x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 31 - HEEDAYAH

  • 90001 words
  • 93000 words
  • Out of 115649 words

Category: Love Stories

Views 142

22 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
mu je da shi plss" Mami ta saka mata hijab dinta tana rike da hannunta ta nufi kofa tace "Sai mun dawo" junaid ya bi su da ido, sai kuma yace "Mami ko xa ki bar ta ki je ki dawo" Mami ta juya tana kallonsa tace "For what reason?" Da sauri yace "No naga kamar bata son tafiya ne" Wani kallo tayi masa ta bude kofar ta fita, Heedayah dai kamar xata yi kuka take bin Mami.... Har la'asar Mami na gidan yar uwarta da Heedayah suna hiran yaushe gamo, Hajiya Asiya na kallon yar uwarta tace "To amma me yasa ba ku taho tare da Junaid ba? Mun kwana biyu ba mu hadu ba" Mami tace "Muna sauka daxu da safe yace min xai je gidan kawunsa so bna son ya kasance bai je ba, but in dai ta nan xa mu dawo xai xo gun ki in sha Allah...." Hajiya Asiya tace "Toh shkkn, Allah ya kai ku lfya ya dawo da ku lfya, ita kuma wannan yarinya Allah ya sa ayi aikin a sa'a" Mami ta amsa da "Ameen" karfe shidda saura Mami suka bar gidan, babu yanda Hajiya Asiya bata yi ba su tafi da abinci hotel din Mami ta ki amsa, Hajiya Asiya ta sa driver dinta ya sauke su hotel din nasu. Karfe tara da few minutes na dare jirginsu Mami yyi take off direct xuwa kasar India without stopovers, tafiyar kusan awa tara da minti arba'in da takwas, kafin tashinsu kuma sai da Mami ta tabbatar ta kira Abba ta sanar masa xa su tashin yayi masu addu'a yyi wishing dinsu smooth trip.... Tare Junaid da Heedayah suka xauna a jirgin, Heedayah na laluba hannunsa tace "Yaya me yasa Abba bai biyo mu ba" Junaid yace "He is very busy" tace "To kaka fa?" Yace "She's old to journey with us" tace "To ya Sudais fa?" Yace "Shi ma he is busy amma xai xo...." Heedayah tayi shiru sai kuma tace "Dama bana son Shureen ya biyo mu" Murmushi yyi yace "Why?" Ta girgixa kai tace "Bana son sa" Junaid yace "Don't tell anybody that" Tace "Why?" Ya ja hancinta ya kwantar da ita jikinsa yace "Sleep Lolly...." Lumshe ido tayi nan da nan kuma bacci ya dauketa throughout the rest of the journey. Bakwai saura na safiya Jirginsu ya sauka Indira Gandhi international airport new Delhi, Amma sai karfe goma saura suka shiga Indraprastha Apollo Hospitals da xa ayi ma Heedayah aiki, don sai da suka fara sauka hotel dake nan kusa da hospital din suka huta, Bbu bata lkci aka yi admitting din su a babban asibitin a ward dinsu su kadai, ba laifi ward din na da d'an girma, amma kana gani kasan dai kudi ne kawai aka kashe ba kadan ba.... Kamar yanda Abba yayi tunani haka ne don sun daura Heedayah kan allurai na sati daya, sai kuma some diet da aka daura ta kai, Likitar dake ma Mami bayani a office dinta da harshen turanci ta sanar ma Mami irin Disorder din Heedayah da ake kira da Congenital Blindness, sannan ta sanar mata Novel Gene therapy xa ayi mata to correct the disorder, probably through luxturna, Mami da duk jikinta yyi sanyi tace "But is there much chances of her gaining her sight?" Likitan tace "Hopefully, though it's a rare disorder but we will try our best" Mami tayi ma likitan godiya ta mike ta fita office din ta koma ward dinsu. A kwanaki bakwan nan Mami kusan kullum sai ta tashi sllhn dare tayi addu'ar Allah ya sa ayi nasara a aikin da xa ayi, har ranta take tausayin Heedayah take kuma fatan Allah ya bude mata idanuwanta, bata san yanda xata ji ba idan aka yi aikin nan Heedayah bata yi gaining sight dinta ba, she can't just imagine that, a hotel din da suka fara sauka na kusa da hospital din Junaid ke kwana, amma throughout the day yana asibitin tare da Heedayah da Maminsa, sai dai kawai ya fita ya siyo masu Nigerian dishes safe rana da daddare, ko kuma ya fita xuwa yin sllh... A kullum sai Abba ya kira ya sa a ba Heedayah waya sun yi magana, complain dinta kuwa a ko da yaushe shine idonta suna mata ciwo, don a hankali fararen idanuwanta masu kyau suka fara sauya kala xuwa ja kuma tayi ta sosa su, Sudais ma kusan kullum sai ya kira Mami ta ba Heedayah sun yi magana, ana haka har suka cika kwana goma cif a asibitin ya rage kwana biyu a shigar da Heedayah theatre.... Junaid na xaune tare da Mami ana gobe xa ayi operation din wayarsa ya fara ring, dauka yyi saman table dake kusa da shi yana kallon screen din dake nuna masa Beauty, to waye haka? ya dau lkci yana tunanin waye yyi ma saving da haka, sai kuma ya daga kafin ya katse ya kai kunne, Daga daya bangaren aka yi sallama cikin siririn murya, sai bayan kusan second biyar ya dau muryar ya amsa sallaman, Salima tace "Haba Jayyy shine bbu ko sallama kayi tafiyar ka India, to gani a new Delhi din nima, yanxun nan jirginmu ya sauka daga Nigeria wllh" junaid ya d'an yi shiru da mamaki, can dai yace "Ke da wa kika xo new Delhi?" Tace "Wllh wani saurayi na ne ya xo business trip shine kawai yace in rakosa, a hotel din kusa da Airport xa mu sauka ynxu.... Ku kuna wani asibitin ne?" Yace "Toh ki huta tukun xa mu yi waya" tace "Toh shkkn Jay, sai anjima dama duk na gaji, wanka xan yi ma yanxu" Yace "Alright" daga haka ya katse wayarsa, Mami na kallonsa tace "Wacece?" Ya kalleta da sauri sai kuma yace "Ohk wata coursemate dita ce from Nigeria...." Mami tace "Ya aka yi tasan kana India?" Yace "I told her I will be coming to India tun last week" Mikewa yayi ganin Heedayah xata sauko saman gadon ya nufeta yace "What happened?" Tace "I want to ease my self" Tashi Mami tayi ta kama hannunta xuwa toilet dake ward din. Washegari da asuba aka shigar da Heedayah theater, a asibitin Junaid ya kwana ranan, coz shi ma he is so tensed, he just don't want to imagine the operation won't be successful, haka ma Maminsa da bata yi wani bacci daren ranan ba, ita kanta Heedayah duk son baccinta bata yi baccin ba daren don idon na damunta sosai, Mami taji tausayinta ba kadan ba, har karfe goma na safiyan Mami na xaune saman darduma hannunta rike da carbi, Junaid yace "Mami baki yi breakfast ba, pls take something" Tace "Toh" Tea ya hada mata a cup ya mika mata ta amsa, Mami bata wani sha shayin ba ta fita ta xauna saman kujeran dake jere gaban theatre din da aka shigar da Heedayah.... Karfe sha biyu likitoci biyu suka fito theater din sanye da gown din operation, Mikewa Mami tayi wanting to hear something from them, da turanci daya likitan yace mata ta kwantar da hankalinta all will be well, daga haka ya wuce, Mami ta koma a hankali xauna, bayan minti talatin wasu likitocin uku suka fito su ma din dai haka suka ce mata, ita dai gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya, daga karshe nurse biyu suka fito, Mami ta kara tashi ta nufesu, su ma dai xancen daya ne suka yi wucewarsu. Sae kusan azahar aka kai Heedayah ward dinta tana bacci, Mami na xaune kusa da ita sai kallonta take an rufe mata idanuwanta da white eye pads, gaba daya she is disturbed and tensed, Junaid dai na tsaye daga gefen gadon ya rungume hannunsa shi ma yana kallonta, wayar Mami ya fara ring ta dauka ganin Abba ne ta daga a sanyaye ta kai kunne, gaisawa suka yi tace "Yanxu aka fito da ita, but akwai eye pads a idanuwan...." Daga daya bangaren Abba yace "Toh Allah ya sa an dace, can I speak to her now?" Mami tace "Bacci take" Abba yace "Toh I will call back later" daga haka suka yi sallama ta ajiye wayar tana kallon junaid tace "Toh baccin me take haka, ko anaesthesia da aka yi mata ne?" Yace "No, anaesthesia din da aka yi mata iya aikinsa bangaren idon, she is not unconscious bacci take" Mami tayi shiru bata ce komai ba.... Har karfe hudu na yamma Heedayah bata farka ba, Junaid ya tafi yyi sllh ya dawo ya tadda Mami na sallahn ita ma, ya xauna kusa da Heedayah ya kamo hannunta yana kallonta ganin sai motsi take, a hankali cikin rawar murya ya ji tace "Mami idona na min ciwo" Ya dafa goshinta still holding her hands tight yace "Xai daina dear...." Ganin xata mike xaune ya dagata ta xauna ta kai daya hannunta idonta, da sauri ya rike hannun ganin cire pads din take son yi yace "Noo don't...." Ta fashe da matsanancin kuka xata kwace hannunta tace "It's paining me" ya ki sake hannun yace "Zanyi tafiyata in bar ki ke kadai a nan if you don't stay still now...." Ganin kukan da take ya rungumeta yace "Toh yi hakuri xa a cire maki yanxu, ki daina kukan, I will call the doctor now" cikin rawan murya tace "Yana min xafi sosai" Mami na idar da sllh dama fita tayi kiran likita don yace idan ta tashi a sanar masa, yana shigowa allurai biyu yyi mata ya sa mata drip ya fita... Ba a dau lkci ba kuma tayi bacci junaid na rike da ita har sannan, Mami ta sake komawa gun likitan don jin abinda ake ciki, nan ya sanar mata nan da kwana uku xa a cire eye pads din a duba idon with hope that tayi gaining sight dinta clearly, kafin kwana ukun kuma xa ayi ta mata injections xa kuma ta dinga shan magunguna, Mami tace "But is there nothing to do about the pain pls?" Yace "The pain will subside before tomorrow...." Mami tace "Are you giving me hope that the operation is successful Doctor?" Likitan ya girgixa kai yace "We are also hoping it's successful, but if it's not, then we will try anoda operation.... The last" Mami ta kasa ce masa komai, can ta mike tayi masa godiya a sanyaye ta fita. Tana komawa ward din Junaid ya kwantar da Heedayah ya mike yace "Xan je in dawo yanxu Mami" Mami tace "Ina xa ka?" Yace "I want to get something, ba dadewa xan yi ba" tace "Ohk, ka siyo fresh milk when coming back" yace "Toh" daga haka ya fita, nan kuwa tun safe Salima ta ishesa da kira shine yyi deciding kawai ya tafi ya sameta inda tace masa take ko xata daina kiransa. Yana tsaya gaban hotel din ya kirata, tana dagawa yace "Ina waje ki fito" tace "Haba ka shigo ka jirani a reception mana Jayy..." Yace "But I can't come in, ki daure dai ki fito Ina sauri ne" tace "Wllh tun safe kai na ke ciwo a kwance ma nake ynxu, bbu ynda Suraj bai yi in raka ba na ki fita, ka daure ka karaso ko reception ne plss Jayy" yace "Alright" daga haka ya katse wayar ya shiga cikin babban hotel din, Yana reception din ya kirata, sae ga ta ta sakko sanye da riga da wando sai black veil da ta daura a kai, shi duk wayar da suke ya kasa yrda da gaske tana India sai ynxu da ya ganta, ta sakar masa murmushi tace "Welcome, mu shiga ciki in daura after dress mu tafi hospital din, tun safe na damu Ina son xuwa wllh" yace "Aa ba a barin mutane fiye da biyu and yau ba visiting day bane" lkci daya mood dinta ya canxa tace "To yaushe ne visiting day din?" Yace "Nan da 3 days" Ta tabe baki tace "Toh mu je ciki" yace "No, na gaisheki, xan koma ynxu coz I need to get them food" Ta marairaice tace "Haba Jayyy, ae ba cewa nayi ka shiga ka dade ba, kawai mu je kaga Inda nake, ni fa bbu wanda yasan ma na taho India, tafiyar ce ta xo min cikin gaggawa, Kuma Suraj bai son tafiya shi kadai dama" Bata jira cewarsa ba ta kama hannunsa tace "Come on mu je plss" da mamaki yake kallonta, can ya janye hannunsa daga nata still following her slowly har xuwa hotel room din da take.




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Junaid ya nufi kujeran dake makeken dakin hotel din ya xauna, gefensa ta xauna tana wani murmushi tace "Me xan kawo maka Jay? Ko in sa a kawo maka abinci?" Ya girgixa kai yace "Nothing, saurayin ki kika biyo India kenan?" Tace "Ehh shi na biyo amma wllh sbda kai na xo, India ai ba wani kasar xuwa hutu bane kasar xuwan marasu lafiya ne, wani saurayina fa tun last week yake son mu je dubai mu huta amma na gwammace in biyo wannan xuwa India duk don sbda kai wllh" Junaid ya gyada kai yace "Ni kuma me xan maki da kika biyosa India sbda ni?" Ta wara ido tace "Just to see you mana, Ina dawowa daga Abuja fa aka ce min kun taho India da makauniyar nan...." Yana kallonta da kyau yace "Kada ki sake ce mata makauniya" Ta d'an yi shiru, sai kuma ta tabe baki tace "Toh ka tafi ko sallama babu shi yasa da na samu opportunity kawai na biyo ka" ta karasa tana murmushi, Ya girgixa kai yace "So this the best life you think you are living right?" Tayi frowning face dinta tace "Ban gane ba, me ya kawo wannan maganan kuma?" Ya tabe baki yace "Anyway shkkn, so yanxu kin gan ni kuma mun gaisa, plss kar ki sake kiran line dina sbda a hospital nake da mara lafiya.... Pls don't call again I beg you" Ta marairaice tace "Wllh tllh sbda kai na xo kasar nan Jay, ka kaini asibitin mana nima muyi jinyar tare" Yace "Aa, idan mun koma Nigeria sai kiyi jinya but not here coz bbu ma wanda yasan kin xo nan, I repeat don't call me again, I don't even want to ask what ur name is, but what ever it is plss don't call my line again Lady" Kwantawa tayi jikinsa kamar xata yi kuka tana shafa kirjinsa tace "Haba Jay...." Turata yyi har sai da ta fadi kasa ya mike yana mata wani kallo yace "Are you stupid?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Tun da nayi respecting dinki na xo har Inda kike kada ki sake kirana, na xo ne dama don kada ki kuma kirana, idan kun gama abinda ya kawo ku ke da saurayin naki ku koma inda ku ka fito tare, we will meet back in Nigeria...." Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo ya bude kofar xai fita suka kusa cin karo da Suraj din, Junaid ya kallesa daga sama har kasa, ya bi gefensa ya fita dakin, Suraj ya kalli Salima da ta kauda kai da sauri, yana nunata da yatsa yace "Dama shi yasa tun jiya kike wasa da hankalina ashe appointment gare ki da wani? To maxa kwashe kayanki ki bar min hotel room dina yanxun nan" Ta masa wani kallo tace "Ae ba wani ya kawo ni kasar ba, yanda muka xo tare haka xa mu koma tare, kawai don ka kawo ni India sai aka ce maka haka xaka dinga samu na baxa ka biya ba kamar wata gareji, to ko garejin ma ae ana biya" ko amsa bai bata ba ya tafi inda jakar kayanta yake ya dauka ya bude kofa ya jefar corridor din hotel rooms din, ya koma ya dauko handbags dinta da sauran tarkacenta duk ya watsar a waje, bude baki tayi tana bin sa da kallo a tsorace ta kasa cewa komai ita ma ya tafi ya ja ta har kofan ya turata waje ya rufe kofar sa. Junaid na isa hospital din dab da magrib Mami tace "Where are you coming from Junaid?" Ya ajiye ledan madaran hannunsa ba tare da ya kalli idonta ba yace "Mami wata frnd dita ce da muka hadu online years back, she's here in india, so shine naje muka gaisa" Mami ta ta6e baki bata ce komai ba, gadon da Heedayah ke kwance ya nufa ya xauna saman kujera yana kallonta, bacci take heavily, kana gani kasan alluran bacci aka mata, ya kai hannu goshinta a hankali ya ji da xafi, Mami tace "Ynxu naje nayi masu complain xafin jikin nata" Ya gyada kai bai dai ce komai ba, Mami tace "Shaheedah called me daxu bayan ka fita" Kallon Mami yyi yace "Ohk" tace "Baban nata ya ji sauki amma sosai koh?" Yace "Ehh ya samu lfya" Wayarsa da ya fara ring a aljihu ya ciro, ya ga Beauty gaban screen din, ya d'an saci kallon Mami dake kallonsa, ya mayar da wayar aljihu bayan ya sa shi total silent, yana ta xaune dakin har Magrib yyi, Mami ta shiga bandaki yin alwala sai da ta fito ya mike yace "Xan je inyi sllh" Mami tace "Ohk" daga haka ya fita, sai da ya fito haraban katon asibitin ya ciro wayarsa ya ga miss calls din Salima kusan ashirin, ya wani buda ido da mamaki yana kallon screen din wayar, sai ga kiranta ya kuma shigowa, dagawa yyi ya kai kunne kafin yace komai ta fashe masa da kuka sosai tace "Jay wllh ya koreni ya watsar min da kaya ganinka da yayi, gashi ni bani da inda xan je bamu da kowa a kasar nan, ko kudin kama hotel ma bani da shi balle kudin komawa Nigeria ni dai kawai biyosa nayi tunda mun saba tafiya tare, yanxu haka ina titi da kayana daga ni sai kudin Nigeria dubu uku a jakata, don girman Allah ka rufa min asiri, nayi ta kiran layinsa ko hakuri ne in basa amma yyi blocking dina wllh" Junaid
End Ads