x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - HEEDAYAH

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 115649 words

Category: Love Stories

Views 132

22 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
"Kai da wnn mana, ni ban san sunansa ba, kai sai ka dinga tsokanata shi kuma sai ya dinga buge min hannu yana min fada" fitowar Mami ya sa Junaid ya mike yace "Mami sai da safe, xan wuce" Mami tace "Ka ci abinci ai?" Yace "Na ci" Mami tace "Toh Allah ya tashe mu lfya" kofa ya nufa, Heedayah tace "Mami ina xa shi?" Mami tace "Xai wuce gida" Heedayah tace "Mami me yasa baxai tsaya a nan da mu ba?" Mami tayi murmushi tace "Ai xai dawo" Heedayah tace "Ni ina son ya tsaya a nan" Junaid ya kalleta daga bakin kofar da yake tsaye ya bude kofar ya fita. Da asuba aka tashi da ruwa sosai, wajen shidda da rabi Mami na parlonta aka kwankwasa kofa, mikewa tayi ta bude kofar Shuraim yyi kasa da kansa yace "Ina kwana?" Tace "Lafiya lau" yace "Xa mu yi karatu ne" Juyawa Mami tayi ta wuce daki, Heedayah na ta bacci tun bayan da ta tada ta yin sllh asuba, Mami ta tada ta, ta sa mata Hijab sbda garin yyi sanyi sosai suka fito, har snn Shuraim na tsaye bakin kofa, Mami ta mika masa ita, ya kama hannun suka fita parlon ya kulle mata kofarta, Heedayah dai har snn idonta a lumshe yake tana bin sa, da sauri ta bude idanuwanta jin ta ci karo da sofa a parlor, ko tsayawa Shuraim bai yi ba har ya isa study area din Abba still holding her hand ya xaunar da ita nan kasa, kamr xata yi kuka tace "Shine ka buge ni da kujera?" Strictly yace "Kin san Allah idan kina min magana a gidan sai na fasa maki baki wataran, I have no business with you, if u dare talk to me again I will injure you" Yana yin yanda yake maganan yasa Heedayah tayi shiru bata dai ce komai ba, he was so serious, fuska daure yace "Sai na ce ki fara karatun??" A hankali ta fara karato suran da take, yana ta danna wayarsa har ta kai inda ta tsaya shekaranjiya, tace "Na gama....." Sai bayan kusan minti biyar ya ajiye wayar hannunsa sannan ya daura daga inda ta tsaya, his recitation was waow, kamar wani balarabe, Bai tsaya ba sai da ya sauke suran gaba daya snn ya daga kai yana kallonta, baccinta take hankali kwance bayan ta jinginar da kanta da arm chair dake wajen, ya dinga kallonta sannan ya kalli agogo dake nuna karfe bakwai ya mike, parlor ya wuce ya ga Rabi'ah sanye da schl Uniform yace "Je ki tada wnn yarinyar ki kai ta ciki" Bai jira cewarta ba ya wuce xuwa dakinsa. Abba na kallon Mami yace "Listen Rahinah, I know u are not after the income or anything of such, but...." Ta girgixa kai tace "But what Barrister? Ba mu yi da kai xan ajiye aiki ba, ba mu yi haka da kai ba, I can't... Aikina ya xama jinin jikina, it's part of me, I like my profession, ko ba komai I do help innocent soul that are not quilty and I enjoy doing that, so why are you trying to deprive me of the joy? Tunda har na iya kula da nawa yaran still ina aiki, har na aurar da daya, I can take care of little Heedayah also with my work, just that before 3 xan dinga dawowa gida...." Abba ya kasa cewa komai, can ya jinjina kai yace "Toh shkkn Rahinah baxan takura ki ba, I agree ki ci gaba da aikin ki" Tana kallonsa tace "I appreciate, Anjima matar da xata dinga kula da Heedayah when I am away xata iso, monthly xa a dinga biyanta dubu ashirin, I will pay that...." Yace "No you don't need to...." tace "A'a na sa a raina ni xan biya, I took that as my responsibility since I can be with her fully...." Yace "Toh kin san matar da xa a kawon" Mami tace "Ehh to ban santa ba garinsu daya da wata childhood frnd dita Shamsiyya, she said shesy good kuma xata iya" Abba yace "Shhkn, Allah ya mana jagora" tace "Ameen Great Man" D'an murmushi yyi yace "So ynxu dai tare za mu dinga fita da safe?" Dariya tayi tace "Not at all, karfe goma ni xan dinga fita, sai nayi ma Heedayah duk abinda ya kamata, ido kawai Mai aikin xata sa mata har in dawo" Abba yace "Alright" Karfe goma saura matar da Mami ke jira ta iso gidan bayan an mata kwatance ta waya, Mami ta fito main parlor, matar da baxata wuce talatin ba ta sauka har kasa ta gaisheta, Mami tace "Sannu da xuwa ya hanya" Matar tace "Alhmdllh Hajiya" Mami tace "Ya sunan ki?" Matar tace "Sunana Karime" Mami tace "Toh karime aikin ki ba wani da yawa bane, amma yana bukatar saka ido da kula..." Karime tace "Duk an koro min Hajiya, Kuma in sha Allahu xan iya, har ma da aikin gida idan da akwai duk xan yi babu damuwa...." Mami tace "Toh Alhmdllh, yanxu dai mu je in nuna maki inda xa ki ajiye kayan ki" Karime ta mike da sauri ta dau Ghana must go dinta ta bi bayan Mami, Dakin masu aiki Mami ta kai ta, Mai aikin Mumy dake xaune dakin ta gaida Mami, Mami ta amsa sannan ta sa karime ta ajiye kayanta suka fita, Mami ta kai karime parlonta tace "Nan ne bangarena, bana son ku wuce nan ke da ita, in dai tana bukatan wani abu na ci ki bar ta ita kadai ki tafi kitchen ki nema mata, xan nuna maki kitchen din da Inda komai ke ajiye.... Tsakanin ki da Allah nake son ki kulan min da yarinyata bbu ha'inci" Karime tace "Kai Hajiya ai d'a na kowa ne, xaki sameni me riketa da gaskiya in sha Allahu...." Mami tace "To maa sha Allah.... Ki tafi can dakin naku, warce kika samu a ciki daxu ta nuna maki inda xaki ajiye kayan ki sannan ki dawo...." Karime ta mike ta nufi kofa tace "Toh Hajiya" Mami ta xauna saman kujera don tayi deciding yau baxata fita ba xata yi monitoring yanda Karime xata kula da Heedayah. Junaid ya mike daga xaunen da yake yace "To Mami ai ni baxan san size din sweater da xan siyo mata ba, Kuma wani irin takalmi kenan?" Mami tace "To kai makaho ne? Look at her mana before going..." Ya dai yi shiru bai ce komai ba, can ya nufi kofa murya can kasa yace "Sai na dawo...." har xai fita tace "Then go with her kar kaje ka siyo wanda baxai yi mata ba har takalman ma a gwada mata, ka siyo ma Farida ma takalma biyu with a sweater" ya juyo yace "Toh" Mami ta kalli Karime dake xaune kasa tace "Ki duba daki ki dauko Hijab dinta da takalmi xa su fita, ai na nuna maki inda suke" Karime tace "Toh Hajiya" Da sauri ta shige dakin Mami, Heedayah dake xaune gefen Mami ta washe fararen hakoranta jin xa a fita da ita, Mami na lura da ita ta girgixa kai ta d'an yi murmushi, Shi kansa Junaid kallonta yake, Karime ta fito da sauri ta sa ma Heedayah hijab dinta da takalmi, Mami ta mike xata shiga daki don dauko turare ta sa mata, Karime ta dauke cup din da Heedayah ta sha cornflakes ta fita xata kai kitchen din da Mami ta nuna mata, a parlor ta tadda Mumy xaune tana kallon tv duk da gaba daya bata ma san abinda ake a tvn ba, Kwarjinin Mumy kadai ya isa a gane ita ma matar gidan ce, Karime ta d'an duka tace "Sannu da hutawa Hajiya" Mumy na kallonta a dakile tace "Yauwa.... Ke ce sabuwar mai aikin da ta xo yau?" Karime tace "Ehh ni ce" Mumy ta d'an saki fuska tace "Sannu da xuwa, daga wani garin kika xo?" Tace "Daga kano na xo Hajiya, a can mariri iyayena suke" Mumy tace "Maa sha Allah, ai ko nasan Mariri..." Karime tace "Allah sarki" Mumy tace "Toh kin ci abinci kuwa" Karime tace "Na ci wllh Hajiya" Mumy tace "Toh ki saki jikinki kin ji, ko me kike bukata ki xo ki sameni...." Karime ta kara dukawa har kasa tace "In sha Allahu Hajiya, Nagode Sosai sosai, Allah ya kara girma" Mumy na murmushi tace "Ameeen" Karime ta mike ta wuce kitchen, Mumy ta bi ta da kallo..... Ba a dau lkci ba sai ga Junaid ya fito rike da Heedayah, Junaid ya gaida Mumy, da fara'a sosai ta amsa tace "Sannu Junaid, xa ku fita ne" yace "Ehh xa mu je mu dawo" Mumy tace "Ke 'yar fara ba gaisuwa?" Heedayah dai tayi shiru, Junaid ya duka dai dai fuskarta yace "Can't you greet?" A hankali tace "ina kwana" Mumy tayi dariya tace "Ina wuni dai xa ki ce baby" Heedayah tace "Ina yini" Mumy tace "Lafiya lau, xo in gyara maki Hijabin" Junaid na rike da Heedayah ya kai ta har gaban Mumy, Mumy ta gyara mata Hijab din tana kara goge mata bakinta tace "Me kika ci haka?" A hankali Heedayah tace "Cornflakes Mami ta bani" Mumy tace "Ahh Lallai ga alama, to sai kun dawo" Junaid yace "In sha Allah" yana rike da hannun Heedayah suka nufi kofa, Mumy ta bi su da kallo har suka fita parlon sannan ta sauke ajiyar xuciya tana jijjiga kafa. Anguwa ce ta manyan mutane da suka yi fice aka kuma san da su a kasa Junaid ya shiga, a hankali yake driving, Lkci lkci yake kallon Heedayah dake gefensa xaune ta jinginar da kanta da glass din motar idonta a waje kamar dai me gani, Junaid yace "Tell me what you are seeing...." ta juyo xuwa Inda take jiyo muryarsa a hankali tace "Darkness" shiru Junaid yyi driving slowly, can ya kamo hannunta daya murya can kasa yace "What color?" Ta wara ido tace "Just dark" Bai kuma cewa komai ba yyi parking dai dai wani gida da yake tunanin gidan da yake nema ne sbda number da ya gani daga gefen gate din gidan, dialing din number dake call logs dinsa yyi ba a dau lkci ba aka daga, yace "Gani a kofar gidan if I'm not mistaken" ajiye wayar yyi bayan an sanar masa ana xuwa, Heedayah tace "Ina muka xo?" Yace "Somewhere" tayi shiru kmr me son gane ma'anar somewhere da yace, can tace "Ohk wani waje?" Murmushi yyi yace "Yes" Bude gate da aka yi yasa ya kalli gate din ta cikin tinted glass dinsa, Mutumin jiya ne ya fito gate din, Junaid ya bude motarsa yana kallon Heedayah yace "Ki jirani in dawo yanxu" Ta 6ata fuska tace "Noo plss go with mee" yace "Yanxu xan dawo am not going anywhere" Ganin kiris ya rage ta fara kuka ya dau wayarsa yace "To rike min..." daga haka ya fita daga motar ya kulle ya nufi gun Mutumin dake tsaye, gaisawa suka yi, Mutumin yace "Fatan dai ban mu yi inconveniencing dinka ba, mu ma anyi delaying flight dinmu ne" Junaid na mika masa wayarsa yace "No, not at all..." Mutumin ya amsa yace "I am very grateful, ni Sunana Ahmad" Junaid yace "I am Junaid" Alhaji Ahmad yace "Nagode kwarai Junaid" Junaid yyi murmushi yace "Babu damuwa, ni xan koma" Alhaji Ahmad yace "Toh Allah ya kiyaye, da numberka ka kirani ai..." Junaid yace "Ehh" Alhaji Ahmad yace "To maa sha Allah I will save it" daga haka Junaid ya koma motarsa ya tada, Alhaji Ahmad dai na tsaye har yyi reverse ya wuce..... Karfe shidda saura Junaid ya koma gida tare da Heedayah bayan ya siya masu rigunan sanyi da takalma ita da Farida, Mami ta dauko eye drop da ya siyo jiya bayan ta kai kayan daki tace "Barrister yace idan ka xo sai ka gaya min yanda xa ayi da wnn" Junaid ya amshi ledan maganin ya fiddo su guda biyu yace "Wannan idan xata yi bacci da daddare xa a sa mata just two drop in each of her eye, shi kuma wnn idan ta tashi da safe, it's should be everyday ba a skipping....." Mami tace "Toh shkkn Allah ya sa a dace, su kuma maganin mene?" Yace "Toh ana sa rai with the help of this idan an xo yin operation din idon baxa a samu matsala ba idan Allah ya yrda...." Mami tace "Toh Allah ya sa" Mami tace "Babu wani wanda xata dinga sha?" Yace "A'a, sai dai in bincika" tace "Toh Shkkn...." Mikewa yyi yace "Ni xan koma Mami" tace "Baxa ka jira ka ci abinci ba?" Yace "Aa xan wuce" tace "Toh sai gobe" Khadijah ce ta shigo parlon Mami da sallama hannunta daya rike da plate me dauke da cake da aka yanka gida biyu yan madaidaita, daya hannunta kuma da wani cake din tana ci, ta karaso gun Heedayah dake xaune tace "Mumy tace ki dauki naki" Mami ta kalli Karime dake rakube waje daya tace "Ki amsa ki ajiye mata" Karime ta taso da sauri ta karba, Khadijah na kallon karime tace "Dayan aka ce ke ma ki dauka" Karime ta kalli Mami, Mami tace "Toh an gode" Khadijah tace "Cousin dinmu ne yyi birthday" Mami tace "Allah ya raya sa" Khadijah ta juya ta bi ta gefen Junaid ta fita, Mami na kallon Heedayah tace "Xa ki ci cake?" Heedayah ta gyada mata kai, Mami tace "Toh bata Karime ke ma ki dau naki" Karime ta mika ma Heedayah daya ita ma ta dau daya ta fara ci, Heedayah na kallon Inda take jin muryar Mami tace "Mami in tsan masa?" Mami ta kalli Junaid dake tsaye bakin kofa har sannan tayi murmushi tace "Cinye kayan ki ya wuce" Juyawa Junaid yyi ya fita dakin, Heedayah ta fara cin cake dinta, dai dai bakin kofar shigowa yau yyi karo da Salima, tana rike da gyalenta da jaka a hannu, suna hada ido ya bata hanya.... Cikin wani siririn murya tace "Noo ka wuce mana ai kai ka bude kofar...." Ya kara kallonta sannan ya bi gefenta yace "Thank you" tace "Haba thank you kuma, ai kai ka bude kofa" shi dai bai tsaya ba kuma bai ce komai ba yyi wucewarsa, ta bi sa da kallo ko kiftawa bbu... Karime ce kitchen bayan Magrib tana dafawa Heedayah Indomie, tana xuba Indomie din cikin ruwan dake tafasa kan gas aka bude kitchen din Mumy ta shigo, ganinta tace "Aiki kike yi Karime?" Karime tace "Ehh Hajiya Indomie nake dafa mata" Mumy tace "To ke kin ma ci abinci kuwa" tace "Ehh dama na rana bai kare ba...." Mumy tace "Na rana kuma, kin ga idan kin kai masu Indomien ki xo ga cous cous a kula ki diba ki ci kin ji, abincin rana ai ya huce yanxu" Karime tace "Toh Hajiya Nagode Sosai" Mumy tace "Amma fa kar ki wani ce ma uwar dakin ki nace ki xo ki amshi abinci ke dai kawai ki shigo kitchen ki diba kije can dakin ku ki ci" Karime ta risina tace "Toh Hajiya" Mumy ta ajiye cup din hannunta ta fita kitchen din.....


Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Washegari karfe goma saura na safe Mumy ta gama shiryawa xata fita office, Tana duban Karime a parlonta tace "Toh ni xan wuce aiki yanxu, sai ki saka ido sosai ki kula da duk abinda nace maki, karfe sha biyu na yi ki daura maku girkin abinda xa ku ci dai dai cikin ku, ita kuma Heedayah xuwa nan da sha daya abinda ki ka ga na hada mata jiya sai ki hada mata ki xuba Madara amma ban da sugar" Karime tace "Toh in sha Allahu Hajiya" Mami ta dau jakarta ta nufi kofa tace "Sai na dawo" Karime tace "A dawo lafiya" Har Mami ta fita ta juyo tace "Kar ki bari ta bar parlon nan komai xakiyi kiyi mata a nan parlon, bana son ku fito" Karime tace "Toh in sha Allahu Hajiya" Mami ta kulle kofarta ta wuce, A main parlor suka hadu da Mumy tana ma mai aikinta magana cikin tsawa, matar da baxata wuce Karime ba sai rawa jikinta yake tana bata hakuri, Mumy na ganin Mami ta dakata da masifar da take, idon da suka hada yasa Mami tace "Mun tashi lfya?" Mumy tayi murmushi tace "Lafiya lau wllh, ya kwanan Baby" Mami tace "Alhmdllh, ya na su Rabi'ah" Mumy tace "Lfya lau, sun ma wuce makaranta ai" Mami tace "Toh maa sha Allah, na fita..." Mumy tace "Toh Allah ya kiyaye hanya" Mami ta amsa da Ameen sannan ta fita parlon, Mumy ta bi ta da kallo har ta rufe kofa, ta wani ta6e baki ta kalli Sajida mai aikinta cike da masifa tace "Kin tashi a gabana ko sai na gaura maki Mari, 'yan aiki ko 'yan wahala, wllh bana son in sake tuna maki sharan dakin yarana idan ba haka ba ni ynda ake canxa sutura haka nake canxa ku don ma ki ji" Mai aikin ta mike da sauri ta tafi dakinsu Rabi'ah, Shuraim dake xaune dining ya ajiye cup din hannunsa ya mike ya dawo parlon, Mumy tace "Amma dai yau baxa ka fita aiki ba...." Yace "Sai da yamma...." Mumy tace "Na ji ma Baffan naku yyi tafiya ko?" Shuraim yace "Ehh yana Abuja" Mumy ta ta6e baki, Shuraim yyi kasa da kai yace "Mumy ki dinga hakuri da mutane don Allah, barin wa ennan bayin Allah, they don't deserve the way u are treating them, they never wished for their selves to be maid, and don't forget no condition is permanent, su Rabi'ah yara ne da baxa su iya gyara dakinsu ba idan sun tashi? Ba fa aikin da suke yi a gidan just gyaran dakin ma sai an masu?? This is...." Dakatar da shi tayi cikin tsawa tace "Rufe min baki malam, ni xaka taso kayi ma fada?" Yace "Ni ba fada na maki ba, I am telling
End Ads