komai, wato kan mai
uwa da wa bi.Bai Kyale duwatsu da bishiyoyin
da suka farfado bama. Nan da nan ya hautsina
dajiin gaba daya. Ba shiri sarki Maharaz, Hibru
da Inmal suka falfala da gudu suka bar inda
dodon yake suna gudu suna waigen halin da
dodon yake ciki. Sai da suka yi dan nisa daga
inda yake sannan suka tsaya suna hangensa..
Dodon bai daina tagagi da walagigi ba har sai
bayan sa'a guda sannan ya yanke jiki ya fadi
kasa rikica! Kamar katon tsauni ya fada cikin
teku domin sai da dajin gaba daya ya yi girgiza.
Da ganin abin da ya faru sai sarkin yaki Hibru ya
cire kambun sarautarsa na sarkin yaki ya
mikawa Inmal ya ce, "Ya kai dana hakika kaine
157
TASKARNOVELS.COM.NG
ka cancanci da wannan kambu, amma ba ni ba".
Da jin haka sai sarki Maharaz ya karbi kambun
daga hannun Hibru ya daurawa lnmal da kansa
a damtsen hannunsa ya dubeshi cikin
murmushi ya ce. Tabbas mahaifinka ya yi
gaskiya, kaine kafi cancanta da wannan kambu.
Ya kai Inmal ka yi sani cewa ko a cikin tarihin
sadaukan da zamaninsu ya gushe ba a taba
samun sadauki mai karancin shekaru irin naka
da ya yi irin wannan bajinta ba.". Gama fadin
hakan ke da wuya sai ga wadansu dakarun sarki
sun rugo garesu da gudu a kasa suna haki. Da
isowarsu sai suka zube kasa, dayansu ya bude
baki da kyar ta ambaci sunan gimbiya Mulaifa
yana mai nuni da hannunsa izuwa ga hanyar da
suka fito..! Kafin kowa ya ce wani abu tuni
Inmal ya falfala da azababben gudu ya bi
hanyar da aka nuna masa. Yana cikin gudun ne
ya hango keken dokin gimbiya Mulaifa a saman
wannan rami mai Zurfi, keken dokin na reto
saura kiris ya subuce zuwa kasa. A wannan
lokaci Mulaifa ta farfado daga dogon suman da
tayi, ta rinka kwala ihu.Koda Inmal ya jiyo ihun
Mulaifa sai ya kara karfin gudunsa har ma yana
daka tsalle yana kara dira gaba. A dai-dai
lokacin da ya yi tsallen karshe kafarsa ta dira
158
TASKARNOVELS.COM.NG
akan bakin ramin, kuma a sannan ne keken
dokin ya subuce ya yi kasa zai nutse izuwa
karshen ramin. Nan take Inmal ya sake daka
tatsalle ya ruko keken dokin da hannu daya
sanann ya ruko dutsen da ke saman ramin da
daya hannun nasa sai gashi keken dokin na
reto,shima Inmal yana reto a sama a lokacin da
Kwanjin hannunsa ya kumbura, jjiyoyin jikinsa
gaba daya suka tashi suka yi burdun-burdun. A
dai-dai wannan lokaci ne gimbiya Mulaifa ta
daina ihu.! Tana daga cikin keken dokin sai ta
kurawa lInmal idanu kawai ta ta kame kuma ta
kasa yin magana saboda tsananin mamakin irin
wannan' gagarumar bajinta da ya yi. Kwatsam!
Sai ga su sarki Maharaz sun iso wajen da gudu,
sannan sai ga sauran gaba dayan jama'ar
rundunar. Duk wanda ya iso ya ga Inmal a sama
yana reto kuma yana rike da keken doki da
hannu daya sai ya kame kamar gunki saboda
tsananin al'ajabi. Abin mamakin shi ne, wai shin
wane irin karfi ne da Inmal har da ya iya rike
keken doki da hannu daya alhalin dawakai uku
ne a jikin keken dokin,nauyinsu ma kadai ya
isheshi bare bare kuma ga nauyin shi kansa
keken dokin wanda aka yi shi da karafa masu
nauyi. Koda isowar sarki Maharaz ya ga halin
159
TASKARNOVELS.COM.NG
da Inmal yake ciki sai ya dubi Dakarun
aljanunsa ya daka musu tsawa ya ce, "Me kuke
jira ne,maza ku kaiwa Inmal dauki.. Nan take
wadansu aljanu guda biyu suka kaiwa Inmal
dauki suka cafoshi tare da keken dokin suka yi
saman ramin, sannan suka kawosu gaban sarki
Maharaz suka saukesu a hankali. Kamar hadin
baki sai sarki Maharaz da Hibru suka risina suka
yi sujjada ga jarumi Inmal. Koda ganin haka sai
gaba dayan dakarun tawagar ma suka yi jinjina
a gareshi. Ita kuwa gimbiva. Mulaifa tana fitowa
daga cikin keken dokin sai ta rungume inmal ta
fashe da kukan farin ciki. Al'amarin da ya sa
gaba dayan jama'ar da k wajen suka hau rafka
tafi. Dajin gaba daya ya cika da tafin yana amsa
kuwa,. Bayan Mulaifa ta janye jikinta daga cikin
na Inmal ta koma gefe daya ta tsaya sai sarki
Maharaz ya zo gaban Inmal ya tsaya yana
murmushi ya dafa kafadarsa ya ce, "Ya kai
jarumin jarumai, kuma gwarzon zamani,hakika
a yau na tsinke da al'amarinka bisa ganin
wannan gagarumar bajinta da ka yi, in ba don
kai ba, bamu san yadda zamu yi da wannan
katon dodo ba, domin koda zamu kashe shi sai
da yawanmu sun hallaka. Bugu da kari gashi a
gaban idanuna ka ceci rayuwar 'yata a lokacin
160
TASKARNOVELS.COM.NG
da babu abin da zan iya yi ma ta tun da ina can
wani wuri dabam. Tsananin karfin gudunka da
karfin jarumtakarka ne ya sa ka sami nasarar
ceto rayuwarta. Ya kai Inmal nayi maka
alkawari lallai zan yi maka sakaiya da lada irin
wanda ban taba baiwa wani ba". Koda jin haka
sai lnmal yai murmushi kuma ya yi godiya. Nan
dai sarki ya bada umarni aka shiga debo mutane
da aljanu wadanda suka mutu da wadanda suka
raunana aka binne na binnewa,wadanda za a
yiwa magani aka yi musu magani. Sai da aka
kwana a wajen sanann da sassafe aka tashi aka
kimtsa aka ci gaba da tafiya. Wannan karon sai
su sarki Maharaz suka ga tafiyar tasu ta kara
sauri ainun, domin dawakansu da rakumansu
suna yin wani irin azababben gudu na ban
mamaki. Suna gifta dazuzzuka tamkar giftawar
tauraruwa mai wutsiya. A cikin kwanaki goma
sha bakwai suka hango tekun bahar Sufiya daga
can nesa. Tun daga nesan suka ga wadansu
Kwari kanana bakake sun cika sararin
samaniya da kan tekun tamkar babu komai a
wajen sai su. Koda Inmal ya hango wadannan
Kwari sai ya cika da mamaki ya dubi Hibru ya
ce, "Ya kai Abbana wai shin wadancan
tsuntsayen wadanne iri ne? Belbelu ne ko
161
TASKARNOVELS.COM.NG
Tsattsewala?". Kafin Hibru ya budi baki ya ce
wani abu sai sarki Maharaz ya tari numfashinsa
ya dubi Inmal ya ce, "Ai wadanda abubuwan da
kake hangowa sun cika sama da kasa ba
tsuntsaye bane, rudunar abokan gabarmu ce,
yanzu haka suna kan laluben inda takobin
SAIFUL LUJARA take ne a cikin kogin". Koda jin
wannan batu sai Inmal ya cika da tsananin
mamaki kuma yaji tsoro ya darsu a cikin
zuciyarsa bisa ganin yawan abokan gabar
wanda idan bai ninka tasu rundunar sau uku ba,
zai gaza sau biyu ba. Cikin matukar damuwa
Inmal ya ce, "To yanzu ta ya ya muma zamu iya
laluben takobin a cikin wannan teku?" Sarki
Maharaz ya ce, "Ta hanyar afkawa abokan gabar
tamu da yaki, idan muka kawar da su sai mu
shiga laluben takobin a cikin kwanciyar
hankali" Koda gama fadin haka sai sarki
Maharaz ya yi shiru bai kara cewa komai ba, a
sannan ne suka fara shaida dandazon abokan
gabar tasu suma su sarki Dujalu suka ankara da
tasu tahowar. Wohoho! Bala'i ba a sa masa
rana. ldan masife ta durfafo, to fe babu abin da
ya isa ya tsaide ita face yar uwarta masifa. Koda
sarki Dujalu ya dago kai ya hango su sarki
Maharaz sai ya kwarara uban ihu ya dakawa
162
TASKARNOVELS.COM.NG
dakarunsa tsawa yuna mai basu umarnin su tafi
su tari abokan gaba tun gabannin su Karaso
bakin tekum. Da jin wannan umarni sai
dakarun aljanu suka bude fuka- fukansu guka
nufi dandazon su Maharaz suna mugun ihu rike
da muggan makamai. Ihu nc wanda ka iya
sabautar da bil'adama su zauce domin gaba
dayan tsuntsayen da ke wajen ma wadanda ke
shawagi a sama sai suku kama fadowa kasa
matattu. Halittun da ke cikin ruwa kuwa sai gani
aka yi gawarwakinsu na tasowa sama saboda
masifar wennan inu na aljanu. Su kansu
jama'ar sarki Maharaz in ba don shi saki
Maharaz din ya taresu da Karfin sihirinsa ba da
nan take gaba dayansu za su kurmance ko su
haukace ko kuma duk su zube kasa matattu.
Lokacin da sarki Maharaz ya ga dakarun aljanu
na sarki Dujalu sun durfafo inda suke sai shima
ya baiwa nasa dakarun aljanun umamin su
taresu. Ai kuwa suma sai suka yi sama suka ruga
kansu tamkar an cilla kibiyoyi. Kafin kiftawar
ido rundunar biyu sun hade a sararin samaniya
sun kacame da fitinannen yaki wanda ya fi
gaban mai tunani ya tunano bare mai misali ya
misalta. Nan fa suma dakarum biladama da ke
kasa na kowanne 6angare suka falfalo da
163
TASKARNOVELS.COM.NG
matsannicin gudu ana kokarin a hadu. Kaico!
Inda ace mutum na nan a lokacin da wadannen
runduna biyu ta yunkura za a hadu ya ga irin
tsanonin yawansu sai ya y tsammemin cewa
gaba dayan mutanen duniya ne za su hade da
gaba dayan daboobin dunya.Ai kuwa bangare
biyun na haduwa a tsakiya aka ruguntsue da
azababban yaki mai dugunzumoa hankali da
tafasa kwakwalwa. Saboda jijigar da kasa tayi a
wann n r na sai da gaba dayan tekunan duniya
suka hausine guka kana ambahiyar ruwa
saboda tekun bahar Sufiya ne no babbar cibiya
na dukkanin tekunan duniya. Wohohol A
wannan rana an yi gumurzu, dauki ba dadi,
artabu, turnuku, ruguntsuni da fafatawa irin
wacce ba a taba yin kamanta ba a duniye, kuma
ba za a taba yi ba. Sai da aka kwana aka yini ana
ragargazar mazajen aljanu da na biladama aka
rinka asarar rayuka amma komai kwarin idon
mutum da iya kallon Kurillarsa bai isa ya iya
tantance 6angaren da ke samun nasara ba. A
duk sa'adda sarki Dujalu ya durfafi wurin sai dai
ka ga fili, duk inda ya sa gabansa sai ka ga maza
na zubcwa tamkar guguwar annoba ce ta fado
daga sama. Haka ma a 6angaren su sarki
Maharaz duk inda sadauki Inmal ya durfafa sai
164
TASKARNOVELS.COM.NG
dai ga yana banke mutane da kirjinsa,
hannaycnsa da kafafunsa suna zubewa kasa
tamkar ana sassabe a gona,an rasa wanda zai
iya tsayar da shi. Sarki Maharaz kuwa yana
amfani da karfin sihirinsa ne kawai domin duk
inda yai numi da sandarsa ta tsafi sai dai ka ga
kawunan bil'adama na gutsurewa suna faduwa
kasa. Sadauki Hibri ma ba a barshi a baya ba
domin shima ragargazar maza yake yana ta yin
ta'adi. A bangaren serki Dujalu ma akwai
wadansu zakwakuran mayakansa guda biyu
wadanda ake kira Matinu da Ratiju wadanda
summa sun addabi jama'ar sarki Maharaz, don
duk inda suka sa gabansu sai dai kaga maza na
ratattakewa. Lokacin da Mutinu da Ratiju suka
hango irin mummunar barnar da sarki Maharaz
da Hibru ke yiwa jama'arsu sai suka yi KUKAN
KURA suka ruga garesu aka ruguntsume da
wani masifaffen yakin. Matinu ya tari sarki
Maharaz shi kuwa Ratiju sai ya tari?
Hibru.Wani abin mamaki shi ne Matinu yana
takama da a karfin tsafi ne zalla ba wai
jaruntaka ba shi kuwa Ratiju tsagwaron
jarumtaka ce da shi kawai sai gashi duk su
biyun sun tari dai-dai da su don haka sai fadan
nasu ya zama abin sha'awa kuma abin tsorO
165
TASKARNOVELS.COM.NG
domin komai zai iya faruwa babu wanda yake
da tabbacin samun nasara akan abokim
gwaminsa saboda karfi yazo daya. Lokacin da
sarki Maharaz ya ga karfin sihirinsa ya zo daidai da na Matinu sai ya cika da tsananin
mamaki domin shi a zatonsa babu mai iya
karawa da shi a fagen yaki face sarki Dujalu
amma sai gashi daya daga cikiin yaran Dujalu ya
bashi mamaki. Abin da sarki Maharez bai sani
ba shi ne,Sarki Dujalu ya boiwa Matinu gabe
dayan Karfin sihirinsa ne yanzu yana wannan
yaki ne da zallar karfin damtsensa. Tab lallai
wani aiki sai cikakkun jarumai marasa tsoro,
duk da nima fa ina cikin jaruman tunda nine na
ke dauko maku rahoto. Zan ci gaba. Da fatan
mun wuni cikin koshin lafiya, sannan duk
wanda yake son complete zai iya tuntubata ta
wannan number 08138873799 kira ko
whatsapp. MAZAN JIYA Littafi na biyu 2 Part
K Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar
Saleh AlQuyraemey Kamar yadda Inmal ya
addabi dakarun Dujalu ya rinka ratsawa ta
cikinsa ta kowanne bangare yana ragargazarsu
haka shima sarki Dujalu ya addabi jama'ar sarki
Maharaz tamkar an auna barnar da suke yi tazo
dai-dai.Ana cikin haka ne sarki Dujalu ya hango
166
TASKARNOVELS.COM.NG
irin mummunar barnar da Inmal ke yi sai
hankalinsa ya dugunzuma kuma ya cika da
tsananin mamakin yadda Karamin yaro ya sami
irin wannan gagarumin karfi haka. Cikin
tsananin fusata sarki Maharaz ya tarwatsa
mazajen da ke gabansa ya falfala da gudun tsiya
tamkar ana shara da tsintsiya ya durfafi inda
Inmal yakc. Ai kuwa sai Inmal ya dago kai ya
hango tahowarsa. Nan take shima Inmal ya
tarwatsa mazajen da suka lullu6eshi ya falfala
da matsanaicin gudu yana banke mutane da
dawakai, rakuma da alfadarai da ke gabansa ya
nufi sarki Dujalu cikin dacin rai da kunar zuci
gami da mugun nufi domin su hadu. Ai kuwa
suna haduwa suka kacame da mugun yaki na
ban tsoro da ban al'ajabi. Tamkar jikinsu ba na
jini da tsoka bane haka suka rinka kaiwa juna
sara da suka cikin tsananin juriya, zafin nama
da bajinta. Sai gashi tsohon kashi ya hadu da
sabon kashi,naci da naci, zuciya da zuciya,
kowannensu yaki yake yi iya karfinsa tamkar ba
za su taba dainawa ba facc an tashi duniyar
gaba daya.Haka dai aka ci gaba da wannan
masifaffen yaki, har sai da rana ta fadi, gari ya
soma duhu. Kai saboda balain artabun da ake yi
a sama da kasa, wato aljanu nayi, mutane nayi
167
TASKARNOVELS.COM.NG
sai da wata irin gagarumar tsawa da walkiya
suka addabi kowa, tartsatsin wuta kuwa ya
rinka fantsama yana haddasa gobara har a cikin
tekun. Babu wani bangare da ke shirin ja da
baya a yakin. Mutane da aljanu suka rinka
zabga gumi, yunwa da kishirwa ta addabi kowa.
Gashi dai an zo da guzurin abincin kuma ga
ruwan teku ana gani amma sai ci da sha ya
gagari kowa saboda bala'in da ake ciki da
mugun tashin hankalin da ake fuskanta. Ba shiri
dan dole kowanne bangare suka busa kahon
janye yakin domin tsananin duhu da hayakin
wuta ya sa ba a shaida juna ha ta kai cewa
idanu sun rufe mnutane sun fara yakar yan
uwansu ma basu sani ba. Koda jin sautin kahon
na kowanne bangare sai duk aka ja da baya aka
daina yakin tamkar daukewar ruwan sama a
lokaci guda. A sannan ne matsafa suka samar da
hasken tsafi kowa ya iya ganin komai. Kaico!
Hakika yaki masifa.Da baiyanar wannan haske
sai ga gawarwakin mutane da aljanu zube a kas
ko ina rututu, babu inda mutum zai iya takawa
da kafarsa face ya taka gawa. Kai har akan
ruwan tekun gawarwaki ne barjik babu adadi
kuma ba kyan gani. Jini kuwa gashi nan yana ta
gudu da malala akan kasa har ya jirkita ruwan
168
TASKARNOVELS.COM.NG
tekun gaba daya yana neman rineshi. Komai
kallon Kurillar mutum bai isa ya iya tantance
6angaren da aka fi yiwa barna ba. A gaba dayan
mazajen da ke filin wannan yaki walau na
mutane ko na aljanu babu mahalukin da bashi
da raunuka a jikinsa,hatta manyan baraden
kuwa, wato su sarki Dujalu da su Inmal. Bayan
kOwanne bangare sun ja da baya nesa da juna
sai aka shiga aikin binne gawarwaki, masu kuka
nayi, masu bakin ciki nayi, kuma a sanann ne
kOwa ya rinka neman ruwan sha da abinci,
sannan kuma aka rinka sanya magani a raunika.
Masu karaya aka rinka gyarasu suna ihu bisa jin
radadi da zogin gyara. Manyan mazaje kuwa,
za ka ga sun yi shiru ko motsi basa yi. In ba don
albarkacin mata ba wadanda aka taho da su
wannan yaki da ba za a sami masu dawaniyar
kula da lafiyar mutane ba domin gaba dayan
mazajen babu wanda bai jigata ba ainun, wasu
ma kamar ba za su rayu ba wasu kuwa sun
gama zama nakasassu ba zama su iya ci gaba da
yaki ba. A 6angaren su sarki Maharaz
kuwa,bayan an kafa tantuna sai sarki Maharaz,
Hibru da Inmal suka taru a cikin tantin sarki
Maharaz kuyangi na sa musu magani a jikin
raunikan jikinsu, gimbiya Mulaifa ce da kanta
169
TASKARNOVELS.COM.NG
take sawa Inmal magani a jikinsa bata yarda
wata kuyanga ta taba shi ba. Bayan an tsaida
jinin da ke zuba a jikinsu kuma sun ci abinci
sun sha ruwa sun sami 'yar nutsuwa sai sarki
Maharaz ya ja dogon numfashi sannan ya dubi
sarkin yaki Hibru ya ce, "Ya kai abokina yanzu a
hangenka me kake ganin zai faru idan aka ci
gaba da wannan yaki?" Koda jin wannan
tambaya sai shima Hibru yai ajiyar zuciya
sannan ya dubi sarki Maharaz ya cc, "Ya
shugabana ni dai a ganina a Karshen yakin nan
RAGAS za a yi kowa da komai sai ya mutu, ka ga
ke nan babu bangaren da zai iya mallakar
wannan takobi ta Saiful Lujara da ke karkashin
tekun nan tun da gashi muna kallon tekun da
idanuwanmu amma shiga cikinta ma ya
gagaremu bare ayi laluben inda takobin take."
Koda jin wannan batu sai Inmal ya yi murmushi
saman ya dubi Hibru ya ce, "Haba ya Abbana
saboda me za ka yi waman batu, ai har abada
mutum ba ya fidda rai ga samun rabo muddin
yana numfashi a doron Kasa. Ni a rayuwata
zuciyata ba ta taba karaya ba bisa samun abin
da zuciyata ke so. Na yi imani da hakan dari
bisa dari saboda haka na Kudurce a raina idan
kowa da komai zai hallaka a bakin wamnan
170
TASKARNOVELS.COM.NG
tekun ya zamana saura ni kadai jal lallai sai na
lalubo takobin saiful Lujara a karkashin
wannan teku kodakuwa zan hallaka a kokarin
hakan. Ai rai ba a bakin komai yake ba muddin
akwai biyan bukata". Koda jin haka sai sarki
Maharaz ya yi murmushi ya cc, "Da kyau
jarumin jarumai, tauraron zamani, ka ci gaba da
jajirccwa bisa wannan Kuduri naka koda kuwa
gaba dayan jama'ata zamu karc ya zamana
saura kai kadai jal. Ka sani ccwa idan har ka
sami nasarar mallskar wannan takobi ta Saiful
Lujara sannan ka mallaki mashin Galilil Haras
da hular Lamsara ka ajiye abin tarihin da babu
wani mahalukin da ya ta6a ajiyewa a
duniya,kuma sai ka sami daukaka wacce babu
wanda zai samu. Ya kai abin alfaharina kuma
mafarkina na gobe kayi iya yinka don ganin ka
cimma buri ka sani cewa rayuwarmu gaba daya
a yanzu ta dogara da iyakar kokarinka domin
karfin sihirinmu da karfin damtsenmu ba za su
iya yin komai ba face kawai kara maka Kwarin
guiwa." Sa'adda sarki Maharaz ya zo nan a
zancensa sai Inmal ya cika da tsananin mamaki
ya dubeshi ya ce, "Ya shugabana ya ya ni da
nake yaro kankani a cikinku za ka ce rayuwarku
ta dogara a hannuna? Ka yi sani cewa ni kaina
171
TASKARNOVELS.COM.NG
na tsorata da al'amarin sarki Dujalu a lokacin
da muka fara fafata yaki ni da shi, domin ban
ta6a ganin mutum mai tsananin karfin dantse
kamar sa ba, gami da zafin nama. Sannan yana
da matukar juriya da naci fiye da yadda nake da
su. Duk da cewar zuciyata bata taba karaya ba
akan dukkan al'amari amma a wannan karon
akwai darsuwar kokwanto a cikinta". Sa'adda
sarki Maharaz yaji wamnan batu na Inmal sai ya
bushc da dariya sannan ya dubi 'yarsa Mulaifa
kuma ya dubi Inmal ya ce, "Ai kuwa idan har
nayi tsawon rai a waman yaki sadakin aurenka
na yata Mulaifa shi ne samun nasararka akan
dauko takobin Saiful Lujara a cikin Karkashin
wannan teku. Idan har ka kasa dauko wannan
takobi to har abada ba za ka auri 'yata ba".
Koda gama wannan jawabi sai sarki Maharaz ya
kishingida bisa shimfidar da yake zaune ya
lummshe idanunsa. Shima Hibru sai ya yi koyi
da abin da sarki Maharaz ya yi.Gimbiya Mulaifa
da Inmal kuwa sai suka Kurawa jumansu idanu
cikin tsananin tashin hankali da fargaba. Nan
take hawaye ya zubowa Mulaifa ta rungume
iNmal tana mai yi masa rada a kunne ta ce,
"Idan har kaunar da kake yi mini ta gaskiya ce
duk yadda za ka yi ka tabbatar da cewa ka
172
TASKARNOVELS.COM.NG
dauko wannan takobi ta Saiful Lujara. Idan
kuwa ka kasa bana tsammanin ccwa zan ci gaba
da rayuwa a duniya". Koda jin wannan batu sai
idanun Inmal suka zazzaro yaji hankalinsa ya yi
mummunan tashi, bai san sa'adda jikinsa ya
kama tsuma ba yaji kamar ya tashi ya ruga da
gudu ya dauki kahon yaki ya busa domin a ci
gaba da wannan masifaffen yaki. Wannan shi nc
abin da ya faru ga su Inmal bayan an fafata
azababben yaki tsakanin ruodunarsu da
rundunar sarki Dujalu a karo