x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - MAZAN JIYA 2

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 55701 words

Category: Romance Story +18

Views 200

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
sami natsuwa da
kwanciyar hankali ba".Koda gama fadin haka
sai sarki lafaru ya zaro wata sharrbebiyar wuka
daga kugunsa sannan yayiwa mahaifin boka
Narwas da mahaifiyarsa kisan wulakanci ta
hanyar yanke makogoransu yanka daya a lokaci
guda.Take jini yai tsartuwa daga wuyansu ya
wanke fuskar boka Narwas.Narwas ya tsandara
ihu kuma ya fashe da matsanaicin kuka.Yana
cikin wannan bakin cikine sarki lafaru yakamo
wadannan 'ya'ya nasa guda uku,wato kananan
yara ya take wuyansu da kafafunsa daya bayan
daya suna ihu yayi musu yankan rago.Gaba
daya mutanen dake wurin sai da suka zubar da
hawaye do tausayi.Shi kuwa sarki lafaru ko
ajikinsa wai an mintsini kakkausa. Yayin da
boka narwas yaga irin kisan wulakancin da
yayiwa 'ya'yansa,sai nan take ya haukace
191

TASKARNOVELS.COM.NG
yakama sambatu.Hakan baisa sarki lafaru ya
hakura ba,sai ya kamo wannan kanwa tasa
kyakkyawar budurwa,wato lasirat ya maketa ta
fadi kasa sumammiya.A gaban jama'a ya
murkusheta ya biya bukatarsa da ita,sannan
itama yayi mata yankan rago.Tun sa'adda
matar Narwas taga yanda sarki lafaru ya kashe
'ya'yanta ukku sai ta sulale kasa sumammiya
bata farfado ba sai bayan yakashe lasirat.Ai
kuwa tana bude ido tayi arba da gawar lasirat a
gabanta sai ta kwala ihu.Nan take nakuda
tazonata.kawai sai sarki lafaru ya kura mata ido
yana ta kyalkyala dariyar mugunta kuma
yahana kowa ya taimaka mata.Sai da ta shafe
sa'a biyu tana nakuda sannan ta haifo tsaleliyar
'ya mace a gaban kowa.Da kanta ta yanke cibi ta
goge jinin jikin Jaririyar.Jaririyar ta kama tsala
kuka har ta yunkura zata baiwa jaririyar nono
sai sarki lafaru ya kwace jaririyar daga
hannunta ya cillata cikin wata katuwar kwata
wacce ke cike da ruwa.Nan take jaririyar ta
nutse izuwa can kasan kwatar kuma gashi
ruwan kwatar mahada ne na kogin garin.Koda
matar Narwas taga ya jefa 'yarta cikin wannan
kwata sai ta sulale kasa sumammiya.Da ganin
haka sai sarki lafaru yasa aka dinga yiwa boka
192

TASKARNOVELS.COM.NG
Narwas azaba iri-iri har sai da ya suma sau
bakwai sannan aka kyaleshi.Nan take sarki
lafaru yasa aka yashe komai na gidansa ba'abar
masa ko tsinke ba har dabbobisa sai da aka
kwashesu daga cikin garke,gonakinsa kuwa
yasa aka konesu sannan aka gine wajen aka
rufe ba shiga ba fita.A sannanne sarki lafaru ya
hau dokinsa yai tafiyarsa izuwa birninsa na
kufa.Yakai wannan sarki,tun daga wannan
lokaci baka sake tambayar labarin boka Narwas
ba. Babban kuskuren da kayi shine barin
Narwas a raye.

Bayan wata ukku da haukacewar boka narwas
wani dan uwansa yazo daga wata kasa dabam
yayi masa magani ya warke daga cutar
hauka.Wannan 'ya tasa jaririya da aka jefa cikin
kwata bata mutuba.Ruwa yataso da ita
sama. wani masunci ya tsinceta ya reneta har
izuwa tsawon shekara bakwai a wannan lokaci
tuni Narwas ya kara samun ilmin tsafi ninkin
wanda yake dashi a da sau dubu kuma yayi
bincike yagano 'ya tasa da aka jefa cikin kwata
bata mutu ba tana hannun wannan masunci don
193

TASKARNOVELS.COM.NG
haka sai yaje ya karbo 'yarsa yaci gaba da
renonta kuma ya bata dukkanin sihirin tsafinsa
ya horar da ita bisa tafarkin dazata dauki fansa
akanka.Ba wata bace wannan 'ya tasa face
SHARLIS Budurwar dakayiwa fyade bayan
dakarunka sun kashe mahaifinta da
mahaifiyarta sun kawota fadarka.Dama boka
Narwas yagayawa sharlis cewa alkadarinka
bazai taba karyewaba sai a ranar dakayi mata
fyade daga wannan rana sadaukantakar ka zata
gushe kuma tsafi zai dinga tasiri a jikinka
sakamakon sihirin dake cikin jikinta yafi
naka.Nasan zakayi mamaki bisa yadda akayi
duk nasan wannan al'amari,amma idan kayi
la'akari da cewa nima tsohon bokane mai nacin
bincike da yawan neman karin ilmi bazakayi
mamaki ba.Yakai wannan sarki kayi shiri domin
gani nan tafe izuwa kasarka nan da cikar kwana
arba'in.Lallai idan nazo sai na kwace duk
dukiyar daka mallaka abakacin harajin danayi ta
baka a baya bisa dole kuma sai na kaskantar
dakai kazama bawa mai kula da turken
dokina.Bazan kasheka ba sai dai ka jira ranar da
sharlis zata dauki fansa a kanka bisa abinda
kayiwa mahaifinta.Ina yi maka albishir da cewa
a halin yanzu sharlis na tare da danka data haifa
194

TASKARNOVELS.COM.NG
dan shekara ukku kuma tasa masa suna
shaddad.Nasani cewa tunda kasa aka kai sharlis
bangarenta a cikin gidan sarautarka baka taba
ziyartarta ba kuma baku sake ganin juna
ba.Lallai abinda kake gudun ya faru sai ya
faru,wato sai ka haifi dan da zai gajeka kuma sai
ya fika shuhura a duniya kuma shine zai zamo
babban makiyinka wanda zai dauki fansar
abinda kayiwa kakansa.Lokacinda magatakarda
yazo nan a karatun wasikarsa sai kawai aka ga
sarki lafaru ya bushe da mahaukaciyar
dariya.Cikin shammace ya zare takobinsa ya
sare kan wannan manzo da ya kawo wasikar
Nan take sarki lafaru yasa aka rubuta wasikar
raddi,a cikin wasikar ya karyata duk abinda
sarki nurbas yayi bayani cewar har yanzu
alkadarinsa bai karye ba,sadaukantakarsa na
nan kuma yana jiran isowarsa su gwabza yaki
domin a bambance tsakaninsu a gane wanda
yake karya.Da aka gama rubuta wannan wasika
sai aka hadata tare da gawar manzon daya kawo
wasikar farko a cikin akwati aka tafi dasu izuwa
birnin zaruf.Sa'adda fadawan sarki lafaru da
sauran jama'ar gari suka ji hukuncin da sarki
lafaru ya yanke akan bayanin da wasikar sarki
Nurbas yayi saisuka shiga wasi-wasi.Wasu suka
195

TASKARNOVELS.COM.NG
fara tunanin cewa har yanzu alkadarin sarki
lafaru bai karyeba duk da cewa yanzu ana yin
tsafi kasarsa kuma yana yin rashin lafiya
sabanin da.Dalilinsu na yarda da hakan shine
inda sarki lafaru yasan duk abinda sarki Nurbas
yayi bayani gaskiyane.To da ba zai taba yarda ya
mai da masa da wasikar raddiba. Abinda basu
sani ba shine,sarki lafaru kundunbala kawai
yayi,saboda taurin zuciya da ki fadi ne irin nasa
yaki yarda ya nuna gazawarsa domin kada
talakkawansasu sami damar da zasu ci
mutuncinsa su wulakantashi bisa mulkin
zalincin da ya yi musu.Amma a zahiri yaji a
jikinsa cewa duk irin jarumtakar da yake da ita
a da yanzu bashi da kaso biyu cikin kaso
darinta.Lokacinda fada ta watse sai mutanen
gari suka tafi suna fadin albarkacin bakinsu bisa
abinda ya faru a fada dangane da wasikar sarki
Nurbas ya aiko da ita da kuma wasikar raddi
wacce sarki lafaru ya aika masa da ita. Wannan
abu daya faru sai ya jefa shakku a zuciyar
dakarun yaki na kasar ya zamana cewa basuda
tabbacin cewa zasu sami nasara idan akayi
wannan yaki da birnin zaruf,kuma basu da
tabbacin bazasu samu nasararba.Dole ne su
zuba ido kawai su jira ranar daza ayi wannan
196

TASKARNOVELS.COM.NG
yaki sugani idan har yanzu jarumtakar sarkinsu
na nan tunda shine abin dogaronsu. Al'amarin
sarki lafaru kuwa,bayan fada ta watse sai ya
shiga cikin turakarsa ya zauna yayi tagumi cikin
tsananin bakin ciki,yana tunani da mamaki bisa
yanda al'amura suka sauya masa.

MAZAN JIYA
Littafi na biyu 2
Part M
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey

Al'amarin sarki Laffaru kuwa,bayan fada ta
watse sai yashiga cikin turakarsa yazauna yayi
tagumi cikin tsananin bakin ciki,tunani da
mamaki bisa yadda al 'amurra suka sauya masa
a cikin shekaru ukku kacal.Nan take ya tuno da
irin tsananin jarumtakarsa ta yanda shi kadai
yana iya yakar gari guda ya cisu da yaki,ya tuno
da irin yadda gaba dayan sarakunan dake
197

TASKARNOVELS.COM.NG
kasashen da suke makwabtaka suke tsananin
tsoronsa tare da yin biyayya a gareshi amma
gashi yau an wayi gari an sami daya daga
cikinsu yana aiko masa da zagi dakuma gadarar
ayi yaki.Nan take hawayen takaici ya zubo
masa.Sarki Lafaru yaci gaba da tunani bisa
makasudin faruwar wadannan al 'amurra wato
haduwarsa da sharlis.Nan take bayanin wasikar
sarki Nurbas yasake fado masa a rai cewar a
halin yanzu Sharlis ta haifae danta kuma 'dan
shekara uku a duniya sannan zai zamo abokin
gabarsa ya dauki fansar abinda yayiwa
kakansa.Sarki Lafaru bai san sanda zancensa na
zuci ba ya fito fili ba ya ce, "Ya za a yi 'dan cikina
yazamo abokin gabata?Lallai idan nabari
wannan yaro yagirma nagama tozarta a
duniya.Yanzu ya za a yi na salwantar da
rayuwar sharlis da wannan yaro data haifa
kuma ya za ayi nayi mugun tanadi bisa wannan
yaki dazamuyi da sarki Nurbas nan da kwana
arba 'in na sami nasara akansa don natsare
mutuncina da darajata a idanun jama'ata da
sauran sarakunan kasashen makwaftaka? "
Lokacin da sarki Lafaru yazo nan a tunaninsa sai
hankalinsa ya dugunzuma fiye da komai ya
tabbatar da cewa yana cikin TSAKA MAI WUYA
198

TASKARNOVELS.COM.NG
domin GABANSA TSINI NE,BAYA SIYAKI.Yanzu
dai gashi yana zaune da abokiyar gabarsa cikin
gidansa kuma babu yadda zai yi da ita.Abu na
biyu kuma yana cikin barazanar sarki Nurbas
wacce idan har bai sami mafita ba nan da kwana
arba 'in zai rasa dukiyarsa,mulkinsa da
darajarsa a duniya gaba daya.A iya rayuwar
sarki Lafaru bai taba jin yayi nadama ba bisa
irin rashin imanin dayake ma mutane ba da
mulkin zaluncinsa sai a wannan karon saboda
da inda bai ci zarafin boka Narwas ba da duk
wannan sauyin al 'amurran na rayuwarsa
bazasu faruba.Haka dai sarki Lafaru yaci gaba
da kukan takaici gami da tunani yakasa zaune
ko tsaye cikin tsananin fargaba da tashin
hankali har dare ya raba sosai yakasa barci.Yana
cikin wannan hali ne wata dabara ta fado masa
ya ce da kansa, "Ai masu iya magana sunce ta
inda aka hau tanan ake sauka.Me zai hana naje
wajen Sharlis na yaudareta ta hanyar neman
gafararta bisa abinda nayiwa mahaifinta kuma
na bata dukkanin abinda take bukata na daga
dukiya domin ta taimaka mini na samu nasarar
yaki akan sarki Nurbas inyaso nima daga baya
sai nashiga neman ilmin tsafi a sirrance kafin
dana ya girma nasami sihirin dazan iya ganin
199

TASKARNOVELS.COM.NG
bayansa shi da mahaifiyarsa ".Koda gama aiyana
hakan sai sarki Lafaru ya fice daga cikin
turakarsa ya nufi bangaren da Sharlis take a
cikin gidan sarautar a wannan tsohon dare.Da
isar sarki Lafaru gidan da Sharlis take sai ya iske
kofar gidan a bude wanwar kuma gaba dayan
dakarun dake gadin gidan a kwance suke suna
ta shara barci,al 'amarin da ya matukar bashi
mamaki kenan.Nan take zuciyarsa ta buga da
karfi yaji tsoro ya darsu a ransa amman sai yai
ta maza ya kunna kai izuwa cikin gidan ya wuce
kai tsaye izuwa wani babban falo,da shigarsa
cikin falon sai ya iske gaba daya tagogin falon
guda goma sha biyu a bude suke kuma babu
kowa a cikin falon har kuyangin dake yiwa
Sharlis hidima kuwa.Sarki Lafaru yaci gaba da
lekawa cikin sauran dakunan gidan guda
bakwai amma duk inda ya leka sai yaga wayam
babu mutum a ciki sai kayan sai kayan alatu
kawai da aka tanada a ciki.Cikin matukar
damuwa da sakar zuci ya dawo cikin gidan in
yaso ya bayar da cigiyar Sharlis a tafi nemanta a
cikin gidan sarautar.Wata zuciyar tace dashi
anya kuwa Sharlis ba ta yi hijira ba daga gidan
gaba daya?Ai tunda yanzu tana da karfin sihirin
tsafi babu abinda bazata iya yi ba. Gama aiyana
200

TASKARNOVELS.COM.NG
hakan keda wuya sai yaji wata irin iska mai
karfi ta taso irin wacce ke tsorata mutane
sannan iskar takulle tagogin falon gaba daya
sannan fitilun dake kunne a cikin falon suka
mutu,wani irin duhu yamamaye idanun sarki
Lafaru tayanda ko tafin hannunsa baya iya gani
kuma har a sannan iskar naci gaba da
kadawa,daga can kuma sai yaji an bushe da
wata mahaukaciyar dariya.Duk da cewa sarki
Lafaru yagane muryar dake dariyar hakan bai
hana yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske a
karon farko a rayuwarsa yaji tsoro ya
shigeshi.Daga can sai dariyar ta dauke iskar
dake kadawa ta tsaya cak sannan haske ya
mamaye falon.Sarki Lafaru yayi arba da Sharlis
cikin shigar fararen kaya zaune akan wata
karagar mulki,sarki Lafaru ya daka mata tsawa
ya ce menene na son ki tsoratar dani?Sharlis ta
bushe da dariya sannan tace ina so na nuna
maka nafi karfinka ta ko ina baka da wata
dabara dazaka iya tsallake sharrina.Kada ka
yaudari kanka yakai wannan sarki domin tuni
alkadarinka ya karye kuma har abada
jarumtakarka bazata taba dawowa ba.Na sani
cewa sarki Nurbas ya tunamaka da kisan
wulakancin dakayiwa kakannina kuma kaso ka
201

TASKARNOVELS.COM.NG
hallakani tun ina jaririya amma dayake ina da
nisan kwana a duniya sai da na rayu.Yanzu
gashi lokaci yayi dazan dauki fansa a kanka to
ka sani cewa ramuwar gayya tafi ta gayya
ciwo.Sharlis taci gaba da cewa da sannu zan
dauki wannan fansa a kanka yadda zaka
dandana azababbiyar wahala irin wacce
waninka bai taba sha ba,sannan ka dandana
dacin bakin ciki marar tukewa.A karshe ni da
dana muyi maka kisan mummuke irin wanda
zamu zare maka ruhin numfash a sannu da
sannu.Ina tabbatar maka cewa baka da tudun
tsira,baka da mafaka ko maboya duk irin mugun
tanadin da muka shirya akanka ni da mahaifina
sai ya tabbata a kanka kuma bazaka fara
dandana azabarmu ba sai bayan 'dana ya
girma.Yanzu menene ya kawoka wajena?"Sarki
Lafaru yai ajiyar zuciya sannan yace,"Nazo ne
naga dana da kika haifa?"Koda jin haka sai
Sharlis ta bushe da dariya sannan ta murtuke
fuska sannan ta ce,"Zanyi maka alfarma guda
daya zaka ganshi yanzu sau daya amma bazaka
sake ganinsa ba sai ranar da zai kasheka." Koda
gama fadin haka sai tayi nuni da hannunta
izuwa kofar wani daki sai kofar dakin ta bude
wani kyakkyawan yaro dan shekara uku yafito
202

TASKARNOVELS.COM.NG
daga ciki yana sanye da fararen tufafi na
alhariri,riga da wando kuma yayi damarar
yaki,da wata karamar takobi ta wasan yara
daure a qugunsa.Koda yaron yaga sarki Lafaru a
gabansa sai ya zare wannan takobi tasa ya rugo
da gudu izuwa kan sarki Lafaru ya kawo masa
duka.In ba dan sarki Lafaru ya goce ba da sai ya
kwada masa takobin a fuska. Cikin sauri Sharlis
ta ruke yaron sannan tace "Wannan shine danka
SHADDAD Kuma na kulla gaba a tsakaninku irin
wacce har abada baza ta gushe ba. Kullum sai na
nuna masa fuskarka a madubin tsafi kuma sai
fuskar taka ta rika barazanar cutar dashi, shi
yara a duk sa'adda yaga fuskarka shima sai yayi
kokarin cutar da ita.Da wannan furuci nake
yimaka sallamar karshe,sai nan da wasu
shekaru zamu sake ganawa". Koda gama fadin
haka sai Sharlis da Shaddad suka bace bat
tamkar basu taba wanzuwa ba a cikin falon.A
wannan lokaci ne sarki Lafaru ya fashe da
kukan bakin ciki bisa ganin yanda aka hadashi
gaba da dansa na cikinsa. Cikin matukar sanyin
jiki da tsananin bakin ciki ya fita daga cikin
wannan gida yakoma can turakarsa inda yaci
gaba da tunani da zarya ya rasa abinda zai
fissheshi a rayuwa.A wannan dare bai runtsa ba
203

TASKARNOVELS.COM.NG
har asuba tayi a sannan ne wata dabara ta fado
masa take kuwa barci ya sace shi bai sani ba sai
da gari ya waye rana ta take sannan ya farka.
Cikin hanzari sarki Lafaru ya tashi yaje yayi
wanka sannan yaci ado tamkar babu wani abu
dake damunsa yawuce fada ya zauna akan
karagar mulki aka ci gaba da harkokin mulki
kamar yanda aka saba yana ta nishadi da
walwala abinsa.Lokacin da ya rage baifi rabin
sa'a ba a tashi daga fadar sai sarki Lafaru ya
bingire daga kan karagar mulkin ya fado kasa
yana shure-shure da numfashi sama-sama
kamar zai mutu. Cikin gaggawa Dakaru suka
daukeshi suka kaishi cikin turakarsa aka
kwantar dashi akan gado sannan aka kirawo
likitocinsa suka shiga ayyukansu amma har
tsawon sa'o'i ba a samu nasarar shawo kan
lalurar sarki Lafaru ba.Koda ganin haka sai aka
tura aka kirawo gaba daya sabbin bokayen da
sukayi shuhura a garin domin su bada tasu
gudunmawar.Nan fa bokayen suka rinka shiga
cikin turakar sarki daya bayan daya kowanne
nayin iyakar kokarinsa amma babu nasara. "
Sa'adda boka na tara ya shiga sai ya dubi sarki
Lafaru dakyau sai yayi murmushi sannan ya
dubi gaba dayan hadiman sarki dake cikin
204

TASKARNOVELS.COM.NG
turakar ya ce, "Kowa ya fita ya bashi wuri." Ba
tare da gardamar komai ba kuwa suka fice.
Fitarsu ke da wuya sai bokan ya karanta wasu
dalasimai na tsafi ya tofa a kowacce kusurwa ta
dakin sannan ya dubi sarki ya ce, "Tashi zaune
ya shugabana. Na sani cewa babu wata rashin
lafiya a tare dakai, wanda kake nema yazo, nine
mai share hawayenka.
Koda jin wannan bati sai sai sarki ya mike
daram ya dubi vokan cikin alamun tsoro da
fargaba ya ce Mene ne tabbacinka na cewar
babau wanda zai ji abinda za mu tattauna a
yanzu.
Da jin wannan tambaya sai bokan ya ce saki
ranka kamar tsumma a randa ya shugabana, ka
sani cewa na tsaface wannan daki da muke ciki
yadda ko makiyarka sharlis bata isa taji abinda
zamu tattauna ba. Yanzu kuma duk matsalolin
da kake ciki zan iya warware maka su idan har
kabi umarnin da zan fada maka. Amman fa bisa
sharadi guda daya, sharadin kuwa shine bayan
bukatarka ta biya zaka raba kasarka da kuma
dukiyarka kaso biyu ka bani kaso daya, idan ka
kuskura ka saba alkawari zan lalata dul kariyar

205

TASKARNOVELS.COM.NG
dana baka, abokiyar gabarka da danta su samu
nasara a kanka.
Sa'adda boka ya zo nan a zancensa sai hankalin
sarki lafaru ya tashi domin yanzu dai ga mafita
da waraka sun zo masa, to amman mene ne
amfanin warakar tunda zai raba kasarsa da
dukiyarsa biyu ya bada rabi, ai idan hakan ta
faru daukakarsa ta ragu a idon sauran sarakai.
Amman daya tuna cewa idan fa bai yi hakan ba
karshenta ne fa ya rasa komai. Lokacin da sarki
lafaru ya gama wannan nazarin a cikin
zuciyarsa, sai ya dubi bokan cikin nutsuwa ya ce
Wai shin da farko ma wane ne kai? Shin yanzu
kana nufin ka ce zaka iya dawo mani da
sadaukantaka ta wacce sharlis ta rabani da ita?
Kuma zaka iya bani nasara bisa yakin da zanyi
da sarki Narwas nan da cikar kwanaki arba'in,
kuma ka kareni daga sharrin sharlis da danta na
yanzu da kuma shekarun gaba masu zuwa.
Koda bokan ya ji wandan nan tambayoyi sai ya
bushe da dariya ya ce Ko shakka babu duk zan
iya yin irin wadannan abubuwa kuma ni
kadaine a nahiyar nan zan iya, musamman idan
ka yi la'akari da yadda duk nasan matsalolinka,
206

TASKARNOVELS.COM.NG
da kuma yadda nasan sirrin abokiyar gabarka
sharlis wacce ke shirin daukar mummunar
fansa a kanka. Da farko dai ni suna na boka
Muzaffar Bn Munzur, kuma ni haifaffen birnin
Kisra ne, amman bisa wata bukata tawa na bar
mahaifata na bazama duniya, yau shekara
arba'in kenan da barina gida, ban sake komawa
ba kuma har yanzu bukatata bata biya ba, sai
idan na biya maka taka bukatar sannan kai
kuma ka cika mani nawa alkawarin da ka
daukar mani, kada kayi tsammanin cewa mulki
da dukiyar da zaka bani sune bukatar tawa, ko
kadan ba su bane, bukatar tawa wani babban
sirri ne wanda duk wanda ya same shi sai ya fi
kowa da komai matsayi a duniya, a iya
bincikena na gano cewa lallai sai na mulki rabin
kasarka, sannan na mallaki rabin dukiyarka, to a
lokacin ne zan kai izuwa wannan matsayi.
Yanzu sai ka saurareni da kyau dan kaji
umarnin da zan baka idan har kana son karfin
damtsenka ya dawo kafi karfin wulakancin da
sharlis da kuma danta zasu yi maka a nan gaba,
nan da cikar shekaru goma sha biyar.
Ya kai wannan sarki da farko dai ina son ka sani
cewa idan har kana son ka karya asirin da
sharlis ta yi maka, har karfin damtsenka ya
207

TASKARNOVELS.COM.NG
dawo kuma ya zamana cewar tsafi b zai sake
tasiri a jikinka ba, sai ka auri budurwar data fi
sharlis kyau a cikin watanni biyu masu zuwa
nan gaba, ita kuwa wannan budurwa duk
duniya a halin yanzu babu wata ya mace data
kaita kyau ana kiranta da suna Ramlatus siyam.
Ramlatus siyam ta kasance yar sarki Hindu na
yanzu wato sarki Nasmir Bn Hayat wabda babu
wani matsafi da ya fishi karfin sihiri a duniya,
kuma babu wani sarki da ya fishi yawan
zakwakuran mayaka wadanda suka siyar da
rayuwarsu dan bauta masa, kai bama
mayakansa ba hatta mutanen kasrasa suna
bauta masa ne, saboda tsananin tsoronsa da
suke ji.
A duniya babu abinda sarki Nasmir yake so
sama da yarsa gimbiya Ramlatus siyam, sabida
haka ne ma ya bata tsaro na musamman a gidan
sarautarsa da karfin sihiri, sannan kuma ya
zuba dakaru kimanin miliyan dubu daya na
aljanu suna shawagi a saman gidan nata dare da
rana dan tabbar da tsaro. A kasan gidan kuwa
ya zuba dakaru miliyan dubu daya na biladama
suna gadi, tunda aka haifeta aka sata a cikin
wannan gida, wanda girmansa ya kai na wannan
208

TASKARNOVELS.COM.NG
birni na Kufa. Gabadaya ita da mahaifiyarta da
barori masu yi masu hidima babu wanda ya
kara shiga gidan ko ya fita face shi kanshi sarki
Nazmir. Babu yadda sarki Nashmir ya amince ya
baka yarshi gimbiya Ramlatus siyam domin ka
aura, sai dai mu sato ta bai sani ba. Sato gimbiya
Ramlatus siyam kuwa daidai yake da mutum
yayi kundubala a cikin
End Ads