kaunata kayi sani cewa ina binka
bashin kubutar da rayuwarka da nayi daga
hannun wadannan muggan aljanu na cikin
kogon Mazubatul Dulshul masu tsaron takobin
73
TASKARNOVELS.COM.NG
Saiful Lujara. Baka da wani abu wanda za ka iya
biyana wannan bashi domin kai fakiri ne a
kaina koda kuwa nan gaba ka mallaki duk
kasashen duniya sun zamo karkashin mulkinka
saboda a cikin wannan gida nawa akwai tsubin
dukiya wacce tafi duk dukiyar duniya yawa. Ina
son ka biyani bashin da abu daya Hantaru ya ce,
"Mene ne abin da kike so na biya ki da shi?".
Maimakon Hayatul Lumihas ta ce wani abu sai
taje ta dauko wani hoto da aka sasssakashi
cikin siffar gunki ta mikawa Hantaru. Da ya
karbi gunkin ya dubeshi da kyau sai ya ga ashe
kamannin gimbiya Hayatul Lumhas ne sak
tamkar an tsaga kara. Hantaru ya sake dago kai
ya ?ubi Hayatul Lumhas ya ce, "Me zan yi da
wannan gunki mai siffar fuskarki?".
Hayatul Lumhas ta ce, "Ina son komai wuya
komai gumu, ka kai wannan gunki izuwa birnin
Hindu ka sada shi ga mahaifiyata sarauniya
Mashlima wacce a halin yanzu ita ce ta gaji
karagar mahaifina. Ka bata Labarina da irin
daular da nake ciki amma ka sanar da ita cewa
burina bai cika ba wanda shi ne burin mijinta,
don haka har abada ba zamu sadu ba kuma
nima ajalina yana daf kamar yadda na
74
TASKARNOVELS.COM.NG
mahaifina ya kasance. ldan kayi haka ka biyani
bashin da nake binka, idan kuma baka aikata
hakan ba kaci amanata". Koda gama fadin
hakan sai Hayatul Lumhas ta juyawa Hantaru
baya ta ce,
"Ka mike ka ci gaba da tafiya izuwa bangaren
gabas za ka riski wata kofa a gabanka da ka
shiga cikinta za ka tsinci kanka a wajen gidan
nan inda za ka iske doki da guzuri wanda na
tanadar maka, amma ka sani cewa daga yanzu
har izuvwa sa'adda za ka isa kofar birnin Darul
Mahabul kana da damar sauya ra'ayi na
dawowa gareni, kofar gidana a bude take gareka
kuma ina mai marhaban da sake karbarka. ldan
kuwa baka dawo ba shi ke nan har abada ba
zamu sake saduwa ba domin ni da kai duk
ajalinmu na kusa."
Koda gama jin wannan batu sai Hantaru ya nufi
gabas yai ta tafiya a cikin harabar gidan ko
Waiwayowa bai yi ba, sai da ya ga ya yi nisa da
Inda ya bar Hayatul Lumhas a sannan ne ya
tuno da irin shakuwar da ya yi da ita a cikin
kwanaki goma sha hudun da kuma irin
dawainiyar da tayi da shi na jinyarsa har ya
sami lafiya. Hantaru ya tuno da irin tsananin
75
TASKARNOVELS.COM.NG
kyawun Hayatul Lumhas da kuma irin daular
da take ciki da matsayinta na 'yar sarkin birnin
Hindu, birnin da a wannan ZAmani duk duniya
babu kamarsa a karfin mulki. Nan take Hantaru
yaji nadama tazo masa, kuma ya kamu da
tsananin tausayin gimbiya Hayatul Lumhas, bai
san sa'adda hawaye ya zubo masa ba, kawai sai
ya waigo baya bisa tunanin ko Zai hangoi
Hayatul Lumhas.
Yana waigowa sai ya ganta a tsaye daf da shi
idanunta sun yi sharkaf da hawaye. Nan take
Hantaru ya rungume Hayatul Lumhas ya fashe
da matsanaicin kuka ita kuwa sai ta bushe da
dariyar farin ciki bisa ganin cewa zuciyarsa ta
karaya ya fasa tafiyar ya barta. Bisa mamaki sai
Hayatul Lumhas taji Hantaru ya yi wuf ya tureta
daga cikin jikinsa kawai sai ya dubeta ya ce,
"Ki gafarceni yake tauraruwar zamani, hakika
ke abar tunawace a zuciyata har abada, kuma
lallai sai na biyaki bashin da kike bina ka fin
cikar ajali, amma ki sani cewa har abada ba za
ki mallakeni ba nima ba zan mallakeki ba
domin ba a yimu domin juna ba Koda gama
fadin hakan sai Hantaru ya juya ya ci gaba da
tafiya abinsa. Kawai sai yaji Hayatul Lumhas ta
76
TASKARNOVELS.COM.NG
fashe da matsanancin kuka wanda ya kara
dugunzuma hankalinsa kuma ya kamu da
tsananin tausayinta har yaji kamar ya hakura da
tafiyar ya koma gareta amma sai ya kanne ya ci
gaba da tafiyar, yana tafe yana zubar da hawaye
har ya yi nisa sosai ya daina jiyo sautin kukan
Hayatul Lumhas a sannan ne ya iso bakin kofar
gidan.
(Ta tabbata dai hayatul lumhas tawace, Ni mai
typing Abu Saleh AlQuyraemey). Da isarsa daf
da kofar sai ya ga kofar ta bude kanta, kawai sai
ya ga wani ingarman farin doki a tsaye shi kadai
yana harbin iska ga jakar guzuri daure a kansa.
Cikin murna Hantaru ya ruga izuwa ga dokin yai
tsalle ya haye kansa sannan ya sakar masa
linzami ya sukwaneshi da gudu izuwa cikin daji.
Daga wannan rana Hantaru ya ci gaba da tafiya
a cikin daji ya kwana nan ya tashi can har
tsawon kwanaki masu yawa amma mamaki ko
sau daya bai gamu da wani mugun abu ba kuma
bai sha wahalar komai ba. Wata rana da
yammaci yana cikin tafiya kawai sai ya hango
kofar birnin Darul Mahabul a gabansa nesa
kadan. Al'amarin da ya matukar bashi mamaki
ke nan, domin da can tafiyar da yake yi kansa a
77
TASKARNOVELS.COM.NG
juye yake bai ma san inda ya nufa ba kawai inda
ya ga dokinsa ya yi nan yake bi baya sauya
masa akala. Koda Hantaru ya hango kofar
birnin Darul Mahabul sai ya cika da tsananin
farin ciki don haka sai ya sakarwa dokinsa kaimi
ya zabureshi da gudu. Da isarsa bakin kofar
birnin sai ya ci gaba da gudu kuma ya rufe
fuskarsa da rawani,
sannan ya boye takobin Saiful Lujara a cikin
jakar guzurinsa bai zame ko ina ba sai gidan
Shurem. Da isar Hantaru kofar gidan sai ya iske
Shaulat matar Shurem ita kadai tana baiwa
dokin mijinta ruwa. Koda Shaulat ta ga mutum
a gabanta bisa doki kuma fuskarsa a rufe sai ta
razana ta yunkura za ta ruga izuwa cikin gida.
Cikin sauri Hantaru ya kira sunanta yana mai
cewa,
"Ya ke kakata yau kuma jikanki kike gudu?"
Koda Shaulat taji muryar Hantaru sai tayi jifa da
bokitin hannunta ta ruga gareshi. Hantaru ya
sauko daga kan dokinsa da sauri suka rungume
juna tana dariyar farin ciki, daga can kuma sai
yaji ta fashe da kuka. Al'amarin da ya matukar
firgitashi ke nan ya janye jikinsa daga cikin nata
da sauri suka fuskanci juna a lokacin da ya rike
78
TASKARNOVELS.COM.NG
kafadunta ya ce, "Ya ke kakata ina dalilin
wannan kuka naki?" Shaulat tayi ajiyar zuciya ta
ce, "Ya kai Hantaru kayi sani cewe bayan
taf?yarku izuwa kogon Mazubatul Dulshal kai
da sadauki Rabbasu don dauko takobin Saiful
Lujara mutane da yawa sun rasa rayukansu
sakamakon mutuwar mahaifin Rabbasu da
kuma mahaifin mijina,
wato boka Sulbaini domin mutuwar tasu ta
kawo rudani da tashin hankali a tsakanin
kabilarmu da kabilar su Rabbasu har tasa muka
dinga yakin sunkuru muna kashe juna sai da
kyar sarki ya tsaida wannan yaki. Ka sani cewa
mijina ya mutu a wannan yak?, yanzu bani da
kowa face mahaifiyarka Salimat da kuma kai a
wannan birni na Darul Mahabul. Koda jin
wannan batu sai Hantaru yaji wani irin mugun
bakin ciki ya rufeshi, bai san sa'adda ya fashe da
matsanaicin kuka ba.
A dai-dai wannan lokaci ne ya hango Salimat ta
fito daga cikin gida ta nufo inda suke hawaye na
zuba a idanunta. Cikin hanzari Hantaru ya ruga
gareta suka rungume juna suka kara fashewa
da kukan murna bisa sake saduwa. Nan dai
suka dunguma su ukun suka shiga cikin gidan.
79
TASKARNOVELS.COM.NG
Bayan Hantaru ya huta kuma ya ci abinci sai
Salimat da Shaulat suka rakashi izuwa inda
kabarin Shurem yake ya durkusa a gaban
kabarin yana kuka, sannan ya yi masa addu'oi
irin nasu na kafirai da suka saba yi. Ba wani
abu bane yasa Hantaru yake wannan kuka ba
face gashi ya dawo daga kogon Mazutbatul
Dulshal cikin nasarar ?
auko takobin Saiful Lujara amma Shurem bai
gani ba. Ya sani cewa a rayuwar Shurem
wannan ce rana mafi farin ciki a rayuwarsa,
wato ranar da zuri'arsu ta ci gasar da ta kasa
kar6o kambunta a wajen zuri'ar su Rabbasu
tsawon shekaru.
Sa'adda Hantaru ya gama 'yan addu'oinsa da
koke-kokensa a kabarin Shurem sai Salimat ta
tasheshi tsaye suka koma cikin daki suka zauna
a sannan ne ya bude jakar guzurinsa ya ?anko
takobin Saiful Lujara ya nuna musu sannan ya
kwashe labarin tafiyarsa kaf ya zaiyane musu
tun daga lokacin suka fara shan wahala shi da
sadauki Rabbasu da kuma sauran wahalar da ya
sha har kawo izuwa lokacin da Rabbasu ya
karaya ya kashe kanSa ya isa cikin kogon
Mazubatul Dulshur da irin gwagwarmayar da
80
TASKARNOVELS.COM.NG
ya yi da masifun ciki har da yadda ya dauko
takobin ya gudu don tsira da rayuwarsa har ya
fadi kasa sumamme ya farfado a gidan gimbiya
Hayatul Lumhas da duk abin da ya faru
tsakaninsa da ita har suka rabu ya taho birnin
Darul Mahabul.
Koda gama wannan labari sai Salimat da
Shaulat suka cika da tsananin al'ajabi kuma
suka jinjinawa Hantaru domin sun san cewa ya
yi gagrumar bajinta wacce abu ne mawuyaci
nan gaba a sami wanda ma zai iya kwatanta
irinta. Haka dai suka ci gaba da hira har dare ya
raba sosai. Hantaru da Shaulat suka kwanta
suka kama barci amma ita Salimat sai ta kasa
kwanciya kuma idanunta suka bushe ya zamana
cewa ko kadan bata jin barci.
Ba komai ne ya haddasa ma ta hakan ba face
tsananin fargaba bisa labarin da Hantaru ya
baiyana ma ta dangane da abubuwan da
gimbiya Hayatul Lumhas ta zaiyana masa akan
ababuwan da za su same shi anan gaba. Tun
sa'adda Hantaru ya tafi neman takobin Saiful
Lujara ya
zamana cewa kullum sai Salimat...
81
TASKARNOVELS.COM.NG
Tun sa'adda Hantaru ya tafi neman takobin
Saiful Lujara ya zamana cewa kullum sai Salimat
tayi mugun mafarki akansa kuma abin da ake
nuna ma ta a cikin mafarki shine,
Hantaru ya rusa ma ta dukkan farin cikin
rayuwarta. Koda ta tuna wadannan mafaekai da
wannan labari da yazo ma ta da shi sai ta
tabbatar da cewa Lallai mafarkin nata zai iya
zama gaskiya.
Bisa Wannan dalili ne Salimat ta kasa barci ta
dinga sakar zuci bata san sa'adda ta fara kuka
ba. Sautin kukan nata ne ya sa Haataru ya farka
daga barci. Koda bude idanunsa ya ga Salimat a
zaune tana kuka sai ya mike zumbur cikin
razana yazo gareta ya rungumeta yana cewa ya
ke, "Ummina kiyi sani cewa har abada wannan
mafarki naki ba zai tabe Zama gaskiya ba, domin
babu wani aba da ya fiki matsayi da
muhimmanci a wajena, na rantse da darajar
82
TASKARNOVELS.COM.NG
kaunar da ke takanina da ke da mijinki har
abada ba zan taba juya mikk baya ba.
Na yi imani cewa babu abin da zai gagari tsafi
saboda haka koda mafarkinki zai zama kaddara
a garemu to ni zan sauya wannan kaddar da
karfin tsafi, bayan mun karbo kambun gasa
wajan sarki an daura aurena da gimbiya Larziya
saboda haka inason gobe da sassafe ke da
Shaulat ku rakani fada domin na gabatar da
takobin Saiful Lujara ga sarki a gaban jama'ar
gari domin burin zuri'armu ya cika nima nawa
burin ya tabbata.
Sa'adda Hantaru ya zo nAn a jawabinsa sai
Salimat taji hankalinta ya dan kwanta, don haka
sai ta share hawayen idanunta ta dora kanta
bisa kirjin Hantaru shi kuwa ya ci gaba da rera
waka, A cikin sanyin murya yana karanto baitoci
masu kwantar da zuciya da sanyayata.
A haka barci ya sace Salimat bata sani ba, Har
gari ya waye Salimat na barci akan kirjin
Hantaru bai yarda ya motsa jikinsa ba don kada
83
TASKARNOVELS.COM.NG
ta farka daga barcin kuma bai daina rera
wannan wake ba saboda tsananin biyayya da
son ganin kwanciyar hankalinta. Hudowar
hasken rana ne yasa Salimat ta farka daga barci,
koda ta ga kanta bisa kirjin Hantaru kuma ta ga
idanunsa wasai babu alamar ya yi barci sai ta
cika da tsananin damuwa ta ce, "Ya kai ?ana ya
ya aka yi nayi barci akan kirjinka amma baka
tasheni ba, domin kaima ka kwanta kayi barcin
kuma mene ne ya hanaka kaima kayi barcin?".
TYPING BY : SHURAIH 99%
Sa'adda Hantaru yaji wadannan tambayoyi sai
ya yi mumushi ya ce, "Ai kwanciyar hankalinki
shi ne nawa, inda baki samu Wannan barci ba
da sai na kwana ina kuka da bakin ciki."
Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ga
jama'ar zuri'arsu na ta shigowa cikin gidan da
murna suna yiwa Hantaru barka da sauka
tamkar an yanke musu dukkan bakin cikin
rayuwa. Al'amarin da ya ?aurewa Hantaru da
Salimat kai ke nan suka cika da mamaki bisa
yadda jama'a suka san cewa ya dawo harma
suke zuwa yi masa barka da sauka.
84
TASKARNOVELS.COM.NG
Abin da basu sani ba shi ne, tun a yammacin
Jiyan wata kuyangar gidan ta watsa labari. Nan
da nan gidan Shurem ya cika ya batse da
jama'arsu tamkar ana wani gagarumin shagalin
biki a garin.
Bayan jama'a sun gama taruwa sai aka cabawa
Hantaru ado sannan aka rakashi izuwa fada ana
tafe ana kade-kade da raye-raye gami da bushe
bushe.
Nan da nan birnin gaba ?aya ya dauka cewar ga
Hantaru can ya dawo gida. Nan fa jama'a suka yi
tururuwa izuwa fada domin su ganewa
idanunsu shin Hantaru ya samu nasarar dauko
takobin Saiful Lujara ne ko kuwa bai samu ba,
sannan suna son su ji labarin Sadauki Rabbasu
yana raye ne ko kuwa ya hallaka a cikin wannan
tafiya.
Lokacin da su Hantaru da sauran jama'ar gari
suka isa fada sai suka iske fadar a cike makil
85
TASKARNOVELS.COM.NG
babu masakar tsinke. Sarki na zaune bisa
karagar mulki ya ci ado na kasaita sai murmushi
yake ya kasa rufe baki dalili kuwa shi ne tuni
bokaye sun bashi labarin cewa Hantaru ya
dauko takobin Saiful Lujara. A hannun daman
sarki gimbiya Larziya ce a Zaune ta caba ado na
ban al'ajabi sai sheki da walwali take tamkar
wata dan daren goma sha biyu, kuma itama tana
ta yin murmushi irin wanda ka iya zauta duk
wani baligi da ya kuskura ya kura ma ta idanu.
Da shigowar Hantaru cikin fadar tare da
jama'arsu sai Dakaru suka tsaida kowa daga
baya, Hantaru kadai aka bari ya nufi inda
karagar sarki take. Tun daga nesa ya hada idanu
da masoyiyarsa gimbiya Larziya ya ga tana yi
masa murmushi tamkar ta mike ta rugo gareshi
amma sai ta kanne. Shima Hantaru haka ya
rinka ji a cikin ransa amma sai ya jure ya rinka
maida mata da martanin murmushin. Sa'adda
Hantaru ya iso kusa da karagar sarki sai ya zube
kasa ya kwashi gaisuwa, fadawa suka karbi
gaisuwarsu sannan sarki ya dubeshi ya ce,
86
TASKARNOVELS.COM.NG
"Ya kai NAMIJIN DUNIYA, ina labarin abokin
tafiyarka Rabbasu, kuma me ka zo mana da
shi?" Sa'adda Hantaru yaji wannan tambaya sai
jikinsa yai sanyi, nan take idanunsa suka ciko da
kwalla. Ba tare da 6oye komai ba Hantaru ya
kwashe labarin tafiyarsu tun daga farko har
karshe ya zaiyane musu.
Yana gama bada labarin sai ya ga ashe gaba
dayan jama'ar da ke fadar kuka suke yi saboda
tausayi a lokacin da shima kansa yana ta zubda
hawaye. Nan take Hantaru ta fiddo takobin
Saiful Lujara daga cikin rigarsa ya zareta daga
cikin kufenta. Koda zare takobin sai haskenta ya
cika fadar gaba ?aya, ta rinka kashewa kowa
idanu.
Gaba dayan bokayen garin da ke tsaye kusa da
sarki sai sukayi sujjada ga takobin suka hada
baki suka ce, "Daukaka da jinjina sun tabbata ga
jarumin jarumai, gwarzon shekara, sadauki
Hantaru mijin gimbiya Larziya". Koda jin
wannan batu sai fadar gaba daya ta rude da
shewa, kida da wake-wake. Sai da sarki ya daga
87
TASKARNOVELS.COM.NG
sandar mulkinsa sannan aka yi tsit! Nan take
sarki ya mife tsaye da kansa ya kirawo Halifan
baban Rabbasu ya karfi kambun gasa daga
hannunsa sannan ya taka yaje gaban Hantaru ya
nuna nasa kanbun ya ce, "Gobe wannan kambu
zai dawo jannunku ku zuri'ar Shurem," Koda jin
haka sai fadar ta sake ru?ewa da shewa.
Sarki ya sake daga kwagirinsa a karo na biyu
aka yi tsit, tamkar mutuwa ta gifta, sannan y
ce,"Hakika sadauki Hantaru ya bar abin tarihi
kuma abin tunkaho a wannan birni namu,
wanda zamu ci gaba da tutiya gami da alfhari da
shi a dukkan sauran kasashen duniya saboda
shi ne jarumin da zai auri 'yata gobe da yamma
anan fadata.
Tabbas Hantaru ye kawo karshen gardama da
gaba a tsakanin zuri'ar makera da ta mafarauta
da a wannan an gari nawA mai albarka saboda
haka A yau na rushe wannan tsohuwar al'ada ta
gasar tseren gudun barewa".
88
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda gama wannan jawabi sai Sarki yaje ya
kama hannun 'yarsa gimbiya Larziya ya ja ta
suka shige izuwa cikin gidan sarauta t?na
waigen Hantaru tamkar ta kufce ta rugo gareshi,
shima Hantaru sai yaji kamar ya ruga ya rukota
amma da ya tuna da cewa gobe ne za a daura
aurenta da shi sai hankalinsa ya kwanta ya bita
da kallo cikin murmushi kawai.
(Hallau dai kuna tare da Shuraih 99%)
Bayan sarki da Larziya sun shige cikin gida sai
fadar ta watse kowa ya kama gabansa. Saboda
tsananin ?oki da murna Hantaru bai yi barci ba
a wannan dare, a yadda ya ga rana haka ya ga
dare, wato dai ya jera kwana biyu ke nan bai yi
barci ba.
Da gari ya waye, tun da sassafe zuri'ar Shurem
suka cika gari da kade-kade da bushe- bushe
gami da raye-raye suka yi ta walima a gidagida, unguwa-unguwa, ya zamana cewa Ana a
bushasha da abinci da abin sha iri-iri a ko ina
cikin birnin Darul Dulshul bisa samun nasarar
?auko takobin Saiful Lujara.
89
TASKARNOVELS.COM.NG
Haka dai aka ci gaba da wannan shagalin biki
har izuwa yammaci. Bangaren zuri'arsu
Rabbasu kuwa banda kuka da bakin ciki babu
abin da suke yi, domin sun yi asarar abubuwa
uku.
Abu na farko da suka rasa shi ne, shugabansu
wato mahaifin Rabbasu sannan sun rabu da
kambun gasa wanda ke hannunsu tsawon
shekara da shekaru. Abu na na uku shi ne,
magajin shugabansu wato sadauki Rabbasu
jarumin da babu kamarsa a gaba daya nahiyar.
La'asar nayi sai fada ta sake cika ta batse jda
ama'a fiye da taron da aka yi na safe, wannan
karon ma gaba daya birnin ne ya cika da baki
daga sauran makotan birane saboda jin cewa za
a daura auren gimbiya Larziya da jarumin da
yaje har kogon Mazubatul Dulshul ya dauko
takobin Saiful Lujara.
Tun ana baiwa baki masauki har sai da takai
cewa an daina basu domin babu. A wannan rana
90
TASKARNOVELS.COM.NG
mutanen birnin Darul Habul sun yi matukar
al'ajabi domin basu taba ganin cikowar jama'a
ba a garinsu irin haka. Abin da basu sani ba shi
ne, fiye da kaso saba in na cinkoson jama'ar ba
mutane bane aljanu ne daga sassa na duniya
suka zo a cikin siffar mutane domin kawai su ga
jarumi Hantaru sadaukin da ya yi gagarumar
bajintar da ta gagari dukkanin sadaukan duniya
tsawon shekaru dubu uku da suka gabata.
Zan ci gaba.
Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake
son complete zai iya tuntubata ta wannan
number 08138873799 kira ko whatsapp.
MAZAN JIYA
Littafi na biyu 2
Part F
Na Abdulaziz Sani m gini
91
Ba tare da 6ata lokaci ba aka daura auren
sadauki Hantaru da gimbiya Larziya a gaban
miliyoyin jama'a kuma aka ?ankawa Hantaru
kambun gasa ya ?aurashi a hannunsa, ai kuwa
fadar gaba daya ta rude da shewa gami da tafi
har kowa yaji kamar kunnensa zai dode.
Nan dai aka cigaba da shagalin biki aka yi ta
watsa dukiya gA maroka da mabukata. Abinci
kuwa sai da ya zamo ga shinan kamar shara aka
rinka yin bolarsu tsibi-tsibi saboda an rasa
yadda za a yi dashi.
Kowa a garin sai da ya cika da mamakin irin
wadatar da aka samu a wannan rana domin
abin yafi karfin iyakar bajintar Sarki, kai da gani
ka san cewa akwai sa hannun aljanu. Haka dai
aka ci gaba da shagalin biki amma har dare ya
soma ango bai ga amaryarsa ba domin tunda
aka ?aura aurensa da ita sai aka shigar da ita
92
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin gidan sarauta aka killaceta a cikin
turakarta aka yi ta tsala ma ta ado iri-irk, idan a
ka yi wannan sai a ga bai yi ba a sake yin wani
har sai da aka yi kala saba'in.
A na saba'in ne matan da ke yin adon suka
gamsu gaba ?ayansu cewar ya yi. A wannan
lokaci dare ya fara tsalawa don haka sai aka
dauki amarya cikin hanzari aka kai ta gidan su
Ango. Bayan masu kak amarya sun watse sai
ango ya shigo ?akin amaryarsa yana sanye da
tufafi masu tsadar gaske na alhariri.