zuciyarta cike da sake-sake da
tunani bisa wannan abu da ya faru tsakaninta da
109
TASKARNOVELS.COM.NG
boka Ardusa. Ba wani abu take tunani da wasiwasi ba face hadarin da ke cikin aikin da boka
Ardusa ya sa ta. Koda takwanta akan gadonta
domin ta mike kafafunta tayibarci sai kawai
tayi arba da wata takarda akangadon. Al'amarin
da ya matukar ba ta tsoro damamaki ke nan
domin a saninta babu wata takarda& cikin
turakar ta ta koda guda daya kuma babu yadda
za a yi a shigo da wani abu ba tare da saninta
ba.Hannun Zarifa na karkarwa ta sa
hannayenta biyu ta dauki takardar wacce ta
kasance fara kal babu zanen komai a kanta.Koda
ta dubi takardar sai ga hoton fuskar boka
Ardusa ta baiyana akai yana mai murmushi a
gareta sannan ya ce"Maza kifadi wadannan
tambayoyi uku gami da amsoshinsu." Koda jin
haka sai Zarifa ta karanto tambayoyin gami da
amsoshinsu. Bisa mamaki sai Zarifa ta ga an
rubuta duk abin da ta fada akan wannan
takarda ba tare da ta ga mai rubutun ba ko
alkalamin da ke yin rubutun. Nan take takardar
ta6ace 6at tamkar bata taba wanzuwa ba a
wajen. Koda ganin haka sai Zarifa tayi
murmushi sannanta kwanta. Kwanciyarta ke da
wuya sai barci yasace ta,bata sani ba. Abin da
bata sani ba shi ne, kafin boka Ardusa ya bace
110
TASKARNOVELS.COM.NG
daga cikin turakar ya busa mata hodar banju ta
shaka, shi ya sa nan da nan barci yakamata in
ba don haka be da ba za ta iya barcin basaboda
tunanin gagarumin aikin da ke gabanta dakuma
sharadin da ke tsakaninta da boka Ardusa. DA
RANAR gasa tazo sai fadar birnin Kisra ta cika ta
batse da mutane duk inda mutum ya duba
gabas da yamma, kudu da arewa sai dai ya ga
kawunan bil'adama fululu babu masakar tsinke.
A tsakiyar fadar ne jaruman gasa suka taru
wadanda gaba dayansu sun kasance sarakai da
attajirai da ma manyan bokaye daga kowanne
bangare a kasashen da ke nahiyar. Sarki
Kusaidu da sarkin Darul Mahabul ne suka shigo
a karshe,bokayensu na take musu baya.
Maimakon su sarki Kusaidu su tafi izuwa inda
karagar mulki take sai suma suka shiga tsakiyar
fadar inda sauran jaruman gasar suke. Saboda
shakkar wanman gasa gaba dayan jaruman da
suka tsaya a tsakiyar fadar su goma ne kacal su
sarki Kusaidu ne suka zamo cikon na shabiyun.
Ba wani abu bane ya janyo hakan ba face
sauran jama'ar da suke son su shiga gasar
wadanda adadinsu ya fi dubu dari bokayensu
sun tabbatarmusu da cewa 6ata lokacinsu za su
yi ba za su iyacin nasara ba. Shi kuwa Sarkin
111
TASKARNOVELS.COM.NG
Darul Mahabul ana i gobe za ayi gasar ne ya
sami f kwarin guiwar fitow awanann gasar
bayan boka Sulbaini da boka Zaharu sun
hakura da kiyayyar da ke tsakaninsu sun hada
karfi da karfe sun binciki amsar tambayar da za
ayi masa ya iya amsawa. Kuma a binciken da
suka yi sai suka kasa gano tambayoyin da Zarifa
za ta yi sai na Marifa suka gani. Koda suka ga
tambayoyin sai suka kasa fahimtar amsoshinsu
har sai da suka tara gaba dayan hadiman
aljanunsu suka bazamasu ?zuwa cikin duniya
wajen tsofafin mutane da aljanu masana ilimin
tarihi. Da Kyar da sidin goshi aljanun suka samo
amsar tarabayoyi biyu. Amsar tambaya ta uku
kuwa ba a sameta ba sai a lokacim da suka fito
filin gasar sannan wani hadimin boka Sulbaimi
yazo da ita. Ai kuwa cikin gaggawa ya radawa
sarki amsar a kunnensa.Koda jin amsar sai
sarki ya cika da farin ciki kuma ya sami
nutsuwar shigar gasar. Jim kadan de shigar su
sarki Kusaidu cikin jaruman gasa sai ga Zarifa
da Marifa suka shigo cikin filin fadar.Kowacce
daga cikinsu ta caba ado na ban mamnaki kuma
na kure adaka,kuyanginta na biye da ita gaba da
baya suna watsa furanni masu kamshi akan
hanyar takawarta. Kamshin turaren da su
112
TASKARNOVELS.COM.NG
Zarifa suka sanya a jikinsu ne ya fara dukan
hancin kowa a fadar.Koda jama'a suka ji
wannan kamshi sai suka waigo suka dubi masu
shigowar,wohoho! Nan fa maza suka rude suka
dimauce, wasu suka kama dalalar da yawu,
basu sani ba wasu kuwa sai suka kama yanke
jiki suna faduwa kasa sumammu saboda sun ga
abin da kwakwalwarsu ba za ta iya dauka
ba.Masu Karfin hali ne suka rinka kuka suna
zubar de hawaye saboda takaici bisa sanin
cewa ba za su taba mallakar wadannan
kyawawan 'yan mata biyu. Tun kafn su Zarifa
su shigo cikin fadar sai Zarifa ta ga Marifa ta sha
lullu6i kuma ta sunku da kanta kas idanunta
basa kallon komai face kasa inda take takawa.
Alamarin da ya dugunzuma hankalin Zarifa ke
nan domin ta san cewa idan har basu hada ido
ba ita da Marifa kashinta ya bushe kuma ba za ta
taba cika burinta ba. Nan fa Zarifa ta fara
tunanin abin de za ta yi domin ta tabbatar cewa
ta hada idanu da Marifa. Inda matsalar take shi.
ne akwai tazara tsakaninta da Marifa kuma
akwai kuyangin Marifa a tsakaninsu. Koda
Zarifa ta ga fuskar Marifa a rufe take sai itama
ta janyo mayafinta tayi lullu6i kuma ta sunkui
da kanta kas amma zuciyarta sai bugawa take
113
TASKARNOVELS.COM.NG
da karfi cikin tsananin tsoro. Zarifa da Marifa
suka ci gaba da tafiya suka nufi inda aka
tanadar musu su zauna amma Zarifa na daga kai
tana satar kallon Marifa ko za ta ga itama ta
dago kai domin su hada idanu, amma bata dago
din ba. Zarifa na cikin wannan satar kallo ne ta
hada ido da boka Ardusa,nan take ya yi ma ta
nuni da idanunsa cewa lallai tayi duk iyakar
kokarinta ta hada idanu da Marifa kafin su isa
inda kujerun zamansu suke. Koda ganin
wannan inkiya sai hankalin Zarifa ya kara
dugunzuma ta shiga tunanin abin da za ta yi ya
zamana cewa lallai ta hada idanu da Marifa
kafin su kai mazauninsu. Sai da ya rage saura
baifi taku goma ba su isa mazaunin nasu
sannan dabara ta fado ma ta. Kawai sai tayi
kamar tayi tuntu6e, cikin shammace ta tafi tagataga ta fadi a gaban Marifa.Cikin mamaki da
kaduwa Marifa ta sunkuya ta dubi Zarifa suka
hada idanu. Suna hada idon sai Marifa taji wani
abu ya soketa a kirji tamker an tsira ma ta
mashi. Saura kiris tayi ihu kuma ta fadi kasa,
amma sai ta daure ta mike ta ci gaba da tafiya. A
sannan ne ta ga Zarifa ta dubeta tayi ma ta wani
irin murmushi na mugunta. Nan take Marifa ta
tsergu da cewa tabbas 'yar uwarta Zarifa tayi
114
TASKARNOVELS.COM.NG
ma ta wani mugun asirin. Zarifa da Marifa sun
dade suna yiwa junansu mugun jifa na sihiri
amma sihirin yaki ya yi tasiri akan kowannensu
kuma duk wajen bokan da suka je yana gaya
musu cewa sai dai su yi hakuri babu wani sihiri
da zai iya huda jikinsu a yanzu,domin
mahaifinsu ya yi musu tsari na musamman babu
wanda zai iya karya wannan sihirin face bokan
da ya yishi kuma ba wani bane face boka
Ardusa. Cikin tashin hankali da mamaki Marifa
ta karasa zuwa kan kujerar da aka tanadar ma
ta ta zauna,itama Zarifa sai taje ta zauna akan ta
ta kujerar fuskarta cike da murmushi,zuciyarta
ta cika makil da farin ciki. Zamansu ke da wuya
sai Alkalan gasar suka fara zartar da aikinsu
aka ware jaruman da ke son Marifa da wadanda
ke son Zarifa. A zaton sarki Kusaidu Sarkin
Darul Mahabul zai shiga cikin sahun masu son
Zarifa amma sai ya ga ya shiga cikin sahun
masu son Marifa. Nan take Sarki Kusaidu ya hau
kan layin masu son Zarife ya tsaya daga Kanhe.
Masu son Zarifa mutum bakwai ne, masu son
Marifa kuwa mutun uku ne,sarkin Darul
Mahabul ya zamo na hudunsu. Saboda haka
sarki Kusaidu ne na takwas a cikin sahun masu
son Zarifa. Be wani abu bane ya sa masoyan
115
TASKARNOVELS.COM.NG
Zarifa suka hi yawa ba face its Zurifa ta baiyana
fuskarta an gani tun kafin a fara gasar don haka
jaruman gasar sun dauka tafi 'yar uwarta kyau
sai da Marifa ta yaye lullubinta gaba daya aka
ga kyawunta de kyawun surar jikinta wanda har
yafi na Zarifa sannan aka dimauce. Shi kuwa
sarki Kusaidu ya zabi Zarifa ne saboda boka
Ardusa ya gaya masa cewa na ta tambayoyin
kadai ya sani amma bai san na Marifa ba.Wani
abin mamaki shi ne duk da cewa Marifa tafi
Zarifa kyau sai sarki Kusaidu yaji yafi son Zarifa
kuma nan take ya kamu da tsananin begenta a
Zuciyarsa. Ba tare da 6ata lokaci ba Alkalan
gasa suka umarci Zarifa da ta mike tsaye ta
karanto tambayoyinta guda uku ga jaruman
gasarta mutum takwas bisa sharadin cewa duk
wanda ya amsa tambayar dai-dai shi ne zai
zamo mijin da za ta aura. Cikin mumushi gami
da takama Zarifa ta mike tsaye ta fuskanci
miliyoyin jama'ar da ke cikin fadara lokacin da
aka yi tsit! Tamkar mutuwa ta gifta. Zarifa ta
bude baki cikin muryarta mai zaki tamkar
sarewa ta ce tambayoyina gareku masoyana su
ne kamar haka. Tambaya ta farko, a duniya
wane abu ne mafi tsananin karfi, karfin da yafi
na radadin mutuwa ciwo kuma yafi karfin
116
TASKARNOVELS.COM.NG
wadatacciyar lafiya dadi a zuciyar bil'adama da
aljanu? Tambaya ta biyu ita ce, "Wacce halittace
me rai tana ci kuma tana sha amma bata kashi
da fitsari?. Tambaya ta uku ita ce"Wane abu ne
wanda idan ya baiyana yana firgita mutane da
aljanu a duk inda suke, idan (kuma kishiyarsa
ya baiyana sai su sami nutsuwa da kwanciyar
hankali?" Sa'adda Zarifa ta gama fadin
wadannan. tambayoyi guda uku sai ta zauna
akan kujerarta takasa kunne tana sauraron
amsae da jarumin farkozai bayar.Gaba dayan
fadar sai ta sake yin tsit! Mutane suka shiga
zancen zuci suna maimaita tambayoyin uku a
cikin zukatansu suna kokarin amsawa. Nan take
jarumin farko ya mike tsaye yace'Amsar
tambaya ta farko ita ce,soyayya,domin karfin
soa cikin zuciya yafi komai tunda mutum ko
aljan zai iya sallama rayuwarsa don yamallaki
masoyinsa haka kuma idan mutum yamallaki
masoyinsa yana jin tsananin farin ciki
azuciyarsa fiye da a bashi komai na rayuwa.
Amsar tambaya ta biyu ita ce babu wata halitta
wacce tana ci kuma tana sha amma bata fitsari
da kashi face shuka, domin taki ne abincinta,
kuma ana zuba ma ta ruwa ta tsotse.Har abada
shuka ba ta fitar da takin da ta tsotse daga
117
TASKARNOVELS.COM.NG
jikinta kuma ba ta fitar da ruwan da ta tsotse a
matsayin bashi da amfani a jikinta. Game da
tambaya ta uku kuwa babu abin dake firgita
mutane da aljanu idan ya baiyana face yaki,
kishiyarsa kuwa shi ne zaman lafiya" Ya yin da
wannan jarumi na farko yazo nan ajawabinsa
sai Zarifa tayi murmushi ta ce"Ya kai wannan
masoyi nawa hakika kayi matukar kokari
domin ka amsa tambaya ta farko da ta biyu daidai amma tambaya ta uku ba daidai bace don
haka sai ka koma gefe daya ka baiwa wanda ke
bayanka wuri ya jarraba sa'arsa ko zai iya amsa
tambaya ta ukun". Koda jin haka sai wannan
jarumi ya kamu da tsananin bakin ciki, nan take
zuciyarsa ta buga ya Sulale Kasa matacce. Cikin
hanzari dakaru suke ruga suka dauke gawarsa
aka yi wajen fadar da shi. Jarumi na biyu ya
matso gaba a lokacin da gaba dayan jikinsa ya
kama karkarwa tamkar an tsamoshi a cikin
ruwan Kankara a lokacin da ake hunturun
sanyi. Jarumin ya yi shiru yana tunani da nazari
a cikin Kwakwalwarsa ya tuna irin nisan tafiyar
da ya sha daga garinsu zuwa wannan birni na
Kisra da kuma ya tuno da miliyoyin darhaman
da ya kashe kafin ya sami damar shiga wannan
gasa. Jarumin ya dada tunawa cewa shi fa dan
118
TASKARNOVELS.COM.NG
sarkin garinsu ne kuma shi kadai ne da namiji a
wajen ubansa mai gadon sarauta. Da ya
tabbatar da cewa bai san amsar wannan
tambaya ta ukun ba, sai ya koma gefe daya yana
mai nuna alamar cewa ya gaza. Nan take fadar
ta rude da ihu har wasu ma na jifansa suna
cewa ya yi abin kunya. Sai da Dakaru suka yi
tsawa sannan mutane suka daina jifan da ihun,
sannan jaruman gasar suka ci gaba da amsa
tambaya ta uku. Har aka zo kan jarumi na
bakwai ba a sami wanda ya amsa dai-dai ba.
Koda aka zo kan Sarki K s?idu s?i fadar ta sake
rudewa da shewa da tafi gami da jinjina.
Maroka suka kama yiwa sarki Kusaidu
kirari,makada kuwa suka kama buga ganguna
da tambura. Sai da Sarki y tsaya a inda zai
amsa tumbayar sannan fadar tayi tsit ya
zamana ba a jin komai face numfashin jama'a. A
wannan lokaci Zarifa ta murtuke fuskarta tana
kallon sarki K s?idu kuma ta kura masa idanu.
Dama haka ta rinka yi duk sa'adda masu gasar
ke amsa tambayoyin sai idan ta ga mutum ya
amsa dai-dai sannan tayi murmushi tayi
bayanin ko ya yi dai-dai. Sarki Kusaidu ya yi
gyaran murya sannan ya yi murmushi ya ce,
"Amsar tambayarki ta uku ita ce, "Haske da
119
TASKARNOVELS.COM.NG
duhu ba wai ya ki da zaman lafiya ba. Dalili
kuwa shi ne, komai jarumtakar mutum ko aljan
idan ya tsinci kansa a cikin matsanaicin duhu
wanda baya iya ganin komai dole ne hankalinsa
ya dugunzuma ya firgice domin bai san abin da
zai faru gareshi ba. Haka kuma idan haske ya
baiyana gareshi ya sami nutsuwa da kwanciyar
hankali tun da zai iya ganin kowacce irin masifa
da za ta tunkaroshi kuma zai yi tunanin hanyar
da zai bullowa masifar ya iya tararta." Koda
sarki Kusaidu yazo nan a zancensa sai fuskar
Zarifo ya fadada da murmaushi ta ce,' Tabbas
kai ne mijina domin ka amsa wannan tamabaya
dai-dai, haske da duhu su ne amsar tamabayata
ba yaki da zaman lafiya ba. Dalili kuwa shi ne,
yaki ba kowa ne ke tsoronsa ba don jarumin da
ya yarda da kansa jarumtakarsa da Karfin
sihirinsa baya tsoron kowanne irin yaki komai
tsananinsa.Haka kuma akwai mutane da aljanu
wadande suka tsani zaman lafiya kO yaushe ma
sun fi so su ga ana cikin tashin hankali, da
kansu ma suke kiran masifu da bala'in". Zarifa
na gama wannan jawabi sai fadar ta rude da
shewa da tafi gami da bushe-bushe da kadekade. Bayan 'yan dakiku sai aka ladaftar da
jama'a suka yi shiru. Alkalan gasa suka tabbatar
120
TASKARNOVELS.COM.NG
da cewa lallai sarki Kusaidu ne ya sami nasarar
wannan gasa cikin masu son Zarifa da aure
yanzu kuma za Zan ci gaba. Da fatan an tashi
lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai
iya tuntubata ta wannan number 08138873799
kira ko whatsapp. MAZAN JIYA Littafi na biyu
2 Part H Na Abdulaziz Sani m gini Typing
Abubakar Saleh AlQuyraemey Ayi hakuri wasu
daga cikin pages din sun lalace dan haka na
tsallake wajen. tsugunna a kofar dakin ya yi ta
rusa kuka kamar ba zai daina ba. Babu irin
rarrashin da Shaulat bata yi masa ba amma sai
ya ki yin shiru bare ta tambaye shi abin da ke
faruwa. Koda ganin haka sai Shaulat tayi
tafiyarta izuwa cikin turakarta suma sauran
mutanen gidan sai suka koma cikin dakunansu
suka rufe kofofinsu. Sai da alfijir ya keto
Hantaru bai tashi daga bakin kofar Salimat ba
kuma bai daina kuka da rokon ta bude masa
kofar ba amma sai Salimat tayi biris da shi.
Lokacin da Hantaru ya tabbatar da cewar
Salimat ba za ta saurareshi ba sai ya mike tsaye
ya shiga cikin dakinsa ya bude wata katuwar
akwati ya dauko ajiyarsa ta takobin Saiful
Lujara wacce ke lullube a cikin mayafi. Hantaru
bai sake daukar komai ba a cikin dakin kawai
121
TASKARNOVELS.COM.NG
sai ya fice daga cikin gidan ya kwanto doki guda
daga cikin bargar dawakai ya hau kansa ya
kama tafiya ba guzuri babu tanadin komai.
HANTARU YA NAUSA cikin daji ya rinka tafiya
ba ji ba gani, dare da rana ko yaushe takobin
Saiful Lujara na rataye a bayansa.Duk sa'adda
ya gaji sai ya yada zango a duk inda ya ga dama,
idan kuma yaji yunwa sai ya yi farauta a cikin
daji ya samo abin kalaci. Haka dai Hantaru ya ci
gaba da tafiya yana ratsawa ta cikin
dazuzzukan masu mugun hadari,amma bisa
mamaki sai Hantaru ta ga ko sau daya bai hadu
da wata muguwar dabba da ta durfafeshi,kai ko
aljanu idan suka hangoshi daga nesa sai su
tarwatse su kama guje-guje suna neman
maboya.ldan kuwa riskarsu ya yi tsulum sai su
kama yi masa sujjada suna tuba da neman
gafara tamkar sun ga mutum a gabansa.
Al'amarin da yai matukar bashi mamaki ke nan.
Abin da bai sani ba shi ne, ba komai ne ya janyo
hakan bs face wannan takobi ta Saiful Lujara ds
ke ratayea bayansa. Sirrinta shi ne, in dai
mutum na tare da ite duk irin halittar da ganshi
sai ta ganshi firgice te razana ainun walau
mutum ko dabba ko dodo. Sannu-sannu darare
na shudewa rana na wucewa har Hantaru ya
122
TASKARNOVELS.COM.NG
shafe wata uku yana tafya har ya iso birnin
Kisra. Da shigarsa cikin garin sai ya sauko daga
kan dokinsa ya daure dokin a jikin wata bishiya
sannan ya cire takobin saiful Lujara daga cikin
mafiyafinta kuma ya zareta daga cikin kufenta
ya ruketa tsirara ya nufi gidan boka Ardusa kai
tsaye fuskarsa a murtuke har tana yatsina
saboda fusata,kuma jikinsa na tsuma. Duk inda
ya ratsa jama'a suka ganshi sai ka ga ana tashi
ana rugawa izuwa cikin gida ana kulle kofofi
saboda ganin Hantaru a cikin mugun yanayi,
kuma ga babbar takobi mai daraja a hanannsa.
Boka Ardusa na kwance a cikin turakarsa yana
faman shara barci abinsa, kawai sai yaji
turakarsa ta cika da hayaniye. A firgice ya farka
ya mife zaune domin wannen ne karo na farko
arayuwarsa da ya taba jin hayaniya a
turakarsa.Boka Ardusa na bude idanunnsa sai
ya yi arba da dukkanin hadimansa na aljanu
sun cika dakin jikinsu na kyarma kamar ace
kyat! su tsure da gudawa. Cijin fushi boka
Ardusa ya daka musu tsawa ya ce, "Ina delilin
shigowarku nan turakata ba tare da izinina ba?
Lallai gaba dayanku sai kun dandana kudarku
domin kun sa na farka a lokacin da na ke cikin
yin barcina mai dadi". Koda jin wannan batu sai
123
TASKARNOVELS.COM.NG
shugaban hedimansa ya zube a Kasa gaban
boka Ardusa ya ce, "Ya shugabana ai yau mu da
kai duk muna cikin mummunan bala'i ne. Mun
zo gareka ne domin ka gaggauta nemo mana
wajen buya har kai kanka kuwa, ka sani cewa a
halin yanzu ga jarumi Hantaru can ya durfafo
wannan gida naka dauke da takobin Saiful
Lujara. Kuma ya taho ne domin ya hallakaka
bisa cin amanar sarki da kayi ka kwanta da
matarsa aka sami cikinsa." Koda jin wannan
batu sai boka Ardusa ya daka tsalle sama ya
tumu da kasa. ldanunsa suka zezzaro,kawai sai
ya ruga da gudu izuwa cikin dakinsa na halwa
domin ya duba wadansu ababan dogaronsa na
tsafi. A wannan lokaci ne wadannan hadiman
aljanu nasa da ya baro a turakarsa duk suka
tarwatse suka tashi sama suka rinka tsala gudu
cikin dimauta ba tare da sanin inda suka dosa
ba. Boka Ardusa ya yi sauri ya debo dukkanin
guraye da layu na tsafinsa sannan ya dauko
kayan yakinsa ya rugo waje da gudu daga cikin
dakin da nuim shima ya tashi sama, kawai sai ya
ga Hantaru tsulum! A gabansa. Boka ardusa ya
yunkura da nufin ya shafi weta laya da ke
wuyansa, sai Hantaru ya sa takobin Saiful Lujara
cikin zafin nama ya sare kan boka Ardusa. Kan
124
TASKARNOVELS.COM.NG
yai tsalle sama ya rabu da gangar jikin, kawai
sai hantaru ya daga daya hannun nasa ya cafo
gashin kan Ardusa a lokacin da gangar jikin ta
sulale kasa ta fadi.Kawai sai Hantaru ya juya
juya ya fice daga cikin gidan ya durfafi gidan
sarki Kusaidu. Sarki Kusaidu na kwance bisa
gado yana jinyar rashin lafiya, kawai sai wani
hadiminsa ya shigo cikin turakar da gudu yana
haki, ya fadi Kasa ya ce, "Ya shugabana gari fa
babu lafiye". Cikin Karfin hali Sarki ya dubeshi
ya ce Yaki ne ya taso mana yanzu-yanzu?".
Hadimi ya ce, "Ai abin da ya taso yanzu yafi
karfin yaki domin danka ne Hantaru ya dawo
rike da takobin SAIFUL LUJARA, har ma yaje
gidan boka Ardusa ya yanko kansa. Kode jin
wannan batu sai sarki Kusaidu ya mike zumbur!
Cikin tsananin farin ciki tamkar bai tabe yin
wani ciwo ba ya ruga waje da gudu yana mai
bude hannayensa yana kwalawa Hantara kira A
wannan lokaci gaba dayan Dakarun gidan sun
dimauce sai guje-guje suke da iface-iface suna
neman