dole ne ki dinga boye
fuskarta da dukkan ilahirin jikinta har izuwa
sa'ar da zata zama budurwa, idan kuma ba haka
ba kuwa to ba zata yi tsawon rai ba, kuma
sannan aljanu zasu rinka shiga jikinta suna
lalata mata rayuwa har ta haukace ko ta hallaka
sabida tsananin kyawunta.
Bugu da kari idan har kina son wannan ya taki
ta samu daukaka da matsayi babba a duniya,
dole ne ki aura mata mijin wannan yarinya yar
sarkin birnin hindu zata aura.
Yake wannan matar sarki kiyi sani cewa Ni suna
na aljani sautul baharu, kuma tun kina jaririya
na kamu da tsananin kaunarki, amma saboda
bana son na cutar da ke shiyasa ban shiga
jikinki ba, domin idan har masoyi yana kaunar
masoyinsa bil'adama ba zai iya cutar da shi ba,
na kasance babban da a wajen sarkin bokayen
aljanu na duniya, saboda haka duk wani sihiri
na tsafi na duniya na gajeshi, kuma komai naake
so a duniyar nan zan iya mallakarsa, amman
bana son komai face na mutu da soyayyarki a
zuciyata da kuma jin kyawawan kalamai daga
298
TASKARNOVELS.COM.NG
bakinki, na sani cewa bai kamata aljani ya auri
mutun ba, tabbatas inda ace ina da ikon sauya
halitta daga aljan zuwa mutum da tuntuni nayi
domin na samu damar aurenki, tun a ranar da
mahaifiyarki ta haifeni na gani a wata rana da
kika fito yawon shan iska, a wannan lokaci an
shifideki akan gado kina cikin turaka, sai na
tsaya daf dake na kura maki idanu, na dinga
maki murmushi kema sai naga kina maida mani
da martanin murmushin kin ta dariya.
Mahaifiyarki na can nesa kadan da ke, koda ta
hango abinda kike yi sai ta cika da mamaki
domin babu kowa a kusa da ke, abinda bata sani
ba shine kina ganina ina ganinki ita ce dai bata
iya ganina, daga wannan rana kullum sai na
ziyarceki sau bakwai domin kuwa sai na kalleki
nake jin dadi a cikin zuciyata, duk ranar da ban
ganki ba kuwa sai na yi zazzabi gami da ciwon
kai, hakika so cuta ne domin tsananin kaunar da
nake maki take take jefani a cikin wannan hali,
haka dai na kasance a tare da ke dare da rana na
zamo kamar mai tsaron lafiyarki, sau tari
iyyaenki sun sha ganin abubuwan mamaki da
dama, domin duk irin abin tashin hankalin daya
durfafo gidanku sai aga an kawar da shi, kuma a
rasa wanda ya kawar da shi din?
299
TASKARNOVELS.COM.NG
Haka dai kika fara girma har kika zama yar
shekara bakwai, a sannan ne kyawunki ya kara
fitowa karara, har mutane suka fara tsammanin
ke ba mutum bace aljana ce, aljanu kuwa sai
suka rinka kawo maki hari ni kuwa sai na rinka
fatartakarsu na hanasu shiga jikinki, bisa
wannan daliline na kulla gaba mai tsanani da
sarkin sadaukan aljanu na duniya, wani aljani
da ake kira da Barzuma ibn Kalsawar. Sai da
muka kwana arba'in muna yaki ni da shi ya
zamana cewa dukkaninmu mun suma sau
saba'in da bakwai jikin mu yayi fatafata da
raunika muka zube muna nufashi da kyar, anan
take aljani Barzuma ya tunkuyi kasa ni kuwa sai
nayi sa'a yan uwana sun zo giftawa suka ganni,
cikin dimauta suka daukeni suka tafi da ni gida
domin ayi jinyata, duk da ina cikin halin jinya
amman ban fasa zuwa wajenki ba kullum sau
bakwai nake zuwa gareki, ina tsaron lafiyarki
dan kada wasu aljanun ko kuma mutane su
cutar da ke. Ko sau daya ban taba bayyana a
gareki ba dan haka kika girma kika yi aure kawo
izuwa yanzu baki taba ganina ba, sai yanzu da
nake maki wannan bayani. Kiyi sani cewa a
ranar da aka daura aurenki da sarki sai da na
suma sau uku saboda bakin ciki, kuma na kwana
300
TASKARNOVELS.COM.NG
arba'in ina kuka da takaici ba ci ba sha, yanzu da
naga zaki haihuwa sai naji soyayyar da nake
maki ta tashi daga kanki ta koma kan yarki da
zaki haifa, nayi alkawari zan ci gaba da tsaron
lafiyar wannan ya da zaki haifa har izuwa
karshen rayuwata, amman ina mai dada yi maki
tuni da cewar lallai ki tabbar yarki ta auri mijin
da yr sarki Nashmir zata aura anan gaba koda
kuwa bakya raye, bani da wata bukata a wajenki
face ki furta mani kalmar karshe ta kauna muyi
bankwana domin ba zan sake bayyana ba a
gareki, amman alkawarin dana dauka akan
yarki lallai zan cika shi, kuma zan dinga bayyana
a gareta ina taimakonta bisa dukkan abinda
take son yi face wanda yafi karfina, wannan
shine kalami na karshe a gareki yake abar
kaunata, wadda nake kwana na tashi da
begenta.
Koda Aljani Sautul Baharu yazo nan a zancensa
sai idanunsa suka ciko da kwalla ya fara zubar
da hawaye. Al'amarin daya karya zuciyar
mahaifiyata kenan, nan take itama ta kamu da
tsananin tausayinsa, ta zubar da hawaye sannan
ta ce Ya kai babban masoyina hakika kaunar da
ka nuna mani ba karama bace, tunda ga shi ka
sallama rayuwarka domin tawa, inda da
301
TASKARNOVELS.COM.NG
tsautsayi da tuni ka mutu sakamakon fafatawar
da kayi da sarkin sadaukan aljanu wato
Barzuma ibn Kalsawar, haka kuma gashi ka
shekara ashirin da biyar kana kaunata da
begena a cikin zuciyarka da karfin tsiya bata
bari ta zugaka ka kashe mijin ba, ko kuma tasa
ka saceni ka kaini can inda babu mai iya zuwa,
lalla? kai masoyina ne na kwarai wanda har
abada bazan taba mantawa da shi ba, na rantse
da darajar iyayena ind ina da ikon suya halittata
daga mutum zuwa aljana da nayi domin na
aureka, na zama abokinyar rayuwarka ta har
abada.
D jin wannan batu sai hawayen farin ciki ya
zubo wa Aljani Sautul Baharu yace yi shiru haka
ya masoyiyata hakika babu wata sauran kalma
mai dadi da zaki furta mani wacce ta fi wannan,
gama fadin hakan keda wuya sai aljani sautul
baharu ya bace bat! Mahaifiyata ta neme shi
sama ko kasa ta rasa, nan fa ta rude ta kama
guje-guje a cikin gidan tana mai kiran sunansa,
amman har ta gaji da yawonta ta hakura. Daga
wannan rana mahaifiyata bata sake ganin aljani
sautul baharu ba har ta bar duniya.
302
TASKARNOVELS.COM.NG
Ni ko tun ina da shekara tara a duniya na saba
da shi, ya zamana cewa dare da rana muna tare,
bamu taba rabuw ba, kuma duk abinda zanyi
shine yake bani shawara, ban taba kaucewa
maganarsa ba. Wata rana ina zaune ni kadai a
cikin turakata sai kawai naga aljani Sautul
Baharu ya bayyana a gabana cikin mugun
yanayi, domin duk jikinsa sarane da takobi jini
na kwarara daga jikin nasa, cikin firgici da
dimauta na mike tsaye na rungumo shi alokacin
daya yanke jiki yana shirin faduwa kasa, nna
take fashe da kuka a lokacin da nake
tambayarsa wanda yayi masa wannan mugun
aikin.
Aljani Sautul Baharu ya bude baki da kyar a
lokacin da numfashinsa ke sarkewa ya kura
mani ido a lokacin da hawaye ke shatata daga
cikin idanunsa, sannan yayi mani murmushin
karfin hali ya ce yake yar babbar masoyiyata
kiyi sani cewa ina farin ciki a yau daya kasance
zan mutu a wannan kyawawan hannaye na ki,
ba wani bane yayi mani wannan mugun aiki ba
face mahaifin Barzuma Ibn Kalsuwar domin yq
dauki fansar kisan da nayi wa dansa, farin cikina
na biyu shine na sadu dake kafin raina ya fita
dan haka yanzu take zan mallaka maki dukkan
303
TASKARNOVELS.COM.NG
wani sirrin tsafina dana gada a wurin mahaifina,
ina mai gargadinki da kada ki kuskura kiyi
amfani da wannan sihiri face a ranar da wani
gawurtaccen boka yazo wanann birni naku da
nufin ya rabaki da mahaifinki, magnata ta
karshe a gareki ita ce duk yadda zaki yi kiyi
domin ki tabbar da cewa kin auri mijin da
gimbiya Ramlatus siyam yar sarki Nashmir zata
aura, ta haka ne kadai zaki iya samun babban
matsayi da daukaka a duniya, yanzu na
umarceki da ki bude bakin ki.
Koda jin haka sai na bude bakin nawa ba tare da
wata gardama ba, nan take naga wani irin jan
hayaki yana fitowa daga cikin bakin aljani
Sautul Baharu yana shiga cikin nawa bakin,
hasken na gama shiga sai jikinsa ya sandare
komai nasa ya daina aiki. Koda ganin haka sai na
rungumeshi na fashe da matsanancin kuka
saboda tsananin shakuwa da shakuwar da nayi
da shi, naji kmaar a sannan ne na rasa
mahaifiyata. Na dade a cikin alhinin rashin
Aljani Sautul Baharu bn samu nutsuwa b sai
bayan wata uku.
Sa'adda Gimbiya Rahila ta zo nan a zancenta sai
boka Muzafar da sarki Lafaru suka cika da
304
TASKARNOVELS.COM.NG
tsananin al'ajabi, boka Muzafar ya ja dogon
numfashi annan ya ce hakika Ruwa baya tsami
banza, ai tunda naji kin fadi sirrina nasan cewa
kina tare da sirrin tsafi mai karfin garske a
jikinki, yanzu na ji labarinki sai kuma ki fada
mana sharadin da kike son gindaya mana.
Tai murmushi tace ai nagama gindaya maku
sharadina a cikin labarin dana baku, sharadin
kuw shine bazan sa aljani Maraful Dauwas ya
biya maku bukatarku ba face kun dauki
alkawari cewa idn har bukatarku ta biya sarki
Lafaru zai aure ni a ranar da ya auri Gimbiya
Ramlatus siyam domin na samu matsayi da
daukaka irin nata, tunda yanzu ni da ita munyi
kunnen doki a fagen kyau.
Lokacin da boka Muzafar da sarki Lafaru suka ji
wannan batu daga bakin Gimbiya Rahila sai
suka dubi jjuna tare da yin shiru har izuwa
tsawon yan dakiku, suka ma rasa abinda zasu
ce, daga can sai boka Muzafar ya dago kai ya
dubi Gimbiya Rahila ya ce ki bamu zuwa gobe
muna da bukatar yin shawara.
Da jin haka sai Gimbiya Rahila ta yi murmushi
sannan ta juya da nufin ficewa daga cikin tantin,
305
TASKARNOVELS.COM.NG
har ta je bakin kofar fita sai ta juyo ta dubi sarki
lafaru ta ce kada ka kuskura ka bayar da
labarina ga sauran abokan tafiyarmu, domin
bana son su san koni wace ce, kuma suga
zahirin kyawuna da surata har sai mun isa
kogon darul ikisina, tana gama fadin hakan sai
ta fice daga cikin tantin ta bar boka Muzafar da
sarki Lafaru a cikin wani irin yanayi na tsananin
damuwa kamar ruwa ya cisu.
Da sassafe su duka suka tashi suka kimtsa,
jaruman biyar suka gyara makamansu kowa
yayi damara sannan boka Muzafar ya dubesu
daya bayan daya ya ce acikin ku waye zai wuce
gaba yayi mana jagora a cikin wannan daji da
zamu shiga?
Ko da jin wannan tambaya sai kowa yayi shiru
aka rasa wanda zai wuce gaba, koda ganin haka
sai sarki Lafaru ya ce ya kai wannan babban
boka kayi sani cewa ai kaine kafi kowa cancanta
da yin jagora a wannan tafiya, tunda kaine uban
tafiya, kuma kafi kowa sanin hanya.
Boka Muzafar ya ce kwarai kuwa haka ne
abinda ka fada, amman ni kaina ina shakkar
abinda ke kan hanyar nan, dan haka ba zan iya
306
TASKARNOVELS.COM.NG
wucewa gaba ba, face na samu wanda zai tayani
jagoranci har na samu kwarin guiwa, caraf sai
gimbiya Rahila ta ce ni zan tayaka jagorancin
wannan tafiya.
Nan take Gimbiya ta wuce can gaba ta tsaya
kusa da boka Muzafar, al'amarin da ya baiwa su
sadauki Haiman mamaki kenan, Zarina ta dubi
boka Muzafar ta ce wai shin ita waccan
budurwar da tayi gangancin shigewa kn gaba
wace ce ita? Me yasa tunda aka fara wannan
tafiya take boye fuskarta da kuma jikinta? Wai
shin ma mene ne amfaninta a wannan tafiya?
Boka Muzafar ya dubi Zarina ya ce Ya Zarina ai
bai kamata ki tambayi kaza hanyar rafi ba,
agwagwa zaki tambaya ki sha labari, babu
wanda zai iya amsa maki wadannan tambayoyi
naki face ita kanta.
Kafin wani daga cikin abokan tafiyar ya kara
cewa wani abu, sai boka Muzafar ya ce in son
duk wnada yasan shi ba jarumi bane ya tsaya a
tsakiya, ku kuma jaruman ku rabu gida biyu,
kaso daya su tsaya a baya, dayan kason kuma su
tsaya a gaba.
307
TASKARNOVELS.COM.NG
Ba tare da wata gardama ba kuwa aka yi hakan,
ya zamana cewa Lumaira, Masnur, mahaifiyar
jarumi Imran sarkin Farisa da Sadauki Shaharan
suka tsaya a tsakiya, Sadauki Haiman da jaruma
Shadira suka tsaya a gabansu, Lumaira, Jarumi
Imran da Zarina uwa suka tsaya a can baya,
faruwar hakan keda wuya sai boka Muzafar da
gimbiya Rahila suka wuce kan gaba suka nufi
cikin dajin, bisa mamaki sai boka Muzafar yaga
sarki Lafaru shine ke biye da su, al'amarin daya
matukar bashi mamaki kenan ya juyo ya
dubeshi gami da cewa ya kai abokina hin ka
manta cewa yanzu kai ba Sadauki ba ne?
Da jin wannan tambaya sai Lafaru ya jinjina kai
ya ce kawai gani nayi duk inda na tsaya walau a
tsakiya, gaba ko baya ban isa na gujewa
kaddarata ba, fatana kawai shine mu samu
nasarar abinda muka fito nema... Kafin Lafaru ya
gama rufe bakinsa sai kawai yaga sun shigo
cikin wani mugun daji mai matukar kwarjini da
ban tsoro, wasu irin dogayen bishiyune a cikin
dajin masu kahonnin, a jikin kahonnin akwai
kwarangal din kawunan bil'adama wadanda
daka gansu kasan sun dade a sagale tsawon
shekaru, domin har yana ta lullube wasunsu, a
kasa kwarangalolin ne birjit babu adadi, ta
308
TASKARNOVELS.COM.NG
kansu suka rika bi suna wucewa, da zarar sun
takasu sai dai kaji suna kakkaryewa da rgujewa.
Ganin wannan kwarangalolin ne yasa su Masnur
suka firgita ainun jikinsu ya kama kyarma,
tabbas inda zasu ji wani kwakkwaran motsi da
nan take zasu saki fitsari ko sun runtuma da
gudu, wani abun mamaki shine Lumaira da ta
kasance makauniya bata firgita ba kamar yadda
sauran suka firgita, kawai sai ta ci gaba da
dogara sandarta tana mai laluben hanya, kuma
tana amfanin da sautin sawun wadanda ke
gabanta, sai da su boka Muzafar suka yi tafiyar
sa'a daya da rabi cif sannan suka iso tsakiyar
wannan daji mai ban tsoro, ba su hadu da komai
ba kuma basu ji motsin komai ba koda kuwa
kukan tsuntsu ne, kwatsam! Suna cikin tafiya sai
suka ga wani abu kamar hayaki bakikkirin ya
cika sararin samaniya kamar hadarine ya
gangamo. Cikin razani kowa ya tsaya cak,
jaruman suka daga makamansu suka tsaya suna
jiran abinda zai biyo baya, kawai sai suka ga
wannan bakin hayaki ya rikide ya koma siffofin
wasu aljanu ababen firgitarwa, nan fa suka
ringa durowa daga sararin samaniya. Aljanun
suna da kawuna irin na birrai, kuma munana ne
basu da kyan gani, gangar jikinsu kuwa siffar
309
TASKARNOVELS.COM.NG
batoyi gareta, suna da kafafu da hannaye guda
shida-shida, a jikin kowanne hannu da kafa
akwai yatsu guda arba'in kuma kowanne dan
yartsa yana dauke da farce mai tsananin kaifi da
tsini tamkar adda sabuwar washi, ko dutse suka
karta da faratan nasu sai dai kaga dutsen na
rabewa gida biyu.
Koda su Masnur suka yi arba da wadannan
dodanni sai suka yanke jiki suka fadi kasa a
sume, saboda tsananin gigicewa, Lumaira ce
kadai ta rage a tsaye itama sabida bata da
idanune amman inda taga wadannan dodanni
aljanun da babu abinda zai hanata sumewa.
Sadauki Haiman, jarumi Imran, Jaruma Shadira,
Gimbiya Zarina, da boka Muzafar kuwa sai suka
dubi junansu, cikin hadin baki suka kwarara
uban ihu sannna suka ruga cikin aljanun suka
hausu da sara gami da suka, amman sai suka ji
kamar duwatsu suke sara, domin jikin aljanun
ko kwarzanewa baya yi, duk sa'adda makaman
su Haiman suka hadu dana aljanun sai dai kaga
tartsatsin wuta yana tashi sama, al'amarin daya
dugunzuma hankalinsu kenan ainun
musamman ma d suka fara jaraba kkarfin
310
TASKARNOVELS.COM.NG
sihirinsu sukaga shima yaki yin tashiri akan
aljanun.
A daidai wannan lokacin ne aljanun suka fara
mayar da martani suka fara kaiwa jaruman sara
da faratan hannunsu domin su nakastasu, kuma
suna ki masu suka a fuska dan su lalata masu
idanu. Haka dai suka ci gaba da shawagi akan
mata suna son su suresu suyi sama da su. Koda
su boka Muzafar suka gane nufin aljanun sai
suka saka matan cikin a tsakiya aka ci gaba da
bakin artabun a haka, ya zamana cewa su boka
Muzafar sun kasa tarwatsa aljanun, haka suma
aljanun sun kasa illatasu balle har su samu
damar sure matan, ana cikin wannan gumurzun
ne wasu daga cikin aljanun masu naci suka
samu nasarar yakushin boka Muzafar da
gimbiya Zarina a hannu, nan take suka kwala
ihu kuma suka zube a kasa a lokacin da jiri ya
debesu.
Koda ganin haka sai wasu aljanun suka yunkuro
zasu yanyamesu domin su dada sassarasu, koda
Gimbiya Rahila ta fahimci abinda aljanun ke
nufin yi sai ta daka tsalle sama ta tarwatsa su da
karfin sarar takobinta, nan fa ta rinka
ragargazarsu cikin tsananin bajinta gami da
311
TASKARNOVELS.COM.NG
al'ajabi, domin tun a saman ta dinga katantanwa
da shawagi tamkar tsuntsuwa hakan yasa ta
addabi aljanun gaba dayansu, kuma ta hana
dayansu ya cutar da su boka Muzafar da ke
kwance a kasa.
Koda ganin wannan gagarumar bajinta da
gimbiya Rahila ke yi sai su sadauki Haiman suka
cika da tsananin mamaki, kuma suka samu
kwarin gwiywar kara zage damtse, nan fa aka ci
gaba da bakin gumurzu mai ban tsoro, ana cikin
haka ne Sadauki Shaharan ya dawo cikin
hayyacinsa ya lura cewa idan aka ci gaba da
wannan yaki a waje daya tabbas su Gimbiya
Rahila zasu gaji, in kuwa suka gaji to sai aljanun
sun samu nasara akansu, koda gama ayyana
haka a cikin ransa sai ya yunkura cikin tsananin
zafin nama ya suri yaro Masnur ya goyashi a
bayansa ya daure shi tamau, sannan ya falfala
da azababben gudunnan nasa, ai kuwa sai wasu
daga cikin aljanun suka rufa masa baya aka kasa
tsere. Nan fa aljanun suka ga abin al'ajabi iri
wanda basu taba gani ba, domin sunga
bil'adama wanda yafi aljani gudu, irin gudun da
Shaharan yake yi yafi gudun tauraruwa mai
wutsiya
312
TASKARNOVELS.COM.NG
.
.
.
Sai kawai suka tarwatse suka fada dajin suna
masu neman maboya, kafin kace kabo babu
kowa a gaban Gimbiya Rahila face aljanun dake
zube kasa nakasassu. Koda ganin haka sai
Gimbiya Rahila ta sunkuya ta sabi Shaharan ta
dirashi a bisa kafadarta ta wuce da shi izuwa
karshen dajin, inda ta kai su jaruma Shadira ta
ajiye.
Su boka Muzafar sun kwakkwance suna jinyar
raunikan jikinsu sai kawai suka hango gimbiya
Rahila ta tunkaro su dauke da sadauki Shaharan
akan kafadarta tana mai tafiyar kasaita tamkar
ta dauko buhun yayi. Da kyar cikin juriya suka
mike tsaye suka kura mata idanu cikin tsananin
mamaki har ta iso garesu, tana ajiye Shaharan a
kasa sai jaruma Shadira ta yi sauri ta zo kansa ta
fara sa mashi magani akan raunin nasa, nan take
jinin dake zuba a bayan nasa ya daina zuba.
Daman tun kafin Rahila ta zo da Shaharan duk
313
TASKARNOVELS.COM.NG
masu raunika an yi masu magani sun dawo cikin
hayyacinsu.
Bayan kamar dakika dari da sittin sai Shaharan
ya farfado, koda ya bude idanunsa sai ya budi
baki ya ce Ina dokina ya ke?"
Cikin fushi Gimbiya Rahila ta dubeshi ta ce da
shi yanzu kai baka damu da rayuwarka ba,
dokinka ne ma a ranka.
Shaharan ya ce ai dana rasa dokina gwara na
rasa rayuwata, tunda saboda shi na siyar da
rayuwata na taho wannan daji. Rufe bakin
Shaharan keda wuya sai ga aljani Marhabul
Zaurus a sama dauke da dokin Shaharan. Cikin
tsananin farin ciki Shaharan ya mike tsaye yana
kallon dokin nasa, aljani Marhabul Zaurus na
sauka kasa sai Shaharan ya ruga gareshi ya
rungume dokin nasa yana shafa wuyansa cikin
murna.
A sannan ne boka Muzafar ya dubi aljani
Marhabul Zaurus ya daka masa tsawa ya ce ina
ka tafi ne tunda muka fara gumurzu da
wadannan mugayen aljanu ban ganka ba?
314
TASKARNOVELS.COM.NG
Marhabul Zaurus ya risina cikin biyayya ya ce
Ya shugabana ka sani cewa idan na fusknaci
wadannan mugayen aljanu dukan falan daya
zasu yi mani na halaka, bisa Wannan dalili ne na
shiga kogon wata bishiya na saje da ita, ina
kallon duk abinda ke faruwa tsakaninku da
aljanun har saida naga jarumar jarumai, kuma
boyayyar basadaukiya ta ragargazasu ta kuma
dauki Shaharan ta tafi, sannan na fito daga cikin
kogon bishiyar kum na dauko dokin Shaharan
na taho nan.
Da jin wannan batu sai boka Muzafar ayi ajiyar
zuciya nan take yaji yayi nadama bisa
jagorantar wannan tafiya, domin a yanzu
zuciyarsa ta karaya, ya fahimci cewar abu ne
mayuyaci gabadayansu su iya tsallake
hatsarurrukan dake wannan daji, tunda gashi
tun kafin su shiga wadannan mugayen
dazuzzukan guda biyar sun raina jarumtakarsu,
kuma wacce ba a taba zaton zata yi wani abu ba
sai gashi ita ce ta fi kowa jarumtaka, kuma inba
dan taimakonta dana sadauki Shaharan ba da
sai kowa ya halaka.
Boka Muzafar ya kira gimbiya Rahila