Inna tace Kinga hijabin naki ma jini yataba gefensa, kawo aje awanke Miki shi
Dasauri baba yace a a, karbi de kibayar dashi, Ko maqotane karbi kibasu, ita sai asake mata wani
Dama ai ya tsufa hijabi aka saka shi Har tsawon wata daya Kuma ai yaci duniya, sai ayi hakuri dashi
Inna tace to maigida tana fita Daga dakin, Shima fita yayi yace mata zanje wajan Malam yahai yarakani can cikin kasuwa, insha Allah yanzu zamu dawo
Inna tace to maigida a dawo lafiya
Yana fita Bai zarce ko'inaba Sai gidan maqocinsa Malam yahai, ya daukeshi suka wuce kasuwa, wajan masu Saida machine yaje yasiyo Sabo dal dashi, sai daukan ido yake, Daga nan suka juyo gida, inna na alwala taganshi yana kiciniyar shigowa da machine (ππ)
Tsaye ta miqe tana daura Dan kwalin kanta daya kunce saboda shafar Kai datayi wajan daura alwala
A a Malam lafiya naganka da machine? Mezakayi dashi Ko acaba zaka koma ja? Yanzu Malam saboda Allah duk Yawan gonakin da Allah yabaka basu ishekaba saika siyo mashin kafara kabu-kabu?
Kansa yadafe da hannunsa alamun maganar Tata harta gundureshi (π€¦π»ββ)
Haba Marka! Haba Marka!
Yanzu wannan tambayoyin dakika jeromin tayaya zan fara baki amsa?
To wannan mashin dakika ga naje nasiyo, bani zanyi kabu-kabu dashi ba, Shalele nah nasiyowa shi, saboda adinga kaita makaranta Ana daukota, munyi magana da Likitan daya wanke mata kafa dazu yace ita mace ce, yakamata tadena Hawa Keke hakanan, saboda gudun matsala
To shiyasa naje nasiyo wannan mashin, nadauka mata Yaron dazai dinga kaita makaranta yana Zuwa yana dauko mana ita, shikuma zan dinga bashi dubu biyar duk Watan duniya (π³ππ» fan's)
Inna da mamaki yagama kashe ta atsaye tace Anya maigida? Anya maigida turbar dakake Dora Shalele akai kuwa me dorewa ce? Yanzu Malam duk gidan nan baka saka mana kayan kallo ba, Amma ita kasaka mata, katifar damuke kwanta haqarqarinmu akai ta tsufa, baka sake manaba Amma ta Shalele Bata shekara, Malam itafa mace ce, duk Daren dadewa gidan wani zata
Ajiyar zuciya yasauke yace, eh lalle Marka sai yau ta tabbatar da abinda nake zargi, Marka zarginki nake akan kulawar danake Bawa yarki ta tsaye Miki a maqoshi ya qarasa maganar yana Dora hannunsa awayansa
Wai shin, Shalele tarbiya ta rasa Ko nutsuwa? Addini tarasa Ko ilmi,? Tataba yi miki rashin kunya? Marka abinda nakeso ki Gane shine, zan Iya sadaukar da komai nawa saboda Shalele nah, ita kadai Allah yabani, Dan haka Marka, yakama kunnansa guda daya yace Iya gani....?
Itama tayi qwafa cikin fishi tace masa Iya qyalewa
Tana Daga cikin dakinta tana jiyo maganganun iyayen nata, inda Sabo yaci ace tasaba da irin wanan fadan nasu, Murmushi tayi Ahankali tace baba da inna ta Kenan
Shikuwa yana idar da sallar magrib yadawo gida shida wata yarinya Amma ta girmi su Shalele sosai, inna Tana rumfa ta idar da sallah tana lazimi tagansu sun shigo, da mamaki tace a a Ramatu kece a gidan namu?
Kafin inna tayi magana baba yace a a Ramatu ki fada mata gaskiya Cewa Zuwa nayi wajan mahaifinki Malam yahai na dauko ki, ki kula da Shalele Tunda ita uwarta tafara gajiya da ita
Murmushi inna tayi tace Malam Kenan, sannan ta dubi Ramatu tace Ramatu wuce ki koma gida kinji, kice Ina babar Taki, Ramatu Saida ta kalli inda baba yake taga yadaga Kai sama alamun akusa yake, sannan tace to inna natafi, Allah yaqara kiyayewa gaba
Amin, inji baba
Ramatu na fita inna tace yanzu maigida saboda Allah kaje Har gida kasako yarinya agaba saboda kawai tazo ta kula da Shalele? Koka manta zawarci take? Kabarta Taji danata yaran mana
, inde akan Shalele ne kayi hakuri insha Allah zan kula da ita, nayima wannan alqawarin
Sai a sannan yasakko Daga dokin naqin dayahau, suka cigaba da firar duniya
Da daddare Yan makarantarsu Shalele sukazo dubawa Ko lafiya yau basu ganta a Islamiya ba, malamai Sai tambayar ta suke, kasancewar yarinya ce ita Mai kokari da hazaqa, kokarin ta ne yasa dayawa Daga cikin malaman nasu take mutuqar birgesu
Bayan sunga ciwon dataji ne suka mata sannu tareda tafiya gida
*******
Shalele kafa ta warke sosai, taci gaba da Zuwa makaranta, Daga bangaren baba babu wani Abu daya sauya wajan Yanda yake nuna mata kulawa
Yau inna ta tashi da zazzabi sosai, akwance ta wuni, Shalele duk ta damu, baba ne yadauki machine din daya siyowa Shalele yakai inna qaramin asbitin Garin, suna Zuwa kuwa likita ya tabbatar musu da Cewa inna nada ciki harna tsawon wata uku da Rabi, baba Kamar yayi hauka Dan murna, itade inna Murmushi tayi, domin kuwa ta riga da tasan dama tana dashi, haka suka dawo gida da wannan daddadan labari, Shalele naji ta dinga ihu da tsallan murna, itama zata samu kanwa Ko Kani
Ko a Islamiya data Bawa qawayenta labari, mamaki sukai tayi, ganin yanda take murna, Kodan Bata ganin yaran ne a gidan su oho
*******
Tilin kayan wanki ne a hannunta ta futo dashi Daga daki, Daga murya tayi ta qwalawa Shalele kira
Shalele!
Shalele!!
Da gudu ta futo Daga daki kanta Ko Dan kwali babu tace na'am inna gani
Watso mata kayan wankin tayi tace gashi nan maza dauke kije ki wanke minsu gaba daya, ta Cilla mata nera hamsin, taci gaba d Cewa ki dauki kudin nan kifita waje shagon ubaliyo ki siyo kilin kiyi maza ki wanke su ki shanya
Shalele Bata kawo komai aranta ba dasauri ta dauka tace to inna, asalima ita murna take akan wankin da aka Bata kasancewar bayi take ba, Bata wani aikin fari bare na baki
Hijabin ta tadauka zunbulele ta fita taje ta siyo kilin din tadawo tahau kan wanki, ta nayi Ahankali harde ta ware tafara dirzar kaya, rana tazo tatarar da ita Har inda take sunkuye tana wankin, gumi sai zirarowa yake Daga kanta
Inna Tana kallanta tadora kafa daya Kan daya, tana girgiza jiki, alamun ashirye take d kowa, kara ta riqe a hannunta tana karkadawa tana Kallan Shalele da Rana take gasawa
Baba yayi sallama yashigo gidan, turus ya tsaya yana Kallan Shalele, itama dasauri tace baba sannu da Zuwa
Da mamaki afuskarsa yace, a a Shalele nah kece kike wanki yau Kuma?
Bata bashi amsa ba sai Daria datayi alamun Ko ajikin ta
Qarasawa yayi cikin rumfar inna take zaune tana kallansu d'ai-d'ai
Yace mezan gani haka Marka?
Asheqale inna t kalleshi tace au Wai danna saka Shalele wanki? Masassara ce ta kamani shiyasa Naga bazan Iyaba nabata, Ko akwai damuwa akan Hakan?
(nikwa nace tofa wata sabuwa πmeyake shirin faruwa a gidan baba ne?
Please Dan Allah Sharhi da comments ππ»
Amnanku ce βπ»
πSHALELAN BABAπ
(Romance)
Writing by Amnah El
7&8
Baba yace babu damuwa, Allah yabaki lafiya
Ko ajikinta tace amin
Shalele nagama wankin ta shanya, tace inna nagama
Can ciki ta amsa mata, alamun aikin bewani dadata da qasa ba
Baba ya kalleta shide duk mamaki yakama shi
Be gama mamaki ba yaji tace, idan kinyi ga tukwane can, kije kidora abincin dare
Dasauri tace Kai inna tun yanzu? Bazai huceba kuwa?
Haka nayi niyya, idan zakiyi kiyi, idan Kuma ban Isa nasaki bane saiki fadamin
Jin wannan furucin nata ne yasa jikin Shalele yayi mutuqar sanyi, dariyar yaqe tayi tace a a Bari in Dora
Shikuwa baba yayi Shiru yanaso yaga gudun ruwan Marka, yaga yau wani take take takeji na rashin mutunci acikin gidansa
Wanke tukwanan tayi ta Dora tuwo da miya, dayake girkin nasu bawani me yawa bane nan da nan tagama, a lokacin baba yana Daga cikin daki yana jiyosu, tazo tace inna angama Shima
Tana karka da kafa tace saiki share gidan ai, ba Tsayawa zakiyi akaina kina kallo ba
Daga murya yayi daga cikin dakin yace ke Shalele, kama hanya ki shirya kitafi islamiyya, kada wanda yake daukar ki Yazo yaga yau kinyi latti
Saida ta kalli inna, Ko zata ce wani Abu, Taji innan tayi Shiru, danhaka tashige cikin dakinta domin shiryawa, tana shigewa ta riqe bayanta alamun wajan ya amsa, saboda rashin Sabo da aiki, agogon dakin ta kalla da sauri ta tashi tashirya cikin uniform dinta, tadau jakar da littattafan islamiyyar suke ciki ta futo, tace inna natafi
, Amma Kamar da qasa take magana, haka inna ta shareta, baba yasake Daga murya yace jeki Shalele nah, Allah yakaremin ke a duk inda kike, Allah yabada sa'ah, Saida tasaki Murmushi saboda jin dadin adduar dayayi mata sannan tace amin baba, tafice da sauri, Zuciyar ta cunkushe da tunanin laifin me tayiwa innarta take wannan fishin da ita, aide aiki ne tabata Kuma tayi, Amma meyasa yau gaba daya ta sauya mata Kamar ba innarta ba?
Acan makaranta ma, anayi musu akdari haka malamin yagama yafita Amma abinda ta fahimta Dan qalilan ne, sabira qawar ta dake gefenta, ta fahimci ba kalau takeba, Dan haka tace HANEEFA SURAJ ADAM, meyake damunki ne yau gaba daya Kamar kina tunani
Ajiyar zuciya tasauke tace wallahi sabira, inna ce yau take fishi Dani, Bansan me nayi mataba
Kafadarta ta dafa tace haba de, keda innarki da ba'a jin kanku? Nafi tunanin wani laifin kikai mata, wanda ke baki saniba
Tace wallahi sabira babu abinda yafaru yau dinnan de
Sabira tace to idan kin koma gida kibata hakuri, insha Allah komai zai wuce, Amma yanzu de ki nutsu akan karatun daya kawomu
Murmushi tayi tace to Qawata godia nake
Cikin gida kuwa Shalele na fita inna tahau fada, amma de Malam kasan abinda kake yi a gidan nan baka kyauta wa Ko? Yanzu Kenan ni ban Isa da wannan yarinyar ba? Shikkenan komai sai abinda kace zatayi? Yarinya babu wanda isa da ita, harni zansa ta aiki Amma kasa yarinya qanqanuwa ta bijiremin
Hularsa yake kokarin sakawa da alama fita zaiyi, yace yanzu Marka mekike so ince dake? Yarinyar Nan de kina gani lokacin tafiyar ta islamiyya ne yayi, yanzu Marka saboda aiki can maras tushe zan daure mata gindi akan ta zauna tayi aiki kada taje makaranta? Toni bazan dauki wannan ba, idan ma wasu ne Daga gefe suke hure Miki kunne to kifada musu sudena, ba'a gidanaba, yana gama fadar haka yasakai yafice yabar mata gidan
Yana fita inna tafashe da kuka, akan Shalele yake fada mata wannan maganganun? Hakika yau tayi DANA SANIN auren surajo, ita Kuma Shalelen ai zata dawo gidan ta sameta, da ita suke zancen
Shalele na dawowa gida gab da magrib tayi sallama tace inna nadawo
Daqyar ta bude baki tace Aina ganki
Murmushi tayi, aranta tace inna Bata huce ba Kenan, buta tadauka ta shiga bayi tayi tsarki, sannan ta futo tayi alwala, tabarmar da inna take zaune anan taje tatada kabbarar sallah, tana idarwa tace inna kiyi hakuri
Mekikamin dazaki bani hakuri
Shalele tace Naga yau duk ranki abace yake, Bansan laifin danayi Miki ba innata Amma kiyi hakuri
Aikin nunamin ban Isa dakeba haneefa, inda na isa dake bazan sakaki aiki kiqi yiba
Da tsananin mamaki afuskarta ta kalli innar Tata, yau inna ce Dakanta take kiranta da Haneefa?
Meyake faruwa ne? Kota manta ne baba yace Sunan mahaifiyarsa ne? Amma Tafadi sunan haka Kai tsaye?
Murmushin dole ta qirqiro tace to inna kiyi hakuri, Bari in tashi in share gidan, kiyi hakuri
Yunqurawa tayi zata tashi, tana tsammanin inna zatace dare yayi tabarshi, Amma sai Taji sabanin haka, domin kuwa inna amsa tabata da Cewa "Dade yafi Miki"
Share gidan tayi tsaf, Daga nan tashige dakinta take ta aikin kuka, Bata sababa, batasan metayiwa inna haka me zafi ba
Koda baba yadawo ma, bece inna takawo masa abinci ba, Shalele ya qwalawa kira taje takai masa abincin sa, haka de ta kwanta ranar jikinta duk yayi sanyi, baba kuwa Baisan abinda yayi yaqara qona ran inna ba, haka nan takejin wata irin tsanar Shalele aranta
*******
Washe gari dataje makarantar islamiyya, haka take fadawa sabira Cewa tabawa inna hakuri fa Amma babu abinda yasauya, sabira tace "kedan bakya karanta littafin hausa nefa, infada Miki akwai wani Novel Dana taba karantawa naji ance Wai masu ciki wani lokacin cikin yana sakasu masifa"
Shalele tace "Dan Allah da gaske kike?"
Sosai makuwa, inji sabira
Hauka da yarinta irin tasu yasaka Shalele yarda da maganar qawarta
********
Kwanci tashi babu wuya awajan Allah cikin inna ya tsufa, daqyar take zama daqyar take tashi, halin datake nunawa Shalele kuwa babu abinda yasauya saide ma qaruwa dayayi, baba yana lura da duk wani take takenta, jira kawai yake yaga ta haihu lafiya, yanzun yana Daga mata kafa ne akan larurar datake jikinta,sauqin Shalele daya, shine makaranta datake Zuwa da safe, dayake yanzun Suna ss1 ne, Amma dazaran tadawo gida tofa babu zama, aiki ne zai biyo baya, tun maganar sabira na yaudararta akan Cewa haka masu ciki suke Har abin yadawo Bata mamaki, domin kuwa qarara inna take nuna tsanar datake yimata
********
Yau takama Laraba, Kuma a yaune inna ta haihu da namiji, baba yayi mutuqar farin ciki, daya Daga cikin qannan inna ne sukazo domin temaka mata
Kayan da akayi haihuwar dashi, aka Bata da jini murja ta meqo mata shi, tana zaune a tsakar gida, ta dungurar da bahon tace ke gashinan dauki kije ki wanke shi
Shalele Bata kawo komai aranta ba, asalima murnar tasamu qani yahana bakinta rufuwa, daukar bahon tayi tace to anty murja, tashige bayi dashi, kwata Kwata batada qyanqyami haka ta wanke wannan kayan jinin tas, ta shanya, ta wanke hannunta da omo, dakin innar Tata ta shiga hankalinta yanaga Yaron tace anty nagama, tameqa hannu zata dauki jaririn
Dasauri inna tasa hannu tace mezaki masa? Kinga barmin yaro na, bazakije ki jagwalgwala Shiba, Har yaushe da hankalina zan Bari ki dauke shi
Idan akwai abinda yafi sanyin jiki Tona Shalele yayi, Kallan anty murja tayi Ko zata yi magana Amma Bata sami komai Daga wajan murja bama sai amsar harara
Haka tataso ta futo jiki asanyaye, salalo salalo
Awannan Karon Kam Bata Iya tsaida hawayen dayake shirin zubo mataba, kuka ta zauna ta rizga, idanunta sukayi jajir, tanajin baba yashigo yabawa murja sako yace murja ga wannan ki dafa mata Ko zataji dadinsa, yafice
Yana fita anty murja ta qwala mata kira, dasauri ta goge hawayen idonta tace gani anty murja, ledar da Baba yabawa murja ta wullo mata Har naman dayake ciki yafara zubewa, tace dauki wannan wulaqantaccen naman ki wanke kidorashi awuta
Wulaqantacce? Naman da baban nata yafita yasiyo da kudin sa ake Kira sa Wulaqantacce?
Batada ikon magana haka tadauka taje ta wanke shi, tadora awuta, albasa ta yanka aciki tasa Maggi da gishiri dasu citta, nan da nan kuwa Qamshi yafara tashi
Haka ta zauna Saida dafawa inna naman, sannan tazuba mata shi a flas, takai tace inna gashi, Ko azuba Miki?
Hararar ta murja tayi tace ke awa? Eye nace ke awa? Kinga jeki ni karki cinyeni da wannan idanun naki me kama Dana mage, gayyar na ayya
Haka yafuto Daga dakin ranta duk ajagule, inna kuwa da harara tabita, tun kafin ta zauna, inna da kanta ta qwala mata kira tace Haneefa futo kidora muku abinci keda ubanki
Ahankali tace "nida ubana"
Sake futowa tayi, tadora musu abincin harta qare, zama tayi domin ta huta, ta tuna da shara, Gara ma tayi, saboda inma batayiba zasu sake tasota
Tana gama sharar, tahada kwanukan gidan zata wanke, randar gidan ta bude taga babu ruwa, taje gaban dakin inna, suna zaune itada murja sun bararraje sunacin farfesun data dafa, cikin tsoron fadansu tace inna dama zanyi wanke wanke ne shine Naga babu ruwa acikin randar
Banza sukayi da ita, babu wanda ya tanka mata acikinsu
Kallansu tayi tasake Cewa Inn... Bata qarasa fadar sunan ba, innar ta hayaiyaqo mata, to Haneefa Bari nazo nasaka hijabi na nadebo Miki ruwan kinji, tsaya gani nan Zuwa
Jiki ba qwari tabar kofar Dakin, dakinta taje tadau hijabi, tazari boket tafice Daga gidan, tuqa tuqa taje tadebo ruwan tadawo, tana dawowa ta shigo zauren gidan tahadu da Baba
Kallanta yayi yace menake gani haka Shalele nah?
Murmushi tayi tace baba babu ruwa a gidan, Kuma baka nan, naduba wajan baba Malam Kuma baka nan shine nace kawai Bari nadebo
"sauke bokitin nan "abinda yace mata Kenan
Laaa baba babu nauyi fa
" nace ki sauke "
Bata sake magana ba ta sauke boket din, yasa hannu yadauka yace mata muje cikin gidan
Itace tayi gaba, yabiyota Abaya, tun kafin su karasa shiga yafara qwalawa inna kira
Marka! Marka!!
Tana Daga cikin dakin ta amsa tace Malam inajinka
Marka wanne irin rashin adalci ne wannan zaki saka Shalele diban ruwa? Har me zakiyi da ruwan dazabaki tsaya nadawo gidan nadauko muku ba?
To yanzu Malam nikakeso nasaka hijabi naje nadebo mata ruwan? Bafa ayimin adalci acikin gidan nan ehe
Qwafa yayi be sake cemata komai ba, yanufi randa yazuba ruwan, sannan yajuya zai ficedaga gidan ya kalli Shalele da ke tsaye Kamar kazar da qwai yafashewa aciki, cikin tausasa murya yace karna qara ganin kinfita waje wani diban ruwa, inde ba makaranta zakiba, bakason naqara ganinki da makayin diban ruwa kinji Shalele nah
Batace masa komai ba illa girgiza masa Mai datayi alamun to
Yana fita inna tadaka mata wata uwar Hararar datasa Shalele sunkuyar da kanta qasa Kamar wata munafuka
Ruwan da Baba yajuye aranda ta Diba tafara wanke kwanukan datayi amfani dasu
********
Ranar Suna yaro yaci sunan kakan Shalele na wajan uwa, mahaifin inna Kenan Abdallah
Amma inna na kiransa da aududu (π€£)
Anyi taron Suna lafiya angama kalau, taro yayi taro, inda baba yayanka wa inna raguna Har biyu saboda hidimar Suna
Yau baba yana gida, suna zaune Dukansu arumfa anty murja Takoma gidan ta, Aududu ne yayi fitsari inna tace Haneefa zoki sakawa Yaron nan ruwa yayi fitsari
Baba ya kalleta da tsananin mamaki, Ko kadan yanzu Bata shakkar fadar sunan mahaifiyarsa agabansa, Ko babu komai ai sirikarta ce, duk da bata a Raye
Hannunta ta dauraye Daga wankin tsarin tuwonsu datake yi, tazo tadauki Yaron ta wanke masa jikinsa, tasaka masa wani