x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - HEEDAYAH

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 115649 words

Category: Love Stories

Views 121

22 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ta fara laluben inda xata ga bread din amma bata gani ba don bayanta yake, karasowa yyi cikin dakin bindigar sa a hannu, duk occupant din dakin suka rike numfashi ganin ya nufo Heedayah da ta hakura da laluben inda bread yake ta sunkuyar da kai, dukawa yyi ya dau bread din ya mika mata yace amsa, tana laluban inda yake, ya kamo hannunta ya sa mata bread din, tana kallon direction din da ta ji hannunsa idanuwanta cike da kwalla a hankali tace "Thank you" ajiye mata ledan ruwa daya yyi ya bar sauran bread din ya mike ya fice daga dakin sauran yan uwansa suka bi sa sannan suka garkame kofar, matar dake kusa da Heedayah ta rungumota hawaye na zuba idonta ita ma, ta amshi bread din ta kunce mata ledan ta mika mata. Zulai da Ladi dai tuni suka handame bread din suna zare ido. Ammi ce kwance gadon asibiti da drip a hannunta, da ido kawai take bin mutanen dake cikin ward din, she looks so sick, Yakumbo na can wani gefe xaune kan kujera tayi tagumi idanuwanta duk a kumbure, wani matsanancin kuka ta saki tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, Allah kai kasan yanda xaka yi da axxaluman bayin nan naka, Ya Allah ka rufa min asiri 'yar Dan uwana ta dawo cikin koshin lafiya, wllh Ita kenan garemu..." Kanwar Ammi dake Ward din ita ma ta fashe da kuka sosai, haka ma sauran mutanen ciki, Mahaifin Heedayah dai na xaune kusa da Ammi yana rike da hannunta, shi ma ko kadan tashin hankali bai boyu a fuskarsa ba, kawai ta maxa yake, Yakumbo ta mike tana hade hanya ta fice ward din kamar xata shide don kuka tana cewa "Shkkn ni dai tamu ta kare, ita kenan gare d'an uwana fa, na cikin ma anyi barinsa sbda wnn tashin hankali, wannan wani irin xalunci ne ake yi haka a duniya ni Khadijah, Allah ka tsine ma duk wanda ya raba mu da Heedayah, Allah ka isar mana, ka dawo mana da ita cikin aminci...." Kanin Abban Heedayah ya mike ya bi bayanta shi ma dai trying hard to control his tears. Kusan la'asar aka bude kofan dakin da su Heedayah ke ciki, ja baya kowa ya dinga yi a tsorace, Heedayah ta mike xaune daga kwancen da take tana kallon inda taji karan budewar kofa, su hudu suka shigo, ko wanne da bindiga, Ogansu na nuna wani matashi yace "Kai taso xaman ka ya xo karshe a nan, Yan uwanka sun yi abinda ake bukata" tashi yyi da sauri yana hamdala sauran mutanen wajen sai hawaye, haka aka fitar da shi, ogan na nuna wani a cikin sauran yace "Kai yan uwanka na raina mana hankali, xuwa gobe idan basu yi complying ba xa mu aika ka barzahu kowa ya huta...." Yana fadin haka ya kalli wanda ke gefensa yace "Cikin yaran nan ka fito da guda daya a cire abinda ake bukata, me siya na kan hanya anjima, gobe da yamma ma akwai me xuwa zai siya" yana fadin haka ya fice, sauran suka bi bayansa, Mutumin daxu da ya kawo masu bredi ne kawai bai fita ba sai wanda aka sa ya dauko yarinya daya ya dinga bin yaran da kallo, Mutumi dai mai bredi ya nufi Zulai ya dagata ya fice tana ihu tana sakar masa fitsari, d'an uwansa ya bi bayansa ya garkame kofar, bbu abinda mutanen cikin dakin ke yi banda hawayen tashin hankali, Heedayah ta dinga waige waige jin ihun Zulai, matar dake kusa da ita ta rungume ta tana kuka sosai, cikin kuka ita ma tace "Aunty ina xa su kai ta??" Matar dai bata ce mata komai ba sai kuka. Washegari har kusan yamma basu samu an kawo masu bredin ma da ake kawo masu ba, Heedayah ta fada ma matar kusa da ita tana jin yunwa ya fi a kirga tun matar na ce mata xa a kawo abinci har ta gaji ita ma tayi shiru, kusan la'asar aka bude kofar wajen, mutumin da ke basu bread ne ya shigo da buhun bread da ruwa, nan duk ya jefa ma kowa, har bread din ya kare amma bai ba Heedayah ba, matar dake kusa da ita har xata yankar mata nata, Mutumin ya karasa ya daga Heedayah cikin kaushin murya yace "Mu je ki amshi naki" cikin rawan baki matar tace "A'a ko in yankar mata a nawa ba cinyewa xan iya yi ba, baxan ma ci ba...." Wani mugun kallo ya dinga mata hakan yasa tayi tsit jikinta na rawa, juyawwa yyi ya nufi kofa da Heedayah dake ihu tana kiran Ammi tana gatsa masa cixo a hannu, bayan ya fita ya rufe kofar, ya toshe bakinta yace "Ke xan halbe ki yanxu idan baki rufe min baki ba" Tsit tayi ko ina na jikinta na rawa tana kallonsa kamar dai tana ganin fuskarsa, xagawa yyi ya canxa hanya yanda sauran yan uwansa dake xaune a baya baxa su gansa ba, cikin hanxari ya karasa bayan wani karamin bukka da suke ajiye makamansu ya ajiyeta bayan Bukkar ya durkusa yana kallonta yace "You don't move, ki tsaya nan har in dawo idan ba haka ba, I have gun...." Kai kawai take gyada masa a tsorace tana komawa baya, ya mike da sauri ya koma inda Yan uwansa ke xaxxaune ana xuke xuke ana buga karta, Makullin mashin dake rataye jikin bishiya ya dauka yace "Xan je amso ruwa in dawo yanxu...." Wani daga cikinsu ya kallesa yace "Oga na hanya da customer fa" yace "Ehh yanxu xan dawo ai" har ya nufi gun da suke ajiye babur dinsu sai kuma ya juya da sauri ya sake komawa dakin da ya dauko Heedayah ya bude ya shiga yana masu wani kallo yace "Ko da an tambayi yarinyar nan kuce ta mutu an fitar da ita...." Tsuru tsuru suka yi suna kallonsa ya juya ya fita ya kulle kofar. Daga haka ya nufi machine ya hau ya tada, a guje ya bar wajen, dai dai inda ya ajiye Heedayah ya tsaya, sai xare ido take tana kalle kalle, ya daga ta ya daura gaban machine din yyi speed off, gudu kawai yake a dajin kamar mai race din motorcycle, tafiyar kusan awa daya da rabi suka yi suka shigo cikin gari sosai, a hankali yake tafiya yana kalle kallen jama'ah dake ta kokarin rufe wajajen sana'arsu kasancewar Magrib ya gabato, sai kuma ya tsayar da machine din ya kashe, sauke Heedayah da tashin ta bacci kenan yyi, ya ajiyeta nan gefen hanya yana kallonta, laluba wajen ta shiga yi, jin ya sake kunna bike din da sauri tace "Noo, Are you leaving me??" juyar da Machine dinsa yyi ya dau hanyar da ya fito with speed, ta fashe da kuka sosai tace "Noo"


⚡ _Heedayah_ ⚡






_By Khaleesat Haiydar_✍🏻







3.....



Heedayah ta fi minti biyar a tsaye tana Shesshekar kuka, jin bbu alamar xai dawo ta fara tafiya a hankali tana yi ma kanta jagora da hannuwanta biyu, da tayi tafiya kadan sai ta tsaya, ihun da taji aka yi wajen ya sa ta tsaya a mugun tsorace, ji tayi kamar an hankadata da katon abu ta fadi kasa, tun tana jin surutun jama'an wajen sama sama har ta daina ji kwata kwata. A hankali Heedayah ta bude ido tana laluba inda take kwance, muryar namiji taji a gefenta yana cewa "Alhamdulillah she is back (Ta farfado....)" Ya kamo hannunta yana mata sannu murmushi dauke fuskarsa, kanta da yyi mata nauyi kawai take gyadawa tana kokarin mikewa xaune, ya komar da ita ya kwantar yace "A'a bari likita ya xo ya duba ki, bari in kirasa, ina xuwa ynxu" ita dai kai kawai take gyadawa, ba a dau lkci ba sai ga mutumin ya dawo da likita, directly Heedayah ke kallon fuskar likitan, ya sakar mata lallausan murmushi wanda bata san ma yana yi ba, likitan ya xaunar da ita ya dafa goshinta yace "Ya jikin baby girl?" Kifta ido ta shiga yi tace "Where am I? (Ina ne nan?)" Yana murmurshi yace "Hospital dear, fatan dai babu inda yake maki ciwo" kanta ta nuna masa, yace "Xai daina in sha Allah, xa a baki magani yanxu" shi dai wanda ya kirawo likitan kallonsu kawai yake, A hankali tace "Xan yi fitsari" likitan ya saukar da ita kasa, yana nuna mata kofar bandaki, hannunsa ta kama, yace "Xa ki iya dear, walk gently now (Kiyi tafiya a hankali....)" kin motsawa tayi, sai kuma a hankali tace "I can't see (Bana gani)" da mamaki likitan da Mutumin da ya kawo ta asibitin ke kallonta, likitan yace "Why? is the eyes paining you? Idanuwan suna maki ciwo ne" Ta girgixa masa kai yace "Toh yi tafiyar ki da kanki" ta rike hannunsa gam kamar xata yi kuka tace "Ae ni bana ganin hanyan" sosai hankalin likitan ya tashi, haka zalika Mutumin dake Ward din da ya mike shima yana kallonta, don gaba daya tunaninsu a lkcn ta dalilin accident din ne vision dinta ya samu matsala, Banda innalillahi wa Inna ilaihi raji'un bbu abinda Mutumin ke furtawa yana kallon Heedayah. Likitoci sun fi biyar a kan Heedayah, all trying to figure out where the problem is, ko wannensu na kokarin gano inda matsalar take amma abu ya ci tura, ita dai sai bin duk inda ta ji motsi take da manyan idanuwanta, duk da ba ganinsu take ba, daga karshe dai aka ba Mutumin da ya kawota shawara kawai ya kai ta asibitin ido, ba karamin tashi hankalin wannan mutumin yyi ba, haka dai ya biya bill din asibitin ya dau Heedayah xuwa asibitin ido dake nan cikin garin kano. Dai dai lkcn da suka shiga haraban asibitin motar optician din dake duba Heedayah tun da aka haifeta har kawo lkcn da aka yi referring dinsu india kuma na fita daga asibitin. Mutumin dake rike da hannun Heedayah bayan ya sauketa daga motar ya duka dai dai fuskarta cike da damuwa yace "Daga yaushe kike daina gani Little girl? What was the last thing u saw? Meye abu na karshe da kika gani?" Tayi shiru sai kuma tace "Nima ban sani ba" Damuwa ne sosai fuskarsa, yace "Toh daga ina kike jiya da magariba kuma ina xa ki? Where are ur parents? Ina iyayen ki" Shiru tayi, staring at him kamar tana ganinsa, nan ya shiga tantaman ganin da tace bata yi, ganin yanda take masa kallon cikin ido ya kai yatsunsa har kusa da idonta yaga bata rufe ba har sai da ya taba lashes dinta, kikkifta idon ta shiga yi, yace "ki min magana, Where are ur parent? Ina iyayenki" Ta girgixa kai tace "I don't know, (Nima ban sani ba)" da mamaki yace "Baki san inda iyayenki suke ba, ina xa ki jiya?" Ta fashe da kuka tace "Nima ban sani ba, kawai an saka ni a mota aka wuce da ni, sai na ji an sake hawa da ni bicycle kuma ynxu ban san inda aka kawo ni aka ajiye ni ba" rasa abun cewa yyi yana kallonta, can dai yace "Ya sunan garin ku?" Tace "Abuja" ya xaro ido ganin dai a garin kano suke ynxu, yace "Ya sunan baban ki?" Tace "Abba" yace "Abba??? Mamarki fa?" Cikin rawar murya tace "Ammi" Innalillahi ya dinga nanatawa a ransa, sai kuma yace "Abuja ya sunan anguwan ku?" Tace "Abuja ne" mikewa yyi just as confused as she is, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna goma na safe, yana rike da hannunta yana mata jagora suka shiga asibitin, Ba su suka fito ba sai kusan Azhar after series of Diagnosis da ya tabbatar da she was born with the blindness, a haka aka haifeta, kuma tana stage din operation din karshe kenan wanda xa ayi mata idan ba ayi nasara ba she will remain blind till the end (Xata xauna a makauniyar ta har karshe...) Alhaji Ahmad na rike da hannun Heedayah xuwa gun motarsa a haraban asibitin, bai ta6a shiga rudani irin na ranan ba, to ina xai kai wannan yar baiwar Allahn, kara kallonta yyi yaga bata wuce autarsa Rabi'ah ba, yanxu ina xai samo iyayenta ko wani wanda ya santa??? Yanke shawarar kai ta police station kawai yayi, yasan su xa su san yanda xa su yi da ita, driving kawai yake absentmindedly ya ji Heedayah tace "Abba, yunwa nake ji" ya d'an kalleta yana ci gaba da tukinsa yace "Me xa ki ci?" Tace "Shayi da bredi da kwai" sake kallonta yyi sannan ya dauke kai, Mintuna kadan ya rage ya isa nearest Police station, sbda yunwan da tace tana ji ya dau wata hanyar daban xuwa wani restaurant, abinda ta ce take so ya sa a kawo mata, ya tabbatar shayin ba xafi sosai sannan ya bude mata bread din da kwai ya mika mata, ganin yanda take ta lalube lalube kar ta kwa6ar da shayin ya mike ya koma kusa da ita, feeding dinta yayi har ta ce ta koshi, Banda kallonta bbu abinda yake yi cike da tausayinta, Bai taba ganin irin haka shi dai ba, yar karamar yarinya da makanta, tace "Abba..." Ya shafa kanta yace "Daughter" murmushinta me kyau tayi tace "Thank you" Bai ce komai ba, Amma naxari me iri iri yake yi a ransa, bayan few seconds ya kalleta yace "Ya sunanki?" Tace "Heedayah" Ya lumshe ido ya bude yace "Heedayah baki san anguwan ku a Abuja ba? Ki tuna da kyau ki gaya min daughter" Tace "Abuja ne gidanmu" ya girgixa kai ya mike yace "Tashi" tashi tayi ya kama hannunta kasancewar ya biya bill din suka fita xuwa gun motarsa, bayan sun bar Restaurant din, ya dau hanyar police station, Yana rike da ita suka shiga ciki, Bai bata lkci ba bayan yayi report ya bar Heedayah tare da su don yana da meeting da xai shiga karfe daya kuma a ranan yake son barin garin kano, sai dai har ya isa inda xa shi hankalinsa ya ki kwanciya, gaba daya ya rasa sukuni.... Washegari karfe takwas a police station yayi ma Alhaji Ahmad to be sure an samu iyayen Heedayah duk da yasan da kyar hakan ya faru a rana daya kawai, Bayan sun gaisa da policemen dake wajen suka sanar masa an kai ta orphanage for the meantime, shiru yyi na few seconds kafin yace "Shikenan, nagode...." Wani police officer yace "We will try our best in sha Allah, an kuma riga da an fara broadcasting tun jiya, so hopefully she will get back to her parent soon, (xa mu yi bakin kokarin mu na ganin ta koma ga iyayenta)" Alhaji Ahmad yace "Allah ya sa hakan" Sallama yyi masu ya bar station din. Ammi dake xaune saman gado a dakin asibiti da take ta kai hannunta xuwa na Mahaifin Heedayah dake xaune gefenta sai dai yyi nisa tunanin da yake, juyawa yyi ya kalleta, hawayen da ke gefen idonta ya gangaro cikin sanyin murya tace "Muhammad pls let nothing happen to my daughter, plss nothing shud happen to Heedayah, (Kada wani abu ya sami Heedayah) ku dawo min da yarinya ta" Uncontrollably ta fara kuka, tun xuwansu asibiti kwana biyu kenan sai yau tayi magana, Alhaji Muhd ya na rike da hannunta trying his best to be strong yace "Nothing dear, I mean nothing will happen to our daughter, (Babu abinda xai sameta) in sha Allah, zata dawo garemu soon da izinin Allah, hukuma na bakin kokarinsu, ki kwantar da hankali don Allah" Kuka kawai take bata ce komai ba, she looks so weak, ya sake hannunta ya fita don kiran likita. Da yammacin ranan Alhaji Ahmad ya gama shirin komawa kaduna, sai da ya bar gida sannan yyi deciding kafin ya tafi ya fara xuwa orphanage da yan sandan suka ce masa an kai Heedayah, Bai yi wani wahalan shiga gidan marayun ba bayan ya nuna Identity dinsa, ya dinga bin yaran dake wasa a waje da kallo, lkci daya idonsa ya sauka kan Heedayah dake rakube can gefe ita kadai staring into space, hannunta rike da ledan biscuit, kallonta ya dinga yi kafin ya nufeta ya duka kusa da ita har sannan bai daina kallonta ba hawaye ne cike manyan idanuwanta, lkci daya ya ji jikinsa yyi sanyi sosai, ya dafa goshinta yace "Heedayah" Hannunsa ta kama kamar tana jiransa a lkcn, sai ta fashe da kuka tace "Abba" Ya jawota jikinsa yace "Why are you crying? (me yasa kike kuka" Cikin rawar murya tace "Suna min dariya bana gani, wata ta karbe min biscuit guda daya, Abba ka kai ni gida gun Ammina...." Bai ce komai ba, can ya mike yana rike da ita yace "Toh daina kuka" goge idonta tayi, yana rike da ita still ya tafi office din shugaban wajen, bayan sun gaisa yace "What are the process before adoption of a child in here? (meye matakan bi kafin daukan yaro a gidan marayu)" Tana kallonsa tace "It's a very long process mister, (Matakan suna da yawa gaskiya" yace "Alright.... I will be back in some minutes time (Xan dawo nan da wani lkci)" kuka Heedayah ta dinga yi sosai da ta gane tafiya xai kara yi ya bar ta, haka nan ya bar ta gun masu kula da marayun wajen ya wuce, police station ya koma. Asp ya ajiye pen din hannunsa yana kallon Alhaji Ahmad yace "So you mean kana son tafiya da ita har lkcn da Allah xai sa a samu iyayenta" Alhaji Ahmad yace "Yes exactly sir" Asp yace "Sai dai kasan da cewar you didn't adopt her, duk lkcn da iyayenta suka bayyana xa a mayar masu da ita" Alhaji Ahmad yace "In sha Allah, Ni ma nafi son haka, and as I have said sbda health issues dinta yasa xan tafi da ita, she won't cope in the orphanage, i will be dropping all necessary information kamar yanda ka bukata duk da ni ba bako bane a gun ka, idan ma baka san ni yanda ya kamata ba, na tabbata kasan Yayana ai" Murmushi Asp yyi yace "Sure, I am not doubting you Barrister, Allah ya
End Ads