Suna idar wa Marka ta sunkuyar da kanta qasa Kamar ta Allah, baba Malam yace yanzu Marka Yaya za'ai? Kina ganin za'a raba gadon Malam surajo ne abawa danki ka sonsa ku kama hanya kutafi gida kokuma Yaya?
Hawayen baqin ciki yazubo mata, tace yanzu Malam yahai ba wannan ne agabana ba, Dan Allah kakiramin Shalele na roqi yafiyarta, wacce irin mace ce ni ace mijina ya mutu da baqin ciki na? Dan Allah ka temaka kakiramin ita
Malam yahai yatashi yaleqa ta katanga yakira Shalele, Aikuwa tasaka hijabi ta futo, tana zuwa inna tafashe da kuka tace kiyafemin Shalele, wallahi ni kaina nasan nacutar dake, kiyi hakuri ki yafemin yata
Ahankali yace to inna nayafe Miki, Allah yayafe mana baki daya
Baba Malam yace to Allah yayi Miki albarka
Dr Bilal yace Amma na kunna wannan wayar babu layi akai, Kuma akwai number damuke San kira acikin wayar
Dasauri Shalele ta dago kanta ta kalleshi cikin faduwar gaba, yanzu Yaya zatayi Kenan?
Marka tayi Murmushi tace, wayar Malam a kashe take yaro, banma taba kunna taba bare nasan akwai layi aciki Ko babu, ni kuwa dagani Har Shalele Bai siya mana wayaba
Dr Bilal yace Innalillahi.... Lokaci daya idanunsa sukai jajir
Gaba dayansu suka bita da kallo, Shalele mamaki yakamata, dama inna ma tasan yayar mamanta? Amma shine Bata taba nunawa ba?
Dr Bilal yace eh inasan ganinta dasauri
Marka tace kada kadamu, Aina fadama Nima Kamar uwa nake wajan Shalele, nayi nadamar abinda nayi mata Abaya, Kuma inde wannan ne karka damu, nasan Hajiya Hafsat, Kuma nayima alqawarin gobe Ko jibi zata gana da Shalele, zansa akai Shalele Har wajanta
Bilal yace Kinga malama ki tsaida mana rana daya, in gobe gobe, in jibi jibi inzo indaukeku amotata muje Dani da Malam yahai muganewa idonmu gidan
Marka to shknn nayima alqawarin kadawo jibi, saimuje gaba dayanmu, sauran magana ta gado Kuma akwai Malam yahai akusa
Dahaka tattaunawar tasu taqare, Baba Malam yace to Shalele tashi mu tafi wajan sabuwa saiki kwana acan, dasauri Marka tace a a ba za'a yi hakaba, Malam yahai nifa Naga Kamar baka yarda daniba, Dan Allah kabarta ta kwana awajena, muyi firar yaushe Gamo, kaga tasamu damar dazata hada Yan kaiyaiyakinta ma
Dr Bilal yace zata kwana, Amma karki yarda kiyi mata wani Abu, idan kika cutar da yarinyar Nan nadawo jibi tasanar Dani ranki zaiyi mummunan baci, inna tace na yarda, wallahi na yarda Dana
Dahaka suka futo Daga gidan shida baba Malam, Shalele Saida tarakoshi Har kofar gida, tace uncle ka gaida su Hajiya, zuba mata ido yayi baice komai ba, baba Malam yana ganin haka yayi Murmushi yashige gidan sa, cikin ransa yana Fatan ace soyaiya ce a tsakaninsu
Tace uncle yakayi Shiru
Hankali nane Bai kwanta da matar nan ba, kina ganin zaki Iya kwana kuwa?
Zan Iya uncle, Koda zataci gaba da ganamin azaba zan jure, Tunda kwana dayane kawai, inma naji bazan jure ba, aiko ta katanga zan dira gidan baba Malam
Daria sukayi gaba dayansu, jin wannan maganar Tata, yace to shknn saina dawo jibin, Ko akwai abinda kike buqata?
Tace a a uncle babu komai, yace to Saida safe yashiga mota yatafi, Saida ta jima Awaje tana Kallan motarsa harta qule sannan ta juya ta shiga gidan
Inna Tana ganin ta tace zo Shalele, adarare ta qarasa tabarmar ta zauna, inna akace kiyi hakuri kinji? Munyi rashin Malam dagani harke saide mu bishi da Addu'ah, ahankali tace hakane inna
Anty murja tace Haneefa kiyi hakuri Dan Allah akan abinda yafaru Abaya, tace babu komai anty
Inna tace to Bari muyi sallar ishsha'i, kema kije dakinki kihuta, ta tashi tashige dakinta, suna idar wa ta kunce gefen zaninta ta dauko Sim card din baba tasaka abakinta ta tauneshi, murja tana kallanta tasaki Murmushi
Tace murja tashi kirakani wani waje, Tunda Allah yayi banida rabon takaba, Daga murya tayi tace Shalele zanje nan maqota nadawo kinji yata
Dasauri ta futo tace to inna saikun dawo, suna fita ta zauna atabarmar tsakar gidan, tatafi duniyar tunani, Allah Allah take jibi tayi taganta awajan dangin mamanta, haka kawai duk da yarinya ce Taji wannan tuban na inna Bai shigetaba, yanzu menene mafita Yaya zatai ta dauke Aududu? Ta wacce hanya?
Su inna Suna fita, ta Cewa murja, ai tarkona yagama ci murja, Allah yakaimu gobe kiga aiki da cika wa, yanzu de rakani gidan ladidi tijara yar Abuja jiya tazomin gaisuwa nasan tana gari,
Sun dauki hanyar gidan ladidi suka hadu da yawale qaninsu wani tantirin mashayi, yawale yace nida nake shirin Zuwa wajan ki kiban na sigari, Marka tace to kaje ka jirani ganinan Zuwa
Yana tafiya murja tace Anya Yaya kina ganin kuwa bazai yiwa yarinyar Nan wani Abu ba? Marka tace kyaleshi yaje, Shima yasamu rabon sa, Aikuwa suka sheqe da Daria suka tafa, suka shiga gidan ladidi, Marka tafara Koro mata kwanan zance dakuma abinda yakawo su wajanta, babu wata wata ladidi tace ta amince, tadauki kudi dubu hamsin tabawa Marka, suka juyo gida
********
Acan gida kuwa yawale yana Zuwa ya kwala sallama Daga soron gidan, Shalele ta leqa tace a a kawu yawale (dayake haka take fada masa)
Yana ganinta haka babu hijabi yaji ya kwadaitu da ita, yajuya bayansa yaga babu kowa, ya lashe baki saikace baqin maye, yace a a Shalele, ashe kin dawo
Eh Wlhy kawu nadawo dazu
Ya matso kusa da ita yace Shalele Shalele, wato dama akwai wata magana data Dade tanacin dunduniyar zuciyata🤣inaso nafada Miki Amma nakasa
Da mamaki tace to inajin ka
Matsota yasakeyi Har yana gogar jikinta, dasauri ta matsa baya, yayi sauri yamata kyakkyawan riqo yace wallahi Ina sonki Shalele, zaro ido tayi ta rufe bakinta da hannunta 😳🤭tace mekace kawu?
Shikuwa yana ganin ta Dage hannunta yayi zuruf yasaka hannunsa Akan kirjinta, Yan madaidaitan na shanunta yakama yafara matsewa
Ai Shalele najin haka tadaga hannu Iya karfinta ta maka masa bugu akansa, tsinanne kasakeni nace, azzalumi, Allah ya isa na, wuta balbal Dan iska
Ta kwasa da gudu tashige dakinta, tasaka sakata, sai huci take, jikinta ko'ina yana rawa
Tana jinsa Yazo gaban dakin nata yadaga murya Yanda zata jishi yace yarinya dakin tsaya kema aida kinji dadi, abin nakima babu laushin kirki da alama nine nafara tabawa, saide Kuma da alama zasuyi girma sosai, kinyiwa kanki, yajuya yafice Daga gidan
Tanajin fitar sa tasaki Ajiyar zuciya, Bai Dade da fita ba su inna suka dawo, tanajin ta tana kwala mata kira, tadaga murya tace inna zazzabi nakeji na kwanta Saida safe
********
Washe gari da safe ta shiga gidan baba Malam suka gaisa, sannan tadawo gida, babu wani Abu da inna ta nuna mata, suna zaune lafiya, Har la'asar, ta shiga daki tana sallar la'asar inna tace Shalele!!!! Dasauri tashafa Addu'ah ta futo, tana futowa taga inna dawata mata gabjejiya, taci kwalliya taci uban mayafi, ta Cewa matar Ina wuni
Ladidi tace lafiya, sannan ta kalli Marka tace to ni zan wuce Marka, inna Marka tace Shalele baki gane wannan bako? Daga Abuja take, maqociyar Hajiya Hafsat ce yayar mamanki, jiya muka hadu nake cemata muma ai Gobe zamuzo
Cikin tsananin murna tace laaaaa Dan Allah kinsan yayar mamata? Ladidi tace yanzu hakama dazaki bini Har wajanta zan kaiki
Inna tace ah meze Hana, Shalele kawai kibita, Tunda muma gobe zamu biyo bayanku dasu Malam yahai, saiki dauki wasu kayan ma kiyi gaba dasu, sauran nakawo Miki goben
Dasauri tace to, tashige dakinta Bata dauki komai ba sai kayanta Kala biyu da photon baba, ta futo suka tafi, inna tace insha Allah muma da safe zaki ganmu kinji? Shalele cikin murna tace to inna saikun zo
Sun futo Daga gidan ta dubi ladidi tace Dan Allah zanyi sallama dasu baba Malam, ladidi tace to shiga amma kiyi sauri
Shalele tashige gidan baba Malam ta inna sabuwa Ina baba Malam, sabuwa tace Malam yafita Shalele, Ina zaki da kaya ahannu?
Tace Abuja zamu, inya dawo kice masa sai sunzo
Inna sabuwa Malam yahai baiyi mata bayanin komai ba jiya, tayi tunanin da wannan baqon likita zasu tafi, danhaka tace to Allah yakiyaye Shalele, tace amin tafice da gudu
Suna fita suka yi bakin titi, suka tare mota suka shiga sai cikin Abuja, tafiya anayi da dadi ba dadi Har dare, mota duk aragargaje, tun tana Kallan hanya harta dawo ta daina ta kwantar da kanta acinyar ta
Sai dare suka isa gidan ladidi, gidane Dan qarami Mai kyau madedeci, daki biyu da falo da tsakar gida,ladidi tafada cikin kujerun falon nata tace wash Allah nagaji wallahi
Shalele kuwa ta zauna akan hannun kujera tace Toni intafi idan kin huta kyazo? Inane gidan Daga ciki? Nagaba ne kokuma wannan na Bayan damuka Bari?
Ladidi ta kalleta tace kije Ina? To Marka aikatau tace nadauko ki nakawo ki Abuja
Kekam Shalele kina ganin dalala 🤣🤣🤣
(tab gaskiya gobe akwai kafce, 💪🏻, menene zai faru idan Bilal Yazo ya iske wannan labari? Anshaqe mata wuya ma yayi mari to inaga ya nemi yarsa 😃😃😃😃yarasa??
Yaya makomar inna Marka gobe?
Duk kubiyoni gobe danjin mezai kaya
Dan Allah Sharhi da comments 👏🏻
Amnanku ce ✍🏻
💕SHALELAN BABA💕
(Romance)
Writing by Amnah El
17&18
Tsananin mamaki ne yahanata magana, aikatau? Batasan lokacin data zame dagakan hannun kujerar datake zaune ba, sai jinta tayi jagwab aqasa
Ladidi tijara tace menene abin faduwa, nabata dubu hamsin kudin aikinki Kenan na wata daya, saboda akan haka nake bada farashin yaran danake bayarwa aiki
Zuwa yanzu Kam Zuciyar ta ta tsike, idanunta qamas babu alamar kuka, meta yiwa inna Marka ne haka datakesan ganin bayanta?tukunnama su waye dangin mamanta? Su waye? Huci tafara Kamar zakanya, idan tayi karatu tazama lauya! Idan tayi karatu tazama lauya saita kashe inna Marka (😠😣😠gaskiya Shalele yau rai yakai mutuqar baci)
Ladidi tijara ganin yarinya ita kadai tana huci Kamar kububuwa tace, zaki dakenine saboda nafada Miki gaskiya? Kinga yarinya ni babu abinda yadameni dake, bazaki rasa ci da shaba agidana, Abu daya nasani bazan barki kije ko'ina ba, batare dakin biyani kudi naba, ki danqamin dubu hamsin indanqa Miki kudin Mota kikoma gidan ku, inba haka ba kuwa Sunana ladidi tijara wallahi tijara zan nuna Miki
Hawaye ne yazubo mata, Bana komai bane saina haushin kanta dataji saboda rashin karbar number uncle Bilal jiya, Allah sarki, yanzu haka yaji ajikinsa ne bazai sake ganinaba shiyasa jiya yacemin shi tuban inna Bai kwanta masa Arai ba
Hannu tasa ta goge hawayen idonta, yanzu Kam Ko ance mata ga hanya Takoma Garin kuje babu inda zata, da masifar yawale zataji Daga karshe ma ya lalata mata rayuwa kokuma da rashin dangin uwa da uba? Yanzu dama inna batasan inda dangin mamanta suke ba shine jiya tayi tuban muzuru ta nuna musu zata kaisu gidan?
Bazata taba komawa kujeba sai tayi aikin da inna ta Dora ta akai, tasamu kudi tazama lauya, Daga karshe taje takashe ta
Allah yakareka Aududu, Allah yakareka a duk inda kake
Kayan hannunta ta zubar aqasan ledar falon ta futo tsakar gida, ladidi na kallanta batace komai ba, aranta tace yarinya bani kudi na, nabaki hanya
Ita kuwa Shalele alwala tadauro tadawo falon ta kunce Dan kwalin kanta ta shinfida tafara rama sallolin dake kanta na magrib da ishsha'i
Ta Dade tana ma kanta Addu'ah itada Aududu, sannan tashafa, ladidi ta tashi takawo mata abinci jallop din shinkafa tace ga abinci kici, girgiza kanta tayi batare da tace mata komai ba, tabe baki tayi ta dauke abincin ta
Awannan wajan datayi sallah anan ta kwana, ladidi tabata wajan kwanciya tayi banza ta qyale ta, itama kuwa ta shareta tashige daki ta dauko katifa babba tashinfida a falon tayi kwanciyar ta, Shalele na zaune akan Dan kwalin ta, anan wajan tazame ta kwanta itama
********
Washe gari da safe wajan karfe goma, wani Alhaji yayi sallama yashigo sai kada key din motar dake hannunsa yake, Bayan sun gaisa da ladidi yace ladidi akwai yarinya kuwa wadda zata dinga yiwa iyalaina wanki da guga ? Shalele tana jinsa tana zaune agefe Ko ina kwana batayi masaba (lalle Shalele ankaita karshe😅😂🤣)
Dasauri ladidi tayi zuruf tace ah haba Alhaji Yusuf ai ba'a rasasu a gidan nan, Bana rabo dasu ai, yanzu ma ga wata nan a zaune idan tayima, ta nuna masa Shalele 😃😃kallanta yayi, yaga yarinya Kamar dutse Ko motsi batayi, yace no ladidi wannan tayi qarama dayawa, bazata Iya daukar nauyin aikin gidanaba, zan dawo wani lokacin Ko za'a samu wata, haka yafice,Shalele tabi bayansa da harara, Dan renin hankali, in banda ma rayuwa harya isa ya kalleta yace tayi masa wanki? Tona ubanta ma batayiba bare nawasu iyalansa😀😃😀
ladidi tazubawa Shalele ido, tayi qwafa
********
Sabuwa yi kokari ki daukomin asuwaki na a daki in samu in fita kofar gida injira Yaron nan likita, nasan yanzu duk inda yake yakusa Zuwa mutafi
Sabuwa tace a a Malam Ina zakuje? Yace Abuja zamu shiga, zamu Kai Shalele wajan yayar mahaifiyar ta
A a Malam ba jiya jiya shi Likitan Yazo yadauki shalelan ba da yamma? Jiya tazo tamin sallama zata tafi,harma ta tambayeka nace kafita, Dama batare take dashi ba?
Gaban Malam yahai yafadi yace Wai wacce shalelan kike nufi ne sabuwa? 😳
Sabuwa tace Shalele nawa ce damu Malam?
To meyasa baki sanar daniba tun jiya sabuwa?
Kamarya? Wai kana nufin baka saniba?
Wajan zama yanema yazauna jagwab aqasa yadafe kansa dake masa ciwon nan take yace sabuwa kin kasheni🤦🏻♂🙆🏻♂😃
*******
Nnamdi Azikiwe international Airport
Cikin takunsa na qaqqarfan namiji yafuto Daga cikin Airport din, yana dauke da brief case dinsa ahannu
Matum biyu ne majiya karfi suka qaraso gareshi da sauri, daya Daga ciki yayi sauri yakarbi jakar hannunsa, dayan kuwa sai muzurai yake yana Kalle Kalle awajan
Kamar kullum yauma wankan Suit yayi, Amma fara, sosai yayi masifar kyau, Kamar ka saceshi, suna futowa waje yanufi wajan da motocin sa suke jere guda uku, daya Daga cikin guard din ne yayi saurin bude masa motar tsakiyar Prado launin ash color,number motar ansa SHAZALI NO.4 yana shiga suka rufe sukajashi Zuwa gida
Megadi najin dirin motocin yatashi yabude da sauri, suka shigo, bude masa motar sukai yafuto, aka biyo bayansa da brief case dinsa
Saida suka kawo shi Har bakin kofar falon sannan yakarbi jakar sa, yace zaku iya tafiya, yajuya yayi cikin falon
Momy na zaune dawasu yara yanmata guda biyu, daya na danne danne awaya, daya nayiwa wani yaro karami home work
Salamu alaikum
Gaba dayansu suka dubi maiyin sallamar, dasauri yaran suka fara Cewa Yaya sannu d Zuwa, daya tashige daki, itama dayar takama hannun Yaron zasu tafi daki, momy tace ke samah, barmin yarona anan, kude kuje
Murmushi Haneef yayi yace to Yanzu momy ni Daga dawowata kinji nayi musu magana ne?
A a ai Kai dinne halin ka nasani Haneef, yanzu zaka fara masifa babu gaira babu dalili
Murmushi yayi baice mata komai ba dama itama batasa ran zaiyi maganar ba
Tace Yaya tafiya? Ansha Italy
Lallausar sumar kansa yashafa yace momy kwana biyun? Ko kinyi missing Dina ne?
A a wanne missing? Inrasa wazan yi missing sai tsohon tuzuru?
Momy I'm tired, zanje part Dina, dasauri yafice yabar falon yayi part dinsa
Yana shiga tun daga falo ransa yafara baci, hannunsa yasa akujerun falon farare, sannan yaduba hannun yaga qura ajiki
Dakin yashiga, ya cire takalmin kafarsa, Taku daya biyu yayi, sannan yakai dubansa ga safar kafarsa, ya cire safar yayi jifa da ita, yafuto yanufi part din momy rai abace, meyasa yaran nan suka renashi ne? Koda yaushe sude kawai burinsu subar masa dakinsa da datti, daki duk ya lalace ko'ina qura
********
Yana parking motarsa yaga Malam yahai zaune a kofar gida yayi tagumi, futowa yayi daga motar yabashi hannu suka gaisa, yace a a yanaganka a zaune anan, tashi mu qarasa mana, yakamata ai su futo mutafi da wuri
Baba Malam yace likita akwai matsala
Wacce irin matsala Kuma? Meyake faruwa ne? Baba Malam yakwashe komai yafada masa Kamar Yanda sabuwa tabashi labari
Becewa baba Malam komai ba yanufi gidan Marka, baba Malam yayi sauri yariqoshi yace tsaya likita mekake shirin yi?
Baba Zuwa zanyi intisa qeyar Marka takaini gidan da takaimin yarinya, domin na tabbata dole akwai saka hannunta aciki, nide banzo na dauke taba, Toda wanne shege zatayi tafiya? (tofa kaji masu yarinya😃😀🤣)
Baba Malam ya lura idan yabar Yaron nan yashiga to za'ai batacciya Dan haka yace muje, muje wajanta tare
Suna shiga gidan kuwa inna na zaune Atsakar gida, ta Dora kafa daya Kan daya, tana ganinsu ta turo Dan kwalin ta Gaba, dama tasan wannan lokacin yana nan Zuwa
Bilal sai huci yake yace ke Ina Haneefa?
Kallansa tayi asheqe tace oho
Zaki fadamin inda take kokuma saina dauki hukunci dakaina?
Tashi tayi tsaye tace ai Bansan Kai qaramin Dan iska bane sai yanzu, kana nufin shekaran jiya Marin dakamin yatashi a banza Kenan? To fansa nadauka, ni Bansan wata Hajiya Hafsat ba, sunan ta kawai nakeji awajan surajo, Sim card dinsa Kuma nice nacireshi na taune, sannan Haneefa dakake tambaya naturata aikatau birni, Bansan awacce duniya takeba yanzu sannan..... Kafin taci gaba da wata maganar ya cire belt din jikinsa yafara dukanta dashi
Ihunta sabuwa Taji, itama tayafa mayafi tabiyo bayansu, Malam yahai tatarar yana riqe Bilal wanda yake dukan Marka haiqam Kamar Allah ya aikoshi, dasauri ta cire mayafinta taci damara dashi, tafara kokarin cetar inna Marka, daqyar Malam yahai ya tsaida Bilal Daga dukan Marka, ransa abace yana huci yafice yabar gidan jikin motarsa ya tsaya, wannan matar meyasa batada Imani ne?
Dasauri yadauko wayarsa yakira police, sannan ne yaji ransa yadan fara yin sanyi, yana tsaye a kofar gidan Har Saida motar police din tazo sannan ya nuna musu gidan, Aikuwa suka shiga aka tisa qeyar inna Marka, Shima yabisu Abaya tareda sabuwa da Malam yahai duk suka rankaya Zuwa police station din
********
Yana komawa part din momy yagansu sundawo falon gaba dayansu, nunasu yayi da hannu yace ku!!! Dukansu suka kalleshi lokaci daya cike da tsoron masifar sa
Ni zaku yiwa rashin kunya Ko? Yaushe nafara wasa daku? Eye