ta tumu da kasa sai
dutsen cikin cikin nata yaji kamar zai tarwatse
don haka bisa dole dutsen ya taho da kansa
izuwa makogwaronta.
Koda jin hakan sai Macijiyar ta wangame
bakinta wanda dutsen ke ciki, sannan ta sake
wangame wani bakin dabam ta sokashi a cikin
wancan domin ta zaro dutsen. Koda dutsen ya
ga haka sai ya rikide ya zama wuta. Ai kuwa
Macijiyar na hadiye dutsen wutar sai tayi
bindiga ta tarwatse, sassan jiikinta ya yi flla-flla
a kasa tamkar an yankashi gutsun- gutsun, sai
ga dutsen wutar ya gangara Can gefe daya. Nan
35
TASKARNOVELS.COM.NG
take dutsen ya rikida ya zama sadauki Hantaru
kwance kasa, duk jikinsa yai kaca-kaca da
raunika, jini na zuba yana numfashi da kyar
kamar ransa zai fita. A Sannan ne nadama tazo
masa, ya tabbatar da cewa abune mawuyaci ya
sami nasarar daukar takobin daraja a cikin
wannan kogo,
musamman da ya dubi ragowar rijiyoyin da bai
bude ba guda ?ari tara da casa 'in da tara.
Babban abin tsoroa gareshi shi ne, rashin sanin
rijiyar da takobin Saiful Lujara ke ciki, ko
shakka babu kowacce rijiya ba Za a rasa mugun
abu ba a ciki. ldan ya bude wadda ya gamu da
abin da zai hallakashi a ciki shi ke nan burinsa
ya yanke, kuma dak wahalar da ya sha a baya ta
zAma a banza.
Hantaru ya tuno da batun mahaifiyarsa Salimat
wadda ba ita ce ta haifeshi ba amma kuma yana
kaunarta fiye da kowaa rayuwarsa sai kuma
gimbiya Larziya wadda a halin yanzu ya kamu
da tsananin begenta har ya amince ya sallama
rayuwarsa domin ya mallaketa. Hantaru ya
tuno da batun cin amanar da mahaifiyarsa ta
jini ta yiwa sarki Kusaidu ita da boka Ardusa.
Lallai yana son ya koma birnin Kisra domin ya
36
TASKARNOVELS.COM.NG
yiwa Farzira da boka Ardusa hukunci bisa
wannan cin amana, kuma ya sadu da sarki
Kusaidu wanda ke matukar kaunarsa a
matsayin dan cikinsa. To amma ai Salimat ta
gargadeshi akan kada ya taba lafiyar Zarifa. Abu
na biyu da ya fadowa Hantaru a rai shi ne, batun
alkawarin da ya ?
aukarwa gimbiya Lazirina cewar duk wuya duk
rintsi ba za su rabu ba, kuma duk bukatar da
tazo masa da ita zai biya ma ta ita. Koda
Hantaru yazo nan a tunaninsa sai zuciyarsa ta
karaya, ya fara tunanin hanyar da zai bi ya yi
jinyar jikinshi sannan ya ci gaba da bude
ragowar rijiyoyin guda dari tara da casa'in da
tara har ya sami wadda takobin Saifal Lujara ke
ciki. Hantaru ya tambayi kansa a cikin ziciyarsa
ya ce, "Yanzu ta ya ya zan reyu a cikin wannan
kogon dutse babu ruwa babu abinci?" Koda
aiyana hakan,
sai idanunsa suka kai kan sassan jikin
Macijiyar da ya kashe da kuma jinin jikinta da ya
malala ya cika kasan kogon wanda za a iya yin
wanka a cikinsa. Hantaru ta daga kansa sama ya
yi arba da wasu tsirarun ciyayi da kananan
bishiyoyi da tsirai da suka tofo a cikin dutsen,
37
TASKARNOVELS.COM.NG
sai farin cilki ya kama shi, don ya fahimci cewa
zai iya rayuwa a cikin kogon izuwa tsawon
kwanaki kadan. Hantaru ta daga kansa sama ya
yi arba da wasu tsirarun ciyayi da kananan
bishiyoyi da tsirai da suka tofo a cikin dutsen,
sai farin cilki ya kamna shi, don ya fahimci cewa
zai iya rayuwa a cikin kogon izuwa tsawon
kwanaki kadan.
Hantaru ya fara da tunanin abinda ya kamata ya
fara yi a yanzu tun da gashi har jiri ya fara
dibarsa sakamakon jinin da ke zuba daga
raunikan jikinsa Lallai ya zama dole ya yi
tunanin abin da zai ya tsaida jinin. Cikin
matukar karfin hali ya mike tsaye yana tangadi
ya kama hawa kan duwatsun dake cikin kogon
yana dogarawa ya isa inda ya hango wata
bishiya mai faffadan ganye.
Sai da ya rage saura baifi taku uku be ya isa inda
bishiyar take sai ya zame ya fado kasa Haka dai
ya daure ya sake tashi ya hau kan ?utse. A karo
na biyu ma bai nasara ba sai ya fado. A karo na
uku ne ya samu dama da kyar ya tsinko ganyen
ya fado kasa a matukar galabaice. Da jen ciki
yaje inda wata busasshiyar karamar bishiya
take ya karyo kirare a jikinta, ya sake dawowa
38
TASKARNOVELS.COM.NG
da baya ya dauki duwatsun wuta biyu ya dinga
gogasu akan wadannan kirare har wuta ta
kama A haka ne ya dinga narka ganyan wannan
bishiya da ya karyo yana mannashi a jikin
raunikan jikinsa. Duk sa'adda ya manna ganyen
sai yaji kamar ya kurrma ihu saboda tsananin
zafi da zogin da ke shigarsa.
Har wani irin gumi da haweyen azaba ne ke
zubo masa. Bayan ya gama sa maganin a jikin
dukkanin raunikan jikinsa ne ya kwanta ya huta
tsawon rabin saa a sannan ne jini ya daina zuba
daga jikinsa ya dawo cikin haiyacinsa sosai. Nan
take Hantaru ya mike zaune ya tsinto sassan
jikin Macijiyar nan ya soka a jikin itace ya gasa,
wato yai tsire.
Haka ya ci gaba da gasa naman Macijiyar har ya
gasa mai yawa ya zamana Cewa naman ya gasu
sosai yadda zai kwana biyu bai lalace ba. Daga
wannan rana Hantaru ya ci gaba da rayuwaa
cikin wannan kogo yana mai ci gaba da jinyar
jikinsa domin ba zai iya ci gaba da bude Sauran
rijiyoyin ba, ya zamana cewa bashi da abinci sai
wannan gasasshen naman Macijiyar, kuma
bashi da ruwan sha sai jininta da ya malala a
kasa. Har sai da jinin Macijiyar ya daskare ya
39
TASKARNOVELS.COM.NG
ZAmana cewa sai ya sareshi da takobi yake sha.
Wannan gasashen naman kuwa sai ya lalace ya
rube har ma ya fara tsutsa, amma a hakan yake
cinsa domin ya rayu kada yunwa ta kashe shi.
Hantaru dai bai samu cikakkiyar lafiya ba sai
bayan kwana goma sha uku. ranar kwana na
goma sha ukun ne Hantaru ya je gaban rijiya ta
biyu ya tsaya yana shawara da zuciyarsa akan
ya budeta ko kada ya bude.
Da zarar ya kai hannu da nufin zai sare mukullin
rijiyar sai hannunsa ya kama karkarwa ya kasa
saboda tsoron kada ya budo abin da yafi na
rijiyar farko balai wanda ka iya zama sanadin
ajalinsa gaba daya. Sai da Hantaru ya jarraba
hakan sai ya kasa sare mukulin, Nan take
Hantaru ya tuno da irin gwagwarmayar da ya
sha a baya da lamarin da ke gabansa na auren
gimbiya Larziya da batun komawa birnin Sin,
sei kawai yi kanin tsoro ya kau dagA zaciyaraa
Nan take ya daga takobinsa sama yana kurma
ihu ya sare makullin.
Nen take murfin rijiyar ya fadi cen gefe daya.
Bisa mamaki sei baiga komai ba Hantaru ya
sake rike takobinasa da kyau ya gyara tsayuwa
ya jiran yaga abinda da zai fito daga cikin rijiyar.
40
TASKARNOVELS.COM.NG
koda ya ji shiru sai ya matsa gaba da nufin ya
wuce kan rijiya ta uku itama ya budeta. Yana
gifta wennan rijiya ta kwatsam sai ya jiyo wani
irin gurnani irin wanda bai ta6a ji ba da huci na
busowa. Cikin razAni Hantaru ya ja aa beya ya
sake gyara tsayuwa Wani irin dogon hannun
bil'adama ne lafcece ya fara lekowa daga cikin
rijiyar,
sannan hannu na biyu ya leko. Daga can kuma
sai ga mutum ya taso sama a hankali gama
mikewa gaba daya. A sannAn ne Hantaru ya gA
she maridi ne. Tun da Hantaru yazo duniya bai
taba ganin bil'adama mai tsananin tsawo da
kauri ba tamkar wannan maridi, domin ita dai
rijiyar zurfinta ya kai kamu dubu, amma gashi
ta yiwa maridin kadan, tsugunnawa ma yai a
cikinta.
Fadinta ya kai kamu arba'in, amma da kyar
maridin ya fito daga cikinta, sai da ya muskuta
kirjinsa sannan ya sami damar fitowa. Hantaru
ya karewa wannan maridi kallo daga sama har
kasa sai zuciyarsa ta karaya ya tabbatar da
Cewa rayuwarsa na tsakanin RAI DA MUTUWA.
Kawai sai yaja da baya ya takure a jikin bangon
kogon, amman bai yar da takobinsa ba. Maridin
41
TASKARNOVELS.COM.NG
ya wangame katon bakinsa ya kurma wani ihu,
wanda ya haddasa girgizar kogon gaba ?aya har
duwatsu kanana suka rinka zubowa kasa. Karar
ihun tasa Hantaru ya yarda takobinsa ya rufe
kunnuwansa har ya tsugunna kasSa yana
neman maboya, domin ji ya yi kamar dodon
kunnensa zai fado kasa. Nan take maridin ya
shako wuyan Hantaru ta baya da
'yan yatsun hannunsa biyu ya ?aga sama
tamkar ya dauki fara, sai ga kafafun Hantaru na
wutsi-wutsil, gaba daya jikinsa na reto. Maridin
ya tsaya yana tunanin irin kisan da ya kamata ya
yiwa Hantaru. Da farko sai ya dunkule hannu ya
kai masa wawan naushi a fuska. Duk da cewa
yana ruke da wuyan Hantaru gam- sai da
Hantaru yi waf ya zunguri idon maridin da f
kafa, domin ya tabbatar da cewa idan maridin
ya gabza masa
Wannan naushi, sai ya tatitse fatarsa tamkar an
taka ayaba akan dutse. Tsokanewar idon da
Hantaru ya yiwa maridin ne yasa ya dimauce ya
saki wuyan Hantaru ya fado kasa, amma huk da
haka sai da hannun Maridin ya nutse a cikin
bangon kogon dutsen tamkar ansa diga da
guduma an buga a cikin bengo sai gashi ya
42
TASKARNOVELS.COM.NG
haddasa wawakeken rami ajikin bangon, amma
bai ji zafin komai ba a hannunsa tamkar ma
takarda ya huda. A fusece maridin ya juyo ya
?aga kafarsa pa y kawowa Hantaru mugun taku.
Cikin matukar zafin nama Hantaru ya goce ya
bar inda yake. Sai ga kafar Maridin ta lume a
cikin kasa iya kaurin gwiwarsa.
De ya zare kafarsa kuwa sai ga rami zururu
wanda za a iya saka mutum uku a ciki a
binnesu. Nan fa aka fara guje guje tsankanin
Hantaru da Maridin a cikin kogon, yana kai
masa wawan naushi da bugu da hannu da kafa
shi kuma yana gOcewa da zallewa. Dak inda
maridin ya gabza sai ya haddasa mugun rami,
walau bango ko kan kasa. Al'amarin da ya janyo
gaba dayan kogon ya
kama rugujewa. Sai ga kafar Maridin ta lume a
cikin kasa iya kaurin gwiwarsa. De ya zare
kafarsa kuwa sai ga rami zururu wanda za a iya
saka mutum uku a ciki a binnesu. Nan fa aka
fara guje guje tsankanin Hantaru da Maridin a
cikin kogon, yana kai masa wawan naushi da
bugu da hannu da kafa shi kuma yana gOcewa
da zallewa. Dak inda maridin ya gabza sai ya
haddasa mugun rami, walau bango ko kan kasa.
43
TASKARNOVELS.COM.NG
Al'amarin da ya janyo gaba dayan kogon ya
kama rugujewa ke nan, ya zamana cewa shi
kansa maridin hankalinsa ya tashi, don haka sai
ya koma gefe daya ya tsaya cak Yana hanki suka
kara kallon- kallo tsakaninsa da Hantaru.
Babban abin da ya fi tayarwa da Hantaru
hankali shi ne, kofar kogon ta rufe ruf, babu ta
inda ma zai iya fita bare ya nemi hanyar gudu
sakamakon rugujewar da kogon ya yi, manyan
duwatsu suka rikito kasa.
Nan fa Hantaru ya aiyana a ransa cewa bashi da
wata mafita face ya tunkari wannan maridi ya
San dabarar da zai bullo masa ya kashe shi.
Dole ne ayi daya cikin biyu, ko shi maridin ya
sami nasara ko shi Hantaru ya samu.
44
TASKARNOVELS.COM.NG
Kamar hadin baki sai maridin da Hantara suka
wangame baki a lokaci guda kowannensu y
kama kwarara ihu.
Abin da ya ?aurewa maridin kai kenan, domin a
wannan karon ihun maridin bai ruda Hantaru
ba, bare ya dimauce har ya toshe kunnuwansa.
Tun da wannan maridi ya wanzu a cikin wannan
kogo tsawon daruruwan shekaru bai ta6a ihu ba
ga duk abin da ya shigo abin ya iya jurewa ba.
Kai bama mutum ba hatta aljan idan yana
Wannan ihu nasa firgicewa suke, wasu su kama
gudawa, Wasu ma sanadiyyar kurmancewarsu
ke nAn.
Idan kuwa mutane ne ma take suke haukacewa,
amma yanzu sai gashi Hantaru ya jure masifar
ihun nasa harma yanA mai da martani da Dasa
ihun.
45
TASKARNOVELS.COM.NG
A zahirin gaskiya Hantaru bu karamar juriya ya
yi ba a wannan karon, domin gaba dayan jikinsa
ya kama tsuma da karkarwa domin ji yake
kamar an dura masa kwari masu yawa ba adadi
a cikin kunnuwansa, suna tsinttsinka jijiyoyin
kunnen, kuma yana jin kamar ana tsotse jinin
jikinsa.
Bayan kowannensu ya yi ihu da kururuwa har
gabadaya kogon ya gama rugujewa, duwatsun
suma suka rikito kasa, al'amarin da ya janyo
Hantaru ya sami sababbin raunika ke nan a
sassan jikinsa, in banda ma yana gocewa da tuni
manyan duwatsu sun danneshi. Shi kansa
Hantaru ya san cewa tsananin sa'a ne kawai ya
ceceshi a cikin wannan kogo, sa'adda yake
rugujewar amma ba zafin namansa ba.
Koda gama rugujewar kogon sai Maridin ya
falfalo da gudu yana take duwatsu suna
rumurmushewa, ya yiwo kan Hantaru gadangadan. Koda Hantaru ya ga mutuwa ta
durfafoshi sai shima ya yi ta maza ya ruga izuwa
kan maridin Shima yana mai ci gaba da kwarara
46
TASKARNOVELS.COM.NG
ihu shima, maridin yana nasa ihun, kowannensu
tafe yake cikin mugun nufi, kai da gani ka san
cewa idan akayi wannan gamo dole ne mutuwa
ta sami rabonta Sai da ya rage bafisaura taku
daya ba A tsakaninsu ba sai Hantaru ya yi sufa a
kasa tamkar akan kankara mai santsi yake ya
shiga karkashin Maridin ya takarkare iya
karfinsa ya gabza masa naushi da hannaye biyu
a marainansa.
Take maridin ya yi suman tsaye ya kame kamar
ya zamo gunki. Cikin zafin nama Hantaru ya
mike zumbur ta bayan maridin yasa guiwar
hannunsa ya doki tsakiyar hannun maridin na
hagu. Take hannun ya karye ya yi kara kas!
Maridin ya kurma ihu ya juyo a fusace ya
kawowa Hantaru mangari da daya hannun nasa.
Cikin sa'a kuwa ya sami Hantaru a kirji. Karfin
mangarin ne yasa Hantaru yai sama ya fado
kasa kan dutse ya baje a sume.
Maridin ya yunkura da kyar yana tafiyar tatata
kamar sabon dan kaciya a lokacin da karyayyen
47
TASKARNOVELS.COM.NG
hannunsa ke gilu-gilu kamar zai fadi kasa ya
nufi inda Hantaru ke kwance a sume.
Nufinsa kawai yaje ya tallafo kan Hantaru ya yi
masa rotse a ka, wato ya dagwargwaza fuskar
Hantaru. Har Maridin ya isa kan Hantaru ya
tsaya, Hantaru bai farfado ba. Nan take Maridin
yasa hannunsa ya tallafo kan Hantaru da nufin
ya naushi fuskar da dukkan karfinsa.
A dai-dai wanann lokaci ne Hantaru ya farfado,
idanunsa suka bude. Koda ya ga maridin ya daga
hannunsa lafiyayyen zai nausheshi. sai ya
yunkura cikin mugun zafin nama ya kamo
kary?yyen hannun ya fincika. Saboda tsananin
zafi da zogin da maridin yaji bai san sa'adda ya
saki ftsari ba.
Kafin ya yi wani yunkuri na cutar da Hantaru
tuni Hantaru ya sake kamo daya Iafiyayyen
hannun shima ya gabza mAsa naushi da guiwar
hannunsa. Take hannun ya karye ya yi kara
48
TASKARNOVELS.COM.NG
kamar na farko. Maridin ya fadi kasa da ruf da
ciki. Duk da haka Hantaru bai kyaleshi ba sai da
ya kama kafafunsa duka biyun da karfin tsiya
suma ya kakkaryasu daya bayan daya.
ihun da maridin ya yi a lokacin da Hantaru ke
karya masa kafafunsa ya ninka wanda ya yi da
furko sau goma, domin gaba daya halittun da ke
dajin sai da suka firgice suka kama sauya sheka.
Sauran wadunnan rijiyoyi kimanin guda dari da
casa in da ya'ya sai da murafensu suka bude,
gaba daya a lokaci guda.
Abinda ya fara yin fitar burgu daga cikin
rijiyoyin shi ne, takobin Saiful Lujara. Wata irin
takobi ce ta musamman wacce aka kerata da
lu'u lu'u sai sheki da walwali take tana kashe
idanu. Nan take haskenta ya haskake kogon
gaba daya. Da wani irin mugun karfin gudu
takobin ta taso sama. Koda Hantaru ya yi arba
da takobin sai ya yi wuf ya taka bayan maridin
ya daka tsalle sama yabi takobin tamkar an
harbashi daga cikin kwari. A can saman ya kamo
murikin takobin. Koda ya sunkuyo da kansa kas
49
TASKARNOVELS.COM.NG
a lokacin da yake durowa sai ya yi arba da
mugayen abubuwan da ke fitowa daga cikin
rijiyoyin, sai hankalinsa ya dugnzunma ainun,
domin ya san cewa irinsa ari ma ba za su iya
hallaka abubuwan ba.
Zan ci gaba.
Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake
son complete zai iya tuntubata ta wannan
number 08138873799 kira ko whatsapp.
MAZAN JIYA
Littafi na biyu 2
Part D
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
50
TASKARNOVELS.COM.NG
Mugayen dabbobin daji ne suka rinka fitar
burgu daga cikin rijiyoyin, mASu yawan tsiya ba
iyaka. Daga manyan zakuna, irin wanda ido bai
taba gani ba, sai manyan Kuraye da Damisoshi,
kuma fitowa suke tayi daga cikin rijiyar kamar
ba za su kare ba. Rijiyar da takobin Saiful
Lujaran ta fito ne kadai wani abin bai sake
fitowa daga cikinta ba. Tun a saman Hantaru ya
kara rike takobin Saifal Lujara da hannayensa
biyu gam-gam. Ai kuwa yana dira a cikin kogon
azababben yaki ya kacame tsakaninsa da
miyagun dabbobin, suka yanyameshi suna kai
masa cizo da yakushi, shi kuwa ya dinga
ragargazarsu da takobin Saiful Lujara, sai dai ka
ga a lokaci guda ya dara dabbobi uku ko hudu ya
tsargesu gida biyu sun zube kasa matattu.
In banda cewar Hantaru mutum ne mai matukar
zafin nama yana kaiwa dabbobin sara ta ko ina,
wato gabas da yamma, kuda da arewa, sama da
kasa, da tuni sun tumurmusheshi. Duk da zafin
naman nasa SAi da suka rinka kartar jikinsa
suna cizonsa amma saboda karfin sihiri kaifin
faratansu dana hakoran nasu baya tasiri a
51
TASKARNOVELS.COM.NG
jikinsa, amma kuma sun kumbura masa jiki sun
taru masa jim.
Babban abin da ya fi tayar Masa da hankali shi
ne, rashin karewar dabbobin, domin yana kashe
su ne wasu na kara fitowa daga cikin rijiyoyin
tamkara sannan ake haihuwarsu. Kuma abin da
ya lura da shi shi ne, babu kokarin da dabbobin
ke yi face su kwace takobin Saifal Lujara daga
hannunsa.
Hantaru ya yi nazari ya fahimci cewa idan da
aka Sami koda rabin sa'a ne a na wannan
gumurza lallai zai gaji har wadannan dabbobi su
kaishi kas su turmusheshi, idon kuwa suka
turmusheshi Lallai za ta kai cewa sun rabashi da
takobin Saiful Lujara, Sannan su hallakashi.
Koda Hantaru ya fahimci haka sai ya fara
tunanin mafita.
Abin da ya fara fado masa a rai shi ne, masu iya
magana sun ce "Gudu ba tsoro bane idan masifa
52
TASKARNOVELS.COM.NG
ta kai masifa " Koda gama aiyna hakan, sai
Hantaru ya shammaci dabbobin nan ya daka
wawan tsalle Sama ya yi fitar burgu daga cikin
kogon, tun da dai saman kogon ya yaye
sakamakon rugujewar da yayi.
Ai kuwa suma dabbobin sai suka daka tsalle
sama gaba dayansu suka bishi a sama. Hantaru
na dira a wajen kogon bisa turba sai ya fara
falfala matsanaicin gudu. Nan fa aka kasa tsere
tsakaninsa da dabbobin. Gudun da Hantaru ke yi
ya wuce gaban misali, domin gudu ne na sihiri,
Sai dai ka ga yana gifta bishiyoyin dajin
giftawar tauraruwa mai wutsiya. Abun takaici
da ya waigo sai ya ga wadannan dabbobi na daf
da shi kamar marabarsu bai wuce kamu daya
ba. Inda zai tsaya da taku daya zasu iya tsalle su
cimmesa, Abin da Hantaru bai sani ba shine
gudun da dabbobin suke yi shima na sihirine.
Sirrin shine duk halittar da ke cikin kogon da
takobin Saiful Lujara take an sihirceta, yadda ba
zasu taba bari kowa ya mallaki takobin ba sai
sun tsare takobin don kar tabar hannunsu.
53
TASKARNOVELS.COM.NG
Inda ace Hantaru ya yar da takobin dabbobin ba
zasu biyoshi ba. Haka dai Hantaru ya cigaba da
matsanaicin gudu, dabbobin na biye da shi daf
da daf suna gurnani da kartar kasa kamar sa ci
babu. shi kansa Hantaru duk da cewar yana da
dakakiyar zuciya a duk sa'adda ya waigo yayi
arba da dabbobin sai yaji zuciyarsa ta karaya
domin ya san cewa akwai iyakar lokacin da zai
iye jure wannan gudu, don haka idan ya gaji
dabbobin za su bankeshi sai abin da hali ya yi.
Komai jarumtakar mutum da juriyarsa idan ya
ga yadda wadannan dabbobi suka tuso Hantaru
a gaba dole ne zuciyarsa ta karaya domin ya san
cewa idan ma zai tsaya ya ci gaba da yakarsu ba
zai iya karar da su ba a cikin kwana bakwai
saboda yawansu. Sai da Hantaru ya shafe sa'a
bakwai yana gudu a cikin daji, wadannan
mugayen dabbobin na biye da shi babu daga
kafa.
Sa'a bakwai na cika ne suka iso cikin wani irin
daji mai yawan surkukiya da duhuwoyi gami da
kayoyi masu tsini. Bisa mamaki sai Hantaru yaji
54
TASKARNOVELS.COM.NG
kayoyin na huda jikinsa har jini na tsartuwa.
Alamarin da ya janyo ya fara layi da tangadi ke
nan. Amma saboda naci da juriya bai fasa gudun
ba su kuwa dabbobin da?a matsawa suke ta
cikin kayoyin tamkar suna hawa