x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - MAZAN JIYA 2

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 55701 words

Category: Romance Story +18

Views 201

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
na farko a bakin
tekun bahar Sufiya. A CAN BANGAREN kuwa,
bayan sun binne na su su sarki Dujalu
gawarwakin kuma an kafa tantuna an duba
marasa lafiya kowa ya dawo cikin haiyacinsa
kuma an kafa tantuna sai sarki Dujalu ya
kadaita da yar uwarsa Hursiya a cikin tantinsa
inda ta rinka sa masa magani a jikin raunikan
da ke jikinsa. Koda ta ga raunikan sun kai guda
bakwai kuma duk masu zurfi ne, wasu ma sai
da ta dinke masa fatar sai zuciyarta ta karaya
bata san sa'adda ta fashe da kuka ba. Cikin
matukar mamaki sarki Dujalu ya dubi Hursiya
ya ce, "Ya ke 'yar uwata ina dalilin wannan kuka
naki?" Hursiya ta dago kai ta dubi sarki Dujalu
cikin tsananin damuwa ta ce, "Ya kai dan uwana
173

TASKARNOVELS.COM.NG
ka sani cewa a duniya bani da kowa face kai.
Zuciyata ta karaya bisa ganin wadannan
manyan raunika na jikinka har ina ganin cewa
abu ne mawuyaci mu sami nasarar wannan
yaki. Yanzu idan babu kai ya ya zan yi rayuwa a
diniya?" Sa'adda Hursiya ta zo nan a zancenta
sai sarki Dujalu ya kamu da tsananin tausayinta
har idanunsa suka ciko da Kwalla sannan ya ce,
Ya ke yar uwata kiyi sani cewa duk irin gumu da
bala'in da za a yi a wannan yaki a ba zan taba
mutuwa ba ammma bincike ya nuna mini cewa
zan shiga mugun yanayi kamar zan mutu da ni
da babban jarumi na cikin abokan gabarmu,
wato wannan yaro Inmal dan sadauki Hibru. Ni
da shi duk ba zamu mutu ba amma duk irin
yanayin da na shiga sai shima ya shiga.A cikin
binciken nawa na gani cewa mutum hudu ne
kacal za su tsira da rayuwarsu a wannan yaki
amma na kasa gano ko su waye, ragowar
mutum biyun bayan ni da Inmal. Abin da nake
so da ke shi ne, kafin a ci gaba da wannan yaki a
karo na biyu ki sulale ki bar wajen nan gaba
daya ki koma can nahiyarmu ki ci gaba da
mulkin Kasarmu ta Hawarul din in da muka
baro mata, yara da tsofaffi, domin idan har baki
koma ba gaba dayan jama'armu za su shafe a
174

TASKARNOVELS.COM.NG
doron kasa a manta damu har abada. Idan har
Inmal ya rigani dauko takobin Saiful Lujara, ki
sani cewa hadimina aljani Baizurul Aufan na can
a baya cikin dajin Saurul yana jiranki domin
tuntuni na shirya hakan.' Lallai za ku yi wannan
tafiya lafiya har ki isa gida babu wani tsautsayi
da zai sameki" Sa'adda sarki Dujalu ya zo nan a
zancensa sai Hursiya ta sake fashewa da
matsanaicin kuka kuma ta rungumeshi ta ce, "Ta
ya ya kake tsammanin zan iya tafiya na barka
anan ana wannan masifaffen yaki? Lallai ba
zanje ko ina ba in ba tare da kai ba, sai dai nima
ajalina ya riskeni anan din. Ai sadauki Hibru ya
yi bayanin gaskiya da ya ce rayuwa ba ta da
amfani idan babu masoyi. Ka sani cewa mulki
da dukiya ba za su taba haifar da kwanciyar
hankali ba a rayuwata muddin babu kai a kusa
da ni. Ka tuna cewa tun da na taso ban san
uwata ba kuma ban san ubana ba sai kai. Babu
wanda na shaku da shi a duniya sama da kai.
Babu irin jin dadin da baka bani ba a kullum
kana riritani baka son koda kuda ya sauka a
jikina. Waye zai iya yi mini irin wannan gata da
ka yi mini? Waye zai iya kare lafiyata kamar
yadda ka kare kuma waye zai soni kamar yadda
ka soni? Na ka-na ka ne har abada ba zan taba
175

TASKARNOVELS.COM.NG
samun madadinka ba. Ina tabbatar maka da
cewa idan zai zamo ni kadai ce na rayu a filin
yakin nan kuma na sami ikon mallakar takobin
Saiful Lujara, ba zan koma gida ba na ci gaba da
rayuwa sai dai na binne kaina a kusa da
kabarinka domin mutuwa ce kadai za ta iya
kawar mini da bakin cikin rashinka." Lokacin
da Hursiya tazo nana zancenta sai shima sarki
Dujalu ya fashe da matsanaicin kuka kuma ya
kankameta a kirjinsa yana mai cewa'Hakika
abin da ke shirin faruwa a gareni yana neman
ya zama dai-dai da yarda rayuwar sadauki
Shaddadu na birnin Kufa ta kasance." Koda jin
wannan batu sai Hursiya tayi wuf ta janye
jikinta daga cikin na sarki Dujalu suka fuskanci
juna sannan ta ce, "Mene na ya faru ga rayuwar
sadauki Shadaddu?". Sarki Dujalu ya sunkui da
kansa kas ya yi ajiyar zuciya sannan ya fara ba
ta labari kamar haka. AWANI ZAMANI can baya,
wanda ya zo dai dai da zamanin sadauki
Hantaru na bimin Kisra,an yi wani azzalumin
sarki a birnin Kufa wanda ake kira da suna
Lafaru ibini Hurdas. Sarki Lafaru ya mallaki
dukiya mai tsananin yawan gaske, kuma sai da
ya shekara arba'in a duniya bai ta6a yin aure ba
kuma bai taba yin rashin lafiya ba koda kuwa
176

TASKARNOVELS.COM.NG
ciwon kai na tsawon dakika daya. Sarki Lafaru
ya kasance sadaukin sadaukai mai dakawa maza
gumba a hannu domin a tarihin rayuwarsa ya
ziyarci yakoki guda dari da ashirin yana samun
nasara kuma ko karce jikinsa ba a ta6a yi ba a
wajen yaki.Saboda tsananin jarumtakarsa, zafin
namansa da kuma tsagwaron sa'a. A rayuwar
sarki Lafaru bai taba yin tsafi ba, kuma tsafi
baya cinsa, baya dogara da komai face
tsagwaron karfin damtse. A kasarsa gaba daya
ba a yin addini ko wanne iri, idan kuwa aka
kama mutum yana wani addini koda a 6oyene
sai an kashe shi. Sarki Lafaru na da wata
muguwar al'ada ta yiwa mata fyade, domin a
duk sa'adda ya ga kyakkyawar mace in dai ya yi
sha'awarta ko matar wa ce sai ya mangareta ta
sume sannan ya biya bukatarsa da ita. Daga
wannan rana sai ya sa a tsare wamnan mace
har tsawon wata shida sai an tabbatar da cewa
bata sami ciki da shi ba sanann zai sa a saketa.
Idan kuwa ta sami ciki ta ke zai sa a hallakata.
Dalili kuwa shi ne, ko kadan sarki Lafaru baya
son ya sami magaji a duniya saboda
jarumtakarsa ta gado ce iyaye da kakanni,
ma'ana babansa ya kasance, shima kakansa
haka yake kuma abin ya biyo salsala tun sarkin
177

TASKARNOVELS.COM.NG
kufa na farko. Lokacin da sarki Lafaru ya sami
tarihin wannan al'amari a cikin kundin tarihin
sarauta na gidansu sai ya kudurce a zuciyarsa
cewa shi ne zai zamo sarki na karshe mai
wannan baiwa ta jarumtaka da karfin lafiya,
don haka ba zai taba yarda ya haifi magajinsa
ba. Wani abin mamaki dangane da rayuwar
sarki Lafaru shi ne a duk shekara sau daya yake
sawa a nemo masa budurwa wacce babu
kamarta a fagen kyawu a kasarsa. Ana kawota
sai ya sumar da ita ya biya bukatarsa da ita.Sai
da ya shekara ashirin akan karagar mulki yana
wannan muguwar dabi'a. A cikin shekara ta
ashirin da daya ne al'amura suka zo da sauyi
domin a wannan shekarar ne aka kawo masa
wata tsaleliyar budurvwa mai suna Sharlis
wacce tsananin kyawunta ya fi gaban kwatance.
Da la'asar sakaliya sarki Lafaru na zaune a
fadarsa an kewayeshai ana fadanci sai ga
Sharlis an shigo da ita. Nan take gaba dayan
mutanen da ke fadar suka rude suka dimauce
bisa ganin tsananin kyawun Sharlis. Shi kansa
sarki Lafaru bai san sa'adda ya mike tsaye ba
jikinsa ya kama tsuma ya taka kafafunsa ya nufi
inda Sharlis ke tsaye sabanin yadda ya saba yi a
duk shekara, sai dai akai budur war har
178

TASKARNOVELS.COM.NG
gabansa. Sarki Lafaru ya iso daf da Sharlis ya
tsaya yana mai kura ma ta idanu a lokacin da
gaba dayan jikinta ke karkarwa saboda tsoro
kuma hawaye na zuba a idanunta. Sarki Lafaru
ya daga hannunsa da nufin ya make Sharlis
domin ta suma ya biya bukatarsa da ita amma
sai ya kasa dukanta. Al'amarin da ya matukar
baiwa kowa mamaki ke nan a fadar aka
mimmike tsaye ana al'ajabi. Koda ganin haka sai
kunya ta kama sarki Lafaru. Nan take ya yi
tsawa ga jama'a ya ce, "Kowa ya fice daga cikin
fadar". Cikin firgici jama'a suka fice da gudu ya
zamana saura su biyu kacal a cikin fadar. Nan
fa sarki Lafaru ya kamo Sharlis ya kwantar da
ita akan karagarsa ta mulki ya biya bukatarsa
da ita. Faruwar hakan ke da wuya sai yaji kansa
ya sara ya kama ciwo. Al'amarin da ya kama
matukar razanashi ke nan kuma ya harzuka.
Kawai sai ya zare takobi zai sare Sharlis. Bisa
mamaki sai ya ga ko gezau bata yi ba bare ta
firgita.Sharlis ta dubeshi a fusace ta ce'Mene ne
ya hanaka ka kasheni? Ai gwara ka kasheni
domin na huta da bakin cikin da ka dasa mini a
zuciyata. Ka yi sani cewa a lokacin da
dakarunka suka je kamoni a can kauyenmu na
Bairul sai da suka kashe iyayena da duk
179

TASKARNOVELS.COM.NG
mutanen gidanmu sannan suka bunkawa
gidanmu wuta kuma suka kwashe duk dukiyar
gidan saboda kawai mahaifina ya ce ba zai
bayar da ni ba. Ka sani cewa yau shekarata
goma sha takwas a duniya kuma tun da aka
haifeni ban taba fita ko ina ba daga cikin
gidanmu kai asalima ban taba ganin wani da
namiji ba face mahaifina domin babu maza a
gidanmu sai mata. A ranar da dakarunka suka
kawo mana farmaki ne na ga maza a rayuwata.
Kaine namijin farko da ya sanni 'ya mace kuma
kaine za ka zamo na karshe domin bokan
mahaifina ya tabbatar
mini da haka. Ya kai wannan sarki kayi sani
cewa tun da aka
haifeni mahaifina ke 6oyeni saboda tsoron kada
na fado
hannunka bisa muguwar dabi'arka da ka saba yi
akan
kyawawan mata, ashe shuka ya yi a idon
makwarwa.
Kuyangar mahaifina ce wacce ya aminta...

180

TASKARNOVELS.COM.NG
ashe shuka yayi a idon makwarwa domin
kuyangar mahaifinace wacce ya aminta da ita
fiye da kowa a duniya kuma itace wadda ta
reneni har na girma taci amanarsa saboda
kwadayin abin duniya ta labartawa dalkarunka
batuna.Tabbas bukatarta ta biya ta sami dukiya
mai yawan gaske ta siyar da mutuncina
gareka.To kasani cewa sakamakon wannan cin
zarafi dakayi mini daga yau burinka ya rushe
lallai sai na haifa maka magaji,daga yau sai
rayuwarka gaba daya ta sauya kai da samun
cikakkiyar lafiya har abada,jarumtakar dakake
takama da ita ta dakushe,duk dukiyar daka tara
ta zalunci sai ta kare,sai ya zamana cewa babu
mai fada aji a garin nan face ni Kafin sharlis ta
gama rufe bakinta tuni sarki lafaru ya kai mata
wawan sara da nufin ya cire mata kai.Bisa
mamaki sai yaga takobin ta wuce ta cikin jikinta
kamar ratsawar ba.

Gaskiya wannan zalunci yayi yawa kuma ni dai
bana goyon bayan sa.

MAZAN JIYA
181

TASKARNOVELS.COM.NG
Littafi na biyu 2
Part L
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey

Koda ganin haka sai sharlis ta bushe da dariya
sannan tace,"Ai tuni alkadarinka ya karye tun
sa'adda ka kasa sumar dani lokacin dazaka tara
dani.Bazaka iya kasheniba kuma bazaka iya
cutar daniba domin daga yau tsafi yafara tasiri
ajikinka.Abinda nakeso dakai kawai shine,ka
rufawa kanka asiri kabar komai a zuciyarka bisa
abinda yafaru yanzu tsakanina dakai.zaifi kyau
kasa a kebeni a gidan sarautar nan inda babu
mai ganina har izuwa lokacin dazan haife maka
danka.Idan ka bini kamar yadda nakeso zan iya
dawomaka da duk abinda karasa amma sai
bayan dana yagirma ya gajeka,idan kuwa kayi
mini taurin kai haka zan barka cikin takaici har
izuwa karshen rayuwarka kuma ina tabbatar
maka cewa bazaka maimaita shekarunka ba a
182

TASKARNOVELS.COM.NG
duniya.wato bazaka shekara tamanin ba a
duniya tunda yanzu ka cika arba'in daidai.Wannan shine furucina na karshe gareka
yanzu saika sanya akaini bangaren dazan zauna
acikin wannan gida naka. Lokacin da sharlis
tazo nan a jawabinta sai sarki lafaru ya fusata
ainun yarufeta da duka.Bisa mamaki saiyaji
ashe iska kawai yaketa duka kawai,gata dai
tsaye a gabansa tana tayi masa dariya amma ya
kasa taba jikinta.Koda ganin haka sai sarki
lafaru yakamu da tsananin bakin ciki yafashe da
kukan takaici.Babu abinda yafiyi masa ciwo face
ganin yadda 'ya mace ta gagareshi alhalin
manyan mazaje ma yazame musu GUGUWAR
ANNOBA,yazamo tamkar dodo a nahiyar gaba
daya har anayi masa kirarida KURA MAI
TARWATSA GARI!Yau gashi kura ta zama akuya
domin bazata iya tsorata kowaba.Sai da sarki
lafaru yadade a tsaye yana kukan takaici sannan
sharlis ta daka masa tsawa tace,"zakayi abinda
na umurceka dayine kokuwa sai na tara
fadawanka da jama'ar gari na tozartaka
agabansu kowa ya san cewa yanzu kai ba kura
bane akuyace. Koda jin haka sai sarki lafaru ya
kwalawa sarkin gida kira.Nan take sarkin gida
yashigo da gudu yafadi gaban sarki lafaru
183

TASKARNOVELS.COM.NG
yadubi sarkin gida yace"maza ka yiwa gimbiya
jagora izuwa bangaren nan daba'a taba
budeshiba
Sarki lafaru yace ina son yanzu-yanzu a bata
bayin dazasu dinga yimata hidima kuma kada
kowa ya kusanci inda take face kuyangin
nata,Koda jin wannan umarni sai sarkin gida ya
cika da tsananin mamaki bisa jin wannan sabon
umarni wanda ya saba da al'adar iyaye da
kakannin sarki. A tarihin gidan sarautar babu
wani sarki da ya taba ajiye mace acikin gidan sai
dai a wajen gidan sarautar amma yau sai gashi
sarki lafaru yakarya wannan ka'ida.Bisa wannan
daliline sarkin gida yatsaya nuku-nuku ya ki bin
umarni.Aikuwa sai sarki lafaru yadaka masa
tsawa,cikin rawar jiki sarkin gida yamike tsaye
zumbur yayiwa sharlis jagora izuwa cikin gidan
sarautar,sharlis ta waigo tayiwa sarki lafaru
murmushin mugunta.Nan take sarki lafaru
yafadi kasa yasake fashewa da kukan zuci don
kada hadiman gidan sujiyo sautin kukansa. Daga
wannan rana komai na rayuwar sarki lafaru ya
sauya,kuma al'amura suka sauya gaba daya
birnin ya zamana cewa matsafa sun sami yancin
kansu suna iya yin harkokinsu a ko'ina kuma
koyaushe sabanin da can da idan aka kamasu
184

TASKARNOVELS.COM.NG
ana kashesu.Mutane suka rinka yin addinai iriiri.a duk bayan kwana talatin ko arba'in sai
sarki yakwanta rashin lafiya har sai an nemo
likitoci sun kawomasa daukiwani lokacinma sai
bokaye sun bada taimako sannan yake samun
lafiya.Duk irin zaluncin da sarki yasabayi na
kwacewa talakkawa dukiyarsu ya daina kuma
har tsawon shekara ukku bai kara yiwa wata
budurwa fyadeba.Gaba daya mutanen birnin
kufa sai da suka cika da matukar mamaki bisa
ganin halayyar sarki ta sauya a lokaci guda.Kai
bama mutanen birninba hatta sarakunan sauran
kasashe dake makwabtaka dashi.Dama dukkan
sarakunan suna tsananin tsoron sarki lafaru
suna biyayyar dole agareshi domin duk shekara
sai kowannensu yakawo haraji maiyawa gami
da bayi. Lokacin da'aka sami shekara ukku da
samun sauyin al'amura ga sarki lafaru sai wani
sarki da ake kira Nurbas wanda ke mulkin kasar
zaruf yakawo haraji da bayi.
Dama can shi sarki nurbas gawurtaccen
matsafine mai taurin kai kuma yanada
zakwakuran mayaka ababan dogaro.A lokacin
da sarki lafaru ya aika masa da sakon ya aiko da
haraji sai yayi taurin kai ya bijirewa
umurnin.Nan take sarki lafaru yayi shirin yaki
185

TASKARNOVELS.COM.NG
shi kadai ya shiga birnin zaruf ya rinka
ragargazar dakaru har sai da ya shiga cikin
fadar sarki Nurbas aka rasa wanda zai iya
kawar dashi.Koda sarki Nurbas yaga karfin
tsafinsa yaki yayi tasiri akan sarki lafaru kuma
ya tabbata kasheshi zaiyi ya mallake kasarsa sai
ya fadi kasa yana kuka da tuba yayi ta neman
gafara,kuma yayi alkawarin cewa duk shekara
zai rinka bayar da harajinsa da bayi sama dana
kowanne sarki.Koda ganin yadda sarki Nurbas
ya wulakanta agaban fadawansa da jama'arsa
kuma ya mika wuya sai sarki lafaru yafasa
kasheshi ya bushe da dariya yafice daga cikin
fadar yatafi abunsa.SARKI Lafaru na zaune a
fadarsa,fadawa sun kewayeshi ana tafiyar da
harkokin mulki sai ga manzo daga kasar zaruf
dauke da wasika.Da zuwan manzon sai ya zube
kasa ya kwashi gaisuwa cikin alamun tsoro duk
jikinsa na karkarwa ya mikawa magatakarda
wasikar shikuma ya warware wasikar yafara
karantata a fili kamar haka; Takarda daga sarki
mai cikakken iko wanda a halin yanzu ya sami
yancinsa Sarki Nurbas na birnin zaruf. Zuwa ga
makaskancin sarki wanda a halin yanzu yazama
akuya ba kuraba..."Koda magatakarda yazo nan
a karatun wasikar sai muryarsa ta sarke kuma
186

TASKARNOVELS.COM.NG
hannunsa yakama karkarwa saboda tsoron
kada sarki ya huce haushi akansa bisa abinda
yakaranto na kaskanci.Lokacin da sarki lafaru
yaji irin wannan cin mutunci da sarki Nurbas
yayi masa a wasika sai ya kamu da tsananin
takaici yaji kamar zuciyarsa zata faso kirjinsa ta
fado kasa,yatuna irin tsananin tsoronsa da sarki
Nurbas keji ada ,amma yanzu shine harda
zaginsa cikin wasika.Cikin karfin hali da
barazana sarki lafaru ya dakawa magatakarda
tsawa yace maza kaci gaba da karanta wannan
wasika muji karshenta nan take magatakarda
yaci gaba da karatun wasika muryasa na rawa
kamar haka;Yakai sarki lafaru mai birnin kufa
kayi sani cewa a halin yanzu tsirara nake
kallonka babu sutura a jikinka,dalili kuwa kayi
sake har sharlis 'yar boka Narwas ta karya
alkadarinka.Nasan cewa kamanta da kowanene
boka Narwas to kayi saurare dakyau yanzu zan
tunamaka shi domin kasan cewa tsohon abokin
gabarkane wanda ya mutu da bakin cikin daka
turamasa amma kuma sai gashi 'yarsa sharlis
zata dauki fansa akanka.
Nan take magatakarda yaci
gaba da karatun wasika muryasa na rawa kamar
187

TASKARNOVELS.COM.NG
haka;Yakai sarki lafaru mai birnin kufa kayi sani
cewa a halin yanzu tsirara nake kallonka babu
sutura a jikinka,dalili kuwa kayi sake har sharlis
'yar boka Narwas ta karya alkadarinka.Nasan
cewa kamanta da kowanene boka Narwas to
kayi saurare dakyau yanzu zan tunamaka shi
domin kasan cewa tsohon abokin gabarkane
wanda ya mutu da bakin cikin daka turamasa
amma kuma sai gashi 'yarsa sharlis zata dauki
fansa akanka.yakai wannan sarki kayi tunani
izuwa kimanin shekaru ashirin baya,a shekarar
daka hau mulki bayan mutuwar mahaifinka
sarki Hurdas. bayan an nada Sarki lafaru a
matsayin sabon sarki,akwai wata rana da ya tafi
rangadi izuwa kauyukan kasarsa har tsawon
kwana arba'in yana kewaye kauyukan kamar
yadda kowane sabon sarki keyi idan ya hau
karaga bisa al'ada.Kauyen daya ziyarta na
karshe shine kauyen Bairul. Da isarsa kauyen
sai ya umurci dukkan attajiran garin dasukawo
masa gaba dayan dukiyarsu.gaba dayansu sai
suka cika umurnin face mutum daya wani
takadarin boka mai suna Narwas wanda kowa
ke shakkarsa a garin.Boka Narwas bai amsa
kiransa ba kawai sai yayi zamansa a gidansa
kuma ya aiko gidan hakimin yace a gaya masa
188

TASKARNOVELS.COM.NG
cewa bazai amsa kiransaba kuma bazai bada
komai ba daga cikin dukiyarsa,koda yaji wannan
batu sai ya harzuka yasa akayi masa jagora
zuwa gidan boka Narwas Da zuwansa ya iske
boka Narwas a kofar gidansa yarike kugu yana
jiransa domin yasan cewa lallai yana
tafe,saboda boka narwas ya yarda da kansa a
fagen tsafishiyasa yake ganin bazaka iyayi masa
komai ba kuma a tunaninsa zai iya hallaka sarki
lafaru farat daya. Da zuwan sarki lafaru sai boka
narwas yafara watsa masa wutar tsafi,bisa
mamaki sai yaga gashi dai wutar ta zuba jikinshi
amma sai takasa konashi.Cikin fusata yaci gaba
da watsa masa abubuwan sihiri kamar
kibiyoyi,macizai da kunamaiamma duk sai suka
ki yin tasiri akansa.Nan take sarki lafaru ya
shako wuyansa da hannu daya ya dagashi
samasai gashi yana kakarin mutuwa idanunsa
sukayi kulu-kulu kamar zasu fado kasa
kafafunsa na wutsil-wutsil a sama,kawai sai ya
fyadashi da kasa ya baje wanwar a sume.Kafin
boka narwas ya farfado daga dogon suman
dayayi sai yasa aka shiga gidansa aka kamo
iyayen boka narwas da matarsa gami da wata
kanwarsa kyakkyawar gaske mai suna lasirat
dakuma 'ya'yansa guda ukku kananan yara biyu
189

TASKARNOVELS.COM.NG
mace daya.A wannan lokaci matar narwas tana
dauke da tsohon ciki haihuwa ya kogobe,amma
saboda wulakanci a kasa dakarunsa suka rika
janta suna fincikarta tana ihu tamkar suna jan
mushe Bayan anzo da iyalan boka Narwas
gaban sarki lafaru sai yasa aka daddauresu a
jikin dirkar gini,shikuwa boka Narwas yasa aka
dagashi sama aka daureshi sannan aka watsa
masa ruwa ya farfado.Koda Narwas yabude
idonsa yatsinci kansa daure ajikin dirka kuma
yaga dukkan iyalansa da iyayensa a daure sai
hankalinsa ya dugunzuma yakurma uban ihu
yafara kokarin kwance daurin da akayi masa da
karfin tsafi amma sai tsafin yaki yayi tasiri.Koda
ganin haka sai sarki lafaru ya bushe da dariyar
mugunta sannan ya murtuke fuskarsa kamar an
aiko masa da sakon mutuwa yakama gashin
kan narwas ya finciko baya da karfi,yayi ihu
sakamakon zafin dayaji,kawai sai ya tofamasa
yawu a fuska yabude baki cikin kakkausar
murya yace.;Ya kai wannan makaskancin boka
kayi sani cewa kayi babban kuskure har da
kake zaton zaka iya bijire mini.Yanzu kayi laifi
har guda biyu.Na farko ka karya dokar kasata
kayi tsafi wanda hukuncinsa kisa ne akanka.Na
biyu nabaka umurnin ka kai min dukiyarka kaki
190

TASKARNOVELS.COM.NG
kaiwa.Ka sani cewa kaine mutum na farko daya
kawo raini a cikin mulkina kuma yakarya
dokata saboda haka bazan kasheka ba sai dai
na nuna misali akanka domin ka zamo darasi
akan masu sha'awar jaraba taurin kai a
garemu.Lallai zan dandana maka azaba irin
wacce ba'a taba dandanawa wani ba kuma zan
cusa maka bakin ciki a zUciyarka wanda har
karshen rayuwarka bazaka
End Ads