x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 36 - HEEDAYAH

  • 105001 words
  • 108000 words
  • Out of 115649 words

Category: Love Stories

Views 156

22 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ba, don da kai ka haifeta baxa ka yi mata sha'awar xuwa makaranta kwana ba, me yasa baka kai 'ya yan cikin ka ba sai ita?? Shi dai rikon amana dama da wahala take sai wanda Allah ya ba..." bata jira cewarsa ba ta fice daga parlon, Mikewa Mami tayi ta nufi kofa Abba ya bi ta da ido har ta fita, Mumy ma ta mike ta fice daga parlon bacin ranta ya kasa boyuwa gaba daya, dakin Shuraim ta wuce direct ta samesa ya shimfida darduma ya dauko qur'ani ya xauna, cikin daga murya tace "Aliyu a kan uban me yasa kace a kai yarinyar makarantar boarding?" Shuraim dake kallonta yace "Aa, naga kamar ba wani son xamanta gidan ake ba...." Tayi masa wani tsawa tace "Uban waye yace maka baya son xamanta gidan?? Kai da wa ku ka yi haka?" Yace "No naji kaka ta ce ta fara rainata, so it's better we shouldn't let that go far..." A fusace Mumy tace "Toh kai Ina ruwanka da xancen da ka tsoma baki? Dangi uwa ko ta uba? Meye hadin ka da ita da har xaka bada shawara kan lamarin ta iyye? Meye damuwar ka da ita nace?" Yana bude qur'anin gabansa a hankali yace "Nima din ban fiye son ganinta a gidan bane shi yasa na kawo nawa shawarar for my own good" Mumy ta jefa masa wani shegen kallo tace "Sau da nawa da nawa kake xaman gidan idan ba gulma da munafurci ba Aliyu?? Sati da lahadin da kake dawowa yi a gidan ne xaka wani ce kai ma ba ganinta kke son yi ba? Uban ma me ta tsare maka tukun? To ynda ka kawo shawarar a kai ta makarantar kwana sai ka koma kace a sa ta a day, in har kana son wanyewa lafiya...." Da mamaki yake kallon Mumy yace "Toh Mumy ke kuwa meye na ki idan an kai ta makarantar kwana? Naga kema ba wani son xamanta kike a gidan ba fa, so it's better she should stay away from this house completely, hankalin kowa xai fi kwanciya, ni na xata ma xaki fi kowa murna da shawarar da na bada, I see no reason da xa ki daga hankalin ki don ance xa a kai ta boarding, sai dai idan da akwai wani abun daban..." Mumy da ta bude baki tana kallonsa tayi shiru ta kasa cewa komai da farko, can ta dake tace "Akwai wani abun kamar me, ban fahimta ba?" yace "No nima ban sani ba, kawai dai nayi tunanin haka ne" Ta hadiye abu da kyar tace "To bari in fito maka a mutum yanxun tunda ba tsoron ka nake ba Aliyu, ban ga dalilin da xa a kai yar tsintuwa tsadadden makarantar kwana da ya fi makarantar da 'ya yan masu gida ke xuwa ba, baxan laminta da hakan ba" wani murmushi Shuraim yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "But ke kika ce baki da ra'ayin a kai su Khadijah makarantar kwana lkcn da na kawo ma Abba shawaran haka few years back, amma in har yanxu kinga kina son su je, ni xan yi ma Abba magana baxai ki kai su ba su ma" Tsawa Mumy tayi masa tace "Wai ban gane alkiblar ka ba Aliyu, kare yar tsintuwar kake yi kke challenging dina ko kuma shawara da ban bukata daga gareka ba kke bani?" Ya girgixa kai yace "Aa ko daya" Tana nuna sa on a serious note tace "Toh tun wuri idan ba haduwa kake son yi da fushina da bala'i ba duk wani abu da ya shafi lamarin yar tsintuwar nan kada ka sake sa baki, nace kar ka sake, bbu ruwanka da duk wani lamari da ya dangance ta ko da kuwa Ubanka ya tambayi opinion dinka, just remain mute" A hankali yace "What if i am also trying to find a way out for my self, as in.... May be I am not comfortable living in the same house with her also, Nima ina neman mafita...." Mumy tace "Toh sai ka tsiri cewa a kai ta makaranta me tsada, Ina aka kai makarantun gwamnati da xaka kira Turkish??" Yace "Sbda hakan kadai xai ba ma Abba karfin gwiwar kai ta, idan da na gwamnati nace a kai ta Abba baxai kai ta ba" Mumy tace "Toh ni ba ruwana da duk wnn, ni kawai ka san ynda kayi ka sa a fasa ma kai ta boarding din gaba daya" Yace "Toh" tace "Toh me??" Yace "Toh in sha Allah" Tace "I am serious Aliyu kada ka raina min hankali" yace "Ehh xan kara yi ma Abba magana in sha Allah" Juyawa tayi ta nufi kofa ya bi ta da kallo har xata fita ta juyo tace "Toh yau litinin me ya hanaka komawa Zarian ma?" Yace "Sai Wednesday in sha Allah" Mumy tace "Ba dai degree kake ba Masters ne, idan xaka tsaida hankalin ka gu daya ka tsaya kayi karatu tsakani da Allah ka tsayar, ni ban ma ga amfanin weekend da kke dawowa ba, Sudais idan ya tafi ba sai bayan watanni me yawa yake dawowa ba, kai kuwa kamar wanda ake mintsili ko kuma wanda yyi wani ajiya a gida yana dawowa dubawa a kai a kai" tana kai wa nan ta fita ta kulle kofar, mayar da dubansa yyi saman qur'anin gabansa ya d'an yi murmushi cikin cool voice dinsa ya fara karatu. Washegari da safe Mami na kitchen tare da Heedayah tana gwada mata yanda xata dinga hada shayi da kanta, A hankali Heedayah ke diban madaran kamar tana tsoronsa har wani rawa hannunta yake yi sai ta xuba a cup, Mami tace "Look, ki nutsu... Ko me xaki yi ki dinga yi gently don't panick, now fetch the Milo also..." Heedayah ta kai cokalin cikin Milo din ta debo, yamutsa fuska tayi tace "Mami me yasa kalan shi haka? And..." Mami ta dakatar da ita tace "Deba nace ki na batan min lkci xan tafi in shirya" Sake debo milon tayi ta xuba a cup, Mami tace "Sugar kuma cube uku xaki dinga sawa" Heedayah ta kirga cube din sugar din ta xuba a cup din, Mami bata bari ta dau flask din da kanta ba don a cike yake, ta xuba mata ruwan xafin cikin cup din dake dauke da kayan shayin, Heedayah sai kallon tiririn dake tashi take ko kiftawa bbu, Mami ta dau bottle water ta karasa cike cup din tace "Idan baki son yyi maki xafi sosai sai ki kara ruwan sha a ciki" Mami ta rufe gwangwanayen madaran ta ajiye su gefe da sugar, daga kai Heedayah tayi suka yi ido hudu da Shuraim da ya bude kofar kitchen din, Mami ma ta juya, sauke kansa yyi yace "Ina kwana" Mami tace "Lafiya lau" ya juya xai fita Mami tace "We are not stopping you from doing what u came to do" Ya d'an tsaya kamar me contemplating ya fita ko ya shiga kitchen din, can dai ya shiga ya tafi gun da mug suke ajiye, Heedayah ta bi sa da kallo, ya dau daya ya dawo xuwa gun flask, a hankali Heedayah tace "Mami shima shayin xai yi ya sha?" Mami tace "Ina ruwanki??" Bin bayan Mami Heedayah tayi ganin xata fita kitchen din da cup din shayin, sai da suka isa kofa ta juya tana kallon Shuraim da ya bi ta da ido shi ma, hade rai tayi ta murguda masa baki har da juya manyan idanuwanta, sai kuma ta fita kitchen din da sauri tana bin bayan Mami. Mami na gama shiryawa, Ta tabbatar Heedayah ma ta gama shiryawa suka fito main parlor a tare ta kulle kofarta, Shuraim ne xaune parlon yana kallon wrestling, Heedayah na kallon Tvn tace "Mami me yasa basu sa kaya ba kamar mu, nima xan iya tsayawa haka??" Mami tace "Ehh tunda baki da hankali" Daga haka ta wuce dakin kaka, Heedayah na biye da ita kamar xata yi kuka, waigo Shuraim tayi ta turo baki ganin yana kallonta ta shiga dakin kaka, bayan Mami sun gaisa da kaka tace "Kaka xan tafi gun gidan Baffansu Junaid" Kaka tace "Au haba, can xa ki yini kenan yau?" Mami tace "In sha Allah" Kaka na kallon Heedayah kafin ta ce komai Mami tace "Go down now and greet her" Heedayah ta durkusa kasa tace "Ina yini kaka" Kaka tace "Toh mu dai ba mu yini ba tukun, da safiyar Allah kice Ina yini?" Mami ta dago Heedayah tace "Toh bari mu je kaka" Kaka tace "Au tare xa ku?" Mami tace "Ehh tare xa mu tafi" Kaka tace "To Amadun ya sani kuwa, don naga bai fiye son ana fita da ita ba" Mami tace "Ya sani" Kaka tace "Toh ki dai kula da ita, ita kuma Hajiya Zuwaira kice Ina gaisheta, Allah yayi mata albarka, mata me mutunci, har na bar gidan girmama ni take ke kyace ni na haifeta, kayana kuwa kullum sai ta sa masu aiki sun wake sun goge min, to bata fiye min wasu ba ma ni, jira in dibar maki kaikayi koma kan mashekiya ki kai mata, kuma kice nace Allah ya mata albarka" Tuni Mami ta fita dakin bayan kaka ta kulle mata iccen hayaki a leda ta amsa, Heedayah dai sai waigo kaka take, kaka tace "Ni dai aniyar ki ta biki, ban gane kan kallon nan ba..." Suna shigowa main parlor Mami ta nufi kofar fita, Shuraim dake xaune har sannan yana kallon wrestling ganin sun hada ido da Mami yace "Allah ya tsare" tace "Ameen" Heedayah bata fasa waigo sa ba har suka isa kofar, ya dau wayarsa yyi kamar xai jefa mata ta fasa ihu ta rike Mami, tuni ya ajiye hannunsa ya maida dubansa kan TV yana kallo attentively, ko juyowa Mami bata yi ba suka fita parlon, Heedayah ta murguda masa baki kafin ta daina ganinsa. A cikin gidan Alhaji Imran Mami tayi parking suka shiga ciki da Heedayah, ta tadda Hajiya Zuwaira da Mai aikinta a parlor, bayan sun gaisa Hajiya Zuwaira tace "Baffa na parlon sa ku je ku gaisa..." Mami tace "Ohk, ku kadai gida yan makaranta na can makaranta" Hajiya Zuwaira tace "Ae kam suna makaranta, jiya Junaid ya je masu visiting gaba daya" Hajiya Zuwaira ta bi Heedayah da kallo don sosai yarinyar ke mata kyau, komai nata burgeta yake bari hancinta da d'an karamin bakinta, idonta kuwa har lkcn basu koma farare ba, Mami ta wuce sama xuwa parlon Baffa, bata fi minti goma sha biyar bs parlon nasa ba bayan sun gaisa ta fito tare da Heedayah, Bedroom din Junaid ta bude, ta gansa kwance yyi rub da ciki yana bacci, Heedayah ta wara manyan idonta ta cikin glasses dinta tace "Mami Yaya" Zame hannunta tayi a na Mami ta shiga dakin da sauri ta hau saman gadon ta xauna dab da fuskarsa a hankali tace "Yaya" Jin bai ce komai ba ta kai hannu dogon hancinsa ta ja, a hankali ya bude lumsassun idonsa, ya sake rufe idon murya can kasa yace "Cutie" Washe masa hakoranta tayi tace "Me kake yi?" Bai bude idon ba har sannan yace "Bacci" tace "Nima xan yii?" Bata jira cewarsa ba ta kwanta yanda ya kwanta kusa da shi tana facing dinsa, bude ido yyi, yyi murmushi har dimple dinsa ya nuna, ta kai finger dinta wajen ita ma tana murmushin, Ta mike xaune tana kallon Mami tace "Mami ni me yasa bani da irin nasa" Kumatunta ta nuna ma Mami nufinta me yasa bata da dimples, juyawa Junaid yyi da sauri ganin Mami ya mike xaune yace "Mami" Mami tace "Karfe goma saura you are still on bed" yace "Aa ban jima da shigowa ba, Ina kwana" Mami tace "Lafiya lau" kallon Heedayah tayi tace "To sakko mu tafi parlor" Tace "Aa Mami xan tsaya da Yaya plss" Mami tace "Ki tsaya kiyi masa me, sakko mu wuce my frnd" Sauka tayi daga kan gadon kamar xata yi kuka ta nufi kofa Junaid ya bi ta da kallo har suka fita, Bangaren Hajiya Zuwaira Mami ta shiga, ta tadda har Hajiya Zuwaira ta sa masu aiki sun hada mata kayan kari a parlonta, Mami tace "Ikon Allah, we just breakfasted before leaving home Hajiya" Hajiya Zuwaira tace "Sai ku kara ai" Murmushi kawai Mami tayi ta xauna, Heedayah ta xauna kasa kamar yanda Mami ta nuna mata ta dinga yi a ko ina, Hajiya Zuwaira ta hada mata shayi ta mika mata, Heedayah ta kalli Mami tace "Mami ai na sha tea" Mami tace "To ke kin ji, she's full" Hajiya Zuwaira tace "Toh ai shkkn, ya kaka fa" Mami tace "Tana can" Hajiya Zuwaira tayi murmushi tace "Uhn kaka sai hakuri.... ga dai dadin xama ga kuma akasin haka" Mami ta girgixa kai tace "Kwanan ta nawa nan?" Hajiya Zuwaira tayi dariya sosai tace "Ranan da kuka koma ranan ta sa a maida ta gida" Mami tace "Bata dai baki wani matsala ba ko?" Hajiya Zuwaira tace "Toh ai duk Inda tsoho yake dama sai anyi hakuri da shi balle tsoho irin kaka, har da rikicin tsufa, ni fa har ta bar gidan nan bana gane gabas dinta balle yamma, ita dai ga ta Nan dai" A hankali Heedayah ta sulale ta fice daga dakin ba tare da ta bari sun lura ba, ta bi hanyar da suka bi xuwa dakin Junaid, bude kofar tayi ta leka ciki, xaune ta gansa gefen gado yana danna wayarsa, ta washe masa hakora ta shiga ciki tace "Yaya" Daga kai yyi yana kallonta har ta iso ta xauna kusa da shi tana kallon abinda yake yi a waya, yyi kasa da murya yace "Wa yace ki shigo dakina?" Tace "Ni ce na shigo da kaina, I want to be with you" Kallon bakinta yake, ta wara masa ido tace "Yaya yaushe xan ga Farida?" Ya dauke idonsa daga lips dinta yace "Ki tambayi Mami mana" Tace "Ce min xata yi bata sani ba, Yaya me yasa sai Shureen ya dinga min haka...." Wayarsa ta amsa a hannunsa ta gwada yanda Shuraim ke mata ta jefar da wayar xuwa bakin kofa, xaro ido yyi yana kallon wayar tasa ya mike da sauri yace "Kee wayana kika wurgar haka?" Tace "Aa haka Shureen ke min" Ya tafi ya dauko wayar yana duba screen din da ya fashe ya dawo ya hade rai yace "Sai nace ki gwada min da wayata?" tace "Toh nima idan ya min haka wayarsa xai fashe haka kenan?" Junaid ya xauna kusa da ita yana kallonta yace "Me yasa yake maki haka" ta bude hannu tace "Ban sani ba, sai ya dinga min haka kuma" kallon yanda ta xaro idonta Junaid ke yi, yace "Haka yake maki?" Ta gyada masa kai, Yace "Toh a ina kike haduwa da shi?" Ta gyara xama tace "A parlor ko a kitchen idan Mami xata bani shayi, sai ya min haka...." Da ido ta dinga bin dakin da kallo alamar haka yake bin ta da kallo, Junaid ya d'an tabe baki yace "Ki gaya ma Abba" Tace "Toh" bude kofar dakin aka yi duk suka juya da sauri, Mami ta hade rai tace "Wa yace ki shigo nan din" Heedayah ta sauka saman gadon da sauri tana nuna Junaid tace "Shi ne" Junaid ya xaro ido yace "Ni?" Tace "Eh" Mami tayi mata alamar da ta xo ta fita, ba musu ta nufi kofar ta fita kafin Mami ta rufe kofar Heedayah ta daga masa hannu suka wuce. Sai kusan yamma Mami ta bar gidan Baffa, tun da suka hau titi xuwa gida Heedayah ke ce mata Mami bamu ga Yaya ba muka tafi, Mami tace "Ai bai dawo ba, gobe xai xo" kamar xata yi kuka tace "Toh" karfe shidda saura Mami tayi parking a compound, Sai da ta sauka motar sannan Heedayah ta sauka, A balcony suka tadda Shuraim xaune yana operating laptop, Ya gaida Mami ta amsa ta shiga ciki, Heedayah ta bi sa da kallo kafin ta shiga ciki ya fixgota yace "Kallon me kike min?" A tsorace tace "Aa" ya daure fuska yace "Me yasa kike kallona nace??" Tace "Kai ma naga ai kana kallona da idonka" hada ido suka yi da Mami ya saketa ta nufi kofa da sauri ta juyo ta wani juya masa ido ta shige cikin parlon Mami ta rufe kofar.... Bayan isha Shuraim na parlon Abbansa kasancewar ya kirasa a waya yana neman sa, Abba ya gama abinda yake, sannan yana kallon Shuraim yace "Shuraim I am worried at sending Heedayah to boarding school as you suggested because, Ina son ta samu ilimin addini sosai, ba boko kawai ba, shi yasa ka ga then banyi supporting xuwansu Rabi'ah boarding din ba, karatun addini nake dubawa" Shuraim ya d'an yi shiru da farko, sai kuma yace "Abba a situation da ake ciki ynxu, boarding din is the best" Abba yace "Koh, then what about islamiyya?" Shuraim yace "Idan sun yi hutu sae ta dinga xuwa" Abba yace "Toh shkkn, but ajin da xa a sa ta fa?" Yace "Jss2.. or 1..." Bude kofar parlon aka yi Mumy ta shigo, Abba ya daga kai yana kallonta, mikewa Shuraim yyi yace "Sai anjima Abba" Abba yace "Alright" Mumy ta bi sa da kallon gefen ido har ya fita. Bayan sllhn asuba Shuraim ya shiga gaida Abbansa, bayan sun gaisa Abba yace "Jiya mun yi magana da Barrister tace min su Farida na kan yin third term exams ne ynxu.... So ynxu sae anyi hutu an koma za ayi enrolling Heedayah, but before then I will get a mu'allim for her da xai dinga mata karatun qur'ani da sauran abubuwan da ya kamata..." Shuraim yace "Mu'allima instead" Abba yace "Really?" Shuraim bai ce komai ba, Abba yace "To bbu damuwa, when are you going to Zaria?" Yace "Tomorrow" Abba yace "Allah ya kai mu" mikewa yyi ya ma Abba sallama ya fita parlon. Karfe sha daya na safe, Heedayah ta fito parlon Mami rike da cup din shayi da ta sha xata kai kitchen, Shuraim na kwance 3
End Ads