x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - MAZAN JIYA 2

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 55701 words

Category: Romance Story +18

Views 196

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
dade yana kuka sai
ya zare wannan wuka daga cikin Larziya ya hau
cakawa jikinsa. Abirka da jikin tsohon sadauki
mai tarin sihirin tsafi sai wukar ta kasa hudashi.
Nan fa Hantaru ya zama kamar mahaukaci ya
rinka wawuro komai yana makawa a jikinsa
don ya kashe kansa ya huta da bakin ciki amma
duk abin da ya cakaa cikin nasa sai ya ki tasiri.
A wannan lokacin babu kowa a gidan sarki
domin gaba dayan mutanen gidan sun tafi
gidan Shurem don yin gaisuwar mutuwar
Salimat. Nan take Hantaru ya dauki gawar
Larziya ya koma da ita gidan Shurem inda ya
iske Sarki da sauran jama'ar gari, Koda sarki ya
hango Hantaru dauke da gawar Larziya sai ya
fashe da matsanaicin kuka kuma nan take
Kwakwalwarsa ta tabu ya kama surutai irin na
mahaukata. Gaba dayan jama'ar da ke wajen sai
141

TASKARNOVELS.COM.NG
da suka afshe da matsanaicin kuka saboda
tsananin tausayin Hantaru da Sarki. Sannu a
hankali Hantaru yazo da gawar gimbiya Larziya
kusa da kabarin mahaifiyarsa Salimat ya ajiye
gawar. Kawai sai ya mike tsaye yaje inda
dokinsa ke daure ya dauko takobin Saiful
Lujara. Koda jama'a suka ga ya zare takobin
daga cikin kufenta sai suka firgice suka kama
guje-guje da iface-iface.Kawai sai Hantaru ya
dubi jama'a ya yi wani dan guntun murmushi
sannan ya caka takobin takobin ta lume ta faso
gadon bayansa. Hantaru ya tafi kasa luu! Ya
durkusa bisa guiwoyinsa ba tare da ya fadi kasa
ba ya zama gawa. Amma har a wannan lokacin
murmushi na fuskarsa bai guseh ba. Faruwar
hakan ke da wuya sai takobin Saiful Lujara ta
zare kanta daga cikin Hantaru ta yi sama ta
luluka izuwa cikin gajimare ta 6ace 6at! A
sannan ne kuma gaba dayan jikin Hantaru ya
sandare ya zamo gunki. Har yau, har kwanan
gobe idan mutum yaje birnin Darul Mahabul ya
ziyarci gidan Shurem zai ga sadauki Hantaru
cikin siffar gunki ya durkusa a gaban kabarin
Salimat da kabarin matarsa gimbiya Larziya da
murmushi a fuskarsa.. LOKACIN DA SARKI
DUJALU ya zo nan a labarinsa sai ya ga idanuun
142

TASKARNOVELS.COM.NG
Hursiya sun cika sharkaf da hawaye saboda
tsananin tausayi. Tsawon yan dakiku daya daga
cikinsu bai ce uffan ba. Daga can sai Sarki
Dujalu ya dubeta ya ce, "Ya ke 'yar uwata yanzu
me kika fahimta a cikin wannan labari na
Hantaru,kuma wane irin darasi kika samu?".
Koda jin wannan tambaya sai Hursiya tayi ajiyar
zuciya ta ce, "Hakika na fahimci cewa a duniya
babu wani abu mai hadarin gaske sama da
soyayya, domin za ta iya sa mutum ya aikata
abin da bai dace ba kamar yadda sarki Kusaidu
ya hadiyi zuciya ya mutu saboda ganin an
kashe matarsa Zarifa da yadda Salimat ta sha
guba ta mutu saboda mijinta Sarki Kusaidu ya
mutu da kuma yadda sadauki Rabbasu ya
murdewa kansa wuya ya mutu saboda ya
fuskanci cewa ba zai taba samun masoyiyarsa
ba Larziya. Uwa uba kuma shi ne,Hantaru
wanda ya sallama rayuwarsa don kyautata wa
masoyiyarsa amma sai gashi a banza ya kashe
kansa bayan ya sha bakar wahala kuma ya sami
daukakar da babu wanda ya sami kamarta a
wannan zamani amma kuma daukakar bata
amfane shi da komai ba. Na yi koyi darusa da
dama a cikin wannan labari, musamman akan,
duk abin da mutum zai so to ya soshi saisa-saisa
143

TASKARNOVELS.COM.NG
kada ya zurfafa.'Abu na biyu kada mutum ya
bari zuciyarsa ta kawatu da son kudi ko
matsayi da yawa domin.zai iya hallaka kowa
domin ya sameta ko da kuwa dan uwansa na
jinine kamar yadda Zarifa da Marifa suka taso a
cikin kiyayyar juna alhalin sun kasance 'yan
uwan juna na jini uwa daya uba daya. Abu na
uku mafi muhimmanci shi ne,daukar alkawari
bisa abin da mutum bashi da tabbacin zai iya
cikawa. Tun da farko inda Hantaru bai dauki
alkawarin zai yi duk abin da Larziya za ta
umarceshi da yi ba da ba zai je birnin Kisra ba
har yai aikin da zai zo yai nadamarsa ba, amma
saboda idanunsa sun rufe akan soyayyarta sai
ya amsa dukkan muradinta. Ya kai dan uwana
kayi sani cewa idan zan ci gaba da lissafo maka
darasin da ke cikin wannan labari sai gari ya
waye ban kare ba." Koda jin wannan batu sai
sarki Dujalu ya bushe da dariya ya ce, "Ai
wadannan darussan ma kadan ne akan wanda
ke cikin labarin sadauki Shaddadu na birnin
Kufa da kuma labarin sadauki Hulkas na birnin
Romaniya". Koda jin wannan batu sai Hursiya
ta goge hawayen idanunta da sauri ta dubi
Sarki Dujalu cikin murmushi ta ce, "Ina rokonka
da ka bani labarin sadauki Shaddadu na birnin
144

TASKARNOVELS.COM.NG
Kufa domin na ji irin abubuwan al'ajabin da ke
cikin tasa rayuwar". Koda jin wannan batu sai
sarki Dujalu ya sake bushewa da dariya a karo
na biyu ya ce;Daga kanki sama ki duba ki gani,
mene ne wancan?". Cikin sauri Hursiya ta daga
kanta sama sai ta ga ashc har alfijir ya keto.
Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke nan
bisa yaddaa aka yi suka shafe sa'oi masu yawa
haka a zaune tana sauraron labari ba tare da ta
gaji ba ko kuma barci ya dauketa ba." Koda
sarki Dujalu ya fahimci cewa Hursiya tayi
mamaki matuka bisa tsawon lokacin da suka
shafe yana ba ta labarin Hantaru, sai ya mike
tsaye ya ce, "Ya ke 'yar uwata ki sani cewa
labarin sadauki Shaddadu ya ninka na sadauki
Hantaru yawa sau biyu,sai dai kawai na gajarce
miki shi saboda haka sai mun sami isasshen
lokaci anan gaba. Yanzu sai ki tashi da sauri ki
koma can tantinki domin kiyi wanka kiyi kalaci
nan da dan lokaci kadan wannan runduna tamu
za ta ci gaba da tafiya domin mu isa tekun
Bahar Sufiya akan lokaci". Gama fadin hakan ke
da wuya sai sarki Dujalu ya juya ya nufi inda
tantinsa yake.Cikin sauri itama Hursiya ta mike
tsaye ta ruga izuwa na ta tantin. Ko rabin sa'a
ba a yi ba gaba dayan rundunar su sarki Dujalu
145

TASKARNOVELS.COM.NG
suka gama kimtsawa,aljanu suka kwashi
mutane da dukkanin kayayyakinsu suka bude
fuka-fukansu suka tashi sama suka fara tsala
matsanaicin gudu suna masu tunkarar tekun
bahar Sufiya. Wannan shi ne abin da ya faru
tsakanin sarki Dujalu da yar uwarsa "Hursiya
bayan ya gama bata labarin sadauki Hantaru
sun kuma kintsawa sun ci gaba da tafya sun
tunkari kogin bahar Sufiya don dauko takobin
SAIFUL LUJARA. ALAMARIN RUNDUNAR
Sarki Maharaz kuwa, lokacin da suka baro
birnin Darul Mahabul sai suka wanzu suna
wata tafiya ta ban al'ajabi, wacce ta baiwa kowa
mamaki, dalili kuwa shi ne, saurin tafiyar ya
wuce misali, domin gani suke yi kamar suna
shafe tafiyar kwana guda a cikin abin da bai kai
rabin sa'a ba. Shi kansa sarki Maharaz yana
mamakin al'amarin amma da ya tuno da
jawabin da ubangijinsa Darbuza ya yi masa
cewar zai gajarce musu nisan wannan tafiya sai
ya daina mamakin komai, hankalinsa ya
kwanta. Sadauki Inmal ko yaushe yana daf da
keken dokin da Mulaifa ke ciki, baya yarda a
sami wata tazara a tsakaninsu don tabbatar da
tsaron lafiyarta. Duk bayan 'yan dakiku kadan
sai Mulaifa ta yaye labulen keken dokin ta leko
146

TASKARNOVELS.COM.NG
wajen sun hada ido da Inmal gami da yiwa juna
murmushi. Haka dai aka ci gaba da wannan
tafiya ba sassauci face idan dare ya yi a yada
zango. Wani lokacin ma in dai akwai hasken
farin wata ba a yada zango sai dai a ci gaba da
tafiya. Hakika masu iya magana sun yi gaskiya
da suke cewa, "Idan ka ga ki gudu, to sa gudu ne
bai zo ba'. Kai tsaye wannan runduna ta su
Sarki.Maharaz ta rinka ratsa dazuzzuka tana
wucewa, komai yawan 'yan fashi ko muggan
dabbobin daji ko muggan aljanu da zarar sun
jiyo takun sawun wannan runduna wacce ke
haddasa karamar girgizar kasa saboda tsananin
yawansu sai ka ga wadannan muggan halittu
sun falfala da gudu sun nemi amuka sun shiqe
sun 6uya domin sun san cewa GABA DA
GABANTA, aljani ya taka wuta. Lokacin da
wannan runduna ta iso cikin dajin Sauratul
Auzur dama sarkin yaki Hibru da sarki Maharaz
ne akan gaba, don haka sai sarki Maharaz ya ja
linzamin dokinsa ya tsaya cak. Nan take kuwa
kowa ya yi koyi da shi,aka yi tsit tamkar babu
mai numfashi a wajen. Sarki Maharaz ya shaki
numfashi sannan ya dubi gabas da yamma,
kudu da arewa sannan ya daga kansa sama ya
sauke ya dubi kasa. Kawai sai ya yi ajiyar zuciya
147

TASKARNOVELS.COM.NG
ya ce,Tabbas abokan gaban gatbarmu sun wuce
ta cikin wnanan daji kimanin kwanaki biyu
rak!da suka wuce, kuma sun fafata kazamin yaki
da daya daga cikin irin mugayen halittun da ke
cikinsa. Ya ku jama'ata kuyi sani cewa masifi da
ke cikin wannan daji sun fi gaban tunanin
bil'adama ko aljan, don haka ba lallai bane
yawanmu, jarumtakarmu da karfin sihirinmu ya
Kwace mu, amma tun da har abokan gabarmu
suka samu nasarar wuce lallai ina sa ran cewa
muna zamu iya wucewa,sai dai bai zamo lallai
ba dukkaninmu mu iya wucewa ba a raye, don
haka sai kowa ya gyara damararsa kuma ya yi
iya kokarinsa domin ceton rayuwarsa". Koda
gama fadin haka sai sarki Maharaz ya dubi sarki
yaki Hibru ya ce, "Ya kai abokina ai sai ka wuce
kan gaba domin a wannan dajin babu batun
karfin sihiri sai dai amfani da tsagwaron karfin
damtse da hikima gami da basira". Da jin
wannan batu sai Hibru ya yi murmushi sannan
ya Kwalawa Inmal kira.Inmal ya zaburi dokinsa
ya rufa inda Hibru da sarki ke tsaye. Hibru ya
dubi Inmal ya ce, "lna son ka kasance kusa da
ni." Inmal ya gigirza kai alamar cewa ya bi
umarni. Nan take Hibru ya sakarwa dokinsa
linzami ya wuce gaba,cikin sauri Hibru ya take
148

TASKARNOVELS.COM.NG
masa baya sannan sarki da sauran jama'a.
Koda fara wannan tafiya a cikin dajin Sauratul
Auzur sai kowa hankalinsa ya tashi ganin irin
yanayin dajin yadda komai a cikinsa ya kasance
a cikin siffar ban tsoro, sannan kuma tunda
suka fara tafiya a cikin dajin ba su ga halitta ko
daya ba koda kuwa kananan Kwari da
tsuntsaye, kuma basa jin sautin komai face
sautin takun sawun dawakansu da rakumansu.
Sai da aka shafe sa'a guda ana tafiya ba a ga
komai ba, kwatsam! Sai aka yi kicibus da gawar
katuwar halittar nan wacce ta danne sarki
Dujalu aka rasa yadda za a yi a zaroshi daga
karkashinta har sai da tsoho Shurkaib ya zo da
shawarar yadda za a iya kubutar da shi. Koda
ganin wannan halitta sai aka yi cirko-cirko ana
kallonta cikin tsananin al'ajabi bisa ganin
tsananin girmanta da siffarta. Nan take sarki
Maharaz ya sauka daga kan dokinsa ya zo gaban
halittar ya tsaya, kawai sai ya dafa gawar
halittar da hannunsa na hagu sannan ya rintse
idanunsa. Nan fa ya rinka ganin duk abubuwan
da suka faru tsakanin halittar da rundunar su
sarki Dujalu tun daga lokacin da suka fara
artabu da halittar har izuwa lokacin da sarki
Dujalu ya sami nasarra kasheta ta danneshi
149

TASKARNOVELS.COM.NG
kawo izuwa sa'ar da aka zaroshi daga karkashin
dabbar da Kyar. Gama ganin wannan al'amari
ke da wuya sai sarki Maharaz ya bude idanunsa
ya dubi Hibru ya ce'Anan gaba kadan zamu iya
haduwa da wata muguwar halittar mai kama da
wannan. Idan har muka sami nasarar halakata
ba zamu sake haduwa da komai ba har mu fita
daga cikin wannan daji". Koda jin wannan batu
sai Hibru ya girgiza kai sannan ya zare
takobinsa. Da ganin haka sai shima Inmal ya
zare tasa. Ganin aka ne ya sa gaba dayan sauran
Dakarun suka kama zare takubbansu. Karar
zare takubban nasu ya cika dajin gaba daya ya
amsa kuwwa. Ba tare da 6ata lokaci ba aka ci
gaba da ratsa dajin. A wannan lokaci kowa ka
dubaa sai ka ga ba a cikin nutsuwa yake ba
saboda fargaba da tsoron abin da za a iya
haduwa da shi. Sai da aka sake shafe sa'a guda
ana tafiyar sannan kwatsam aka yi arba da
wani garkeken dodo mai tsananin tsawo, fadi
da kauri. Saboda tsawon dodon ya kere gaba
dayan bishiyoyi,duwatsu da tsaunikan da ke
dajin. Dodon na da Kwala-Kwalan idanuwa
jajaye kamar an gasa dan buda a cikin wuta,k
ma girmansa ya kai na kwan jimina. Yana da
wawakeken hanci tamkar an bude kofar gari.
150

TASKARNOVELS.COM.NG
Fadin bakinsa kuwa da zurfinsa tamkar rijiya
hakar mutanen farko. Saboda fadin dodon ya
cika hanyar gaba daya babu ta inda za a iya
wuce face ta karkashin kafafunsa da ya dan
warasu. Gaba dayan jikin dodon a murde
yake,kuma kwarin fatar jikinsa tamkar da dutse
aka yi ta. Jikin nasa duka a lullube yake da
gashi, kuma wani irin gashi ne mai tsawo da
tsini tamkar allurai aka lillika. Koda dodon ya
yi wani irin gurnani sai gaba dayan mutane da
aljanun rundunar suka firgice suka dimauce. Da
yawansu basu san sa'adda suka saki
makamansu kasa ba suka juya da baya da gudu.
Kai ba ma su ba, hatta dawakai da rakuma
firgicewa suka yi suka tarvwatse suka kama
gudu a cikin dajin. Wasu a garin gudun ne ma
suka rinka fadawa cikin mugayen ramuka suna
hallaka,wasu suka rinka fadawa kan kayoyi da
itatuwa suna cakewa. Wadanda kuwa basu sami
damar quduwa ba sai suka rinka zubewa kasa
sumammu. Sarki Maharaz, Hibru da Inmal ne
kadai basu firgice ba amma suma sun tsorata da
ganin wannan dodo kuma sai aka rasa wanda
zai karasa inda dodon yake. Sannan nima
Abubakar sam wannan dodo bai tsoratani ba
saboda na kasance jarumin namiji aha dan kar
151

TASKARNOVELS.COM.NG
wasu suke na tsorata ne shiyasa na dakata anan.
Zan ci gaba. Da fatan mun wuni cikin koshin
lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai
iya tuntubata ta wannan number 08138873799
kira ko whatsapp. MAZAN JIYA Littafi na biyu
2 Part J Na Abdulaziz Sani m gini Typing
Abubakar Saleh AlQuyraemey Lokacin da
dodon ya ga mutum uku raklA gabansa tamkar
an ajiye kadangaru a gaban mikiya, sai shi
kansa ya cika da mamakin su Hibru, kawai sai
ya tsaya yana kallonsu suma suna kallonsa
jikinsu na tsuma. Gimbiya Mulaifa kuwa,
lokacin da jama'a suka firgice, sai dawakan
keken dokinta suka juya da baya da gudu a
dimauce suka nufi wani rami mai zurfin gaske.
Mulaifa ta rinka Kwala ihu tana neman a
taimaka mata, amma da yake iface-iface ya yi
yawa a wajen babu wanda ya tuna da
al'amarinta tun da nafsi-nafsi ake yi. Ai kuwa sai
dawakan suka fada cikin wannan rami, karshen
keken dokin ne ya makale a jikin wani dutse
mai gwafa daga sama ya kama reto. Tuni a
wannan lokaci gimbiya Mulaifa ta suma a cikin
keken dokin da ke reto a sama sakamakon
tsananin razanar da tayi bisa ganin wannan
rami mai zurfi da ta fada. Tsawon 'yan dakiku
152

TASKARNOVELS.COM.NG
ana kallon-kallo tsakanin wannan dodo da su
Hibru,amma sun rasa abin da ya kamata su yi.
Daga can sai Hibru ya yi ta maza ya rugo da
gudu izuwa kan dodon. Dodon ya kawo masa
mangari da hannunsa guda. Cikin zafin nama
Hibru ya sunkuya kuma ya yi alkafira a kasa a
karkashin Kafafun dodon, a lokacin da hannun
dodon ya bugi iska ya tafi ya share wadansu
manyan bishiyoyi guda bakwai da ke tsaye a
jerc. Gaba dayan bishiyoyin sai da suka
tun6uko daga cikin Kasa har jijiyoyinsu suka
zube kasa saboda tsananin karfin dantsen
dodon. Kafin dodon ya juya bayansa inda Hibru
yake sai Hibru ya dankara masa sara,take
tartsatsin wuta ya tashi sakamakon haduwar
takobin da gashin jikin dodon. Kawai sai Hibru
ya ga hayaki na tashi a gaba dayan jikin takobin
tasa, kuma ko ina a jikin takobin ya huje saboda
tsinin gashin dodon ne ya caccaketa. Koda
dodon ya juya bayansa ya yi arba da Hibru sai
ya kai masa cafka. Hibru ya yunkura domin ya
goce, amma sai dodon ya sami nasarar
dankarsa kawai sai ya dagoshi sama ya
wangame bakinsa zai jefashi ciki ya lankwame.
Koda Inmal ya hango abin da ke shirin faruwa
ga mahaifinsa sai ya falfala da matsanaicin gudu
153

TASKARNOVELS.COM.NG
irin wanda bai taba yi ba a rayuwarsa kuma ya
daka wawan tsalle ya dira akan cinyar dodon ya
kama kafarsa ya dinga hawa samansa tamkar
kadangare na hawa bango. Kafin dodon ya jefa
Hibru a cikin bakinsa tuni Inmal ya isa kan
kafadar dodon ya caka masa takobin a cikin
katuwar Kwayar idonsa.B& shuri dodon ya saki
Hibru ya fado kasa kuma y kurma ihu irin nasu
na dodanni a lokacin da Kwayar idon nasa ta
fashe ruwan jini ya balle tamkar an bude
IDANTYAR RUWA? Nan fa dodon ya haukace ya
rinka kai naushi, bugu da taku da hannaycnsa
da Karafinsa ya zamana ccwa yana tarvwatsa
bishiyoyi da duwatsun dajin suna fashewa da
ratattakewa. Duk inda dodon ya kai takau da
kafarsa sai ka ga kasa ta rufta tayi rami
zururu.In ba don Inmal na da matukar zafin
nama ba da tuni dodon ya tattakeshi shi da
Hibru amma sai Inmal ya suri Hibru tamkar ya
suri dan yaro ya goyashi a bayansa ya falfala da
mzteznaicin gudu suka kasa tsere da
dodon.Dama:tmi shima sarki Maharaz ya cika
wandonsa da iska ya tashi sama da karfin sihiri
ya ruga izuwa cikin daji. Inmal ya ci gaba da
gudu iya karfinsa amma da ya waigo sai ya ga
wannan dodo daf da shi. Babban abin da ya fi
154

TASKARNOVELS.COM.NG
tayarwa da Inmal hankali shi ne, takun kafafun
dodon bisa kasa yana haifar da girgizar kasa a
dajin gaba daya, kafin Inmal ya isa wurin ma sai
ya ga kaser gabansa ta zabtarc tayi rami, sai ya
daka wawan tsalle ya tsallake ramin. Shi kuwa
dodon komai zurfin rami da fadinsa da ya daga
kafarsa daya sai ya shallakeshi. Lokacin da
Inmal ya fara wannan gudu ne ya lura da halin
da jama'arsu suka shiga,kawai sai gimbiya
Mulaifa ta fado masa a rai, nan take Inmal yaji
dukkan tsoro ya gushe dage Zuciyarse,kawai sai
ya ga wamman gudun da yake yi bashi da wani
amfani gwara ma ya tsaya ayi dik abunm da za a
yi. Lokacin da Inmal ya fara wannan gudu ne ya
lura da halin da jama'arsu suka shiga,kawai sai
gimbiya Mulaifa ta fado masa a rai, nan take
Inmal yaji dukkan tsoro ya gushe dage
zuciyarse,kawai sai ya ga wamman gudun da
yake yi bashi da wani amfani gwara ma ya tsaya
ayi dik abunm da za a yi. Koda gema aiyana
hakan sai Inmal ya yiwa kafaraa birki ya
tsuginna kasa ba zato.Ai kuwa sai wannan dodo
ya shallakeshi bai sani ba. Cikin tsananin zafm
nama Inmal ya yi jifa da Hibru can gefe daya
samnan ya sake daka tsalle ya haye kan dodon
ya rinka gudu a kansz kamar yadda ya yi dazu
155

TASKARNOVELS.COM.NG
domin ya iss kan kafadarsa. Koda dodon ya
fahimci nufinse sai ya rinka kai masa wawan
duka da hanaunsa,shi kuwa Inmal ya ringa tsalle
yana gocewa da kauccwa yana ta tsallc-tsalle a
kansa. Abin da ya baiwa Inmal mamaki shi ne,
yadda wannan gashi na jikin dodon mai tsini
kamar kayoyi bai sossokeshi ba. Abin da Inmal
bai sani ba shi ne, akwai tsumin maganin kaifi
da tsini a jikinsa, kuma tun yana jarir
mahaifinsa Hibru ya rinka shayar da shi
wannan tsumi. Hibru na zaune a kasa dirshan
yana kallon wannan gumurzu da ake yi
tsakanin dodo da Inmal. Al'amarin da ya
matukar bashi mamaki ke nan, domin ya san
cewa shi kansa ba zai iya wannan bajinta ba
wacce Inmal ke yi domin zafin namansa ya
wuce gaban kwatance. A dai-dai waman lokaci
ne sarki Maharaz ya baiyana daf da Hibru
shima ya zauna kusa da shi yana kallon abin da
ke faruwa. Sai da aka shafe sa'a uku ana bakin
gumurzu tsakanin wannan dodo da Inmal,babu
irin kokarin da dodon bai yi ba akan ya make
Inmal ko ya damkeshi da hannu amma sai ya
kasa saboda tsalle-tsallen da Inmal ya dinga yi a
kansa tamkar dan biri akan bishiya. Sai da
Inmal ya galabaitar da dodon sosai sannan ya
156

TASKARNOVELS.COM.NG
sami nasarar sake soke daya idon ya fashe.
Wannan karon da dodon ya wangame bakinsa
ya kwarara ihu sai da gaba dayan bishiyoyin
dajin suka kakkarye suka zube Kasa. Kuma
wani irin feshin wuta ne ya rinka fita daga
bakinsa yana haddasa gobara.Al'amarin da ya
dugunzuma hankalin su sarki Maharaz ke nan
sai da sarki Maharaz ya yi amfani da karfin
sihiri wajen kashe wutar. Lokacin da wannan
dodo ya zama makaho wato duk idanun nasa
biyu Inmal ya fasa su sai ya kara haukacewa ya
rinka duka da fatali da
End Ads