x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - HEEDAYAH

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 115649 words

Category: Love Stories

Views 139

22 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
a hankali taga bacci yake, tayi tiptoeing har xuwa hanyar dakin kaka sannan ta bude kofar very careful don ma ko kadan kofar baya kara, fridge ta nufa ta ajiye eye drops din ta juyo da sauri ta fita ta kulle kofar, sannan ta sauke ajiyar xuciya, tana isa cikin parlor ta kara lekan Shuraim da ko motsawa bai yi ba, ta wuce dakinta hankali kwance tana gode ma Allah. Sbda baccin da Mumy bata yi ba da wuri sai kusan karfe takwas na safe ta tashi duk da ta tashi sllhn asuba, taga har su Khadijah sun wuce makaranta, bandaki ta fara shiga sannan ta fito ta tafi parlor, dai dai nan Kaka ta fito, Mumy na murmushi tayi kasa tace "Sannu kaka, fatan kun tashi lfya?" Kaka tace "Wani lafiya an shigo an sace ma yarinya magani, a kira min Amadu" Kasake Mumy tayi tana kallon kaka, kaka ta nufi bangaren Mami tana cewa "Bari inji ko wnn matar ce ta shigo ta kwashe magungunan yarinya sbda ta nuna min ban isa da ita ba" Kaka ta shiga buga kofar Mami, Mami na fitowa kaka tace "Rakiya Ina maganin da kika shigo kika kwashe?" Da mamaki Mami tace "Magani kuma kaka?" Kaka ta saki salati tace "Toh wllh barawo ya shigo ya sace maganin da kika kawo jiya, ba a kan friji nace ki ajiye ba??" Mami tace "Ehh nan kuma na ajiye" Kaka tace "Toh ko sama ko kasa, dakin na can na hargitsa wai ko ma ya shige wani lungun ne amma wllh ban gani ba, Ina Amadu" Mumy dai ta kasa motsi inda take, Mami ta kalleta na yan sakwanni sannan ta dauke kai, Kaka da kanta ta tafi ta kwankwasa ma Abba kofa yana fitowa tace "Amadu barawo ya sace maganin Deedayah, wllh da shi muka kwanta muka tashi ba shi" Da mamaki Abba yake kallonta, tace "Wllh ba xancen wasa ba kana kallona" Mumy dai fa an kasa motsin kirki sai imagining take to ko dai cikin mafarki ta mayar da maganin bata mayar a xahiri ba, Shuraim ya sakko downstairs jin muryar Kaka ya cika gidan, ya karaso yana kallonta yace "Me ya faru?" Kaka tace "Shureen maganin Deedayah aka rasa wanda ya dauke, ni kuwa yau xan ga 6atar nono a kirjin budurwa...." Kallonta kawai Shuraim yake with surprise, can ya kalli Mumy dake tsaye sai wurga ido take, Kaka tace "Al-qur'an kira xan yi in sa a ja min Yasin, in dai ba a fito min da maganin yarinyata ba sai na kai kudi an ja min yasin" Abba dai bai ce komai ba, Mami na tsaye just watching everybody, Kaka ta nemi kujera ta xauna tana hada xufa tace "Ka ji min dai, to wllh ba ruwana sai dai cikin mutum ya kumbura, me Deedayan ta tsare maku da xa a dauke maganinta, ko uban wani ne ya siya mata maganin banda Amadu???" Abba yace "Junaid ne ma ya siyo ba ni ba" Kaka ta mike da sauri tace "Au Junaidu ne ma, to dama idan ba kai din ba ko shi wa gareta da xai siya mata, wllh Amadu ka ja su daki kayi masu magana cikin nutsuwa su fito min da maganin yarinya kar abu ya baci tsakanina da su, xan fa mance sanin da na masu in sa a ja masu Yasin" Tana fadin haka ta juya ta nufi dakinta fuska daure, Shuraim ya bi ta da kallon gefen ido, Cike da karfin hali Mumy tace "Ikon Allah...." Mami ta ta6e baki ta juya ta koma dakinta, Mumy tace "To magani kafafuwa garesa da xa a nema a rasa?? Anya kaka ta san Inda ta ajiye maganin kuwa?" Abba na kallon Shuraim yace "Xan sa Junaid ya tura maka sunan eye drops din, sai na maka transfer ka tafi pharmacy ka siyo su" Shuraim yyi kasa da kai, Abba yace "Ko baxa ka samu xuwa ba..." Kafin yace komai Mumy tace "Baxai samu ba mana, shi da yake fita aiki Barrister, Ina ji fa ranan Baffa ke fadan baya wani xuwa aikin sai ya ga dama to idan ba matsala kke son ja masa gun Baffan nasa ba ina xai je samo wani magani ynxu da safe" Tun da ta fara magana Abba ke kallonta keenly, can ya gyada kai ya wuce bangarensa, Shuraim dai bai iya ya daga kansa ba, Mumy ta hade rai bayan tafiyar Abba murya can kasa tace "Did you know anything about the missing eye drops Aliyu??" Ya daga kai da sauri yana kallonta yace "Ni kuma Mumy, ni ban ma san da wani eye drops a gidan nan ba, I know nothing about it, ban ma san kalarsa ba" Mumy ta kauda kai tana naxari to wai ko dai mafarki tayi ta mayar da drops din dakin kaka?? Ganin Shuraim ya fara wucewa ta kara daure fuska tace "Wait, ko da wasa kar ka fita gidan nan da sunan tafiya siyo ma tsinanniyar yarinyar nan magani.... I'm instructing you not to do so" Da mamaki ya tsaya yana kallonta, can yace "Toh idan Abba ne yace in je fa Mumy?" Rai bace Mumy tace "Ni kuma nace baxa ka je ba, ko tsallake maganata xaka yi??" Yace "Amma ai baxan iya ce masa A'a ba kamar ynda kema baxan iya ce maki A'a ba" tace "Wannan ya rage naka kai da shi, ni dai nace idan ka fita gidan nan siyo maganin makafi to ba da yawuna kayi hakan ba" Fitowar kaka ya sa ta ja bakinta tayi shiru da sauri, Kaka dake sanye da hijab hannunta rike da Heedayah tace "Ga shi na fiddo dubu daya ta xan je siyo maganin idon a kemist, daga can kuma xan tafi gun da xa a ja min yasin na tsakani da Allah...." Mumy tace "Haba kaka yanxu fa nake cewa xan shiga a sake duba dakin da kyau ko...." Kaka ta katse ta a fusace tace "Tunda kinga alamar na fara makancewa kamar Deedayah ba, wllh tllh baxan yi kaffara ba wani algungumin ne ya shiga ya dauke maganin nan, to ni abinda har yanxu ban gane ba a nan shine, bakin ciki ake ma yarinyar kar idon ya warke ko me?? Anya wasu xa su gama da duniya lafiya kuwa, Junaidu ya cire kudi domin Allah ya siyo mata magani amma wani mara tsoron Allah ya bi dare ya sace, tunda nake ban ta6a ganin irin haka ba sai gidan Amadu, gidan Umaru basa haka kwata kwata, in haka ne lauyancin karya Amadu ke yi kenan, lauyancin karya mana tunda ya kasa kama wanda ya sace ma Deedayah magani, ita ma amaryar da naji ance lauya ce ashe ta karya ce, lauyoyi biyu a gida a tafka wnn uban sata amma a kasa kama barawon har war haka?? Aa ba ruwana gwara inyi ta kai na, dubu daya da dari biyar dina ya biya min bukata, dubu daya in bada a kemist su bani maganin guda biyu, dari biyar kuma in tafi gidan Ta salla ta rakani inda xa a ja min yasin...." Shuraim was trying hard not to laugh sai sunkuyar da kansa yake yana shafa gashin kansa, Fitowar Abba yasa ya daga kai yana kallon Abban nasa, Abba yace "Ina kuma xa ki kaka?" Tace "Ina ne kuwa baxan je ba Amadu, Kai baka san wnn yar amana ce Allah ya baka ba xaka barta ta walakanta a gidanka, wani axalumi ya sace mata magani kayi shiru" Abba yace "Xan je siyo maganin ai ynxu" Kaka tace "A'a ai tunda nayi niyya sai na siya ga dubu dayana xan je kemist da ita ynxu" Abba ya tsaya kallon kaka kafin yace "Ae ko wani daya ya kusa dubu ashirin da biyar" Kaka ta gwalo ido tace "Me din?" Abba yace "Bari ynxu xanje in siyo in kawo maku" Shuraim dake kallonsa a hankali yace "Abba I will go..." Abba yace "Noo, Kar ka damu" Shuraim yace "Amma kace I should get it" Yace "Ehh na canja shawara, you don't worry" Daga haka Abba ya fita, Shuraim ya bi sa da kallo, Mumy ta kyabe baki, Kaka na kallon Heedayah ta dunguri kanta tace "kin dai ji nawa ake siyar da maganin d'an cikin roban nan, to idan ba tsoron Allah ba uban me muka hada da ke xa mu dinga kashe maki kudi haka, kin ji fa wahalan da d'a na yake, dubu hamsin xai kashe da safen nan a kan lalurar ki, to wa xai saka masa kuwa banda Allah? Ba dangin iya balle na Baaba fa" Mumy tace "Abinda ke damuna kenan kaka daga karshe ma a saka ma mutum da sharri" Kaka ta kalleta tace "Toh Ina ruwan ki, kudin ki ko na Amadun??" Kaka na fadin haka ta ja hannun Heedayah suka koma daki.... Mumy ta wuce nata dakin don duba drops din ko bata mayar da gaske ba, Mumy ta tsaya da mugun mamaki a gaban madubinta tana naxarin to waye ya shiga dakin kaka ya dauke maganin nan, kaf ta duba dakinta bbu, ita dai tana da yakinin ta mayar wajajen karfe biyu da wani abu na dare ba wai mafarki ba, hankalinta yyi mugun tashi don gashi an kara wargaza wnn plan din ma, ta dau wayarta rai ba dadi ta wuce bandaki. Har Mami ta gama shirin fita office hankalinta ya kasa kwanciya, she is so disturb, ko kadan bata ji xuciyarta yyi na'am da komawar Heedayah gun kaka ba, ko ma waye ya dauke eye drops din nan yyi hakan ne da wata manufa na cutarwa, cuta kuma me girma ba karami ba, bata san ta ina xata fara billowa kan a bar Heedayah wajenta ba, gaba daya taji bata yi trusting kowa na gidan ba, they all look guilty, both mother and Son, sannan masu aikin ma haka kawai taji hankalinta bai kwanta ba bata yrda da su ba, sannan Rabi'ah da Khadijah ma halin uwar garesu bbu abinda suka mance nata, kaka kuma from many indications taga baxata cutar da Heedayah ba balle kuma a je ga wanda yyi sanadin xuwanta gidan wato Abba, dauke Heedayah daga wajen kaka isn't going to be easy but she will try, ynda take jin Heedayah bata jin xata bada space a cuceta a gidan nan sai iya inda karfinta ya kare, da haka ta fita xuwa parlon Abba sanin bai fita ba, Yana parlon nasa da Shuraim dake xaune kasa, Abba na kallonta yace "Xaki tafi office...." Tace "Yes, but barrister har yanxu baka ce komai ba a kan the missing eye drops.... This is a very serious issue to address to with immediate effect, Sannan nasan ka fini sanin koma wanene ya dauke eye drops din nan ya dauke sa ne da manufa biyu xuwa uku which I won't mention cos you know...." Abba dake kallonta yace "Gaskiya ne, I will see to that" tace "And pls ko xaka yi ma kaka magana Heedayah ta komo wajen??" Abba ya d'an yi shiru, sannan yace "Will see to that too" Mami tace "Alright thank you, sai na dawo" daga haka ta fita, Shuraim ya bi ta da kallon gefen ido, dakin kaka Mami ta tafi, ta samu kaka ta hada ma Heedayah shayi me kauri ga ledan bredi guda ta ajiye mata, Kaka tace "Har xa a fita kenan" Mami ta xauna kusa da Heedayah tace "Ehh kaka, Ina kwana?" Kaka tace "Lafiya lau, kawai sai muka wayi gari da alhinin an sace maganin Deedayah" Mami tace "Allah dai ya kyauta...." kaka tace "Ameen fahhh, ga dai sabo Amadu ya siyo ya kawo na boye, ita kanta Deedayan ma baxan bari ta san Inda na boye ba balle wani" Mami tace "Yauwa gwara haka kaka" Kaka tace "Ni fa sai nake ga kamar Maryam ce ta dauke, ke baki ga duk ta rude ba??" Mami ta d'an yi murmushi bata dai ce komai ba tana gyara ma Heedayah gashinta, Kaka tace "Toh wllh sai dai ta cuci kanta ba dai Deedayah ba, me yar yarinyar ta tsare mata" Mami na kallon Heedayah tace "Did you pray today?" Heedayah ta gyada mata kai, Kaka tace "Toh wai sauran kayan nata fa? Ko in tafi in kwasa da kai na ne?" Mami ta kalleta tace "Kayan wa?" Kaka tace "Deedayah mana, ko kaya kala uku kadai xan dinga sa mata kamar fatararru?" Mami tayi shiru, kaka ta mike ta ci gaba da abinda take, Mami tace "To sai dai na dawo kaka" daga haka ta fita dakin, Kaka ta ajiye tsumman hannunta tace "Anya wannan Rakiyan na da saiti ma kuwa, ke dai ba don Amadu ba baxa ki san yarinyar nan ba, ke ba dangin iya tsakaninki da yarinyar nan balle na Baba to don me xaki dinga nuna fin karfi a kanta??" Kaka ta xauna ta rike ha6a tace "Ha'an, yau ga fitinanniyar mata ni Fatee, ko dai kanwar uwar Deedayah ce ita bamu da labari....." Hango ledan da tayi a gefen kofa ya sa ta mike tace "Ji ledan da gantalallen can ya kawo jiya ko meye a ciki...." Daga haka ta nufi ledan ta dauka tana leka ciki....



Heedayah ba kyauta bane na kudi ne, do not read without subscription, patronize ur novelist and read happily with out any thought... It's 300 via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence of payment via WhatsApp 07087865788




Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍



Kaka tace "To dama idan ba shi din ba waye xai siyo min Apple manya haka? Ai sai dai Shureen din" Heedayah tace "Ni bai siyo min ba kaka?" Kaka ta kalleta tace "Ke kuma a wa? Ae sai dai in d'an yankar maki idan nayi niyya" Karime ce tayi sallama bakin kofar parlon Mumy ta shiga ciki, Mumy tace "kulle kofar, Sajida ta ga tahowar ki?" Karime ta kulle kofar tace "A'a wanka ta shiga" Mumy tace "Toh mu shiga daki, ba wani aiki bane linki xa kiyi min" Karime tace "Toh Hajiya" Mumy ta shigar da ita bedroom dinta, 'yan kaya ne da basu fi biyar kan makeken gadon dakin, Mumy tace "Ga su nan basu da yawa" Karime ta fara linke kayan, Mumy ta nemi waje ta xauna tana latsa wayarta, ganin Karime har ta kusa gamawa Mumy tace "Hajiyar ta fara sake maki kuwa?" Karime tace "Aa, yau ma tace min tunda Heedayah ta koma gun kaka to idan na gama aikin da xan yi a bangarenta in yi wucewata can dakinmu, ko don d'an kallon da taga Ina yi ne yasa ta fadi haka..." Mumy tace "To banda abun ki ba ga TV a nan ba Karime, duk sanda kike son kallo ki shigo nan kawai, ae xuciyar daban ne, kowa da irin tasa...." Karime tace "Kuma haka ne wllh, ke kam naki daban ne...." Mumy tayi shiru jin ringing din waya a parlonta, mikewa tayi da sauri ta fita parlon, Shuraim ta gani tsaye yana kallon screen din wayarsa dake ring, ya daga ya kai kunne tare da sallama, Mumy ta juya ta koma dakinta da sauri ya bi ta da ido still answering his phone call, alama tayi ma Karime da cewa kar ta kuskura ta fito, sannan ta juyo ta kulle kofar ta dawo parlon ta xauna, Shuraim ya gama answer wayar da yake yace "Mumy xan d'an fita in dawo" Tace "Toh Allah ya kiyaye, yanxu dai kai baxa ka dinga sa manyan kaya ba Aliyu, wllh suna maka kyau amma baka so, even if it's just once a week banda Fridays ka dinga sa wa" Bai ce komai ba ya nufi bedroom dinta, bata san lkcn da ya nufa dakin ba kawai gani tayi ya bude xai shiga, ta mike da sauri tace "Me xaka yi ciki Aliyu??" Tuni ya shiga suka yi ido hudu da Karime, sai a sannan ya juya ya kalli Mumy yace "Gaban mirror xan je" Bai jira tace komai ba ya wuce ciki, Karime dake tsaye kamar munafuka ta risina tace "Ina kwana yallabai" Ko kallonta bai yi ba ya nufi gaban mirror ya tsaya, Mumy dai na tsaye ta kasa bin bayansa, Karime ta fito dakin kamar munafuka tace "Hajiya na gama" cikin daga Mumy tace "Toh dama wani linki ne tun daxu kamar warce na sa kwalemar dakin gaba daya?" Karime ta nufi kofa da sauri ta fita, Shuraim ya fito daga dakin, Mumy ta hade rai tace "Ajiya kayi min a dakin da ka shige min bbu excuse Shuraim??" Yace "Na bar comb dina a nan ai jiya" Yana fadin hka ya nufi kofa, Tace "Shuraim Ina ga fa gwara in sallami mai aikin nan tawa kawai, bbu abinda take tsinana min sai magana ma da take yawan sanya ni, dubi fa wnn yarinyar yaushe ta xo gidan amma na gwammace in sa ta aiki a kan Sajida, cikin dadin rai xata maka komai fess fess, to ni kuma nayi ta kiranta kenan uwar dakinta tayi wani tunanin daban? Yanxu ma nasan uwar dakin nata bata sani ba ta xo, tun safe na kira Sajida ta xo ta min gyaran nan ban ganta ba shine na kira ita wannan din, matsalar ta daya wnn bata da wani wayewa...." Shuraim dai bai ce mata komai ba ya bude kofa yace "Sai na dawo" bin sa tayi da kallo har ya rufe kofar, ta xauna a hankali saman kujera tana naxari.... Mumy ce xaune dakin Hajiya Sadiya, da Hajiya Baturiya, Mumy tace "Sadiya tunda kin sa6a harka da Mutumin nan ki lallaba
End Ads