x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - MAZAN JIYA 2

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 55701 words

Category: Romance Story +18

Views 191

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
da ke tsakanin kafar halittar zuwa
kasa sai da Dujalu ya shafe dakika dari shida da
sitin yana saukowa kasa.
Sa'adda Dujalu yaji kafafunsa sun dira bisa
turba sai ya yunkura ya kara daka tsalle sama
tamkar akan sifirin ya dira, a lokacin ne kuma
halittar ta tsugunno kasa da nufin ta talitseshi
da guiwarta amma sai taji guiwarta ta bugu da
kasa ta nutse cikin kasar ta haifar da katon rami
mai zurfin kamu dubu. Kafin halittar ta zare
guiwarta daga cikin karkashin kasa tuni Dujalu
ya sake isa kan kafadarta. Kafafunsa na dira
akan kafadar sai ya sake daka tsalle yai sama ya
isa dai-dai fuskarta sai kawai ya soka takobinsa
izuwa cikin hancinta guda. Ai kuwa sai halittar
18

TASKARNOVELS.COM.NG
ta kwarara uban ihu bisa tsananin zafin da zogin
da taji tayi taga-taga da baya. Tuni takobin
Dujalu ta makale cikin hancin halittar, shi kuwa
sai ya rike takobin da hannayensa biyu yana
reto a sama kuma ya cigaba da kokarin zare
takobin amma sai ya kasa.
A duk sa'adda ya girgiza takobin sai halittar ta
kara kwarara ihu ta kawo masa cafka da
mangari amma sai ya wurkila kafafunsa ya goce.
Shi kansa Dujalu ya yi mamakin yadda ya kasa
zare takobin duk da cewa gaba dayan nauyinsa
a kanta yake.
Daga can sai Dujalu ya yi amfani da dukkan
karfinsa ya finciko takobin ya zarota daga cikin
hancin halittar. Takobin na zarewa sai ga jini na
shatata tamkar teku ta balle.
Dujalu ya rikito izuwa kasa, itama halittar sai ta
taho kasa a sandare. Dujalu da halittar suka taba
turba a lokaci guda. Kafin Dujalu ya goce wuyan
halittar ya fadi a tsakiyar cikinsa, amma sai ya yi
gwafa bai taba jikinsa ba, amma ya rufeshi
yadda ba zai iya fitar da kansa ba.
Halittar dai ko motsi bata sake yi ba, domin
19

TASKARNOVELS.COM.NG
ta zama gawa. Har a sannan kuma jini na malala
daga cikinta yana kwarara a dajin, tamkar
ruwan samansa ake yi. Dujalu dai bai san
sa'adda ya bushe da dariyar farin ciki ba, bisa
ganin wannan gagarumar nasara da ya samu ta
hallaka halittar, amma da ya dago kai ya dubi
wuyan halittar wanda yai gwafa a kansa ya
tokareshi sai hankalinsa ya yi mummunan tashi
domin bai san yadda zai iya ture gawar haittar
ba ya fito, saboda jikin halittar ba zai saruba da
takobi bare ya sareshi. Dujalu na cikin wannan
tunani ne ya hango yar uwarsa Hursiya ta rugo
gareshi da gudu ita kadai tana murmushin farin
ciki. A sannan ne kuma aljani Rauzuf ya farka
daga dogon suman da ya yi, ba zato kuma sai ga
sauran dakaru suna fitowa da dai-dai daga
wuraren da suka buya sunaa rugowa wajen
Dujalu suna ihu bayan hari. Duk wanda yazo ya
ga wannan katuwar halitta kwance a kas a
mace sai ya cika da tsananin mamaki. Nan fa
dakaru suka kama fashewa da murna suna yiwa
Dujalu jinjina. Duk wannan abu da ke faruwa
zuciyar Dujalu tafarfasa take kamar za ta fone
saboda tashin hankalin da yake ciki na ganin
kansa a karkashin gawar halittar bisa sanin
cewa ba zai iya fitowa ba. Daga can sai Hursiya
20

TASKARNOVELS.COM.NG
ta lura da fuskar Dujahu ta fahimci cewa lallai a
cikin tsananin damuwa yake. Cikin firgici
Hursiya ta dubeshi ta ce, "Ya kai dan uwana ina
dalilin wannan matsanaiciyar damuwa a
gareka?". Koda jin wannan tambaya sai sarki
Dujalu yai ajiyar zuciya cikin karaya ya ce, "Ya
ke 'yar uwata kiyi sani cewa wannan murna da
kuke yi bisa samun nasarata dai-dai take da
farin ciki da zuwan mutuwata. Ki dubi yadda na
kasance a karkashin gawar wannan halitta,
yenzu ta ya ya za ku iya zaroni daga
karkashinta, shin a cikinku Wane ya yi tunanin
wannan hali da na ke ciki?" Sa'adda Hursiya taji
wannan tambaya sai ta dubi gawar halittar da
kyau ta ga yadda ta rufe Dujalu ruf babu wata
karamar kofa da za a iya zareshi. Nan take
hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abin da
ke ma ta dadi a duniya, don haka sai ta mike
tsaye ta dubi gaba dayan dakarun da ke wajen
mutane da aljanu ta daka musu tsawa. Gaba
dayan dajin yai tsit! Kowa ya zuba ma ta idanu.
A sannan ne hawaye ya zubo daga idanun
Hursiya ta budi baki ta ce, "Ashe gaba dayanku
nan taron banza ne taron wofi? Ku dubi halin
da sarkinku ke ciki, ashe dayanku ba zai yi
21

TASKARNOVELS.COM.NG
tunanin hanyar da za a bi a zaroshi ba daga
karkashin gawar wannan halitta ba?". Koda jin
wannan batu sai kowa yai tsuru- tsuru ya shiga
taitayinsa aka marmatso ana nazarin yadda za a
yi a janye gawar katuwar halittar daga kan
sarki Dujalu. Nan fa aka shiga yin shawarwari.
Wasu zaratan jaruman yaki guda uku, wadanda
babu kamarsu a cikin dakarun suka ware gefe.
Zan ci gaba.
MAZAN JIYA Littafi na biyu 2 Part B Na
Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh
AlQuyraemey
Daya daga cikin wadannan zaratan jarumai
aljani sunansa Karbazu, a gaba dayan dakarun
aljanun da ke wajen babu sadauki kamarsa,
kuma ma'abocin hikima ne da sanin dabarun
yaki daya kuwa mutum ne, sunansa Barsuma.
Barsuma shi ne sarkin yakin birnin Hawaru din.
Shima ya kasance gagarumin sadauki kuma
gwarzon mayaki a cikin jinsin bil'adama
wadanda babu kamarsu a gaba dayan nahiyar.
Shima ya kware matuka a sanin makama da
dabarun samun nasara a yaki. Mutum na uku
wani tsohon sadauki ne wanda shekarunsa sun
haura casa'in amma har gobe yana dakawa
22

TASKARNOVELS.COM.NG
matasa gumba a hannu wanda ake kira da suna
Shurkaib bin Dallas. Lokacin da Kurbazu,
Barsuma da Shukaib suka ware gefe daya
domin su yi shawara bisa dabarar daza a yi a
sami nasarar zaro sarki Dujalu daga karkashin
gawar halittar sai Karbuza ya dubi Barsuma da
Shurkaib ya ce,"Yanzu ku mene ne shawararku,
ta ya ya kuke ganin za mu iya zaro sarki ba tare
da lafiyarsa ta tabu ba? Abu na farko dai, janye
gawar wannan halitta daga kansa ba karamin
aiki bane, saboda girmanta da nauyinta. Idan
gaba dayanmu zamu taru ba zamu iya ture ta ba
da karfin tsiya. Idan muka ce zamu zauna anan
muna kula da sarki har izuwa
lokacin da halittar za ta rube mu sassareta to
tabbas warinta ma zai iya zama ajalinmu gaba
daya. Yanzu sai ku fadi shawarwarinku kafin na
fadi tawa ku ji mu zabi wadda za ta fi inganci"
Koda jin wannan batu sai tsoho Shurkaib ya yi
murmushi ya ce, "Ni ba zan fadi tawa dabarar
ba sai naji taku, kuma zan fadi tawa dabarar ne
bayan an jarraba taku ba a sami nasara ba,
kuma bisa sharadi guda". Koda jin wannan
batu sai mamaki ya kama Karzuba da Barsuma.
Barsuma ya ce, "Ya kai Shurkaib ka shiga
taitayinka fa ka san abin da kake fadi. Yanzu har
23

TASKARNOVELS.COM.NG
ka isa ka sanya wani sharadi don ceton rayuwar
sarki? Baka tsoron cewa idan dabararmu ta yi
nasara sarki ya kubuta fishinsa zai iya tabbata
akanka?". Koda jin wannan batu sai Shurkaib ya
bushe da dariya, sannan ya ce, "Ku a tunaninku
ni ina tsoron mutuwa ne? Ku tuna cewa
shekaruna sun haura casa'in a duniya,
na haifi ya'ya, ya'yanma sun haihu, nayi yakeyake da dama ba adadi. Babu irin masifar da
ban gani ba a duniya, kuma babu wani buri da
ban cika ba face guda daya, kuma yanzu ne na
samu damar da zan cika wannan buri nawa bisa
wannan uzuri da ke gabanmu. Inaa tabbatar
muku da cewa duk dabarar da za ku kawo
domin a kubutar da rayuwar sarki ba za a yi
nasara ba.
Tawa dabarar ce kadai za a bi a samu nasara.
Yanzu na baku dama ku fara gabatar da taku
dabarar idan ba a dace ba sai na fadi tawa, idan
har sarki ya amince da sharadina". Sa'adda
Karbuza da Barsuma suka ji wannan batu, sai
suka fara cika da mamakin Shurkaib suka
tabbatar da cewa da gaske yake. Karbuza ya ce,
"Shi ke nan ai yanzu sai ka zo mu je wajen sarki
domin mu gaggauta yin abin da ya kamata mu
24

TASKARNOVELS.COM.NG
yi domin bata lokacinmuu cikin wannan daji
tamkar baiwa abokan gaba dama ne su rigamu
zuwa inda takobin Saiful Lujara take." Koda jin
haka sai Basuma da Shurkaib suka ce a cikin
hadin baki, "Zancenka dutse ne". Nan take su
ukun suka dawo inda sarki Dujalu ke kwance a
karkashin gawar wannan halitta.
Duk su ukun suka durkusa a gabansa. A
wannan lokaci Hursiya ta tallafo kan sarki
Dujalu ta dura masa ruwa a baki. ya sha. Gama
shan ruwan nasa ke da wuya ya yi arba da su
Karbuza tsugunne a gabansa sai ya fusata ya ce,
"Me kuke jirane har yanzu baku yi tunanin
dabarar da za ku yi ba ta ceto rayuwata?"
Kurbazu ya numfasa ya ce, "Ya shugabana ai
abin da muka je muka tattauna ke nan, kuma
kowannenmu yana da tasa dabarar dabam.
Zamu fara jarraba tawa dabarar, in yaso a
jarraba ta Barmusa, idan tawa ba tai nasara ba,
idan shima tasa bata yi ba sai a jarraba dabarar
Shurkaib.
" Sarki Dujalu ya ce, "Na umarceku da ku aikata
hakan cikin gaggawa domin idan muka kara
kwana hudu anan cikin wannan daji rundunar
Su sarki Maharaz za ta zo ta riskemu. Ni kuwa a
25

TASKARNOVELS.COM.NG
shirina shi ne mu rigasu zuwa tekun bahar
Sufiya ya zamana cewa kafin su isa tuni mun
danko takobin Saiful Lujara." Karbuza ya dubi
dukkanin dakarun aljanun da ke wajen ya ce,
"Na umarceku da ku ruga izuwa cikin wannan
daji ku tsunko murtuka murtukan jijiyoyin
bishiyoyi dogaye ku zo da su yanzu.
Kafin Karbuza ya gama rufe bakinsa tuni gabe
dayan dakarun aljanun sun bace bat! Kafin
cikar dakika sittin sai gasu sun dawo dauke da
dogayen jijiyoyin murtuka-murtukan bishiyoyi
masu yawan gaske tamkar za su yiwa dajin gaba
daya rufi da su. Ba tare da bata lokaci ba
Karbuza ya umarcesu da su kukkulla jijiyoyin
wasu jikin wasu. Nan da nan aka samar da
dogayen igiyoyi na jjiya barkatai.
Karbuza ya saké bada umarnin a daura jijiyoyin
a jikin gawar katuwar halittar. Kowacce
doguwar jijiya daya aka sa kartin aljanu majiya
karfi guda dubu suka riketa. A kalla an sami
sama da aljanu miliyan daya. nan take aka basu
umarni da su ja igiyar sama a lokaci guda,
domin su daga gawar sama daga kan sarki
Dujalu domin sami damar zareshi. Aljanun gaba
dayansu suka tattaro karfin daratsensu suna jan
26

TASKARNOVELS.COM.NG
jijiyoyin a lokaci guda. Maimakon gawar
halittar ta rabu da kasa, sai gaba dayan
jijiyoyinPartFaka daura a jikinta suka tsittsinke,
aljanun suka fado kasa gaba dayansu Al'amarin
da ya baiwa kowa mamaki ke nan a wajen,
kuma hankalisu ya dugunzuma. Sarki Dujalu ya
juyo da wuyansa da kyar ya dubi Barsuma cikin
alamun karayar zuciya ya ce,
"Ya kai Barsuma babban gwarzo, NAMIJIN
DUNIYA, mai dakawa maza gumba a hannu, ka
ga yadda dabarar Karbuza ta kare, kai kuma
wacce dabara ke gareka?" Barsuma yai gyaran
murya sannan ya ce, Ina son aje a nemo mini
giwaye adadin ninkin wannan aljanu sau dari.
Ma'ana kowanne aljani guda giwa dari ce za ta
wakilceshi, sanann a nemo mini dogayen
sarkoki murtuka-murtuka na karfe a daura a
jikin gawar wannan halitta sannan a daura a
jikin giwayen domin su ja sarkar su janye
gawar".
Koda jin hake sai dakarun miliyan dubu daga
cikin aljanun sulka 6ace bat a lokaci guda. Kafin
kiftawar ido sai gasu sun dawo tare da
wadannan giwaye da sarkokin karfe. Kamar
yadda Barmusa ya bada umarni haka aka yi,
27

TASKARNOVELS.COM.NG
amma koda giwayen suka yunkura suka ja
sarkokin karfen, sai sarkokin suka tsittsinike
saboda tsananin nauyin katuwar halittar sai
gani aka y giwayen na faduwa wasu na danne
wasu. Nan fa hankali ya kara dugunzuma fiye
da ko a yaushe, zuciyar sarki Dujalu ta kara
karaya ya fitar da rai ga cikar burin rayuwarsa
ya fara tunanin cewa tabbas ajalinsa ya gabato.
Duk da sanin hakan sai ya yi ta maza ya dubi
Shurkaib ya ce,
"Ya kai tsoho mai dabara, ya kai tudu mai nisan
da yaro ba zai hango ba. Ya kai masanin jiya,
kuma masanin gobe, ka ga yadda dabarun yan
uwanka suka kasan ce. Ka sani cewa karfin
tsafina da karfin damtsena ba za su ceceni ba
daga cikin wannan hali da na shiga ba, wacce
dabara ce da kai wadda in dai aka yi ta zan tsira
da rayuwata?
Na yi maka alkawari idan har ka ceci rayuwata
duk abin da kake bukata zan baka shi in dai
akwai shi anan duniya domin rayuwata ta fishi
daraja a idanuna". Sa'adda tsoho Shurkaib yaji
wannan batu na sarki Dujalu sai ya cika da
tsananin farin ciki bai san sa'adda ya saki
murmushi ba sannan ya dubi Dujalu cikin
28

TASKARNOVELS.COM.NG
nutsuwa ya ce, "Ya shugabana idan na fadi
dabarata ba a cimma nasara ba na yarda kasa a
kasheni a take a wannan wuri. To amma ka sani
cewa ba zan fadi dabarata ba face ka dada
jaddada alkawarin da ka furta yanzu kuma ka
rubutashi a rubuce tare da sa a buga hatiminka".
Koda jin haka sai sarki Dujalu ya girgiza kai
yana mai nuna alamar cewa ya aminta da hakan.
Nan take ya sa aka kawo masa tauwada da
alkalami gami da fatan rubutu.
Har ya dangwalo tawada zai yi rubutun bisa
fatar sai Hursiya ta yi sauri ta rike hannunsa a
lokacin da hawaye ke zuba daga idanunta ta ce,
"Haba ya dan uwana ina amfanin rayuwa idan
buri bai cika ba? Yanzu idan Shurkaib ya ce
abin da muka fito nema ya ke so fa". Koda jin
haka sai kowa da ke wajen yai tsuru-tsuru har
shi kansa sariki Dujalu kuwa.
Shi kuwa tsoho Shurkaib sai ya yi murmushi ya
ce "Ko kadan bani da muradin kayan yakin
MAZAN JIYA" Da jin hake sai sarki Dujalu yai
mumushi, nan take ya yi rubutun yarjejeniya
cewa ya amince duk abin da Shurkaib ya furta
yana so zi bashi bayan dabararsa ta cimma ga
ci. Bayan ya gama rabutawar ne aka kawo
29

TASKARNOVELS.COM.NG
hatimi ya buga, kuma ya mikawa Shurkaib bada
shakkar komaiba. Shurkaib ya karbi fatar
yarjejeniyar ya sanyata cikin aljihunsa sannan
ya dubi gaba dayan aljanun da ke wajen ya
ce,"A cikinku wane ne mafi sanin sirrin hakan
kasa?", Koda jin haka sai wani tsamurmurin
aljani ya daga hannu ya ce, "Yau shekarata dubu
saba'in ina sh akin hakan kabari a garinmu"
Shurkaib ya dubeshi yai murmushi ya ce,
"Matso nan kusa da inda sarki yake. Ina son ka
haka rami karami dai-dai fadin gangar jikin
sarki a farkashinsa yadda zai fada cikin ramin
ba tare da kasa ta zabtare ba gawar wannan
katuwar halitta ta sake danne shi ba". Nan take
kuwa wannan aljani ya bi wannan umarni ya
kama aikinsa. Ko sa'a daya bata cika ba sai ya
kammala aka ga sarki ya fado cikin ramin daga
karkashin katuwar gawar halittar.
Cikin matukar zafin nama akayi sauri ake zare
sarki Dujalu daga cikin ramin. Ai kuwa ana
gama zareshi ke nan sai kasar wajen ta rusa
saboda nauyin gawar halittar, gawar ta lume a
cikin ramin, dajin gaba daya ya kama girgiza
saboda gawar halittar, ta ci gaba da nutsewa
izuwa cikin karkashin kasa. Ba shiri kowa da
30

TASKARNOVELS.COM.NG
kowa ya kama gudu. Sai da aka yi gudu na sa'a
shida sannan aka isa inda kasa bata girgiza
sannan aka tsaya ana haki. Daga inda aka
tsaitsaya ana iya hango yadda komai na
wancana dajin ya nutse izawa cikin farkashin
asa ya zamans cewa ba sauran bishiyoyi da
duwatsu wadanda ake iya hangowa.
A wannan lokaci ne kowa hankalinsa ya dawo
jikinsa. Bayan an nutsu sai sarki Dujalu ya tako
da kafafunsa yazo gaban Shurkaib ya tsaya daf
da shi yadda har suna iya jin numfashin
junansu. Sarki Dujalu ya dubeshi cikin
murmushi ya ce, "Yanzu sai ka fadi muradinka
naji domin na cika alkawarina". Koda jin haka
sai kowa ya yi tsit! Dajin gaba daya yai shiru
tamkar mutuwa ta gifta,
kamar suma sauran halittun da ke dajin sun yi
shiru suna sauraron munafunci. Tsoho
Shurkaib yai gyaran murya ya ce, "Ba wani abu
nake so ka bani ba face auren yar uwarka
gimbiya Hursiya, kuma ba nine mijinta ba, dana
za ka aurawa". Koda sarki Dujalu yaji wamnan
batu sai gaba dayan jiikinsa ya kama karikarwa
saboda tsananin bakin ciki, zuciyarsa ta kama
tafarfasa kamar za ta kone. Nan nan Dujalu yaji
31

TASKARNOVELS.COM.NG
nadama tazo masa bisa alkawarin da ya dauka,
saboda wasu babban siri da ya 6oye a cikin
zuciyarsa wanda duk duniya babu wanda ya
sanshi face shi kadai. Inda sarki Dujalu ya san
cewa abinda Shurkaib zai bukata ke nan da ya
zabi a barshi a cikin halin da yake ciki ya rasa
rayuwarsa,
burinsa ya rushe in yaso gimbiya Hursiya ta
koma gida ta ci gaba da sarauta. Kawai sai aka
ga idanun sarki Dujalu sun kada sun yi jawur
tamkar an gasa danbuda a wuta. Cikin sanyin
jiki ya sunkui da kansa kas ya ce,Lallai zan zamo
mai cika alkawari a gareka bayan mun samo
abin da muka fito nema" Koda gama fadin haka
sai sarki Dujalu ya tafi izuwa gaban wata
korama ya zauna ya kurawa ruwan koramar
idanu yana zubda hawaye.
Ya yin da Hursiya ta ga hakan sai itama ta nufi
inda yake. Koda sarki Dujalu ya waigo ya ga ita
ce ke tahowa gareshi sai yai sauri ya goge
hawayensa. Hursiya tazo ta zauna daf da shi
sannan ta dubeshi cikin murmushi ta ce, ya kai
dan uwana ina dalilin da yasa na ka ga shiga
cikin halin damuwa bisa jin bukatar tsoho
Shurkaib? Shin baka son na auri dansa ne
32

TASKARNOVELS.COM.NG
saboda bai kasance jininmu ba?". Lokacin da
sarki Dujalu yaji wannan tambaya sai ya dubeta
ya maida mata da martanin murmushin cikin
yake sanann ya ce, Ya ke 'yar uwata kiyi sani
cewa bukatar Shurkaib tazo mini da shammace,
ban taba tsammanin cewa kece muradinsa ba
ga dansa. Ki tuna cewa a tarihin
zuri'armu babu wani jininmu da ya taba auren
bare, yanzu gashi Shurkaib zai karya mana
wannan tarihi. Bugu da Kari, ina bakin ciki ace
ranar da babu ni, mulkinmu da dukiyarmu da
duk wannan daukaka da nake nema mana a
yanzu Za ta koma wajen zuri'ar tsoho Shurkaib,
domin idan kika auri dansa tamkar hakan ta
tabbatu ne."
Lokacin da Dujalu yazo nan a zancensa sai
tausayinsa ya kama Hursiya ta rungumeshi ta
fashe da kuka. Shi kuwa sai ya cika da tsananin
farin ciki a cikin zuciyarsa. Hakika rashin sani
yagi dare duhu. Inda Hursiyya ta san sirrin da
sarki Dujalu ya boye ma ta da taji ta tsaneshi
fiye da yadda ta tsani mutuwarta Haka dai
Hursiya da sarki Dujalu suka ci gaba da hira a
nan bakin koramar har izuwa lokaci mai dan
tsawo. Da fatan an tashi lafiya, sannan duk
33

TASKARNOVELS.COM.NG
wanda yake son complete zai iya tuntubata ta
wannan number 08138873799 kira ko
whatsapp. MAZAN JIYA Littafi na biyu 2 Part
C Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar
Saleh AlQuyraemey Daga can sai Hursiya ta
dago kai ta dubeshi ta ce, "Ya ki ?an uwana kayi
sani cewa zuciyata ta kasa samun sukuni saboda
rashin jin ci gaban labarin sadauki Hantaru.
Lallai ina son naji yadda karshen rayuwarsa ta
kasance".
Sa'adda sarki Dujalu yaji wannan batu sai ya yi
mrumushi sannan ya ce, "Ya ke yar uwata dama
na san cewa kina cikin kaguwa bisa son jin ci
gaban wannan labari, saboda haka Zan yi iyakar
kofarina na kammala miki wannan labari kafin
wayewar gari, domin so nake gobe da sassafe
mu ci gaba da tafiya domin mu isa tekun bahar
Sufiya akan lokaci, kafn su sarki Maharaz su zo
su riskemu".
Ya yin da Hursiya tajii wannan batu, sai ta cika
da farin ciki ta nutsu tana mai kurawa sarki
Dujalu idanu, shi kuwa sai ya yi gyarsn murya
ya cigaba da ba ta labari kamar haka. Lokacin
da hantaru ya zama katon dutse wannan
jibgegegiyar Micijiyar ta hadiyesthi, sai
34

TASKARNOVELS.COM.NG
macijiyar ta shiga cikin wani irin mugun hali
domin dutsen ya zame ma ta masifa a cikin
cikinta, yai ma ta nauyi, ya ZAmana cewa da
kyar ta ke iya motsawa. Koda taji dutsen na
damunta sai ta fara kokarin ta sake yin amansa
waje da karfin taiya. Idan ta turo dutsen izuwa
makogwaronta sai dutsen ya koma da baya,
wato ya ki yarda ya ito.
Nan fa Macijiyar ta kama tumuwa da kasa, tana
dukan kowacce kusurwa ta kogon da
kawunanta, al'amarin da ya sa gaba dayan
kogon ya ragurguje ke nan ya kama girgiza. A
duk sa'adda micijiyar
End Ads