x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - MAZAN JIYA 2

  • 21001 words
  • 24000 words
  • Out of 55701 words

Category: Romance Story +18

Views 198

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
inda za su shiga su buya domin sun san
cewa basu issa su tari Hantaru ba bare har su
hana sh y n abin da ya zo yi. Shi kuwa sariki
Kusaidu ko kadan bai damu da wannan hali da
dakarunsa suka shiga ba kawai burinsa shi ne
125

TASKARNOVELS.COM.NG
ya ga ta inda Hantaru zai 6ullo ya tareshi su
rungume juna yaji dumninsa kirjinsa. Sarki
Kusaidu ya ci gaba da gudu a cikin gidan
sarautar ya shiga wannan sako ya fita ya shiga
wancan loko yana ta Kwalawa Hantaru
kira,amma bai ganshi ba. Shi kuwa Hantaru
lokacin da ya shigo ciki gidan sarautar sai ya
ruga lzuwa cikin wani surfuki inda babu wanda
zai yi zaton shigarsa wajen sannan ya rikide ya
zama gashin dawisu ya nufi dakin gimbiya
Zarifa Duk wannan hayaniya da ke faruwa a
cikin gidan sarauta Zarifa bata san da ita ba,
domin tana can cikin kewayenta a cikin baho
tana wanka a cikin ruwan kumfa mai kamshi.
Tana cikin wannan hali ne ta ga wani gashin
dswisu mai kyau ya shigo cikin turakar. Koda
ganin gashin dawisun sai ta tsaya cak ta kura
masa idanu, daga can sai ta bushe da dariya ta
ce, "Lale marhabun da dana na cikina wanda ya
zo domin ya sare kaina ya kaiwa matarsa".
Kode jin wannan batu sai wannan gashin
dawisu ye rikide ya zama Hantaru sai gashi
tsaye a gabanta rike da kan boka Ardusa a
hannun hagu jini na diga a jikin ken. A hannunsa
na dama kuwa takobin Saiful Lujara ce sai sheki
da walwali take ta haskake bandakin gaba
126

TASKARNOVELS.COM.NG
dayansa tamkar an kunna fitilu a cikinsa guda
dubu. Cikin sanyin jiki da matukar mamaki
Hantaru ya dubi Zarifa a lokacin da hawaye ye
zubo masa ya ce, "Ya ke Ummina ina dalilin da
ya sa kika ci amanar sarki Kusaidu kika sadu de
bokansa aka samu cikina? ya ya aka yi kika
ganeni a yanzu da na shigo cikin wannan
kewaye a cikin siffar gashin dawisu?" Koda jin
wadannan tambayoyi guda biyu sai Zarifa ta
sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan
ta tsuke fuska ta ce, "Ya kai dana ina son ka sani
cewa in dai don biyan bukatar rai, mutunci da
dukiya ba a bakin komai suke ba, saboda
bukatar cika burin zuciyata ne na ci amanar
sarki na sadu da bokansa aka sami cikinka
kuma na bashi kai a matsayiin dan cikinsa har
ya soka fiye da komai a duniya. Tabbas burina
ya cikan tun da na sami nasarar kawar da 'yar
uwata Marifa domin na mallaki dukiyar da
mahaifinmu ya bar mana ni kadai.Sai dai kash!
Har yanzu ban mallaki dukiyar ba, bakin cikin
hakan ne ya sa naji bana tsoron mutuwa don
haka idan ka kasheni a yanzu zan kasance a
cikin farin ciki tum da burina bai gama cika ba a
duniya. Abin da zan sanar da kai shi ne, kaima
baka isa ka shiga kogon da aka ajiye wannan
127

TASKARNOVELS.COM.NG
dukiya ba domin ka debota ka kaiwa matarka
Larziya domin a lokacin da na fahimci cewa ba
zan iya mallakar dukiyar ba face na samo
takobin Saiful Lujara sai hankalina ya
dugunzuma na baza manzanni a duniya suka
rinka ziyartar manyan bokaye akan yadda zan
iya kona wannan dukiya gaba dayanta yadda
har abada babu wanda zai moreta. Sai da
manzannina suka shekara goma sha biyar suna
wannan aiki sannan suka samo mini sihirin da
na sami damar kona dukkan wannan dukiya ta
zama toka. Yanzu haka idan ka shiga inda
dukiyar take za ka iske babu komai a ciki face
toka. Game da tambayarka ta biyu kuwa, ina
son ka sani cewa komai sammakonka wani a
tafe ya kwana. Saboda tsananin yawo na a cikin
duniya wajen bokaye sai da na mallaki dukkan
sihirin tsafi na duniya wanda ban samu ba
kawai shi ne wanda ke jikin takobin Saiful
Lujara. Ka ga ke nan a duk matsafan duniya
yanzu babu wanda ya fini karfin sihiri face
kai,don haka duk irin yanayin da mutum zai
juye izuwa wata siffar da na kalleshi sai na
ganshi a zahirin siffarsa ta gaskiya. Yanzu gashi
a matsayinka na dan da na haifa a cikina baka
kaunata ka tsaneni kamar yadda ka tsani
128

TASKARNOVELS.COM.NG
mutuwarka. Dukiyar da na ke ta hankoron
mallaka tafi karfina ina ji ina gani, mijina da
yake mutuwar sona fiye da komai a duniya na
hainceshi na ci amanarsa kuma ya san duk abin
da na aikata amma saboda tsananin son da yake
yi mini ya danne komai a zuciyarsa ko a
fuskarsa bai ta6a nuna mini ba". Sa'adda zarifa
tazo nan a zancenta sai idanunta suka ciko da
Kwalla hawaye ya fara zuba sannan ta ci gaba da
kallon Hantaru tana mai cewa,"Ya kai dana
yanzu mene ne amfanin zamana a duniya? Ina
ribar da na samu tun da har yanzu abin da na
shuka ban girbi komai ba? Hakika nayi nadama
tun daga lokacin da 'yar uwata Marifa ta fada
mini maganganun cewar za ta rabu da ni ba a
son ranta ba duk da cewa bama son juna
saboda ko babu komai ni jinin ta ce. Duk
sa'adda na tuno da kalamanta sai nayi kuka na
zubar da hawaye, yanzu ne na gane cewa
duniya ta rudeni na bi son zuciyata nayi biyu
babu don haka yanzu bani da sauran buri a
duniya wanda ya fi na bi 'yar uwata Marifa
izuwa inda ta tafi. Ina tabbatar maka da cewa
idan ma ka tafi yanzu baka kasheni ba sai na
kashe kaina. Bakin cikina shi ne na ri ga na
lalata maka taka rayuwar domin kaima ba za ka
129

TASKARNOVELS.COM.NG
taba samun sukuni ba da kwanciyar hankali."
Lokacin da Zarifa ta zo nan a zancenta sai jikin
Hantaru ya yi sanyi, yaji ba zai iya sare kanta
ba, kawai sai ya fashe da kuka cikin tsananin
bakin ciki. Zarifa ta dubeshi ta ce, "Maza ka yi
abin da ya kawoka domin wannan kukan ba zai
fishsheka ba. Idan kuma ba za ka iya kashe ni
ba to ni ka bani takobin Saiful Lujara na sare
maka kai sannan na kashe kaina.! Kafin
Hantaru ya ce wani abu sai Zarifa ta fito daga
cikin bahon wakan ta fisge takobin Saiful Lujara
daga hannunsa ta daga sama za ta sare masa
kai. Cikin zafin nama Hantaru ya cafki takobin
ya Kwace takobin sannan ya datse ma ta wuta,
sai ga kanta na lilo a hannunsa. A dai-dai
wannan lokacin ne sarki Kusaidu ya banko
Kofar kewayen ya shigo. Da shigowarsa ya yi
arba da kan Zarifa a hannun Hantaru jini na
zuba sannan ya ga gangar jikinta kwance a Kasa
faca-faca da jini. Koda ganin wannan al'amari
sai sarki Kusaidu ya hadiyi zuciya nan take ya
fadi kasa matacce. Hantaru ya kwarara uban
ihu ya fadi kan gawar sarki Kusaidu ya
rungumeta kuma ya fashe da matsanaicin kuka.
Sai da aka kwana goma sha bakwai ana kuka da
bakin cikin mutuwar sarki Kusaidu a cikin
130

TASKARNOVELS.COM.NG
birnin Kisra. Shi kuwa Hantaru saboda tsananin
bakin ciki ma kasa zama ya yi ayi jana'izar Sarki
da shi. A wannan rana ya shirya ya tafi kogon da
mahaifin su Zarifa ya 6oye wannan dukiya.
Bisa tarihi tun bayan mutuwar mahaifin su
Zarifa ba a taba samun wani mahaluki da ya
shige shi ba walau mutum ko aljana, amma a
wannan rana sai ga shi Hantaru ya sa takobin
Saiful Lujars ya sare wata bakar kofa ta karfe a
jikin kogon. Take kofar ta rufta ciki ta fadi
Fasa.Duk da cewa kogon a can bayan gari yake
sai da aka jiyo karar faduwar kofar a can cikin
bimin Kisra, saboda girman kofar da nauyinta
domin inda Kartin aljanu majiya karfi guda
dubuc casa'in za su hada karfi ba za su iya
banke kofar ba har su kaita kas. Kai sabods
karfin sihirin da ke jikin kogon ko fara ce ta
gifta ta kusa da kogon sai ta fado kasa
matacciya bare mutum ko aljan. Bayan Hantaru
ya banke kofar ta fadi kasa sai ya kunna kai
cikin kogon ba tare da fargabar komai ba. Duk
da cewa kogon na da tsananin duhu ko tafin
hannu mutum ba ya iya gani amma da shigar
Hataru cikin kogon sai ya haskake gaba daya
albarkacin hasken takobin Saiful Lujara.Kawai
sai ya ga babu komai a cikin kogon face bakar
131

TASKARNOVELS.COM.NG
toka tuli a ko ina, sama da kasa. Koda ganin
wannan al'amari sai Hantaru ya durkusa kasa
bisa guiwoyinsa ya fashe da kukan bakin ciki. A
sannan ne ya gasgata maganar Zarifa cewar ta
gama kona dukiyar gaba dayanta amma a
sa'adda ta gaya masa sam bai yarda ba. Sai da
Hantaru ya dade a durkushe a kasa yana kukan
takaici da bakin ciki. Abin da ya fara fado masaa
zuciya shi ne ya ya Larziya za ta karbeshi idan
ya koma gareta babu wannan dukiya sai kan
mahaifiyarsa Zarifa?" Haka dai Hantaru ya ci
gaba da tunani mai zurfi a zuciyarsa ya tuna
cevwa shi fa yanzu ya rasa babban masoyinsa a
duniya wato sarki Kusaidu, wanda ya rage
masa kawai mutum biyu ne, daga Salimat
wacce ta shayar da shi ta reneshi a matsayin
dan cikinta sai kuma matarsa Larziya wadda
take kuma take &matsayin 'yar uwarsa ta jini ta
hanyar haduwar jini tsakanin mahaifiyarsa
Zarifa da mahaifiyarta Marifa. Idan Salimat taji
cewar Sarki Kusaidu ya mutu sakamakon ganin
gawar Zarifa da wane matsayi za ta dubeshi?
Kawai sai Hantaru ya aiyana a ransa ya ce,
"Lallai ba zan baiyana ma ta gaskiyar al'amari
ba har sai ta dawo birnin Kisra da kanta taji
abin da ya faru". Bayan Hantaru ya gama Kulle132

TASKARNOVELS.COM.NG
Kulle a zuciyarsa sai ya mike tsaye cikin sanyin
jiki da tsananin damuwa da bakin ciki ya fice
daga cikin kogon gaba daya ba tare da bata wani
lokaci ba ya hau dokinsa ya ci gaba da tafiya ba
sassauci ya durfafi birnin Darul Mahabul.
KAMAR YADDA ya shafe watanni yana tafiya a
lokacin zuwansa birnin Kisra haka ya sake
shafe wadannan watanni ya dawo birnin Darul
Mahabul, kuma a wannan karon ma takobinsa
bata sha jini ba, domin babu wani abu da ya
kawo masa farmaki walau mutum, aljan ko
dabba har ya iso kofar birnin Darul Mahabul.
Da zuwansa bakin kofar birnin sai ya ja
linzamin dokinsa ya tsaya cak! Yana tunani.Abin
da ya fara fado masa a rai, ina ya kamata ya fara
zuwa? Shin wajen mahaifiyarsa Salimat zai je
ko kuwa gidan sarki zai wuce domin ya ga
masoyiyarsa abar begensa dare da rana wato
matarsa kuma 'yar uwarsa Larziya? Nan take
Hantaru yaji zuciyarsa ta cika da tsananin farin
ciki,domin ya san cewa a yau ne zai more
amarcinsa da Larziya, amma da ya tuna cewa a
cikin abubuwa guda biyun da Larziya ta ce ya
zo ma ta da su guda daya kacal ya zo da shi,
wato kan mahaifiyarsa Zarifa sai hankalinsa ya
dugunzuma ainun yaji zuciyarsa ta fara bugawa
133

TASKARNOVELS.COM.NG
da karfi kamar za ta tsage ta fado kasa ba don
komai ba sai don tunanin cewa ba lallai bane
Larziya ta amince da shi ba kuma za ta iya kashe
kanta bisa bakin cikin rashin cika burin
mahaifiyarta. Hantaru ya tuno da batun
Salimat, take yaji kijin nasa ya ci gaba da daka
da sauri da sauri duk da cewar ya yanke
shawarar ba zai gaya ma ta ainahin gaskiyar
al'amarin da ya faru ba. Sai da Hantaru ya shafe
rabin sa'a a tsaye akan dokinsa yana ta sakar
zuci, fargaba da tunanin abinda zai fishsheshi
sannan daga karshe ya yanke shawarar ya fara
zuwa gidan Shurem domin ya sadu da Salimat
saboda ya san cewa ya tafi ya barta a cikin
tsananin fishi da bakin ciki, bai san halin da
take ciki ba yanzu. Lallai ya zamo wajibi a
gareshi yaje gareta ya nemi gafararta kuma ba
zai yarda te san da mummunan bamar da ya
aikata ba a can birnin Kisra har reyuka uku
suka salwanta. Lokacin da Hantaru ya fara
tafiya ya nufi hanyar de za ta kaishi gidan
Shurem, sai ya tuna cewa ai yana dauke da kan
mahaifiyarsa Zarifa a cikin jakara guzurinsa
wanda ya zuba masa wani ruwan sihiri wanda
ya hanashi rubewa. Nan take Hantaru ya ratse
hanya ya shiga cikin daji ya isa har karkashin
134

TASKARNOVELS.COM.NG
wani tsauni mai duhuwa ya saula daga kan
dokinsaya tsaya cak! Ya dubi gabas da
yamma,kudu da arewa bai ga kowa ba kuma bai
ji motsin komai ba. Har tsawon lokaci yana
tsaye a hakan. Koda ya tabbatar da cewa babu
mai ganinsa sai ya haka rami a gaban wata
siririyar bushiya ya binne wannan kai na Zarifa
sannan ya koma da baya ya kau kana dokinsa ya
durfafi gidan Shurem. Tun dage nesa Hantaru
ya hango kofar gidan Shurem a ciko makil da
zuriarsu ta makera, jama'a na tsaitsaye sun yi
tsit ba a jia muryar kowa face sautin
numnfashinsu. Koda ganin haka sai zuciyar
Hantaru ta buga da tsananin karfi irin bugawar
da bai tafa ji ba a rayuwarsa. Cikin tsananin
fargaba ya iso cikin taron, ai kuwa jama'a na
hangoshi sai aka dare aka bashi banya ya kutsa
ta tsakiyarsu bisa dokinsa ya iso tsakiyar
harabar gidan. Koda ya yi arba da abin da aka
shimfide a agabansa sai ya tsandara uban ihu
ya fado kasa tim! Daga kan dokinsa ya fashe da
mataanaicin kuka yana mai buga kansa a jikin
dirkar gini, har kan nasa ya fashe jini ya ringa
zuba. Cikin sauri wasu karti majiya karfi su uku
suka kamashi suka rirrikeshi don kada ya ci
gaba da buga kansa a jikin dirkar ginin wacce
135

TASKARNOVELS.COM.NG
ita ma kanta ta fara tsattsagowa tana barazanar
rugujewa. Ba wani abu Hantaru ya yi arba da
shi ba face gawar Salimata shimfide idanunta a
Kafe kamar za a yi ma ta magana ta amsa.
Hantaru ya ci gaba da rusa kuka da ihu tamkar
mahaukaci sabon kamu har ya zamana cewa
gaba dayan jama'ar da ke wajen sun tsorata
ainun sun fara watsewa don tsoron kada ya
zare takobinsa ya hausu da sara. Shaulat da ke
tsaye a kansa tana ta faman zubar da hawaye ta
kasa cewa da shi komai,sai ta sa hannunta cikin
aljihu ta dauko wata guntuwar wasika ta
mikawa Hantaru. Hannun Hantaru na karkarwa
ya karbi wasikar ya budeta ya fara karantawaa
fili, kamar haka; Ya kai dana Hantaru,kayi sani
cewa ka bani kunya, kuma ka bani mamaki,
domin a zatona za ka janye mugun nufin da ka
tafi da shi izuwa birin Kisra, amma sai gashi
soyayya ta sa idanunka sun rufe ka manta da
muhimmancina a rayuwarka Ka tuna cewa
babu wani mahaluki da nake so a wannan
duniya sama da Sarki Kusaidu,gashi ka kashe
matarsa Zarifa a dalilin ganin gawarta da ya yi
shima ya hadiyi zuciya ya mutu. Ka tuna cewa
babu wani mahaluki da nake soa wannan
duniya sama da Sarki Kusaidu,gashi ka kashe
136

TASKARNOVELS.COM.NG
matarsa Zarifa a dalilin ganin gawarta da ya yi
shima ya hadiyi zuciya ya mutu. Ka tuna cewa
yanzu na rasa mijina, kuma na rasa kakana boka
Sulbaini da mahaifina,wanda ya rage mini kawai
ita ce mahaifiyata da kai,kuma yanzu na
tsaneka kamar yadda na tsani dukkan
makiyana a duniya.Na san za ka yi mamaki bisa
yadda aka yi na san duk abin da ka aikata a
birnin Kisra, amma idan kayi tunani ba abin
mamaki bane tun da matsafa basu kare ba a
doron kasa. Tun daga ranar da ka bar nan birin
ka tafi ?zuwa birnin Kisra har ka je ka kashe
boka Ardusa, sannan ka je ke kashe Zarifa kawo
izuwa barowarka birin Kisra duk na gani a cikn
madubin tsafi. Koda na gama ganin wannen
al'amari sai na fashe de matsanancin kuka na
kamu da Babban bakin ciki kuma nan take naji
duniyar ta yi min kunci bani de bukater na ci
gaba da rayuwa Bisa wannan delili ne na sha
guba a ranar de ka iso nan birnin Kisra.
Wanann shi ne kelamaina na karshe a gareka ya
kai dana. Ina mai yi maka bushara da cewe
rayuwar duniya be ta da wani dadi idan har
babu masoyi. Tabbas ka zame mini bakin takobi,
kumna bakin kumurci mai mugun dafi. Ina mai
shawartarka da ka bi rayuwar duniya a sa nu
137

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma ka sani cewa baka da babban makiyi a
rayuwarka sama da zuciyarka tun da ba za ka
iya sarrafata ba. Ka sani cewa a duniya bebu
abin da ya fi soyayya karfi de dadi, kuma babu
abin da ya fita wahala da hadari. Har abada ba
zan koma Kisra ba..." Zan ci gaba. Da fatan
mun wuni cikin koshin lafiya, sannan duk
wanda yake son complete zai iya tuntubata ta
wannan number 08138873799 kira ko
whatsapp. MAZAN JIYA Littafi na biyu 2 Part I
Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar
Saleh AlQuyraemey Sa'adda Hantaru ya zo nan
a karatun wasikarsa sai ya sake fashewa da
matsanaicin kuka ya rungume gawar Salimat a
kirjinsa ya yi ta kuka kamar ba zai taba dainawa
ba. Da Kyar da sidin goshi kuma da rarrashi
gami da lallami aka banbare gawar Salimat
daga hannunsa, sannan aka haka kabari aka
binneta.A bakin kabarin nata Hartaru ya kwana
yana kuka har gari ya waye rana ta take.
Saboda tsoron fushin Hantaru sai aka rasa
wanda zai zo ya rarrasheshi. Hatta Shaulat ma
kasa zuwa ta yi. Lokacin da Hantaru ya gaji da
kuka har ya zamana cewa ruwan hawayensa ya
kafe kuma muryarsa ta dashe, kuma
numfashinsa na sarkewa sai ya sulale kasa
138

TASKARNOVELS.COM.NG
sumamme. Sai da Shaulat ta debo ruwa ta
watsa masa sannan ta bashi a baki ya sha
sannanj ya dawo cikin haiyacinsa.Koda ya nutsu
sai ya mike tsaye ya fice daga cikin gidan
Shurem ya durfafi gidan sarki kai tsaye,yana
tafe yana tangadi kamar wanda ya sha giya ya
bugu saboda tsananin yunwa da kishirwar da
ke jikinsa gami da dumbin bakin ciki. Da zuwan
Hantaru kofar gidan Sarki sai ya ga kan
mahaifiyarsa Zarifa a cake jikin itace. Al'amarin
da ya matukar firgitashi ke nan ya cika da
tsananin mamaki. Shi dai a saninsa ya binne
wannan kai a can cikin daji a lokacin da babu
wanda ya ganshi. Abin tambaya anan shi ne,
wane ne yaje ya tono kan ya kawoshi nan?
kuma ya ya akayi aka san inda kan yake? Ba
zato ba tsammani, sai Hantaru ya hango gimbiya
Larziya ta fito daga cikin gidan Sarki ita kadai
tana sanye da wata farar doguwar riga mai
shara-shara wacce ke baiyana gaba dayan
kyakkyawar surar jikinta.Fuskarta a cike take
da annuri kuma ta goya hannayenta a gadon
bayanta. Koda ganinta a cikin wannan hali sai
Hantaru ya cika da tsananin farin cikiya
yunkura zai ruga da gudu izuwa gareta kawai
sai yaji ta daka masa tsawa ta ce, "Dakata!Anan
139

TASKARNOVELS.COM.NG
inda kake ya kai masoyina". Cikin matukar
kaduwa da mamaki Hantaru ya tsaya cak a inda
yake ba tare da ya yi gardama ba. Kawai sai ya
ga hawaye ya zubo daga cikin idanun gimbiya
Larziya sannan ta dubeshi ta ce, "Ya kai
masoyina abin begena dare da rana,kayi sani
cewa na yaba da tsananin kokarinka bisa
kokarin cika alkawarin da ka daukar mini kuma
na tabbatar da cewa kana kaunata fiye da komai
a duniya.Sai dai kash! Baka sami nasarar cika
mini burina ba kuma baka da laifi ko
kadan,murmushin da ka ga nayi maka dazu shi
ne murmushin karshe tsakanina da kai, kuma
shi ne na bankwana. Lallai ban ga amfanin
zamana a duniya ba tun da na kasa cika
alkawarin mahaifiyata wanda na yi rantsuwa da
soyayyata a gareta a akansa. Kayi hakuri ya kai
masoyina kuma ka gafarta min bisa tafiyar da
zan yi na barka, ka sani cewa idan ma na zauna
ba zan yi nisan kwana ba domin ciwon zuciya ne
zai kasheni. Da wannan furuci nake maka
bankwana na karshe. Idan har akwai wata
rayuwar bayan ta duniya ina fatan mu sake
saduwa". Koda gama fadin hakan sai gimbiya
Larziya ta fito da hannayenta daga bayanta sai
ga wata sharbebiyar wuka a hannunta. Koda
140

TASKARNOVELS.COM.NG
Hantaru ya hango wannan wuka sai ya falfalo da
matsanaicin gudu domin ya hanata aikata abin
da take nufi. Amma da yake bakin alkalami ya
riga ya bushe kafin ya iso gareta da tazarar taku
uku kacal, tuni ta soka wannan wuka a cikinta,
kawai sai ta sulale kasa matacciya. Hantaru ya
fada kan gawar Larziya ya fashe da kuka, ko
kadan ba a jin sautinsa kuma wanda babu
hawaye. Bayan Hantaru ya
End Ads