x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 30 - HEEDAYAH

  • 87001 words
  • 90000 words
  • Out of 115649 words

Category: Love Stories

Views 135

22 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
baki yace maki har da ke ne a tafiyar kika hada uban kaya haka?" Kaka tayi shiru tana kallonsa bayan ta hadiye wani yawu da kyar, ya danne dariyar sa yana xare mata idanuwansa yace "Mami da Shuraim ko Junaid ne ai xa su yi tafiyan ai, ko mafarki kika yi xa a je da ke ne baki ba mu labari ba kika tsiri hada kaya" Kaka ta juya a hankali tana kallon Baffa dake danna waya, Sudais yace "To ba a ma barin tsofaffi su shiga asibitin, don su ma tsoffin kansu ai cutane...." Baffa ya jefa masa wani kallo, ba shiri yyi shiru trying hard not to laugh, kaka dai magana ya makale mata sai 'yan idanuwa, Baffa yyi gyaran murya yace "Kina ji kaka, kece baki fahimci abun nan ba tun farko, kinga dole ana son a samu masu ilimi sosai su je tare da ita, sannan kin san ynda xaman asibiti yake kuma a gaskiya baxa ma su barki ki xauna ciki ba tunda kin manyanta, shine muka yanke shawara da Amadu cewar Hajiya Rahinah da Shuraim ko kuma Junaid su tafi can din tare da ita don shi Sudais baxai je ba yace, Kinga ai duk masu ilimi ne, komai xuwa xai yi da sauki tare da su, ke kuma daga baya ko kafin a sallame su ne sai a kai ki ki sauka hotel a dinga kai ki asibitin kullum kina dubata...." Kaka ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Toh daga kai har Amadun da duk wanda ya kawo wannan shawaran ku je na bar ku da Allah...." Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta kwantar da kanta saman katon akwatinta, Baffa ya bude baki yana kallonta ya kasa cewa komai, Sudais duk irin yanda yake dakewa bai san lkcn da ya fashe da dariya ba har da kyakyatawa, Baffa ya juya fuska daure yana kallonsa, Mikewa yyi da sauri yana kokarin hadiye dariyar sa yace "Meye kuma abun barin jama'ah da Allah kaka?? Daga fadin gaskiya?" Cikin rawar murya ta dafe kirjinta tace "Ae sun cuce ni ne sun toxarta ni sun kunyata ni Sudess, yanxu da wani idon xan kalli duniya ince masu ba da ni xa aje ba? Dama ashe Deedayah na da wani me muhimmanci bayan ni a rayuwar nan bani da labari? Ashe dama Rakiya munafuka algunguma ce ita ma bani da labari?" Wani kukan ta kuma rushewa da kai kace yarinya ce, Sudais yace "Toh ai ba ace baxa ki je ba fa kaka, cewa aka yi su fara yin gaba daga baya sai ke da Abba ku bi su" Kaka ta dakatar da kukan da take yi ta daga hannu sama da sauri tace "Aa wllh na yafe suyi ta tafiya har bangon duniya idan da matsallaki su tsallake bangon duniyar ma bbu abinda ya sha ma Patuu kai, dama ai ban hada uban komai da shegiyar makauniyar ba karambani na ne" Mikewa Baffa yyi ya fita dakin gaba daya ransa a bace, Sudais na nunata yace "Ke dai kin fiye wahala da neman fitina, tsofe tsofe da ke ina kike son a kai ki? Jinyarki xa aje india ayi ko na Heedayah?" Kaka na nunasa ita ma tayi fici fici da ido tace "Wllh tllh idan ka bari na maka baki sai ya bi ka, uwarka ce tsohuwa ba ni ba, to sae me don su Umaru da Amadu sun munafurce ni? Ae dama munafukan ne tun suna yara, Ga dai gari da yawa maye ae baya ci kansa ba, dama yanxun nan xan bar gidan nan inga shegen da xai hanani in tsine masa bbu ruwana" Tana fadin haka ta mike ta fara neman gyalenta tana matsar kwalla, Sudais sai kyalkyala dariya yake yace "Sai ki fi ruwa gudu ai, mu ba mun huta da wahalar ki ba ma, dama duk kin addabemu kin dame mu" Kaka ta juya tana kallonsa ta nufesa ta cakumosa tana huci tace "Don kaza kazan ka nice wahalalliya??" Gwalo yyi mata ta kara rushewa da kuka ta sakesa ta xauna nan kasa tana rera kuka, suka yi ido hudu da Heedayah da hayaniyar kaka ya tasheta ta mike xaune tana bin ko ina da kallo, a mugun fusace kaka tace "Munafuka maxa sauko min saman gadon kar in jefar da ke" Turo baki Heedayah tayi xata sauka, Sudais ya karasa yana dariya ya kama hannunta ta sauka, kaka tace "Dama duk a xo a fitar min da kayanta daki na kada in konasu wllh wllh" Sudais ya nufi kofar fita da Heedayah yace "Baxa dai kije India ba idan xa ki sa ma ranki salama ki saka, ance maki tsofaffi na fita India ne, ke a dole xa a hau jirgi, to sai a dau na annabawa dai" Daga haka ya fice da sauri kafin ta ce komai, ya nufi part din Mami. Baffa na tsaye compound tare da Shuraim da ya ki shiga dakin kaka shi dai, Baffa ya kalli Shuraim yace "Me yasa baxa ka bi su Shuraim? Barrister ya ce min da junaid xa su tafi" Shuraim ya shafa kansa yace "Haka nan kawai Baffa" Baffa yace "But you need to go as your father's representative tunda shi baxai samu xuwa ba, shi Junaid can go anytime" Shuraim yayi murmushi kawai bai ce komai ba, Muryar Mumy suka ji ta leko tace "Ni na hanasa tafiya Doctor, tunda ba a maida uwarsa bakin komai ba a gidan uban me xai je yi masu India?" Baffa ya juya yana kallonta, can yace "Wnn ba girman ki bane Maryam" bata tanka sa ba ta juya ta koma, Baffa ya girgixa kai bai ce komai ba, Suna tsaye har Abba ya dawo ya samesu wajen, Abba na ganin yanayin yayan nasa dama bai ce komai ba duk suka shiga cikin gidan, parlor suka tadda kaka tana jan akwatin ta fuska a tsuke, Mumy na daga dining tana dariya kasa kasa dadi kamar ya kasheta, Abba yace "Ina kuma xa ki Baaba?" A mugun fusace tace "Rufe min baki algungumi, Ina ruwan ka da inda xa ni??" Ya kwantar da murya yace "Kinga Baaba, tafiyar ma an fasa har sai an maki visa sai duk ku tafi tare" Tace "Oh oh ba ruwana su yi tafiyarsu, kada wanda yace min komai, ni dai an walakanta ni an cuce ni, Allah ya hada mu a kiyama gaba daya kawai...." Xaunawa Baffa yyi saman kujera ya jinginar da kansa yana kallonta, Abba dai bai ce komai ba, Junaid ne ya shigo parlon da sallama, Kaka ta saki jakarta tayi mitsi mitsi da ido tace "Junaidu ashe dama uwarka bata da kirki ban sani ba, Ashe sai a hada baki da ita a cuceni ban sani ba, ni tunda nake Maryam bata ta6a min abinda Rakiya tayi min ba wllh" Da farko tsaye yyi bakin kofar, sai kuma ya karaso yace "Me ya faru kaka?" Kaka ta sakar masa kuka tace "Da hadin bakinta aka yanke shawarar baxa a je India da ni ba wajen gyaran idon Deedayah" Junaid ya d'an bude ido yace "Aa kaka ai dole ma xa ki je, ga visa nan ana maki, idan ya so bayan an gama ni da ke sai mu bi su daga baya, nima ai ba binsu xanyi ba ynxu..." Ta marairaice tace "Toh ai su basu ce min haka ba cewa suka yi ban da ni kawai, wani har ce min yyi nima kai na cutar ce me xai kai ni India, wato wai nice cuta, har da ce min wahalalliya, abinda ni dai nasan ubansa ya xaga ba ni ba" Junaid yace "Aa kiyi hakuri don Allah, tafiya kam xa ayi da ke in sha Allah, kawai dai daga baya ne xamu bi su" Kaka tace "To da wa da wa xa a tafi din yanxu?" Yace "Mami da Shuraim" Mumy dake dinning har sannan ta sakko xuwa cikin parlon cike da gadara tace "Nace Babu inda Shuraim xai je, a nemi wani amma ba shi ba, indai har ni da na haifesa ban cancanci xuwa ba to shima bai cancanta ba, kada a sake ambaton sunansa a masu tafiyan" Kaka ta bude baki tana kallonta tace "Waye wannan kuma? Daga gidanku kika xo da Shuraim din da xaki nuna mana iko a kansa ko kuwa shakiyanci ke damun ki? Kaji min jarabbiyar mata dai, to wllh sai an je da Shuraim, Kai idan xuciya ta debeni ma sai ince shi kadai xai kai ta gyaran idon kada wanda ya bi su, ke a wa xaki ce baxai je ba wahalalliyar mata kawai, nan nan kanwarki ta xo nan gidan ranan kamar abun arxiki amma sbda tambadewa na samu labarin ba a gidan take kwana ba sai ta fita da daddare ta dawo mana da safe, to gidan ubanwa take kwana, baki dau mataki kan wnn lamarin ba sai don ance Shureen xai je indiya da Deedayah? " kaka ta kalli Abba a fusace tace "Kai Amadu da wa da wa xa a tafi goben?" Yace "Rahinah da shi Shuraim, daga baya sae ke da junaid ku bi su" kaka tace "Toh dole da Shuraim xa a tafi, idan ma kowa bai je ba sae Shuraim yaje wllh" Mumy tace "Ohk, ya tafi bakina ma ya ishesa ai" Kaka ta nufeta tana tafe hannu tace "Bakin ki na banxa na hofi, bbu abinda bakinki xae mashi, ae ubansa xai yi ma biyayya don hka a gantale bakin ki xae xaga duniya ya dawo ya fada kanki ba dai kan jikana ba, gantalalliya kawai" a nutse Mumy tace "In har Shuraim ya taka ya fita gidan nan xuwa wani kasa wllh sae na tsine masa" tana fadin haka ta bar parlon kamar xata tashi sama, Shuraim dai na tsaye gefen Abbansa, kaka tace "ke kuma tsinuwar Allah ya tabbata a kan ki ba na mutum ba, xan ga uban da ya isa ya hana Shuraim xuwa India" Abba da gaba daya ransa ya gama baci ya bi bayan Mumy, Baffa dai ya ta6e baki bai ce komai ba, kaka na kallon Junaid tace "Ni dai ko xaka kai ni gidan kawun ka ynxu, wllh raina baci yake idan Ina ganin mutan gidan nan, Ka kai ni can ko xa a kwantar min da hankali" yyi murmushi yace "Toh mu je kaka" tace "Amma ae abun ba hauka bane bana kai masu katon akwati ba bari in bude in dau kayana kala ko goma ne" Shi ya ja mata akwatin har dakinta tana biye da shi tana goge guntun hawayenta... Washegari da asuba Mami ta gama duk shirinta, ta shirya Heedayah, suka fita xuwa parlon Abba, Abba da ya gama hada duk medical report din Heedayah a envelope ya mika ma Mami yace "Amma xa mu tafi ku yi ma Kaka sallama tukun koh" Mami ta amsa tace "In sha Allah" Abba ya kalli agogo yace "We need to hurry up, sbd kar ku yi missing train din" Mami tace "Haka ne" Abba ya dau wayarsa yana mamakin rashin ganin Shuraim a masallaci don bai dde da shigowa daga masallacin ba shi ma, Dialing number sa yyi ya ji switched off, ya kuma kira a kashe, Mami dai kallonsa kawai take bata ce komai ba, Abba ya dinga kallon wayar tasa, can ya mike yace "Mu tafi kawai in kai ku gidan Honorable din daga can Junaid ya kai ku Train station" Tace "Shuraim din fa?" Yace "Don't worry about that" Mai gadi ne ya shigo ya dau kayan Mami da Heedayah ya sa bayan motar Abba, Mami tace "Toh baka yi ma daughter din taka Addu'a ba Allah ya sa ayi aiki a sa'a" Abba yyi murmushi yana kallon Heedayah dake sanye da kananun kaya sai baby Hijab dake kanta tana rike da hannun Mami, kamo hannunta yyi yace "Safe trip dear, Allah ya kai ku lafiya ya sa ayi komai a sa'a, ya baki lafiyan idon ki" Ta kamo hannunsa a hankali tace "Abba xan fara gani nima?" Yana murmurshi yace "In sha Allah Dear" ta d'an yi shiru sai kuma tace "Toh baxan fara ganin Ammi na ba?" Abba da Mami duk suka yi shiru suna kallonta, hawaye ne ya kawo idonta tace "Tace min ita xan fara gani fa" Abba ya jawota jikinsa yace "Xa ki ganta in sha Allah daughter, Mami ma ai Ammin ki ce" Ta gyada masa kai, ya share idonta suka nufi gun mota Mami na biye da su a sanyaye, Sai bayan da ya shigar da Heedayah motar Mami tace "Baxa ayi ma matarka sallama ba?" Yace "No, rabu da ita" Mami bata kuma cewa komai ba ta bude front seat ta xauna suka fita gidan xuwa gidan Alhaji Imran Baffansu Junaid, Dakin da aka sauke kaka Mami ta shiga da Heedayah bayan sun gaisa da Hajiya Zuwaira a dakinta, kaka na xaune ko haske gari bai yi ba ga kayan karin kumallo iri iri a gabanta tana hada shayi cikin katon mug, Mami ta xauna saman carpet tana murmushi tace "Ina kwana kaka" Kaka tace "Lafiya lau, to Ina xan samu haka a gidanku??" Murmushi Mami kawai take, can tace "Toh mu kaka xa mu tafi ayi mana addu'a, Allah yasa mu je a sa'a ayi a sa'a, ku kuma Allah ya kawo ku lafiya" Kaka tace "Toh Allah ubangiji ya kai ku lafiya, ya sa wnn marainiya ta fito lafiya, Allah kar ya bamu kunya yasa idanuwan nan su rufa mana asiri su budu" Mami ta yi kasa da kanta tace "Ameen" Kaka tace "Toh matso da ita in yi mata addu'a" Mami ta maida Heedayah kusa da kaka, kaka tayi duk suran da ta sani da su ayatul qursiyyu da Amanar rasulu duk ta tofa mata tace "Allah ubangiji ya sa ayi aikin a sa'a, ya rufa mana asiri ki fara ganin kowa kamar yanda ake ganin ki, daga karshe kuma Allah ya bama d'a na ladan uban kudin da ya kashe maki, Allah yayi masa albarka yasa kema ki ji k'an sa wataran kada ki yi mana butulci..." Heedayah dai tayi shiru staring into space, kaka tace "Kaji gantalalliya, baxa ki ce Amin ba, ko kina da niyyar butulcin ne ya sa kika yi shiru bamu da labari" Mami tayi murmushi tana kallon Heedayah tace "Say Ameen daughter" a hankali Heedayah tace "Ameen" Kaka tace "Toh maxa ku tafi kada jirgin ya tafi ya bar ku ba mutunci ne da su ba haka suka so min xuwa umrana na karshe Allah ya fi su" Mami tace "Toh Kaka, mun gode da addu'a, baxa ki fito ku gaisa da barrister ba" Tace "Waye kuma Barrister? Don Allah ki rabu da ni kada raina ya baci, yyi ta kansa inyi ta nawa kawai" Mami ta mike tace "Toh Allah ya sada mu da alkhairinsa kaka" Kaka tace "Kiyi addu'a sosai kafin ku hau wnn bala'in na bature wai jirgi" Mami tace "In sha Allah" kaka tace "Da Shuraim din dai xa a je koh?" Mami tace "In sha Allah" Kaka tace "Toh duk Allah ya tsare ku, yayi maku albarka, ya sa ayi wnn aiki a sa'a sai mun xo ni da Junaidu" Mami tace "In sha Allah kaka" daga haka ta fita dakin, Abba na xaune parlor da Alhaji Imran, Ganin Mami yace "Lkci fa na wucewa kada kuyi missing train" Mami tace "Ka samu Shuraim din?" Abba yace "No tare da Junaid xa ku tafi" Shiru Mami tayi, Ya mike yace "Yeah, na kira junaid din ya shirya ynxu" Mami ta xauna tare da Heedayah, Alhaji Imran yace "Allah ubangiji ya tabbatar da alkhairi a tafiyar" Mami tace "Ameen Baffa" Ba a dau lkci ba sai ga Junaid da traveling bag dinsa ya sakko kasa, Abba na kallonsa yace "Hope baka ce ma kaka komai ba" junaid yace "Aa ban shiga ba" Abba yace "Good" Har motar Abba dake parke waje Alhaji Imran da matarsa suka raka su, Alhaji Imran na kallon junaid yace "Nayi maka transfer yanxu Incase da bukatar wani abun a can, Allah ya kai ku lfya, ya sa ayi aikin a sa'a" Junaid yace "Toh Baffa Allah ya saka da alkhairi" Abba yyi ma Alhaji Imran godiya haka ma Mami sannan suka dau hanyar train station na Hayin rigasa, Junaid na xaune back seat da Heedayah, ta kwantar da kanta saman shoulder dinsa a hankali tace "Good morning...."


Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍



Har suka isa train station din bbu wanda yace komai cikin motar, Abba yyi parking duk suka sauka suka shiga ciki with their luggages, shi dai Junaid na rike da hannun Heedayah, Abba bai bar tashan ba kuma sai da ya ga tashin train dinsu xuwa Abuja.... Kasancewar sai tara na dare flight din nasu na Qatar airways xai tashi kamar yanda aka sanar masu bayan sun je airport din, hotel kawai Junaid ya kama masu kusa da Airport din, Bayan Azahar Mami ta idar da sllh ta shirya xata tafi gun step sister dinta da ke nan garin Abuja, shigowar Junaid kenan daga masallaci yana kallonta yace "Ina xa ku Mami?" Tace "Xan je gidan Asiya ne in dawo yanxu" yace "Ohk..." Mami ta ajiye ma Heedayah dake xaune saman gadon hotel din takalminta ta kamo hannunta tace "Sauka ki sa takalmin ki" Heedayah tace "Mami da Yaya xa mu je?" Mami tace "Aa ina ruwanki da wani Yaya" Tace "Mami
End Ads