ta amsa gaisuwan mai aikin sannan ta kama hannun Heedayah suka koma ciki ta kulle kofar, Mami na kallon Heedayah tace "Ina me koya maki karatun?" Heedayah tace "Mami bai koya min komai ba" Mami tace "Me yasa?" Heedayah ta 6ata fuska tace "Mami mugu ne, I don't like him to teach me anymore...." Mami dai bata ce komai ba ta wuce can bedroom da ita, Heedayah tace "Mami he is wicked, ni nafi son wannan din nan ya koya min" Mami tace "Wa?" Shiru Heedayah tayi sai kuma tace "Yace min sunansa Fatima shi ma, kilan baya son gaya min sunansa" Mami na kallonta tace "A ina yake?" Heedayah tace "Wanda ya xo jiya ya tafi da ni" Mami tace "Sunansa Junaid, but you call him Yaya" tace "To, na fi son Yaya ya dinga koya min" Mami bata kuma cewa komai ba ta xaunar da ita saman gado tace "Kwanta kiyi baccin ki xan je in hada maki breakfast" daga haka ta fita dakin, Heedayah ta kwanta. Mami na tsaye kitchen su Rabi'ah suka shigo ajiye plates da cups da suka yi breakfast duk suka fice bbu wanda yace mata komai, ta gama dafa Indomie da kwai da shayi da take yi ma Heedayah ta fito kitchen din, a parlor ta tadda Abba alamar he is going out kuma ita yake jira ta fito kitchen, yana kallonta yace "Ina Heedayah, bata gaisheni ba yau" Mami tace "Let me bring her" daga haka ta wuce bangarenta, Duk wannan abun Mumy na ta kai komo parlon kai kace wani abu take yi, Abba dai bai ce mata komai ba don har ranan bata gaishesa bata masa magana a gidan, Yana ta tsaye parlon Shuraim ya fito shi ma xai fita, Abba yace "Yaushe rabon ka je gaida kaka Aliyu?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Abba bana dawowa da wuri ne ynxu" Abba yace "Ohk yau ka je ko da kuwa tsakar dare ka dawo, and you go with Heedayah ita ma ta gaisheta, she is complaining ba a kai ta ba jiya da naje...." Shuraim ya kalli Abba, amma bai ce komai ba, Abba yace "Su Khadijah ma nace idan sun dawo islamiyya su wuce can, so idan ka je sai ku dawo tare gaba daya" Mami ce ta karaso rike da Heedayah, Abba na kallonta ya dafa kanta yace "How are you dear?" Tace "Good morning Abba" yace "Morning Daughter, kun yi karatun yau koh?" Ai ko rufe baki Abba bai yi ba Shuraim ya nufi kofa, Heedayah tace "A'a bai min ba" Abba ya kalli Shuraim da har ya isa kofa cikin tsawa yace "Aliyu" Mumy ta karaso cikin parlon da sauri tace "Ba gane Aliyu ba?? Shi Aliyun malami ne ko kuma makafi na haifosa ya xo ya dinga yi ma karatu, kaga a gaskiya barrister ku tsaya iya Lane din ku kai da Sabuwar matarka da makauniyar ka a gidan nan, ku fita harkarta da ta 'ya yana, Yaushe aka sa Shuraim ya dinga koya mata karatu bani da labari? Kanninsa da suka fito ciki daya ma an ga yana koya masu karatu balle makauniya, to wllh ni a kiyayeni a gidan nan, ku bar ni kawai yanda ku ka gan ni ayi ta tafiya a haka kar ku kai ni bango...." Abba yana kallon Shuraim da kyau yace "Me na ce maka jiya da asuba?" Yyi kasa da kai bai ce komai ba, Abba yace "Good, idan kana son ganin the other side of me ka sake tsallake magana ta a gidan nan, wllh sai dai ka tafi wani gidan uban amma ba wannan gidan ba, yanda uwarka ta isa ta fada maka kaji, haka nima, idan kuwa watsar da maganata xaka dinga yi a kan wani banxa son xuciya na uwarka to you have to change anoda father and anoda home, Kuma ni nayi instructing dinka ka dinga koya ma Heedayah karatun qur'ani in har ka isa ka tsallake instruction din in gani" A mugun fusace Mumy tace "To sai me don kace ya canja uba ya bar gidan nan?? Kansa farau barrister? Ai ba abun mamaki bane don ka fadi haka tunda an gama da kai an shanye ka, nan gaba mu ma duk kora mu xaka yi ka cika gidan nan da agololi da 'ya yan tsintuwa, Kuma in har ni na haifesa baxai koya ma wata makauniya karatu ba tunda ban ce yaje xai gani ba" Dariya Mami tayi ta kama hannun Heedayah ta koma bangarenta tana girgixa kai, Shuraim dai bai iya yace komai ba, ya juya ya nufi kofa ya fice daga parlon, Banda kallon Mumy bbu abinda Abba yake as if thinking of how to punish her, cike da neman fitina tace "Ehh ka kalleni da kyau, cewa nayi in dai ni Maryam ina gidan nan wllh wllh Shuraim baxai koya ma wata shegiyar makauniya karatu ba, uwar me ya hada da ita xaka ce ya koya mata karatu???" Calmly Abba yace "Maryam ki tafi gidanku sai na neme ki, bana son in dawo in tarar da ke gidan nan don wllh in har na dawo na same ki a cikin gidana to na sake ki...." Yana fadin haka ya nufi kofa walking just as the barrister he is, Mumy ta bude baki ta bi sa da kallo a sanyaye ta kasa cewa komai.... Kuka bbu irin wanda Mumy bata yi ba a dakinta, ta kira duk kawayenta ta sanar masu abinda ake ciki, Hajiya Sadiya ce ta samu karshe a waya, Hajiya Sadiya ta dinga salati tana cewa "Ki tafi gida kuma?? Anya kan barrister daya kuwa, yaushe kika dawo daga gidan xai ce ki koma? Ehh lallai bbu lafiya, ba dai kin tsaya fi'ili wai ke baxa ki je a nema maki taimako ba, ke da kika fi kowa imani, to wllh taki ta sameki, shegiya nake idan haka yar bokon nan ta shigo maki gida, wllh da shirinta ta shigo, lafiyayyen shiri kuwa, mance komai xaki yi Maryam mu tafi mu san nayi kafin lkci ya kure maki, ba fa karamin case bane wnn wllh, tunda kike da barrister ya ta6a cewa ki tafi gidanku, ki xauna fa kiyi naxari, to wllh ana dab da kwace maki gida da mijin ki, wnn makauniya dai ta jaza maki abubuwa iri iri a rayuwa, duk ita ce silar faruwar komai" kuka kawai Mumy take kamar ranta xai fita tana cewa "Wlh Sadiya na canxa xuciyata xan iya kashe yarinyar nan idan hakan kadai ne mafita gareni, ta tarwatsa min farin ciki, ta tarwatsa min gida, a kanta barrister yake min duk abubuwan nan, ga kishiya ta sa an rangada min...." Sadiya tace "Bbu wani lkcn kuka da kumfar baki Maryam, ki dau duk abubuwan da kike bukata ki baro gidan nan kafin ya dawo saki ya tabbata a kanki, ki taho nan gidana mu san abun yi cikin gaggawa, maxa ki fita daga gidan, Kuma a gaban yar bokon yace ki tafi gida?" Mumy ta kara rushewa da kuka tace "Wa ya sani ma ko tana labe duk tana ji, ni dai ga ni nan xuwa ynxu" daga haka ta katse wayar ta shiga hada yan kayanta da sauri kar barrister ya dawo, cikin mintunan da basu wuce goma ba ta bar gidan xuwa gidan Sadiya. Mami na xaune parlonta misalin karfe biyar na yamma da frnds dinta uku da suka kawo mata ziyara, ko marmarin xaman main parlor din gidan bata ta6a yi ba tun xuwanta, hatta bakinta bata bari su xauna main parlor, nata parlon take kawo su, bata ma san Mumy bata gidan ba tun safe, aka kwankwasa kofar parlonta, mikewa tayi ta isa bakin kofar ta bude, Shuraim ne tsaye sanye da kananun kaya, yyi kasa da kai yace "Ina yini?" Tamkar ana tilasta sa ya gaisheta can ciki ciki, Tace "Ya aka yi?" Bbu walwala yace "Abba yace xa mu je can gidan kaka da ita" Mami tace "Ita wa?" Yace "Yarinyar" Mami tace "Yarinyar bata da suna?" Shiru yyi mata, can yace "The blind girl" Mami tace "Toh ka kirasa ka tambayesa sunanta, kada ka sake xuwa min bakin kofa kana neman blind girl I don't have any" tana fadin haka ta rufe kofarta almost on his face. Da ba don ya san Abbansa is jet angry at him ba kuma kar ya sake wani laifin da wucewarsa kawai xai yi ba tare da Heedayah ba, gaba daya ya rasa yanda xai yi, bayan kusan minti biyar ya sake kwankwasa kofar, ba Mami bace ta bude kofar wnn karon, Barrister Zuwaira ce ta bude, yace "Ina yini?" Tace "Lafiya lau.... A carbon copy of ur father facially but not physically, ba haka Barrister Ahmad yake ba gaskiya, be human plss, let me get u the little girl" daga haka ta juya ta koma ciki ya bi ta da wani irin kallo, sai ga ta ta dawo da Heedayah da Mami ta sama Hijab har kasa duk da kananun kaya ne sosai jikinta tunda gidan Kaka xa a je, Barrister Zuwaira ta mika masa hannun Heedayah da ta bata fuska, ya kama hannun nata, ta rikesa gam ya juya ya bar wajen, bin sa kawai Heedayah ke yi kmr xata yi kuka har suka fito balcony, a dai dai nan ya kwace hannunsa daga nata ya sauka balcony din fuskarsa daure, a hankali take tahowa bayan ya saketa, shi ko har ya fara tafiya ya tuna few stairs dake wajen ya juya da sauri.... Bai yrda ta kai kasa ba ya dauketa irin rikon newborn with both hands, ba karamin tsorata tayi ba jin ta tafi xata fadi sae kuma taji an dauketa bata fadi ba ta ta6a kirjinsa kamar xata yi kuka tace "Ni dai baxan je ba kuma...."
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Masu complete Heedayah hope har kun gama karantawa🌚
Shiru har ynxu banji sharhin karshen book din ba, duk da nima ban san me ya faru karshen ba😯
Shuraim bai saurareta ba har ya isa motarsa ya bude back seat ya jefata ciki ya kulle sannan ya xaga ya bude maxaunin driver ya shiga, tuni Mai gadi ya bude masa gate ya fita gidan, Har ya isa kofar gidan Baffa bai kalli Heedayah dake bayan mota ba, ta rungume hannu kamar xata yi kuka, a compound din gidan yyi parking, sai a sannan ya kalleta ta madubi, ya wani hade rai kamar tana ganinsa, d'an tsaki ya ja ya bude motar ya sauka sannan ya bude mata side dinta yace "Fito min a mota" Ta make kafada a hankali tace "Ni ka maidani wajen Mami baxan fito ba...." Yace "Kee.... an ta6a xaneee ki???" Bai jira cewarta ba ya jawota ya fiddo ta daga cikin motar ya ajiyeta kasa ya rufe motarsa yace "Idan ina magana kina yi sai na fasa maki baki wllh...." Ta fashe da kuka sosai tace "To me bakina yyi maka, ni bana sonka you are wicked...." Sudais ya hango ya fito daga cikin gida, hakan yasa ya kai fuskarsa dai dai nata yace "Xa ki san I am wicked soon...." Daga haka yyi wucewarsa ya bar ta nan a tsaye, yana kai wa inda Sudais yake, Sudais yace "why are you leaving her all alone, how did u expect her to walk alone" Shuraim yace "Toh ni d'an jagoranta ne aka ce maka??" Bai jira cewar Sudais ba yyi wucewarsa ciki, Sudais ya karasa inda take da sauri ya kamo hannunta ya duka yana kallon manyan idanuwanta da ya cika da hawaye yace "What happened cutie..." Cikin rawar murya tace "I hate him...." Sudais ya rungume ta yana goge mata hawayen idonta yace "Noo cutie cry no more, mu tafi ciki ki gaida kaka...." Kamar ko jira take ta fashe da kuka sosai, rikicewa Sudais yyi ya shiga lallashinta, har sai da ya ga tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya, lkci daya ya ji ransa ya baci, ya mike ya kama hannunta suka wuce ciki, parlon kaka ya tadda Shuraim, Kaka sai harkar gabanta take tana 'yan wake wakenta na tsofaffi ko kallonsa bata yi ba kamar yanda shi ma bai kalli inda take ba yana danna wayarsa, Sudais na kallonsa fuska daure yace "Shuraim why will you leave the innocent girl all alone...." Shuraim yace "Plss Sudais don't question me, I am not ready to answer you..." kaka ta ajiye tsummar hannunta tace "Me ya faru Sudess?" A fusace Sudais yace "Kawai barin yarinyar yyi ita kadai a tsakar gida ya san ba gani take ba, what sort of nonsense is that" Kaka ta nemi waje ta xauna tayi tagumi a hankali tace "Ohh naga abinda ya isheni ni patuuu, Kai amma dai Amadun ne gantalalle wllh, me yasa xai hada baiwar Allah da bata san komai ba da wannan katon mutumi, wato Amadu ya raina mugun halin d'an nan nasa koh? Bai san abun ya wuce misali ba, ya wuce hankali ya dauka ba ko, Wllh shuree yake ko wa?? ba shi da xuciya me kyau ina fada kuna ganin kamar wasa nake, Baka ga ko gaisheni bai yi ba da ya shigo yana jiran ni in gaishe sa d'an banxa, ni dai ba ruwana don na haifi ubanka ba yana nufin ina da wani alaka ko dangantaka da kai bane, kayi ta kanka inyi ta kai na, makauniya kuma sai Allah ya saka mata tunda bata cuce ka ba...." Sudais dai sai hararan Shuraim da yyi kamar bai san suna yi ba a parlon yake, wayarsa kawai yake dannawa, kaka ta kamo hannun Heedayah ta xaunar da ita saman kujera tace "Sannu da xuwa Deedaya, ai da kyau tunda ba a titi ya gantalar da ke ba yyi wucewarsa ya ja ma d'a na fitina, haka nan muke fama da shi da mugun halinsa, mu ma ba kyale mu yyi ba, Bai san ba sonsa Allah ya fi yi da ya bar sa da idanuwansa ba ke kuma ya barki bbu idanuwa, shi fa Allah ba ruwansa gobe Shuree na iya tashi ya gansa a duniyar makafi to sai yyi yaya??" Tsaki Sudais ya ja ya fice daga parlon, Shuraim ya bi sa da wani kallo ta gefen ido, Kaka ta bude fridge ta fiddo malt ta bude mata tace "Wnn yaron kirki Junaidu ya xo jiya ya kawo min su da yawa, to bai fiye min wasu ba Allah na tuba, bbu abinda fa na hada da shi, kawai dai babarsa na auren d'a na ne, amma ko shekaranjiya sai da ya xo nan gaisheni muka yi ta hira gwanin ban sha'awa, to wasu ma idan suka xo sai dai su dinga tunanin ynda xa su cuceka kafin su wuce.... To ni dai bbu ruwana" A hannun Heedayah Kaka ta saka malt din, Heedayah ta fara sha a hankali tana lumshe ido, Kaka ta xauna tace "Toh madallah, yau dai na gama aikin da wuri, na gode ma Allah" Shuraim ya kashe wayarsa calmly yace "Ina yini Kaka?" Tace "Lafiya lau wllh, ai tun safe sae ynxu na gama kimtsa ko ina, baka da lafiya ne na ganka duk wani iri yau?" Yace "Lafiya ta lau" tace "Atoh naga duk ranka a bace ne ai, ko kai ma in kawo maka mantinan ne?" Ya girgixa kai kawai, tace "Toh in xubo maka abinci, shinkafa ce dai da miya" nan ma ya girgixa mata kai, tace "Toh ban da abinka meye na bacin rai kuma Mai gida, da shi Amadun yace ka kawota nan sai kace masa gaskiya kai kana da wajen xuwa, ae ba ajiye ka yyi ba, ban da neman magana irin tasa kai xai sa kayi ma yar makauniyar direba, shi da ya jajubo ta ba sai ya kawota da kansa ba, ni ba ruwana bana son rashin gaskiya, abu dai ba ayi tsakani da Allah, ae baxa ka rasa uxurin gabanka ba kai ma" Mikewa Shuraim yyi ya dau bottle water daya a fridge yace "Xan shiga in gaida su Umma" Kaka tace "Toh sai ka dawo, sai dai yau ko yar kazan nan ba a kawo min ba Mai gidan, ko da yake ina xaka kawo min kaza an hada ka da yarinya ba dangin iya balle na baba...." Fita yyi parlon, kaka ta tabe baki ta mike ta dau tsumman ta ci gaba da goge gogen da tace ta gama, Heedayah na gama shan malt din ta jefar da can din nan parlor, kaka ta leko daga d'an kitchen dinta tana kallonta tace "Ehh lallai, to sauka ki dauke ki fita da shi bola, ae ni ba baiwar Amadu bace balle ke" Heedayah ta sauka da sauri ta durkusa tana laluba Inda xata ji can din, kaka tace "Laluba gefen ki maxa ki dauke ki fitar min da shi ni ba yar bola bace, kaji min yarinya in mata inuwa tayi min rana, duk gidan nn bbu wanda na bai wa mantinan nan sae ke, shine xaki walakanta min parlor" Heedayah ta samu ta dauke can din ta mike duk a tsorace, a hankali tace "To bana gani" kaka tace "Hagun ki xa ki bi ki fita, ni xa kiyi ma karya kice ba kya gani" dai dai nan Sudais ya shigo parlon, kaka tace "Kaji wai xata je ta yarda gwangwani ta ja min salalan siya wajen Amadu Sudess...." Tsayawa Heedayah tayi tana kalle kallen kamar mara gaskiya, Sudais ya kama hannunta suka fice daga parlon, kaka tace "A'a, yau ga ikon Allah, ya xan ce a kawo min yarinya takanas kuma ka xo ka dauketa Sudess" tuni Sudais ya kulle mata kofarta, ya wuce xuwa dakinsa yana rike da hannun Heedayah, Heedayah ta ta6a hannunsa tace "Waye kai?" Ya kai bakinsa kunnenta yace "Heedayah ne ni" tana jin muryar sa ta washe hakora tace "Baka bani sauran chocolate dina ba" yace "Shi xan je in baki yanxu" ta kankame hannunsa tace "Mu tafi gida wajen Mami da kai sai mu bar wnn mugun a nan plss" dariya yyi ya wara ido yace "Da gaske" ta gyada masa kai