Wallahi doctor akwai matsala, qanina Yana kwance a asbiti saboda yarka, but doctor yace dole sai an Nemo masa abinda yakeso ko hankalin sa zai kwanta, dan Allah doctor na roqeka, kayi hakuri, nayima alqawarin zanyima bayanin komai idan muka hadu
Amma yanzu yaya za'ayi mu ganka yanzu?
Saida yagama shan qamshi sannan yace gaskiya yanzu na tashi daga aiki ne, saide ku Bari zuwa gobe, kusameni a office saimuje
No bani zanzo ba doctor su momy ne
Saida yayi hamdala a ransa Jin iyayen Yaron ne zasuzo, dadin yanda zai nuna musu yarinyar tanada daraja tana amfani
Yace babu damuwa, zan turo Miki adrees din asbitin sai suzo gobe dasafe su sameni
Toshikkenan doctor godia nake
Dahaka sukai sallama, aikuwa a lokacin yaturo musu adrees din komai
Ita Kuma tabawa momy
Sai a lokacin hankalin haneef yadan kwanta
********
Momy tace hajiya hafsat babu lokacin bayani, Ina haneefa?
Tace haneefa tana daki, Afrah jeki Kirata
Afrah na zuwa suka futo tare, ganin su momy yasa gabanta yafadi, lokaci daya tahade girar Sama data qasa
Mami Tana ganin yanayin ta tasan cewa ba lafiya ba
Har qasa ta tsugunna tace daddy ina kwana, momy Ina kwananku
Atare suka amsa Mata, momy tace haneefa kiyi hakuri kinji? Dan Allah ki yafe mana abinda muka Miki, dan Allah naroqeki kiyi hakuri kizo muje kiga haneef, kina sonsa Yana sonki, mukam indan Tamu ne mun amince wallahi🤣🤣
Duk falon ita aka zubawa ido, Kanta aqasa tace momy kiyi hakuri, ni yanzu Bana Sansa
Shalele sai kumburi take, wallahi badan Mami tace dole saitazo ba, wallahi da bazata zoba
Anty jidda da Ajmal ne a Dakin nasa, sai gani sukai baqi suna shigowa
Haneef Yana dago kansa yayi ido hudu da shalele, yakafeta da kallo, Ajmal na zungurinsa Amma inaaa🤣🤣hankalin yatafi
Hajiya hafsat na ganin kallan da haneef yake Mata ta fahimci komai, Kenan haneefanta ce take Aiki a gidan su? Kenan haneefa haneef yadauka suka fita qasar waje? Ita din tagani a TV Kenan? Itace momy suka Kora agidansu?
Lalle akwai matsala, dole sai haneef yagane kuransa, aiko ameer dinta ne yadauki haneefa suka tafi wani waje batare da sanin taba dole zata masa hukunci
Dan haka bataga laifin shalele ba, datace Bata sonsa yanzu
Anty jidda tana kallan Samah da Bilal suna hararan juna, tace to yau kuma masifa ce tahadu daa San girma kenan🤣🤣
Tana juyawa taga Ameer Yana satar kallan Safah, itama tana Kallansa qasa qasa 🤣🤣
Tasake juyawa taga shi haneef ya kafe haneefa da kallo
Tayi murmushi wannan tun kafin ayi abin kunya agaban surukai Gara su fice, Allah yaso babu sajidanta 🤣🤣🤣da abin yayi yawa, Dan haka tace daddy, momy, Mami muje waje mudan basu waje
Aikuwa duk suka fice daga Dakin
Suka barsu su biyu
Zama tayi Akan kujerar tana zumbura baki
Shikuwa sai Kallanta yake kamar yaga sabuwar halitta 🤣
Yajita Sarai, murmushi yayi yace congrats Ina tayaki murnar samun mamanki, but banji abinda kike fadaba
Cikin fishi tace cewa nayi ni Bana sonka, kuma abiyani bakina, bazan yardaba
Kallanta yayi yace oh really?
(naji korafinku, kuma ngd Sosai, insha Allah zamuci gaba kamar yanda muka saba, nagode Sosai da kaunarku agareni 🙏🏻)
Wanda sukaga banyi musu refly Akan comment dinsu ba suyi hakuri,massages ne sukamin yawa wallahi
Menene zai faru tsakanin Dr Bilal da Samah? Me damo sarkin hakuri Ameer yake nufi da daya sarkin hakurin Safah?
Anya kuwa Haneef zai Samu haneefa cikin sauqi dangane da furucin hajiya Hafsat?
Muhadu gobe idan Allah ya Ara mana lokaci 😃
Mrs Usman ce✍🏻💕SHALELAN BABA💕
(Romance)
Writing by Amnah El
(🙏🏻kuyi hakuri Dan Allah bisa mistek din Dana Samu jiya wajan rubutu, akwai inda ya goge atsakiya, inda su daddy sukaje suka nemi Bilal, da irin Jan ajin daya musu kafin yakaisu gidan hajiya hafsat, dakuma sabanin da suka Samu shida Samah Har suke hararar juna a asbiti, da irin yanayin da momy tashiga itada daddy lokacin dasuka tabbatar shalele yar'uwarsu ce, sannan ne akayi inda daddy yace a Kirata kuma aka Kirata tace bataso, kungane yanzu? To wajan me ya goge wallahi, babu yanda zan gyara saboda nariga nayi posting dinsa, Amma wasu sunce sun gane ahakan, ngd, dafatan za'a Fahim ceni 🙏🏻)
39&40
Yunqurawa yayi yatashi Yana yamutsa fuska, alamar baijin dadi Sosai
Yataso yazo gaban kujerar da take Kai, ya tsugunna, yakafeta da lumsassun idanunsa, sannan yasaka hannunsa yakama face nata, yamatso da bakinsa dab da nata, Cikin sauri ta qwace Fuskarta, takawar da Kanta gefe, murmushi yayi, kikace nabiyaki bakinki, to tayaya zan biyaki idan banyi Miki irin nada ba?
Kallansa tayi tafashe da Kuka, ta Dora Kanta Akan jinyarta tana Kuka Sosai harda shashsheka, Shikuma gashi a tsugunne a gabanta, Hakan da tayi saiya qara musu kusanci Sosai
Meyasa take Kuka? Anya kuwa su momy basu zagi yarinyar nanba? Jin kukannan nata yake Har cikin ransa, jiyake kamar yajata ya rungume ta a jikinsa ko zaiji dadin lallashinta
Sumar kansa yashafa, yayi ajiyar zuciya, kansa yamatso dab da nata datake sunkuye tana Kuka, saitin kunna ta yasaka bakinsa, "kiyi hakuri, nasan iyayena sun Bata Miki rai, kuma nasan cewa abinda suka Miki ne Nima yashafeni Har kika fadaamin wannan maganar,
(aikwa de hakane shazali tunda a lokacin Ina ganinta ta lumshe ido 🤣🤣🤣)
Yaci gaba da cewa amma kiyi hakuri, nizaki duba basuba, Dani Zaki zauna ki rayu kiyi Zaman aure Dani basu ba, Koda ace kowa baya sonki aduniyar nan ni Ina sonki haneefa, kiduba kiga halin danake ciki, soyaiyarki ce tasa na kwanta a gadon asbiti, kiyi shiru, insha Allah komai zai wuce, watarana su momy zasu soki, kiyi hakuri, kada kisake cewa bakya sona, inba hakaba wallahi zan tabbata a gadon asbitin nan
Yahade hannayensa kiyi hakuri, ki yafewa iyayena 🙏🏻
Adede lokacin iyayen nasu suka dawo Dakin, anty jidda na ganin qaninta a tsugunne agaban shalele mamaki yakamata, lalle soyaiya Mai gyara mutane, yau haneef dinta ne agaban qaramar yarinyar nan, kome yake rokonta? Oho musu
Jin sun shigo dakinne yasa yatashi yakoma gefen gadon sa ya kwanta
Mami tace a a Dana wanne kwanciya kuma Bayan ka ware Sarai, Saida ka ganmu zaka koma Kan gado ka nade 🤣🤣
Duk Dakin sukai Daria
Daddy yayi gyaran murya yace to alhmdlh, godia ta tabbata ga Allah daya bamu ikon haduwa a wannan wajan, yadubi shalele da idanunta sukai jajir saboda Kuka yace Haneefa takanki zan fara, kiyi hakuri dangane da sabanin fahimta da aka saamu, munsan cewa mu masu laifi ne agareki, Amma kiyi hakuri komai ya wuce, kada kisake cewa bakya son haneef, Koda bakya yimasa so na aure aayanzu Kam haneef dan'uwanki ne, dole Zaki soshi kuyi zumunci
Kiyi hakuri kinji yata? Ahankali ta share qwallar idonta, tadaga masa Kai, haneef Yana Kallanta, bayasan kukannan datake, jiyake kamar Shima yayi, Amma tayaya ta zama yar'uwarsa?
Daddy yakatse masa tunani da fadin, haneef, Samah, Safah, dakuma ke jidda, Haneefa yar'uwarku ce, itace yar gidan qanwar mahaifiyar ku, ke jidda da haneef zaku Iya saninta, nasan iklas da fadilama zasu Santa, yanayin rayuwa ne yasa tazo Aiki gidanmu, kuma alhmdlh mungodewa Allah dayasa zuwan nata yazama me mana alkhairi gaba dayanmu,
Sannan ya nuna musu Mami yace nasan kun Santa, duk da ba ziyartar juna akeba, wannan itace wadda suke ciki daya da zainab mahaifiyar haneefa, ga babban danta Ameer, dakuma qaramar Afrah
Hajiya hafsat kiyi hakuri, munsan cewa abin babu dadi, Amma idan Zaki duba zakiga komai yafaru ne bisa rashin Sani, kuma munyi DANA SANI Akan Hakan
Mami tace babu komai Alhaji, Allah yakiyaye gaba, Dukansu sukace amin, doctor yazo zai duba jikin haneef sai gani yayi daki yacika dam da mutane, yace a a, yau ko Dan qaramin biki ake a Dakin ne?
Ajmal yace ai wannan yawuce qarami doctor saide babba 🤣
Yace to masha Allah, Bari na dubashi, Yana juyawa sai yaga Dr Bilal, yace a a kamar babban doctor nake gani
Bilal yayi murmushi yace wallahi nine, nazo ganin marar lafiya ne tare da yata
Wacece yar taka? Yanuna haneefa yace gatanan a zaune, ai itace yarinyar da marar lafiyar taka yake nema
Cikin Daria doctor yace alhmdlh, gaskiya naji dadi, to ai kawai Bari nabaku waaje saika dubashi
Dr Bilal yace a a haba doctor qarasa aikinka wlhy, Nima daganan wucewa zanyi nakoma wajan aiki
Likitan ya dubi daddy yace Alhaji wannan abokin aikinmu ne, Amma sune manyanmu, Aida nasan kun sanshi da tun farko ma can wajansa zan turaku
Samah tayi sauri tace ai doctor nan dinma yayi, mungode
Tajuya ta kalli Dr Bilal tasaakar masa harara, Shima anasa bangaren hararar yasakar Mata
Doctor na dubashi yace zasu Iya tafiya, idan wani Abu yataso zasu Iya zuwa wajan Dr Bilal
Tashi sukai suka tafi, haneef farin ciki yacikashi, ashe ma yar'uwarsa ce, aikuma yanzu maganar momy taqare, saura ta daddy, Shima insha Allah komai zai wuce
Suna zuwa harabar hospital din, momy tace ai hajiya hafsat saimu wuce gida gaba daya ko, Kinga yau sai mu wuni tare
Mami tace hajiya muje
Shalele ko kallan haneef batayi, Ana cewa a shiga Mota ma cikin sauri tashige, haneef na ganinta, yasan saboda shi take komai
Suka tafi gidan suma, direct part din haneef sukayi, Ajmal yace lover boy, yanzu shikkenan ka ware ko? Wai Dan Allah abokina me kake rada Matane muka shigo Dakin
Hararar sa yayi yace to bazadai kajiba, wannan sirrin Wanda suka kusan shiga daga ciki ne 🤣
To idan tayi tsami maji☺
Ai bazatayi Bama
Ameer yayi Daria yace wa Ajmal tokai kaji sai kayi hakuri sirrinsu ne
Ajmal yace rabu dashi Ameer, zaiyi bayani ne
********
Yanmatan Dukansu suna dakinsu Samah, afra ta miqe agado tana daddanna waya, Samah takamo hannun shalele tace kiyi hakuri yar'uwata, nasan nayi Miki laifi Mai yawa, Amma kiyi hakuri ki yafemin, Kodan yayana da yar'uwata
Nima wannan masifar tawa tana damuna wani lokacin 🤣🤣wallahi, kuma duk saurayinki ne yagogamin wallahi, dan Bahaka yanbiyu na takeba Safah
Afrah Tai Daria takalli shalele tace toke saiki zauna tana fadawa saurayinki magana
Murmushi tayi tace babu komai Safah, Allah yakiyaye gaba kuma
Bari inje wajan baba Hanne, ta yunkura tatashi, Samah tariqeta tace a a wallahi, babu inda zakai zama zakiyi muyi fira
Safah tace ni wallahi harna matsu ma Inga aurenku keda Yaya, saboda Inga yanda zai nuna Miki soyaiya, idan kaganshi haka kamar bazai yiba
Amma nasan mutane masu shiru shirun nan, sun Iya soyaiya Sosai, akwai lokacin Dana ganku afalo kuna Daria, sainaga kamar ba yayan Dana saniba
Samah tace Nima sun birgeni lokacin Dana gansu afalo tana mopping Shikuma Yana gefenta yawani Matso Yana Mata rada, baki gansu ba wallahi
Afrah tace Amma ku kuwa kuncika Yan sa'ido wallahi 🤣
Samah tace a a barmu mugani, taa kalli shalele tace wannan baban naki yacika son girma dayawa wallahi, kamar shi yafi kowa, jiyafa da zamuje gidan Mami nazauna akusa dashi amota wallahi haka yasa kafa ya danne min kafata, bakiji zafi ba, gashi fari tass Amma zuciyar sa baqa😏
Shalele tace kede Samah kifadamin gaskiya idan kina ciki, Kinga Dan fari zubin larabawa
Haba de sister haneefa, harfa cewa yayi zai zaneni, idan na aureshi kuma ai dukana zaiyi
Afrah tace Nima ina ganin ku a asbiti kuna hararan juna, wasu kuwa kallan kallo suke qasa qasa waisu ustazai 🤣🤣
Safah tayi murmushi laaa Wai Yaya ameer ke babu komai wallahi, kawai Kallansa nayi sai aka Dace Shima ya kalleni
Afrah tace um wannan kallo kuwa da yawa yake🤣🤣
Samah tace waike Afrah dawa za'a yi?
Saida tayi fari da idonta 🙄wallahi wani Dan abokin daddy ne, Yana Lagos, a India nahadu dashi
To Allah yakaimu musha biki, inji shalele
Duk sukai caaa akanta, bikinku de
Rufe kunna ta tayi tace nashiga uku, to naji🤣
********
Dukansu sun hadu a dining suna cin abinci, haneef Kam babu kunya yaje ya zauna akusa da kujerar da shalele take
Sunacin abincin wasu na satar kallan juna su ameer Kenan 🤣
Wasu kuma suna Saka ido irinsu afraah da Ajmal 🤣🤣
Shikam haneef ko kallan shalele bayayi, itama haka
Mutanan wajan kuwa kowa Yana mamakin wannan sharewa tasu, shi kansa Ajmal yayi mamaki
Garin Kalle kallan nasa yaje ya qware🤣
Yafara Tari,ya sunkuya yariqe kirji
Safah dake kusa dashi tabashi ruwa
Wai kawai dagowar dazaiyi saiyaga kafar haneef Akan ta haneefa 🤣🤣tab gaskiya shazali Dan duniya ne
Shine asama ya nunawa mutane babu ruwansa da ita, Amma daga qasa Yana abinda yaso, ashe shiyasa ya maqa daga gefen ta
Shazali na ganin Ajmal yaqi dagowa yasan cewa yaga komai
Safah tace Yaya Ajmal ga ruwan, sannu
Dagowa yayi yace yawwa qanwata, ya kalli haneef, kallan nasan komai 🤣
Shima yadaka masa harara
Yaci gaba da shafa kafarta da tashi kafar, Sarai tana jinsa, Amma ta shareshi, duk wani iri takeji, tajanye kafarta yasake Dora Mata, kowa ya kalleshi bazaice wani Abu yana faru ba, Amma itakam ta naji ajikinta, sai kuma Ajmal daya gansu🤣🤣
Al'amarinsa Yafara fin karfinta, Bata isa tace yabiyata ba🤣, tunda dazu ma data fadi haka taga abinda ya biyo baya
Dan haka ta share shi, Har suka Gama, da zasu tafi ameer yakoma wajan Mami ya yi Mata rada
Tace Dan Allah ameer ya kyaleni
Momy tace meyake faruwa ne hajiya hafsat?
Ameer naji momy tayi magana yayi wuf yafice daga falon
Mami tace tun dazu Yaron nan yadameni Wai a fadawa daddy shi Yana son yanbiyu, shine yanzu yake sake cemin Wai kada namanta de🤣
Safah kuwa kamar tashige cikin qasa Dan kunya, cikin gudu Takoma dakinsu 🤣
Momy tace to ai shikkenan, kuma menene abin boye boye baanda abin ameer, ai Dani yasamu Kai tsaye ya fadawa
Mami tace ai ameer dakike ganinsa Har yafi wata macen kunya
Momy tace ita ma Safah haka take, Allah yasa ayi Damu
Duk sukace amin
Momy tace Amma de hajiya ai zakibar shalele anan gidan kukutafi ko, tunda Dama anan take
Mami tayi murmushi ai hajiya an maidata makaranta, gobe zata fara zuwa, yauma abinda yasa batajeba saboda zuwanmu nan ne
Lokaci daya kunya takama momy, meyasa ma tayi wannan tambayar, duk Zaman yarinyar agidansu Basu taba tunanin Sakata a school ba, Allah de yakiyaye gaba
Tace toshikknn yaushe abbansu zai dawo?
Gobe zai dawo
Toshknn Allah yakaimu, muma zamuzo idan yadawo din
Haka suka tashi suka fara haramar tafiya, haneef ya matsa kusa da Afrah yace qanwata idan kunje gida Dan Allah kice tabude wayarta
Afrah Tai Daria tace to yayanmu
Shalele taje kusa da anty jidda tace mama zamu tafi, kicewa sajida da ayaz zan kirasu
Aimunyi fishi haneefa
Kiyi hakuri mama, naso nazo gidanki Bayan nabar nan, Amma kiyi hakuri,
Toshikknn haneefa ki kiramu iidaan kunje
Duk sukai rakosu wajan Mota, suka shiga suka tafi, Ajmal da haneef sukayi hanyar part din haneef din
Ajmal yace Wai Naga mutuniyar taka sai fishi take dakai
Meyake faruwa ne Naga mutuniyar taka sai basar wa take
Murmushi yayi, zata Dena, fishi take Dani
Ajmal ansamu abinda akeso, shide arayuwarsa Yana so yadinga Jin dramarsu 🤣🤣🤣
Yace fishin me?
Wai fishi take saboda nayi kissing dinta
Kiss haneef😳😳
Innalillahi....
To sarkin kwakwazo, menene aciki danna fadama gaskiya, kissing dinta nayi, shiyasa take fishi kuma nabata hakuri, itama abin dayasata fishin nasan abinda su momy suka Mata ne, Amma a lokacin ai batama nunamin komai ba,
Ajmal yace lalle haneef Kai Dan duniya, inbanda iskanci kayi abun kazo kana fadaamin haka
To Kai nasan me kakeyi da yata?
A a a a, mezan Mata shazali? Inda nine nayi Mata ai sai ka daure ni
Babu wani dauri Ajmal, kawai ni abinda nasani shine da inje inyi Abu aboye, Gara inyishi afili, Wanda suka nuna basayi din ai ba'asan me sukeyi aboye ba, itama kuma nasan fishi ne yasata fadar haka, insha Allah zata yi hakuri
Ajmal yace eto kanada gaskiya
To shine take fishi, Wai dazu ma ita Bata sona, nabiyata bakinta
Me Ajmal zaiyi inba Daria ba, bakin zaka biyata?
Haneef yace to yarintarfa, Aida ta tsaya Dana biyata, kaga daga nan ma nasake tsotsa
A a shazali kafi karfina, wannan Gara ayi muku auren nan muhuta
Ayima na gaba daya de muhuta, dan renin wayo
********
Bayan kwana biyu su daddy sukaje gidan hajiya hafsat, nemawa haneef auren haneefa shida makusantan abokansa
Daddy yace to Alhaji Tahir, kaji kaji abinda yakawomu
Alhaji Tahir yace to ai Alhaji bukar, wannan ba abin damuwa bane,saide wannan yarinyar akwai babanta Bayan ni, mahaifinta tun kafin yarasu yace yabashi ita halak Malak yariqe ta amatsayin Uba, dan haka Bari nakirashi nasanar dashi halin da ake ciki, nan kuwa aka Kira Bilal yace zaizo daga baya, yabashi Dama yayi komai, ai Shima mahaifinta ne,
Nan daddyn Afrah yayi masa godia yaakashe wayar, sannan yadubi su Alhaji bukar yace, Dama Nima inaso inzo da tawagata nemawa Dana ameer auren yar wajan ka