x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - HEEDAYAH

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 115649 words

Category: Love Stories

Views 153

22 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
"Lfya lau, ga wannan yarinyar ki kula da ita, ki bata abincin nan, sannan ki taimaka mata tayi wanka ki mata shimfida ta kwanta, tana da matsalar ido" Matar ta kama hannunta da sauri tace "To in sha Allahu Alhaji" daga haka ya juya ya bar wajen bayan yyi mata sai da safe. Washegari da ya kasance lahadi bacci yan gidan suka dinga yi har karfe takwas, Hajiya Maryam ta sakko parlor wajajen tara don ganin ko Saudat ta gama shirya breakfast, Kitchen ta sameta tana juye ruwan Lipton dake ta kamshi a flask, alamar dai ta gama komai shi kadai ya rage, Heedayah na xaune daga kusa da kofa hannunta rike da cup din shayi da Saude ta hada mata ga plate din kwai da dankali da plantain, Hajiya Maryam ta wani xaro ido tace "Saudat me xan gani haka? Wa ya saki wannan aikin, a ina kika ga yarinyar? Ko a ina kika santa?" Da sauri Saudat ta xube kasa tana gaisheta tace "Hajiya... Alhaji ne ya kawo min ita jiya da daddare yace in kula...." Tsawa tayi mata da karfi tace "Toh wllh a bakin aikin ki, da ya kawo maki ita baki iya xuwa ki sameni ba? Kawai sai ki yanke hukunci sbda ke ke ajiye da kanki? To wllh kin gama min aiki a gidan nan yau, yanxun nan xa ki kama gabanki" Hakuri Saude ta dinga bata a tsorace tana cewa "Hajiya wllh Alhaji ne ya kawo min ita kiyi hakuri ki rufa min asiri, ni ban san komai ba" Hajiya Maryam tace "Ni dai nace kinyi na aikin ki wllh, maxa tattara yanaki yanaki" daga haka ta juya ta fice daga kitchen din tana huci. Karfe goma Alhaji Ahmad ya dau Heedayah suka fita xuwa parking space, Hajiya Maryam dake xaune ta bi sa da kallon mamaki sannan ta kalli Shuraim dake operating laptop a parlon tace "Ka gani ko Shuraim, gaskiya abun nan ya fara bani tsoro, wannan abu ba na hankali bane... Something is wrong somewhere, what is wrong with your father" Shi dai kallonta kawai yake bai ce komai ba, wayarsa ya fara ring ya dauka ganin Abbansa ne ya kai kunne, Daga daya bangaren Abba yace "Ka gaya ma babarka karfe sha daya ne meeting din don Dr ya kirani xai yi tafiya" Shuraim yace "Toh Abba" Daga haka ya katse wayar, Yana kallon mahaifiyarsa yace "Abba yace Baffa xai yi tafiya, so da wuri xa ayi meeting din" mikewa Hajiya Maryam tayi tace "Toh ai a shirye nake sai ka kira kanninka duk mu duguma xuwa gidan, wato baxai iya gaya min ba sai dai ya bada sako a bani, to duk muje ayi ta ta kare yanxu" Babban gida ne sosai don har ya fi na Barrister Ahmad girma, Shuraim yyi parking a parking lot din gidan, Mumy ta fito ta nufi hanyar shiga gidan, direct dakin Hajiya Amina Uwar gidan Alhaji Umar ta nufa, bayan sun gaisa Hajiya Amina tace "Daxun nan Alhaji ke ce min akwai meeting wai kuna hanya, ni dai nace to Allah ya sa lafiya" Mumy tace "Ina fa lafiya, wllh ba lafiya...." Tsaf ta kwashe ma Hajiya Amina abinda ke faruwa ta sanar mata, Hajiya Amina ta buda ido sosai tace "Iko sai Allah, to meye ma'anar hakan da Barrister yyi??" Mumy tace "Ni nasan masa, ni dai wllh wllh kinji rantsuwar musulmi koh?? To yarinyar nan baxata xauna tare da ni ba, ba ruwana.... Haka kawai ban san hawa ba ban san sauka ba yanda duniyar nan ta lalace..." Hajiya Amina tace "Toh ai dama bbu wannan xancen, taya xaki rike yar da ba a san tushenta ba, kada ki kuskura wllh, Wai kuma makauniya kamar dai a wasan kwaikwayon hausa..." Mumy tace "Ke ki bari kawai, nasan karshe Dr yace a barta gidan nan...." Da sauri Hajiya Amina ta katse ta tace "Wajen wa??? Haba wannan ai labari ne, bbu wanda xai soma wannan gangancin..." Dariya Mumy tayi tace "Toh ba sai abokiyar xaman ki ta riketa ba" Hajiya Amina tayi tsaki tace "Ai sai dai ta kai ta gidansu amma wllh bbu wajen xaman yarinyar nan a gidan nan" Mumy tace "Atoh, taimakon da idan kayi ma yanxu yake xame maka jaraba" Mikewa tayi tace "Bari in je in gaida tsohuwar can..." Hajiya Amina tace "Tana can kuwa yau bbu mutunci ta tashi...." Mumy tayi dariya tace "Ni dai Allah ya dube xuciyata ya rabani alakakai..." Hajiya Amina tace "Wa?? Ai xance komawa gidan ki take yanxu" Mumy tace "Tabdi, xaman mu baxai yiwu ba, wnn karan karara xan fito inyi magana" daga haka ta fita dakin. Da sallama Mumy ta bude kofar wani daki ta shiga ciki, babba daki ne sosai bbu abinda bbu a ciki irin dai na tsoffi, Shuraim na xaune kusa da wata tsohuwa da tayi tsit lkci daya ganin shigowan Mumy, Mumy na murmushin yake ta xauna kasa tace "Sannu Kaka...." Tsohuwar na gyara daurin dankwalinta tace "Sannu..." Mumy tace "An tashi lafiya kaka" kaka tace "eh toh lafiyar kenan, amma kin gan ni nan?? Wllh tun safe bbu karen da ya leko ni a gidan nan har shi Umarun, hana rantsuwa dai ya shigo da Asuba ya gama xamansa a can na kusan minti talatin ya fita, wllh Maryam gidanki ya fiye min nan sau goma, gwara ke da yunwa kawai kike bari na...." Mumy ta hadiya abu da kyar ta sunkuyar da kanta, Kaka tace "Kinga wannan bakar matar Amina?? Ni dai ina ga da kyar ta wanye lafiya, ni dai ki tafi da ni gidanki" Da sauri Mumy tace "Ai hakuri ake yi a ko ina kaka, ko ina hakuri ake ba wai wani abu ba, kawai ayi ta hakuri tunda Doctor ya fi son yana ganinki kusa da shi, kuma ma hakan ya fi wllh, yanxu ma meeting muka xo yi bbu lafiya" Da sauri kaka tace "Me ya faru kuma?" Mumy ta gyara xama tana tabe baki, nan ta tsara ma Kaka duk yanda aka yi daga daren jiya har xuwa safiyan yanxu har da kari, Kaka da ta gwalo ido tana kallonta tace "Ba lafiya, shi Ahmadun yace bbu wanda ya isa ya saka shi ya kuma hanashi?" Mumy tace "Toh nima dai ban gane kan lamarin ba, abun dai gashi kamar almara" Kaka tace "Toh ina yar makauniyar take yanxu?" Mumy tace "Tun sassafe ya fice da ita ko bi ta kanmu bai yi ba....."


⚡ _Heedayah_ ⚡






_By Khaleesat Haiydar_✍🏻






6.......

Kaka ta rike ha6a tana kallon Mumy tace "Lallai ba lafiya, Kar ki yarda, ba mu san irinta ba, kuma ba ma bukatan sani, ba ruwana da jajibe jajibe gaskiya, to meye kuma na tsinto yarinya kamar wanda nace ma je ka kagani, to ni dai ba ruwana, mu je ayi meeting din gaba daya, ai kin ga ko shigowa gaisheni ma bai yi ba tunda ya tsinto wata uwar tasa a titi jiya, kuma ace min lafiya qlau, a'a wllh ba lafiya" sosai hankalin Mumy ya kwanta jin furucin Kaka, Kaka ta mike ta nufi kofa Mumy na biye da ita tana murmushi, Shuraim ya bi su da kallo kafin ya mike shi ma ya fita parlon. Babban parlor ne me dauke da tsadaddun kujeru ba masu hayaniya ba, Hajiya Amina da kishiyarta Hajiya Hauwa na xaune parlon sai Safiyya, Nafisa da Aisha 'ya yan Hajiya Amina, Jamila da Zainab 'ya yan Hajiya Hauwa su ma na xaune parlon, Khadijah da Rabi'ah duk suna parlon su ma, Abba na xaune tare da Heedayah da ya xaunar gefensa, Alhaji Umar ma na xaune idonsa a kan tv dake nuna tashar Aljazeera, a tare Hajiya Maryam ta shigo parlon da kaka da ta tsuke fuska, Abba dai kallon mahaifiyar tasa kawai yake har ta xauna, Shuraim ne ya shigo da sallama ya nemi kusa da Khadijah ya xauna sannan ya gaida su Hajiya Amina da Baffansa, d'a murmushi ya amsa gaisuwar cousins din nasa mata dake kallonsa gaba daya, Baffa ya rage volume din TV din yace "Ina Sudais?" Safiyya tace "Bai dawo training ba" Baffa ya gyada kai alamar gamsuwa, Abba na kallon kaka yyi kasa da kai yace "An tashi lafiya kaka?" Kaka tace "A'a ba ruwana, lafiya lau na tashi" tana magana ne tana kallon Heedayah kasa kasa, Rabi'ah da Khadijah suka gaisheta su ma, tace "To duk ku tashi ku fita, ko kun ga sa'annin ku a nan, wannan ai ba maganan yara bane, babban magana ce, Yaron kirkin nan kadai ya cancanci xama a nan, duk ku fita" Hajiya Hauwa tayi murmushi tana kallon Shuraim da ya sunkuyar da kansa, Mikewa su Khadijah suka yi gaba daya har da su Safiyya suka fita bbu halin ko yi mata kallon banxa, shiru ne ya biyo baya a parlon, Baffa ya bude wajen da addu'a, bayan haka ya kalli Hajiya Maryam yace "Why did u invite our mother in here?" Ta gyara xama tace "Bcos it's necessary, she needs to know what's happening" Bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds ya daura da cewa "Ba wani abu ya tara mu nan ba... jiya da maraice Barrister ya dawo gida da wata baiwar Allah wanda hakan ya kawo rashin fahimta a can gidansa, ga kuma yarinyar dai xaune kusa da shi...." ya fadi haka yana nuna Heedayah wanda duk kana ganinta kasan a tsorace take, Ya ci gaba kamar haka "Duba da irin xamanin da muka tsinci kan mu na yanxu a gaskiya hakan ba shawara bace me kyau it's risky bringing the little girl home, sai dai me??? Mu duba wannan yarinya, har nawa take gaba daya, duk magidancin kwarai ya ga yarinyar nan that looks helpless a hanya ba lallai ya iya wuceta bai yi making effort din taimakon ta ba, ko min kankantar taimakon kuwa, sai dai shi barrister nasan taimakon ya yanko sa da girma ne tunda har gidansa ya kawo wannan baiwar Allah, wanda ba kowa xai yi hakan ba a xamanin nan na yau gaskiya, ba wai ina nufin hakan da yyi kuskure bane amma in the other way round xa a iya kiransa da kuskure...." Kaka dake ta hararan Baffa ta yi kwafa tana girgixa kafa, Baffa ya ci gaba "Amma kuma xai iya yiwuwa yaga kawota gidan shine kadai mafita duba da cewa she is unsighted.... Har xuwa lkcn da Allah xai bayyana iyayenta" Calmly Hajiya Maryam tace "Idan Allah bai bayyana iyayen nata ba fa?" Baffa yace "Wannan kuma baxa a rasa yanda xa ayi ba in sha Allah, Hajiya kar ki manta one knows not where his or her reward lies, sannan muna da baya, we should always try positioning things in our shoes" Girgixa kai tayi irin ba mutunci tace "Toh ni ban hanasa riketa ba Doctor, Amma Wallahil Azeem ba ni xan rike masa ita ba,... Ya nemi inda xai kai ta, ko kuma ya bar ta nan wajen ku ai duk daya ne..." Da sauri Hajiya Amina ta kalleta da wani expression, Kaka ta kyabe baki tace "To duk kun gama??" Duk aka yi shiru ana kallonta, ta gyara xama tace "Toh maza tun muna mu bakwai ba mu dawo mu takwas ba a parlon nan Amadu ya maida wnn yarinya inda ya dauko ta, mu ba gantalallu bane, bamu sa6a kwashe kwashe ba a dangi, baxa kuma a fara ta kan d'a na ba...." Shiru ne ya biyo bayan abinda Kaka tace a parlon, Abba da Baffa sai kallonta suke, Hajiya Maryam taji kamar ta tashi ta rungume kaka don farin ciki, Hajiya Amina kuwa sai murmushi take kasa kasa, Hajiya Hauwa dai sai kallon Heedayah da ta makale jikin Abba take, Bude kofar aka yi wani matashi ya shigo da sallama, sanye yake da sport wears, they have many resemblance in common with Shuraim, sai dai ya girme ma Shuraim da shekara daya duk da ba wai hakan ya nuna bane, bin occupant din parlon yyi da kallo, coz he knew nothing about the meeting, ya kalli kaka da ta tsuke fuska ganinsa tace "Kai ka ji wani neman fitina gun Mutumin nan ko sudais...." xaunawa yyi gefenta coz yasan she will brief everything a nan take kafin ma ace masa komai a parlon, ta gyara xama tace "Kanin ubanka dai ya xama abinda ya xama, Wai kaji yarinya ya tsinto ya kawo gida ba dangin iya balle na baba, har yana ikirarin bbu wanda ya isa ya hanasa abinda yyi niyya bai san magana xai dawo kunne na ba, Toh mu xuba da shi, idan shi ya haifeni ai yanxu kowa xai sani, kuma nace masa maxa ya mayar da ita kada raina ya bace...." Murya can kasa Sudais yace "Wacce yarinya ce?" Heedayah ta nuna masa rai bace tace "Gata can kamar mage...." Sudais ya kalli Heedayah da ta makale Abba, sannan ya kalli Abba da Baffansa da suka kasa cewa komai, ya maida dubansa kan Kaka, lkci daya ya hade rai yace "Toh meye don an taimaki wannan yar yarinyar, ni na ma xata wani babban abu ne ya faru a gidan, ynxu ba fata ba yau ace Safiyya ko Jamila sun 6ace baki son wani ya taimaka masu kenan? Kika san dalilin da yasa Allah ya rabata da iyayenta?? Ke da xaki yi fatan Allah ya bayyana su...." Katse sa tayi da sauri tace "Kun ji min fitsararren yaro ko?? to ce maka nayi ban yi addu'ar Allah ya bayyana iyayen nata bane?? Ni dai ba ruwana ka daina min sharri, dama kwana biyu na fita harkan ka a gidan nan sam baka da mutunci ka rainani...." Ya mike yace "A'a ni ban rainaki ba kaka ke dai baki son gaskiya, kawai ki bar Abba ya rike yarinyar a ci gaba da neman iyayenta, ynxu idan ya mayar da ita kika san hannun wanda xata fada, kinsan fa idan ta fada hannun mugaye ke ma kina da kwamasho me girma, sannan kin fi kowa cewa aji tsoron Allah, kuma ga lamarin da ya kamata mutum ya ji tsoron Allah nan...." Tagumi kaka tayi tace "Kuna dai ganin Aliyu ko?? To ba komai rayuwa ce ai" Hajiya Maryam dake ta xufa sai kallon Sudais take tana hadiye abu da kyar, Baffa dai ya jinginar da kansa da kujera yana kallon d'an nasa, Abba kam kansa na kasa shi ma yana saurarensa, Hajiya Amina duk uwar hararan da take xabga ma d'an nata yaki kallon direction dinta, Hajiya Hauwa banda murmushi bbu abinda take, Sudais na kallon kaka yace "Kawai dai yanxu sbda tsoron Allah ki bari Abba ya nemo iyayenta, kuma ta xauna har sanda Allah xai bayyana su...." Kaka tace "To ni dai ba ruwana, dama Maryam ce tace bata yadda ba banda haka ni meye nawa?? ai d'a na kowa ne bawa sai me shi, me ta min da xan koreta banda abun ka sudais? Amadu yayi ta rikonta har Mahadi ya bayyana ma bbu abinda ya sha min kai ni dai...." Sudais ya shafa kansa yace "Idan ya kai xuciyar ki ce masa xa kiyi kin amince ya riketa" A mugun fusace tace "To ya rike ta mana, ni ina ruwana, ai d'a na kowa ne, amma gaskiya ka daina min rashin kunya xan hada ka da ubanka, kaf ka raina ni tamkar ynda uwar ka ta raina ni" ya d'an bude ido ya juya ya nufi kofa xai fita Kaka tace "Allah yyi min tsari da kai ni dai katon banxa" Abba ya mike xai fita rike da Heedayah, Hajiya Maryam ta mike da sauri tace "Wllh to ka nemi inda xaka kai ta ba gidana da na yarana ba..." Kaka ta bude baki tace "Naga bala'i, gidanki kuma Maryam?? Ta ina hakan ya faru" Baffa yace "Wait Ahmad it's better kasan inda yarinyar nan xata xauna, u can't force her to hold the little girl, it's not even possible, tunda tace baxata riketa ba baxa ayi mata dole ba" Abba ya juya yana kallonsu gaba daya kafin yace komai Hajiya Hauwa tace "Babu damu Barrister, ka kawo min ita ni xan riketa in sha Allah har iyayenta su bayyana, Allah ya shige mana gaba, yayi mana mai kyau..." da sauri kaka ta katseta tana wurwurga ido tace "Ki riketa a wani gidan Kuluwa??? Kaji min mata ba tsoron Allah kamar gidanta, Haka kawai ba mu san ko mayya bace yarinya dare daya ta karar damu a gidan a shiga uku xaki wani ce xaki riketa, shi dai Ahmadun da yaga xai iya ya tafi can ya karata, ni dai Allah ya rufa min asiri ba shi kadai na haifa ba, in dai har ina gidan nan yarinyar nan baxata xauna ba, idan ko xata xauna sai dai a sallameni in tafi, bbu ruwana da kwashe kwashe ta kaina nake" tana fadin haka ta juya masu baya kamar karamar yarinya, Baffa dai sai kallon D'an uwan nasa yake, Hajiya Maryam kuwa sai hararansa take tana girgixa kafa tana wani murmushi irin ba shi da wata mafita kuma ai, ya gyada kai yana kallonta da kyau yace "Shikenan, Xan auro warce xata rike ta a satin nan in sha Allah" Daga haka ya fice daga parlon rike da Heedayah, kasa motsi Hajiya Maryam tayi jin abinda yace ta bi sa da kallo baki bude, Kaka tayi wani dariya tace "Atoh dai, tun ba yau ba dama nake cewa kayi aure ka ki, yanxu ai gashi xaka yi ba don Allah ba, xaman ka da Maryam ko kaddara, gwara ka auro warce xata rike yar da amana don a ynxu kam yarinyar bata da maraba da marainiya, tsinanne ne kadai xai ki taimakon ta...." Ta gefen ido Baffa ya kalli mahaifiyar tasa yyi saurin sunkuyar da kai.


⚡ _Heedayah_⚡






_By Khaleesat Haiydar_✍🏻






7......

Sudais na tsaye compound din gidan nasu Abba ya fito rike da hannun Heedayah, Sudais ya nufe sa ya gaishesa da ladabi, Abba yace "Lafiya Aliyu, ya weekend?" Sudais yace "Alhmdllh sir...." Yana kallon Heedayah ya kai hannu kanta yace "How are you?" Shiru tayi bata ce komai ba, Abba yace "Talk to him Heedayah" tana rike da hannun Abba a hankali tace "I am fine"
End Ads