ku kuma...." Tana fadin haka ta mike ta fita parlon, Abba sai kallon Mami da gaba daya mood dinta ya canxa lkci daya yake, can tace "Plss Barrister kayi ma kaka magana, try to let her understand cewar ba mai yiwuwa bane ni bani da iko da Farida wajen yayan Mahaifin ta take, let not make things complicated pls Barrister" shi dai bai ce mata komai ba, kaka na fita dama wayarta ta dauka ta lallaba ta kai ma Farida can bangaren Mami wai ta kira mata Junaid, junaid na daga kiran kaka ta fita da sauri, tayi kasa da murya suka gaisa tace "Kana ji na Junaidu, duk Inda kake ka taho yanxun nan xaka kai ni anguwa ko Rakiya kar ka sanar ma, kana isowa bakin get ka kirani sai in fito" Junaid dake kwance yace "Toh bari in taho kaka" tace "Yauwa Allah maka albarka, Ina jiran ka yanxun nan" daga haka ta katse wayar ta wuce dakinta tana cewa "Gantalallu wa enda basa son abun arxiki, ni bana biye ta taku ba" Kaka na komawa bangarenta sai ga Abba ya shigo da sallama, ya xauna saman kujera gaba daya he look confused, can yace "Kaka yanxu kinga cikin watan nan xa a fitar da Heedayah waje gyaran idonta, so yanxu kinga ai babu wani abu a gabanmu da ya wuce wnn..." Kaka tayi saurin cewa "Haba?? Kuma sun ce idon xai gyaru kuwa? Amma dai da ni xa a je koh? Kasan bata da kowa sai Allah sai ni" Abba yace "In sha Allah...." Kaka tace "Toh yaushe ne tafiyan in fara hada kayana?" Yace "Nan dai da sati uku" Kaka tace "Atoh Allah ya kai mu lafiya, Allah ya dubemu idonta ya bude ni dai" Abba yyi kasa da murya yace "Don haka kaka ki bar ko wani xance yanxu mu ji da gyaran idon da xa a fita yi" kaka ta kallesa tace "Atoh shkkn na bar xancen har sai idon Deedayata ya bude" Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, ya mike yace "Bari in je kaka, a taya mu da addu'a, ana kan processing din fitan ne" kaka tace "To wani kasar xa aje?" Yace "India" kaka ta washe baki tace "Xa mu ga su Hamita da muganbo kenan Amadu??" murmushi kawai Abba yyi ya fita daga dakin kaka ta mike ta daga hannu sama tace "Allah ka dubi yar marainiyar Allah ka bude mata idanuwanta, ka bude mata ido ya Allah ko son jikinta xai ragu" Karfe takwas dot Junaid ya kira kaka yace yana kofar gida, ta dau Hijabinta ta boye ta fito parlor tana kalle kalle xata fita, Shuraim dake xaune dinning yana shan tea ya bi ta da ido har ta fice daga parlon da sauri, Junaid ya sakko ya bude mata back seat yana gaisheta da ladabi, ta amsa tana washe baki tace "Allah yayi maka albarka Junaidu da bani da kai ai da nayi kuka yau, ni dai wllh ka fiye min kowa ma" murmushi kawai yyi ya tada motar, sai da suka bar layin suka hau saman titi yace "Ina xa mu kaka?" Tayi kasa da murya tace "Yau xumunci kawai nake son yi, kaga ai bai dace ace har yanxu ban san kowa naku ba, to don haka gidan yayan Mahaifin ka xaka kai ni mu san juna" Junaid was so surprise ya dinga kallonta ta madubi yace "Gidan Baffanmu?" Kaka tace "Ehh shi, ai xa a samesa yanxu da safe koh?" Yace "Ehh na bar sa a gida" Kaka tace "To maxa kai ni kar yyi ficewarsa, gwara xumuntakar tamu yyi karfi" murmushi kawai Junaid yyi ya dau hanyar gidan yayan late Abbansa.
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....
Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍
Parking Junaid yyi a compound din Baffan sa, ya sauka ya bude ma kaka bayan motar, ta fito tana kare ma kantamemen gidan kallo baki bude tace "Nan ne gidan kawun naka?" Junaid yace "Nan ne" kaka tace "Ikon Allah, to mu shiga, Allah ya sa bai fita ba dai...." Junaid ya shiga gaba tana biye da shi yace "Yana nan ai, ga motarsa" Kaka ta kalli motar da ya nuna mata tace "Kamar irin motar Umaru kuwa" Babu kowa parlon da suka shiga, Kaka ta xauna tace "Wato basu tashi ba kenan ana ta bacci" Junaid yyi murmushi yace "Bari in masu magana" daga haka ya wuce sama, kaka ta dinga bin parlon da kallo ta rike ha6a murya can kasa tace "Toh ai masu kudi ne su ma, ba gidan tsiya Shureen dina xai fada ba, ko gidan Umaru bai kai haka ba" Ba a dau lkci ba Junaid ya dawo tare da wata dattijuwa, Ta xauna tana kallon kaka da fara'a tace "Sannu da xuwa Mama, Ina kwana" Kaka ta kalleta tace "Lfya lau wllh, kece matar gidan?" Matar na murmushi tace "Ni ce Mama" Kaka tace "Atoh ya yara, ya gida" Matar tace "Alhmdllh wllh, fatan kun xo lfya?" kaka tace "Toh Alhmdllh, ba ma wanda yasan na fito sai shi Junaidun, nace dai yau bari in xo inyi xumunci ku san ni in san ku, bana biye ta Rakiya da Amadu ba, ko karyawa ban yi ba wllh na fito" Matar tace "Ikon Allah to bari a kawo maki kayan kari yanxu, tashi mu je daga ciki Mama, sannu da xuwa" Kaka tana washe baki mike tace "Toh" har parlonta ta kai kaka, ba a dau lkci ba aka cika gaban kaka da kayan karin kumallo, flask din ruwan Lipton me kamshi, soyayyen dankali da kwai da plantain, katon bread, sai wainar shinkafa da lafiyayyen taushe, ga farfesun kayan ciki a gefe, Kaka na kallon masu aikin dake ta jera mata abincin tace "Babu darduma in sauka kasa??" karamin carpet me laushi suka shimfida mata ta sauko kasa bayan ta cire Hijabin ta, komai sai da kaka ta diba ta ci a abincin, sai da taji tayi nak murya can kasa tace "Toh ko nan nace xan dawo da xama ai bbu me ce min komai tunda an xama daya yanxu..." Sallama aka yi kofar parlon Kaka ta amsa wani dattijjo da baxai wuce 65 ba ya shigo parlon, kasa ya xauna yace "Sannu da xuwa Baaba" Kaka na washe baki tace "Sannu, kai ne kawun Junaidun?" Yace "Ehh nine, Ina kwana" Kaka ta gyara xama tace "Lafiya lau, yau dai nace bari in xo in ganka ka gan ni, idan na biye ta uwar Junaidu baxa ayi xumuncin ba ma, kasan yaran ynxu basu san amfanin xumunci ba" Yyi dariya yace "Gaskiya ne Baaba, to ya ku ka baro mutan gidan?" Tace "Lafiya lau, ko sanin na fito ma basu yi ba, nace inyi maxa in xo kar ka fita, tunda shi Amadu na ga karfe takwas xuwa tara yake ficewa" Yace "Wannan gaskiya ne" Kaka tace "Toh bayan xumunci kuma a gaskiya har da alfarma na xo nema a gun ka" Ya xauna da kyau yace "Toh ina sauraron ki Baaba" Tace "Ba wani abu bane d'an nan, jikana Aliyu na xo nema ma auren 'yar ka, wato Farida, kaga dai Aliyu ni na haifi ubansa Amadu, tunda nake ban ta6a ganin yaro da ya tashi bashi da matsala irin Aliyu ba, bbu ruwansa da kowa, ba shi da abokin fada, kai in takaice maka shi ba me magana bane ma, to shine na ya6a da hankalin farida tunda ta xo kuma ta xauna dakina, komai ita ke min wllh, ko nayi laifi da nayi wnn tunanin bawan Allah, amma dai ya ma sunan ka tukun" Yace "Sunana Aminu" Kaka tace "Toh ai sunan babana kenan, Allah sarki, to yanxu ya kaga..." Yace "Batu ne mai kyau wannan Baaba, amma sai dai Farida ynxu karatu take wllh" Kaka tace "Oh oh Allah, karatu na hana aure ne wai dama? Ku me yasa ku ka bari boko yyi maku kaca kaca haka, Shi kansa Amadun fa haka yace min, meye a ciki idan anyi auren ta ci gaba da karatun ta, ynxu shekararta nawa ma dai tukun?" Yace "Bata cika sha shidda ba ma" Kaka tace "Shine tayi girma haka? Toh kaga kuwa ai aurar da ita shine rufin asirin mu da ku, kaga dai takanas na taso da kafafuwana na sameka a gida sbda alkhairin da nake nema da ku, a gaskiya idan kace min A'a raina xai baci Aminu, da girmana na taho wajenka.... Kuma da Rakiya ta san gidan banxa ne gidan Amadu ai baxa ta shigo ba...." Yana murmushi yace "Gaskiya ne Baaba, in sha Allahu tunda ba fin karfina alfarmar da kika xo nema yyi ba xanyi bakin kokarin ganin komai ya tafi yanda kike so, amma sai Farida ta gama secondary in sha Allah" Kaka tace "Toh tunda dai ka amsa ai shkkn, kwana nawa ne xa a ga ta gama sakandarin, shi ma massers dinsa yake yi a Zaria, kaga sai su gama lkci daya kenan, bari anjima shi xan ma kira ya mayar da ni gida sai ka gansa, yana nan ko yatsa ka sa masa a hannu baxai ciza ba, yaron kirki me girmama na gaba da shi, Kai ni ko rashin kunya na jika da kakan nan ma ni bai ta6a min ba, tamkar uwarsa haka yake min biyayya" Shi dai murmushi kawai yake yace "Toh shkkn Baaba xan fita wajen aiki sai na dawo, ai kina nan?" Tace "Aa ina nan kilan har ka dawo, yanxu fa na xo" yace "Toh maa sha Allah, sai anjima" tace "Allah maka albarka" ya amsa da Ameen ya fita. Yana fita wayar kaka ya fara kara ta fiddo a jaka da sauri, da yake ta san Inda ake dannawa ta danna ta kai kunne, Muryar Mami taji, kaka tace "Ke ba fa wani waje naje ba, gidan ta salla na tafi, anjima in sha Allahu xan dawo" Mami tace "Toh shkkn, amma ba sallama kaka" Kaka tace "Ehh to da yake tafiyar ta gaggawa ce, anjima dai xan dawo in sha Allah" Mami tace "Toh Allah ya dawo da ke lafiya" kaka tace "Ameen" daga haka ta katse wayar ta ajiye ta jawo sauran farfesunta tana lasa. Har aka yi Magrib Kaka na gidan Baffansu Junaid, Matarsa kuwa Hajiya Zulaiha bata bar Kaka ita kadai ba, tare suka yini, a xamansu na yan awannin nan abinda kaka ta manta ne kawai bata gaya mata ba, tarihi iri iri, Wanda ya kamata da Wanda bai kamata ba, tun mijinta na da rai har sanda ya rasu, amma ko da wasa kaka bata gaya mata halin Mumy ba, Hajiya Zulaiha dake yanka ma kaka kankana bayan anyi sllhn Magrib tace "Na kirasa yana hanya ynxu Mama" Kaka tace "Toh kinsan shi xai mayarda ni gida kar in gigita 'ya yana suyi xaton 6ata nayi shi sa na damu" Hajiya Zulaiha tayi dariya tace "Kila yana can gun budurwar sa tun da kika ga har war haka bai shigo ba" Kaka tace "Au, yana da budurwa kenan?" Hajiya Zulaiha na dariya tace "Kwarai kuwa" Kaka tace "ikon Allah, ko da yake ga Shureen ma Ina kokarin ganin yayi aure nan da 'yan watanni balle Junaidu, da kyar idan bai girmi Shureen ba ma" Hajiya Zulaiha tace "Lallai kam" Kaka tace "Ko da yake ga Farida ma naji shekarunta ba wasu shekaru bane amma duk ta balaga, kusan sa'ar Khadijahn Amadu ce fa, Ita kuma Rabi'ah sa'ar Deedayah Ina jin, don duk kwailaye ne" Hajiya Zulaiha dai tayi dariya ta ajiye ma kaka kankanan tace "Bari in je inyi sllh Mama, amma da kawai kiyi kwanan ki a nan Mama" Kaka tace "A'a ba mutunci gare su Amadu ba sai su iya min fada ba ruwana, bari dai in tafi ba dai na ga gida ba" Hajiya Zulaiha tace "Toh shkkn Mama" daga haka ta fita parlon.... Tana fita da minti sha biyar Junaid ya shigo, kaka tace "Ashe kana da budurwa Junaidu, yanxu matar kawunka ke ce min tadi ka tafi" yace "Aa gidan abokina nake" tace "Au, to in tashi mu tafi kada su Amadu su yi ta nemana koh?" Yace "To mu je kaka, ai kin ci abinci" Kaka tace "Idan ma nace ban ci ba, ba sai Allah ya kama ni ba, Tuwo ce fa malmala uku aka saka min ga miyar kubewa duk nama da Ganda ga kifi, ga kuma lemo me sanyi... To ina xan samu haka gidan Amadu?? Gaskiya matar nan ta san mutunci, baka ga ba wllh sai ji take da ni, komai ta rarumo ta kawo min, daxu da rana har kwadon zogala ta min bayan shinkafa da miya da uban nama da ta xubo min, ni dai gaskiya an karrama ni a gidan nan, ai Rakiya sai dai ince Allah yyi mata albarka kawai, danginta sun san mutunci kam" Murmushi kawai Junaid yyi yace "Idan kin gama shiryawa Ina parlor kaka" Kaka tace "Toh, d'an Albarka" Sai bayan kusan minti ashirin kaka ta sakko da handbag dinta, tana kallon yan matan gidan guda uku dake xaune parlor tace "Toh ko Sudess ma idan ya samu daya daga cikin wa ennan bai gode ba, ynda yan mata ke wahala ynxu...." Har parlon Baffan Junaid kaka ta shiga, yace "Aa Baaba ai na xata kwana xa kiyi a nan" tace "Aa su Amadu xa su min fada" Yace "Ikon Allah, toh Junaid xai maida ki amma" tace "Eh yana jirana ma yanxu haka" mikewa yyi yace "Toh Ina xuwa Baaba" yashiga dakinsa sai gashi ya fito ya mika mata dubu goma da ladabi yace "A siya goro Baaba" Kaka ta amsa ta saka a jaka tace "A'aaahh ayi haka d'an nan, ai da ka bar shi wllh, toh Allah yayi maka albarka, nagode ka ji" yace "Godiya ya tabbata ga Allah" rakata yyi har xuwa parking space tare da Hajiya Zulaiha da ta bata atamfa da turarurruka, tayi ta daga masu hannu tana washe baki har motar ya fita gidan, bayan sun hau titi tace "Gidan ma babu wahalan ganewa kaga idan xan dawo baxan sha wahala ba koh" Yace "Haka ne kaka" Tare Junaid da Kaka suka shiga parlor, Rabi'ah dake kwance parlon tana kallon Tv tace "Sannu da dawowa kaka" kaka tace "Yauwa.... Junaidu tafi ka dauko min Deedayah ga sauran nama na kulle mata a leda" yace "Toh" daga haka ya nufi part din Maminsa, Rabi'ah tace "toh mu fa?" Kaka da ta nufi dakinta tace "Uwar me na hada dake banda dai ke jikata ce, idan Maryam ce ko Amadu kya gaishesu a kwance?" Daga haka ta shige dakinta. Mami na kallon Junaid bayan ya gaisheta tace "Daga ina ku ke?" Yace "Gidan Baffanmu" Mami tace "Baffan ku? Kai da kakan?" Yyi yar dariya yace "Da sassafe ta kirani wai in xo in kaita" Mami ta dinga kallonsa da mugun mamaki tace "Sai ka kai ta?" Yace "To meye a ciki Mami?" Mami ta mike tace "Why didn't you call and ask for my opinion Junaid???" yyi kasa da kai yace "Mami naga ba wani abu bane, ai kowa ya san tsoho..." Xata yi magana aka bude kofar, shiru tayi kaka ta shigo tace "Ina Deedayan?" Mami tace "Sannu da xuwa kaka" Kaka tace "Yauwa Ina Deedayah ga nama na kullo mata" Mami tace "Suna parlon Barrister" Kaka tace "Kai Junaidu tafi ka dauko min ita, Ina iya shiga parlon yanxu Amadu ya rufeni da bala'i" Mikewa yyi ya fita parlon, Kaka tace "Wllh anguwa naje ke dai Rakiya, mutum yyi ta xaman gida kamar bashi da jama'ah" daga haka ta fita ta bi bayan Junaid da sauri, tun kan ya shiga parlon Abba ta tsayar da shi tayi kasa da murya tace "Kar ka gaya masu daga Inda muke, cewa kawai xakayi a bakin titi ka ganni ka dauko ni, har ita Rakiyan kar ka gaya mata kaji" Yana murmurshin karfin hali yace "Toh" daga haka ya shiga parlon ta koma nata dakin.... Washegari Sunday da safe Shuraim ya shiga gaida Abbansa, Abba na aiki system dinsa ya amsa yace "Anjima xaka ajiye Farida makaranta" Ya kalli Abba amma bai ce komai ba, Abba yace "Before then, xan maka transfer ku je tare tayi shopping, da yamma sai ka ajiye ta schl din" yyi kasa da kai yace "Toh" Abba yace "That's it, Kai yaushe xaka wuce Zarian?" Yace "Gobe da safe" Abba yace "Allah ya kai mu" mikewa yyi, ya ma Abbansa sallama ya fita, direct dakin kaka ya nufa, Kaka na ta gyara kayan da ta binciko a press din dakin, Heedayah kuma na kwance saman gado tana cin naman da kaka ta kawo mata, kaka kuma na bata labarin irin abubuwan da ta ci a inda taje jiya, Heedayah tace "Toh baki gaya min sunan wajen ba...." Kaka tace "Toh wai ina ruwanki, ke dai kawai ki bari, akwai abinci a gidan" Heedayah ta tallabi chin dinta tace "Toh shine ni baki je da ni ba?" Kaka tace "Ai kinsan a boye na bar gidan shi yasa, amma ba gashi na kullo maki sauran nama ba" Shuraim ya bude kofar ya shigo dakin, kaka tayi tsit da bakinta tana ci gaba da linkin ta, Murya can kasa Heedayah tace "Kaka waye?" Kaka tace "Iska ce ta turo kofa" Heedayah ta turo baki tace "Na xata wnn Shureen din nan ne...." Kaka tace "Shureen kuma, me xai shigo ya min, baki ga tun wayewar gari bai ko shigo gaidani ba" Heedayah