka? Allah yasawaqe ko maza sunkare 🤣budemin kofa nafita Malam
Aikuwa aure dole, da kinqi da kinso saikin aureni, a Hakan kuma mazan basu qare dinba kinaji kina gani dolen dolenki ki zama tawa
Batace masa komai ba tafara kici kicin Bude kofar saide abin takaicin yaqara Bude Mata
Kanta tadafe 🤦🏻♀sai hawaye, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, yace sorry, yamiqa Mata hannu yace Bani Abdallah na saina Bude Miki kifice
Tayi banza ta kyaleshi🤣
Yace, kibanishi mana, tasake shareshi, yasaka hannu zai daukeshi da kansa, Tariqe Yaron gam 🤣
Cikin fada yasake cewa nace kibani shi nabude Miki kifice kinqi Bani, kinzo kin tisani agaba kinamin ihu, mekikeso namiki? Yamaida hannu Kan Aududu Yana kokarin daukeshi
Itama tafara kici kicin rikeshi 🤣, Garin kokarin qwatar yaro hannunsu ya sarke da juna, lokaci daya wani irin shock ya kamasu, cikin sauri kowa ya janye hannunsa
Ta Dora Kanta a jikin Aududu tasaki Kuka, wallahi ka budemin
Yaya zaiyi? Yahadu da wadda tafishi masifa 🤣ai dole yabude
Bude Mata yayi, tasa kafa kuwa tafice da d'an ahannunta 🤣
Ajiyar zuciya yasauke yabisu da kallo cike da birgewa, kuma wallahi saita aure shi, azuba agani🤣
********
Suna shiga falon sai Mami suka gani ita kadai, cikin fara'ah ta kallesu tace a a yau yanbiyu ne a gidan Namu? To wacece ne acikin ku Samah ce ko Safah? 🤣
A a, sajida sannunku da zuwa, ta kalli Safah, kuma ke Banda abinki sai kiyi shiru🤣, aini ba sirikarki bace maminki ce, taso kidawo nan ki zauna, ta nuna Mata waje kusa da ita
Cikin kunya ta girgiza Kanta, murmushi Mami tayi tace tokushiga Dakin nasu, suma su Haneefan suna ciki
Sajida tace to Mami, suka miqe sukayi ciki
Mami tabi Safah da kallo, ita kunya ameer kunya, ko Yaya za'ai wannan Zaman aure 🤣🤣
Samah ce tashigo da yaro ahannu, mami ta kalleta taga alamun kamar tayi Kuka, ga kuma yaro a hannun ta, Amma Sai tayi shiru, Har qasa itama ta gaisheta cikin fara'ah Mami tace Samah sannunku da zuwa, wannan din Yaron Waye ahannunki?
Bilal ne yayi sallama yashigo, ta kalleshi, anan Mami tagane Kenan Dan nasane, Samah tatashi tayi hanyar Dakin da batasan ma ko shine nasu haneefa ba, sai tayi dace shine 🤣
Mami tace a a likita bokan turai, Saida yashafa sumar kansa yagaishe ta cikin murmushi
Tace lafiya kalau muke baban haneefa, Ina kasamo mana yaro ne?
Ina Tambayar Samah Naga tana kallonka, ga idonta kamar tayi Kuka
Mami Abdallah nefa, qanin haneefa, nakawo Mata shine, rannan munyi magana da ita tace tana so naganshi, nakawo Mata shi, shine Samah ta karbeshi
Kuka kuma saboda nace ta aure nine, shine take Kuka, waai ko maza sun kare🤣
Murmushi Mami tayi, Kai Bilal wannan fadan naku babu ruwana aciki, yafi karfina😃
Tatashi tsaye Bari naturo Maka abban afran Yana ciki
Shima yabita cikin murmushi yace to Mami
********
Tana shiga Dakin duk suka bita da kallo, sajida tace kaga masoya
Ku futowarku daban ce
Qyaleta tayi tanemi waje a gefen gadon ta zauna, ta ajiye Abdallah, shalele tasa hannu ta daukeshi cikin murna, ya kalleta yaga baisan taba aikuwa yafara Kuka
Takalli Afrah tace Kai kiga Yaron nan Afrah nizaiwa qiwa, Afrah tace ato Ina yasanki
Sajida tace wallah muma bai sanmu ba, Amma damuka daukeshi baiyi Kuka ba
Shalele tace aikuwa wallahi saide kayi, saina daukeka🤣
Yaro kuwa yasaki Kuka
Ta Kalle shi tace Kai Aududu, tsabar rashin m karasa wa zakayiwa qiwa saini?🤣
Afraah tace Dan Allah ki ajiye Yaro yaje gun Wanda yakeso anan,kawai kin matsa masa
Sajida tace kawoshi, takarbeshi, aikuwa yayi shiru, suna zaune Yana hannun sajida saiya koma wajan Samah, Kodan yaga ita tashigo dashi ne oho
Ita Kuma tana cike cike da haushin Bilal, kuma tashigo ma ba Wanda ya kulata🤣, saita shareshi, kawai tasaka Kanta acinya tasa musu kuka
Kunsan Yaro, idan yaga babba Yana Kuka Shima kukan yake, dan haka Shima Aududu yasaka Kuka
Duk suka juya suna kallan su, Safah tace a a me aka musu ne, dagake Har Yaro kuna Kuka
Afrah tace Samah meyake faruwa?
Tayi musu shiru
Shalele tace Samah kode keda uncle Bilal ne?
Duk tayi shiru ta Qyalesu
Safah na ganin haka tafara hawaye, tace Samah Wai miye na kukan,? Wallahi idan baki daina kukan nanba Nima bazan Dena ba, ai kinsan de abinda Hakan yake jawo mana
Sajida tayi murmushi tace um yau munga Yan biyu🤣🤣, wato muda ba Yan biyu ba, mune kukan baya jamana komai 🤣
Afrah tace sajida Dama haka suke?
Haka suke wallahi, daya na Kuka yanzu dayar ma zata fara koba dalili, aide yanzu kingani, tunda bataji komai ba tahau kukan itama🤣, idan jinya daya takeyi to itama dayar yanzu zakiga ta kwanta, Dama can haka suke, karku damu
Shalele tace haba sis sajeey yazakice karmu damu
Tatashi ta dawo kusada Samah tace Samah, dan Allah meyake faruwa?
Cikin Kuka tadago Kanta tace Wai cewa yayi wallahi saiya aureni, nace masa banaso banaso Amma yace shi wallahi saiya aureni, nikuma wallahi bazan yardaba yaje ya aureni yakaini gidansa yaita jibga🤣🤣
Shalele tace Waye? Wai uncle Bilal din kike nufi?
Ta daga Kanta alamun eh
Aikuwa suka kwashe da daria 🤣
Safah ta share hawayenta ta harari Samah, tashige toilet domin wanke idonta 🤣
Afrah tace kuma yanzu menene abin Kuka Samah?gayen baida matsala, kawai de kunsamu sabanin fahimta ne, ni banga aibunsa ba
Afrah tace to sister haneey tsoho🤣Kema Naga alama zamanki dashi yafara shafa Miki son girman
Tace eh naji
Sajida tace yanzu de Samah kiyi hakuri, Kinga dukanmu muna San abin nan, idan kika amince shikkenan zance ya qare
Safah data futo daga toilet itama tace ku kurabu da ita, tana Sansa gulma ce, gashi nan ta riqe masa da, idan Bata Bata Sansa ai bazata so Yaron saba
Afrah tace laaa waiji kuke dansa ne?qanin haneefa nefa, Yana son Yara ne kawai shiyasa ya riqeshi
Samah da sai yanzu tayi magana tace au dama ba dansa bane shine yaketa nuna min wani iko? Harda cemin nabashi dansa ni driver yakawo ni?
Wallahi DANA SANI tun a lokacin zan ce masa yabari saiya Haifa tukunna
Dukansu suka hade Mata baki sukace saikun Haifa de, 🤣🤣
Sajida tasake cewa Dama yanzu ga sister haneefa nan🤣
********
Yayi shiru a office dinsa shi kadai, ga ayyuka agabansa nan yakasa qarasawa, yarinyar nan tana so ta kashe shi,🤦🏻♂tun ranar dasukazo gidansu Har yau taqi Bude wayarta, Yaya takeso yayi? Hauka takeso tasashi kuma Bayan jinyar daya kwanta adalilinta?
Wayarsa tayi qara, yadauka yakara akunne, yallabai anturo design din takalman dakayi magana a kansu tun jiya Amma bakayi maganar meeting din da za'a yiba
"Zan nemeka Bayan naduba" abinda yace Kenan, daga daya bangaren akace Okey sir
Turo kofar office din nasa akayi, wani ma'aikaci ne, yace yallabai ga wadannan takardun Wanda zaka duba ne kafin a shiga meeting, anriga da angama aikin komai, saide dubawarka dasaka hannun ka da ake jira