x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 13 - MAZAN JIYA 2

  • 36001 words
  • 39000 words
  • Out of 55701 words

Category: Romance Story +18

Views 204

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
rami mai zurfin kafa
dubu, ya kai wannan sarki idan har ka samo
sa'ar auran gimbiya Ramlatus siyam to a ranar
da ka kwanta da uta a wannan lokaci ne sihirin
daya shiga jikinka zai karye, sannan karfin
damtsenka zai dawo. Ka sani cewa koda
karfinka ya dawo ba zaka iya yiwa sharlis da
danta komai ba, kuma wannan da data haifa sai
ya girma ya zama gawurtaccen sadauki da babu
kamarsa a duniya karfin damtse dana sihiri,
kuma babu wanda zai iya tunkararsa har ya
hanashi halaka ka, face yar da zaka haifa da
gimbiya Ramlatus siyam nan da shekara daya
idan har ka samu nasarar auranta a cikin
watanni biyu masu zuwa. Hanya daya zamu bi
mu samu haduwa da gimbiya Ramlatus siyam
kafin cikar watanni biyu masu zuwa, hanyar
kuwa ita ce dole ne muyi shiri ni da kai mu tafi
kogon darul iksina dake can karshen birnin sin
209

TASKARNOVELS.COM.NG
domin mu sadu da aljani Maruful dawwas,
domin shine kadai aljanin da zai iya sato mana
gimbiya Ramlatus siyam aga can birnin Hindu,
kuma ya ganota gaemu cikin kwanaki ashirin da
biyar kacal! Amman ka sani cewa kafin mu isa
can kogon darul ikisina daga nan sai munyi
tafiyar kwanaki talatin da uku, kaga kenan idan
ka hada da kwanaki ashirin da biyar da aljani
Maruful dawwas zai yi ya kawo mana gimbiya
Ramlatus siyam akan lokaci, kuma idan har aka
gota kwanaki sittin koda yini daya ne to fa
aurenka da ita bazai taba yiwuwa ba, ka sani
cewa akwai tashin hankali gami da bal'ai iri-iri
akan dazuzzukan da zamu ketare kafin mu isa
kogon darul ikisina, inda aljani maraful dawwas,
ina mai tabbatar maka da cewa mu biyu kacal
face da taimakon asu manyan jarumai guda
shida wadanda suma basu da wani buri face
suje kogon darul ikisina omin debe tsumin
wannan maganin da zai warkar da masoyansu
daga cutuka daban daban. Dukkanin wadannan
jarumai sun kasa zuwa wannan kogo na darul
ikisina saboda dole sai da ni dinnna sannan zasu
iya zuwa, kasancewar ni kadaine nasan hanyar
da za a bi aje wannan kogo na darul ikisina anan
cikin duniya, ni kuma nayi al?awarin cewa
210

TASKARNOVELS.COM.NG
bazan jeba duk da cewa idan naje zan samu
damar cika babban burina na duniya, sai a
yanzu da matsalarka ta taso sannan na san cewa
burina zai cika, idan har na taimakeka
matsalarka ta kau kuma ka cika alkawarin daka
daukar mani, wadannan jarumai abokan
tafiyarmu duk suna zaune ne a kasashe daban
daban, amman duk zan iya kaimu wurinsu cikin
kwana daya bisa taimakon wani babban
hadimina mai suna Shaibatul Barbus. A halin
yanzu duk duniya babu wani aljani da ya ke da
gudun Shaibatul Barbus da zafin namansa face
aljani maraful dawwas, har ma shi ninka
Shaibatul Barbus sau goma a komai, shine
dalilin daya sa zai iya shiga fadar sarki Nashmir
ya sato gimbiya Ramlatus siyam ba tare da ya
halaka ba.
Jarumi na farko abokin tafiyarmu shine Sadauki
Haiman wanda ke zaune a birnin Misra, ahalin
yanzu duk duniya abu jarumin da ya kai Haiman
iya sarrafa takobi, domin idan yana rike da
takobinsa yana iya sare kawunan mutane ko
aljanu guda dubu a cikin dakika biyar, dan haka
komai yawan dandazon dabaru in har ya
shigesu sai ya trwatsa su, ka yi sani cewa a cikin
daji na farko da zmau riska kafin mu isa kogon
211

TASKARNOVELS.COM.NG
darul ikisina akwai wadansu mugayen maridai
wadanda adadinsu ya kai miliyan dubu,
wadannan maridai saboda tsananin tsawonsu
idan mutum ya daga kai ya kallesu sai yaga
kamar sun hade d sararin samaniya. Komai
yawan runduna ta aljanu idan tazo giftawa ta
saman wadannan maridai sai sun cafcakosu sun
ciccinyesu, babu wanda zai iya tarwatsa
wadannan maridai har mu samu ratsawa ta
cikinsu mu wuce ta cikinsu face Sadauki
Haiman, amman fa wannan ba yana nufin cewa
ya zama wajibi dukkaninmu mu tsallake sharrin
maridan, komai zai iya faruwa ga dayanmu,
domin tsafi da karfin jarumtaka ba zasu cecemu
ba face sa'a da tsananin rabo.

Zan ci gaba.

Da fatan mun wuni cikin koshin lafiya, sannan
duk wanda yake son complete zai iya tuntubata
ta wannan number 08138873799 kira ko
whatsap
212

TASKARNOVELS.COM.NG

Fiye da shekaru dubu baya mutane da aljanu
suka daina ratsa wannan daji, Sadauki Haiman
na da wata kyakkyawar mata guda daya wacce
aljanu suka shafeta ta makance, babu irin
neman magani da bai yi ba domin idanunta su
bude amman abu ya gagara, sai daga baya ya
gano dole sai na rakashi izuwa kogon darul
ikisina ya debo wannan tsumin maganin ya
baiwa matarsa ta wanke fiskarta sannan zata
warke. Wani abun mamaki shine Lumaira matar
Sadauki Haiman tun tana jaririya wannan lalura
ta makanta ta sameta, dan haka bata taba ganin
kalar iyyaenta, danginta da mijinta ba, kuma ba
baiwa Haiman auren Lumaira ba sai bisa
alkawarin komai dadewa sai ya nema mata
magani. Sau bakwai sadauki Haiman yana zuwa
wajena akan batun tafiya kogon darul ikisina
sannan yana mani alkawarin zai biya dinare
dubu, amman sai nake fada mashi lokacin
tafiyarmu bai yi ba, lallai idan lokacin tafiyarmu
yayi zan nemeahi da kaina.
213

TASKARNOVELS.COM.NG
Abikin tafiyarmu na biyu ba kowa bane face
Jaruma Shadira ta birnin Baitul Halwal, a halin
yanzu duk duniya bau wanda ya fi jaruma
Shadira iya harbi d kibiya, domin tana iya harba
kibiyoyi guda dari a cikin dakika Ashirin, tana
da wani irin kwari na musamman mai harba
kibiyoyi Ashirin a lokaci guda. Tsananin zafin
naman jaruma Shadira yafi gaban tunani, acikin
daji na biyi da zamu wuce kafin mu isa kogon
darul ikisina, akawai wasu mugayen burirrika
kimanin guda dubu dari hudu, wadanda suke
yawo a sama tamkar tsuntsaye domin suna
dauke da fuka-fukai, kuma suna da zara-zaran
farata masu tsananin kaifi da tsini, wanda da
zarar sun cafi wuyan mutum sai dai kaga sun
cisge masa kai, tabbas jaruma shadira ce kadai
zata iya tarwatsa mana wadannan mugayen
burirrikan har mu samu damar ratsawa da
wannan daji mu wuce, wannan baya nufin
dukkaninmu zamu iya tsallake sharrin
burirrikan dukkaninmu face sa'a da kuma
nasara. Jaruma Shadira tana da wani dn uwa
nata wani karamin yaro mai kimanin shekaru
tana ana kiransa da suna Masnur, tunda aka
haifi Masnur bai taba magana ba, kuma shima
aljanu ne suka shafeshi aka tabbatar da cewa
214

TASKARNOVELS.COM.NG
bazai tab warkewa ba face an debo wannan
tsumin maganin na cikin kogon darul ikisina an
bashi ya sha.
Jaruma Shadira tana matukar kaunar Masnur
fiye da komai a duniya, domin su goma sha daya
ne a wajen mahaifinsu, amman mutum tara duk
sun mutu saura su biyu kacal, sakamakon wani
azababben yaki da aka yi a kasarsu, wanda aka
kashe kaso takwas cikin kaso goma na jama'ar
kasar gaba daya. A wannan ya?i ne su jaruma
Shadira suka rasa iyayensu da dukkanin
danginsu, saboda haka Shadira ta dauki
alkawarin cewa ko da zata rasa rayuwarta sai ta
nema wa dan uwanta magani, domin babban
burinta shine taji ya budi baki ya ambaci
sunanta kafin ajali ya risketa, bisa wannan
daliline ma yasa jaruma Shadira taki yarda ta yi
aure duk da cewa ta kasance kyakkyawar
budurwa abar kwatance.
Abokin tafiyarmu na uku shine jarumi Ishran Bn
Suhairu wanda ke zaune a birnin Istim, a halin
yanzu duk duniya babu wanda ya fi jarumi
Ishran iya sarrafa sanda, domin idan yana yaki
da sanda a hannunsa komai yawan abokan gaba
dayansu bazai iya taba jikinsa ba, sabida zafin
215

TASKARNOVELS.COM.NG
namansa da kuma karfin dukansa, kuma yana
iya shafe kwana biyu yana yaki ba tare da ya
nuna alamar gajiyawa ba.
A cikin daji na uku da zamu wuce kafin mu isa
kogon darul ikisina akwai wadansu mugayen
tsuntsaye wadanda adadinsu ya kai kimanin
dubu dari biyar da arba'in. Kaifi da tsini baya
tasiri a jikin wadannan tsuntsaye, haka ma
karfin sihiri, sai dai a makesu da sanda ko icce,
idan wadannan tsuntsaye suka karci jikin
mutum da faratansu ko kuma da tsinin bakinsu
take wajen zai zama gyambo har da tsutsa, babu
wanda zai iya trwatsa mana wa?annan
tsuntsaye mu iya ratsawa ta cikin dajin face
Jarumi Isran Bn Suhairu. Isran yana da
mahaifiya wacce ta tufa tukuf ainun, ammnan
tunda aka haufeta bata taba taka kafafunta ba,
domin a lankwashe suke kamar lauje, kuma
itama aljanu ne suka shafeta, babu irin neman
maganin da ba a yi ba, amman abu ya gagara, sai
daga baya bikaye suka tabbatar da cewa sai an
shafa mata ruwan wannan maganin na kogon
darul ikisina annan zata warke ta iya mikewa.
Isran yayi alkawari koda zai rasa rayuwarsa sai
yaje kogon darul ikisina ya debo wannan
magani, sau tara Isran yana zuwa wajena akan
216

TASKARNOVELS.COM.NG
na rakashi kogon darul ikisina, amma sai na
fada masa yayi hakuri sai idan lokacin tafiyar
tamu yayi zan nemeshi da kaina.
Abokin tafiyar mu na hudu ba kowa bane face
Gimbiya Zarina ta birnin Farisa, a halin yanzu
duk duniya babu wanda ya lakanci sanin sirrin
daji sama da Gimbiya Zarina, domin tafi kowa
kwarewa a iya farauta da sanin sawun ko wace
irin dabba gami da hadarinta. A cikin daji na
hudu da zamu ratsa kafin mu isa kogon darul
ikisina akwai mugayen dabbobin daji wadanda
suke lambo da buya, sai dai kawai mutum yaji
sun dira a jikinsa sun turmusheshi, kafin ya
ankara sun halakashi, akwai hanyoyi da wurare
a dajin wanda dabbobin basu isa su bi ba,
wadannan hanyoyine kawai mutum zai bi ya iya
tsira daga sharrin wadannan dabbobin, domin
dabbobin dake wannan daji basa jin sara sa
suka kuma tsafima baya tasiri a jikinsu. Gimbiya
Zarina ce kadai zata iya fitar damu daga cikin
wannan daji.
Sarkin Farisa ya kasance dan uwa ne a wajen
Zarina, kuma tagwaye aka haifesu tamkar an
tsaga kara haka suke a kamanni, sannan sun
kasance kyawawa ne na gaban kwatance, tunda
217

TASKARNOVELS.COM.NG
sarkin Farisa ya girma ya zama saurayi bai taba
sha'awar ya mace ba, domin aljanu sun shafi
al'aurarsa. Babu irin neman maganin da ba'ayi
ba amman abu ya gagara. Daga baya ne bokaye
suka tabbatar da cewa sai an debo masa tsumin
ruwan maganin kogon darul ikisina yayi tsarki
da shi sannan zai samu lafiya har ya iyayin aure.
Zarina da sarkin Farisa sun shaku ainun, kuma
ko kadan batason taga abinda zai bata masa rai,
a duk lokacin da sarkin Farisa a tuno da wannan
lalura tasa sai yayi ta kuka da bakin ciki, kuma
sai ya kwana uku bai ci abinci ba, ganin wannan
hali da yake shiga ne yasa Gimbiya Zarina ta
dauki alkawari cewa koda zata rasa rayuwarta
sai ta je kogon darul ikisina ta debo wa dan
uwanta tsumin wannan maganin.
Zarina ta yi alkawarin zata bani dukiya iya
adadin abinda ta gada a wajen iyayensu akan na
rakata zuwa kogon darul ikisina, amma sai na
fada mata tayi hakuri sai lokacin tafiyar yayi,
itama zan nemeta da kaina.
Abokin tafiyarmu na biyar shine Sadauki
Shaharan Bn Lawwar na birnin Hairussalas, a
duniya kaf babu wani mutum mai karfin gudu
218

TASKARNOVELS.COM.NG
bisa turba tamkar Sadauki Shaharan, domin
yana iya shafe gudun zira'i saba'in a cikin
dakika sittin, a cikin daji na biyar da zamu ratsa
mu wuce izuwa kogon darul ikisina akwai wata
katuwar kunama guda daya jal, wacce ta
kasance mai tsananin karfin gudu, domin udan
ta kasa tsere da dawakai tana basu raya ta zira'i
arba'in, kuma komai jurewar gudun mutum sai
ta kureshi ta harbeshi, da zarar dafinta ya shiga
jikin mutum take yake dahuwa ya narke kamar
an kada ruwan kwai. Akwai wani ruwan kogi a
karshen wannan daji, idan har mutum ya kasa
tsere da wannan kunama kuma ya rigata fadawa
cikin wannan kogi tana fadawa cikin kogin nan
take zata mutu. Babu wanda zai iya kasa tsere
da wannan kunama kuma ya rigata fadawa cikin
wannan kogi face Shaharan, idan ya samu
nasarar hakan ne zamu iya ratsawa ta wannan
dajin ba tare da wannan kunama ta halakamu
ba.
Sadauki Shaharan yana da wani ingarman doki
mai tsananin gudu, tamkar shi kansa, shi dai
wannan doki Shaharan yana shiga gasar tsere ta
duniya da shi, sau shida ana yin wannan gasa a
birnin Hairussalas yana lashewa ya zama
zakara. Kuma duk bayan shekaru hudu ake yin
219

TASKARNOVELS.COM.NG
wanna gasa, yanzu abokan gasar tasa sunyi wa
dokin nasa asiri ya gurgunce gashi saura
shekara daya ayi wannan gasa. Babu irin neman
maganin da Sadauki Shaharan bai yi ba amman
sai abu ya gagara, daga karshe ne shima bokaye
suka tabbatar masa d cewa shima sai ya samo
tsumin ruwan magani a kogon darul ikisina an
shafa a kafafun dokin sannan zai iya mikewa har
yayi wannan gasa.
Ssadauki Shaharan ya bugi kirji kan cewa koda
zai rasa rayuwarsa ne to tabbas sai yaje kogon
darul ikisina ya debo ruwan wannan magani,
saboda gasar da za'ayi a shekara mai zuwa ita ce
ta karshe, kuma zakaran daya lashe gasar za a
bashi auren yar sarkin birnin Hairussalas gami
da dukiya mai tsanin yawa da har mutum ya
mutu bai isa ya karar da ita ba.
Dama can Sadauki Shaharan ana yana mutuwar
son gimbiya Sharilat yar sarkin birnin
Hairussalas domin dare da rana a cikin begenta
yake, yana raira mata wakoki yana zubar da
hawaye, a rayuwar Sadauki Shaharan sau daya
ya taba ganin Gimbiya Sharilat, tun daga
wannan rana kuwa bai sake yin bacci da

220

TASKARNOVELS.COM.NG
daddare ba saboda tsananin begenta, kuma ba
zai baccin ba face ya mallaketa ta zama matarsa.
Abokin tafiyarmu na shida ba wani bane face ni
kaina, ni kadaine nasan hanyar da za bi a riski
wadannan dazuzzuka guda biyar, kuma
masifaffu sannan har abi ta cikinsu a isa kogon
darul ikisina. Lokacin da boka muzafar ibn
Mauzar yazo nan a jawabinsa sau yayi ajiyar
numfashi domin makogwaronsa da harshensa
su huta bisa doguwar maganar da yayi, shi
kansa sarki lafaru sai da jaya dogon numfashi ya
ajiye sabida tsananin mamaki, bisa jin wannan
dogon bayanin da kuma sanin gagarumin aikin
dake gabansu kan wanna tafiya mai tsananin
hadari da wuya.
Boka muzafar yayi gayaran murya sannan ya ci
gaba da bayanu kamar haka al'amarin aljani
Maruful Dauwas kuwa, wanda zamu rik a cikin
kogon darul ikisina kuwa mu nemi taimakonsa
akan yaje ya sato mata gimbiya Ramlatus siyam,
abune mai tsananin hadari a garemu, ya kai
wannan sarki kayi sani cewa shi dai aljani
maruful Dauwas ya kai shekaru ubu biyu da dari
biyu a cikin kogon darul ikisina, kuma tunda ya
shiga kogon sai yayi zamansa bai sake fitowa ba
221

TASKARNOVELS.COM.NG
balle yaga mutum ko aljan dan uwansa, haka
kuma bai sake shakar iska irin ta duniya ba,
sannan kuma bai kara ci ko shan wani abu ba,
dalili kuwa shine duk halittar data shiga cikin
kogon darul ikisina ba zata sake jin yunwa ko
kishin ruwa ba, kuma duk irin cutar dake jikinka
sai ta warke, ko yaushe kogon a ni'ima yake
babu zafi hakazalika babu snyi, bugu da kari
idan har halitta ta shiga cikin wannan kogo to fa
sai ta ninka adadin shekarunta sau dari a duniya
sannan zata mutu walau mutum, aljan, dabba ko
kuma kwaro, duk da cewa kawai wadannan
ni'imomi a cikin kogon darul ikisina kulum
aljani maruful Dauwas kulum cikin kuka da
bakin ciki yake, kuma sai yayi kwana arba'in
yana raira wakar bege ga masoyiyarsa Gimbiya
Rashmin yar sarkin aljanu na birnin Hindu, har
takai cewa hawayen nasa sun taru sun zama
kamar kogi a cikin kogon darul ikisina, wanann
kogi shine ruwan maganin da jaruman biyar
suke bukata.
Yau kimanin shera dubu biyu da dari biyar
kenan da mutuwar Gimbiya Rashmin wacce ta
kashe kanta sakamakon mahaifinta sarkin
aljanu na birnin hindu ya ki yarda ya aurar da
ita ga bawanta aljani maraful Dauwas. Tun
222

TASKARNOVELS.COM.NG
Aljani Maraful Dauwas yana da shekaru bakwai
da haihuwa yake bauta a gidan sarkin aljanu,
kuma Gimbiya Rashmin sa'arsa ce, wato kai
daya suka taso, kuma tun a sannan shine
bawanta mai kula da turakarta, abincinta gami
da lafiyarta kasancewarsa dan babban likitan
sarki.
Sarkin aljanu ya aminta kwarai da aljani Maraful
Dauwas, kamar yadda ya aminta da mahaifinsa
marigayi, kuma yana kaunarsa matuka, ba wani
abu ne yasa Sarki aljanu yake matukar kaunar
shi ba face abubuwa uku;
Na farko shidai aljani Maraful dauwas
sadaukine, kuma tun yana yaro yake daka wa
maza gumba a hannu a duk sa'ar da aka fita
yaki.
Abu na biyu yana da matukar karfin gudu a
sararin samaniya fiye da tunanin mai tunani,
dan haka duk wata bukatar sarki ta gaggawa
shine ake aikawa.
Abu na uku shine, shidai aljani Maraful Dauwas
yana da amana matuka, domin komai yawan
dukiya idan aka bashi ajiyarta bazai taba koda
adadin kwayar zarra daga ciki ba, atakaice dai
223

TASKARNOVELS.COM.NG
yadda sarki ya aminta da aljani Maraful Dauwas
bai aminta da dukkanin iyalansa da matansa
gami da sauran fadawansa ba. Kai wani lokacin
ma bashi da abokin shawara face aljani Maraful
Dauwas, duk da kasancewarsa karamin yaro
amman akwai tunani gami da hangen nesa.
A kwana a tashi sai gimbiya Rashmin ta girma ta
zama kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance,
ya zamana cewa a wannan zamani babu
kamarta a dukkanin matan aljanu na duniya,
dan haka sai ?a?an Attajirai, bokaye, sarakai
masu is da kansu suka rinka zuwa neman
aurenta, ita kuwa sai ta ki yarda ta fidda gwani
daga cikinsu.
A wannan lokaci dare da rana gimbiya Rashmin
na tare da bawanta Aljani Maraful Dauwas,
hatta mahaifiyarta bata shaku da ita ba kamar
yadda ta shaku da bawan nata, kuma babu
abinda ke rabasu face kwanciyar bacci, wani
lokacin ma Gimbiya Rashmin ata barin Aljani
Maraful Dauwas ya fita daga turakarta koda
tana jin bacci, idan yaga haka sai ya shiga raira
mata waka mai dadi, a cikin waken kalamai ne
na koda kyawunta dan haka bata sanin sa'ar da
bacci ke saceta sabida jin dadin waken.
224

TASKARNOVELS.COM.NG
A sannan ne yake samun damar fita daga cikin
turakarta ya tafi nasa dakin. Ga bako idan yazo
gidan sarautar sai ya dauka cewa Aljani Maraful
Dauwas da Gimbiya Rashmin yan uwa ne na jini
ba bawa da uwargijiyarsa ba.
Alama daya ce zata tona asirin hakan ganin
yadda Aljani Maraful Dauwas ke yin aikin bauta
a gidan sarautar da kuma yanayin suturar da
yake sawa wacce bta kai darajar ta ?a?an
sarakai ba.
Lokacin da sarkin aljanu yaga jama'a sun
dameshi akan zuwan neman auren yarsa, sai ya
kira Gimbiya Rashmin ya ce da ita "Ya ke yata na
baki kwana arba'in kacal da ki fiddar da gwani
daga cikin masoyanki, in ba haka ba kuwa zan
baki wanda nake ganin ya dace da ke"
Ko da jin wannan batu sai hankalin Gimbiya
Rashmin ya dugunzuma ainun, ta ce ya kai
abbana ka yi sani cewa ni ban ta?a yin soyayya
da wani da namiji ba, koma ban san ma mece ce
soyayya ba, ya za a yi kazo ka yi mani titsiye a
rana ?aya kace na fitar da gwani a cikin
masoyana, alhalin duk samarin dake zuwa

225

TASKARNOVELS.COM.NG
wajenka suke zuwa ba wajena ba, kuma babu
wanda na tana yin hirar dakika daya da shi.
Koda jin wannan batu sai sarki ya turbune fuska
tare da cewa Ya ke yata kiyi sani cewa idan baki
yi aure a yanzu ba kimata da mutuncina ne zasu
zube a idon duniya, domin dukkan masu sonki
da aure sun kasance manyane a cikin al'ummar
aljanu na duniya, shawara daya da zan baki
itace kije ki samu wanda kike ganin kin yarda da
shi, walau a cikin kawayenki ko yan uwanki, ko
kuma mahaifiyarki kice da su suyi maki
cikakken bayani akan irin namijin da ya kamata
ki aura, kuma su fayyace maki mene ne so,
domin ki san mahimmanci soyayya dan jada ki
auri namijin da bakya kauna a cikin zuciyarki.
Koda sarki ya gama fadin haka sai ya mike tsaye
ya fice daga cikin falon da suke zaune, fitarsa
keda wuya sai gimbiya Rashmin ta shiga zancen
zuci tare da cewa To ni yanzu wa ya kamata
naje nayi wa wadannan nan tambayoyi, nikam a
duniya babu wanda na yadda da shi sama da
bawana aljani Maraful Dauwas, sabida haka
lallai da shi zanyi wannan shawara.

226

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda gama ayyana haka sai gimbiya Rashmin ta
tafi izuwa turakarta, da shigarta cikin turakar
sai ta iske Maraful Dauwas ya gama kimtsa
komai na dakin yana gyara mata shinfida.
Rashmin ta zauna a gefen gadon nata a lokacin
da Maraful Dauwas ya kammala aikinsa tare da
juyawa zai fice daga dakin, kawai sai yaji ta kira
sunansa, kuma ta yafito shi da hannu tana mai
yi masa nuni da ya zo ya zauna a gefen gadon
kusa da ita.
Koda ganin haka sai zuciyar Maraful Dauwas ta
buga da karfi, yaji kamar an doki ransa da
guduma, tsoro ya kamashi. Amman sai yayi ta
maza ya je
End Ads