kawo gidan nan ba mu da labari, kaya wai me yawa..." Kaka tace "Kayan me??" Mumy tace "Ni kaina bansani ba, ance dai kayan na nan bangaren" Kaka tace "Au, wai tsaraban da yayo ma Deedayah?" Mumy tace "Toh shi din kenan" Kaka tace "To sai aka yi yaya? Ai kaya basa wajen Rakiya suna wajena, waye ya xo amsa?" Umma da ta daure fuska tace "Ni na xo amsa" Kaka ta kalleta daga sama har kasa tace "Haba, to sannu da xuwa Amina, bakin cikin ne ya motsa kenan yau, to bari kiji ko Umaru yyi kadan ya amshe ma Deedayah kayan da Sudess ya siyo mata balle ke, kuma in sha Allahu yau xata fara saka kayan sai in ga ta tsiya, ke kuma Maryam har kin mance hijaran da kika yi na kwana biyar a gidan nan bayan kin sa an sace Deedayah kin maido ta, kin manta yanda kika dawo duk a lalace shine xaki sake shiga wani kess din da sassafe koh, to wllh Rakiya kiris take jiran ki ko bata fada ba ni na sani, haka kawai duk kun bi kun sa ma makauniya ido, to wllh karyan ku, tunda ina sonta Rakiya na sonta Sudess na sonta, Junaidu na sonta shi Amadu ba wai mun gama sanin xuciyarsa bane, to kowa ma ya ki ya indai mu muna sonta" Umma ta fiddo wayarta tayi dialing number Sudais yana fara ringing ya daga, strictly tace "Kana ji na Aliyu??" Sudais yace "Ina ji Umma" tace "Wannan kayan da ka kawo gidan Barrister da sunan kayi ma makauniya tsaraba maxa maxa ka xo ka amshe su ka kawo min dakina, idan kuwa ba haka ba wllh wllh ka canxa wata uwar...."
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....
Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍
Kaka dake ta kallon Umma baki bude ta saki salati tana tafe hannu, ganin Umma ta yanke wayar bayan ta gama magana kaka tace "Toh yanxu dai kafin ince komai so nake a fara gaya min munafukin da ya kai maki xancen nan, idan kuma baxa ki gaya min ba sai in sa a kira min Umaru ya kira ki ya tambaye ki nasan shi xa ki gaya masa, don gaskiya idan aka ki fada min wanda ya kai gulman nan kunnen ki, toh gwara in tafi duk inda xan tafi kawai...." Kaka na fadin haka ta tafi daki, Mami kuma ta nufi kofar fita Umma ta bi ta a fusace tana cewa "Kema ba ina ce kina da d'an ba, me yasa baki dinga makala masa makauniyar ba sai 'ya yan mutane?? To wllh daga ke har shegiyar yarinyar ku fita harkan d'a na...." Mami ta tsaya so pissed off tace "Look plss woman, get back home, sit ur son down, warn him seriously to stay away from the little girl, or from this house as a whole, you can't just come here and be displaying how mad you are plss.... behave like a literate for once, this is a very simple issue to address to alone without u causing commotion, komawa gida xa kiyi ki kira d'an ki ki xaunar da shi ki ja masa kunne cikin nutsuwa, in har ya dauke ki uwa to bbu abinda xai sake kawo sa gidan nan balle ya xo gun Heedayah, amma kawai kin xo kina ma mutane hayagaga a gida, why not behave like the elderly lady you are?? Wnn fa ba abun tada jijiyoyin wuya bane, in har d'an ki na jin maganar ki to fa baxai kusanci abinda baki so ba, plsss I have very important things a gabana than listening to ur bull shit... So excuse me" Mami na fadin haka ta fice daga parlon, Umma da ta saki baki tana sauraronta ta bi ta da sauri tana cewa "Toh ai asirin da kika masa kilan baxai ta6a barin ya saurareni ba, don naga ba iya Barrister kadai mugun abun ki ya tsaya ba, waye bai san da asiri kika shigo gidan nan ba, kuma wa ya sani ko ke kika lika ma barrister makauniyar duk don ya aure ki??" Mami ko juyowa bata sake yi ba balle ta tanka ta, Mumy da ta bi bayan Umma ta dinga cewa "Toh ai fada ma 6ata baki ne Amina, tuni aka shaida min ta asirce barrister sai yanda tayi da shi, shine ta koma kan Sudais...." Mami ta bude motarta ta shiga tana answering call da ya shigo wayarta, Kaka ce ta fito dakinta rike da wayarta, ganin Farida rike da hannun Heedayah xa su fita parlon ta nufeta tana mika mata wayar hannunta tace "Maxa kira min Umaru, yana nan xa ki ga ansa Dakta... Yi maxa kirasa" Farida ta amsa ta nemo number Baffa sannan tayi dialing ta mika ma Kaka jin ya fara ring, Baffa na dagawa kaka ta nemi kujera ta xauna ta fashe da kuka tace "Umaru ashe dama matarka Amina gantalalliya ce bani da labari, me nayi mata xata xo har gida ta min wankin babban bargo don wnn yaro naka Sudess ya yo ma Deedayah tsaraba?? Ni fa na ce yyi mata tunda ba wai gata gareta ba kowa na mata kallon yar tsintuwa, shi kansa Amadun da ya rabota da titi har yau ko tsinke bai ta6a siya mata ba, shi dai ya kawota kawai ya jibge mana ita, sai Rakiya ke ta siya mata kaya duk da dai ita ma kayan anna take siya mata wasu guntaye kmr ta6a66iya, to laifi ne don ynxu Sudess ya mata tsaraba daga kasan waje?? To wllh ka taho gidan Amadu yanxun nan ka titsiye Amina sai ta gaya maka uban da ya kai mata rahotun an ma Deedayah tsaraba, idan ba haka ba ni gaskiya an ci mutunci na kawai an keta min rigar mutuncina" Baffa dake ta sauraronta yace "Ikon Allah, haka ya faru?" Kaka tace "Aa karya nayi maka" Baffa yace "A'a ba haka nake nufi ba kaka, kawai gani nayi...." Ta katse sa da sauri tace "Baka ga komai ba Umaru, ba ruwana da bayanin ka, so nake kawai ka kamo hanya ka xo ka ritsa Amina ta fadi shegen da ya kai mata gulman Sudais ya yo ma Deedayah tsaraba, idan ko ba haka ba to xan tattara ya nawa ya nawa in san inda dare ya min, baxan xauna a ci mun mutunci ba kayi shiru" Baffa ya girgixa kai yace "Toh sai na xo" Ko amsa bata basa ba ta katse wayar, ta mike ta nufi kofa da sauri, Tijara iri iri Umma ke ma Mami a tsakar gidan Mami taki ko da kallon inda take har Farida da Heedayah suka karaso gun motar, Umma na kallon Heedayah tace "In sha Allahu a makance xa ki dauwama ki kare, tunda har kika shigo gidan mutane kika tarwatsa farin cikin da aka gina da dadewa, lkci daya kin tarwatsa komai, ae ko xuwan ki familynmu sharri ne ba alkhairi ba..." A nan Mami ta kalleta tana murmushi tace "Kya ga dauwamammen makanta kuwa a gidanki...." Umma tayi wani shewa tace "Bakin ki ya sari danyen kashi, sai dai a gani a naki xuri'ar, mu kam kaf dangi daga farko har karshe bbu nakasasshe..." Muryar kaka suka ji tana cewa "Toh Amina idan kin gama ki shigo daga ciki ki xauna, tafiya bai ganki ba, Umaru na hanya" Mami na kallon kaka tace "Kaka sai mun dawo" Kaka tace "Toh a dawo lfya Rakiya, da yake ke ba xaman banxa kike ba ina xa ki samu lkcn gantalallu da ko sakandarin basu kare ba, ita fa Maryam iyakarta aji biyu na sakandari Amadu ya gaya min, ita kuma Amina dama ko makarantar Ina jin bata ta6a yi ba don ko 'yar turancin nn ban ta6a ji tayi ba shekarata biyu gidan Umaru, kawai dai Allah ya ba 'ya yana jahilai sai xuba jahilci suke a gida ba kakkautawa" Mami ta tada motarta ta nufi gate da mai gadi ya bude mata tuni ta fita. Baffa ne xaune parlor a gidan Abba bayan la'asar, sai Umma da kaka sannan Sudais, Mumy sai kai komo take a parlon kamar me yin wani abu, Baffa yyi gyaran murya yace "Da farko dai xan fara baki hakurin rashin xuwa da ban yi da wuri ba sbda marasa lfya da na tsaya dubawa asibiti, sannan ina kara baki hakuri da abinda ya faru daxu da safe...." Kaka ta ta6a baki ta rungume hannu tace "Haka dai" Baffa ya kalli Umma yace "Ke me ya kawo ki gidan nan daxu da safe?" Tace "Kayan da Sudais ya kawo gidan na xo amsa" Baffa yace "Wasu kayan?" Tace "Ai shi ya san wasu kayan ne Dr...." Kaka ta dakatar da ita tace "Kafin a je da nisa, Ina son sanin wanda ya gaya maki Sudess ya kawo kaya gidan nan, don banda ni sai shi sai wannan sumu sumun yaron Shureen bbu wanda ya sani, har ita Deedayahn bata sani ba balle uwar goyonta Rakiya, to ynda kika samu labari kawai nake son sani yanxu" Baffa na kallon Umma yace "A ina kika ji xancen" Umma ta d'an yi shiru na wasu seconds kafin tace "Shi din da bakinsa ya gaya min ba kowa ba" Kaka ta kalli Sudais da sauri tace "Wai??" Yyi kasa da kansa yyi shiru, har sai da Baffa ya sake cewa "Plss kar ka bata min lkci malam, I have important things" Sudais ya daga kai ya kalli Umma dake hararansa yace "Ehh nine" Kaka tayi tagumi tace "Toh abu ya lalace kenan ai, kai kuma ashe haka kake bakin ka baya haila?? me ya kai ka don ka yi abun arxiki kaje kana terere kana fada ma duniya?? Aa lallai Sudess ya xama abun tsoro" Baffa dai ya jinginar da kansa da kujera so pissed off da wnn batun mara amfani garesa, Umma tace "Don haka ynxu idan bai maido kayan can gida ba ya nemi wata uwar amma ba ni ba" Kaka na kallon Baffa tace "Ni kuma idan har Sudais ya maida mata kayan ta sa hannu ta amsa baka sallameta ta tafi gidansu ba ka nemi wata uwar ba ni ba Umaru" Baffa ya kalli Umma da ta bude baki tana kallon kaka, Kaka ta mike tace "Duk shawaran da aka yanke ni dai ina daki, kaya na fita daga dakina dama Amina ta fita daga gidanka, to ni ba gantalalliya bace" Tana fadin haka ta nufi dakinta tana cewa "Kuma duk wanda yace Deedayah xai sa ma ido sai dai ya mutu muruss, ni ma ba gashi gantalallen bai min tsaraba ba amma na hakura ban ma yarinyar bakin ciki ba, to meye wasu xa su yi mata bakin cikin tunda har na kai xuciyata nesa ni ban mata ba, da ni azzaluma ce da ba cewa xan yi xan kai kayan kasuwar 'yan koli in siyar ba, amma ae bance haka ba" Baffa ya mike yace "To shawara ta rage kuma gare ku, but let me tell u this Amina, duk ranan da kika sake janyo na baro gun aiki unnecessary ranan won't be funny for me and you" daga haka yyi ficewarsa daga parlon, Umma ta dinga kallon Sudais da idanuwanta da suka kankance, shi dai bai iya ya kalleta ba, can ya mike a hankali ya nufi dakin kaka, yana shigowa tace "Meye kuma ka biyoni? Ae tunda ka fita har waje ka dawo baka kawo min ko tsinke ba to xaka iya bada min shinkafar 6era a abinci, wai Deedayah, to uwar me ka hada da Deedayar bani da labari?" Ya mata wani kallo yace "Toh ki fito min da kayan" kaka tace "Sae dai in fito maka da Umaru, kaya kam bbu wanda ya isa ya sa in fito da shi, Allah ya tarwatsa duk me yi ma marainiyar nan bakin ciki" Ya fi minti uku yana ta kallonta tana harkan gabanta, can ya juya ya fice daga dakin ta bi sa da harara tace "Da baki kmr gidan tsutsa, sae shegen surutu kmr mace" Tsaye ya ga Umma a parlor tare da Mumy ko wannensu rai bbu dadi, Umma tace "Kasan Allah Aliyu, wllh ka sake shigowa gidan nan ni dai ban yafe maka ba, bbu kai bbu gidan tunda Mahaukaci ka xama, ita makauniyar kanwata ce ko ta ubanka da kayi mata siyayya hka, to wllh ka sake kallon ko da inda take kai da Allah.... Kaya kuma basu ci bulus ba duk ma wanda yyi amfani da shi Allah ya isa wllh" tana kai wa nan tayi ma Mumy sallama a fusace ta fita, Mumy na kallonsa tace "Ni ka ban mamaki wllh Sudais, kana da dangantaka da yar tsintuwar ne?" Yace "Ina da shi mana, 'yar uwata ce ita musulma" Mumy ta hade rai tace "Ohh wato ni kake da bakin mayar ma magana koh?" Yace "Toh Mumy fisabilillah meye don nayi ma marainiyar tsaraba, kowa fa ina masa idan na tafi...." A fusace tace "Kana masu uban me?? Shi biscuits din da chocolates ne tsaraban? Ka tashi ka cika akwatuna har uku kamar me kai lefe sai kace mara mafadi, to gidan ma gaba daya an hana ka shigowa sae in ga ta tsiya... Yarinyar kawai matsiyaciya mara gata duk ta tarwatsa gida" Ya girgixa kai yace "Ae kam tana da gata...." Yana fadin haka ya nufi kofar fita daga parlon, muryar kaka yaji tana cewa "Ni dai ban yafe rashin tsaraban da baka min ba" ko kallonta bai yi ba har ya fice daga parlon.... Heedayah ce xaune garden din gidan da malamin da ke mata karatu, a final year Engineering student, baxae wuce ashirin da shidda ba, tana xaune saman one of the two comfortable chairs da Abba ya siyo gidan don koya mata karatu, shi ma malamin na xaune saman guda daya da textbook din Basic science a hannunsa, bayanin topic din da ya mata ranan take masa, ko tsallaka word daya bata yi ba a abinda ya koya mata, a nutse take masa bayanin, directly yake kallon cikin idanuwanta without even blinking, duk wannan abun Shuraim na xaune balcony a sama doing nothing yana kallonsu lkci lkci, shi kansa malamin bai san yana wajen ba, can dai Shuraim ya mike ya tsallaka gwangwanin Coke da ya ajiye wajen ko budewa bai yi ba ya fita balcony din, cikin few minutes ya shigo garden din, tun daga nisa idonsa ke kansu, Heedayah ta turo baki tace "Toh ban yi dai dai bane, why don't you want to compliment me?" Ta fadi haka ne sbda shirun da ta ji Malamin yyi bayan ta ce masa ta gama, Malamin na hango Shuraim yace "Yess, that's excellent of you, I know u can do it...." Tayi murmushinta me kyau tace "Da gaske?" Shuraim na isa wajen yana kallon Malamin yace "Karfe nawa kake gama lesson din?" Malamin na kallon agogo yace "Saura minti ashirin..." Shuraim yace "All same, akwai hadari garin you can leave now, sae da safe....." yana fadin haka ya kalli Heedayah ya wani hade rai yace "Tashi" a hankali ta mike tsaye staring into space, fuska daure ya fixgo hannunta ya bar wajen tana biye da shi kamar xata fadi, malamin ya bi su da kallo, Suna shiga parlor ya kai ta har kofar dakin kaka yyi abandoning dinta sannan yyi wucewarsa sama. Heedayah ta samu dai ta bude kofar ta shiga, Kaka xaro ido tace "Har kun yi me??? Anya wannan yaron ba 419 yake ma Amadu ba kuwa, ba fa a titi ake tsintar kudin ba, me ya koya maki haka da wuri har ku ka tashi?" Heedayah ta turo baki tace "Ko ba wnn bane ya dawo da ni wai akwai hadari ko gama karatun ba mu yi ba" Kaka ta mike tace "Wa?" Ta yatsina fuska tace "Ni manta sunansa nake, wannan din nan dai" Kaka tace "Atoh ce min xa ki yi wancan sumu sumun, me yasa ku ka biye masa, gantalalle ne fa, lkcn yana karami baki ga kukan da yake tsalawa ba idan xa a kai sa makaranta, kwata kwata bai son karatun, ya fi so yyi ta xaman gida yana kassara min Amadu da kashe kudin yagwat, to shine xai maki bakin ciki yanxu sbda d'an turancin da kike ji?? Bakin xuciya fa garesa ci gaban ki ne baya so...." Lkci daya kaka tayi tsit ganin Shuraim tsaye bakin kofa don a bude Heedayah ta bar kofar, kaka tace "Toh kuma ai hadarin idan ya kare maki sai ya sa maki wani cuta, ni kaina fa idan ana hadari bana yarda in fita ko nan da kofa balle ke me lalura, ae da kyau da ya koro ki...." Heedayah ta wani turo baki tace "Kaka karya fa yake yi bbu wani hadari wllh, ai banji kamshin ruwa ba, kuma bbu ko wani iska kawai dae shi mugu ne...." Kaka tace "Kul.... bar ce ma baba yana karya bbu kyau, kuma ba mugunta bace lafiyar ki yake ji shi sa yace ki shigo kar iskan yamman ya kare maki, abinda likita ne shi ma ya san illan haka....." Heedayah ta laluba gefen gado ta xauna tace "To Ina ruwansa da ni? Ko English language fa ba mu yi ba ya dawo da ni, kuma sae sauri yake sbda in fadi inji ciwo" Kaka ta saci kallon Shuraim dake tsaye yana kallon Heedayah, tace "Ke kuma ya xa ki ce haka, ubansa fa ne ya tsinto