x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - SHALELAN BABA

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 64847 words

Category: Love Stories

Views 84

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
daya? Nabaku hakuri Nabaku kunqi ku Rabu Dani? Tafashe da kuka tace Dan girman Allah ku qyaleni, wallahi Daga yau babu ni babu Shalele
Hanyar datake Bima bazan sake biba, wallahi idan naqara kwanaki awannan dakin me duhu mutuwa zanyi

Ke Dalla malama kiyi mana Shiru, babu me sakin ki, sai oga Bilal yabamu dama, inna Marka tafashe da kuka

********
Yau Tunda lesson teacher dinsu yatafi ta lura sister ta tana cikin damuwa, Bari tayi Saida suka shiga dakinsu sannan tace sister meyake damunki?

Cikin damuwa tace babu komai sis

A a Haneefa, kada ki boyemin Dan Allah, idan damuwar ki karatu ne ai mama tace kiyi hakuri mu gama wannan term din idan zamu koma first term tare za'a maidamu, muyi zamanmu ajinmu daya, mu dawo gida ga mama, to Menene Kuma abin damuwa? Yau Watan ki daya a gidan nan, Ina lura dake kina Yawan tunani Haneefa, meyake damunki?

Kafin Shalele tace wani Abu wayarta tayi qara, tana dubawa tayi Murmushi, ta Daga tace Yaya Ajmal, zan kiraka, I am busy now
OK Yaya bye

Kashe wayar tayi tace, inajin ki sister, cikin damuwa tace sister nakasa cire shi araina, tana fadar haka tafada jikin Sajida tasaki wani irin kuka

Jikin Sajida yayi sanyi, tafara Bubbuga bayanta Ahankali, tace kiyi hakuri sis, waye shi din? Fadamin waye?

Batace uffan ba ta dauki wayar sajidan ta shiga gallery takamo photon sa ta nuna mata

Dasauri Sajida tace Innalillah.. Wai uncle Haneef?

Anty jiddah dataji su Shiru, ta biyo su dakinsu domin ganin ko kalau suke?
Takama handle din dakin zata shiga saita fasa, ta tsaya Taji me Haneef yayi? Me qaninta abin sonta yayi?

Cikin daki kuwa Shalele tana hawaye tace eh shi Sajida, Ina sonsa wallahi, nayi nayi nacireshi Daga Raina nakasa

Amma sis Haneefa Yaya akai kika sanshi hakika fara sanshi? Kokuma awannan Dan zaman dakikai ne a gidan momy?

Ba anan bane Sajida, tun aqauyanmu nafara ganinsa, tiryan tiryan tabata labarin komai

Ajiyar zuciya Sajida ta sauke, gaskiya sis kinyi kokari, na tausaya Miki, Nima fa haka infada Miki lokacin Ina zuwa gidan momy nake ganin Yaya Ajmal shida uncle Haneef din, wallahi sis tun daga lokacin naji inata tunaninsa, Amma ni da Allah ya rufamin asiri sai akai dace Shima yace yana sona, to kinji inda nadanji sauqi

To Amma matsalar uncle Haneef dinne baya Zuwa gidan nan bare muyi masa Yan dabaru Ko zamuja hankalinsa, Amma kiyi hakuri wannan girman kan nasa da miskilancin dayake ji dashi zamu sauke masa shi tas🤣😃, Yanda nakeso Yaya Ajmal ya Aure ni, kema sai uncle Haneef ya aureki, Kinga shikkenan mun auri abokai Ko?
Shalele tayi Murmushi suka rungume juna

Anty jiddah datake tsaye abakin kofa Daria ta Kamata, lalle yaran nan wato dan'uwan nata ake hadawa tarko tana zaune bonono

Barin kofar Dakin tayi, ta shiga duniyar tunani, yanzu Haneefa Nason Haneef, ga Haneef Kuma a gida anhadashi da manyan mata, Yaya zatayi ta temaki yarinyar Nan, tanajin Haneefa aranta Kamar itace ta haifeta, dole zata temaka wa yarinyar tasamu abinda takeso (to gafa second Bilal 😃🤣😃)

Zama tayi akan kujera ta dauki wayarta takira Haneef yana dagawa babu alamar wasa atare da ita tace sai yaushe zaka zo gidan? Kokuma Sai nan da wasu watanni? Haneef nakusa Yin wata biyu rabon Dana ganka fa, aiki hauka ne? 🤣

Oh anty jiddah Kin cika damuwa wallahi 🤦🏻‍♂, yanzu natashi Daga wajan aiki, zan shigo kafin natafi gida

Batace masa komai ba takashe wayarta

Qwala musu kira tayi, dasauri suka futo falon, ta zuba musu ido tana qare musu kallo, babu abinda yaranta suka rasa, musanman ma Haneefa, zaman datayi a gidan tana hutawa, tana abinda takeso, hankalinta kwance, yasa komai nata yasake futowa musanman hips dinta, yaqara bajewa, sai shining yarinyar take, insha Allah zatayi duk Yanda zatayi taga Haneef ya Aure ta, wannan ai bazai Iyu ace Haneef yayi rashin taba

Qawancen su ya birgeta, basa boyewa juna komai, gashi yau dalilin Haneefa itama tasan damuwar Tata yar

Mama gamu, inji Haneefa

Anty ta jiddah ta kalleta, riga da sket ne ajikinta, dinkin yayi bala'in karbar ta, rigar me breas cup ce sai tayi Kamar tasaka brezia, nan kuwa Bata sakaba

Tace dama zan fada muku ne abbanku yace gobe yanada baqo da safe, kunga yanzu yamma tayi, inaso ku shiga kitchen kufara Har hada abubuwan dazamu girka masa, abinda babu sai nayi masa waya yataho dashi kafin yashigo da daddare

Atare suka ce to, sukayi kitchen din, anty jiddah tabisu da kallo, tayi Murmushi, su Sajida masu tarko😃Wai Har sunyi girman dazasu San wani Jan hankalin samari, oh zamani

Suna aiki a kitchen, saminu yayi parking motarsu, dasauri yafuto yace saminu minti biyar, zanga anty jiddah na futo mu wuce gida

Cikin girmamawa saminu yace to yallabai afuto lafiya

Kai tsaye falon nata yashiga, Kamar kullum yana cikin suit, light blue, yayi bala'in yin kyau
Anty jiddah na ganinsa tace hmm ai wallahi nakusa fishi

Murmushi yayi, banda rikicin anty ya za'ai naqi Zuwa, ai dole ne inzo de in ganki, yanzu ba shikkenan ba?
Ina yaran suke ne?

Ayaz yatafi ball tun dazu Bai dawo ba, sai su Sajida Suna kitchen, ta Daga murya tace Sajida, ga uncle dinku Yazo kuzo ku gaisa

Sajida najin ance uncle taja hannun Haneefa tace laaa kinji uncle dinma Yazo, zo muje

Um um sister jeki, ni wallahi gabana faduwa yake

Au bazaki ba? Aikwa saina fadawa mama, ta juya ta fita, tana zuwa falon tafada jikin Haneef tace uncle sannu da zuwa
Uncle bakasan Zuwa why?

Saida ya lakace mata hanci yace to my daughter yanzu gashi nazo

Anty jiddah Tace a a Ina HANEEFA?

Tazo su gaisa mana, ta Daga murya tace HANEEFA! HANEEFA!!!?

cikin ransa yace HANEEFA, suna me dadi, wacece wannan me irin sunansa?

Yanda anty jiddah take Qwala mata kira yasa ta futo dasauri, gabanta yana faduwa, Har falon taje, Amma takasa kallansa, saita kalli anty jiddah Tace mama gani

Bakiga baqo bane?

Sai a lokacin ta Kalle shi, idonsu yahadu, dasauri ya janye idonsa jin Gabansa yana faduwa, ahankali tace masa "Ina yini?"

Yasake kallanta yace "lafiya"

Juyawa tayi zata koma kitchen Sajida ma tabi bayanta tace uncle bye bye, yace ok my daughter

Yabi bayansu da kallo, Amma azahiri hips din Shalele yakafe da kallo, yana ganin yanda suke Juyawa

Anty jiddah na lura dashi, tace mekake ganine?

"no anty babu komai fa, wacece wannan din? "

Au Wai baka gane taba? Haneefa cefa yarinyar datake gyarama daki, harna taho da ita

Yace ok, yasake bin hanyar kitchen din da kallo

Anty jiddah tanaso ta qureshi Tace Wai kalau kuwa?

Oh Allah anty nace Miki babu komai, kawai de Naga tanada komai ne, like yar tsana haka, shiyasa nake kallanta

Haneef me kace? Yar tsana?yar ta wace yar tsana?

Murmushi yayi dimple dinsa yafuto yace Kinga anty ni sai wani lokacin ki gaida doctor idan Yazo, Daria tayi tace to zaiji, Shima dasauri yafice Daga gidan, anty jiddah Tace mataki na farko Kenan, zakaga yar tsana😃

********
Washe gari gida ya kaure da Qamshin girki, kowa yaci kwalliya Ana jiran Zuwan baqon Abba, sun jera komai a dining, sun dawo falo Suna zaune Dukansu

Tsayawar motar Abba sukaji, hakanne ya tabbatar musu da Cewa Abba Yazo shida abokin nasa
Da sallama suka shigo cikin falon, Dukansu suka maida hankalinsu wajan kofar falon

Lokaci daya Shalele ta miqe tsaye tace Uncle Bilal !!!

Cikin tsananin mamaki yace Haneefa

Dama Kaine baqon Abba?

Ai kafinma yayi magana tatafi da gudu ta rungume shi

Lokaci daya Anty jiddah Taji kishi, yauga yarinyar datake so qaninta ya Aure ta tana qirjin wani daban ba Haneef ba

Dasauri yafara janyeta Daga jikinsa gudun kada tasashi a wani Hali uba yayi abin kunya😃🤣
Wayarsa yadauko Daga Aljihun wandon jeans dinsa, yayi kira yace hello inspector zaku iya sakin matar nan yanzu

Daga hannunsa yayi sama, yace alhamdulillah, Allah nagode maka, Haneefa jeki dauko jakar ki, yau qafarki qafata








Anya kuwa anty jiddah zata yarda tabar Shalele?

Toshi kima Bilal me yarinya Anya yau kuwa zai iya barin Shalele tasake subuce masa?

Yaya makomar Haneef Shazali?


Muhadu Zuwa gobe idan Allah yabamu lokaci



Masu Cewa nayi 2pages kuyi hakuri, babu lokaci, kowacce mace Bata rasa ayukan gida, shiyasa yau nayi dayawa saboda ku😃😃😃Amma da tun lokacin da anty jiddah tajisu Suna sirri zan tsaya, saboda ku naqara masoyana, ku kasance tare Dani, Nima Ina sonku sosai





Sharhi, share, comment, Dan Allah 🙏🏻




Amnah El ✍🏻

💕SHALELAN BABA💕
(Romance)

Writing by Amnah El

25&26

Doctor Sulaiman yace a a doctor Bilal me kake nufi ne? Wai shin dama kunsan junane?

Anty jiddah tayi Ajiyar zuciya tace haba doctor, me kake nufi da qafarka qafarta? Ina ne zaka tafi da yata?

Doctor Bilal yayi Murmushi yakamo hannun Shalele suka zauna akujera, Suma su anty jiddah duk suka nemi waje Suka zauna
Ya kallesu da kyau yace Haneefa yata ce, dama nemanta nake ido rufe, bansameta ba, mahaifin ta tun kafin yarasu yace nadauketa yabani ita halak Malak, nazama uba agareta, sharrin matar ubane yasa Har tazo gidannan domin yi muku aiki, Amma wallahi da gatanta, daddynta yana raye🤣😃(su daddy manya, Kai Bilal ka shige su da son girma)

Ahankali anty jiddah tasaki boyaiyar Ajiyar zuciya, sai yanzu hankalinta ya kwanta da Bilal, Amma da Kam gaskiya qaninta take tayawa kishi

Tace doctor Haneefa ba aiki tazo yi gidan nanba, a gidan mu take aikin, nikuma na dauko ta na riqeta tamkar yata, yanzu doctor idan karabata da yaran nan Suma kansu ba zasuji dadi ba, sun riga da sun saba, doctor ayi hakuri abar mana ita mana

Kallan Shalele Bilal yayi, da gaske kinason zaman dasu?

Duk su Sajida suka bita da kallo

Ahankali ta Daga masa kanta alamar eh tanaso

Yasake Cewa kina ganin nan din babu damuwa Ko?

Babu damuwa uncle, mama tana sona sosai, Abba ma haka, sun riqeni amana Kamar Yanda kayi

To alhamdulillah Tunda de yanzu nasan gidan da kike, to hankali na zaifi kwanciya

Ya kalli su anty jiddah, yanzu de matar aboki kin qwace wa uba yarsa karfi da yaji

A a doctor to yanzu saida muka saba zakace qafarka qafarta fisabilillah
Yanzu de Tunda nagama jin matsayar zance, babban baqon mu Kuma baban yata, yatashi abinci yana jiransa

Duk falon sukai Daria

Gaba dayansu suka rankaya Zuwa dinning, anacin abinci kowa nata fara'ah, wannan ya tsokani wannan, wannan ma haka, Har suka kammala
Suka dawo falon suka zauna anata kallo, Amma Shalele tana gefen Bilal Suna fira qasa qasa, cikin nutsuwa

Ya kalleta yace yarinyar uncle duk kin canja kin girma, ai Gara Dana ganki Dan inje gida infara Tara kudin da zanyi bikin yata

Cikin kunya ta rufe ido, Kai uncle Dan Allah ni bawani Aure da za'a min yanzu

Aikuwa Aure dole yarinya
Kina nufin haka zan zuba Miki ido Ina Kallan ki?

(tofa Kamar shidin yayi🤔😃) To garama ki shirya, Abdallah fa yana wajena

Cikin rashin fahimta tace Abdallah...

To yar qauye Aududu

Cikeda murna tace laaaaa uncle Dan Allah? Yaya akai inna tabaka shi?

Nan take Bilal yabata labarin komai, Aikuwa ta dinga Daria, itama tabashi labarin Yanda sukai da ladidi tijara Bayan sun taho

Yace ai Ko yaushe Naga wannan matar, saina nuna Nima Dan tijara ne, ba'a taba yata a zauna lafiya

Qasa qasa yayi da murya sosai cikin rada yace mata aide da gaske nan din babu wata matsala Ko? (tab wallahi Bilal idan anty jiddah tajika nide ba ruwana🤭🤣)

Shalele tayi Murmushi tace eh uncle babu komai fa wallahi, Ina anty Sady da Hajiya?

Duk Suna nan kalau, zance kina gaishe su, idan nasamu lokaci ma ai zanzo na daukeki muje

Doctor Sulaiman yace wato de yanzu baqon namu ya zama Iya baqon Haneefa ita kadai

Daria Bilal yayi yace to abokina tuba nake, sannan yajuyo sukaci gaba da firar Dukansu

Dazai tafi gida, Har wajan mota suka rakashi, yashiga motarsa yadauko ATM dinsa guda daya, yace wa Shalele ki riqe wannan ATM din, Ko zaki buqaci kudi aciki, ni inada wani, sannan ga kati na nan, duk numbers Dina Suna jiki, idan wata matsalar ta tashi, zaki Iya nemana, pin din ATM din qarshan number tane, kingane?

Eh uncle nagane, nagode sosai, Dan Allah ka gaisheda hajiya sosai, da Aududu, da anty Sady

Karki damu my daughter zasuji, Saida taga fitar sa, sannan ta juya cikin gidan itama, ayaz ne kawai Afalo, anty jiddah tana daki wajan Abba, sai kawai itama tatafi dakinsu ta adana katin da ATM din cikin jakar kayanta, a gado ta zabe kusa da Sajida Suka fara maida baccin gajiya, kasancewar sunsha aikin tarbar baqon abbansu

********
Juyi yayi akan gadon nasa, yasake Jan blanket dinsa fari qal qal dashi, akaci gaba da bacci
Azahiri ma maganar sa Ahankali yakeyi Kamar mace, yanzun ma hakance ta kasance dashi cikin baccin, ahankali yabude bakinsa yace "karki tafi"

Yaci gaba da baccin kadan, alamar mafarki yakeyi, da aka jima ma cikin sigar shagwaba yasake Cewa "nace karki tafi fa"

Ahankali yasaka hannu yaja Fillo din dake gefensa ya rungume shi aqirjinsa sosai yace "Stay with me please"

Yaci gaba da baccin sa cikin kwanciyar hankali, wayoyinsa guda uku dake ajiye akan bedside drawer ne daya Daga ciki ta dauki qara

Runtse idanunsa yayi, ahankali yabude idon nasa, lokaci daya yaji wani irin bacin rai, meyasa za'a kirashi akatse masa mafarkin sa? Waima da meyasa ya manta ne Bai kashe suba?

Yanajin wayar na ringing harta katse be Iya dauka ba, Saida aka sake kira akaro na biyu ne sannan ya meqa hannu yadaga, Ajmal ya akayi?

Kai Sarkin nawa, kazauna Kanata kwalliya kaiba budurwa ba, already anyi sadaka dakai, kaqi futowa office da wuri, mutane Suna nemanka wayoyinka duka a kashe, shine wani daga ciki yakirani yace idan inada wani layin Naka infadama Suna can Suna jiranka akan meeting din dazakuyi

Ajmal, kafada musu su dage meeting dinnan, banida lafiya bazan Iya fita ko'inaba

Dasauri Ajmal yace what? Ganinan Zuwa

Shima Haneef anasa bangaren ajiye wayar yayi yazuba wa saman dakin nasa ido, bagarama rashin lafiya ba akan wannan tsinannan tunanin dayake🤦🏻‍♂

Tun shekaran jiya yake Fama da tunanin yarinyar Nan, shi Kam wannan yarinyar inaga masifa take neman zame masa

Tashi yayi yafuto falo da kayan motsa jiki ajikinsa, Kamar kullum yauma Saida ya ajiye robar ruwa agefensa me sanyi, sannan yafara motsa jikin

Yayi Nisa da motsa jikin kawai ya tuno idanun nan nata, zazzaqar muryarta "Ina yini"?

Ya tuna gaisuwar datayi masa, lokaci daya jikinsa yasaki, gudun dayake yi yadena, ya sunkuya yakama gwiwoyinsa da hannayen sa, Kamar me ruku'u yana maida numfashi

Awannan halin Yazo ya riskeshi, dasauri Yazo yadago shi, subhanallah abokina Ko ciwon cikinka ne yatashi? Shazali shiyasa nace kadena durawa kanka wannan maganin, shikkenan Kai dakaji yar sha'awa saikaje kakama magani kasha, sannu...

Yaga alama idan Bai dakatar da wannan gayen ba, bazai daina zubaba, shi Ko gajiya bayayi da magana, qwace jikinsa yayi yace Dan Allah Malam cikani,yamiqe yadauki ruwansa ya kwankwada

Cikin mamaki Ajmal ya kalleshi, kaiiii, au Wai dama kalau kake shine kasa nabaro aiki na nataho wajan ka?

Bece dashi komai ba, yayi wajan kujerun sa yazauna, ya Dora kansa akan kujerar

Ajmal yace abokina what happen?

Bude ido yayi ya kalleshi, Ajmal meyasa me idan kaga wasu mutanan sai kaji gabanka yana faduwa haka?

Ajmal yace mutane Kuma? Kamar suwa?

"Ina nufin Kamar mace haka "

Zaro ido yayi😳mace kagani gabanka yafadi?

Ahankali yace" yes "ba sau dayaba, duk ganin Dana mata

Um tab, gaskiya abokina nide a Iya sanina, alamu ne na kamuwa da so

What? So? sofa kace Ajmal, ni inso wannan yarinyar? Yarinyar Dana haife.... Saikuma yayi Shiru yazari wayar Ajmal dake gefe yashiga danne danne

Tsayawa yayi ya karanta abinda yaduba, yayi cilli da wayar kan kujerar dasuke, yace "shirman banza"

Ajmal yadauki wayarsa yaga abinda shazali yaduba, ya kwashe da Daria, au baka yarda da maganar Dana fadama ba Saida ka duba a Google?
Yasake kwashe wa da Daria yace Allah sarki, ashe wannan ne rashin lafiyar dakake, shiyasa yau kaki Zuwa office, abokina wacece wannan yarinyar? Wacce me sa'ar ce? Daga fara kamuwa da sonta anqi Zuwa office Tokuma idan aka aureta Yaya za'ai Kenan? 🤣😂😃aikin za'a ajiye duka?

Ajmal kadena Daria mana, wannan abin fa ba abin Daria bane, da gaske banida lafiya, kullum naganta sai gabana ya fadi, kaga wannan ma ai babbar jinya ce, ni babu wani so danake wa kowa, Daga Kai Har Yan Google din duk qaryar banza ce, aikin banza aikin wofi 🤣

Me Ajmal zaiyi inba Daria ba, yace gaskiya ne abokina, wanan Kam babbar jinya ce

Tsaki Haneef yasaki yatashi yashige dakinsa, Daga nan yayi toilet domin watsa ruwa

********
Suna zaune akan gadon su, da daddare Suna fira, Sajida ta dubeta tace Wai kuwa sister Dan Allah jiya da uncle Yazo Yaya kikaji?

Ajiyar zuciya ta sauke tadauki Fillo ta Dora a cinyarta, ai wallahi bakiji Yanda naji dadi ba, Kamar karna bar falon, saide Kuma ba dama

Um ai sister Haneefa shiyasa danaji ance Yazo nace kizo muje kikaqi Zuwa

Ke gabana nefa yaje faduwa, Kuma ni idan Ina ganinsa sai Inga yamin kwarjini nakasa komai, Ko kallansa kasawa nake wallahi, ninarasa wannan wanne irin so ne

Lalle sis, wanne irin kwarjini? To tsaya anan yana Miki kwarjini wadancen yanmatan su kwace Miki shi(karfin Hali irin ya zama natan nan🤣🤣)

Toya zanyi sis Sajida, shi din wani irin mutum ne na daban, ga aji, jiya fa Wai nace Ina yini, akace min "lafiya" shikkenan fa bass
Bakiji Yanda yasake birgeni ba, Allah Kasa idan akwai Aure atsakanina dashi Toya tabbatar mana da alkhairi, idan Kuma babu Allah kaciremin Sansa araina
Dasauri Sajida tace akwai ma insha Allah sis, babu wani family dazaki tafi, kina nan a shazali's family insha Allah
sukasa Daria gaba dayansu

********
Yashirya kansa cikin qananun kaya, sai zuba Qamshi yake
Momy da daddy Suna zaune, ya tsugunna Har qasa ya gaishe su, ya kalli daddy yace daddy dama.. I want talk with you

Inajin ka Haneefa

Am daddy gyaran dakin da yaran nan sukemin bayamin, kwata Kwata
End Ads