x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - HEEDAYAH

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 115649 words

Category: Love Stories

Views 124

22 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
soyayyar mijin ki baxai bar ni inyi hakan ba..." Tana fadin haka ta ja hannun Heedayah suka fita xuwa gun mai gadi tace "Salisu ka tattaro abokanan ka masu gadi ka fitar min da wasu mashaya da suka shigo min gida, and from henceforth duk wanda ya xo ka fara sanar min kafin ya shigo" da sauri ya fita yin yanda tace.


Start patronizing Heedayah lovely fans.... last free update later at night in sha Allah😍

07087865788.....



⚡ _Heedayah_⚡






_By Khaleesat Haiydar_✍🏻





Tun da Hajiya Maryam suka dawo gida da kawayenta take kuka kamar ranta xai fita, ji take kamar ta bude ido taga cewar duk mafarki take, ya xa ayi Barrister ya mata kishiya bata mutu ba?? Hajiya kyauta tace "Ke Maryam bari ki ji in gaya maki, idan xaki share hawayen ki ki san nayi ki share, don 6ata lkcn ki kawai kike, wllh wannan kukan baxai fisshe ki ba, wajen nan dai da baki son xuwa dolen ki nan xa aje da ke yau a san nayi, don wnn mata ni dai da kamar wuya mijin ki ya fasa aurenta duk haukan ki kuwa, na farko in dai kyau ne baxa ki nuna mata komai ba, ke diplomar ma da ya kika kare? Ita kuwa lawyer ce fa me xaman kanta, kinga kenan ta kure karatu, ga shi da gani dai kin san ba cikin wahala take ba tana da kudin ta, ke dake buga buga ki raruma gun miji fa?? ni wllh ba karamin kwarjini matar ta min ba ma, da ba ku fito ba dama ni wucewata xan yi kar ta sa a daure mu kamar yanda tace" Hajiya Maryam ta katse ta a fusace tace "Ni fa da ku ke gani nan babu abinda ya isa kai ni gun malami a duniyar nan, ku dai ku bar ni inyi ta kai na kawai idan baxa ku bani shawara ba, ni kadai raina na ishi kowa, wllh karuwar nan baxata shigo min gida a matsayin kishiya ba, muna nan da ku kuma xa ku ce na fada, ita kuma wnn makauniyar dama sai dai ta kara shiga duniya wani ya tsince ta a wani garin amma ba mijina ba...." Tana kai wa nan ta mike ta dau gyalenta tana share idonta, Hajiya Sadiya tayi wani dariya tana kallon kyauta tace "Bar ta, xata dawo ta same mu ne ai" Ficewa Hajiya Maryam tayi daga dakin rike da makullin motar ta..... Direct gidan Dr Umar ta nufa, yau dai ko shiga bangaren matan gidan bata yi ba ta nufi gun kaka, da sallama ta bude kofar parlon kaka dake uwar daka ta fito da sauri tana cewa "huuu Ko waye don Allah ya share kafarsa ga tsumma na ajiye bakin kofa, wllh kazamai ne matan gidan ko sharan kirki basa yi a makeken parlon nan nasu sai a tattako a xo a yasar min a nawa parlon...." Hajiya Maryam ta dinga goge kafarta a tsummar kamar an aikota, kaka tace "Aa Maryam daga ina haka da sassafe kuma" Ta karasa cikin parlon ta xauna kasa cikin sanyin murya tace "Daga gida kaka, ina kwana" Kaka ta xauna tace "Lafiya dai naga idonki a kukkumbure ko Balaraba ce ta rasu??" Ta fashe da matsanancin kuka tace "Ba lafiya ba wllh kaka...." Kaka tace "Ikon Allah me ke faruwa Kuma? Ni dai jiya Amadu ya shigo min da rana wai ya xo gaisheni a nan kuma yake ce min wai aure xai kara har ya samu matar yar kaduna ce, ni dai nace masa ba ruwana, ana xaune lafiya fitina ya shigo ciki, to daga haka ni bai ce min ga abinda ke faruwa a gidansa ba...." Cikin kuka sosai Mumy tace "Abinda ya kawo ni kenan ma kaka, wai aure fa xai kara...." Kaka ta saki salati tana tafe hannu tace "Ohh ni na ga abinda ya isheni ni Rahamar ubangiji, me Amadu ke nema a duniya da xai kara aure ana xaune qlau, ni dai yana gaya min ce mashi nayi ba ruwana, don bn san kan xancen ba...." Mumy ta share idonta tace "Idan ma sbda wnn baiwar Allahn ce ya kawota kawai xan riketa na amince" iyakar wnn furucin da Mumy tayi bakinta, don kuwa ta sha alwashin ko an fasa auren aka kawo mata Heedayah sai ta sake lulawa da ita wani duniyar daban, duniyar ma na kauye, can xata sa aje a wurgar da ita don ma kada mistakenly wani me rufin asiri ya dauketa har ya taimaka mata, a yanxu dai duniya bbu wanda taji tana tsana kamar wnn yar yarinyar, har ta mance rabon ta xubda hawaye ta shiga tashin hankali da xai hanata bacci sai a dalilin Heedayah, Kaka tace "Aa ni ya kawo min ita ma nan kawai xan riketa, kar a ja maki kaffara kina xaman xamanki, dama bbu me min wanke wanke da shara tsigalallun yaran nan duk ba kulasu nake ba ta kaina nake" Mumy tace "Makauniya ce fa kaka" kaka tace "To makafi basa wanke wanke da shara aka ce maki Maryam, ai dai naga ba kuturwa bace, sai in kada mata kumfar in sa mata ruwan dauraya in ajiye mata kwanukan in xaunar da ita ta wanke min su tass" Mumy tace "Aa kaka wahala kawai xata baki, ni din dai xan riketa, ai d'a na kowa ne" Kaka tace "Atoh dai, ki kwantar da hankalin ki kawai, bbu wani xancen kara aure in dai da raina tunda xaki riketa, to idan ba toxarci Amadu ke son mana ba meye kuma karin aure ana xaune kalau, wannan ne kuma bai haifu ba gaskiya don baxan yrda ba" Mumy taji hankalinta ya d'an kwanta, tana share idonta tace "Toh shkkn kaka nagode" Kaka tace "Haba godiyar me kuma, ai yi ma kai ne, yanxu shawarar da xan baki a nan shine ki dau kayan ki kala daya ko biyu ki tafi gidanku, idan ba haka kika yi ba Amadu baxai dawo hankalinsa ba, ki tafi da fitsararrun 'ya yan nan naki ki bar masa gidan ba kowa sae kujerunsa da tv, nan xaki ga ya shiga taitayinsa wllh, kaddai ki gaya ma wnn dunkum din d'an naki kudurin ki don wllh hana ki xai yi ya cuce ki, ki bar masu gidan shi da ubansa kawai" Mumy da ke kallon kaka tana jinjina shawarar ta a ranta, tayi murmushi tace "Gaskiya ne kaka, hakan xan yi in sha Allahu ina komawa kuwa" Kaka tace "Atoh maxa tashi ki tafi tun yanxu ki hada hada kayan, ai mu xamaninmu haka muke yi, idan miji ya musguna maka ka hada kayanka ka bar masa gidan sa, xo ki ga yanda hankalinsa xai tashi kuwa...." Mumy ta mike tace "Toh sai anjima kaka, nagode sosai, Allah ya kara girma, sai mun yi waya" daga haka ta fita, kaka ta bi ta da kallo har ta rufe kofa sannan ta ta6e baki ta juya ta koma cikin dakinta tana cewa "To ai idan Amadu ya fasa auren nan ma ni sai naji dalili wllh, da kaina xan kai sadakin auren, huuu wai ba kunya ba tsoron Allah matar da ke bari na da yunwa me saka min nama tsoka daya ce wannan fa jama'ah, Ehh lallai duniya ya lalace....." Da yammacin ranan Abba ya tafi gidan Barrister Rahinah don sake tabbatar da abinda ta gaya masa a waya da safe, nan ta nuna masa she is serious, ko da wasa bata sanar masa cewar Hajiya Maryam ta xo gidanta ba, yana murmushi yace "Toh nagode Rahinah, in sha Allah gobe xa mu je can gun kawun ki..." Mami tace "Allah ya kai mu...." Basu wani jima ba ta koma cikin gida don tace masa girki take, shi kuma ya wuce. Mumy na komawa gida dama ta hada kayanta ynda Kaka tace mata, ta hada har da na su Khadijah da Rabi'ah ta bar gidan, makarantar su ta fara biyawa ta sanar masu inda xasu sameta idan an tashi sannan ta wuce gidan kanwar Mahaifiyarta dake nan kaduna. Mami ce xaune study area dinta tana kallon files din gabanta, gaba daya mood dinta isn't okay, ta kasa gane ko she is making the right decision marrying barrister, har xuciyarta tana son taimakon Heedayah amma ba irin taimakon da xai kai ta ga aure ba at this stage, ta jinginar da kanta da kujera tana tunanin ta ina xata fara sanar ma yaranta wannan xance me girma, amma kuma ai idan bata Aure Barrister ba ta 6ar matarsa ta ci bulus kenan, ta shigo har gida ta yi mata cin mutunci sannan ta bar ta haka nan, muryar junaid taji yace "Mami aiki kike?" Ta daga kai da sauri ta kallesa don bata ji shigowansa ba ma, ta mayar da glass din da ta sakko idonta tace "Sure, ka shigo kenan" yace "Nayi sallama naji shiru" ya ja kujera ya xauna yace "Mami this two days naga kamar kina da damuwa, meye matsalar ki gaya min" shiru tayi kuma bata daga kai ta kallesa ba, yace "Talk to me Mami" ta sauke ajiyar xuciya tace "Junaid barrister ne ya xo min da xancen da ya saka ni cikin damuwa kwarai, I don't know I am really confuse junaid...." Yana kallonta sosai yace "Me ya faru Mami?" Ta kuma yin shiru, bayan few seconds taga bbu wani amfanin boye boye kuma, nan ta sanar ma d'an nata intention din Barrister Ahmad a kanta, junaid bai iya ya ce komai ba na kusan second talatin, can dai yyi gathering courage ba tare da ya kalleta ba yace "Toh, idan hankalin ki ya kwanta da hakan Mami, Allah ya sa shine mafi alkhairi a gare mu baki daya" kallonsa kawai take bata ce komai ba, ya mike yace "Na xo daukan system dina ne" daga haka ya wuce sama ta bi sa da ido, dakin Farida ya bude, ya ga Heedayah kwance edge din gadon tana bacci, riga ne da wando jikinta kamar dai 'yar turawa, he wondered if she is neva tired of sleeping, karasawa cikin dakin yyi walking slowly ya isa kusa da gadon yana kallonta, a hankali ya mayar da ita tsakiyar gadon ya gyara mata dogon gashinta dake rufe idonta, jin an bude kofar dakin ya mike tsaye da sauri, kafin Mami tace komai yace "A gefen gadon na sameta...." Mami ta gyada masa kai kawai, ya juya ya fita dakin.... Da daddare Barrister ya tafi gidan Yayansa, bayan sun gaisa da kaka yace "Na je can gida na tarar Maryam ta kwashe yara sun bar gidan Baaba" Kaka tace "Kila ganin gida taje...." Shiru yyi yana kallon mahaifiyar tasa, kaka tace "Toh ina dama xata je idan ba ganin gida ba, ai ta kwan biyu bata je ba, kaga kai kuma kafin ta dawo sai amaryarka tayi kokari ta tare xuwa nan da ranan juma'ah tunda yau talata, wannan makeken bangaren da nake sauka sai ka sa a gyara ma amaryar ayi fenti da komai da komai kawai, ita kuma Maryam ban ce ka kirata ba balle kace xaka mata fada, uwarta taje gani...." shigowar Baffa ya sa Kaka tayi gum, ta sauya xancenta. Ranan juma'ah aka daura auren Barrister Ahmad da Barrister Rahinah, though they did it in a confidential way, bbu wani gayya, duk abubuwan nan dake faruwa Hajiya Maryam na can ta lula xuwa gidan wata childhood frnd dinta a Zaria tare da su Rabi'ah wai kar barrister ya biyota gidan kanwar mamarta, ita a dole sai ta basa wahala, Shuraim kadai take kira don samun update, sai dai me? Shi ma bai san da auren ba sai a ranan juma'ar, shi ma kuma da asuba Abban nasa ya sanar masa a masallaci da suka hadu, he was so shock ya ma kasa cewa Abban nasa komai, haka nan Abba ya wuce ya bar sa wajen a tsaye, ita kanta Hajiya Amina mum din su Sudais ranan ta ji xancen daurin auren daga bakin Baffa da safe, nan tayi ta kiran Hajiya Maryam amma wayarta a kashe, bata fasa kira ba har sai da aka daura wnn aure amma bata samu Mumy ba..... Washegarin ranan da ya kasance Saturday Mami xata koma can gidan Barrister Ahmad, shopping suka tafi tare da Heedayah, Farida da First daughter dinta Amira dake aure a Abuja, su dai sun yi farin ciki da auren mahaifiyar tasu kilan hakan ya rage mata damuwa sosai, don duk sun san barrister Ahmad, A cikin mota Amira tace "Kinga yanxu Mami sai ki bar ni mu tafi da Farida sai ta dinga xuwa maki hutu kawai ko" Mami dake ta tunanin makomar autar tata tun bayan da aka daura aure don bata ta6a jin tafiya da ita gidan barrister ba, baxai ma yiwu bane, ta kalli Amira tace "Alright dear" Amira na dariya tace "Kinga cikin ruwan sanyi kin bani ita" Babban shopping mall Mami tayi parking suka fita, Amira na rike da hannun Heedayah suka shiga ciki gaba daya, shopping sosai Mami tayi, yaranta na taya ta, Mami da ta lura Heedayah ta gaji da jan ta da ake ta yi, duk ta yi wani laushi, kana ganinta kasan ko kadan bata sa6a da wahala ba koma wani iri, Mami tayi murmushi ta samu kujera nan kusa da counter ta xaunar da ita sannan ta koma gun yaranta, a kan idon wani mutumi dake tsaye shelf din turare yana diba, ya cire glasses dinsa yana kallon Heedayah sannan ya kalli Mami da ta sha corner xuwa gun su Amira....




End of free pages


The book Heedayah is 300 via transfer

Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment 07087865788

No regrets....
Patronize ur novelist lovely fans, Allah ya maku albarka ya raba ku da iyaye lafiya...💖



Mutumin ya ajiye turaren hannunsa ya isa gun Heedayah ya tsaya dab da ita yana kallonta bayan yyi make sure bbu me kallonsu yace "How are you?" Juyowa Heedayah tayi da sauri, lkci daya ta mike tana waige waige, shi dai bai sake cewa komai ba yana kallonta, kamar xata yi kuka tace "ka dawo xaka kai ni gun Ammina ne?" Jin shiru, ta kai hannu to see if he is still there, komawa gefe yyi yace "Ina Ammin taki take?" Tace "A can gidan Yakumbo mana" xai yi magana ya ga Mami ta tsaya daga inda take tana kallonsu, lkci daya ya juya ya koma shelf din turaren da ya baro, Mami ta nufo Heedayah da sauri ta kamo hannunta tace "Me yake ce maki?" Heedayah da ta 6ata fuska xata yi kuka tace "shine ya sa ni a bicycle muka tafi..." Mami ta juya wajen da taga Mutumin ya tafi taga wajen wayam, da ido duk ta bi wajen amma bata ga alamarsa ba, Heedayah da hawaye ya cika idonta tace "Baya son inje wajen Ammina" kama hannunta Mami tayi suka bar wajen har sannan tana kalle kallen mall din ko xata ga wannan mutumi, sai da suka biya abubuwan da suka siya sannan suka tafi mota, Mami na kallon Heedayah tace "But ya akayi kika san shi ne?" Tace "Na ji voice dinsa, shine...." Mami bata kuma cewa komai ba har suka bar shopping mall din. Bayan Magrib Shuraim ya iso gida, rabonsa da gidan tun jiya juma'ah da safe, dama ko wajen daurin auren Abban nasa ma bai je ba, sau daya ya kalli motar Abban nasa dake parking space ya dauke kai, ya fita motarsa ya rufe ya wuce xuwa entrance din gidan, bbu kowa parlon, ya tafi parlon Abbansa, sallama yyi still standing at the door, Abba dake rike da makullin mota alamar xai fita ne, ya amsa masa sallama sannan ya bude kofar ya shiga, Heedayah ce xaune parlon kan lallausan carpet da plate din watermelon a gabanta tana sha, kasa karasawa parlon yyi tun da ya ga Heedayah, sai da Abba ya daga kai ya kallesa sannan cike da kasaita ya karasa ciki, gaba daya bbu wani annuri a fuskarsa, can gefe ya duka yace "Ina yini Abba" Abba yace "Lafiya lau" mikewa yyi ya nufi kofa Abba ya bi sa da ido har ya fita, a compound Abba ya samesa xaune shi dai bai ce masa komai ba ya fita da motarsa da nufin maida Heedayah can gidan Mami. Washegari lahadi Abba ya tafi can gidan Mami don ranan xasu tafi gidan Baffa Mami su gaisa da kaka, Abba ne ke driving Mami na gaban motar Heedayah kuma na baya a xaune, jifa jifa suke magana da ya shafi field din aikinsu, Mami dake danna wayarta ta kalli barrister tace "Hope ba dadewa xa mu yi ba wajen mama coz xa mu yi sallama da Amira nan da sha biyu xa su wuce" Abba ya d'an yi shiru kafin yace "I mean it Rahinah... Farida baxata je Abuja ba, are you trying to show ni ban isa riketa ba" Mami tace "A'a ae hutu xata je, in sha Allah xata dawo soon..." Yace "Wani hutun?" tace "Mid term...." Yace "Am damn serious baxata xauna Abuja ba" Mami tayi murmushi tace "To shkkn" a haka suka isa gidan Baffa, bayan Abba yyi parking ya juya yana kallon Heedayah da tayi lamo jikin motar, yace "Heedayah" ta xauna da kyau da sauri tace "Abba" murmushi yyi yace "Hope
ba bacci xa ki yi ba" ta girgixa kai tace "A'a" Ya kalli Mami da ke kallonta ita ma, Mami tayi murmushi tace "Heedayah is more than lazy, tafi son tayi ta bacci" Shiru Abba yyi bayan few seconds yyi kasa da murya yace "Look Rahinah... my mother can be very weird at times kin san ynda tsoffi suke, I know she will welcome you wholeheartedly but.... Akwai halin tsufa dai, so get prepared Mamin Heedayah and Farida...." murmushi kawai tayi, ya bude motar ya fita, ita ma ta fita ta sakko da Heedayah, main parlor Mami ta xauna tana amsa gaisuwan da Yan matan gidan ke mata, Hajiya Hauwa dake kitchen ta fito don ganin su waye, ganin Abba tace "Sannu da xuwa barrister" yace "Sannu Hajiya Jiddah ya gidan" tace "Gida Alhmdllh" da fara'a tana kallon Mami tace "Sannu da xuwa Hajiya, sannun ku da xuwa"
End Ads