x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - MAZAN JIYA 2

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 55701 words

Category: Romance Story +18

Views 195

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ya iske
amaryarsa zaune a gefen gado ta sha lullu6i
fuskarta a rufe.

Cikin matukar farin ciki ya karasa gareta
fuskarsa cike da murmushi ya kasa rufe baki.
Hantaru ya zAuna daf da Amaryarsa sannan
yasa hannayensa biyu ya yaye labulen da tayi.

93

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ya yi arba da fuskarta sai hankalinsa ya
dugunzuma ainun, ya dubeta cikin tsananin
mamaki ya ce, "Ya ke masoyiyata abar begena
dare da rana ina dalilin zubar Wannan hawaye
na idanunki? Ki sani cewa yau rana ce ta farin
ciki ba ta bakin ciki ba. Ina son ki gaya mini abin
da ke damunki ko mene ne shi in dai ina da ikon
kau da shi, sai na kawar da shi."

Sa'adda gimbiya Larziya taji wannan batu sai
tayi ajiyar zuciya tayi shiru kamar ba za ta ce
komai ba, daga can sai ta daga kai ta dubi
Hantaru ta ce, "Ya kai mijina hakika baka san
komai na ba domin baka san labarina ba kawai
ka zo garin nan ne a matsayin bako kana ganina
ka kamu da kaunata. Ina son na sanar da kai
cewa ina cikin wani bakin ciki tsawon shekaru
wanda duk duniyar nan babu wanda zai iya
kawar mini da shi face kai.

Ka saurari labarin da zan baka yanzu da kunnen
basira domin ka fahimci matsalar da kuma
babban burin da ke gabana." Sa'adda Larziya ta
94

TASKARNOVELS.COM.NG
zo nan a zancenta sai tayi shiru gami da ajiyar
zuciya sanann ta ci gaba da labari Kamar haka

"Mahaifina bai taba yin soyayya ba da wata ya
mace har ya hau karagar mulkin wannan birni
na Darul Mahabul kuma sai da ya shekara hudu
akan karaga bai yi aure ba. Al'amarin da ya dami
fadawansa kenan da sauran al'umman gari ke
nan suka dameshi akan batun lallai ya kamata
ya yi aure domin ya tsare mutuncinsa da
masarautar gaba ?aya.

Lokacin da mahaifina ya ga jama'a sun matsa
ainun akan wannan batu sai ya tara dukkan
jama'ar gari ya ce, "Idan har ana son ya yi aure
dole ne ayi abu biyu. Abu na farko dole ne a
samo masa kyakkyawar budurwa wacce babu
kamarta a gaba daya nahiyar kuma dole ne a
shirya gagarumar gasa irin wacce ko a tarihi ba
a taba yin kamarta ba". Sa'adda sarki ya gama
jawabi sai hankalin kowa ya dugunzuma aka
rasa wanda zai ce kala.

95

TASKARNOVELS.COM.NG
Daga can sai Wazirin sarki ya mike tsaye ya dubi
sarki ya ce, "Ya shugabana hakika ka zo mana da
baban al'amari wanda ba zamu iya saurin yanke
hukunci ba face ka bamu lokaci mu yi tunanin
mafita.

Dole ne mu nemi manyan bokayen kasar nan
domin su yi mana bincike bisa wannan
al'amari".

Koda jin haka sai sarki ya yi murmushi sannan
ya ce, "Ya kai waziri na baka wuka da nama
akan kaje ka zartar da komai amma ka sani
cewa kwana goma sha hudu kacal na baka".
Koda gama fadin haka sai sarki ya mike tsaye ya
shiga cikin gida, a sannan ne fadar ta watse
kowa ya kama gabansa.
Al'amarin Waziri kuwa, bayan ya bar fada sai ya
kira wadansu
manyan hadimansa amintattu guda hudu ya
basu wasika suka

96

TASKARNOVELS.COM.NG
yi hawa izuwa manyan garuruWan birnin guda
hudu akan su je su gaiyato manyan bokayen da
ake takama da su. Su kuwa bokayen da ake
takama da su a cikin birnin Darul Mahabul guda
biyu ne kawai wato boka Sulbaini da mahaifin
Rabbasu suma sai WAZiri ya kirasu ya sanar da
su cewa, "Ya tura a kirawo sauran bokaye kasar
guda hudu domin a ZAuna gaba daya a tattauna
akan matsalar sarki. Koda jin haka sai Sulbaini
da baban Rabbasu suka yi murmushi, Sulbaini
ya ce, "Ya kai waziri ai ka wahalar da kanka ne
kawai domin mu kadai mun isa mu fadi hanyar
da ZA a bi a warware matsalar sarki, to amma
masu iya magana sun ce ba a kwacewa yaro
garma kuma dan hakin da ka raina shi ke tsone
maka ido. Babu mamaki wani daga cikin
wadannan bokaye yazo da wani abin wanda
yafi namu don haka zamu jira isowar sauran
bokayen hudu" Sa'adda waziri yaji wannan
batu sai yai murmushi sannan yayi godiya ga su
boka Sulbaini ya sallamesu. Bayan kwana tara
daidai sai ga wadannan bokaye sun amsa kiran
Sarki. Da zuwan su sai waziri ya tara su a cikin
gidansa tare da su boka Sulbaini sannan ya yi
bayanin abin da yasa aka tara su kuma aka
bukaci kowannensu ya fadi tasa shawarar. Daya
97

TASKARNOVELS.COM.NG
bayan daya sai bokayen suka rinka nuna hoton
budurwar da sarki ya kamata ya aura da inda
take da kuma irin gasar da ya kamata ayi ta
neman aurenta, a cikin madubin tsafi. Ya yin da
bokan farko ya nuna tasa sai waziri ya kidime
domin gani yake kamar a duniya ma kaf ba za a
sami kamar ta ba, amma da boka na biyu ya
nuna tasa sai ya ta fi ta waccan nesa ba kusa ba.
Haka abin ya kasance bi da bi ta biyu ta fi ta
farko, ta uku ta fi ta biyu, kuma ta hudu ta fi ta
uku. Lokacin da aka zo kan baban Rabbasu sai
ya nuna wata kyakkyawar budurwa wacce ?uk
ta fi sauran kyau ya ce, "Wannan sunanta Zarifa
kuma yar wani babban attajiri ce a birnin Kisra,
tabbas a gaba dayan wannan nahiya babu mai
kyau kamarta a can birnin Kisran ma tana da
masoya da yawa 'ya'yan sarakai da 'ya'yan
manyan sarakai da ya'yan manyan attajirai da
kuma 'ya 'yan manyan bokaye. A halin yanzu an
rasa wanda za a baiwa ita daga cikin masoyan
nata, amma komai na hannun sarkin Kisra, shi
ake jira kawai ya yanke hukuncin akan ta. ldan
har sarki ya sami nasarar auro Zarifa za a
shirya gasar Jarumtama ta musamman a
tsakanin manyan mayaka domin Su debewa
jamaa kewa a lokacin da ake shagalin bikinsa.
98

TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da waziri ya ga Zarifa a cikin madubin
tsafin Baban Rabbasu kuma ya gama sauraron
jawabin Baban Rabbasu sai ya ude, kuma ya
cika da tsananin al'ajabi ya ce, "Na rantsed
darajar iyayena babu wata nahiya da za aje a
SAmi kyakkawar mace kamar wannan Zarifan,
don haka lallai zan kaiwa sarki labarinta domin
ya shirya da kansa yaje ya nemi aurenta a can
birnin na Kisra. Koda jin haka sai boka Sulbaini
ya bushe da dariya, al'amarin da ya matukar
baiwa kowa mamaki ke nan a wajen, aka yi tsit
ana kallonsa kawai. Daga can sai boka Sulbaini
ya tsuke bakinsa ya murtuke fuska sannan ya
nutsu ya dubi kowa daya bayan daya ya ce,
"Akwai wata budurwar wacce idan ba ta fi
Zarifa kyau ba sai dai su yi kunnen doki
sunanta Mafira, kuma 'yar uwar Zarifa ce uwa
daya uba daya suke, wato Hassana da Hussaina
ne amma ita Mafiran tun da aka haife ta bata
taba fita ba daga cikin gidansu domin dare da
rana babu abin da take so face ta Zauna a cikin
lambun gidansu tana kallon tsuntsaye da
kananan dabbobin daji. Idan ka ga ta fita daga
cikin wannan lambu sai idan lokacin barcinta
ya yi" Koda Sulbaini ya zo nan a ZAncensa sai ya
fiddo madubin tsafinsa ya ajiye a gabansu
99

TASKARNOVELS.COM.NG
waziri kuma ya shafeshi da hannun dama. Take
fuskar Mafira ta baiyana akan madubin da
kuma dukkan surar jikinta. Koda ganinta sai
waziri da sauran wadannan bokaye hudu suka
rude fiye da lokacin da suka ga Zarifa domin a
zahirin gaskiya Mafira ta fi Zarifa tsawo da
yalwal gashi. Boka Sulbaini ya ci gaba da bayani
ya ce, "ldan har sarkinmu ya sami nasarar auro
Mafira za shirya gasar kamo barewa tsakanin
zuri'ar makera da zuriar mafarauta na wannan
birni kamar yadda aka saba yi a kowacce
shekara domin a taya sarki murnar wannan
biki nasa. Da jin wannan batu sai waziri ya sake
rudewa ya rasa hukuncin da zai yanke akan
budurwar da sariki ya kamata ya zaba tsakanin
Zarifa da Mafira. Baban Rabbasu ya murtuke
fuskarsa zuciyarsa ta kama tafarfasa saboda
kishi da bakin ciki akan boka Sulbaini ya zo da
abin da ya zama kishiyar nasa. Lokacin da boka
Sulbaini ya ga baban Rabbasu na kumburekumbure da bata rai sai shima ya murtuke
fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa,
har ma jikinsa ya kama tsuma, al'amarin da ya
firgita waziri ke nan da sauran wadannan
bokaye hudu domin sun san cewa idan
wadannan hamshakan bokaye biyu suka
100

TASKARNOVELS.COM.NG
kacame da fada ba karamin bala'i ne zai faru ba,
wata kila ma sai gidan gaba daya ya rushe ko
kuma ya kama da wuta. Koda waziri ya fahimci
haka sai ya mike zumbur ya dubi boka Sulbaini
da Baban Rabbasu ya ce, "Yanzu ina son gobe da
safe ku hallara a fada, domin kowannenku ya
nunawa sarki fuskar budurwar da ya zaba masa
in ya so sai sarki ya Zabi wacce ya fi So da
kansa." Koda jin haka sai boka Sulbaini da boka
Zaharu suka mike tsaye suka tafi ko sallama
babu. Kashe gari kuwa da sassafe sai ga boka
Sulbaini da boka Zaharu a fada, sun hallara.
Bayan sun zube kasa gaban sarki sun kwashi
gaisuwa sai waziri ya maida bayani bisa duk
abin da ya faru jiya a gidansa tsakanin sa da su
boka Zaharu. Sa'adda Sarki ya ji wanann bata'u
sai ya cika da matukar farin ciki yai shiru yana
tunani har tsawon 'yan dakiku. Daga can sai ya
yi gyaran murya ya ce, "Ya ku wadannan
manyan bokaye na birnina abin takama a
gareni, ku yi sani cewa bana bukatar ku nuna
mini fuskokin wadannan yan mata guda biyu.
Abin da nake so da ku shi ne, ku yi shiri ni da ku
da waziri da kuma wasu tsirararun dakaruna za
mu yi tafiya izuwa birnin Kisra. Ina son
kowannenku ya yi amfani da iya karfin sihirinsa
101

TASKARNOVELS.COM.NG
domin na sami nasarar auro budurwar da ya
za6a mini. Duk wanda ya bani sa'ar dana auri
Zabinsa lallai zan yi masa kyauta ta musamman
kuma Zan bashi girma na musamman a cikin
masarautata. Ina so ku gane cewa a cikinku bani
da gwani ko abin so sai wanda kokarinsa ya sa
na auro budurwar da ya zaba mini. Da wannan
furuci nake sallamarku domin ku je gida ku yi
duk shirin da ya kamata. Lallai i yanzu ZA mu
kasance masu jiranku anan fada". Koda Sarki
ya gama wannan jawabi sai ya mike tsaye ya
shiga cikin gidan. A sannan ne boka Zaharu da
boka Sulbaini suka kalli juna cikin harara a
lokacin da idanuwansu suka kada suka yi jawur
kamar an gasa dan buda a wuta. Daga can sai
kowannensu jikinsu ya kama tsuma kamar za su
kaure da fada har wani irin tiririn hayaki ne ke
fita daga cikin kunnuwansu, baminsa da
hancinsu. Koda ganin wannan al'amari sai
hankalin gaba ?ayan jama'ar da ke fadar ya
dugunzuma aka fara mimewa ana ficewa da
sauri. Shi kuwa waziri sai yai sauri ya kama
hannun boka Sulbaini ya jashi suka fice daga
cikin fadar yana jansa da hira cikin lafazi mai
taushi domin ya sanyaya masa zuciya. Nan take
waziri ya sa aka kawo keken dokinsa suka shiga
102

TASKARNOVELS.COM.NG
ciki tare suka ZAuna sannan aka ja suka tafi. Sai
da waziri ya kai boka Sulbaini har kofar gidansa
yana tausar zuciyarsa akan kada ya daka ta
boka Zaharu su yi fada tun da idan suka yi fada
sai sun dagula hankalin kowa a garin kuma sai
kwanciyar hankali da zaman lafiya ya yi
karanci. Sa'adda boko Sulbaini ya ji wannan
batu sai ya yi murmushi ya ce, "Ya kai waziri
kayi sani cewa kiyayyar da ke tsakanina da
boka Zaharu ta gado ce domin tasowa muka yi
muka ga iyayenmu da kakanninmu na yinta. Ina
tabbatar maka da cewa har abada ba zamu
daina wannan gaba ba face dayanmu ya ga
bayan ?aya ko kuma idan mun yi RAGAS. Bugu
da kari ka sani cewa ni daga zuri'ar Makera na
fito shi kuwa daga zuri'ar mafarauta yake, gabar
da ke tsakanin wannan Zuri'a biyu ta fi shekara
dari ana yinta kuma har duniya ta nade ba za
daina ba. Ni kam zan yi iya kokarina na ga cewa
ba mu yi rigima ba ni da shi a cikin wannan
birni namu face idan ta kure babu yadda zan yi"
Nan dai Waziri ya yiwa boka Sulbaini sallama ya
tafi gida. A daren Wannan rana babu wani
mahaluki da ya yi barci a cikin birnin Darul
Mahabul saboda wata irin tsawa mai firgitarwa
aka rinka kwadawa a Sararin samaniya har
103

TASKARNOVELS.COM.NG
tartsatsin wuta yana zubowa kasa. Duk wata
dabba mai rai ko shuka idan wannan tartsatsin
wuta ya fado ma ta, nan take take konewa
kurmus. Duk wani mai tsautsayi da ya sake ya
fito waje kuwaa wannan dare sunansa gawa.
Kai ba ma mutane ba hatta Aljanun da ke ZAune
a birnin saida suka yi hijirar dole a wannan
dare suka bar cikin garin suka koma can nesa
da gari cikin dazuzzuka basu dawo ba sai da
gari ya waye. Ba komai ne ya haddasa duk
wannan bala'i ba face fishin da su boka Sulbaini
suka yi da juna. Wato a cikin daren ne suka
rinka aikawa junansu da masifu iri- iri amma
maimakon masifar ta sauka a kansu sai ta rinka
kwamarzuwa da yar uwarta a sama cikin
sararin samaniya tana zubowa kasa kan mai
uwa da wabi. Kashe gari kuwa da safe, Sarki,
Waziri da Dakarun rakiya mutum dubu biyu
suka yi hawa cikin shigar yaki mai kwarjini da
ban sha'awa Sannan aka tanaji guzuri mai yawa
bisa kan rakumi dari biyu sanann aka kimtsa
wadansu kuyangi guda goma wadanda za su yi
wa sarki hidima a cikin tafiyar. Sarki bai fito ba
daga cikin gida sai da boka Sulbaini da boka
Zaharu suka iso.
MAZAN JIYA Littafi na biyu
2 Part G Na Abdulaziz Sani m gini Typing
104

TASKARNOVELS.COM.NG
Abubakar Saleh AlQuyraemey Ciki na sani
kuma na zo ne domin na taimakeki na biya miki
bukatarki". Koda jin wannan batu sai mamaki
ya kama Zarifa kuma ta cika da dumbin farin
ciki. Ba tareda fargabar komai ba Zarifa ta
zauna daf da boka Ardusa ta kura masa idanu
tana mai sauraron abinda zai fada ma ta. Boka
Ardusa yai murmushi gami da gyaran murya
sannan ya ce, "Ya ke ma'abociyar
kyawu,tauraruwar kyawawa, ina son ki sani
cewa na san baki da wani buri wanda ya fi ki
daukaka a duniya fiye da dukkan sauran mata,
kuma kina son kimallaki dukiyar da babu mai
kamarta. Tabbas idan kika yi abubuwan da zan
umarceki sai bukatarki tabiya. Yanzu nazo
gareki a sirrance lallai ki rike sirrin kada ki
kuskura ki gayawa wani wannan sirri na
zuwana wajenki koda bukatarki ta biyane idan
kuwa kika fadi sai dan da za ki haifa yazamo?
sanadin ajalinki". Koda jin haka sai Zarifa ta ja
dogon numfashi ta ce,'Ai kuwa ba zan taba
gayawa wani wannan sirri ba". Boka Ardusa ya
ce,' Na san kin yi mamakin yadda aka yi na
kawo kaina wajenki, to amma ba abin mamaki
bane idan kika yi la'akari da matsayina a yanzu
na bokan da yafi dukkan bokayen duniyar nan
105

TASKARNOVELS.COM.NG
karfin sihiri, amma kuma ina daga cikin
talakawan bokayen. Yau shekarata ashirin da
biyar ina bauta a karkashin wannan masarauta
ta birnin Kisra kuma akwai alkawari mai nauyi
tsakanina da dangin su Sarki Kusaidu cewar ba
zan daina bauta a garesu ba sai bayan shekara
hamsin, kin ga ke nan a gaba akwai shekaru
ashirin da biyar. A ka'idar wannan alkawari ban
isa na yiwa wani aiki ba face su idankuwa na
kuskura na yiwa wani aiki mutuwa zan yi domin
an yi alkawarin ne a cikin sihirin tsafi bisa
amincewar mahaifina da mahaifin sarki
Kusaidu. Yanzu na zo wajenki ba aiki zan yi
miki ba kawai zan gaya miki abubuwan da za ki
yi ne a kanki domin bukatarki ta biya, ladana a
wajenki abubiyu ne rak. Abu na farko,bayan
bukatarki ta biya za kibani kanki na sanki 'ya
mace domin a rayuwata nayi alkawarin ba zan
ta6a kwanciya da wata 'yamace ba sai wadda
take da tsananin kyawu nagaban kwatance,
kuma wadda ta kasance 'yar attajirin da babu
kamarsa a wannan nahiya gabadaya,gashi kuma
na yi dace na sameki. dace na sameki. Ladana
na biyu shi ne, za ki raba dukiyarki gida biyu ki
bani rabi bayan mutuwar 'yar uwarki Marifa
domin a sannan ne za a baki gaba dayan
106

TASKARNOVELS.COM.NG
dukiyar da mahaifinki ya bari. ldan kin amince
da wannan sharadi yanzu take zan gaya miki
abubuwan da za ki yi ki samu cikar burinki.
Sa'adda boka Ardusa ya zo nan a zancensa sai
hankalin Zarifa ya dugunzuma ainun ta rasa
abin da ke ma ta dadi a duniya ta mike tsaye
dagakan gadonta ta kama kaikawo da tunani
bisa hukuncin da ya kamata ta yanke akan ta
yarda dashi. Abin da ya fara fado ma ta a rai shi
ne ya za ayi ta bayar da wannan kyakkyawan
jiki na ta ga boka Ardusa tsohon da ya kai sa'an
ubanta alhalin tana takama da tsananin kyawun
da babu mai tabata face babban Basarake ko
mashahurin attajiri. Abu na biyu da ya fado ma
ta a rai shi ne, yaza a yi ta raba wannan dukiya
ta ta mai tsananin yawa ta baiwa wani rabi,
wacce ta ishi mutum rayuwa a duniya koda zai
shekara dubu Lokacin da boka Ardusa ya ga
Zarifa ta shiga halin rudewa da wasi-wasi sai ya
mike tsaye yadubeta ya ce, "Wai shin kin manta
ne da abin da bokaye da dama suka gaya miki
cewa babu mai iya biya miki bukatarki face ni.
Idan zuciyarki bata gamsu da al'amarina ba shi
ke nan ni zan yi tafiyata na barki da wayonki".
Koda jin haka sai Zarifa ta yi sauri ta shagaban
boka Ardusa ta ce, "Ya kai wannan sakin
107

TASKARNOVELS.COM.NG
bokaye ka yi sani cewa jikina da dukiyata ba
abakin komai suke ba muddin zan sami biyan
bukata Lallai na amince da dukka wanann
sharadi naka don haka kayi sauri ka sanar da ni
abubuwanda zan yi domin bukata ta biya".
Koda jin haka sai boka Ardusa ya yi murmushi
ya ce, "Kafin nayi miki bayanin abubuwan da za
ki yi kuma kika yi su kika sami nasara sannan
daga baya kika yi min butulci, ma'ana kika ki
cika mini alkawari, lallai zaki mutu a cikin
kwanaki talatin cicif bayan yin aurenki. Haka
kuma dole ne ki ci gaba da bani kanki a duk
sa'adda na bukace ki, idan kuwa kikaki asirinki
zai tonu kuma ki rasa abin da kika samu a
rayuwa. Yanzu sai ki saurareni da kyau domin
kiji duk abubuwan da zan gaya miki wadanda za
kiyi su bukatarki ta biya. Abu na farko da za ki
yi shi ne, dole ne ki fada mini tambayoyi guda
uku wadanda mahaifinki ya fada miki ki
tambayi masu neman aurenki gami da
amsoshinsu domin nasanar da sarki Kusaidu su
ya sami damar aurenki.Kin ga idan kika auri
sarki Kusaidu za ki sami damar da babu wata
mace da ta samu a duniya domin shi ne sarkin
da a tarihi sarakan duniya babu masarautar da
ta fi tashi tsohon tarihi da daukaka da karfin
108

TASKARNOVELS.COM.NG
mulki. Duk sarkin da ya yi zamaninsa har bayan
shudewarsa ba a mancewada shi da matansa
domin har a fadar sarkin Aljanun duniya ana
rubuta tarihinsu a ajiye, atakaice dai sai sunanki
ya bazu ko ina a duniya kinga ke nan ko ta nan
kin yiwa 'yar uwarki Marifa fintinkau. Abu na
biyu da za ki yi shi ne, ki samo kasko i yi fitsaria
cikinsa sannan ki diga digon jininki a ciki, sai ki
kira sunan 'yar uwarki sau uku ki tofa a ciki
sannan ki wanke idanunki da shi amma a ranar
da za a yi gasar neman aurenku. Dazarar 'yar
uwarki Marifa ta hada idanu da ke awannan
rana ba za ta yi wata goma sha uku ba aduniya
za ta mutu, idan kuwa baki hada idanu daita ba
to kece za ki mutu a cikin wata goma sha ukun.
Wannan shi ne iyakar abin da za ki yi. dukkan
burinki ya cika..Da wannan furuci nake miki
sallama sai mun hadu a ranar gasa." Kafin
Zarifa ta bude baki ta ce wani abu tuni boka
Ardusa ya yi girgiza ya bace 6at. Al'amarinda ya
matukar baiwa Zarifa mamaki ke anan domin
ya tafi ba tare da ta fada masa wannan
tambayoyi uku ba, wadanda zai sanar da sarki
Kusaidu gamida amsoshinsu. Zarifa ta koma
kan gadonta
End Ads