x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - MAZAN JIYA 2

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 55701 words

Category: Romance Story +18

Views 208

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
kofar suka yi a
karon farko, lokaci daya kuma suka tsuke
bakinsu suka yi tsit tamkar mutuwa ta gifta ta
tsakaninsu. Sarki ya dubi wasu zakwakurarun
dakarunsa mutum hudu ya ce da su maza ku
kama wannan baki ku kaisu kurkuku ku kullesu,
lallai ba kalau suke ba aljanu ne suka shafesu.
Gama fadin hakan da wuya sai wadannan
dakaru hudun suka tasarwa su Lafaru. Da zuwa
sai suka kai hannu zasu cafkesu, cikin matukar
zafin nama na gaban kwatance boka Muzafar ya
cafi hannun nasu su hudun a kuma lokaci guda
ya kakkarya su, tamkar ya karya sillen kara.
Dakarun suka rusa ihu tare da gaduwa kasa, kaji
aikin sadaukai maganin maza.
Koda sarki da sauran dakarunsa suka ga abinda
ya faru sai duk suka zare makamansu uka afka
wa su boka Muzafar, kawai sai lafaru ya ruga
izuwa maboyarsa ya labe, shiko boka Muzafar
sai ya tari rundunar shi kadai aka kacame da
245

TASKARNOVELS.COM.NG
mummunan yaki. Nan fa boka Muzafar ya
gagaresu kuma ya addabesu ya zamana cewa
baya saransu da takobinsa sai dai ya kare
dukkanin harinsu, sannan ya riga gabza masu
naushi da hannu da kafa, komai girman kato
idan boka Muzafar ya yi masa naushi daya sai ya
kife kasa kuma ba zai sake mikewa ba. Boka
Muzafar ya rinka tsale a saman dakarun nan
yana shawagi tamkar tsuntsu mai fuka-fukai,
yayi tq zubar da su kasa yana masu sarkiya ya
hana dawa tsayuwa, kafin rabin sa'a ta cika ya
bazar da mutum dari a kasa.
Koda sauran dakarun nan suka ga abinda ke
faruwa sai suka zubar da makamansu suka mika
wuya, sarkinsu ne kawai ya ki mika wuya, kawai
sai ya sakko daga kan dokinsa ya gyara
tsayiwarsa kuma ya rike takobinsa da hannu
biyu ya tsaya cak a waje daya.
Koda ganin haka sai boka Muzafar ya dubeshi
saman yayi murmushi ya ce Ya kai wannan sarki
mene ne dalilin da yasa ba zaka mika wuya a
gareni ba, alhalin kasan cewa ba zaka iya samun
snasara a kaina ba?

246

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan tambaya sai sarkin yayi ajiyar
zuciya cikin alamun takaici ya ce Ya kai wannan
Sadauki mai jarumtaka ta ban al'ajabi yi sani
cewa har abada sarki sarki ne, bazai taba mika
wuya a rabashi da mulkinsa, dukiyarsa ko kuma
yayansa ba face bisa dole idan ya ga ya kasa
kare kayansa, ya za a yi n dauki yata ta cikin
kuma da hannuna na baka ita aro bansan me
zaku yi da ita ba, kuma ma bn san ka ba, ai sai
dai ku fara kasheni sannan kuje ku dauketa.
Da jin wannan batu sai boka Muzafar ya risina
ga sarki ikin girmamawa ya kai gaisuwa tare da
cewa Ni din nan ba sarki bane na kasance boka
ne, amman ina girmama sarauta, ya kai wannan
sarki hakika ka burgeni da ka zama mai kishin
jama'arka, mulkinka gami da iyalanka. Nikam.ba
zan kasheka hakazalika bazan kashe kowa a
cikin garin nan ba domin kawai nazo daukar
yarka, amman fa duk wanda yayi gigin hanani
daukarta to fa lallai ne zai rasa hanaye gami da
kafafu, idan har baka son wannan birni naka ya
zama na nakasassu ina mai shawartarka daka
bani Gimbiya Rahila salin alin na tafi da ita.
Da jin hka sai sarki ya daka wa boka Muzafar
tsawa ya ce da shi Bafa zai yuwuba, idan har
247

TASKARNOVELS.COM.NG
kaga ka tafi da ita totabbas sai dai idan bana
numfashi.
Lokacin da boka Muzafar ya ji wannan batu sai
ya fisata ainun ya zare takobinsa ya ruga izuwa
kn sarki, shima sarkin sai ya daga takobinsa
sama ya ruga gareshi, saura kiris su hadu sai
kawai sukaga gimbiya Rahila ta dako wawan
tsalle tare da dura a gabansu, duk su biyu sia
suka ja da baya suka yi cirko-cirko kamar
zakaru suna masu kallonta cikin mamaki bisa
yadda akayi ta bayyana tsulum a gabansu.
Gimbiya Rahila ta kalli mahaifinta a lokacin da
idanunta suka ciko taf da kwalla, suka fara
zubar da hawaye ta ce Haba ya abbana yanzu
akna rayuwata kadai sai ka bari a maishe da
jama'arka nakasassu, ka tuna cewa a garin nan
akwai iyayenka, kakanninka gami da yan
uwanka, kuma su ka fara samu kafin ka sameni,
kada ka manta ni ya mace nake, mokai daran
daewa dole ne muyi aure mu rabu ko da kuwa
wani bai zo ya rabani da kai da karfin tsiya ba,
ina mai rokonka da ka hakura ka bayar da ni ga
wadannan mutanen domin naje nayi masu irin
aikin da nake so, sabida bana son mutum daya
ya jara cituwa a wannan birni bisa sanadiyyata,
248

TASKARNOVELS.COM.NG
daga kjarshe idan da rabon sake saduwa
sainkaga na dawo gida, idan kuma na mutu acan
sai ka rungumi kaddara domin ita rayuwa tana
da lokacinta, idan babu mutuwa ai akwai tsufa
da rashin lfiya.
Lokacin da Gimbiya Rahila ta zo nan a zancenta
sai jikin sarki yayi sanyi, kawai sai ya karasa
gareta ya rungumeta suka gashe da kuka tare
domin tunda aka haifi Gimbiya Rahila bata taba
rabuwa da mahaufinta ba daidai da rana daya,
dare da rana suna tare har ta girma ta cika
budurwa face makwanci idan dare yayi.
Ko da ganin yadda sarki da Rahila ke kuka
rabuwa da juna sai tausayinsu ya kama boka
Muzafar da sarki Lafaru har basu san sa'adda
idanunsu suka cika da kwalla ba.
Nan take boka Muzafar ya ji yayi nadama bisa
wannan babban buri da yasa a gabashi, tunda ga
shi a sanadinyyar haka ya zama bakin takobi
mai raba mai masoya. Boka Muzafar ya tuna
cewa shifa a yanzu bashi da kowa a duniya
iyayensa sun mutu tun yana yaro dan shekara 6
matarsa ta mutu a lokacin da ta zo haihuwar
fari, dan cikin nata ma sai ya zo a mace, to tun
249

TASKARNOVELS.COM.NG
daga sannan bai sake marmarin yin aure ba,
bugu da kari tun yana karami aka kmashi a
matsayin bawa, aka daukeshi daga garinsu na
asali aka tafi da shi can wata nahiyar da ban da
shi da dangin iya balle na baba.
A lokacin ne aka siyar da shi ga wani
shahararren boka wanda yayita bauta a gareshi
har ya shekara ashirin da biyar, a sannan ne mai
gidan nasa ya mutu ya gaji sirrinkan tsafinsa
saboda tsananin biyayyar da yayi wa mai gidan
nasa.
Koda boka Muzafar ya tuna cewa shifa yanzu
bama zai tuno asalin inane mahaifarsa ba, balle
ya tuno da danginsa ba, sai ya koma can gefe
daya ya hada kai da gwiywa ya kama kuka. Yana
cikin wannan hali ne yaji an dafa kafadarsa,
koda ya dago kainsai yaga ashe sarki Lafaru ne
tsaye a kansa, koda Lafaru yaga hawaye a cikin
idanun boka Muzafar sai jikinsa yayi sanyi
sannan ya ce da shi Y kai wannan shu'umin
boka kuma sadaukin boye ina dalilin wannan
kuka naka alhalin ga shi bukatarmu ta biya,
mahaifinta ya hakura zai bamu Gimbiya Rahila.

250

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan tambaya sai boka Muzafar ya
yi ajiyar zuciya sannan ya share hawayensa ya
ce Ya kai abokin tafiyata, ka sani cewa duniya
babu ranar bakin ciki kamar ranar rabuwa da
masoyi, hakika na kamu matuka da tausayin
wannan sarki da yarsa, bisa yadda zasu yi
rabuwar dole ba a son ransu ba, kuma hakan ne
ya tuno mani da asalina na kasancewata
maraya, wanda ma ba zai iya tuno mahaifarsa
ba bare danginsa, hakika kaddara ta yanke mani
kauna da farin cikin rayuwa wanda har abada
bazan samesu ba domin kowa ya bar gida gid ya
barshi.
Yayin da sarki Lafaru ya ji haka sai shima ya
tuna cewa shima fa yanzu bashi da kowa face
mulkinsa sai kuma dukiyarsa da ya baro a
birnin Kufa, nan take ya sake tunawa yau fa
saura kwanaki arba'in yayi yaki da sarki
Nurwas na birnin Zaruk kuma ga shi gashi
yanzu ya bar kasar, to wai shin yanzu za a yi
wannan yakin ko kuma ba za a yi ba? Idan kuma
aka yi yakin suwa za su samu nasara?
Shin wannan halifa nasa wanda boka Muzafar
ya kirkira zai iya kare birnin daga sharrin sarrki
Nurwas da dakarunsa? Shin da gaske ne idan
251

TASKARNOVELS.COM.NG
basu samu nasara ba bisa abinda suka fito nema
ba shida boka Muzafar dansa Shaddad zai girma
ya zama babban makiyinsa har kuma ya
kasheshi?
Sarki Lafaru yana cikin wannan tunani ne
Gimbiya Rahila da mahaifinta suka zo kansa
suka tsaya, cikin hanzari boka Muzafar da sarki
Lafaru suka mike tsaye suna masu fuskantarsu.
Sarkin ya dubi boka ya ce ya kai wannan
Sadauki mai jarumtaka ta al'ajabi, kayi sani
cewa ban kasance boka ba, dan haka ban san
irin aikin da yata zata yi maku ba? Amman da
ganin fuskokinku baku yi kama da makaryata ba
kuma ba zaku kasance masu kin cika alkawari
ba, abu daya nake zargi akanku bai wuce rashin
aldalci ba ga duk wanda ke karkashinku sannan
zaku iya yin komai dan ganin bukatarku ta biya.
Ni dai yanzu ga yata nan na damkata amana a
hannunku bana bukatar na ji abinda zaku yi da
ita, amman ina son ku kasance masu rike
alkawari ku dawo mani da ita lafiya kamar
yadda kuka yi alkawari da farko. Idan kuwa
kuka ci amanata to kuma amana zata ci ku.

252

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda gama fadin haka sai sarki ya sake
rungume Gimbiya Rahila a kirjinsa tare da
fashewa da matsanancin kuka itama kawai ai ta
kama kukan, da kyar suka kasi juna kana daga
bisani suka yi bankwana. Daga nan sarki da
dakarunsa suka juya suka shige cikin birnin na
su.
Sarki na waigen yarsa gimbiya Rahila yana mai
zubar da hawaye, haka itama, haka dai suka ci
gaba da daga wa juna annuwa har suka kule.
Ba tare da wani bata lokaci ba, boka Muzafar
sarki Lafaru da gimbiya Rahila suka fito daga
cikin wannan birni inda suka iske aljani Maraful
Dauwas a zaune yana jiransu. Nan take duk su
ukun suka haye bayan aljani Marhabul Zaurus
shi kuwa sai ya bude fuka-fukansa ya tashi sama
ya luluka a cikin gajimare sannan ya tsaya cak a
cikin iska.
Koda ganin haka sai boka Muzafar ya daka masa
tsawa tare da cewa Me kake nufine da zaka
tsayar da mu cak a sararin samaniya?
Cikin razana da biyayya aljani Marhabul Zaurus
ya rusuna ya ce Ya shugabana ai baka fada mani
inda zamu je ba, umarninka nake jira?
253

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin haka sai boka Muzafar yayi ajiyar
zuciya sannan ya ce Yanzu mun hau mataki na
farko a wannan gagarumar tafiya da ke
gabanmu, saura mataki na biyu wanda shine
tafiya zuwa dauko abokan tafiyarmu. Ya kai
Marhabul Zaurus na umarceka daka kaimu
birnin Misra domin mu sadu da sadauki
Haiman, kafin Boka Muzafar ya gama rufe
bakinsa tuni aljani Marhabul Zaurus ya dubi
bangaren kudu ya falfala da matsanancin gudu
cikin gajimare tamkar tauraruwa mai wutsiya.
Tunda aka fara wannan tafiya hira ta barke
tsakanin sarki Lafaru da boka Muzafar, ita kuwa
gimbiya Rahila sai tayi shiru kawai ta kishingida
kamar tana yin bacci idanunta a lumshe bata
tanka masu ba.
Sarki Lafaru ne ya fara yin gyaran murya
sannan ya dubi boka Muzafar ya bushe da
dariya, al'amari da ya baiwa boka Muzafar
mamaki da haushi kenan, ya dubeshi a fusace ya
ce ina dalilin wannan dariyar ta ka?
Sarki Lafaru ya hadiye rai sannan ya ce Gani
nayi ni da kai duk mun kai shekaru dari a
duniya amman hr yanzu bamu da kwanciyar
254

TASKARNOVELS.COM.NG
hankali, sannan muna da buri mai tsauri a cikin
zukatanmu, kamata yayi ace a yanzu muna cikin
rayuwar farin ciki da nutsuwa tare da iyalanmu.
Da jin wannan batu sai boka Muzafar ayi
murmushi sannan ya ce Ai shi rai da kake
ganinsa baya rabuwa da buri, daga lokacin da
mutum yayi aure babu abinda zai fara tunani
sama da haihuwa. Idan ya samu haihuwar sai
kuma ya fara tunanin tara dukiyar da zai baiwa
dansa, idan tafiya tayi tafiya aka tara abin
duniya ya taru sosai sai a fara hangen mulki,
idan mulkin ya samu sai a fara hangen daukaka,
a lokacin da daukakar ta samu zaka ga tsufa ya
fara zuwa, to a Sannan ne lafiya zata yi karanci
dan haka sai kaga kullum a cikin neman lafiya
ake, wani har ya mutu ba zai samu lafiyar ba,
wani kuma sai kaga yau da lafiyar gobe kuma
babu, haka dai rayuwa zata kare amman buri
bai kare ba walau yaro matashi ko tsoho.
Koda boka Muzafar ya zo nan a jawabinsa sai
Gimbiya Rahila ta yi caraf ta tari numfashinsa
tare da cewa Wanne abu mutum zai yi domin ya
iya sarrafa zuciyarsa da kwadayin burika?

255

TASKARNOVELS.COM.NG
Boka muzafar ya amsa mata da cewa babu wani
abu mai kore burika daga cikin zuciya face ya
dauki hakuri, kuma ya rike gaskiya da amana,
idan har yayi hak to samu da rashi ba zasu
dameshi ba.
Rahila tayi murmushi ta ce nda kunyi aiki da
wannan maganar da ka fada yanzu da bazaka
rabani da mahaifina ba domin kuje ku bayar da
ni ga aljani Maraful Dauwas na maye gurbin
masoyiyarsa gimbiya Rashmin.
Koda jin wannan batu sai boka Muzafar da sarki
Lafaru suka zazzaro idanu cikin tsananin
mamaki suka kasa cewa komai, tsawon yan
dakiku su dukansu sunyi shiru daga can sai
boka Muzafar yayi ajiyar zuciya ya ce Yake
Gimbiya Rahila ya akayi kika san wannan
al'amari namu alhalin baki kasance matsafiya
ba, haka shima mahaifinki bai kasance matsafi
ba?
Rahila ta girgiza kanta cikin alamun takaici
sannan ta ce Ashe baku yi mamaki ba lokacin da
na bayyana tsulum a tsakiyarku ba sa'adda kai
da mahaifina kuke shirin kaurewa da yaki, a
cikinku babu wanda yaga ta inda na fito kawai
256

TASKARNOVELS.COM.NG
nasan kun ganni ne tsulum a tsakiyarku, to ka
sani cewa bana tsafi amman ina mu'amala da
matsafa, kuma suna sanar da ni duk irin abinda
zai faru gareni a yanzu ko a nan gaba. Kuma
suna bani taimako, inda ban san abinda zai faru
a gareni a cikin wannan muguwar tafiya da
zamuyi ba da bazan biyoku ba, ku sani cewa a
cikin wannan tafiya da zamuyi zamu sha bakar
wahala wacce zamu gwammace mutuwa da
rayuwa, amman a karshe wasu daga cikinmu
burinsu zai cika, wasu kuma zasu samu nakasa
wacce zasu mutu tare da ita, wasu kuma
gabadaya ma zasu rasa rayuwarsu, ina mai
shawartarku da kada kuyi mani tambaya bisa
bayanin dana yi maku, domin ko zaku kasheni b
zan iya amsa maku tambayar ba, daga yanzu
bazan kara cewa uffan ba har sai mun usa
wadannan mugayen dazuzzukan guda biyar,
wadanda sai mun ratsa ta cikinsu ne sannan
zamu isa kogon darul ikisina lallai acan ne zaku
sake tsinkewa da al'amarina, abu na karshe da
zan fada maku shine kunyi babban kuskure da
har kukw tunanina a matsayina na bil'adama
zan iya maye gurbin aljana, ai kama da wane
bata wane, ina mai shawartarku daku sauya
tunani gami da shawara bisa magana daya
257

TASKARNOVELS.COM.NG
wacce zaku je wa da aljani Maraful Dauwas da
ita har ya amince ya biya maku bukatarku, idan
kuma kun kasa tunanin hanyar da zata fissheku
ni ina da dabara wacce dole ne aljani Maraful
Dauwas ya amince yabi umarninku, amman
bazan furta maku ba face kun dauki alkawarin
cewa nima xaku biya mani wata bukata tawa ta
musamman, ku sani cewa kuna da isasshen
lokaci nayin tunani gami da shawara daga yanzu
har izuwa sa'ad da zamu isa kogon darul ikisina.
Koda gama wannan dogon bayank sai Gimbiya
Rahila ta koma ta kishingida ta kama bacci
abinta, tamkar a cikin turakarta take.
Boka Muzafar da sarki Lafaru kuwa sai suka
sunkuyar da kawunansu kasa suka fada kogin
tunani saboda tsananin mamakin al'amuran da
suka ji daga bakin Gimbiya Rahila. A daidai
wannan lokaci ne suka fuskanci cewa Aljani
Marhabul Zaurus na sakkowa kasa wne, koda
suka leko kasa sai sukaga ashe har sun iso
birnin Misra. Nan take Marhabul Zaurus ya
durfafi wani katon gida kayataccen gaske irin na
sarakai, ya sauka a tsakiyar farfajiyar gidan,
acikin wani tafkeken lambu wanda ke cike da
furanni iri-iri masu dadin kamshi, sanann kuma
258

TASKARNOVELS.COM.NG
a wani bangaren kayan marmarine kala-kala
kamar irin su inibi, baure, fasa dabur da dai
sauransu. Tsuntsaye kuwa gasu nan kyawawa
iri-iri wank kalarma mutum bai taba ganin
irinsa ba.
Nqn take sarki Lafaru da gimbiya Rahila suka
kamu da tsananin sha'awar wannan gida, domin
ya isa a kirashi da aljannar duniya. Da saukar
aljani Marhabul Zaurus a cikin wannan
kayataccen labu sai boka Muzafar ya sauka daga
kansa da sauri sannan ya yafito gimbiya Rahila
da sarki Lafaru da hannu yana mai yi musu nuni
da su biyoshi a baya. Ba tare d gardamar komai
ba kuwa suma suka sauka daga kan aljani
Marhabul Zaurus suka bi bayan boka Muzafar
da sauri.
Boka Muzafar ya dinga kuntsawa ta hanyoyi
daban daban ta cikin lambun kamar tafiyar ba
zata kare ba a haka dai har suka iso bakin wani
katon daki, tun kafin su iso kofar dakin suka
hango wata tsaleliyar budurwa mai tsananin
kyawu na ban al'ajabi ta fito daga cikin wani
daki tana dogara sandar zinare a hannunta.
Kallo daya Gimbiya Rahila tayi wa budurwar ta
tabbatar da cewa ta isa a yi kwatancenta a
259

TASKARNOVELS.COM.NG
bangaren kyawu domin tasan cewa dolene ta
ruda maza. Budurwar tana sanye da wata riga
doguwar riga launin ruwan kwai ta siliki, wanda
aka yi wa ado da zanen furanni na ruwan zinare,
takalman dake kafarta kuwa da lu'u lu'u aka yi
su, shima launin ruwan kwai, gashin kanta dogo
ne da ya zuba har kan gwiywarta kamar zai
shari kasa, kuma ya kasance bakikkirin sai sheki
da walwali yake yi. Tana da daradaran idanuwa
wadanda idan ta dubi mutum da su sai yaji
kamar zai shide saboda tsabar kyawunta,
hancinta dogone kuma siriri kai kace lika mata
shi aka yi, bakinta kuwa dan kankani ne kamar
da alkalami aka zanashi, kirjinta a ciki yake shi
kuma cikinta a shafe yake kamar bata taba cin
komai ba a duniya, kugunta kuwa kirar
kalangune ya fashe, mazaunanta nada tudu
sosai, kafafunta sirarane kuma tana da zararan
yan yatsu na hannu da kafa, tana da dunguniya
mai tudu kuma kafafun nata a mike suke sambal
babu karkata ko kadan, kkaurin jikinta
madaidaicine fatar jikinta kuwa kamar idan ka
latsa jini ne zai tsattsafo saboda haske, Kash! Sai
dai duk tsananin kyawu wannan budurwa abu
daya ne tawayarta, bakomai bane illa makanta.

260

TASKARNOVELS.COM.NG
A lokacin da budurwar ta tunkaro inda su boka
Muzafar suke, Gimbiya Rahila ta gane cewa
makauniya ce, saboda ganin yadda take laluben
hanya da sandar hannunta, tana xuwa daf da su
boka Muzafar sai ta tsaya fuskarta na kallon
gefe tayi murmushi sannan ta ce Lale marhabun
da manyan baki masu daraja, ku zo mu karasa
wajen masoyina.
Koda jin wannan batu sai Gimbiya Rahila da
sarki Lafaru suka cika da tsananin mamaki, na
yadda akayi ta san da zuwansu da kuma yadda
akayi ta tsaya a daidai inda suke alhalin bata
gansu ba tunda ba ido ne da ita ba.
Kamar budurwar ta san abinda Sarki Lafaru da
gimbiya Rahila ke wasi-wasi a zukatansu kawai
sai ta dago kai a karo na biyu ta yi murmushi
sannan ta ce Kada kuyi mamaki bisa tsayuwata
anan daf da ku, domin ina amfani da numfashi
ne ba idanu ba, ko mutum, aljan ko dabba idan
suna nesa da ni koda tazarar takai ta kamu
arba'in ina iya jin numfashinsu wannan ba tsafi
bane baiwace kuma da ita aka haifeni tun ina
jaririya. Yadda aka yi kuwa nasan da zuwanku
shine Masoyina ne yayi bincike a cikin hallarar
tasfinsa ya hangoku. Ku yi sani cewa yau nida
261

TASKARNOVELS.COM.NG
masoyina muna cikin farin ciki mara misaltuwa,
saboda sanin cewa lokaci yayi da zamu cika
burinmu, mu kuma yaye bakin cikin daya
addabemu tsawon shekara da shekaru.
Koda gama fadar haka sai budurwar ta juya tayi
masu jagora har izuwa cikin wannan babban
dakin, da shigarsu cikin wannan daki sai Rahila
da Lafaru uka zama cikakkun yan kauye saboda
ganin irin kayan alatun da aka shirya a ciki, nan
take sarki Lafaru ya gane cewa fadarsa bata
wuce akurki akan wannan ba, kuma kayan
kawar da aka zuba a dakin zasu iya siyen na
fadarsa sau dari, zaune akan wata kujera ta
jauhari sadauki Haiman ne, kunyangi da barori
sun kewayeshi suna yi masa hidima, wasu fifita
suke masa da mafifici na gashin dawisu, wasu
kuwa gyara masa kayan jikinsa suke yi, wata
kuyanga na tsaye a gefe guda sai kirari take
masa tana cewa Hutawarka lafiya sadauki mai
kamar sarki, gaisheka abul saifu, kaine kafi
kowa iya sarrafa kai, jan gwarzo kake
End Ads