x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - MAZAN JIYA 2

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 55701 words

Category: Romance Story +18

Views 203

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ya zauna nesa kadan da ita yana daridari domin a iya shekarun daya kwashe yana yi
mata bauta yauce ranar farko data tab
umartarshi daya zauna kusa da ita.
Koda taga yadda yake dari+dari sai ta bushe da
dariya ta cw haba ya kai abokina mene ne kuma
haka naga kana rawar jiki, bafa wani abu zanyi
maka ba, shawara kawai nake so ka bani, domin
babu wani mahaluki dana aminta da shi sama
da kai.

227

TASKARNOVELS.COM.NG
Sa'adda da aljani Maraful Dauwas yaji wannan
batu sai hankalinsa ya kwanta har ya saki
murmushi tare da cewa To ina sauraronki fadi
bayaninki naji kuma zanyi iya kokarina wajen
baki shawarar da zata fissheki.
Gimbiya Rashmin tayi gyaran murya sannan ta
fara da cewa Ya kai abokina kuma amintaccena,
kayi sani cewa ayau din nan sarki ya kirani
kuma yace na fidda gwani daga cikin masoyana,
ni kuwa sai nace da shi ya za a yi na fidda gwani
alhalin bantaba yin soyayya ko da dayansu ba,
kuma bnsan ma meye soyayyar ba. Koda jin
haka sai yace dani naje na nemi wnada na
aminta da shi ya bani shawara akan irin mijin
daya kamata na aura, kuma yayi mani bayanin
mece ce soyayya domin na fahimta sosai.
Lokacin da Gimbiya Rashmin ta zo nan a
zancenta sai Aljani Maraful Dauwas yayi
murmushi sannan ya ce aiko kinyi tambaya
gareni mai sauki kuma mai saukin bayani, da
farko dai ina so kisan cewa ita soyayya wata
abace wacce ake fara yinta bisa gamon jini,
amince da kuma yarda da juna, daga nan sai
sabo gami da shakuwa su sa tayi karfi ainun a
cikin zuciyar masoya, har takai cewa suna son
228

TASKARNOVELS.COM.NG
kasancewa a tare ko yaushe. Idan soyayyar tasu
ta kara karfi sai suji cewa duk wuya d tsanani bq
zasu iya rabuwa da juna ba, kuma basu da burin
daya wuce su zama abokan rayuwa ga junansu,
wannan shine abinda ake kira soyayya.
Shawarar da zan baki dangane da irin mijin da
ya kamata ki aura shine kada ki duba
matsayinsa, mulkinaa ko kuma daukakarsa, kiyi
duba izuwa halaye na gari, shi din mai gaskiya
ne, shin idan aka bashi b zai ci ba, shin zai iya
kare mutuncinki gami da lafiyarki, kuma zai iya
sallama rayuwarsa domin kare ta ki, shin idan
yayi alkawari yana cikawa, tsawon wane lokaci
kuke tare sannan ya girman shakuwarku ta ke,
yau udan babu mahaifinki zai ci gaba da
darajtaki gami da ririta ki, waye zai iya jibantar
alamarinki duk sa'ar da wata masifa ta fado
maki ba tre da yayi shakkar komai ba.
Wadannan sune abubuwan da ya kamata kiyi
amfani da su wajen zaba wa kanki mijin da zai
dace da ke.
Sa'adda da Maraful Dauwas ya zo nan a
zancensa sai kawai yaga hawaye ya zubo daga
idanun Gimbiya Rashmin, al'amarin da yayi
matukar dugunzuma hankalinsa kenan ya
razana kuma ya sakko kasa daga kan gadon, ya
229

TASKARNOVELS.COM.NG
tsugunna bisa gwiywoyinsa yana mai cewa ki
gafarceni ya shuga ta idan har bayanin da nayi
maki ya bata maki rai.
Koda jin haka sai Rashmin ta share hawayebta
sannan itama ta mike tsaye ta kama hannayen
aljani Maraful Dauwas a karo na farko a
rayuwarsu ta tadashi tsaye ta ce Ya kai
amintaccena ka yi sani cewa ba komai bane yasa
kaga wannan hawaye nawa ba face sai a yaune
na san cewa akwai magani a gonar yaro, amman
rashin sani ya hanashi amfani da maganin.
Lokacin da kake ta yi mani wannan jawabin sai
na fahimci cewar babu wani mahaluki da yake
da wadannan abubuwa daka lissafo wanda na
sanshi a rayuwata face kai, kqine kadai
mahalukin da nayi sabo da shi, kuma na shaku
da shi ainun, tun daga kuruciyata kawo izuwa
girmana, kaine kadai wanda nasan cewa zai iya
sallama rayuwarsa domin tawa sabida ka
tseratar da rayuwata sau ba adadi, kainne kadai
nasan cewa na bashi amanata amman bai ci ba,
kaine wanda baka taba karya mani alkawari ba,
kuma kaine kadai nasan cewa ko babu ran
mahaifina zaka ci gaba da darajta ni, ashe kuma
lallai kaine namijin d ya dace na aura dan haka
sunanka zan ambata a wajen mahaifina.
230

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda gimbiya Rashmin ta zo nan a zancenta sai
Maraful Dauwas ya kamu da tsanankn tsoro
kuma ya fisge hannunsa daga cikin nasa da
sauri, a sannan ne shima hawaye ya zubo daga
cikin idonsa kuma ya dan ja baya daga gareta ya
ce "Ya shugabata ina kika taba ganin bawa ya
auri yar sarkinsa, har abada ruwa ba sa'an
kwando bane, ina mai rokonki da ki taimakeni
kuna ki janye wannan batu daga zuciyarki gami
da bakinki, ki tuna cewa mahaifinki yana da zafi,
idan har kika furta masa wannan al'amari zna
iya fuskantar fushinsa, kuma allura zata tono
garma, wata kila ma sanadin rabuwarmu kenan.
Koda jin haka sai gimbiya Rashmin ta rugo
izuwa kan Aljan Maraful Dauwas ta rungumeshi,
sannan ta fashevda kuka tana mai cewa aiko
idan aka rabani da kai duk wanda zai aureni sai
dai ya kwanta da gawata amman ba ni ba.
Kafin Maraful Dauwas yace wani abu sai kawai
suka ga an turo kofar dakin da suke ciki an
shigo, ba wani bane ya shiga ba face sarki da
mahaifiyar Gimbiya Rashmin sunata hira gami
da dariya, koda suka yi arba da Gimbiya
Rashmin tana rungume da aljani Maraful
Dauwas sannan duk su biyu suna hawaye, sai
231

TASKARNOVELS.COM.NG
sarki ya kwarara uban ihu cikin tsananin fushi,
nan take dakarinsa suka rugu da gudubizuwa
inda suka ji ihun sarki, da zuwansu sai sarki ya
ce dda su su kama Maraful Dauwas uyita
dukansa har sai ya suma sannan su kulleshi.
Ai kuwa nan take wadannan dakarubsuka cika
aikin sarki, a lokcin da Gimbiya Rashmin ta
rinka ihuwa gami da kururuwa tana kokarin ta
kifa kansa dan su daina dukansa, amman sai
sarki ya riketa gam da hannunsa biyu, a gaban
idonta aka sumar da masoyinta aljani Maraful
Dauwas aka kuma tafi da shi.
Nan take itama Gimbiya Rashmin ta sulale kasa
sumammmiya.
Cikin firgicewa da dimaucewa sarki da matarsa
suka shiga yi mata fifita, da kyar da shidin goshi
suka samu ta farfado. Daga wannan rana
Gimbiya Rashmin ta kwanta cuta ya zamana
cewa kullum tana kwance kuma bakinta baya
ambaton komai face bawanta kuma masoyinta
aljani Maraful Dauwas. Hakan bata sa sarki yayi
umarni akan a saki Aljani Maraful Dauwas daga
kurku ba, kawai ma sai ya mayarvda hankalinsa
akan nema wa yarsa Rashmin magani, har sai da
232

TASKARNOVELS.COM.NG
takai cewa an hada da karfin sihirin tsafi wajen
juyar da kwakwalwar gimbiya Rashmin akan ta
manta da bawa Maraful Dauwas sannan aka
samo kanta ta samu lafiya.
Shiko bawa Maraful Dauwas a kullum sai an
gana masa azaba kala dubu a cikin wannan
kurkukun, ya zamana cewa ya lallace kuma ya
rame sanna ya fita daga cikin hayyacinsa, komai
rashin imani da tausayinka idan ka dubi aljani
Maraful Dauwas a wannan lokaci ole ne ka
zubar masa da hawaye.
A ranar da aka daura auren Gimbiya Rashmin
da dan sarkin aljanu na birnin Misra ne, to a
ranar ne wannan asiri da aka yi mata na juyar
da ?wa?walwarta ya karye, kuma a daidai
lokacin da ango ya shigo dakin amaryarsa, koda
amarya ta dago da kai taga ba Maraful Dauwas
bane sai ta kwala uban ihu, kuma ta dauki wata
wuka dake ajiye a bisa tebur bisa faratin yayan
itatuwa ta soka wa kanta a ciki, nan take ta
sulale kasa matacciya.
Nan fa ango ya dimauce har bai san sa'adda ya
fice waje da gudu ba.

233

TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da labari ya iski sarki cewa ai Gimbiya
Rashmin ta kasshe kanta sai ya kmau da
tsananin bakin ciki, nan take ya hadiyi zuciya
shima ya mutu.
Shiko aljani Maraful Dauwas sai da ya shekara
dari biyu a cikin wannan kurkukun a tsare, ba a
kuma sake shi ba sai bayan da mahaifiyar
Gimbiya Rashmin ta mutu, aka nada sabon sarki
a garin.
Koda aka saki Aljani Maraful Dauwas daga
kurkuku aai yaji gabadaya ya tsani kansa kuma
ya tsani duniyar, dama tun yana kurkukun
labari ya riske shi cewa Gimbiya Rashmin ta
kashe kanta, dan haka shim aai ya fara kokarin
kashe kan nasa, ammab sai dakarun dake
tsaronsa suka sa ido soaai a kansa dare da rana
bisa dole ya hakura da batun kashe kansa.
Lokacin da Aljani Maraful Dauwas ya fice daga
kurkukun kuma yajinya tsani duniya da duk
abinda ke cikinta sai ya yanke shawarar ya kai
kansa inda b zai sake ganin mutane ko aljanu ba,
domin ya karasa sauran rayuwarsa ta duniya,
bisa wannan dalili ne ya tafi can karshen birnin
sin ya shiga cikin kogon darul ikisina ya rufe
234

TASKARNOVELS.COM.NG
kansa a ciki har zuwa tsawon shekaru dubu
biyu da dari biyu bai fito ba balle yaga koda
hasken rana, dama can shi kogon darul ikisina
kogo ne da yayi kaurin suna a duniya kuma
babu mai iya shigarsa face wand ya san wasu
dalasuman sihiri wadanda na musamman ne
guda bakwai, sai mutum ya karanta wadannan
dalasuman n tsafi a fili sannan kofar kogon zata
bude, idan kuwa yayi kuskure a wajen karanta
dalasiman sau daya to shikenan har abada kofar
ba zata bude ba, koda kuwa zai sake karantawa
sau dubu.
Shi kansa Aljani Maraful Dauwas ya gaji wannan
dalasuman ne a wajen kakansa na dari da
ashirin da biyu, kuma ba a rubuce suke ba a
cikin kundi ko littafi, akan cinyarsa ta hagu aka
rubuta su da wata wuka ta sihiri yadda har
abada babu wani abu da zai iya goge su koda
kuwa wuta ce.
Lokacin da boka Muzafar Ibn Mauzar ya zo nan
a labarinsa sai sarki Lafaru ya vika da tsananin
mamaki kuma hankalinsa ya dugunzuma
sadoda tunanin gagarumin aikin dake gabansa
da daharinsa gamj da wahalar dake cikinsa yafi
dukkanin dadin da zai biyo baya. Bayan sarki
235

TASKARNOVELS.COM.NG
Lafaru yayi dan nazari sai ya dubi boka Muzafar
cikin nutsuwa ya ce Ya kai wannan babban
bako, ina da tambayoyi kwarara a gareka;
tambaya ta farko ita ce shin kaima kana da
wadannan dalasumai na tsafi ne guda bakwai
wadanda za'a karantasu kofar kogon darul
ikisina ta bude ne, tambaya ta biyu ta yaya kake
ganin cewa aljanu Maraful Dauwas zai amince
ya fito daga cikin kogon darul ikisina har yaje
fadar sarki Nashmir ya sato mana gimbiya
Ramlatus siyam alhalin ya tsani duniya da duk
abinda ke cikinta, tambaya ta uku ita ce me yasa
aljani Maraful Dauwas baiyi tawaye ba a lokacin
da mahaifin gimbiya Rashmin yasa aka yi masa
dukan kawo wuka har aka kaishi kurkuku,
bayan aljanin ya kasance gawurtaccen jarumi
mai tarwatsa maza a filin daga.
Sa'adda boka Muzafar ya ji wadannan
tambayoyi guda uku sai ya bushw da dariya
sannan ya ce Ya kai wannan sarki k yi sani cewa
makaho baya cewa ayi wasan jifa face ya
tabbatar da cewa ya taka hoge, kamar yadda
aljani Maraful Dauwas ya gaji wadannan
dalasiman tsafin haka nima na gajesu a wajen
kakana na uku, kuma duk duniya mutum hudu
ne masu wannan dalasuman tsafin sai kuma
236

TASKARNOVELS.COM.NG
aljanu uku, a cikin mutane saura mutum biyu jal
a raye daga nk sai sarkin birnin Hindu wato
mahaifin gimbiya Ramlatus siyam, a cikin aljanu
kuwa saura aljani Maraful Dauwas kawai.
Dangane da tambaya ta biyu kuwa hakika babu
kalaman da zamu fadawa aljani Maraful Dauwas
ya amince yayi mana wannan aiki domin dukiya
ko mulki basa gabansa, abu daya ne zamu je
masa da shi idan muka yi sa'a ya amince, kayi
sani cewa a yamma da birnin Misra bayan
mutuwar Gimbiya Rashmin da shekaru hamsin
an haifi wata kyakkyawar budurwa mai
tsananin kama da gimbiya Rashmin tamkar an
tsaga kara harma ta fi Rashmin kyawun sura,
kai inda za a hada Rashmin da budurwarnan
mai suna Rahila da sai mutum yayi tsammanin
cewa tagwaye ne, zamu dauki Rahila mu tafi da
ita can cikin kogon darul ikisina domin aljani
Maraful Dauwas ya ganta da idanunsa, tabbas
idan yayi arba da ita zai cika da mamaki wata
kila ma yayi tunanin ko fatalwal masoyiyarsa ce
Rashmin, nan take sai muyi masa al?awari cewa
zamu bashi ita ya aura amman bisa sharadin zai
biya mana bukatarmu, ko shakka bana yi nasan
aljani Maraful Dauwas zai bari wannan tayi ya
wuce shi ba, game da tambayarka ta uku kuwa
237

TASKARNOVELS.COM.NG
dalilin da yasa aljani Maraful Dauwas bai yi wa
sarki tawaye ba shine akwai alkawari mai karfi
da mahaifinsa ya dauka kan cewa har abada
shida zuri'arsa baza su taba yi wa sarkk tawaye
daga yin bauta ba, face shi da kansa ya daina
bukatarsu. Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa
yanzu take ba tare da bata wani lokaci ba zan
daukeka mu aiwatar da wannan gagarumin
aikin da ke gabanmu, amman kafin mu tafi sai
na kirkiri mai irin kamanninka sak kuma na
kwantar da shi bisa gadonka, ya cigaba da
rashin lafiya hadimnaka na ci gabada yi masa
hidima har izuwa lokacin da zamu dawo saboda
mu bagarar da matarka sharlis, domin idan taga
baka nan na san tabbas sai ta yi kyakkyawan
shiri, kuma muddin ta gano zata iya tarwatsa
shirin namu dan dukkanin wani sihirin tsafi da
nake takama da shi itama tana da shi, da abu
daya kacal na fita, wannan abu ba komai bane
face wayo gami da hangen nesa, kasan ance duk
wanda ya rigaka kwana dole ne ya rigaka tashi.
Koda jin wadannan batutuwa sai sarki Lafaru ya
dubi bboka Muzafar cikin tsananin farin ciki ya
ce ai nima wayo ne ya ceceni yanzu nayi kamar
bani da lafiya har nazo na sameka.
238

TASKARNOVELS.COM.NG
Muzafar yayi murmushi yace ai koda baka yi
wannan wayo ba, lallai sai na zo gareka a
sirrance tunda nayi bincike naga amfaninka a
cikar burin rayuwata.
Sarki Lafaru ya yi murmushi sannan ya ce da
boka Muzafar na rokeka daka gaggauta dauke ni
daga cikin wannan gida domin mu tafi biyan
bukatar abinda ke gabanmu, ahalin yanzu ji
nake kamar akan kaya nake.
Kafin sarki Lafaru ya gama rufe bakinsa tuni
boka Muzafar ya shafi jikinsa da hannunsa na
hagu, kawai sai yaga Husaininsa ya fito daga
cikin jikinsa, hatta kayan da ke jikin Husaini iri
daya ne babu banbanci ko kadan, kawai sai
Husaini ya je ya kwanta akan gadon sarki, boka
Muzafar ya sake dafa kafadar Sarki Lafaru nan
take suka bace gaba dayansu, basu bayyana a ko
ina ba sai a birnin Kufa a gaban wani narkeken
aljani mai matukar girma gami da ban tsoro,
kuma muninsa ya wuce ayi misali idan mutum
ya kalli fuskar aljanin zai iya haukacewa nan
take, amman da yake sarki Lafaru ya saba gamo
da ire-irensu a baya kafin alkadarinsa ya karye
sai bai tsorata ba ainun.

239

TASKARNOVELS.COM.NG
Ba tare da bata lokaci ba boka Muzafar ya kama
hannun Sarki lafaru ya jashi suka hau kan
wannan narkeken aljani sannan Muzafar ya ce
Ya kai Marhabul Zaurus maza ka kaimu can
yammacin birnin Damaskas a ajiye mu a garin
su kyakkyawa Rahila.
Da jin wannan umarni sai Aljani Marhabul
Zaurus yayi murmushi mai kama da gurnanin
zaki ya ce an gama ya shugabana, nan take
nakeken aljanin ya bude fukafukansa ya tashi
tre da lulawa cikin gajimare yana mai keta gizagizai tamkar tauraruwa mai wutsiya
Tafiyar da suka yi bata kai ta rabin sa'a ba suka
iso yammacin birnin Damaskas, aljani Marhabul
Zaurus ya sakko kasa ya dira bisa turba a bakin
kofar wani babban birni wanda suka iske kofar
a rufe, dakarun yaki kimanin su dubu suna
tsaitsaye a bakin kofar rike da muggan makamai
suna gadi.
Ba tare da boka Muzafar ya ce da sarki Lafaru
wani abu ba sai kawai ya sauka daga kan aljani
Marhabul Zaurus ya nufi wajen masu gadin
kofar kai tsaye. Koda ganin haka sai Sarki Lafaru
ya sauko da sauri ya bishi a baya cikin sauri240

TASKARNOVELS.COM.NG
sauri gudu-gudu har ya tarar da hi suka kasara
wajen masu gadin kofar a tare. Da zuwansu sai
Boka Muzafar ya dubi shugaban dakarun ya
daka mashi tsawa sannan ya ce, Ya kai wannan
bawan sarki maza ka ruga wajen sarkinku ka
fada masa cewa ni boka Muzafar ibn Mauzur
gani na dura a kasarsa kuma ina son ya bani
aron yarsa Rahila zan dawo da ita bayan
kwanaki sittin da biyar.
Koda jin wannan batu sai gabadaya dakarun
suka kyalkkyale da dariya, haka suka yita yi
kamar ba zasu daina ba, daga can sai shugaban
nasu ya dubi boka Muzafar ya ce Kai ko wane
irin mahaukaci ne, kuma a ina ka taba ganin uba
ya bada aron yarsa budurwa balle kyakkyawa
kamar Rahila, wai shin zautuwa k yi ko kuma
basirarka ce ta toshe?
Koda jin haka sai zuciyar boka Muzafar ta kama
tafarfasa tamkar zata kone daga can kuma sai ya
daga hannu ya sharara wa shugaban dakarun
mari, sabida zafin marin sai da yayi katantanwa
sau uku kuma yaga taurarin wuya. Boka
Muzafar ya dubeahi a fusace tare da cewa
ubanka ne ya zautu amman ba ni ba, kuma mai
tosashiyar ?wa?walwa...
241

TASKARNOVELS.COM.NG
Kafin Muzafar ya gama rufe bakinsa tuni
shugaban dakarun da sauran yaransa sun zare
makamansu tare da yi masa kawanya, koda
ganin haka sai shima boka Muzafar ya zare nasa
takobin suka kacame da azababben yaki, shi
kuwa sarki Lafaru sai ya buta a bayan wata
bishiya yana mai leken abinda ke faruwa.
Kaico! Hakika maza sun fadi, lokacin da Sarki
Lafaru aga ana wannan gumurzu tsakanin boka
Muzafar da dakarun nan sai yaga boka Muzafar
ya zame masu alakakai, amman shi gashi a labe
ya kasa kai masa dauki sai hawayen takaici ya
zubo masa, saboda tunow da cewa da fa shi
Gwarzon Sadauki ne mai tarwatsa gungun maza
kuma komai yawansu a filin daga, amman yanzu
ko mutum daya ba zai iya gwabza yaki da shi ba,
domin yana jin rashin karfi a jikin nasa yadda ko
takobi ba zai iya dagawa ba.
Lokacin da boka Muzafar yaga wannan dakarun
yakin su dubu ya zame masu alakakai yana ta
kashesu tamkar guguwar annoba ce ta sauka a
wannan birni, su kuma sun kasa koda lakutar
jikinsa, sai ya raina jarumtarsu, dan haka sai ya
maida takobinsa cikin kufe ya ci gaba da
gumurzu da su babu makami a hannunsa. Duk
242

TASKARNOVELS.COM.NG
wanda ya kawo masa sara ko suka sai ya kauce
ya gabza masa naushi daya take zai baje a kasa
sumamme.
Koda sarki Lafaru ya hango irin wannan
tsananin gagarumar jarumtaka da boka Muzafar
ke yi, sai ya cika da tsananin mamaki domin ko
shi kansa sa'ar da yake da karfin damatsensa
bai yi tsammanin ya taba jarumtakar da ta kai
irin wannan ba, kuma a cikin tsananin zafin
nama kamar haka.
Cikin abinda bai wuce dakika hamshin ba, boka
Muzafar ya bazar da dukkanin dakarun su dubu
a kasa, daga sumammu sai karyayyu babu
wanda zai iya mikewa tsaye a cikinsu.
Koda ganin haka sai boka Muzafar yasa kafarsa
ta dama da doki kofar shiga garin wacce aka yita
da zallar bakin karfe, mulmulalle mai tsawon
kamu dari gami da fadin kamu saba'in. Nan take
kofar ta jijjege daga jikin katangar ta fadi kasa
rikica! Karar katuwar kofar ce ta cika garin
gabadaya, ta dugunzuma hankalin dukkan
mutanen garin har suka fara tsammanin cewa
rundunar yaki ce ta kawo masu harin sumame.

243

TASKARNOVELS.COM.NG
Nan da nan Sarkin garin da kuma hadimai suka
debo makan yki sama da su dubu dari uku suka
yi hawa Bisa dawakan tare da sukwanosu zuwa
bakin kofar birnin domin su tari Abokan gaba.
Da isowar sarki da dakarunsa sai suka cika da
tsananin mamaki da suka ga mutum biyu jal sun
tunkaresu.
Sarkinsu ya dubi boka Muzafar da sarki Lafaru
ya daka masu tsawa ya ce Ina sauran dakarun
naku suka buya, shin kunzo da wani sabon salon
yaki ne da kuke ganin zaku iya cutar da mu da
shi ne?
Koda jin wannan tambaya sai boka Muzafar ya
dubi sarki sannan ya ce mu ba yaki ne ya
kawomu ba, ba kuma mu biyu muka zo ba,
wadannan masu gadi naku da kuke gani a kasa
tamkar tsommokara taurin kai suka yi mana,
suka ki isar da sakonmu a gareka, bisa wannan
dalili ne na fusata n banke kofar wannan birni
naku na shigo. B wani abu ne ya kawo mu ba
face mun so ka bamu aron yarka dan tayi mana
wani aiki na kwana sittin da biyar kacal, ina mai
tabbatar maka da cewa zamu dawo maka da ita

244

TASKARNOVELS.COM.NG
cikin aminci da salama kamar yadda muka
karbeta daga hannunka.
Lokacin da boka Muzafar ya zo nan a zancensa
sai sarki da dukkanin dakurunsa suka bushe da
dariya, kamar yadda masu gadin
End Ads