sa shi a sojan su karata can" Mikewa Farida da Heedayah suka yi suka bi bayan kaka. Shuraim na tsaye dakin Mumy dake ta masa fada kamar xata ari baki, shi dai bai ce mata komai ba, tace "Banda ka haifi yaro baka haifi halinsa ba ina ruwanka da lamarin su a gidan nan? Ka hada wani abu ne da yarinyar da xaka amshe mata waya da sunan discipline? Ina ruwanka da ita nace" ya shafa kansa still bai ce komai ba, tace "Toh wllh ka kiyayeni a gidan nan, banda baka kishina kai ko kallon yar nan xaka yi balle ka amshi wayarta Aliyu" Wayarsa dake hannunsa ne ya fara ring, Mumy tayi shiru tana kallonsa, yace "Abba na kirana" Mumy tace "Wannan damuwarka ce, ni dai idan har baxaka fita hanyar makiyana a gidan nan ba to wllh sai dai ka canxa wata uwar ba ni ba" juyawa yayi ya nufi kofa ya fita, a main parlor ya tadda kaka tana dube dube kamar munafuka, tana ganinsa ta hade rai ta hau kakkabe kujerun parlon tana cewa "Mata duk kazamai kawai" yayi wucewarsa bangaren Abba, tana ganin haka ta nufi dakinsa da sauri ta shiga tana kalle kalle, saman madubi ta ga wayoyi har biyu a ajiye da dubu biyar ta kwashe duka ta fice. Shuraim yace "Abba Heedayah take koya ma ynda ake operating waya shi yasa na amshe" Abba yyi shiru yana kallonsa haka ma Mami dake parlon tana xuba ma Abba abinci, Mami ta dauke kanta ta ci gaba da abinda take, can Abba yace "A ina ka gan su?" Shuraim yace "Can baya" Abba yace "That's wrong, and you did the right thing collecting the phone, ka rike wayar wajen ka nan da kwana biyu sai ka bata" Shuraim ya dago kansa yace "Ita ma bai kamata ta rike waya ynxu ba, she still in Jss2 I think" Abba yace "Haka ne but assuming a gidan nan take ni baxan bari ta rike waya ba, but tunda ba a nan take ba we have no say, ka maida mata wayarta after two days..." Shuraim yace "Idan xata koma makaranta xan bata amma ba ynxu ba" Abba ya kalli Mami da bata kalli Inda suke ba yace "Ur opinion Rahinah" Mami ta kallesa tace "Duk ynda kayi dai dai ne barrister" Abba yace "Alright, ka bar wayan gun ka Shuraim" Shuraim yace "Toh shkkn" daga haka ya mike ya fita parlon. Karfe tara da rabi kaka na xaune dakinta ta daura kafa daya kan daya ta gama cinye kazar da Junaid ya kawo mata tana sakace hakori Shuraim ya shigo, tana ganinsa ta ci gaba da sakace sakacenta tana lumshe ido, ya bi dakin da kallo sannan ya juya ya fita, bangaren Mami ya nufa ya bude parlon ya shiga, bbu kowa parlon amma yana jin muryarsu a daki, karasawa yyi bedroom din ya bude kofar, Xaune suke kan gado suna kallo a laptop din Farida, Heedayah na sanye da yar rigar bacci iya cinya haka ma Farida, Farida ta xaro ido, da sauri ta rufe jikinta da Pillow tana kallonsa, Heedayah ta sauka saman gadon da gudu ta shige bandaki ta rufe, yana kallon Farida yace "Bani wayar da kika shiga dakina kika dauka" Ta xaro ido tace "Ni?? I didn't take any phone wllh, tun daxu muna kallo a nan ban fita ba" ya fi minti daya yana kallonta sannan ya juya fice daga dakin, ya koma dakin kaka, kaka ta kallesa tace "Sojojin ne suka baka pareti da daddaren nan, naga ka shigo daxu baka ce min komai ba, gashi ka sake dawowa" Yace "Ina wayoyin da kika dauka a dakina?" Kaka ta mike tsaye ta wani xaro ido tace "Wayoyi kuma?" Yace "Ehh" Ta nemi waje ta xauna har ta fara salati sai kuma ta sakar masa kuka tace "Tunda uwata ta haifeni bbu wanda ya ta6a tsareni yana tuhumata a kan sata, satar ma ta waya, Shureen in rasa abinda xan sata a gidan nan sai waya? Ashe ma gantalalliyar barauniya ce ni, in saci motocin Amadu in gudu mana idan haka ne, Amma sai ka shigo min tsakar dare kace Ina wayar da na sata??" Shuraim ya gyada kai ya juya ya fita dakin. Bai sake maganar wayar ba har gari ya waye, Farida na share ma Kaka dakinta, Heedayah na kwance saman gado tana kallo a laptop, kaka tace "Shiru Shureen bai sake shigowa nemo waya ba gashi har karfe goma ko dai ya hakura ne, ni dubu biyar din ma kasuwa xaku je min ku siyo min kayan ciki in narka uban farfesuna mu yi sati muna ci, kayan cikin dubu biyar ai xai cika wancan kwallan ko?" Farida ta juya tana kallon katon abinda kaka ke nuna masu, kaka tace "Har yawuna ya tsinke maxa gama sharan ku tafi da wnn mara amfanin ku siyo min kayan cikin" Farida tayi kasa da murya tace "Ke dai kar kice masa komai a kan wayar ki ci gaba da boyewa" Kaka tace "Toh da fa, ai ni tasa wayar ma da kyar idan ba chechenia xa ku rakani ba in siyar da 'yar banxa in siyo kan saniya inyi farfesuna" Farida ta fashe da dariya har da kyakyatawa, murya can kasa tace "Xan raka ki wllh, gashi naga shi ma IPhone din ne har ya fi nawa" Kaka tace "Toh ko in shirya yanxu?" Farida tace "Shirya" mikewa kaka tayi xata fiddo da sabon kayanta, Ganin cup da Heedayah ta sha shayi ta kalli Heedayah dake kwance tace "Kai ni dai wnn yarinya ta isheni wllh, kwata kwata ba a morarta, son jikinta har tsoro yake bani ni dai, to Amadu kike jira ya dauke maki kopin nan ko Rakiya??" Heedayah ta sakko saman gadon ta dau cup din ta nufi kofa kaka ta bi ta da harara tace "Toh meye ma amfanin bude idon da Amadu ya kai ki aka yi idan ba asaran kudi ba" Heedayah na fita dakin ta wuce kitchen, Khadijah dake xaune dining ta bi ta da harara, ita dai ko kallonta bata yi ba, ta bude kofar kitchen din ta shiga, ta ajiye cup din a sink kenan ta ga Shuraim tsaye kitchen din yana hada shayi, sunkuyar da kanta tayi xata fita, yace "Zo nan" kin tsayawa tayi ta ruga da gudu ya kamata kafin ta isa kofa, kuka ta sakar masa a tsorace tace "Ni ban yi komai ba wlh, kaka ce tace in kawo cup din kitchen" leka parlor yyi ganin Khadijah ya rufe kofar kitchen din, har wani rawa jikinta yake yi sbda tsoro, ya jinginar da ita da kofa yace "Wa ya shiga dakina ya dau waya?" Ta bude hannu da sauri tace "Nima ban sani ba, bani bace wllh" kalle kallen kitchen din ya fara yi taga ya kallo inda muciya yake, xaro ido tayi ta rungumesa a rikice tace "Wllh Kaka ce ta dauka ta boye a dakinta, a cikin akwatinta ta boye" Bai san lkcn da yyi murmushi ba yana kallonta duk da ta boye fuskarta jikinsa, a hankali cikin rawar murya tace "Yanxu xa su je su siyar da wayan da Farida"
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng