x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - HEEDAYAH

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 115649 words

Category: Love Stories

Views 123

22 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
taya ka riko har kafin Allah ya bayyanar da mahaifanta" Alhaji Ahmad yace "In sha Allah, nagode sosai for understanding me" Wani short note Asp din yyi a takarda yayi stamping sannan ya kira wani police officer ya koma orphanage din tare da Alhaji Ahmad don dauko Heedayah. Har sannan Heedayah na xaune inda Alhaji Ahmad ya bar ta tare da daya daga mai kula da su, sai dai mai kula da su din bata gun, ita kadai ce xaune gwanin ban tausayi, har sannan ta ki cin biscuit din, Bbu 6ata lkci aka basa ita ya bar orphanage din bayan ya sallami police officer din, he can see how happy Heedayah was bayan sun shiga mota, ganin tana ta kokarin bude biscuit din hannunta ya amsa ya bude mata ya mika mata, tace "Abba xaka maida ni gun Ammina da Abbana?" Ya shafa kanta yace "In sha Allah daughter" tayi murmushi sosai tana cin biscuit din hannunta, seat belt ya sa mata, yana kallon agogo dake nuna masa biyar saura yan Mintuna, ya gama addu'o'in da xai yi sannan ya dau hanyar fita kano xuwa garin kaduna.....




Yan Niger Khaleesat bata iya rubutun Hausa xalla bbu turanci ba, kun ban wahala a page din nan😩


Free pages dai bbu yawa😉


07087865788


⚡ _Heedayah_ ⚡






_By Khaleesat Haiydar_✍🏻






4......


Har suka shigo cikin garin kd wajajen karfe tara na dare bacci Heedayah take, slowly yake driving bayan ya shigo anguwar da gidansa yake, anguwar so silent ga fitilu ta ko ina da ya haska anguwar kamar da rana, bakin wani gate ya ja ya tsaya yyi horn, wanda hakan ya farkar da Heedayah, laluba motar ta shiga yi tace "Abba...." yana kallonta yace "I am here..." Bata kuma cewa komai ba dama kawai so take ta tabbatar bai bar ta bane, ya d'an yi murmushi ya ja motar xuwa cikin babban compound dake dauke da gida ginin duplex bayan Mai gadi ya bude masa gate da sauri, parking yyi a space din da aka tanadar domin parking a compound din, wani matashi ne da baxai wuce 28 ba ya fito daga cikin babban building din gidan, ya nufo parking space din, Alhaji Ahmad ya kashe motar ya bude ya fito, Matashin ya d'an risinar da kansa yace "Sannu da hanya Abba" Alhaji Ahmad yace "Yauwa sannu, but ka damu ka kirani tun jiya da kake min sannu da hanya ynxu??" Yana fadin haka ya wuce sa ya xaga daya side din motar, da ido dogon Matashin ya bi sa bai ce komai ba, Alhaji Ahmad ya bude door din side din da Heedayah take, ya kamo hannunta ya sakko da ita daga cikin motar, Matashin ya d'an koma baya yana kallonsu a bit surprised, Alhaji Ahmad yace "Ka fiddo min laptop dina bayan motar, they are some other things ma ka taho da su ciki" Yana fadin haka ya nufi entrance din shiga gidan yana rike da Heedayah, Matashin ya bude motar ya dauko abinda yace masa sannan ya bi bayansu, Alhaji Ahmad na shiga parlor Rabi'ah da Khadija suka taso da gudu don rungume sa, sai dai ganin Heedayah da yake rike da duk suka tsaya basu karasa gun nasa ba, Khadija tace "Who is she Dad?" Yana kokarin cire takalminsa yace "Sabuwar 'yar uwar ku" kallon juna Khadija suka yi da Rabi'ah, ya karasa parlon ya xaunar da Heedayah kan kujera sai dai ta ki sakin hannunsa kmr xata yi kuka tace "Abba kar ka bar ni don Allah" Yace "Noo baxan bar ki ba, we are home yanxu" Yana fadin hka ya kalli Khadijah yace "Ina Mumyn ku?" Khadijah ta d'an cinno baki tace "Upstairs" ya daga Heedayah ya wuce sama da ita, Khadija da Rabi'ah suka juya suna kallon yayansu dake tsaye bakin kofa yana kallon ikon Allah shi ma, da sauri suka nufesa a tare suka ce "Ya Shuraim who is she? Wacece ita" Ko kallonsu bai yi ba, ya nufi part din Abbansu don ajiye masa system dinsa dake hannunsa. Alhaji Ahmad ya bude kofar parlon Mai dakinsa still holding Heedayah's hand, dai dai fitowar ta daga bedroom dinta, ya xaunar da Heedayah saman kujera kafin yace komai tana kare ma Heedayah kallo daga sama har kasa tace "Waye wannan kuma Barrister?" Yace "sannu da hanya ya kamata ki fara min sannan tambayoyin ki su biyo baya" a takaice tace "Toh sannu da hanya, wacce yarinyar ce wannan ka shigo min da ita har parlor?" Sai a sannan ya daga kai ya kalli matar tasa yace "Bakuwa ce" Ta d'an yatsina fuska tace "Bakuwa kuma? Daga ina? Kuma ina xa a kai ta?" Yace "Eh bakuwa.... Daga kano, kuma nan xata xauna in sha Allahu rabbi" Da mugun mamaki tace "Yar wacece ita din?" Yace "Baiwar Allah ce..." A kufule tace "Plss be straight barrister, ina ka samo yarinya? Kowa ma bawan Allah ne ai" Barrister yace "Gashi nan na gaya maki, what else did you want to know, me kuma kike son sani" kamar jiran tambayar take ta mayar masa da amsa da sauri tace "Manufar xuwanta gidan nan, sannan mun hada wani dangantaka ne da ita??" Ya gyara xama yace "Manufar xuwanta gidan nan shine don ta xauna da mu na wani d'an lkci, dangantakar mu kuma kawai shine kasancewar ta 'yar uwar mu musulma" Kallonsa ta dinga yi, surprised, Furious, and mad at the same time.... Blankly tace "I don't get you Abban Shuraim, ban gane abinda kke nufi ba, a ina kasamo wannan yarinyar??" Ya mike yace "Her parents are missing, so we need to look after her kafin Allah ya bayyanar da iyayenta, all that aside, she is blind Hajiya Maryam, makauniya ce...." Yana fadin haka ya fita daga parlon..... Hajiya Maryam da ta bi sa da kallon mamaki lkci daya tace "Tabdijam!!! Toh sannu Humanitarian, Do-gooder.... sai kuma nace maka gidana orphanage ne (Gidan marayu) ko kuma police station?? to wllh ka saurareni da kyau, yarinyar nan dai baxa ta xauna gidan nan ba, me muka hada da ita daga ganin yarinya a titi ka kinkimota ka kawo mana gida wai iyayenta sun 6ata kamar wasu gyada, Anya ma Barrister kasan me kake yi kuwa, yanda duniyar nan bbu gaskiya kwata kwata kowa ya xama mugu ya xama abun tsoro ka dauko mana yarinya ka kawo gida?? A'a wllh ba gidana ba, ka dauketa ka kai ta police station ko kuma ka kai ta gidan marayu" tana fadin haka ta wuce dakinta rai 6ace don daukan wayar ta, Heedayah dai na xaune sai kallon direction din da masifar ke tashi take yi, gaba daya a tsorace take, lkci daya hawaye ya kawo manyan idanuwanta.... Bayan minti biyar Hajiya Maryam ta fito dakinta tana kallon Heedayah tana huci ta daka mata tsawa tace "Ke maza tashi ki fita ki ban waje kar in illata ki...." Mikewa Heedayah tayi da sauri ta fashe da kuka tana laluben hanya tace "Abba where are you" muryarsa ta ji yace "I am here...." Har ya karaso cikin parlon kallon Hajiya Maryam yake, calmly yace "Wannan ya xama na karshe a gidan nan, kar ki sake yi mata tsawa, nace a gidan nan Heedayah xata tsaya har sai an samo iyayenta, I mean my words" bude baki tayi tana kallonsa da farko, sai kuma tayi wani murmushi me sauti tana tafe hannu tace "Toh sannu Humanitarian, idan ni ban kai inyi magana ka ji ba nasan baxa a rasa wa enda xa su yi maka ka ji ba, look Ahmad it's not as if i am being wicked, ni ba muguwa bace Allah ya ga xuciyata kawai xamanta ne damu bna so don hankalina bai kwanta da hakan ba, to wai ma akan me xata xauna da mu, kai da kke lawyer ai ya ci ace ka fi ni sanin me duniya ke ciki, to idan ba akwai wani boyayyen lamari a kasa ba daga xuwa meeting kano sai ka dawo da yarinya wai ka tsince ta a titi bbu iyaye, Kar ka manta idan kai lawyer ne to ni kuma matar lawyer ce...." Ya dakatar da ita yace "Wallahil Azeem Maryam wannan yarinya a hanya na hadu da ita kamar ynda na fada maki, mota ce ta bigeta muka yi asibiti da ita, I was there har ta farfado.... Let just stop all this, Maryam put Rabi'ah or Khadijah in her shoes plss" a mugun fusace tace "Allah ya kiyaye, I can't imagine my children in her shoes, why will I? Kar ma ka gaya min haka, Ni dai abinda na sani shine hankalina bai kwanta ba kuma baxai ma ta6a kwanciya da yarinyar nan ba, wa ya sani ma ko aljana ce da gashi haka??" Bai kuma ce mata komai ba ya kama hannun Heedayah dake kuka a hankali ya fita parlon da ita xuwa downstairs.... Hajiya Maryam ta kasa zaune a parlon nata sai xagaye take, bude kofar aka yi Shuraim ya shigo da sallama can kasa, Hajiya Maryam ta kallesa da sauri tace "Shuraim kana ganin mahaifinku koh? Me yake nufi da kawo mana yarinya gida ba dangin Iya balle na Baba, ya san yar wacece ko ma shegiya ce bai sani ba kawai ya kawo mana ita gida, wllh something is fishy, kuma in dai yarinyar nan xata xauna gidan nan sai dai mu bar masa gidan shi da ita gaskiya, don mu ba gantalallu bane, wai kuma makauniya ce kai ka ji fa???" Tun fara maganar ta sai a sannan Shuraim ya kalleta da sauri jin wai makauniya ce, Tayi mitsi mitsi da ido tace "Wllh haka yace Makauniya ce bata gani, kuma naga alamar hakan, she is blind, oh innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, me ya samu Barrister ni Maryam... Anya kuwa yana right senses dinsa??" Shuraim dai bai ce komai ba ya juya xai fita, a mugun fusace tace "Toh malam ba shiru xaka yi ba ka wani juya sumui sumui xaka wuce, xuwa xaka yi ka samesa tunda yana jin maganar ka, ka lallabasa ya fitar mana da yarinyar ya kai ta police station, bbu ruwana da gayyar tsiya, yarinyar nan baxata kwana gidan nan yau ba..." Shuraim na fita ya nufi Part din mahaifinsa, ya bude kofar parlon da sallama, Heedayah ce kawai xaune kasan carpet dake parlon ga cup din fresh milk a hannunta, jin an bude kofa ta dakatar da shan madaran da take yi tana waige waige, bai kalli direction dinta ba ya nufi dakin Abbansa, sallama yyi bayan ya amsa masa ya shiga, xaune ya samesa gefen gadonsa, ya karasa ya xauna nan kasa gabansa yana kallonsa yace "Ya hanya Abba?" Abba ya kallesa yace "Alhmdllh..." Shuraim ya d'an shafa kansa yace "Abba, akan wannan yarinyar....." Sai kuma yyi shiru, Abba yace "Yes, what about her? Ina jin ka" Shuraim yace "Is she suppose to be here?" Abba yace "Of course, ai nan din gidana ne ba na wani ba, so why won't she be here?? Me kuwa xai hana xamanta a nan tunda na amince da hakan?" Shuraim ya girgixa kai alamar ya rasa abinda xai ce, Abba yace "Yes gidana ne, ba naka ba, balle na Mahaifiyar ka" Shuraim yace "But Abba hakan ba dai dai bane, bbu abinda muka hada da ita, ba mu san ta ba, we don't even..." Dakatar da shi Abba yyi so pissed off yace "Get out my frnd, who are you to question my orders? And don't u even have human conscience? Xaka so kanwarka ta tagayyara a rayuwa?" Mikewa Shuraim yyi yace "I am sorry" daga haka ya nufi kofa ya fita, satan kallon Heedayah yyi, lkci daya ya wani hade rai ya fice daga parlon.



07087865788


⚡ _Heedayah_⚡





_By Khaleesat Haiydar_✍🏻






5....

Jin budewar gate ya sa Alhaji Ahmad ya mike ya isa jikin tagar dakinsa yana kallon compound din gidan don ganin wanda xai fita, motar yayansa ne ya shigo compound din, ya bi motar da kallo har yyi parking, sannan ya girgixa kai ya koma ya xauna... Ba a dau lkci ba kuma wayarsa ya fara ring, ya duba ganin yayan nasa ke kiransa ya mike ya fita dakin, kwance ya ga Heedayah ta fara bacci nan kasa, ya d'aga ta ya kwantar kan kujera sannan ya fita, direct main parlor ya wuce, ya tadda wansa Alhaji Umar zaune saman kujera ga Hajiya Maryam xaune parlon ta sha kunu kai kace bata ta6a dariya ba, xaunawa yyi ya gaida Yayan nasa, Alhaji Umar ya amsa yana kallon Hajiya Maryam yace "Me ke faruwa Maryam" Ta kwantar da murya tace "kana ji Alhaji, Ko awa daya ba ayi ba da dawowan barrister daga kano, amma sai me??" Nan ta kwashe komai ta tsara masa, tana matsar kwalla tace "Saninta muka yi Alhaji? Ko me muka hada da wannan yarinyar? Mun san me yasa iyayen suka jefar da ita da har shi xai daukota, to gaskiya naga abun ba wanda hankali xai dauka bane shi sa na kira ka don kayi intervene don gaskiya I don't know what came over Barrister, ban san me ya samesa ba, kawai muna xaman xaman mu ya ja mana magana...." Alhaji Umar na kallon kanin nasa yace "Barrister wace yarinya ce wannan ka dauko ka kawo cikin gidan ka?" Alhaji Ahmad ya jinginar da kansa da kujera yace "Doctor nasan da kai ka ga yarinyar nn xaka yi fiye da abinda nayi ma... Sincerely I mean no harm to my family, taimako kawai nayi sbda Allah, and I thought they will also welcome the idea, na xata xa su so taimakon da nayi...." da sauri Hajiya Maryam ta katse sa tace "To family dinka basa son taimakon nan gaskiya, ur idea isn't welcome, kawai ka maida ta inda ka ganta, idan kuma xuciyar ka baxai yarda ka maida ta ba to ka kai ta gidan marayu..." Wani kallo ya jefa mata yace "Baki isa ki bani order a gidana ba Maryam, I did what I know is right, you are not in the place to kick away my decision, nace baki isa ba" Alhaji Umar na kallonsa yace "Hold on bawan Allah, bana son hayaniya, ka saurareni...." Alhaji Ahmad yace "Dr if you are in anyway doubting me ka kira abokin ka Asp Usman, he will explain everything to you, Babu abinda xai boye maka, shi ma ya bani go ahead din tahowa da yarinyar when I request doing so, ban taho da yarinyar nan ba sai da izini da sa hannun Asp...." Mikewa Alhaji Umar yyi bayan shirun wani lkci yace "Ynxu ina yarinyar take?" Barrister ya mike yace "Mu je ka ganta tana sama parlona" Bin bayansu Hajiya Maryam ma tayi xuwa part din mai gidan nata da sauri, kallon Heedayah dake bacci Alhaji Umar ya dinga yi kafin yace "She so little" Alhaji Ahmad ya bude hannunsa yace "Of course she is" hannu Alhaji Umar ya kai goshinta ta bude ido da sauri ta kamo hannun tace "Abba..." Ya d'an yi jim sai kuma yace "How are you?" Shiru tayi tana kokarin mikewa ya dagata ta xauna, Hajiya Maryam sai kyabe baki take fuska a murtuke tana kauda kai, Alhaji Umar ya girgixa kai ya sauke ajiyar xuciya yace "This is serious... abinda xai faru ynxu shine ke Maryam kiyi hakuri ta kwana xuwa gobe xa a san ynda xa ayi in sha Allah, they will be a meeting tomorrow at my resident idan Allah ya kai mu" shi dai Barrister bai ce komai ba, Hajiya Maryam tace "Allah ya kai mu, amma wllh baxan rike yarinyar nan ba Kun ji rantsuwar musulmi sai dai duk abinda xai faru ya faru" daga haka ta fice daga parlon duk suka bi ta da ido. Karfe goma Barrister Ahmad ya fita parlonsa xuwa parlon Hajiya Maryam, kallo take ita da Rabi'ah da Khadijah a parlon nata, Khadijah tace "Toh Mumy me yasa bai kai ta orphanage ba??" Hajiya Maryam ta kyabe baki tace "Neman suna mana, ke ko bayan lawyer gashi Humanitarian din da ya laka ma kansa, to wllh ba dai wannan gidan ba, dai dai nake da su dukka...." Rabi'ah tace "And kuma yace makauniya ce fa" Hajiya Maryam ta dau apple din gabanta tace "Ko kurma ce sai ya fitar da ita gidan nan, ban gama wahala da nawa yaran ba baxai kwaso min wata can ba, ba dangin iya balle na baba, shi dai ya cika fitina ne kawai" Khadijah tace "Ni dai idan yace nan xata xauna gwara in koma gidan Aunty Fatima, I can't stay in the same roof with her, what if muguwa ce" Hajiya qMaryam tace "Sai dai shi da ita su bar mana gidan...." Shigowan Abban yasa tayi shiru, Yana kallonsu gaba daya yace "Bani da abinci a gidan nan yau kenan?" Hajiya Maryam tace "Ohh na xata you are full ai da naga kafi concentrating kan yar tsintuwa, ban san kana tare da yunwa ba, Rabi'ah go and serve him downstairs" kallonta kawai yake kafin ya gyada kai ya juya ya fita parlon, a hankali Khadijah tace "Abba is just acting strange, dubi fa ko kula mu bai yi ba tunda ya dawo..." Hajiya Maryam tace "Atoh ina xai kula ku ga makauniya ya saka a gaba Khadija" Rabi'ah ta tashi ta fita don kai ma Abban nata abinci parlonsa, Yana xaune parlon yyi nisa tunanin da yake, ta ajiye abincin tace "Abba ga abincin" yace "Baxan ci ba, ki dibar ma yarinyar nan kawai ki fita da sauran" ta kalli Heedayah dake kwance fararen idonta a bude, ta d'an hade rai ta bude abincin ta diba kadan ta daura nama daya, kallonta kawai Abban nata yake yi yace "Add the meat" Ta kara daura wani naman sannan ta mike ta fita da sauran abincin. Mikewa yyi ya tafi gun Heedayah yace "kina Jin yunwa ko?" Ta gyada masa kai, ya kama hannunta ya dau plate din abincin ya fita, main parlor ya koma, ya shiga wani d'an corridor ya kwankwasa daya daga kofofi biyun dake wajen, wata matashiya da baxata haura talatin da biyar ba ta bude kofar, ganinsa ta durkusa da sauri tace "Sannu da dawowa Alhaji, ina yini" yace
End Ads