x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - HEEDAYAH

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 115649 words

Category: Love Stories

Views 150

22 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
you what I think is right" Ta kuma yi masa wani tsawan tace "Baka isa ka gaya min what to do and what not to do ba, out of my sight now.... Duk walakanci da cin fuskan da ubanka ke min a gidan nan ka ta6a tunkararsa ka gaya masa what is right? Sai ni marainiyar wayon ka, to baka isa ba ne...." Shuraim ya shafa kansa bai dai ce komai ba yyi wucewarsa dakinsa, ta bi sa da wani irin harara tace "Wawa kawai...." Karfe sha daya da rabi Karime ta fito hada ma Heedayah cornflakes, Mumy ce xaune parlor da Hajiya Sadiya, Karime ta duka har kasa ta gaisheta, da fara'a Mumy tace "Lafiya lau Karima, ya aiki" Karime tace "Mun gode Allah" Mumy tace "Toh madalla" Karime ta gaida Hajiya Sadiya ita ma ta amsa sannan ta mike ta wuce kitchen, Hajiya Sadiya na kallon Mumy murya can kasa tace "Ita ce mai aikin" Mumy ta gyada mata kai, Hajiya Sadiya ta jinjina kai alamar gamsuwa, can sai ga Karime ta fito rike da cornflakes da ta hada, Mumy tace "Ga kwai can da na soya a kitchen ki dauka, na ci ya isheni gashi ba almajirai a nan" Karime tace "Toh Hajiya Nagode" xata koma kitchen din Mumy tace "Toh ajiye kofin cornflakes din kar ya xube, ta ajiye ta wuce kitchen din da sauri da sauri, Mumy ta kalli Hajiya Sadiya dake mata magana cikin rada, Mumy ta gyada mata kai kawai, Karime ta fito dauke da tulin kwai a plate, Mumy tace "Ki fito da ita mana ta sha cornflakes din a nan, gashi nn ma duk ya jike...." Karime ta d'an fara kame kame, tace "Hajiya dama Madam tace kar take fitowa ne, komai xa mu yi muyi a can ciki" Mumy dake saurarenta sosai tace "Ayyo, toh tunda ita ta kawo ki ba ni ba shkkn kai mata ciki, dama so nayi in d'an sa ki gyaran bangarena ne, shi sa nace ki fito da ita nan sbda a sa mata ido, amma dauka ki wuce xan yi da kai na, na aiki tawa mai aikin kasuwa ne dama shi yasa" Karime ta d'an risina tace "A'a ba haka bane Hajiya kiyi hakuri, d'an dai gyaran bangaren ki ai xan maki, bari in kawo ta nan din" Mumy tace "Aa kar uwar dakin ki ta ga kin karya mata doka kiyi laifi...." Karime tace "A'a da wuri ae xan yi in gama" daga hka ta wuce ciki, sai ga ta ta fito da Heedayah dake sanye da wando iya gwiwa da karamin riga an daure mata kalabanta waje daya, she look more of a half cast sbda irin haskenta, dai dai fitowar Shuraim waya kare kunnensa da ganinsa kasan fita xai yi, Karime ta ajiye ta nan gefen Mumy ta dauko cornflakes din ta sa mata a hannu tace "Toh gashi ki sha masaran naki 'yar kyakkyawa" Shuraim dai sai kallonsu yake walking slowly, Heedayah ta laluba cokalin ta deba content din cup din ta kai baki, girgixa kai tayi ta fito da na bakinta saman tafin hannunta da sauri tana yamutsa karamin bakinta tace "Yyi soakkk....." Mumy ta saci kallon Hajiya Sadiya ta dalilin hakan kuma ta hango Shuraim da ya tsaya don bata san ya fito ba duk da kamshin turaren sa da ya gauraye parlon, Karime na kallon Heedayah tace "Kika ce?" Heedayah na kara tofar da sauran na bakinta tace "Xai sa in yi amai, it's soft" Mumy tayi murmushi tace "Kai yaro ma dai, wai tana nufin ya jike, ki hado mata wani kawai" Karime tace "Au... toh..." Sannan ta dau cup din ta wuce kitchen da sauri, ba a wani dau lkci ba ta dawo da wani Cornflakes din a cup ta mika ma Heedayah, sannan ta kama hannunta ta juye na bakin ta da ke kai kan nata hannun, Heedayah ta fara shan cornflakes din, Karime ta tafi kitchen ta xubar da na hannunta ta dawo tana kallon Mumy da ladabi tace "Ina xa a gyara maki?" Mumy tace "Ki tafi sama xaki ga kofofi duk ki shiga ko wanne ki share ki goge" Karime ta risina tace "Toh Hajiya" daga haka ta wuce sama, Shuraim ya karasa dinning ya xauna, Mumy ta d'an kalli Inda yake, sai kuma ta juya tana kallonsa da kyau tace "Ba fita xaka yi ba?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ehh ina jiran Umar ne..." Mumy tace "Toh ba sai kaje can gidan nasu ka samesa ba" Shuraim yace "Yace in jirasa a nan...." Mumy tace "Toh ma yaushe ku ka fara fita da Umar?" Shi dai Shuraim bai ce komai ba, Mumy ta kalli Hajiya Sadiya tayi tagumi, Hajiya Sadiya tace "Ni da ka d'an taimaka Shuraim ka amso min MTN nan waje naga da wani me kiosk a layin..." Ya kalleta sannan yace "Toh bari in maki transfer kawai...." Hajiya Sadiya tace "Aa kar ka wani ba kanka wahala, ga kudin ka amso min" Yace "Gashi ina yi, na ma yi ynxu" Hajiya Sadiya bata sake ce masa komai ba, Mumy dai ya girgixa kafa take, Tasss Heedayah ta shanye cornflakes din cup din tace "I want to take water" Mumy ta d'an kalleta tace "Sai jira ta xo ta baki ai" Shuraim dai yana ta danna wayarsa, har Karime ta fito bayan kusan minti talatin, tace "Hajiya duk na gyara na goge" Ba tare da Mumy ta kalleta ba tace "Sannu" Karime ta daga Heedayah tace "Mu je ki kwanta lkcn baccin ki yyi" Heedayah tace "Xan sha ruwa" Karime ta ja ta har xuwa gun da fridge din dinning area yake, Heedayah ta taji ta taka abu me tudu, tsayawa tayi ta kara kai kafarta kan abun, Shuraim ya dauke idonsa daga kan screen din wayarsa yana kallonta, ta kara takasa, ta kuma takasa just wanting to know what she's matching, ta kara cire kafarta ta kara mayarwa, Karime dai na kokarin dauko mata ruwa a fridge bata ma san me ake ba, Heedayah ta duka ta sa hannu tana lalubawa ta ji me take takawa, dagota yyi ya rike duk hannunta biyu ya bugesu da karfi, sannan ya ja kunnenta daya fuska daure yace "Dutse aka ce maki kike takawa??" Kara buge hannunta yyi ya ja kunnenta ta fashe da kuka sosai, Karime dai ta ja gefe bata ce komai ba, cikin kuka Heedayah tace "Sai na gaya ka da Mami, ni ba Ina ce baby na taka ba" Ya buge bakinta ya tura ta can kusa da Karime, duk wnn abun Mumy na kallonsu amma bata ce komai ba, Karime ta kama hannun Heedayah bayan ta dau ruwan tace "Kayi hakuri Yallabai, bata sani bane" Ya hade rai yace "Ku fita gabana ke da ita" Karime ta bar wajen da sauri tana rike da hannun Heedayah dake rusa kuka, Sai da ta xo wuce Inda Mumy take, Mumy tace "Sai hakuri, ita tsiwa shi kuma saurin hannu, haka nan dai" Karime ta wuce part din Mami rike da Heedayah dake Shessheka, Sai da suka shiga ciki Mumy tace "Ai kaga irinta, ba dai ana ganin ni bala'e'iya bace, to gashi tun ba a je ko ina ba bakin yarinya ya fara budewa tana ma mutane fitsara, ai kadan kayi mata na so ka yi mugun xaneta ne, rashin idon ya ci uwarsa, wllh idan yarinyar nan ta samu waje duk taka ku xata yi a gidan nan, kuma ubanku baxai ce komai ba tunda idonsa ya rufe.... Kai kuma ka xo ka xauna ma mutane a parlor ka hanasu sakata da can kana xaman parlon nan ne ko neman magana???" Shi dai bai ce mata komai ba, can ya mike ya nufi kofa yace "Sai an dawo" daga haka ya fita parlon, Hajiya Sadiya tace "Ai kuma ya lalata mana shirin yau sai mu tari gaba...." Mumy da ranta ya kara baci tace "Ni fa da ba don idon da kika dinga min ba gabansa ma xan iya duk abinda xan yi, to tsoronsa nake ji ko ubansa xai min?? Wllh ke ce kika hanani" Sadiya tace "A'a ke dai, ai komai yana son sirri a rayuwa, ni sai naga kamar da wata manufa ya xauna parlon har ya ki fita siyo min kati, ni kinga ko godiyar katin ban masa ba ma, ke dai kawai ki sa ma ranki salama ba dai duk ana tare a gidan ba, kuma da alaman jawo hankalin yar kauyen nan ba abu bne me wuya, da ganinta xata so abun duniya ne sosaiiii, bbu abun hanxari a wannan lamarin mu bi komai a sannu...." Mumy tace "To ko da wata manufan ya xauna akwai yanda xai yi da ni ne balle ma bbu wata manufa kawai coincidence ne, ke baki ga irin jibgar da yyi mata ba ynxu bbu ko shakka bbu, da kyar idan hannuwanta basu tashi ba, ai ko kadan bai bada goyon bayan kawota da ubansa yyi ba, kawai dai kin san sa da xurfin ciki ne, Amma har ynxu ina lura ba wani shiri suke yi da uban ba duk kan wnn case din...." Hajiya Sadiya tace "To ke dai kiyi ga kyautata ma wnn yar kauyen, step by step xa mu yi ta abun mu bbu wanda xai xarge mu ko da kuwa alkali ne shi ba lauya ba, lkci daya farat din da kika so ayi da farko shi xai ja a xarge mu, amma kinga wnn bbu wanda xai kawo mu a rai" Mumy tace "Haka ne kam" Hajiya Sadiya ta mike tace "Yanxu dai xan wuce, gobe in sha Allahu xan xo da karfe sha daya" Mumy tace "Toh Allah ya kai mu din, ina nan ina jiran ki" Har bakin gate Mumy ta rakata sannan ta dawo tana jin ranta fari fat.... Karfe uku da 'yan mintuna Mami ta dawo gidan, Bbu kowa parlor ta shiga part dinta, Karime na xaune saman kujera tana ta kallon tashar Hausa ga dambun nama cikin leda a hannunta tana ci cike da jin ddi, Heedayah kuma na rakube kasa a xaune ta kwantar da kanta saman kujera, Karime ta mike da sauri ganin Mami tana mata sannu da xuwa ta amshi ledan hannunta da handbag dinta, duk idon Mami na kan Heedayah da ta mike da sauri jin shigowar Mami, Mami tace "Karime ya xa ki bar ta ita kadai xaune a kasa??" Cikin rawar Karime tace "Aa, sauka tayi Hajiya ai tare muke, naga kamar ta fi son kasan ne" Mami tace "Meye wnn a hannunki??" Karime ta hadiye abu da kyar tana kara tuna warning din Mumy tace "Aa ba wani abu bane, dama naje wanke filet ne sai na hadu da Sajida Hajiyar da take ma aiki ta bata dambun nama shine ta debar min a leda, har nace ta bari amma ta tilasta ni na amsa, shine na shigo na tsam ma Hinda sai na ke cin sauran yanxu" Mami tace "Bbu wani alaka tsakanin ki da kowa na gidan nan banda gaisuwa, kin ji me nace?" Karime tace "In sha Allahu Hajiya, dama ni ba ruwana da kowa tun safe muke nan xaune, to naje wanke wanke shine...." Mami bata tsaya kara saurarenta ba ta kama hannun Heedayah suka wuce ciki, Karime gabanta sai faduwa yake, ta isa a hankali jikin kofar dakin ta makale don jin me Mami xata ce mata..... Har dai ta gama labenta bata ji komai ba, ta koma ta xauna, nan ko tsoro ne ya kara shiganta da ta tuna Mami fa na iya Kiran Sajida kila ta tambayeta, nan ko ko maganan kirki bai hada su da Sajida ba tun jiya da ta xo, Mami ta gama sauya kayanta ta xauna gefen gado tana kallon Heedayah da tayi shiru tace "Me ya same ki daughter?" A hankali Heedayah tace "Mami wnn Mutumin ya dokeni a hannuna kuma ya ja min kunne...." Hawaye ta fara tana Shessheka, Da mamaki Mami tace "A ina ya gan ki?" Cikin kuka sosai tace "Xan sha ruwa, shine ya ja min kunne na, yanxu kuma hannuna na min ciwo" Mami ta daga hannunta tana kallo snn ta fita dakin xuwa parlor, da sauri Karime ta mike tace "Hajiya a debo abinci ne?" Mami tace "Me ya fitar da Heedayah daga bangaren nan?" Karime da cikinta ya hautsine tace "A'a Hajiya bata fita ba, da yake in taji alamar xan fita yin wani abu sai tace sai ta bi ni baxata tsaya ita daya ba, ni kuma tausayi take bani sai in kasa fita in bar ta, wllh a tare nake yin komai da ita ki kirata ki tambayeta, wllh Hajiya...."


Heedayah isn't free, don't read for free and burden ur self....

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....


Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍



Mami tace "A kan wani dalili kuma aka doki hannunta kina wajen?" Karime dake xufa daga ciki tace "Cewa tayi xata sha ruwa muka tafi can inda firiji yake a parlor, to cikin rashin sani ta taka wani bawan Allah dake xaune wajen Ina tunanin shi ma d'an gidan ne, shine shi kuma rashin hakuri ya buge mata hannun ya xata da gangan tayi hakan kila" On a serious note Mami tace "Ki saurareni da kyau ki ji, ko da wasa bana son Heedayah ta sake fita parlon nan bana nan, ba komai yasa na dauke ki aiki ba sae don ki kula da ita don ni bbu abinda ya gagareni na aikin gida, shima daukan ki da nayi don bana xaman gida ne, Banda haka ni baxan dauke ki ba...." Hakuri Karime ta dinga ba Mami tana duke a kasa, Mami tace "Gargadi na karshe nake kara maki, ko nan da kofa kar ki sake fitar min da yarinya, idan kuma kinga baxa ki iya aikin ba ki sanar min tun wuri in san abun yi....." Mami bata kuma saurarenta ba ta wuce daki, Karime ta sauke ajiyar xuciya ta xauna nan kasa a hankali har sannan gabanta na faduwa, a wannan marran wa xai daukeka aiki ya biya ka dubu ashirin, aikin ma raino kawai, sai dai can cikin garin Abuja kila, tunanin hakan yasa tayi tagumi tana tunanin ynda xata kara rike aikinta hannu bibbiyu... Mumy na kitchen da Sajida wajajen biyar da wani abu kasancewar ranan ta amshi girki tun xuwan Mami gidan, masifarta da ihu da take ma mai aikin har parlor, kmr jiran mistake take ta fara fada ba ji ba gani, bude kofar kitchen din aka yi ta juya tana kallon kofar fuska daure, Sudais ne tsaye sanye cikin kananun kaya hannunsa rike da leda sai makullin mota, ta saki fuska tace "A'a... kai kuma daga ina haka...." Yana murmurshi yace "Daga gida, Ina yini Mumy?" Tace "Lfya lau, ya su Hajiyar ka?" Yace "Suna gaishe ku" ta rike ha6a tace "Yaushe rabon ka xo gidan nan Sudais, anyaa...." Ya shafa gashin kansa still smiling yace "Mumy ae sbda aiki ne, ina su Rabi'ah?" Tace "Basu dawo islamiyya ba, nasan ynxu ma suna hanya..." Yace "Ohk..." Daga haka ya juya ya bar bakin kofar kitchen din, har xai xauna parlor sae kuma ya nufi part din da Kaka tace masa nan ne wajen Mami, Mumy ta ajiye wuka da albasan hannunta ta bi sa da kallo cike da mamaki har ya isa bakin kofar Mami ya kwankwasa a hankali, ba a dau lkci ba Karime ta bude kofar, da farko ca take Shuraim ne sbda resemblance din su, ta gaishesa da ladabi ta basa hanya, ya shiga parlon dake ta kamshi ta kulle kofar, Mumy dake ta lekowa har taga shigansa ta kai hannu ha6anta idonta ya kankance, sai kuma ta ajiye wuka da albasan hannunta ta fice kitchen din xuwa bangaren ta.... Sudais na kallon Karime da ta koma gefen da take xaune ta xauna yace "Babu kowa ne?" Tace "Aa suna ciki" daga haka ta mike ta nufi kofar dakin ta kwankwasa a hankali a d'an tsorace, Mami ta bude kofar tace "Ya aka yi?" Ta sunkuyar da kanta yace "A'a dama bako ki ka yi" Mami ta kalli parlon suka yi ido hudu da Sudais karasowa cikin parlon tayi ya gaisheta da ladabi, ta amsa da fara'a tana masa sannu da xuwa tace "Ya su Kaka da mutan gidan?" Yace "Suna gaishe ku" tace "Maa sha Allah muna amsawa, welcome" Mami tasa Karime ta kawo masa ruwa da drink a fridge, ta xauna kan kujera tana kallon film da ake a tv, Bayan few seconds tace "Kai ne kayi karatu Malaysia koh?" Yace "Eh Degree" tace "Maa sha Allah, Barrister yace min chemical engineering kayi right?" Yace "Ehh haka ne..." Tace "Good, it's a nice course" yana shafa kansa a hankali yace "Heedayah bacci take?" Mami tace "A'a tana ciki" yace "Dama kaka ta bada sako a kawo mata ne" Mami ta mike tace "Allah sarki, tana ciki, let me get her" daga haka ta wuce dakin sai gata ta fito da Heedayah, har gabansa ta kai ta sannan ta dau wayarta da ke ring kan kujera tace "Give me few mins let me pick a call" yace "Alright Ma" daga haka ta wuce daki, Heedayah ta wara idanuwanta jin muryar sa tana tattaba Hannunsa cikin siririyar muryarta tace "Ka xo gidan mu yau koh?" Ya dafa forehead dinta yace "Nima ai gidan mu ne...." Ta kyalkyale da dariya tace "Aa, gidanku ai gidan wnn matar nan ne me fada" Sudais ya ja hancinta
End Ads