Ai inde haneef ne zaiyi yafi haka ,itama narasa dalilin bin saurayi gidansu,hakan ba mutuncin mace bane ga me hankali
Tashi muje muyi girkinmu kinji
Tashi sukai suka shiga kitchen, cikin ranta tana tunani yaushe ne lesson teacher din zaizo ?tayaya zataje ta tambayeshi ?
Tana wannan tunanin baba tace kinga wannan kunun gyadar karbi kiyi da kanki yau nagani
Yauwa baba kullum saikin dama kunun gyada wai waye yakesha ?Alhaji ne?
A a yata haneef ne,ai shi yanasansa dayawa
,yanzu ma dazan samu mekai masa sai akai masa yasha
Shiru tayi tana tunani ,kota karba ne ?wannan ce kawai hanya mafi sauqi dazata kaita gareshi
Cikin kunya tace to baba ki aikeni mana
Baba tayi murmushi dama ta manya tamata🤭😃
Tun dazu taga tana tunani, tasan Kuma tunanin haneef take, tasan sarai tana sansa tun lokacin datayi mata wannan tambayoyin
Zubawa tayi ajug tasaka mata akan try da qananun kofuna ,tace to dauki kije yata
Aikuwa tayi wuf tadauka tatafi🤣😂
********
Kadan kadan gabanta yake faduwa harta tura kofar falon nasa ahankali tashiga
Adede lokacin yayi shirin motsa jiki ,dagashi sai farar singlet da gajeren wando 🤭🤣
Sau daya ta kalleshi tayi sauri tasauke idonta Qasa
Bata taba ganin namiji azahiri ba ahaka saide ko yan ball kokuma a TV
Wannan wanne irin jiki gareshi duk a mummurde ?kalli qirjinsa duk gashi
Lokaci daya taji tsoro duk ta diririce ,ita kuwa meyakaita San wannan qaton ?Ina zata kaishi?
Shima yana dago kansa yaganta yakafeta da wani irin kallo
Shi saida yaganta ma yatunada maganar karatun su
Dakuma kayan daya siyo mata jiya🤣🤭
Ahankali ta qarasa wajansa tace Uncle ina yini
Gashi wai inji baba
Bece mata komai ba yazauna a kujerar ,itama ahankali ta tsugunna agabansa tafara zuba masa kunun acikin cup (🤭to ita kuma wannan me za'ace mata kenan ?)
Tadauka ta miqa masa
Yana kallanta yasaka hannu ya karbi kunun ,ahankali yafurta "thank you so much"
(Tab gaskiya shalele kinyi sa'ah yau Haneef shazali ne dakansa yake gode miki😃)
Zama tayi aqasan kujerar shikuma yana kai azaune,yana satar kallanta Qasa Qasa
Wasa take da yatsun hannunta ,cikin ransa yace masha Allah dogaye dasu
Yar yarinya da ita me hankali hartasan takawowa babba abu tazuba masa da kanta
🤣🤣
Yaga tazauna bata tafiba ,shikuma dai bazai koretaba ,inda zataci gaba da zamama anan beqi su tabbata ahakanba🙈
Ganin baida niyyar yimata magana cikin ranta tace maganina kenan ai da shegen cusa kai 🤣🤣qilama ya gane sansa nake shiyasa yake manna min🤣
Tana jan yatsun hannunta tace uncle dama maganar karatun
Cikin sigar rada kamar me tsoron wani yajisu yace oh karatunki ko ?
Jeki dauko littafin
Batace masa komaiba tatashi tafice,kenan shine zaiyi mata karatun ?to Allah yasa de yasaka kayansa kafin tadawo🤣🤣
Tana zuwa part din Momy ko kallan kitchen batayiba tashige dakinsu ta dauko littafin nata tatafi,baba hanne kawai sai gilmawarta tagani da littafi ahannu tayi murmushi tadaga hannunta sama Allah kasa abinda nake tunani yazama gaskiya,tacigaba da aikinta
Tana komawa falon nasa, taganshi da baqar jallabiya ,ahankali tasaki ajiyar zuciya ,taje gabansa tamiqa masa littafin tace gashi
Karba yayi yabude ya dudduba sannan shima yadawo kasa yazauna yana fuskantarta
Cikin qwarewa yakeyi mata explain din komai ,yanayi yana Watso mata tambayoyi Tana bashi amsa ,suna karatu yana nazarin yarinyar
Yalura batasan kallansa kome yasa ?
Abinda ya fahimta ga yarinyar shine tanada ilmi amma meyasa iyayenta basu sakata a makaranta ba suka barta Tana aiki ?meyasa ?
Har suka gama karatun bata kalleshi ba ,tatashi zata tafi yace "kinga"
Saida yadauko yatsaya yakasa fita ,yanzu me zai fada mata ?
Wata dabara ta fado masa ,yasaki ajiyar zuciya yafuto
Tana nan atsaye,ya miqa mata ledar "gashi inji qawarki"
Kallansa tayi "sajida?"
Yes ita
Tasaki murmushi tasa hannu zata bude yayi sauri yace no kibarshi idan kinje ciki kya duba
Tace to ,tareda ja masa kofar
Saida yaga fitarta sannan yayi ajiyar zuciya,yana ganin hakan yafi ,wayarsa ce tayi qara dasauri ya duba yaga abokin karatunsu ne daga kano Abbas
Yana dagawa yace shazali Allah yasa de baka manta da maganar taron nanba gobe
Wanne taro Abbas?
Taron da za'ayi a Russia mana na qarawa juna sani dakuma habbaka harkar kasuwanci,kada kacemin ka manta
Kansa yashafa yace Abbas wallahi na manta
,kawai nahakura bazan samu zuwaba
Mekake nufi ne shazali?
Taron nan dakai aka hada meeting dinsa da yanda zai kasance ,tayaya zakace bazakajeba?
Abbas banyi visa ba,yaushe zan samu viza ayau zuwa gobe?
Haba shazali meyasa kacika damuwa ne ?waya daya zakai kayi magana zance yawuce,nidama zan fadama ne nariga Dana tura musu sunayen mu ,sun tanaji hotels da abubuwan daya dace,kuma kada ka manta kowa da matarsa zaije idan bakada ita saikaje da budurwarka
Budurwa Abbas😳
Yes haka qa'idar take ,menene abin damuwa shazali dama kowa ya matsu yaga yarinyar dazaka Aura, kaga shikkenan saiku tafi tare ,nima daga nan zan dauki matata
Amma abbas ni.....
Dan Allah karkace komai shazali saimun hadu ,qit yakashe wayarsa
Innalillah....wayyo Allah na,meyasa Abbas zai masa haka ?meyasa ?
********
Tana zuwa dakinsutafara duba ledar hannunta ,brezia ce aciki masu kyau,kai sajida da jaraba take saida ta biyota dashi kenan🤣🤣amma ina tasamu kudin dazata siyo wannan ?dan daga gani kasan zasuyi tsada
Nunawa baba tayi,baba kinga kayan da sajida ta aikomin dashi
Yanzu uncle yayimin karatu shine yabani yace injita
Baba tace kai amma sunyi kyau sosai yata,yauwa baba bani aron wayarki nakirata nayi mata godia🙆🏻🤭
Baba tabata wayar me tocilan
Aikuwa tasaka number sajida aciki tayi kira ,dama ta riqe number
Sajida na dagawa tace mata sis naga saqo nagode,gaskiya sunyi kyau kuma kamar kin gwadani wallahi zasumin Dede
Wanne saqo kenan Haneefa ?
Saqon brezia mana dakika bawa Uncle yakawomin
Zaro ido sajida tayi tace brezia😳
A a ni wallahi ban bashi komai ba,ke rabona da uncle tun kina gidan
Innalillah...sajida me kike nufi ?
Menake nufi koke me kike nufi ?ai dama nafada miki abunnan gasu nasiyo mana daga mkrnta kikaqi karba kisa
Kinga yanzu ai gashinan shi yasiyo miki
Shalele tace nashiga uku sajida meyasa ya siyamin?
Cikin daria sajida tace oho muku wayasani ko shima gani yayi suna tsone masa ido ?🤣🤣😃
Batace mata komaiba takashe wayar,karfa zancen qawayenta na kuje ya tabbata,mijinta ne zai gwadata yaji adadinsu sannan yasiyo mata
Wayyo Allah itakam yau tashiga uku,🙆🏻da wanne ido zata kalleshi?
Baba hanne tayi murmushi dan tagama jin komai,dama tasan yaran nan kamarfa sunfada son junansu,inba hakaba shi meyasa zai siyo mata idan ba sonta yakeba?
tace yata to menene abin damuwa ?ai Haneef kamar yayanki ne
Cikin shagwaba tace Kuma baba saiya siyomin wannan ?kinga fa
Baba tayi daria tace to ayi hakuri mana tunda anriga ansiyo ai sai kisa 🤣😂
aranar haka tawuni adaki ,taqi yarda tafuto danma kada taganshi
********
Washe gari tunda safe yayi report a office cewa zaitafi Russia wajan taro na tsawon kwana uku
Ajmal yayiwa waya yasanar dashi komai, ajmal yace to ai bawani abin damuwa bane,ni ina ganin kawai kaje kadauki Hairat kutafi,dan tadanfi hajara wayewa
Sannan ita tanaji da tashen boko, nakega bazaka samu matsala da itaba
Wato duk da baka nemeniba ,sai yanzu da buqatarka tatashi zaka nemeni,?wato zakaje dani taro danna rufama asiri🤣😂
Cikin bacin rai yace kinga....
Katseshi tayi,Malam kajuya katafi babu inda zani ,kaje wulaqancinka ya nema ma wata
(yauwa hairat nuna masa de mata sunada daraja suma🤣)
Bece da ita uffan ba yaja motorsa yabar gidan
Haushi yaji dabai karbi number hajara ba ,yanzu dolensa yaje gidan baida wani zabi
Yana zuwa gidansu kuwa aka kaishi falo ,hajara tafuto, ta tsaya akansa takama qugu tariqe
Shima tsaye yatashi yace hajara akwai inda nakesan ki rakanine
Nice zanma rakiya haneef? Ina zakaje da mummunar mata?Aida kunya ,kaje de ka nemi sarauniyar kyau ta duniya🤣🤭😃🤣
Tana fadar haka tashige ciki tabarshi anan
Da bacin rai yataho gida ,ko Neman ajmal baiyiba bare yasanar dashi abinda yake faruwa 🤣🤣
Part dinsa yaje yadauki kayansa ,yawuce part dinsu Momy yayi mata Sallama itada daddy
Yafuto harabar gidan yasaka jakar sa amota,yadafe kansa da hannunsa🤦🏻♂
(tofa yau taqarewa maza😂🤣)
Wayarsa ce tayi ringing yana dauka yace Abbas ya ake ciki ?
Shazali gani nida madam zamu wuce ,saikunzo ko ?
Cikin damuwa yace gaskiya..Abba..bansamu...
Haba shazali ,dan Allah karkace komai,danni harna Riga nasanar da friend's dinmu cewa zakazo mana da matar dazaka aura😳🤣
Cikin damuwa yace Abbas kakasheni🤦🏻♂🤣
Acikin gida kuwa shalele suna kitchen itada baba ,tace baba nagaji zanje daki nahuta,baba tace to yata Dan Allah dauki wannan towel din kidan shanya min shi akan fulawa,saikije ki kwanta
Towel din tadauka zata futo
Tana futowa adede kofar lokakcin Kuma Samah takawo kai itama
Aikuwa sukai gware
Cikin masifa tace ke wacce irin kidahuma ce ?bakya kallan gabanki ne ?
Tafara shanya towel din kenan yaji alamar motsin mutum
Dago kansa yayi ya kalleta,doguwar riga ce ajikinta ta atamfa
Ahankali yace "bakijiba"
Sai akai dace kuma maganar tasa ta tabbba,batajinba🤣
Yo magana ce anayinta kamar ba'aso🤣🤣😂
Sake daga murya yayi yace "qawar Sajida"
Ahankali ta juya taganshi atsaye ajikin motarsa
Besan sunanta bane yace qawar sajida ?
Qarasowa tayi wajansa,tace Uncle gani
Ahankali yatako yazo gabanta ,yasaka hannu yabude mata mota dakansa (tab matsayi🤣)
Kallan rashin fahimta tayi masa
Shima yagane hakan,lokaci daya yasha kunu ya tamke fuska cikin Qasa Qasa da murya yace "shiga mota mutafi"
Yafada mata hakanne saboda yana tsoron itama kada yace tarakashi tace bazata ba ,dan haka yasha kunu yace tashiga sutafi
Ganin babu alamar wasa a fuskarsa yasa babu musu tashiga ,yarufe ,sannan ya zagaya yaja motar sukabar gidan
Tab wayaga shalele a Russian😱
To masu korafi banyi typing ba jiya shikkenan de magana ta qare gashi har yau din tazo 😃
Tunda nafara rubuta littafin nan bantaba fashin turo mukuba,ai yakamata nima amin azuri,na kwana daya de
Nidama namuku uzuri tunda nasan soyaiyarku ga SHALELAN BABA ne yasa kukai hakan
Sharhi ,comment,share ,dan Allah karku manta🙏🏻
Amnah El💕SHALELAN BABA💕
(Romance)
Writing by Amnah El
31&32
Tunda suka fara tafiya babu Wanda yayiwa dan'uwansa magana
Ita sai kumburi take saboda Samah ta bata mata rai
Juyo da kansa yayi ya kalleta yaga sai cika take tana batsewa ,toya zai mata ?yasan bacin ran baiwuce tace yadaukota daga gida batasan inda zasuba ,idan kuwa ya kuskura yayi mata magana tace yamaidata gida tofa shi shikkenan tasa taqare dan baisan kuma wazai kamaba🤣
Danhaka shima yashareta yaci gaba da driving dinsa kawai
Kai tsaye wajan passport sukaje ,yanayin parking ya kalleta yace "muje"
Kallansa tayi sannan ta kalli jikinta,batada ko mayafi
Shima bece mata komai ba sai zagayowa dayayi side din datake yabude mata kofar motar,ganin da gaske yake yasa ta warware dankwalin kaanta tayafashi ,dukda beje mata ko'inaba
Tun kafin sushiga cikin wajan taga mutane sai gaidasu suke
Suna shiga cikin office dinkuwa dasauri ma'aikatan dakansu suka tashi suka basu abin zama
Abinka da manyan mutaje,nan take yadauki kafa daya yadora akan daya ,sabanin ita datai zamanta normal
(🤣to su shalele ba'a sababa)
Ahankali suka bashi hannu suka gaisa,sannan yace akwai tafiyar da zamuyi ne very important, but batada passport
Tafiya zasuyi ?ina zai kaita ?aikuwa bari su fice daga nan ta tambayeshi
Haba yallabai haneef,ai yanzu za'ayi mata, photon ta suka dauka,nan take suka fara yimata
Shikuwa gogan ya harde akujera yana danna wayarsa
Daya daga cikin su ne yafara yimata tambayoyi tana bashi amsa
Sunanki ranki yadade
Tace Haneefa Suraj Adam
Shekaru fa
Tafada masa komai ,yabata wani Biro dayake daure da wata na'ura yace tazo tayi sign
Tatashi tayi ,sannan tadawo kusa dashi tazauna
Suna zaune kawai sai gani tayi dayan ma'aikacin yace yallabai an gama komai
Yataso yamiqa masa ,karba yayi yace godia nake
Sannan yadauko ATM card dinsa yabasu,suka saka cikin p.o.s dinsu ,dakansa ya karba yacike musu komai har adadin kudin sannan yazare abinsa
Fara'ar dataga sunayi kadai ya tabbatar mata da cewa kudin daya basu ya wuce Qa'ida
Futowa sukai,suka nufi wajanda motarsa take
Yanda yake bude mata mota kadai zaisa kagane tanada muhinmanci awajansa
Sun fara tafiya ,ta kalleshi taga fuska atamke
Amma dukda haka saida tace Uncle ina zamuje ?
"Unguwa"
Abinda yace mata kenan
Shiru tayi ta rabu dashi ,basu tsaya ko inaba sai wajan saloon, yana tsayawa ya kalleta yace "futo"
Saida ta kalleshi sannan tafuto ahankali,shagon suka shiga babba ne sosai da fadi ,ayi saloon ,ayi makeup, ga kayaiyaki dasuke siyarwa agefe
Suna shiga yasake qarewa wajan kallo
,matar yarece ba bahaushiya ba,saide tanada yara mata masu yimata aiki hausawa
Tana ganinsa tafara fara'ah ,itade shalele aranta tace ikon Allah shi ansanshi ako'ina kenan
Gefe daya suka koma yayi mata bayanin komai ,sannan ya dubeni yace kije,shikuma yafice
Zaije yakai passport's dinsu wajan visa dakuma nema musu ticket din jirgin dazai tashi anjima
Matar dakanta tafara aiki akaina bata bawa yarantaba
Sannan sukaje wajan kwalliya ,ta tsantsara mata kwalliya ,lokaci daya tasauya kai bazakace shalelan baba ta qauyen kuje kaganiba🤣dan qaramin lips dinta bata cika mata janbaki ba ,kawai pink din jambaki tasaka mata shima kadan
Agogon hannunsa ya kallah,wannan wanne irin gyarane ,yadauki lokaci sosai
Wajan zama suka bashi,amma bai zaunaba ,a tsaye yake yafara zagaye wajan ahankali yana duban agogo
Aciki kuwa wajan kaya suka shiga ,matar tayi shiru tana tunanin wanne kaya oga yasaka
Jijjiga kai tayi bayan tagama tuno kalar suit din datake jikinsa ,milk colour
Tadauki doguwar Riga fitet gwon me kyau ,rigar batada ado sosai sai dutsina dake jikinta farare masu qyalli,kafadar rigar ayanke take ,irin me bulalliyar kafadar nan ,tabata tasaka ,aikuwa Riga tazauna mata sosai ,musanman hips dinta yabada tashi gudunmawar ,dan kwalin rigar babba ne danhaka tayi mata rolling dashi
Yana aikin zagaye falon sukazo suka sameshi,matar tace yallabai shazali we are finish
Yana juyowa yaganta lokaci daya gabansa yafadi ,kasa dauke ido yayi akanta ,matar ta kalleshi ,ta kalli shalele ,gaskiya ya'iya zabe,sunyi mutuqar dacewa da juna
Gyaran murya tayi ,dasauri ya kalleta ,yace sorry fa ,yabats ATM dinsa suka saka,dakansa yatura musu kudin
Sannan yajuyo ya fuskanci shalele datake tsaye tana kallan ikon Allah, su Kansu maaikatan wajan sunyi bala'in birgesu
Ahankali yatako yazo wajanta yamiqa mata hannunsa
Hannunsa ta kalla ta kalleshi,yaza'ai yariqe mata hannu?
Sake kallansa tayi ,taga yakafe mata idonsa,ahankali ta Dora hannunta akan nasa,lokaci daya suka karbi wani saqo daya ziyarci cikin jikinsu
Hannta Yakama suka fita ,yabude mata motar dakansa tashige sannan yaja suka tafi ,suna tafiya yadauko wayarsa yayi dialling number Anty Jidda, tana picking yace Anty zamu danyi tafiya ne
Tafiya kuma haneef ?kaidawa ?
Yanzu de Anty tunda kikaji an nemi izni awajanki kigane mana
Bazan ganeba,naqi nagane din ,kafadamin kaida waye ?
Wayyo Allah Anty,Nide babu ruwana tunda nafada miki
Sarai tagane inda zancensa ya dosa ,yafuto fili yace da haneefa muka tafi,shine bazai iyaba,gaskiya haneefa saitayi da gaske inma auren wannan yaron tayi kafin ta saitashi
Murmushi tayi ,haneef, Ina zaka kaimin yarinya?
Anty zamuje Russia ,wajan wani taro ,kwana uku kacal Anty nah
Innalillah...haneef zaka dauki yata kutafi wata uwa duniya har tsawon kwana uku amma kanacemin kacal
Wanne irin kacal
To Anty yaza'ayi
Yanda za'ai kawai kadawomin da yata
Wata irin daria yayi Dabe shiryaba,yace Anty amisali?
Cikin ranta tace kai wannan da jaraba take ,tace tafiya?
Samah ce ko Safah?
Safah tace Samah ce ,tasan idan tace safah ce zata raina mata hankali ,amma samah datake da masifa ,yanzu za'a zauna lafiya
Tace OK ,ina yayanku ?
Wallahi Yaya yayi tafiya yanzu
Hajara tace yayi tafiyar da gaske kenan
Murmushi tayi,wallahi kuwa ,Yaya anacan sararin samaniya yanzu ,🤣,saide kiyi hakuri dabai sanar dake qasar dazai tafi ba ,may be yana fadawa mutane masu muhinmanci ne awajansa
Tana gama fadar haka ta rufe kofar ,hajara tace wannan yarinyar karya takemin ,ba samah bace ,safah ce,dukda samah tanada masifa ai tana sona
Ko sake nocking batayiba taja Jakarta takoma gida ,dama dan mamanta ta matsa matane akan tazo tabishi ko hakan zaisa su qara son juna 😃
********
Malam yahai katemaka ka kiramin wannan yaron dayasa aka rufeni,na nemi yafiyar shalele awaajansa
Sannan inji Yaya Dana yake?
Ina aududu na,tunda suka