x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 16 - MAZAN JIYA 2

  • 45001 words
  • 48000 words
  • Out of 55701 words

Category: Romance Story +18

Views 202

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
zakin
dawa, kaine fasa taro tarwatsa runduna, komai
yawan runduna indai kaizo kai zaka zama
Gwarzo.

262

TASKARNOVELS.COM.NG
Da shigar su sarki Lafaru sai sadauki Haiman ya
mike cike da farin ciki ya ruga wajen boka
Muzafar suka rungume juna sannan ya kama
hannunsa ya kaine har kan karagarsa suka
zauna.
Nan da nan kuyangi suka kawo wa Sarki Lafaru
abinci da abin sha iri-iri na alfarma suka kimtsa
cikinsu. A wannan lokaci duk bayan dakika biyu
sai gimbiya rahila da Sarki Lafaru sunyi satar
kallon Lumaira matar Sadauki Haiman saboda
mamakin tsananin irin kyawunta. Koda satki
Lafaru ya kwatanta kyawun sharlis dana
Lumaira sai yaga kamar baki da fari ya hada
wato Lumaira ta yi wa sharlis fintin kau, nan fa
Sarki Lafaru ya shiga zancen zuci yana mai cewa
Yanzu n bbanda rashin godiya irin na Sadauki
Haiman akan me zai damu dole sai ya nemo wa
Lumaira maganin wannan ciwo na makanta
tata, dubi irin daular da yake ciki, sannan duk da
cewa makauniya ce tafi masu idanun kyau gami
da ban sha'awa, gata bulbul kamar tsada, ya za a
yi ina matsayinta na yarda har wani abu ya
dinga sosa mani zuciya a wannan duniya.

263

TASKARNOVELS.COM.NG
Ita gimbiya Rahila irin wannan tunani sak ta yi a
cikin Zuciyarta, tamkar sun hada baki ita da
sarki Lafaru.
Bayan anci abinci an gyatsene sai Sadauki
Haiman ya dubi boka Muzafar ya ce Mene ne
abin yi?
Boka Muzafar ya ce ku muke jira kugama shiri
mu cigaba da tafiya, da jin haka sai Sadauki
Haiman yayi murmushi ya ce Ai mu yau
kwananmu ashirin da gama shiryawa, daman ku
kawai muke jira ku iso.
Gama fadin hakan keda wuya sai Haiman ya
mike tsaye ya kama hannun Lumaira wacce ke
zaune daf da shi ya tasheta tsaye suk nufi
hanyar fita. Cikin hanzari kuyangi suka debo
wasu jakunkuna guda biyu na guziri suka bisu a
baya.
Sarki Lafaru, Gimbiya Rahila da boka Muzafar
basu tsaya bata lokaci ba suma suka bi bayansu,
gabadayansu suka dunguma izuwa inda suka
bar aljani Marhabul Zaurus suka hau kansa suka
zazzauna, amman sai gasji kamar bai dauki
komai ba saboda fadin gadin bayansa da kuma
girman halittar jikinsa.
264

TASKARNOVELS.COM.NG
Nan take boka Muzafar ya dubi aljani Marhabul
Zaurus ya ce maza ka kaimu gidan jaruma
Shadira ta birnin Baitul Haiward, kafin boka
Muzafar ya gama rufe bakinsa tuni aljani
Marhabul Zaurus ya bude fuka-fukansa ya
luluka sama. Tafiyar sa'a uku kacal yayi ya iso
birnin Baitul Haiward ya sauka a kofar gidan
jaruma Shadira. Cikin hanzari suma suka sakko
daga aljani Marhabul Zaurus, gabadayansu sai
suka yi cirko-cirko suka rasa abinda za su yi
domin kofar gidan a rufe take fam kuma babu
masu gadi, shidai wannan gida na jaruma
Shadira yana da girma sosai harma ya ninka
gidan Sadauki Haiman sau biyu amman wani
abun mamaki shine ko kadan ba a kawata gidan
ba. Boka muzafar ya karasa ya kwankwasa
gidan har sau uku bai ji an amsa ba, kuma ba a
bude kofar ba. Kawai sai yayi amfani da
sihirinsa domin ya bude kofar, amman sai kofar
taki budewa al'amarin da ya baiwa dukkaninsu
mamaki kenan. Koda ganin haka sai Boka
Muzafar ya ja da baya ya rugo a fusace ya naushi
kofar da dukkan karfinsa kamat yadda yayi wa
kofar birnin su gimbiya Rahila, kawai sai ya ji
kamar dutse ya nausa domin ko motsi kofar
bata yi ba. Shima Sadauki Haiman sai ya jaraba
265

TASKARNOVELS.COM.NG
tasa Sadaukantakar ya sari kofar da
rantsatssiyar takobinsa, take tartsatsin wuta ya
tashi amman ko kwarzanewa kofar bata yi ba.
Ba zato a ba tsammani sai kawai suka ga wani
yaro wanda bai fi shekara tara ba ya bayyana
tsulum a gabansu yana murmushi, kawai sai
yaron yasa yatsansa guda ya tura kofar, take
kofar ta bude wanwar yaron ya shige cike yana
mai yafitosu da hannu cewar su biyo shi a baya.
Saboda tsananin mamakin yadda yaron ya iya
bude kofar sai dukkaninsu suka kasa shiga cikin
gidan har sai da suka ji muryar jaruma Shadira
tna mai kyalkkyala masu dariya sannan suk
shiga ikin gidan.
Da shigarsu cikin farfajiyar gidan sai suk yi arba
da jaruma Shadira a tsaye ta rataye wata katuwr
baka a bayanta, da wani katon kwanson kibiyoyi
wanda a cikinsa akwai kibiyoyi dubu biyu.
Koda Lumaira ta yi arba da Shadira sai ta kura
mata idanu cikin tsananin mamaki, su sarki
Lafaru kuwa basu san sa'adda da suka wangame
baki ba suna al'ajabi, ba komai ne ya haddasa
hakan ba face yadda Lumaira da Shadira suka yi
kunnen doki a tsakanin kyau. Komai na halittar
266

TASKARNOVELS.COM.NG
jikinsu ya zo iri daya, abinda ya banbanta su
kawai shine kamannin fuskokinsu, amman
komai iya kallon kurillar mutum da iya
banbance al'amura bai isa ya tantance wacce
tafi wata kyau ba. Nan take kishi ya kama
Shadira bisa ganin kyakkyawa kamarta.
Shiko sadauki Haiman da yaga irin kyawun
shadira kuma yaga cewa tana da idanu bata
kasance makauniya kamar matarsa Lumaira ba,
sai ta ayyana a ransa cewa inama ace duk matan
nan biyu nawa ne, ai da babu sauran damuwa a
tare da ni a wannan duniya.
Cikin karfin hali Shadira ta taho wajen boka
Muzafar ta ce Lale marhabun da abokin tafiya, ai
na dade da gama kimtsawa ina jiranku yanzu
kawai tafiya ta rage mana.
Boka Muzafar yayi murmushi ya ce Nasan da
haka ya ma'abociyar kibiya, ina fatan kin tanadi
dukkanin guzurinki?
Jaruma Shadira ta juya da dubi dn uwanta
Masnur cikin tsananin farin ciki sannan ta bude
hannayenta ta durkusa bisa gwiywoyinta ta ce
ta ho mu tafi ya kai dan uwana lokacin yanke
bakin cikinmu yayi.
267

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai Masnur ya rugo da
gudu zuwa kan Shadira ya fada kan kirjinta suka
rungume juna.
Ba tare da bata lokaci ba sum suka debi
guzurinsu suka bi wannan tawaga aka wuce
zuwa birnin Istin gidan Jarumi Imran Ibn
Shuhairu. Da saukar su boka Muzafar a tsakiyar
gidan su Imran sai suka iske shi a zaune a gaban
mahaifiyarsa wacce ta kasance tsohuwa tukuf
yana bata abinci a baka da hannunsa saboda
tsufa, da kyar ma take iya hadiye abincin, wani
lokacin ma sai ta furzo da abincin waje ya bata
wa Imran fuska tamkar ta kasance jaririya
amman ko damuwa Imran bayayi sai dai kawai
ya goge fuskarsa, itama ya goge mata baki
sannan ya ci gaba da bata abincin. Duk da cewa
jarumi lmran yaga zuwan su boka Muzafar
kuma yayi murna da ganinsu, amman bai
sauraresu ba sai da ya tabbatar da cewa
mahaifiyarsa ta koshi da wannan abinci, sannan
ya dauketa ya goyata a bayansa sannan ya dauki
wata kyakkyawar sanda ya jingina a jikin bango,
ya dubi boka Muzafar ya ce Lale marhabun ya
kai wannan babban boka tare da abokan tafiya,
yanzu sai mu wuce gaba ko domin bani da wani
268

TASKARNOVELS.COM.NG
sauran shiri na gama, daman ku kawai nake
sauraro.
Nan take boka Muzafar ya mika wa jarumi
Imran hannu suka gaisa ya cw Gaisheka
ma'abocin kyautat wa mahaifiyarsa, hakika kai
din abin jinjinawa ne, taho mu kara gaba. Koda
gama fadin haka sai boka Muzafar ya juya ya
nufi inda aljani Marhabul Zaurus yake tsaye
yana jiransu, kowa kuma sai ya bi bayansu
?uww. Jarumi Imran ne a karshe goye da
mahaufiyarsa kwance a gadon bayansa wacce
take cikin dimbin farin ciki, bisa ganin cewa yau
ne zasu tafi neman maganin larurarta, babban
abinda ya daure wa Lumaira da Shadira kai
shine, tunda suka shigo cikin gidan Jarumi
Imran ko kallon daya daga cikinsu bai yi ba balle
ma har tsananin kyawunsu ya burgeshi. Kuma a
koyaushe hankalinsa na kan mahifiyarsa, ko tari
yaji ta yi sai ya tambayeta ko tana da wata
bukata? Su kansu su sadauki Haiman suna
mamakin jarumi Imran a zukatansu suna masu
cewa shiko wannan jarumi wane irin mutum ne
haka, wnada bai damu da komai a duniya ba
face mahaufiyarsa, wacce ko kuda baya son yaga
ya sauka a jikinta, gashi kuma mahaifiyar tasa ta
tsufa tukuf, a koyaushe ma lokaci zai iya yin
269

TASKARNOVELS.COM.NG
halinsa, abinda basu sani ba shine, jarumu
Imran yayi alkawari a zuciyarsa cewa har abada
bazai saurari aure ba, kuma bazai nemi muli ko
dukiya ba face yaga mahaifiyarsa ta samu lafiya
kafafunta sun mike har ta iya takasu, idan kuwa
bata samu lafiya ba har salar da ajalinta ya
risketa, to shima har nasa ajalin ya zo ba zai
nemo komai a duniya ba face abincin da zai ci
dan ya rayu. A kullum idan jarumi Imran ya dubi
mahaufiyarsa yaga yadda kafafuwanta suke a
kanannade sai ya fashe da matsanancin kuka ba
zai daina ba har sai ta rarrasheshi da kanta ta
kuma kwantar masa da hankali, ba wani abu
bane yasa jarumi Imran yake matukar son
mahaifiyarsa ba illa cewa ta sha matukar wahala
akansa, tun daga lokacin da ta haifeshi
kasancewarsa maraya domin ubnsa ya mutu, to
sai ta tafi dashi izuwa gidan mijinta ya zama
agola.
Sun sha matukar wahala a wannan gidan mijin
nata a hannun yayan mijinta kafin daga bisani
mijin ya rasu, kuma a lokacin ne yayan mijin
suka sake ninka tsanar da suka yi wa jarumi
Imran da mahaifiyarsa, har ya zamana cewa
basu yarda an raba gadon mahaifinsu da
mahaifiyar Imran ba, da kyar ma suka yarda
270

TASKARNOVELS.COM.NG
suka zauna a cikin dakin kiwon dokin mai gidan.
Da yake a wannan lokacin Imran yana yaro
karami ba zai iya yi wa kansa komai ba, balle
har yayi wa mahaifiyar tasa, ita take fita da jan
ciki taje tayi aikatau a makota sannan ta samo
masu abincin da zasu ci ira da danta da kyar, su
kuwa wadannan yayan miji nata kullum suna
bushasha da abinda mahaifinsu ya mutu ya bar
masu gado, ko loma daya ta abinci basa ba
Imran da mahaifiyarsa. Sau bakwai yayan mijin
suna yi wa Imran dukan tsiya, kuma dukan ma
na kawo wuka, wani lokacin ma sai au dauke shi
su jefashi cikin rijiya ko kogi domin ya mutu
suna yin haka ne dan su cusa wa mahaifiyarsa
bakin ciki dan hakan yayi sanadiyyar ajalinta,
amman da yake Jarumi Imran na da tsawon rai
bai mutu ba, kuma a duk sa'adda uka jefashi a
cikin rijiyar ko kogi da yake mahaifiyar tasa ta
iya ruwa kuma a lokacin da take budurwa tana
da yar jarumtaka, idan sun jefashi mahaifiyar
tashi ce take zuwa da jan ciki ta fada cikin rijiyar
ko kogin ta lalubo shi ta fito da shi tana kuka ta
ci gaba da jinyarsa har ya samu lafiya.
Lokacin da mahaifiyar Imran ta fuskanci cewa
idan ta ci gaba da zama gidan wannan
Marigayin miji nata tofa lalla? wata rana
271

TASKARNOVELS.COM.NG
wadannan yaya nasa zasu samu nasarar hallaka
mata da, sai wata rana da daddare ana tsala
ruwan sama da walkiya suka saci jiki tare da
ficewa daga cikin gida, gashi mahaifiyar Imran
bata da kafafu da jan ciki take tafiya, kuma gashi
dan yayi yaro ba zai iya daukarta ba, saboda
haka lokacin da yaga tana jan ciki tana tafiya da
kyar kuma ruwa na dukanta, sai ya kamu da
tsananin tausayinta har ya fashe da kuka, a haka
dai suka samu da kyar da shidin goshi suka yi
nisa a cikin daji suka shiga cikin wani kogon
dutse suka fake.
Daga wannan rana suka cigaba da rayuwa a
cikin wannan kogon dutse, ya zamana cwa
mahaifiyar Imran tana kula da shi matuka, da
jan ciki take zuwa farauta ta samo masu abincin
da zasu ci, duk da cewa dajin da suke ciki akwai
mugayen dabbobin daji da kuma kwari kamar
macizai kunamu da sauransu, amman duk da
haka duk abinda taga zai cutar da danta tofa sai
inda karfinta ya kare, akwai wata rana da wata
kura mai fama da jin yunwa ta shigo cikin kogon
da suke, a wannan lokaci Imran na kwance
yanata sharar bacci abinsa, baima san cewa
kurar ta shigo ba. Ita kuwa mahaifiyarsa tana
can cikin wani loko a kogon, kai tsaye kurar ta
272

TASKARNOVELS.COM.NG
nufi inda Imran yake kwance da nufin cinye shi.
Koda mahaifiyar ta hango wannan kura ta nufi
inda danta yake, sai ta ji dukkan wani tsoro da
fargaba ya kau daga cikin zuciyata, cikin zafin
nama ta yi adungure sau uku sai gata a gaban
kurar. Ai kuwa sai kurar ta fada kanta suka
kacame da fada, kacaniyar da suke yi ne
tsakanin wannan kura mai jin yunwa da
mahaifiyar Imran ce tasa ya farka daga baccin
da yake yi, ko da yaga kura ta turmushe
mahaifiyarsa ta yagalgala mata jiki, sai ya rusa
ihu ya dauki ice tare da nufar kurar, wannan ihu
da Imran yayi ne yasa kurar ta daga
mahaifiyarsa da sauri. Koda ta ganshi rike da
wannan icce sai ta fara ja da baya-baya har taje
bakin kofar kogon ta tsaya.
Haka aka ci gaba da kallon kallo tsakaninta da
Imran, abinda ya daure wa kurar kai shine,
yadda Imran ya kasa jin tsoronta har ya taso zai
yaketa domin ya ceci rayuwar mahaifiyarsa
alhalin yana karamin yaro ba zai iya cutar da
kurar ba, gashi dai kurar a yunwace take
matuka, tana ta dalalar da yawu kuma ga
kanshin jini tana ji a jikin mahaifiyar Imran
wacce take kwance magashiyan, kuma ba zata
iya kare kanta daga komai ba, wank iko na Allah
273

TASKARNOVELS.COM.NG
sai kurar nan ta kasa afka wa mahaifiyar Imran.
Kawai sai ta juya ta fice daga cikin kogon, a
sannan ne Imran ya juya ya ruga wurin
mahaifiyar tasa yana mai fashewa da kuka, a
lokacin da take numfashi sama-sama tamkar
zata mutu sakamakon jinin dake zuba a sassan
jikinta.
Imran ya dimauce ya rasa irin agajin da zai
baiwa Mahaifiyarsa, da kyar mahaifiyar tasa ta
iya bude baki ta fada masa yadda zai ceci
rayuwarta, ta fada mashi cewa yaje ya tsunko
wani ganye ya daka shi sannan ya shafe mata
akan raunin jikinta.
Nan take kuwa ya cika wannan umarni, yana
shafa mata jini ya daina zuba a jikinta. Sai da
Imran ya kwana arba'in yana jinyar
Mahaifiyarsa a cikin wannan kogo, da baki ta
rika koya masa yadda zai je ya samo masu
abinci, wanann icce wanda ya kori kura da shi,
shine ya zama masa makami, ya dinga buge
kananan dabbobi suna mutuwa, sai kuma ya
jasu da kyar ya kai cikin kogon da suke a
matsayin abincin da zasu ci. Daga sannan ne fa
zuciyarsa ta bushe kuma ta kekeshe ga barin
tsoron komai a dajin, kuma kullum sai ya dauki
274

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan icce yayita sarrafa shi, kamar yadda ake
sarrafa takobi dan koya wa kansa yaki.
Ance sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje
ba, hak dai Imran da mahaifiyarsa suka ci gaba
da rayuwa a wannan daji, har ya girma ya zama
gagarumin sadauki, kuma jarumi mai ban
al'ajabi, ya zamana cewa indai yana rike da
sanda komai yawan mugayen dabbobin daji sai
ya tarwatsasu ya kashe na kashewq wasu kuma
su gudu. Kai sai da takai cewa gabadaya
mugayen dabbobin daji suna tsoron Imran, bisa
dole sukayi hijira su da yayansu suka bar inda
suke. A wannan lokacin ne mafarautan da suke
zuwa farauta wannan daji suka ankara da Imran
har suka kai labarinsa wajen sarki, musamman
sarki ya taka da kafarsa ya ziyarci Imran da
mahaifiyarsa. Sarki yayi matukar mamaki yadda
har suka rayu a wannan mugun daji mai
tsananin hadari, a dalilin haka ne sarki ya
shawarci Imran da ya zama daya daga cikin
dakarunsa, idan har ya amince da haka to zau
basu gida a cikin gari, gami da dukiya mai tarin
yawa.
Cikin farin ciki Imran da mahaifiyarsa suka
karbi wannan tayi da yayi masu, haka suka bar
275

TASKARNOVELS.COM.NG
daji suk koma cikin gari suna masu fuskantar
sabuwar rayuwa.
Yakin farko da jarumi imran ya fita ya nuna
matukar jarumtaka ta ban al'ajabi, wacce ba a
taba yin kamarta ba a tarihin nahiyar gabadaya,
domin shi kadai ya yaki dakaru dubu saba'in da
sanda, ba da takobi ko mashi ba, ya kashe fiye
da rabinsu yayin da sauran suka ga haka sai
suka tsere.
Tun daga wannan rana sarki ya daukaka Imran
a fadarsa, kuma ta bashi sarautar sarkin
yakinsa, ya zamana cewa sun samu daula mai
yawa. Wata rana shi da mahaifiyarsa suna zaune
sai kawai yaga ta kura masa idanu hawaye na
zuba daga cikin idanunta.
Nan take hankalinsa ya tashi ya ce, Ya ke
ummina ina dalilin wannan kuka naki?
Koda jin wannan tambaya sai ta yi ajiyar zuciya
ta ce Ya kai dana ka yi sani cewa ba komai ne
yasa na zubar da hawaye ba illa tsananin
takaicin zuwan ranar da zaka yi aure bani da
ikon da zan mike da kaffuna na taka rawa dan
tayak farin ciki, haka kuma gashi tsufa ya
276

TASKARNOVELS.COM.NG
riskeni, abune mawuyaci ma naga ranar
aurenka.
Koda jin wannan batu sai imran ya fashe da
kuka sannan ya rungume mahaifiyarsa a
kirjinsa yana mai cewa yake ummina lallai ba
zaki mutu ba sai kinga aurena, kuma duk inda
zan tafi neman magani bisa wannan lalura taki
sai na nemoshi kin warke.
Da jin wannan batu sai tausayin dan nata ya
kamata ta ce kada ka wahalar da kanka ya dana
domin mahaifinka ma akan neman maganina ya
rasa tasa rayuwar, bokaye sun tabbatar da cewa
bazan taba warkewa ba, face na wanke kafafuna
da ruwan albarka na cikin kogon darul ikisina,
daga nan zuwa kogon darul ikisina tafuya ce ta
shekara da shekaru, kuma akwai mugayen
dazuzzuka har guda biyar kafin a isa kogon
darul ikisina. Fiye da shekaru dubu biyu babu
wani mahaluki daya ratsa ta cikin wadannan
dazuzzuka ya isa kogon darul ikisina a raye.
Saboda tsananin son da mahaifinka yake mani
ne yasa ya saci jiki ba tare da na sani ba, ya nemi
taimako a wajen bokaye, ya tafi zuwa kogon
darul ikisina omin samo mani magani wannan
cuta tawa, sai wasikarsa kawai na smu akan
277

TASKARNOVELS.COM.NG
gado a cikin dakina, yana mai bar mani bayani
akan cewa Shifa ya tafi kogon darul ikisina
domin nemo mani magani, ammn bashi d
tabbacin zai yi nasara ya dawo a raye har mu
sake saduwa, wasiyyarsa a gareni shine na kula
da duk abinda zai haifa walau mace ko namiji,
kuma na sallama rayuwata domin kare abinda
zan haifa, saboda fatan sa anan gaba idan dana
ko yata suka girma n basu labarin irin tsananin
soyayyar dake tsakaninmu, har yau har gobe
tunda mahaifinka ya tafi kogon darul ikisina ban
sake jin duriyarsa, a duk sa'adda na bude
akwatunsa naga irin suturunsa sai na fashe da
matsanancin kuka wannan shine alilin da yasa
na sallama rayuwata dan kare taka tun kana
yaro karami, domin na cika wasiyyar umarnin
mijina.
Lokacin da mahaifiyar Imran ta gama bashi
wannan labari, sai ya sake fashewa da kuka ya
kankameta a kirjinsa yana mai cewa Ya ke
ummina kiyi sani cewa son da nakemaki a
yanzu ya ninka wanda mahaifina ke maki sau
dubu, sabida haka ina tabbatar maki da cewa
omai dadewa sai n ida abinda mahaifina ya
kasa, lallai nine zan samo maki maganin cutarki
acan kogon darul ikisina, tabbas mutuwa ba
278

TASKARNOVELS.COM.NG
zata rabamu ba face naga ranar da kika mike
tsaye kika taka da kafafunki kika cashe rawa a
ranar bikin aurena. Daga yau nayi al?awarin ba
zanyi soyayya ba kuma ba zanyi aure ba har sai
na samo maki wannan magani, kuma ba zan
nemi mulki ko dukiya ba.
Wannan shine abinda ya faru a shekarun baya
tsakanin jarumi Imran da mahaifiyarsa.
Ba tare da bata lokaci ba Imran ya goya
mahaifiyarsa a bayansa, sannan ya dauki jakar
guzurinsa suka dunguma shi da su boka
Muzafar suka je suka haye bayan aljnai
Marhabul Zaurus, shi kuma ya tashi da su sama
suk ci gaba da tafiya suka durfafi birnin Farisa
dan zuwa gidan gimbiya Zarina.
Tunda aka fara wannan tafiya ya zama cewa
hankalin jarumi Imran akan mahaifiyarsa yake
baya ci ko shan komai face yga ta koshi, haka
kuma baya iya yin bacci a duk sa'ad da take
bacci sai dai ya sata a gaba ya rinka kallonta
yana kuma gadinta har sai ta farka daga baccin
sannan shima yayi nas, kai ko tari tayi sai ya
tambayeta tana bukatar wani abu ne? Ganin
yadda jarumi Imran ya damu ainun da
279

TASKARNOVELS.COM.NG
mahaifiyarsa yasa jaruma Shadira taji ya
burgeta, aiko bata ankara ba ta ji ta kamu da
tsananin kaunarsa, don haka sai ta rinka yawan
satar kallonsa. Shiko da ya lura da halin da take
ciki sai ya daure fuska a gare ta, al'amarin da ya
matukar tayar mata da hankali kenan, ta rasa
abinda ke mata dadi a duniya, domin bata taba
yin soyayya ba, amman yanzu ga
End Ads