tace "To kaka wai me yasa yake yi ma mutane mugunta? Ni fa bana son sa" Kaka tace "Haka nan Allah ya halicce sa, Kuma ya xa ayi ki so sa, ke da baki hada komai da shi ba...." Heedayah dai tayi shiru sbda kamshin turare da ta fara ji, kaka tace "Tun yana karami duk da baya magana haka yake narkan 'ya yan mutane, yyi ta cin xali, uwarsa kuma tayi ta goyon bayansa" Heedayah dai bata ce komai ba, Kaka tace "Ya kika yi shiru kuma" Heedayah ta turo baki a hankali tace "Bayan yana dakin xaki ce min baya nan" Kaka ta kyalkyale da dariya, Shuraim da ya wani hade rai yana kallon Heedayah yayi kwafa ya juya ya fice, Heedayah dai bata ce komai ba ta wani cinno baki, kaka tace "Atoh, yarinya sai fitsara da gulma wai don ma bbu ido..." Da rana Farida ba don ranta ya so ba ta shirya xa su je shopping kamar yanda ita ma Abba ya gaya mata, Heedayah ma ta sa Hijab dinta don tare Mami tace su je, can kofar gida yyi parking don ma kar Mumy tayi noticing xa su fita, Farida Ta bude ma Heedayah back seat tana rike da hannunta ta shiga, ita kuma ta shiga gaba, ko kallonsu bai yi ba ya tada motar suka bar layin. Wani shopping mall xai shiga Farida tace "A na gaban nake yi shopping, nan ba dukka abinda nake so suke da shi ba" Ya wani daure fuska bai dai ce komai ba ya shiga yyi parking ya kashe motar, Farida ta dauke kai ta ta6e baki ta bude motar ta sauka, ta bude side din Heedayah ta kama hannunta ta sauka, ta gefen ido yake kallon Heedayah da Hijab dinta ya wuce gwiwa da kadan, sae pink wandon dake jikinta amma bai kai ankle dinta ba, Farida xata rike hannunta su wuce ciki ya fixge hannun yace "Wa xata bi a hakan???" Farida ta kalli Heedayah daga sama har kasa, ya bude bayan motar yace "Maida ta ciki" Farida tace "But there is nothing wrong with her dressing, I dressed same also" Da kansa ya mayar da Heedayah da ta fashe da kuka cikin motar ya rufe, Farida ta rungume hannunta ta hade rai ta jingina da motar tace "Ni na ma fasa shopping din" Wani kallo yyi mata yace "Gaura maki Mari xan yi idan baki shiga mun wuce ba" Ta fashe da kuka tace "Toh why will u lock her all alone cikin motar, don't you know there is heat, ni baxan bar ta ita kadai ba" Atm card dinsa ya ciro ya mika mata still frowning his face yace "Double five, double zero.... Tafi kiyi shopping dinki ke kadai" Ta leka motar tace "Toh xaka tsaya da ita ne" Kin bata amsa yyi, ta amshi ATM card din ya bude maxaunin driver ya shiga ya xauna, A hankali Farida ta nufi cikin mart din. Heedayah dai ta daina kukan da take sai share idonta take, ta gaban madubin motar yake kallonta, bayan kusan minti goma jin shirun yyi yawa ta matsa a hankali kusa da driver seat ta sa hannu xata lalabu ko akwai mutum a nan, Kirjinsa ta ta6a ta janye hannunta da sauri ta koma ta xauna tana turo baki... Bayan wani 15 mins din sai ga Farida ta fito da labourer dake dauke da ledojin kayanta, Bude booth yyi kafin su karaso, mutum ya saka kayan gaba daya a ciki ta bude jakarta ta ciro kudi ta basa sannan ta bude back seat ta shiga ta rufe tana kallon Heedayah tace "Didi na siyo maki chocolates and Biscuits har da teddy..." Heedayah ta wara ido ta kamo hannunta tace "Thanks Farida" Ya d'an ta6e baki ya tada motar yayi reverse ya bar shopping mall din. Karfe biyar saura Farida ta gama shirin komawa makaranta, Heedayah har da hawayenta daga Inda ta xauna ta takure kanta, Mami da ta ji tausayinta sosai tace "Ku tafi tare Farida, sai ya dawo da ita" Farida da duk jikinta yyi sanyi ta kama hannun Heedayah suka fita parlon xuwa dakin Kaka su yi mata sallama, Shuraim na xaune main parlor da makullin motarsa cox Mumy bata gidan, Ya bi su da kallo yace "If she is not changing that clothe she shouldn't bother entering my car..." Farida ta juya tana kallonsa don tun da take bata ta6a jin yyi magana me tsayi hka ba, ta dauke kai ta ta6e baki, Heedayah ta rike hannun Farida sosai kamar xata yi kuka tace "Pls kice Mami ta bani dogon Hijab in sa" Farida ta d'an ja tsaki suka koma bangaren Mami, Mami na kallon Heedayah daga sama har kasa tace "Does he have any business with her dressing, ko ya siya mata Hijabs ne? Or is he stupid??" Farida dai bata ce komai ba ta dauko ma Heedayah wani Hijab din har kasa ta saka sannan tayi ma Mami sallama suka fita, Kaka har da kwallarta, ta daure ma Farida cin cin da bai fi kwaya shidda ba a leda ta mika mata tana cewa "Ashe baki nan xa a kai Deedayah India" Farida tace "Kilan muna jarabawa lkcn" Kaka tace "Toh ai shkkn, Amadu yace min nan da sati uku ne, ga kayana har na hada" Farida tace "Toh Allah ya kai mu" Kaka ta dauko maltina daya ta kara mata, ta rakasu har bakin motar Shuraim, tana kallon Shuraim tace "Toh ko in dauko gyale mu tafi tare Shureen?" Ya gyara xama yace "Ehh" Da sauri ta juya ta koma ciki, ya tada motarsa ya fice daga gidan, Heedayah ta rufe fuskarta a Hijab tana dariya a hankali, Farida kuwa sai hararansa take.... Suna Isa makarantar Shuraim yyi parking, tsadaddun motoci ne iri iri an kawo students, Farida ta kamo hannun Heedayah tace "Till I come back Didi..." hawaye ya kawo fararen idanuwan Heedayah, ta madubi Shuraim ke kallonsa, Jikin Farida yyi sanyi tace "Baxan dade ba xa mu yi hutu...." Heedayah ta fashe da kuka sosai ta daura kanta saman jikin Farida, Shuraim ya hade rai yace "Malama sauka ki bude booth ki sauke kayan ki" Ta galla masa wani harara tana share idonta ta sauka motar, sauka yyi shi ma don sauke mata kayan don ya san sun mata nauyi, Heedayah na jin haka ita ma ta bude motar ta sauka, Tsaye yake jikin black ride dinsa ya rungume hannu idonsa sanye da bakin space, he looks so gentle and calm, dai dai saukowar Heedayah, a hankali ya cire Glasses din idonsa yana kallonta, Shuraim kawai gani yyi ta ci karo da daya daga jakan Farida da ya sauke kasa Farida kuma tana gun booth tana fiddo kananun ledojin, kafin ya karasa ya riketa tuni ta fadi kasa, shi kansa Mutumin har ya taho da sauri kafin ta kai kasa ganin Shuraim sai kuma ya tsaya cak, Shuraim ya dagota yace "Wa yace ki sakko?" Ta fashe da kuka tana yarfe hannunta tace "Wayyo na buge kafana, and there is sand in my eyes" Tuni Farida ta durkusa kusa da su tana ma Heedayah sannu, da ma sauran mutanen wajen, Bude idon Shuraim yyi, yyi blowing mata iska gently, ganin yanda ake kallonsa kawai ya dagata ya bude back seat ya sa ta ciki, ya karasa sauke ma Farida kaya yace "That's all" daga haka ya bude back seat din ya shiga yana kallon Heedayah dake ta murxa idonta matsawa yyi kusa da ita ya dafa forehead dinta yana kallon cikin idon, ta kauda kanta kamar xata yi kuka tace "Ya daina" Saketa yyi still looking at her eyes.... Tuni Mutumin ya shiga mota ya mance abinda ya kawosa bakin makarantar ya tada motarsa yana kallon motar Shuraim ta madubi, Shuraim ya daga hijab dinta ya kalli kafarta ya ga just little bruises ne a farin kneel dinta, Bude motar yayi ya sauka ya koma driver seat, ya tada motar yana fara tafiya Mutumin ya bi bayansa......
*pls fans masu son min magana su dinga typing instead of voice note, cox listening to voice note is stressful wllh, idan typing ne cikin few seconds mutum xai karanta yyi replying nn take, but voice note yana cin time when they are other messages to reply to, thanks for understanding*
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Shuraim bai yi wani nisa ba ya kula da motar bayansa dake bin sa, slowly ya dinga tafiya to see idan motar xai yi overtaking dinsa ya wuce, but sai ya ga motar ya ki yin hakan sae ma rage nasa tafiyar da yyi shi ma, Shuraim ya samu waje yyi parking har sannan yana kallon motar ta madubi, Mutumin dake cikin motar dake ta lura da Shuraim shi ma kuma ya san Shuraim ya gano yana bin sa ne kawai yyi wucewarsa bai tsaya ba, Shuraim ya bi motar da kallo har da plate number din motar, juyawa yyi ya kalli Heedayah dake xaune bayan motar, she looks so sad kiris ya rage ta fashe da kuka daga ynda tayi da fuskarta, dauke kansa yyi ga mamakinsa har sannan motar bai bace masa ba, sbda a hankali me motar ke tafiya kan less busy road din, Shuraim ya kalli layin dake gefensa kawai ya karya kan motar ya shiga layin.... Sai kusan Magrib Shuraim ya isa gida, a hankali yake tafiya ganin motar Mumy dake tsaye bakin gate tana jiran me gadi ya bude gate din, sae da ta shiga snn yyi parking gefen flowers dake gaban gate din ya kashe motarsa, Mai gadi na ganin baxai shiga gidan da motarsa ba ya kulle gate din, Shuraim ya juya yana kallon Heedayah dake bacci bayan motar, sauka yyi motar ya kulle ya nufi cikin gidan, tsaye ya ga Mumy alamar shigowarsa take jira, ya karasa Inda take ya gaisheta tace "Daga ina kke da magariban nan" Yace "Asibiti" tace "Ohk, goben xaka tafi Zarian?" Yace "In sha Allah" tace "Toh nima xan je Zarian gobe, amma bance ka gaya ma kowa ba, karfe nawa xaka fita?" Yace "Takwas..." Tace "Toh kayi hakuri ka bari karfe tara, kafin nan Abbanku ya fita" Shi dai kallonta kawai yake don ya san basu da 'yan uwa a Zaria, can yace "Me xaki je ki yi a Zaria Mumy?" Mumy tace "Yar Hajiya Sadiya ba can take aure ba, to ta haihu gobe suna, ko barka ban je ba, kuma idan na gaya ma Barrister ba lallai ya yrda ba, ni ko Sadiya ai ta wuce haka a wajena" Shuraim yace "Aa da dai ki fara sanar ma Abba Mumy" Mumy ta daure fuska tace "Toh ban yi niyya ba" Bai kuma cewa komai ba ta juya ta nufi cikin gidan ya bi ta da kallo har ta shiga parlon snn ya juya ya koma waje, Bude back seat yyi Heedayah ta bude ido da sauri, hannunta ya kama ya saukar da ita daga cikin motar ya kulle motarsa, har da xai mika ma Mai gadi hannunta ya kai ta ciki sai kuma kalli cikin compound din ya shiga yana rike da hannunta, yana isa balcony ya bude kofar parlon yana kallon ciki, bbu kowa hakan yasa ya shiga parlon da ita ya kai ta har kofar dakin kaka sannan ya juya ya fita xuwa masallaci, Kaka da ta fito daga bandaki tayi alwala tace "Waye wnn?" Heedayah tace "Ni ce" Kaka tace "Toh ai na ganki, sai yanxu ku ka dawo kai faridan makaranta?" Heedayah ta gyada mata kai, Kaka tace "To ina Shureen din?" Heedayah tace "Nima ban sani ba, ya wuce" Kaka ta ta6e baki tace "Toh me yasa kika yo min nan, Rakiyar bata nan ne" Heedayah ta turo baki tace "Toh ai shine ya kawo ni" Kaka tace "Toh ni dai na gyara dakina na share, na sa turaren wuta, gadon ma yau ko hawa ban yi ba tun da garin Allah ya waye" Heedayah ta turo baki ta juya tana laluba hanya da hannunta ta fice daga dakin, Kaka tace "Haka kawai ba kya ma mutum taimakon komai sai dai ki lalata waje gantalalliya" Mumy da fitowar ta kitchen kenan ta bi Heedayah da ido har sai da ta isa kofar parlon Mami, Dai dai fitowar Sajida dakinsu ganin Heedayah ta karasa don ta bude mata kofar, juyawa Mumy tayi ta wuce parlonta kafin Sajidan ma ta ganta... Sai da Heedayah ta shiga ciki sannan Sajida ta kulle kofar ta wuce. Karfe tara da rabi Mumy ta kira wayar Shuraim, yana xaune dinning da cup din shayi a gabansa, Ya daga kiran Mumy tace "Abbanka fa ya fita, baka gama shiryawa bane ko in tafi in hau motar haya kawai?" Yace "Na gama" katse wayarta tayi, ya mike ya tafi dakin kaka, Heedayah ce kwance saman gadon tana ma Doll din da Junaid ya siya mata kitso, Kaka kuma na bandaki tana wankewa, Heedayah ta dakatar da kitson da take ba Doll din jin an bude kofa tace "Waye?" Ya kalleta ya dauke kai, bata kuma cewa komai ba sbda kamshin da ta ji, Ya xauna yana jiran fitowar kaka, sai ga ta ta fito tana cewa "Masu aikin jaraba kawai sun bari bandakina xai dafe in shiga uku in lalace, Banda dai ma lalacewa ta sameni ina ni ina bar masu bandakina su dinga wanke min...." Shuraim dake ta kallonta yace "Xan wuce Zaria" Kaka tace "Tohhh da sassafe haka shureen" Yace "Eh" Tace "Toh Allah ya kiyaye hanya, ni dai ko kwandala bani da shi a dakin nan, dama Umaru ne me bani, gashi yau kwana daya bai xo ba" Mikewa yyi ya mayar da wayarsa aljihu, tace "Toh ko dari biyar baxa ka d'an bani ba Shureen, bani da ko sisi fa" Yace "Ni da bana maki komai kuma yau xa ki ce in baki kudi?" Kaka tace "Toh ai dama idan ba kai ba waye me min, shi Sudess yan matan da ya tara gabansa ma sun ishesa, Amadu kuma kaga ynxu ta kudin da xai kai makauniyar nan gyaran ido yake, da kyar idan ba sai an kashe kusan miliyan biyar ba tunda India ne, ai kaga ta kassara min d'a na kawai, wa gareni dama banda shi, shi din kuma ga uban abinda ke gabansa ba dangin iya balle na baba, Umaru dama yau sati rabona da kudinsa, sae dai ya xo ya karaci xamansa ya fice, toh ya ake son inyi da raina" Shuraim ya tabe baki yace "Toh nima bani da shi" Daga haka ya fita daga daki, kaka ta bude baki ta bi sa da kallo, can kuma tace "Toh kada Allah ya sa ka samu, marowacin banxa kawai solobiyo" Ko saurarenta bai yi ba, yana fita sai ga Mumy ta shigo dakin, Ta xauna ta gaida kaka, kaka ta amsa xata koma bandaki, Mumy tace "Kaka xanje gidanmu ne Salima bbu lafiya" Kaka ta dawo tace "Toh ba dole ba, yarinya sai gantalin duniya take an rasa me gaya mata gaskiya, kamar abun arxiki Amadu ya daukota kusan shekara sha biyu da suka wuce amma uwarki ta amshe ta wai autarta, to yau ina uwar taki take, ba gashi ta tafi ta barta ba, yarinya duk ta lalace wa yasani ma ko bin maxa take, da ynxu tana wajen Amadu har ya aurar da ita ta haifi 'ya yanta...." Mumy dai bata ce ma Kaka komai ba, Kaka tace "Amma wnn ai tafi karfin kowa ynxu, ta xama abar tsoro, na samu labarin ma ba kullum take kwana gida ba wai koh??" Mikewa Mumy tayi tace "Toh sai na dawo" daga haka ta nufi kofa ta fita, kaka tace "Toh Allah ma dai ya sa ba ciki ne da ita ba, tunda cewa kika yi bata da lfya, toh a dawo lfya Maryam" Mumy dai tayi wucewarta bata tanka ta ba Karfe Goma da rabi suka isa Zaria, Shuraim na kallon Mumy dake ta danne dannen waya yace "Ina ne gidan?" Tace "A'a kawai ka samu waje ka ajiyeni xan nemi adaidaita sahu, kilan kana da lectures kar in shiga hakkin ka" yace "Sai goma lectures din" Mumy tace "Ba dai ni nace ka ajiyeni ba wai" Bai kuma cewa komai ba yyi parking, Mumy ta sauka motar tace "Toh Allah ya bada sa'a" yace "Ameen, amma wani anguwar xa ki?" Tace "Saboda ga ka ubana?" Yace "A'a I was thinking ko anjima xan xo in maida ke kaduna ne" Tace "A'a, xan samu motar haya" Daga haka ta tsayar da adaidaita ta shige, ya tada motarsa ya wuce... A cikin adaidaitan Mumy tayi dialing number Sadiya tace "Toh ga fa ni na shigo Zarian Sadiya" Hajiya Sadiya ta gaya mata sunan wani filling station wai ta jirata a nan, Suna isa gidan man Mumy ta sauka ta ba Mai adaidaitan kudinsa tana jiran Hajiya Sadiya, bayan kusan minti ashirin sai ga Hajiya Sadiya, Mumy tace "Kin fa ce min kin fito gida ashe baki fito ba" Hajiya Sadiya tace "Wllh hatsari me Muni aka yi kafin Jaji, shine ya haddasa go slow" Mumy tace "Toh Allah ya ji k'an musulmi, ynxu ina muka nufa?" Hajiya Sadiya tace "Tashan da xa mu je mu hau motar garin mana" Wani adaidaitan suka samu ya kai su tashan, Mumy sae cewa take ni dai Allah ya sa kafin karfe hudu xa mu koma Kaduna, gidanmu nayi ma Barrister karya nace xan je" Hajiya Sadiya tace "Gwara ke an san baki gida, to ni Alhaji bai ma san na fito ba" Mumy ta biya masu kudin motar suka shiga suna jiran ya cika a tashi..... Tagumi Mumy tayi tana kallon katon Mutumin dake gabansu, Hajiya Sadiya na xaune gefenta ita ma tana kallonsa, bayan kusan minti goma Mutumin yyi gyaran murya yace "Toh ga dai abubuwa da yawa na gani, masu kyau da mara su kyau, da farko dai da fatan a shirye kike Hajiya Maryam don nan ba da dadewa ba babban d'an ki xai yi aure...." Mumy ta kalli Hajiya Sadiya